Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu Lokaci guda, Uncle Zaid Allah ya sa Alheri" "ke dallah rufe min baki, me kika sani, banza samna kawai, in banda banza wa ke bada goyon baya a mata Kishiya? Bazan hanashi Aure ba, amma saidai ya zabi daya, Saidai a fara daura Aurenku in kin haihu yana iya Auren" Nene ta karashe ta na me hararar Zainab da ta gama tsorata da Nene, Mami tace "Kiyi hakuri Nene, da Nasiba aka fara Sa Rana, da ita zaa fara daure Auren"
Zaid ya dafe kai yace "Nene wallah ban isa in Wulakanta Nasiba ba, ya zaayi in Wulakanta ta? Ina mata tanadi ne, tanadin da zata fi kowa Farinciki da faruwar shi, ina so taji dadi har karshen rayuwarta, na sa ma mata wanda zai so ta ya kula da ita fiye da ni, na gano wanda ya fi ni sonta, na kuma gano ina ma Nasiba So irin na Uba da Diya ne" Seebi da Rafeeq suka tsura ma Uncle Zaid ido, Rafeeq fargaba ce, fargaban wanda Uncle dinshi ya samo ma Nasiba, Nene tace "Zaid me kake nufi ne na kasa gane komai, meyasa kake maganar Wani bayan ga ka?" a takaice yace "Saboda ba ni zan aureta ba" duk suka ware ido "Rafeeq zai aureta, Ya fi ni sonta, ya fi ni k'aunar ta, kuma zai kula miki da ita fiye da zatonki" Nene ta murtuk'e fuska tace "Waye Rafeeq?" Zaid yayi Murmushi yace "Dunkum Naki" Nene ta dafe kirji tace "Allah ya tsari Kakata Laminde, Dunkum din zan baiwa Nasiba, koo a mafarki" kan Rafeeq a k'asa, ya shiga duniyar tunani, son Uncle Zaid na ratsa shi, Uncle Zaid ba zai ta6a hutawa ba sai ya mallaka mishi Seebi, da me zai saka ma bawan Allahn nan?.
Ai Nene in gaya miki, Dunkum dinki na son Seebi yanda baki tunani, kuma nagane ta na sonshi, shiyasa zan aura musu junan su, kuma kinsan kin fi son farincikinta fiye da na kowa ko? to Rafeeq ne farincikin ta, kar ma ki shiga tsakani don tun Asali Seebi bata taba so na ba, tana dai ganin girma na ne shiyasa ta amince da Aurena, in kin musa gata ki tambaye ta" Nene ta kalli Seebi, tace "Ke Seebi wai haka? Wai dunkum kike so" Nasiba ta daburce ta fara girgiza kai alamun aa,bata san yanda aka gane cewa tana son Hamma Rafeeq ba" Nene tace "magana zakiyi ki na gyada kai kamar k'adangaruwa" Nan ta k'ara rudewa, "E- aa, aa bana so" Nene ta ta6e baki, tace "Ja'ira, ba ta iya k'arya ba, duk yanda tayi k'arya sai ka dagota, Aishatu son shi takeyi Wallahi, amma kin bada ni wallahi, ki rasa wa zaki so sai Dunkum? Dunkum fa Seebin Nene, yo ni ko a k'afa aka daura min Dunkum ai sai na kwance" Rafeeq ya dago kai ya kalli Nene, suka galla wa juna harara.
Zaid yayi murmushi yace to Alhamdulilah yanzu dai Tare zaa daura Aurenmu, sai A fara Shirye shirye, Daddy yace "Zaid think of what you are doing, ya zaayi Rafeeq yayi aure yanzu? He will only hurt her with his attitudes, dont do this" Zaid ya kallo yayan shi yace "Yaya, this is my descison, Rafeeq is My Son, and i can get him Married whenever i want" Alhaji Habib ya ja baki yayi shiru, Mami ta dan ji wani Sanyi a ranta da abu yazo da sauki da haka, dama bawai ba ta son Rafeeq da Seebi bane, aa tana dai Son saka ma Zaid hallacin da ya mata. Zaid ya ma Mami ido, Mami tace "Zainab tashi mu shiga ciki ko? I know you must be tired" Zainab tayi Murmushi Ta mik'e Aneesa ta karbi Ayman da ke bacci a hannunta ta hau da ita sama din kwantar da ita, Daddy ya bi bayan Mami, Zaid ya Mik'e yace "bari naje na dan watsa ruwa donAllah Nene ki dan kwada min Zogale yanzu" Nene ta galla mai harara Zaid ya fice yana daria.

