Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na kwarai shine wanda be shiga hakkin da ba nashi ba" Yarinyar ta kama hannun Nasiba, kamar zatayi kuka, donAllah ki taimakeni, ki yarda dani" Cikin masifa Nasiba tace "Sabida mene zan yarda dake? Bansanki ba, bansan komai game dake ba, kinzo kina sani abubuwa? Toh wannan karon ba zan tainaka miki ba, kizo kiyi abunda kike sani da kanki, duk nisan da kike kizo ki yi aikin ki da kanki, idan kinso daga yau ki di ga zuwa min da mummunar siffa, ki hanani bacci, ba zanyi yanda kike si ba" . Yarinyar tayi dan murmushi, tace "da zan iya da nayi" Nasiba tace" zaki iya mana tunda kina tunanin ni zan iya" tace ke zaki iya don kina nan duniya, ni kuma ba zan iya ba, don bana duniya" cikin firgici Nasiba tace "me kike nufi da hakan?" Yarinyar tace " *My Name was Rafee'ah Habib Lema, na Rasu Shekara daya da Rabi da suka wuce*".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

*Allah Sarki Yanuwa da Abokan Arzikki, da Masoya❤ duk na ga sak'onnin Ta'aziyoyin da kuka min, nagode Allah shi karb'a, ya biya ku, shikuma mamaci Allah ya ji k'anshi (Baba Hashimu) Allah ya gafarta mishi, Allah kasa ya huta. Da duk Musulman da suka riga mu Gidan Gaskia, mukuma in tamu tazo, Allah ya sa mucika da kyau da Imani Amin, Nagode Nagode Nagode, Allah ya barmu tare.👏🏽👏🏽👏🏽.*

Pg3⃣5⃣

Firgici da tsoro suka ziyarci zuciyar Nasiba, ta fara karkarwa, ta na ja da baya, baki na rawa tace "Fa+ta-talwa" Rafee'ah ta yi saurin cewa "DonAllah kar ki ji tsoro, banda niyyar cutar dake, ke musulma ce, kuma kinyi Imani da hakan, karda ki sa ma ranki ni Fatalwa ce, ni ba Fatalwa bace, da iko da k'uddirar Allah nazo miki a Mafarki, Mafarki kike yi dani, DonAllah ki kwantar da hankalin ki, banda niyyar cutar da ke .(Mu sani Ba Fatalwa a musulunci, Wanda ya mutu ya mutu, ba yanda matacce zaizo cutar da kai, in ka ga Mattace a ido, to gizo yake maka, ko kuma kayi mai mugun abu kafin ya mutu, ka sa ma ranka ne,shine kake ganin kamar zaizo maka, amma Tabbas ana mafarki da Matattu, _to Nasiba dai Mafarki takeyi da Rafee'ah_.)
Nasiba ta sauke numfashi, hankalin ta ya dan kwanta, Sai da Rafee'ah ta ga Nasiba ta samu natsuwa sai tace "Kamar yanda nace, ina so kin dan wanene Rafeeq, ina so ki shiga Rayuwar Rafeeq, ina so ki sauya duk wani abu da ya danganci Rafeeq, ina so ki warware zare da abawan cikin gidan Lema, akwai abubuwa da yawa da zaki fuskanta, akwai hadari a cikin wannan aikin, amma ki sa Allah a gabanki, ba zai barki ke kadai ba, sai kin jure kin daure". "Bazan iya ba, ni ala musuru ce? Da zan miki duk wadannan abubuwan? Saboda mene zaki dinga bibiyata cikin mafarki kina sani abubuwa?" inji Nasiba, Rafee'ah ta nuna ta da yatsa, tace saboda *"KE ALHERI CE"* cikin rashin fahimta Nasiba tace *"NI ALHERI CE?"* Rafee'ah ta gyada kai tace *"Eh, KE ALHERI CE"* ba za ki gane ba yanzu, amma a sannu zaki fahimci dalilina na ce miki haka, ta dan sasautar da murya tace "Nasiba, Rafeeq yaya na ne ina sonshi sosai, Rayuwar shi na cikin 6ata, ki taimake ni ki min wannan aikin, Allah kadai zai biya ki" Nasiba tayi shiru tana tunani, tabbas ita shaida ce kan halin Rafeeq na Shariya, da k'yaliya, itana tana kwadayin jin labarin shi, kuma tasan tabbas yana cikin damuwa, chan tace "Shikenan, Allah ya mana jagora" dadi ya lullube Rafee'ah, tace "Nagode Sosai, but one more thing, you must not tell anyone about your Dreams and your Mission, kar ki gaya ma kowa, komai kusancin ki da mutum, ki min Alkawari kinji?" Nasiba tace "InshaAllah ba wanda zai sani" Nagode sosai, ki fara binciken ki da wuri, ba mu da lokaci" Rafee'ah tace "InshaAllah". Rafee'ah ta mata sallama ta tafi, daidai nan Nasiba ta sauke ajiyar zuciya me nauyi cikin bacci, gyara kwanciyarta tayi.

