Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuka tace "Ahh kai ke da Sannu" be kulata ba ta tashi dauko Magani don ta zan silar zuwan kenan, Ganin haka Nasiba ta matsa kusa dashi tace "Hamma ka ci abinci?" kamar ba zai amsa ba yace "i am not hungry" ta marairaice tace "DonAllah in dafa maka ko Indomie ce?" shiru yayi kamar be ji ta ba, har ta cire rai zai amsata ta mike don komawa mazaunin ta, cikiciki taji yace "Ki dafa min" Da sauri ta juyi da murmushi dauke kan fuskar ta, daure wa yayi kamar ba shi yayi maganar ba, da sauri ta zura Hijab ta bude jakkar School dinta, yana kallonta, sai da tayi hanyaf fita ta tsinkayi muryar shi yace "Ina zaki" tace "Shagon Ummu Sudais zanje in siyo Indomie din" (GWS Ummu Sudais ILY). Guntun tsaki yayi ya mik'e ya zura takalman shi ya fita daidai ita yace "Ki barshi" tace "Hamma-" katse ta yayi ta hanyar daga hannu yace nace "ki barshi ko? Koma ciki" ba musu ta dawo ciki amma ranta ya baci, to meye abun daga murya? Nene ta fito da Goran Maganin a hannunta tace "Ina Dunkum din?" Seebi ta ta6e baki tace "ya tafi" Nene ta daga murya tace "Kika barshi ya fita?" Seebi cike da takaici tace "rike shi zanyi ince ya dawo? Nene tace "ke tamabyar ki nayi bace miki nayi ki zagar min uwa ba" Seebi dai ba ta sake magana ba ta shige Daki.

Chan sai ga Rafeeq ya shigo da Carton din Indomie da crates din k'wai guda biyu, Nasiba na ganin shi tayi saurin tashi ta tarye shi don ta ga yanda yake tafia kamar zai kife, tace "Hamma you dont have to do that" hararar ta yayi yace "jeki dafa min, i am hungry" wani dadi taji ya lullube ta da sauri ta aje kwalin gaban Nene, Nene ta kalli Rafeeq tace "Sannu fa" wani murmushi ya kubce mai, wai shi take koyo, wannan tsohuwar is full of wonders.
_Bayan Minti 15_
Gaban shi ta dire Indomie din da aka dafa da ruwan Magani da fried Egg, kamshin ya cika mai hanci, tuni ya fara Salivating, Ba wasa ya hau cin indomie din yana jin dadi, Nene ta ta6e baki tace "kadifiri, a gama jin dadi a zo a kur6i magani" ai ko yana gama sha, ta zuba magani a cikin spoon tace "Kar6i" warin maganin ya daki hancin shi, ga shi ya ci k'wai haka kurum yaji amai ya taso mai, ya fara k'ak'arin amai, ganin yamutse yamutsen fuskan da yakeyi sai tayi zaton iyarshege ne, da sauri ta toshe hancin shi, kafin ya ankara ta mai dure, ta juye maganin a bakinshi, ta sa gudan hannubta ta damk'e bakin Rafeeq, gashi be nunfashi, be da zabin da ya wuce ya hadiye maganin, sai da yayi sakwan 15 kafin Nene ta sake shi, Nasiba ta kasa ce ma Nene komai don tasan yau akwai dirama, da gudu ta bulbulo mai ruwan Maganin shi ta mik'a ma Rafeeq, ba sanya ya kafa kai ya shanye ruwan, ya juyo ya na ma Nene wani irin kallo. Kunnenta ta kama da hannu biyu tace "Sori Gaye" Sosai ta bashi daria, kauda kai yayi lokaci daya ya murtuk'e fuska, chan kuma yace "kina da hayaniya, ki dinga yin abu a hankali" Nasiba ta bude baki, a zatonta Nene zata balbale shi da masifa, sai ta bata mamaki da cewa "Naji Dan gaye na, ga Farar ka tun rannan na ajiye maka" ta ciro Farar a gefen Tabarma da yake dare ne ba wanda ya lura dashi. Murmushi Rafeeq yayi wanda ya sa fuskar shi kyau Sosai ya sa hannu ya amsa tare da kallon Nene, Nene ta san me zai ce, a tare sukace "Sannu Fa" Nene da Nasiba suka sa daria, shi dai Murmushi kawai yayi. Nasiba tace a ranta "Finally these two are getting along. Lallai magani ya fara aiki so soon"
***********
Bayan Kwanaki Goma(10days later)

(Kuyi hakuri da page din nan, girman Alkawari ya sa nayi typing page din, Zan dasa daga nan gobe InshaAllah👻)

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

This page is for you my Everlasting Babe Miemee 👄Bee❣and My Coach Lubie Maitafsir❣ Aunty Sis and I love you two to the moon and back #1love.