Baka jin komai sai k'aran Ac din da ke Parlorn, kamar ba wasu hallittu a ciki, tana nan durkushe a k'asa, shima daga dayan gefen yana durkushe a k'asa, Nene ta kalli wannan ta kalli wannan, da ta ga zaman bana k'arewa bane sai ta tashi ta fita, to hakan ma bayan fitar ta, sai da suka fi 15mins, ba wanda ya tanka ma danuwansa, Seebi sai wasa take tayi da 'yan yatsunta, shi ko tarrarabin yanda zai fara mata magana yakeyi, sai ya bude baki zai yi magana sai ya kasa, kirrr yaji wayanshi alamun shigowar message daga Uncle Zaid, ya bude message din *"Drop the Ego, Pride and Whatsoever, Tell her how much she mean to you, Tell her how much you love her"* Rafeeq ya karanta message din yayi dan guntun tsaki, shifa abunda ke bashi wahala kenan bayani da baki, ta ya zai fara mata wasu surutai, ya sake sakin tsakin. Bayan nan ma wani mintuna goma suka k'ara shudewa, Nasiba ta aiyana a ranta ba zai mata magana ba, Uncle Zaid yayi kuskure da yace Feeq na sonta, ta mik'e tsaye tayi hanyar Sama, be an kara ba sai ganinta yayi zata fara taka bene, guntun tsaki yayi yayi saurin shan gabanta, ya zuba mata daradaran idanuwanshi cikin nata, da sauri ta runtse ido, wani kallo yake binta dashi, yana k'are mata kallo, nishadi na shigar shi, cikin kasan mak'oshinsa a hankali ya furta "Naseeebahh" a hankali ta soma bude idonta ta sauke su fes a kansa, ba zata iya jure kallon shi ha ta kawar da kai gefe, toh anzo gurin, besan me zai ce mata ba, sun kusa minti bakwai a tsaye ya rasa ta inda zai fara magana, sai ya bude baki zai ce wani abu sai ya kasa, da ta gaji da tsayuwa tace "Hamma zan hau sama, ka dan matsa daga hanya" Rufe idonsa yayi ya fara zubo zance kamar Radio, shi kansa be san me yake fada ba ga abunda yace "Nikam Soyayyah bata cikin kaya, love was Really not my thingy, I was a real time Player, banda burin Love, because a gani na bacin lokaci ne, I had more than a Hundred Girlfriends, banda Damuwa ko kadan, all i do is Eat, Pray, Sleep, Dump a girl, Repeat... Why? Because i am Rafeeq Freaking Lema. A rana daya mata fiye da goma za su kawo min kansu su bani kansu tun kafin na shiga Jami'a, amma sai Allah yayi ni ba mazinaci bane, Allah ya jarabbeni da k'addarori da dama, na shiga halin Bakin Duhu ta yanda na cire rai daga rahamar Allah, duk da haka abun baya damuna, i enjoyed myself being the IDGAF (ban damu da kowa ba, lols) about anybody, not even my Dad, the only humanity left in me was the love of My Uncle Zaid, Ibada ma a lokacin zan yi ta, amma ba kamar yanda ya kamata ba, Sallah ma sai na ga damar yinta nakeyi, na shiga Halaka fa ba tare da na nuna damuwa ta a hakan ba, Rana daya Allah ya jefo ki cikin rayuwata dalilin Sanadi, Sanadin Alkhairi, Naseebah, tun farkon haduwar mu dake na san Akwai Dalilin da ya sa ki ka shigo rayuwata, tun farkon haduwar mu na fara ganin haske a rayuwata, Damuwar wani ba damuwata bane ba, amma damuwarki damuwata ce, na fara damuwa da lamarinki, duk yanda na so in k'untata miki, ina kasawa, theres Something about you that i just dont know how to put it, amma All i know is KE ALHERI CE, you are a Blessing, you and your Entire Family, and let me say Something that i've never said to you in a Nice way, THANK YOU, Thank You Naseebah Muhammad".