_7:50am_

"Nene yi zaman ki, barin je in siyo k'osan", aa Seebi budurwa dake sai a ga kin tsaya bakin titi siyan k'osai? Yo meye? Wa ke bina bashi?" ni zanje, ba me bina bashi" Nene tace "kawai sai a ga yar budurwa kamar ki na bin layin k'osai?" Nasiba tace "ni kuma gani mara tausayi, kina fama da Masassara don kar ace gani budurwa, sai in barki kije siyan k'osai, to ba dani ba, kinga tafiya ta" Nenen tace "ai sai kiyi, tun yaushe zazzabin ya sauka?" Nasiba ba ta tsaya tanka ta ba ta fita daga dakin, Nene kuwa ta dan kishingida, ko minti daya baayi ba wayar Nasiba ta hau ruri, Nene ta buga tsoki " wani dan anacen ne ke kiran waya da fara saffiyan nan? Sun maida waya Kamar wata Ramadana, haka ta dinga mita har wayar ta tsinke, chan ta hau ruri, Nene ta mik'e ta zaro wayar k'ark'ashin pillown Nasiba ta latsa tare da cewa "Hello" "Assalam Alaikum Seebin mu ni da Nene" Nene tace "Laaah, Zaidu bawan Allah, Kai ne?" yayi murmushi kamar yana gavanta, yace "Eh Nene, nine, kamar kinsan kiran nan naki ne" tace "Allah ko? In ka ji kira Samu ne" yayi daria, yace "Addua nake buk'ata, an tura ni Ingila wani Aiki, kuma zanyi sati 3zuwa wata 1 a chan, shine muke barar addua" tace ai addua kullum cikin yinta muke, Allah ya kareka daga masu jan Kunne" yace "su waye masu jan kunne?" "Tabdijam! Turawa mana" Dariya Zaid yayi sosai, tace "Af! Daria na baka ko? Ai turawa muggai ne, sai an hadasu da *Li'ilafi kuraysh*" Sosai Zaid ke dariya, yasan idsn ya biye ma Nene, haka zata dinga sa shi daria har yayi missing flight dinshi, yace "nikam ina Seebin mu?" Taje siyo K'osai da burodi" Zaid tayi dan jim, Nene ta fuskanci shirun Xaid, Ehtace "kai ma kagani ai, gardama tsiya gareta sai da nace mata ta bari in siyo, tace wai aa, wai ban lafiya ita zata ta siyo" Zaid yace "baki Lafiya Nene? "Zazzabi ne ya lullube ni jiya da daddare, amma yanzu ta sauka, na ji sauki" "Nene ko zakije asibiti? "Kai ni rabani, komi Asibiti, to naji sauki" yace "to shikenan Nene, ni zan tafi, kice da Seebi zan kirata idan na sauka" Nenen tayi Murmushi tace "to Zaidun Seebi, Allah ya tsare ya kare ya bada saa" kiris ya rage dadi ya kashe Zaid, yaji dadin wannan kalami na Nene, yace "Amin Nenen mu".