Pg4⃣7⃣

"Oh shit! sorry Angel i didnt mean to shout at you" duk yayi wani iri kamar me shirin kuka, 6are baki ta sake yi, kamar ana k'wak'ule mata idanuwa, kuka Rafeeq ya fashe dashi sosai, be son kukan Ayman, yana waigawa ya ga Uncle Zaid ya idar da Sallah ya tsaya yana kallon su kamar TV, ganin Rafeeq na kuka ya sa Zaid daria, da sauri Rafeeq yayo kan Zaid kamar zai kife shi da duka don takaici, yana kallon su amma ya k'i cewa komai, "Uncle please make her keep quite" a tak'aice Zaid yace "No, i didnt make her cry, you make her calm" Cikin marairaicewa Rafeeq yace "pleaseee" Zaid ya ksrbeta, tana ganin shi tayi lamo tana ajiyar zuciya, Zaid yace "ka duba bayan Seat akwai Basket dinta ka kawo min, she must be hungry" da gudu Rafeeq ya fita waje duk ya bi ya rude, Zaid ya bishi da ido ya na Murmushi, chan sai gashi ya dawo da Basket din Abincin Ayman-Rafee'ah, Zaid ya ce bude flask din ka zuba ruwan zafi a bowl din ciki, Sai da ya dauraye Dan kwanon kafin ya bude flask din, Zafi rau kamar yanzu aka zuba a ciki, tun Ruwan Zafin da Mami ta sa musu a flask ne da safe, har yanzu be huce ba, nan Zaid yayi guiding Rafeeq ya dama mata Baby food din, Zaid ya lasa yaji yayi daidai ya shiga bata a baki kamar yanda ya ga Mami nayi, ta dinga sha har tayi gyatsa, Zaid yace "kwaso kayan booth din gaba ki daya, banda Trollys din, akwai dan kit daga gefe kayan wankan ta na ciki" haka Rafeeq yaje ya dauko, suka tu6eta a tare, tayi kashi a pampers dinta, Rafeeq ya rintse ido tare da kawar da kai gefe ya mata tsarki, hannun kamar zai yaddashi, Zaid ya dinga musu daria, a tare suka mata wanka da ta juya ta hada ido da Rafeeq sai tayi kamar zatayi kuka(😩) Da sauri Zaid "zaice yi shiru babyn hammanta" sai tayi shiru ta fasa kukan, haka suka gama mata wanka duk sun jik'e kayansu kamar sunyi wasan ruwa, kusan Minti 30 suna shiryata kafin Zaid ya hadata da chocholate daTeddy bear, Daga Rafeeq har Zaid suka zube kan Gado yaraf a gajiye, suna maida numfashi kamar wanda suka shekara suna aiki, Rafeeq cikin gajiya yace "You should get married, only to someone who will take good care of her" Zaid shima yana maida numfashi, be ta6a wahalan Ayman ba kamar haka, lallai Mami na k'ok'ari, shima a gajiyen yace "Yes, you are right, i'll get married soon" suka kalli juna suka sa dariya. Jin horn din Motar Alhaji Habib yasa Zaid mik'ewa, yace "Yaya ya dawo" Rafeeq be ce komai ba, Zaid ya mai nuni da Wata Leda yace "ga tsaraban ka chan" murmushi kawai yayi ya bude ya ciro kwalin Turare, da agogo, da links na kaya, da pack din Vest, sai takalmi. Murmushi Rafeeq yayi yace "You are the best".

"Babyn hamman ta zo muje mu gaida Yaya" Zaid ya kalli Rafeeq yace "ko kuka takeyi akace yi shiru babyn hammanta zakaji tayi shiru, she has no idea who the hamma is, yau ta ganshi tana mai RM" murmushi kawai yayi yace "A sannu zata san waye Hamman ta" Rafeeq ya mike ya nufeta yace" zo muje gun Hamma" ga mamakin shi ta mika mai hannu shi kuwa ya sa6e ta, suka fita, Zaid ya dauki ledar Tsaraban da ya ma 'yan cikin gida.