Zatayi magana ya katse ta hanyat cewa "Shhh, ban gama ba, thats a short story, And this, i dont know how to put this, i am not good in expressing myself, from What i noticed, Baki da Damuwa, baki da Hayaniya, Baki da matsala ko kadan, Unlike your Neh-neh" Murmushi mai sauti tayi, ya sausauta murya cikin murya me kama da Rad'a yace "Ina Sonki Seebin Nene, Ina Sonki Sosai" wasu zafafan hawaye taji sun fara sauko mata, Hawayen Farin ciki, rudewa yayi ganin tana fitar da hawaye, guntun tsaki yayi ya ciro Handky daga cikin Aljihun shi, "Lord of Mercy! Fine! Ba kya sona shiyasa kike kuka, ki share hawayen ki, kiyi hak'uri, I know what to do, Zan bar garin kafin daurin Auren, don nasan Uncle Zee ba zai taba saurarena ba idan nace na bazan aureki ba, kinga idan bana nan ba zaa daura auren ba" a ranta tace "What is his Problem? Why is he acting so stupid? Tana so tace mishi tana sonshi, tana so ta gaya mishi tana son aurenshi, amma dole ta share shi ko don ya cire wannan zafin rai din. Ta goge fuskarta, yace "Cry nomore, forget all i said, kawai consider everything i said a mistake" haushi ya tunik'e ta, ra6awa tayi ta gefenshi ta hayewarta Sama ba tare da ta ce dashi komai ba. Guntun tsaki yayi ya bi ta sama da sauri, don gani yake idan ya barta ta tafi he's lost her forever, kuma baya son wannan damar ta wuce shi, Sake shan gabanta yayi, ta daure fuska tace "Lafiya? Hannun ta ya kamo ya rik'e, ya murza a hankali, kasa kwace hannunta tayi, sai dai ma ta runtse idonta, don tana iya hawaye, a hankali yace "Baby" da sauri ta vude idonta yace "please dont go, dont leave me, I love you so much Wallahi, i want to be with you, i cant live without you, You are my Forever" wani murnan dadi ya risketa. Bari ta dan ja ajinta, sai ta yi k'okari wucewa yayi saurin tare ta, ji yayi ya ba kanshi haushi meyasa ba zai barta ta tafi ba, meyasa ba zai barta ta wuce ba, yana da Pride but shes stomping on his Pride, yana Son k'yaleta, amma son da ya ke mata ya wuce nan, daure fuskar shi yayi tamau, yace "Baby listen to me, i dont care if you love me or not, all i want is fr you to be here, all i want is your presence, I just want to be with you, i dont know much about Love, but what i believe is that
'You don't have to be in a relationship before u love somebody' i hid my love for you for a long time, i dont regret loving you withou you knowing, i dont mind keeping it much longer without admitting it to you, because thats the way I love, I love inside my heart Thats the way i show my love. i love you so much, i love only you, Oh God! Enough of this, i've said enough, i am not asking you to Love me back, I know i'm one hellof a guy, but all i want is for you to please Stay with me, stay around."
Kasa magana tayi saboda wani yanayi da ta shiga, da ya lura da hakan ya sake kamo hanayenta ya murza a hankali yace "You have the whole day to think about it, I'll respect all your decision but please don't choose to leave me, I'll be a better person for you, I'll make you believe in me, I can be what you want me to be, I'll make you see that I can be anything, you want from me I promise" ya saki hannunta ya sauka k'asa ita kuma ta haye Sama tana jin wani farinciki Mara misaltuwa.