*Kaskon Mai K'osai*

Lubbatu mai k'osai (Sorry Lubie😂) ta shahara gun soyen k'osai, ga dadi, ga tsafta, gaban kaskonta mutane ne sosai suna jira a soya a basu, Nasiba na daga cikin masu jira, tayi tagumi daga gefe tana tunanin Mafarkin ta na daren jiya, tana tunannin yanda zata bullo wa lamarin, taya zata shiga Rayuwan R-Lema ba tare da taimakon kowa ba? Ta ya zata san ko shi waye ba tare da ta tambayi Zaid ba? Allah ka kaow min Mafita" sama-sama ta ji firan Lubbatu mai K'osai, da wani dan datijjo, da alamun Customern ta ne inda datijjon ke cewa "Ni banga k'awar fada ta yau ba, da ta na nan ba zan gaji da jiran layin nan ba" lubbatu tayi daria, tace " nima bangan ta ba yau, da ta na nan da ta dinga mitar har yanzu ba a soya min nau ba?, ko kuma tace ta rigaka zuwa nan" daria yayi yace "aiko idan zan wuce gida zan biya gidan ta inji ko lafiya yau ba ta fito siyen k'osai ba" lubbatu mai k'osai tace "anya Maigadin Gidan Lema ba da Aminene za'ayi ba?" ya fashe da darian jin dadi yace "ai na fi k'arfinta" Nasiba da ta yi k'ask'e tana jin su, a ranta ta maimaita "Maigadin Gidan Lema? Isit possible gidan su R-Lema yake Gadi?" Don tana da tabbacin wuraren nan gidan su R-Lema yake, kuma tabbas maganar Nenen ta suke yi, Allah sa haka ma, Don ta fara aiwatar da aikinta tun wuri.
Ba jimawa a aka sa ma Baba Maigadi Gidan Lema k'osan shi, cikin saa a ka zuba ma Nasiba nata, Baba Maigadi yayi Gaba Nasiba tabi bayan shi, tace "ina kwana baba?" da faraa yace "lafiya lao Jikata" haka suka cigaba da tafia har Nasiba tazo gida, zata shige kenan yace "Jikata dan tsaya?" cikin gidan nan zaki shiga?" tayi murmushi tace "eh, Baba" yace "ko Aminene na ciki? Na jita shiru yau bata zo siyan k'osai ba" tace "eh ta na nan, bata ji dadi bane jiya da daddare " yace "Assha! DonAllah kice da ita, Maigadin Lema na Sallama" bawai don tana da tabbas ba tace "Baba kai Maigadin su Rafeeq ne?" ya washe baki yace " Yo eh, ai nine Maigadin su, tun lokacin Iro Kakan Rafeeq kenan" Murmushin Nasara Nasiba tayi, tace "Baba, barin maka Sallama da Nenen" ta shige gida.

"Nene ana Sallama da ke?" Nene tace Sallama kuma? Wanene? Seebi cikin sigar zolaya tace "bazawarin ki" ke zan saba miki, badai Zaidu bane don yanzu ya kira yace an turashi Ingila aiki zaiyi wata Guda" Haka kurum Nasiba taji ba dadi, zata yi kewan Zaid, tace "wani Maigadin gidan Lema" murmushi Nene tayi tace "Danrainin wayau, nasan zuwa yayi jaje na yau be ganin ba a gurin siyan K'osai" Nasiba tace "Toufa, har kun saba da Shi, ko dai ko dai?" harara Nene ta jefeta da shi, tace barin je mu gaisa" Nasiba tayi saurin cewa aa, barin dai ce ya shigo sai ma in shek'a mana koko, Nene ba ta ce komai ba Nasiba taje ta shigo da Baba Maigadi.