Shekara kusan daya da wani abu rabon da ya taka koda k'ofar parlorn cikin gidan, tana hannunshi ya dinga bin parlorn da ido, yana nan yanda yake, a hankali ya shiga tunano bak'in abun da ya faru, tun daga Randa yaga Mamin shi da wani a daki zuwa ranar rasuwar Rafee'ah, dalilan da ya ke hanashi tunkarar dakin kenan, ya juya zai koma, Zaid yayi saurin girgiza kai yace "mu shiga" ba musu ya bi bayanshi suka hau Sama har Parlorn Daddy. Daddy na ganin su ya mik'e tsaye, bawai mamakin dawowan Uncle Zaid yakeyi ba, aa Mamakin ganin Rafeeq yakeyi a cikin gidan a Saman shi, hawaye suke shirin bullo wa yayi saurin tare su, ya wayance da amsar Ayman hannun Rafeeq, Zaid ya durk'usa yace "Barka da Dare Yaya" Daddy yace "Engineer, saukar yaushe?" "Jiya na dawo" sai ga Saude ta shigo tana takun ta, wai ita tazo taryar Miji, aiko ganin Zaid ya sa ta 6are baki "Meema ga Uncle Zee" "inalillahi" zaid ya furta a ranshi, kafin ya ankar sun rugo da gudu ita da Aneesa wai su zasu mai Oyoyo, da azama ya mik'e yayi saurin mik'a musu ledar Tsarabar su don ya san dukkan su ba mai hankali ciki suna iya fado mai, Meema da ta shagala da kallon Zaid, bata taba ganin hallita me kyaun Zaid ba, Zaid ya gama tafiya da ita, wannan karon ko ta halin k'ak'a sai ta samu cikar burin ta, Dole Sai ya aureta, like hell look at him, ya hadu ne, balle ya sha madarar England, duk ya k'ara cika, ya kusa 40 amma dubeshi kamar dan 25, ita kadai take tunaninta. Aneesa da dadi ya gama kasheta, yau Rafeeq ya zo Sama, ta matsa kusa dashi "Yaya Rafeeq, wata sabon ganin" dogon tsaki ya ja ya mik'e tsaye, tunda Shigowar Sauda ya fara ganin duhu, ya kalli Zaid yace "Uncle I'll be downstairs" be jira cewar kowa ba ya fita ya sauka k'asa. Aneesa tace "kagani Uncle Zaid? Yaya Rafeeq ya tsaneni, ba yason ko magana in dinga mishi, duba fa yanzu yana ganina kamar ya ga kashi, shine ya fita" "Ki cigaba da hakuri" kawai yace da ita. Saude tayi k'wafa ta juya taga Alhaji Habib Dauke da wata kyakywan diya tace "Alhaji ina ka samo yarinyar nan? Yayi danyi yak'en takaici yace " 'yar gurin Zaid ce" ai ko Meema tayi saurin cewa "Laaah Ayman ce yau a gidan mu, daddy kawota, Aneesa ma ta yi hanzarin cewa ni za a ba ita, saude ma tace " ku bari in fara daukarta, ai tana nan gidan, ganin su uku sunyo kanta gadangadan, hakan kuwa ya ba Ayman tsoro ta fashe da wani irin kuka, Zaid ya dafe kai ya girgiza kai, Alhaji Habib yace "kunga kun bata tsoro, Karbeta Injiniya" Zaid yace "k'uiya gareta bata yarda da kowa" ya sa hannu ya amsheta. Saude tace "baka taho da nanny dinta ba?" a ranshi Zaid yace "Nanny dai? Dama Ayman na da Nanny?" Meema ce cikin kissa tace "kema Sis banda abunki wace Nanny zai zo da? Bayan ya kawo Ayman wurina ai ba sai yazo da wata ba, i know how to take care of kids more especially my Daughter" Saude da Aneesa suka sa Shewa, wannan gaskia ne, shidai Zaid wani yak'e kawai yakeyi, wanda da shi gwara yayi kuka, har yanzu Ayman ba ta daina Tsala kuka ba.
"Ka san kuwa tana yarda da Nasiba? Duk k'uiwan Ayman bata yi ma Nasiba, don har goyata takeyi taje gidansu da ita idan tayi bacci ta maido min ita, so nasan ba zaa sanu matsala ba ko kwana nawa zatayi gun Nasiba da kakarta" Muryan Mami ya ji a kanshi a lokacin da ya tuna labarin da ta bashi kan shak'uwar Nasiba da Ayman.
da sauri ya sauka k'asa Meema zata bishi Daddy yayi saurin cewa "da kin barshi ya lallasheta, sai ya maido miki ita tunda a gurinki zata kwana". Dadi ya kamata don duk zaton ta, ita aka kawo ma Ayman.