A k'asa yayi kicibus da Nene, da alamun La6e ta musu, wani Murmushin me k'ular da mutum Nene ta ke ma Rafeeq, ya tsaya daf da ita ya murtuk'e fuska kamar ba shi yanzu taga yana kwantar da kai ba, yace "Ya akace?" tayi daria tace "Miskili kafin Mahaukaci ban haushi, kai Dunkum kar ka ga turanceta ka gama yi, na fahimci komai wallahi, ashe nima ina jin turanci bansani ba sai yau, ka tona Sirrin dake ranka, to na daiji komai, ana so ana kaiwa kasuwa, ai Seebi ba irin matan da aka yaudara bane, Allah ne ya kamaka" ta dinga surutu har ya fara ji kanshi na sarawa, ya dode kunnensa yace "Kina da Hayaniya, haba ki dinga shiru mana" ta daga kafada tace "Shikenan, da zan je in shawo maka kanta ne, ta amince ta aureka amma tunda baka so kaga tafiya ta" ta juya "Oh Shit" yace ya bi bayanta tare da rik'o hannunta yace "Haba Neh-neh, kiyi hakuri kinji?" Nene a shek'e da daria tace "to ka gaya min tsakani da Allah kana sonta?" da sauri yace "I love baby more than life itself" ta mai wani mugun kallo ta dai san me I love you ke nufi,amma sauran surutan ne ba tagane ba tace "Uban me kace?" "Oooops ina nufin ina sonta sosai, fiye da komai" ta yashe baki tace "Nima i lobiyu Dunkum" Idonshi ya kada a sama kafin ya rungumeta yace "Sunana Rafeeq" tace "har abada sunanka Dunkum" Ya saketa yace "Neh-Neh ki bar ce min Dunkum" ta buga tsaki tace "Kai ni fa sunana Nene, ka daina ce min wata Neh-neh kamar wata mallamar Choci" ta sake tsakin ya kalleta yayi guntun Murmushi yace da ita "Dunkuma Dangin Tsaka kawai" aiko Nene ta bishi da gudu ya ruga a guje.

"Lesh kana ina?" i've got some good news for yah, alright i'm coming" Mota ya ja Sai Farm house dinsu Maalesh, suna hadewa Rafeeq ya rungume Maalesh, Maalesh yace "Guy howfa? Na dade banga ka cikin irin farincikin nan ba" cikin Doki Rafeeq Yace "Aurena da Naseeebah in 10days time" Are u kidding me? No i'm not wallahi, nan Feeq ya kwashe komai ya gaya mai, Sosai Maalesh yayi murna tare da bashi tabbacin Nasiba na son shi Kawai yaje ya fara shiri, Maaleah yace "Naseebah is a blessing, we have to make her Marriage a meomorable one, dama na san da shirye shiryen su don dama sun sa zatayi aure, So yanzu dai muje mu ga Miemee don k'ara shirya abun, Rafeeq ya daure fuska yace "kaje dai, wannan yarinyar shes lousy, ta cika Hayaniya" Maaleh ta daure fuska yace "danubanka thats my girl, bansan iskanci" Rafeeq yayi daria yace what a perfect match, dukkanku kuna da hayaniya" Maalesh ya kaimai duka.
*******••••••********
"Alright, i know you dont like me, as a matter of fact i dont like you too, but since you are Baby's friend and my Bff's girlfriend, i have no choice than to put up with you" Miemee ta harareshi, tace "Wallahi da zan ba Seebi Shawara taji da nace kar ta yarda ta aureka, now i have to tolerate you" Maalesh yace "oya, Feeq, Beautiful ya isa, Enough of this arguments, gwara muyi shirin abunda zai birge kowa a bikin nan, ba fada na hada ku kuyi ba, dole sai kunyi settling differences dinku" Miemee tace "Fine, barin kira Ushee sai mu hade muyi planning bikin".

Washegari Uncle Zaid ya koma Kaduna don fara shirye shiryen gyaran Gidanshi, Ilu Direba kuma ya kai Mami, Nene da Zainab Kano, Kasuwa sukaje don hado Lefen Zainab, Mami tace ki saki Jikin ki ki zabi duk abunda kike so, kar kiji komai in abu ya miki ki dauka kawai, haka suka hado lefe Akwati 6, a ranar suka dawo Katsina.
Inda WasheGari Kuma Nene da Mami da wasu Yan uwan Mamin suka nufa Kaduna don kai Lefen Zainab.