Bayan sun gama kalaci ya musu Sallama, Nasiba tace "barin raka ka baba" yace to Jikata, ya kalli Nene yace to "Aminene, Allah ya kara sauk'i, sai na sake zagayowa" cikin wasa tace " Idan zaa dawo a dawo da karin ciwo, bawai azo a isheni da dimin surutu ba" Gabaki daya suka sa daria..

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg3⃣6⃣

A hanya, Nasiba ta dinga jan shi da fira, da yake Baba Mai gadi saurin sabo ne dashi, nan da nan yake bata amsar tambayoyin da ta ke mai, Nasiba a ranta tace "Hanya Mafi saukake da zan san ko kai waye Rafeeq" Baba mai gadi yace "ke Nasiba, kinga har kin rakoni Gida, na jaki da yawa" tace "lahh har mun iso? Ya nuna gidan da yatsa, yace "ga gidan nan" gabanta ya yanke ya fadi, wani irin Tamfatsetsen gida ta gani, gidan ya hadu, a ranta tace "So this is where you live R-Lema" Baba yace to ki koma gida Nasiba, sai nazo gobe, ta dan marairaice fuska tace "Baba nasan Nene ta koma bacci, idan ba damuwa in zauna nan in tayaka fira" bench ya dauko ya ajiye gaban Gidan, ta Zauna, yayi daria yace wani irin fira zamuyi? tace "labari zaka ban" "wani iri kenan" a ranta tace "Astagfurullah Zanyi karya" ta sausauta murya tace "Baba labarin Rafeeq zaka bani, Makarantar mu daya, da ni budurwar shi ce, yana sona sosai, amma rana daya ya sauya min, ina son shi kamar me, amma sai naga ya daina kulani, yanzu ko gani na yayi kallo ban ishe shi ba, shine nake tunanin ko yaudarata dama chan yakeyi?" da sauri ya girgiza kai yace " kar kice haka, Rana daya Rafeeq ya sauya ma kowa, Rana daya K'addara ta gifta ma Rafeeq" Nasiba tace Baba ka ban labari *Wanene Rafeeq* Ajiyar Zuciya yayi, yace Rafeeq D'a ne kamar kowa, mai fara'a da son Jama'a, kinji kinji................ Tsaf Baba maigadi ya kwashe ya bata labarin duk abunda ya sani game da Gidan Habib Lema har zuwa zaman da sukayi yau. Sosai Nasiba ke kuka har da Majina, lokaci daya tausayin Rafeeq ya lullube ta, Sam bata ga laifin Rafeeq ba, lallai Rafeeq abun tausayi ne, Lallai Rafeeq na buk'atar taimako.