A k'asa ya ga Rafeeq a dafe kai, duk yanda yake jin kukan Ayman a ranshi, ya fi tsanar ya ga Aneesa da Uwarta shiyasa ya kasa komawa sama da yaji kukan Ayman, Zaid ya kalleshi yace " Start the Car" ba gardama ya fita da sauri ya fada motar shi, ya kunna Zaid na zuwa ya shige, suka fita daga gidan, a hankali Rafeeq yace "Ina Zamu?" a wahalce Zaid yace "Gidan Nene" don har yanzu Ayman bata abr kuka ba, cike da mamaki yace "What? Gidan Nene? Are you kidding me? Sabida me? Why there of all places" Zaid ya kalleshi yace "Sabida chan tazo hutu, akwai matsala ne?" da sauri Rafeew yace "yes big one, matsala babba" "that woman is very noisy, and annoying tana da Hayaniya" Zaid yace "Thank you, but She's living with them for as long as my stay in KT" sai da Rafeeq yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya murtuk'e fuskan nan da ta samu sassauci kwana biyu, sai ya koma dunkum din shi yayi focusing kan tukin shi har k'ofar gidan Nene.

Har Cikin Gidan Baba Maigadi yai mata Iso, da Aneesa ta ci karo, wani kallon da ta watsa mata yasa hanjin cikinta kadawa, "ke wa kike nema?" baki na rawa Nasiba tace "Alhaji na ke nema" "burauba, daddy na kike nema? Uban me zai maki? Shegia karuwa har gida" hayanniyar da Aneesa keyi ne ya sa Hajia Sauda saukowa tace "Anee ke da waye? Ta bi Nasiba da ido, haka kurum taji gaban ta ya fadi, nan ta ji ta tsani Nasiba, ke me kikeyi a gidana karfe 7 din dare? Nasiba tayi shiru, karaf Aneesa tace " Wai Daddy take nema" Meema tace " ke ko turo ki akayi ki kashe shi? Ko ki fadi me kika zoyi ko miyi miki Zindir Wallahi" jikin Nasiba ya fara rawa, da ta sani da ta yarda sunzo da Nene, don sai da ta buk'aci ta rakota saboda dare amma tace "aa ta bari zata iya, ai dare be gama yi ba, kuma yanzu za ta dawo. Nadamar rashin barin Nene ta biyo ta. Sauda tace "kai ku amso min ledar nan, k'ila kayan Asiri ne a ciki, ana so a juye hankalin Mijina" Meema da Aneesa su kayo kan Nasiba, matuk'a ta gama tsorata, Meema ta damk'o ledar, *kar ki bari kowa ya ga magungunan na sai Alhaji, don kiga yan gidan na cikin Zargi, ba mu san waye mugun a ciki ba* maganar Mallam Usman ya fado mata, da sauri ta fizge ledar daga hannun Meema, Meema kuwa ta kamtse Nasiba da Mari, marin da bata taba gani anyi ma wani ko da a film ba, wani ihu ta saka, ihun da ya fargar da Alhaji Habib da ke sama, yana jin hayaniya k'asak'asa, ya sauko da sauri ganin yarinyar nan me kama da Rafee'ah durkushe rungume da wani abu Aneesa da Meema suna ta jibgarta kamar Allah ya aikosu, ya sa shi karasawa gurin ta da gudu, ya dagota, Saude ta sake "Salati, shikenan Karuwar sa ce, dube yanda ya dagota, Alhaji wannan 'yar cikin ka ka ke bi?" ya dago jajjayen idonshi ya kalleta, amma sai ya kasa magana, yace "Nasiba, tashi mu tafi" tana kuka ta mik'e, Sauda tace "Alhaji kar ka fita" chak ya tsaya, amma ga mamakinta sai yace "Kiyi hakuri yanzu zan dawo" ya ja Nasiba har gun Motarshi, ya mata umurni sa ta shiga, Saude kuwa kamar wacce aka dasa a gurin idonta ya koma bula(lols i cant even imagine) "wata sabuwa inji yan chacha" yau Alhaji ne da mata gardama? "Meema tace Lahhh sis ya fita, ya fara miki gardama" Sauda ta yi wani ihun takaici ta bar gurin kamar zata tashi sama.
********
Sai da ya fita bakin Gate ya danyi parking, yace "Diyata, ban san ta inda zan fara baki hakuri ba, ni na ja miki, kiyi hakuri donAllah, ta tsagaita kukan tace bakomai Daddy, ta ciro ledar da mik'a mai tace " gashi inji Mallam, yace zaka dinga sha Safe, Rana Dare, kuma ka dage da Addua, ka dinga tsayuwar Dare, InshaAllah zaka fita daga sharrin me sharri" yanda take mai bayani sai yaji ta burgeshi, ya ji ya na sonta, irin son da yake ma Rafee'ah, yake ji dama diyar shi, ya nisa yace "Nagode kinji? Allah ya miki Albarka", ya sa hannu ya ciro kudi masu yawa ya bata, ta girgiza kai tace " Aa ba zan amsa ba, DonAllah nayi" yace "nasani ni na baki ki karba" ta ki tace "zan je Gida" yace "barin fara kaiki Asibiti a duba ki" tace "haba ba komai" yace "Kinga fuskar ki ya kumbura, dole a duba ki" tace "Allah bakomai zanje gida kafin Nene ta shiga damuwa" yace "dama zan biki in ba su hakuri kan abun da ya faru a sanadiyata" tace "daddy thats not necessary please" ya nuna ta da yatsa yace "bana son musu, ki nuna min hanyar Gidan ku" tace "to a sanyaye" ta shiga nuna mai hanayar Gidan