Gidan shiru daga Aneesa Sai Seebi, yana shigowa ya haye Sama straight, Aneesa ya gani tafi to daga dakin su Nene, ya mata rada is she inside? Anee tayi Murmushi tace "she's in, Goodluck" ya shiga a hankali, ta ja ganinshi tayi wuf ta mik'e tsaye, ya tsareta da idanu, sai ya ga ta k'ara kyau, yace "Baby, ya kike?" cikin muryar da bata san tana da irin shi ba tace "nika bar ce min Baby" yace "Saboda ba kya so na? da sauri tace "Ni ka bar cewa bana sonka" yace "Kina So na?" tace "Ni na hallicceka da zan ce bana sonka?" ya danyi jim, da wata ke wana shi haka da tuni ya ba banza ajiyarta, amma Nasseba ce, ba zai iya shareta ba. Yace "I came for my answer, na baki kwanda daya kiyi tunanin, ki gaya min" ta fara jan aji kamar shi a gurin, tace "Toh tunda Uncle Zaid ya matsa sai anyi auren, ai banda choice ko? Dim yaji wani iri, yace " So You are accepting because of Uncle Ziad? Kai tsaye tace "Ina ganin girman shi i cant say no to him" yace "Baby, i dont care if you are getting married to me For the sake of some, like i said ba ina so ke ki soni bane, i just want me to be loving you, to take care of You, and to give you the best things in life, thats all i ask, amma if really zaki chuta da Aurena, ki gaya min, Wallahi ba zaayi ba, don kinsan your happiness is all i want, amma please kar ki gujeni, ke kadai kikasan yanda zaki zauna dani, ke kadai ki ka shanye abubuwa da dama game dani, Please Baby" duk ya bi ya susuce, ya mugun k'askantar da kanshi, kamar ba Rafeeq Freaking Lema ba, tausyain shi ya kama ta a hankali, ga ta kuma bata dauki duniya da zafi ba tace "Hamma Rafeeq, Please kar ka k'ara hadani da Allah, ka wuce matsayin ka tsaya ka ta rok'ona haka, zan Aureka" Wani farinciki ya lullube shi, shi fa wani abun ma be san yanayi ba, So Makaho ne, idonshi ya rufe, be ji be gani ya shiga Murna, da bata ja baya ba da ya rungumeta, yace "I Love you Baby, say you love me too Please" kunya ya kamata tace "Barin shiga Toilet" ta fada toilet ya yi wani Murmushi ya waiga kan gado ya ga wani dan karamin Ribbon pink color, ya dauka yayi kissing kafin ya bar dakin.

*Satin Biki *

Nene ta nemi izinin komawa Gidanta gun Alhaji Habib, Saboda yanuwanta na nesa da na kusa da zasu zo bikin, Alhaji Habib ya sa aka bude gidan aka share Nene da Mak'arabanta suka koma chan don ba su Mami space su ma danginsu sun fara zuwa, Gwaggon Nasiba da ke Jigawa tazo, tunda tazo ta hau gyara Nasiba ciki da waje,
Ranar Talata aka fara Events, Waazi akayi a Multipurpose, inda Malama Zahida (Mrs Muhammad) ta waazantar da su, ta ja ma Nasiba kunne kan bin miji da shawarwari da dama. Ranar Laraba kuwa Bridal Shower ne, Miemee ta fi 1 daya tana ma Seebi kwalliya, bayan ta saka wata Azababen gown milk color ta daura karamin Crown a kanta an baza gashin da ya sha Stretching a baya, Nasiba sai da ta tsorata da ta ga kanta a Mirror, tayi wani irin Masifar kyau, bata taba irin wannan kwalliyar ba, ta kalli Miemee tace "wai haka zan fita gurin nan?" Miemee ta harareta, to uwar ustazai, ko a kawo miki Nikab ne?" Usheey tayi daria tace "Nasiba kar ki damu, daga yau shikenan, mu je suna jiran mu" Seebi tace "Wallahi Nene ba zata bari na fita haka ba" Usheey tace kuyi gaba, barij je in janye hankalinta don naga ta rako wasu su gaida Mami" Takalma Me tsini ta saka tana tafia kamar wata bishiya, suna sando kar Mami Ko Nene su gansu, Miemee na jan hannunta iya kuka tana tafia dakyar sakamakon takalman ta, ba ta ankara ba taji ta bige wani abu, baki bude yake kallonta, Wai Naseebah ce nan? Kallon kallo suka tsaya yi, Miemee ta tabe baki tace "Muje Seebi, friends na chan na jiran mu" bakin Seebi na rawa tace "Ok" zata ra6a shi ta wuce ya kamo hannunta, wani yar taji, Miemee zatayi magana yace da ita, "ki tafi, zan kawota" Miemee tace please "Yaya Rafeeq, sauri fa muke, past 5" yayi dan guntun tsaki ya kawar da kai gefe, shi be saki hannun Seebi ba shi be ce komai ba, Seebi tace "Sorry Miemee, ku tafi ga mu nan zuwa" Miemee tace "Argh, Wallahi Mijinki dinnan sai a hankali"tayi gaba, Rafeeq ya wani wana kanshi a sama, Wani mayatacen kallo ya bita dashi, duk ta bi taji kunya ta tsargu, baki na rawa tace " Hamma, suna jirana, tun dazun suke min waya, we need to go please" matsowa yayi daf da ita ya kai bakinshi kan kunennta tare da fadin "You are a Blessing Baby(KE ALHERI Ce), I Love you with all My heart"
Aikam jikin Nasiba ya hau kyarma, ba ta son yana kusanto ta haka, ya lura da halin da yake ciki, ya kashe mata ido yace "Yadai Baby?why are you blushing? Do you want me to kiss you?" ai da sauri ta juya har tana turgude wa, yace "Hey easy mana kar ki fadi, wasa ne" ita dai bata da sukuni sai da ta ga ta yi nesa dashi, still dai cikin motar haka ya dinga binta da kallo har suka iso Soli Center idan zasu yi Bridal Shower din.