Baba Maigadi yace "Nasiba mun dade zaune a nan, ki tashi ki tafi Gida" ajiyar zuciya ta sauke tace "Baba, Labarin Rafeeq na cike da Abubuwan ban Alajabi da Mamaki, da tausayi, baba yanda kasan a fim" Baba maigadi yace a takaice ma kenan, "zato zunubi amma ina Zargin Matar Ubanshi Saude ga duk wani abun da ke faruwa cikin gidan nan, ban taba dai ce ma kowa komai ba" da sauri tace "Saboda me kace haka Baba?" "Saboda randa aka ce an kama Mahaifiyar Rafeeq da kwarto cikin daki, Saude ta fito ta aikeni siyan Gayen lataz, kafin na dawo har an saketa, tun daga rannan komai ya sauya, Alhaji be kara maganar da kowa ba, kinga kuwa beyiwu haka, ko yaya ne sai an maida magana, amma ko maganar ka mishi zai nuna be ma san wacece Aisha ba, kinga ko anan akwai ayar tambaya, sai maganar Karatun Rafeeq, makarantan ku daya, ke kinsan irin kokari da fasahar da Allah ya bashi, amma har yau ya kasa gamawa, abokin shi Maalesh har ya gama bautar k'asa, nan ma akwai ayar tambaya, sai maganan Rasuwar Rafee'ah, mutuwa dole ce ta na kan kowa, Ana gobe Rafee'ah zata rasu, ta fito da Cooler abinci ta fito nan tana zolaya ta, tace dani "Baba, yau da Hammana zan ci abinci" nace kice sanwa kika ma yayanki tace "Aa, antu saude ta dafa mana" ta shiga ciki, chan sai ta fito, nace har kun cinye? Tace "be ci ba ya riga da ya siyo nashi, ni kadai naci, ko na juye maka sauran a plate? Nace "aa Rafee'ah nagode" washe gari Rafee'ah tace ga garinku nan. Tunda Aisha ta bar Gidan nan, ban kara cin komai na Gidan ba, don ba bani ake ba, ruwa Saude bata taba miko min ba, Alhaji be taba cewa don me baa bani abinci ba, shi da ke ganin girma na da darajata, Zaid kadai ke min ihsani, da idan kinga yanda muke wasa da daria da Rafeeq, abun ba aa magana, amma yanzu komai ya jagule, ni Wallahi ina Zargin Saude, hanalina be kwanta da ita ba". Nasiba ta nutsu ta na jin Zancen baba Maigadi tace "Allah shi saka ma wanda aka zalunta" yace "Amin" horn akayi da k'arfi, jiki na rawa yace ina zuwa ya shiga gidan da sauri ya wangale Gate din, Meema ce da Aneesa cikin wata katuwar Mota, Meema ta harari megadi tace uban me ya hanaka bude gate da wuri? Yace "kiyi hakuri" tsaki ta buga ta figi motar da Sauri Nasiba ta ja baya don kiris ya rage su bi ta kanta. Saida ya kulle gate din ya dawo gun Nasiba tace baba su waye wannan? Yace "Kanwar Saude ce, da diyarta, in sukayi wani abun sai ki rantse su 'yayan alhaji ne, ita Aneesar naji labari har ta koma Aneesa Habib Lema a Makaranta" Nasiba ta jinjina kai tace "baba barin wuce" nan sukayi Sallama.

Tun kan hanya Nasiba ta hau tunanin yanda zata fara wannan Mission dinta har ta je gida tana sak'a da warwara, ta rasa yanda zata yi, amma abun da ta kudirta a ranta, Zata taimaki Rafeeq, zatayi yanda Rafee'ah ta bukace ta da tayi, nan Allah ya cire mata duk wani tsoron abun da zai je ya dawo, ta san its not an easy thing, amma haka kurum zuciyar ta ta amince da duk halin da zata shiga, zata yi sacrificing kanta, she's willing to take the risk, bayan jin ta bakin Baba Maigadi, da hujjojinshi na Zargin Matar Baban su Rafeeq,komai zai zo mata da sauk'i, nan ta gane ba Rayuwar Rafeeq kadai zata shiga ba, Rayuwar Gidan Lema gaba ki daya zata shiga "So help me God". To tambayan shine "Ta yaya zan shiga Rayuwar su Gaba ki daya?" zuciyarta tace "barin jira Rafee'ah a mafarki".
Da daddare sai juyi take don tayi Mafarki, amma Shiru ba Rafee'ah, washegari ma kwatakwata batahi mafarkin komai ba, kwana 3 ta jera tana jira tayi Mafarki da Rafee'ah amma shiru, tace ma kanta " it seems like i am on my own, Allah ka taimake ni."