"Ahhh muryar wa nikeji kamar muryar Zaidu bawan Allah?" Murmushi yayi yace "nine dai Nenen mu ni da Seebi" tace wacece wannan take ta tsala kuka haka? Ya mik'a mata yace "Jikar ki ce" ta amsheta ta tillata sama ta chafe, ta fara yi mata tawai har sai da tayi shiru, kafin ta shiga daki ta goyeta tsaf da zani, kafin ta fito, ta kalli Rafeeq da ya sha mur tun bayan Sallamar da yayi lokacin da suka shigo be sake magana ba da murmushi tace "Ah ah, gaye ya akayi ne? Naga fuskar ka yau kamar lokacin da kake Dun... Sai kuma tayi shiru tare da sa hannunta kan baki tana daria" guntun tsaki ya ja ya kawar da kai gefe, gyatsine tayi irin i dont care dinnan, tace kaji dashi "dunkum dangi tsaka" ya kalleta da sauri, tace "kaji ai cewa nayi dunkum, ko ba tsaki yayi ba? Magani sai ya fara aiki, sai abu ya rikice, to yau obados (over dose) zan baka.Tsakin ya kuma yi, shi dai Zaid daria yake tayi, yace " Nenen mu mun same ku lafiya?" ta janyo kujera ta zauna tace "Lafiya lao mutan Ingila, haka ka koma? Kaga yanda kayi kyau kuwa? Kamar da Amurka(America) daria kawai yayi, Daria kawai yayi, tace "Wannan fa?" ta nuna bayanta, yayi murmushi yace " 'yar guna ce" tace "Ahh wannan ba jika bace, wannan diyata ce, ni diya zanyi da ita, ina Mamar ta ta? Tsaki Rafeeq yayi yace " she asks to many questions, tana da damuwa gata da hayaniya" shifa a ranshi yayi maganar be san maganar ta fito fili ba, Nene ta mik'e ta shiga daki sai gata ta dawo da igiyar chargy na radio ko fitila, cikin daga murya tace "Zaidu bawanAllah, yau ko ni ko Dunkum, ta hau k'okarin kwance Ayman da ke bayanta, wai zata ma Rafeeq dukkan tsiya, Zaid yayi saurin tashi, don shi a zaton shi wasa takeyi, amma yanda ya ga ta dage ya sa shi bata hakuri, shi kuwa Rafeew yana nan ko gezau beyi ba tace " Haba Zaidu Bawan Allah, na dade ina hakuri da Dunkum, sai yayi ta gaya min Maganganu yana min turanci, rannan har bangaje ni yayi ya bi ta kaina ya wuce, Nagaji, yau ko ni ko shi" Zaid ya shiga bata hakuri, yana ma Rafeeq ido da ya bata hakuri, shi kam ya dauke kai kamar be san ta nayi ba, ana Cikin haka ne Nasiba tayi Sallama. Daga muryarta Nene a san cewa ba lafiya, duk suka zuba ma Soro ido, Nene tayi saurin karasawa gunta tace " Seebin Nene, me ya samu fuskar ki?" Nasiba tace "bakomai" tayi gaba ta tsaya kusa da Uncle Zaid tace "Ina wuni? An dawo Lafiya" ba ta jira amsarshi ba tayi gaba zuwa daki, don idan ta tsaya dogon magana ta na iya fashewa da kuka. Zaid duk ya bi ya damu yana so ya ji matsalar ta, "Ke Seebi" inji Nene, chak Nasiba ta tsaya da ta ji yanda Nene tayi kiranta in a serious tone, Nene ta matso kusa da ita tace " ni nasan ke baki da abokan fada, baki da neman tsokana, kina da gaskia ana iya dukkan ki ki kasa magana, ki gaya man, wani dan abun uban ne ya bugeki har ya kumburan maki da fuska? Kamar jira takeyi ta fashe da kuka, Nene ta sake hawa sama tace "a gidansu Dunkum din ne a ka bugeki? Eyi? Ki gaya min" ita dai bata fasa kukan ba, Rafeeq yayi guntun tsaki ya matso kusa da ita yace "kinje gidan mu ne?" yo eh daga gidanku take "Me kika je yi a gidanmu? Eh?" Nene cikin fada tace "kai dallah dakata min, go gefe, zaka tasata a gaba kana mata fada, sak'o takai ma babanka, shine aka samu watsatssu da suka mata hakan? To wallahi ba zan yarda ba ko uban waye ya taba man 'yar jikata sai ya yaba aya zak'inta"
Sai yanzu Zaid yayi magana duk da be gane me suke nufi ba duka ya kalli Rafeeq yace "Calm down Feeq, Nene fada ba zai maganace komai ba, bari ayi abun a tsanake, Seebi, su waye suka buge ki?" cikin sheshekar kuka tace "wasu mata ne su biyu, don sunce in basu ledar hannuna nak'iya shine mamansu ta sa su suka dinga duka na, sai da babansu yazo ya k'wace ni tare muke yana waje" a hankali Rafeeq yace "Aneesa da Meema" Nene tace "Babbar Balaeen chan, wallahi da Aneesar, da uwarta da wace tsiya sun tsokalo tsuliyar dodo, ba su san da su ta6a Seebi gwara sun kamu da farar masassara, yau sai na gwada musu wacece Aminene Mamman" ta figi hijabinta da ke kan igiya, ai ko duk suka yo kanta, Zaid yayi saurin rik'e mata Hijab, ai ko ta daddage ta buge hannun Zaid, daidai Soro ta ci karo da wani Mutum ta kalleshi galala tace "kai kuma fa?"