Yace "Oya Baby, have fun ina nan ina jiranki"
Ta kalleshi tace"Hamma ka tafi ba maza" yace "I know, Event din mata zalla ne, an gaya miki da harda maza zan bari ki fito haka ne? Ina nan ina jiranki je ki gama" tace "Haba Hamma, ka tafi donAllah zamu koma da Su Miemee" yace "Alright Fine, Sai kin gaya min magana me dadi" ta runtse ido tace " Alright Baby, you go now, i'll see you later" cikin murna yace "What did you just called me? Baby?" Kunya ta ji zata bude k'ofa ta fice ya kamo hannunta, ta na waigowa ya kashe mata hoto, bata shirya ma hoton ba, amma tayi mugun kyau, ya musu Selfie, Sun hadu sosai a hoton, wayarta yayi k'ara tace "Hamma lemme go please" yace "I love you kinji?" cikin k'osawa tace !Naji let me go please" ya kai hannunta kan bakinshi yayi kissing, ta waro ido yace "yadai?wannan zare ido haka? Alright Bye, Call me when you are done" ya mata unlocking k'ofa ta fita, Su Miemee na jiranta a Entrance suna shiga aka sa ihu, Bridemaids sun sha kyau sun gaji, haka aka fara gudanar da bridalshower.
WasheGari kuma Iyalan Gidan Lema da Seebi suka wuce Kaduna banda Nene don jamaa sun Mata yawa, A ranar zaayi Arabian Night din Aunty Zee da Uncle Zee, sun isa wurin k'arfe 1, Straight Gidan Su Aunty Zee sukayi, an karbe su cikin mutumci, Mami ta shiga Sallah, Umma ta sa aka raka Seebi gidan da Amare suke, inda Ake yaryara ma Aunty Zee Lalle ja da Baki, sunji dadin ganin juna, Aunty Zee tace "Yauwa ga dayar Amaryar nan, ita nace zaki ma wa" Me lalle tace "aiko ga ta nan tayi shanb'ar suka dara".

Arabian Night
Larabci kawai kakeji na tashi, saboda K'awayen Aunty Zee da sukazo daga Sudan Maza da Mata don tayata murna, Ko wanne ka gani da Jallabiya jikinsa,
Seebi ta sa Jallabiya baka tayi kyau Sosai, ta bi Amare gurin Dinner, motar su ta tsaya, ta fito, Wayarta taji yayi Ringing ta ciro Baby na ta gani, tana dauka yace "Uhibukki kasiran ya habibty" daria tayi sosai, yace "kinyi kyau sosai Baby" tace "Da larabci zaka fada hakan ma" yace "Na farkon ma Uncle Zee ya gaya min, and i really cant remember" daria tayi tace "Munzo gurin dinner" yace "ai ina kallon ki kinyi shigar larabawa" waige waigen idan zata ganshi ta farayi, yace "Duba hagunki, ta na duba wa kuwa sai ganin shi tayi kan wani Black RangeRover spot, rabin jikin

Please Login or Register in order to submit comment