*5:50pm*

"Sannu Nene" Nasiba tace cikin damuwa, tun kwana 2 da suka wuce Nene ke kwance, ta rasa me ke damunta, ta k'i yarda suje Chemist, kuma ta k'i yarda Nasiba ta gaya ma Abban ta, Nasiba duk ta shiga wani yanayi, a iya wayon ta, ba ta taba ganin Nene tayi ko da ciwon Kai ba, cikin rashin kuzari Nene tace "Wai uban meye zaki tasani gaba ki zabga uban tagumi kina kuka iyi? Ko kinga na mutu ne? Nasiba tace "Nene nifa ban taba ganin kiyi ciwo ba" Nene tace da yake ni Waliyya ce sai in k'i ciwo, ko kullum in banda lafiya sai inzo inyi kwance kamar wata ke a gurin, to Nasiba ko ciwon Ajali ne me zuwa ma mutu farat daya, to barin bar miki wasiyya" da sauri Nasiba ta tashi ta shiga daki ta bar Nene kwance tsakar gida, don ta san Nenen k'arfin hali kawai takeyi tana maganar nan, kuma idan ta biye mata sai ta sa ta kuka don Bakin Nene ba ya shiru. Nasiba ta rasa yanda zatayi, ba ta san kiran Abban ta don ta san shi da damuwa, yana iya kamo hanyar Katsina da Marecen nan, ya zatayi? Bata gama tunanin ba Wayar ta ta hau ruri da sauri ta dauka + ta gani wato lambar waje ne, ta dauka da Sallama, a dayan bangaren "Waalaikum Salam Seebin mu ni da Nene, ya kike ya karatu? Tace " Uncle Zaid, Alhamdulilah, ya Aikin? Yace "Alhamdulilah, ina Nenen?" kamar jira take ta fashe da kuka, lokaci guda Zaid ya rude, "me ya faru? Me ya same Nene? Wani abin yake faruwa a katsinar? Ki min magana Nasiba" daga jin muryar shi kasan hankalin shi a tashe yake" ta dan tsagaita tace "Uncle Zaid, Nene ba ta da Lafiya, tun kwana 5 da suka wuce, ina tsoron wani abu ya same ta, ban taba ganin ta haka ba, amma ta k'i yarda muje Asibiti ko nagaya wa baba na" Zaid yayi dan shiru yace "no wonder, randa na kira naji muryar ta wani iri, ashe ba lafia, kuma bata gaya min ba" "ai ba zata gaya maka ba, don Nene wata irin mata ce me Zurfin ciki, nima don ta kai kuri na san cewa bata jin dadi, har yanzu bakin ta ya ki mutuwa" Zaid yace "ki kwantar da hankalin ki, ki tashi kuyi shirin Asibiti aje a dibo ta" Nasiba tace Uncle Zaid " ba zataje ba, Nene is so stubborn" yace "trust me on this ki kai mata wayan".

Haka ta mik'e ta kaima Nene Wayar, Nene ta amsa da Sallama, Zaid ya gaida ta, "lahh, Zaidu bawan Allah, kaine Ya Ingilar?" yace "Alhamdulilah, ashe ba kiji dadi ba?" saida Nene ta wurga ma Nasiba harara kafin tace "Kai kalau nake" "Aa Nenen mu, ga muryar ki nan, ni dai ki tashi ki kimtsa gashi na turo a zo a kaiki Asibiti, donAllah kar kice Aa" ba yanda zatayi tace "Toh Zaidun Seebi, tunda yanzu maganar ta kadai kake ji" duk sukayi daria, ta mik'e da k'yar ta shiga bandaki, yace "Nasiba, ku shirya za a zo a kaiku Asibiti" tace "Uncle Zaid ina iya kaita, ba sai an zo ba" yace "don't be silly, zan sake kira inji ya jikinta" dif ya katse wayar. Nasiba tayi murna, tace "Allah Sarkin Uncle Zaid, Our Guardian Angel."