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

_Nagode da Adduoin ku, masu kirana da masu min message a Whatsapp da Sms Ina godia, ina muku Albishir da naji Sauk'i sosai, kuma zaa cigaba da yanda akeyi InshaAllah. Allah ya bar Zumunci.

Pg4⃣8⃣

Duk suka bi bayan Nene, Rafeeq na gannin baban shi a ranshi yace "Interesting! Daddy a gidan Nene" shi kuwa Zaid cewa "yayi Yaya me kakeyi anan?" nan Nene ta gano bakin Zaren tace "touu Alhaji Habib Lema ne, gaya min, da saninka ne Matarka da 'yayanta suka ma jika ta mugun bugu?" Alhaji Habibi duk ya daburce, be taba ganin tsohuwa me masifa haka ba, yace "kiyi hakuri Wallahi ba da sani na bane, ni ne na kar6eta" Nene tace yo abun azziki kayi? Dalilin wa aka bugeta? Nace dalilin wa? A hankali yace "kiyi hakuri a dalilina ne, hakan bazai sake faruwa ba" tace "k'warai kuwa, hakan ba zai taba sake faruwa don yau watna cin ubansu ya tashi, har matarka" tayi hanyar fita da sauri Seebi ta rik'ota, duk suka shiga bata hak'uri tana cicijewa banda Rafeeq da ya koma gefe yana Murmushi, ya tabbatar Nene yar daru ce, da k'yar suka shawo kanta don tana ganin kimar Zaidu dan Albarka, ta dawo ta zauna kan kujera, Nasiba tace ma Daddy kayi hak'uri, shez always like this" murmushi ya mata yace "karki damu" ya zauna kusa da Zaid dake kan tabarma, cikin gunguni Rafeeq yace "ai da kun kyaleta taya zata je gidan mutane ta buge su?" ashe ta ji shi cikin fada tace "Ai da kun bari naje sai ka ga ta yaya naje har na musu dukkan tsiya, sai ka tantance, kaima bawai k'yaleka nayi ba" Uncle Zaid yace "Feeq quiet!".



Please Login or Register in order to submit comment