A karo na 3 Ya shiga lalluben layin Rafeeq, sai ya kusa shiga sai ya datse kiran, don yana fargaban abun da zai ce mai, Rafeeq be son irin haka, amma ya zaiyi? He is his only choice, chan dai yayi shahada ya sake kiran wayar Rafeeq, ringing biyu Rafeeq ya dauka ya kafa a kunne ba tare da yace komai ba, Zaid yace "hello son, ya kake?" kamar ba zai yi magana ba yace " Barka da Yamma" Zaid yace "Kaci abinci?" "Uhm" kadai yace, Zaid yace "Rafeeq ka tuna Nene? Wacce kama granddaughtern ta Assignment last week? Kamar ba zai tanka ba yace "yeah" " she's sick wallahi, she's been sick for days" a ranshi yace to why are u telling me? Allah ya sa ba cewa zaiyi inje in gaishe ta ba don ba zuwa zanyi ba, shiru be ce komai ba Zaid yace "Kaji ai?" da kyar yace "Allah ya bata lafia" "Amin, Rafeeq i want you to do something for me, DonAllah ka dauke ta ka kaisu Asibiti" cike da mamaki yace "What??" Zaid yayi saurin kwantar da kai, donAllah they need help, kaisu Asibiti kawai zakayi, this is all i'm asking for, Please" dif Rafeeq ya kashe wayan, takaici uwa ya kashe shi, shi be san meyasa Uncle Zaid ke sa shi yawan magana ba, in banda neman Magana shi zai kaisu Asibiti? Why they need help, shi First Aid box ne? Kai akwai Sakel, shi be kai kanshi Asibiti ba zai kai wasu? Ga Maalesh baya nan, to ko dai ya kira musu Ambulance? Amma Uncle Zaid ya fi k'arfin ya sashi abu ya k'i yi, be da wani Zabin da ya wuce mik'ewa ya shiga mota.

Daga gidan su zuwa gidan su Nasiba yayi tsaki yafi dubu, gashi yanzu fi Minti 5 yana tunanin yanda zai shiga gidan, Kamar yayi kuka, Ya ciro wayar shi ya tura ma Zaid text, "i'm there" don be son mishi magana a halin yanzu, Zaid yayi saurin kiran Nasiba, yace "ku fito yana waje" ta shaida mai da yanzu zasu fita. Ya tura ma Rafeeq da cewa "there are coming now, kindly greet the sick person please, Please Rafeeq, for me" tsaki ya buga Wannan Uncle Zaid din yana sani abun da ban yi niyya ba, takaici ya hana shi tsayuwa, ya koma motar shi ya Zauna" ba ayi minti Daya ba Nasiba ta fito rik'e da Nene, ta waiga ta waiga bata ga kowa ba, daga chan taga wata jan mota mai bakin Gilashi, da alamu ba kowa ciki, "to ina wanda Zaidun ya aiko?" "inaga bai karaso ba, mu koma daga ciki" duk wannan lek'e lek'en da sukeyi Rafeeq na kallon su, ganin zasu koma ciki ya sa shi yin horn, Nasiba ta juya inda taji horn, ta ga haske a ta cikin motar nan zuciyar ta ya bata, R-Lema ke cikin motar chan, ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai zata samu ta shiga rayuwar shi, tace "Nene, ga motar chan" "wanchan mota kalar jini, ga bak'in windo shi kike nufin mu shiga?" cike da takaici tace "toh, ko Uncle Zaid din ne zai sa a cutar da mu?" da sauri tace "ni ba haka nace ba muje muje kar ki kaini gaba" su ka karasa har inda yayi parking, har yanzu be fito ba, Hannu ta sa ta bude k'ofar baya, Nene ta shiga da Sallama ita ma ta bita ta shiga ta rufo kofar, Nasiba ta kalleshi tace "ina wuni?" be amsa ba, shi dai ya tsinci kanshi da cewa "Ya jiki? Sannu da jiki" Nene ce da fara'arta tace "Naji sauki sosai" be sake magana ba ya ja motar, cikin nutuswa yake tuk'in shi, Nasiba na karantar duk wani abu da yakeyi, tausayin shi take ji sosai, ba tasan lokacin da hawaye suka soma zubo mata ba, tayi saurin

Please Login or Register in order to submit comment