Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zaid yace "Yaya wai ne ya faru? Wani Sak'o Nasiba ta kai maka? Ajiyar Zuciya Alhaji Habib yayi, ya fayyace musu komai tun haduwar su a Gun mallam, har zuwa yanzu da ta kawo mai magani, Zaid ya jinjina kai yace "Ashe ba nikadai nake ganin Nasiba kamar marigayiya Rafee'ah ba" Nene tace "kama sukeyi ne wai?" Alhaji Habib ya bata amsa "basa kama anma yanayinsu iri daya komai" Rafeeq dai be je komai ba, sai kallont yakeyi, ita kuma hankalinta baya nan yana gun Aymana da ke rik'e a hannunta, hayaniyar Nene ya hanata bacci, Zaid yace "Yaya to maganin dai ka sha su yanda ya kamata, don ka daina jin Yanda kakeji Allah ya sa a dace" yace "Amin" Zaid yace "Feeq ka je gida ka kwaso kayan Ayman, dare na k'ara yi" a zucciye yace "Seriously shes sleeping here? Cikin daga murya Zaid " Yes Rafeeq, shes sleeping here" kamar zaiyi magana ya fasa ya wuce fuuu kamar zai tashi sama, Nasiba ta bishi ido a ranta tace"why? Yana da matsala ne don zata kwana nan?" ta ta6e baki.
"Engr. nace baza ka kai Rafeeq gun Malamin nan me magani ba, yana maganin Sihiri ko asiri, ko aljannu, da masu taurin kai, abunda ya sa na yarda Mallamin, ba dan tsubbu bane, kuma be aiki da Aljannu, da kalmar Allah da Adduoi da suek a cikin Kurani da Hadisi ya ake amfani, ba a san inda zaa dace ba, wannan zucciya ta Rafeeq na bani tsoro" Zaid yace "Duk da akwai Chanji a halaiyar Rafeeq zan kai shi a duba shi, Nasiba kin san wurin ai? Idan kim dawo school gobe sai ki rakamu, Nasiba tayi gyaran murya tace "da akwai abunda baku sani ba Uncle, Rafeeq Yana na magani already, ko yau da Daddy ya ganni a gun Mallam Ruwan maganin shi na koma an so mai don wanda aka bashi da farko ya k'are, Ruwan Adduoi ne, ya maida shi ruwan sha, in kuma a gidannan zai ci Abinci, to da ruwan maganin ake mishi dahuwar, sai kuma Wani maganin hadin magunguna, shigen naka ne Daddy, shi maganin zai sa mai hakuri da dangana a zuciyar shi, to Alhamdulilah an fara samun Nasara".

"Allahu Akbar" inji Daddy, "Engr. Ka lura da wani abu game da Rafeeq bayan dawowan ka?" Zaid yayi murmushi idonshi kan Seebi, duk ta gama tafiya da imanin shi tsaf, maganarta yanayinta, komanta y bureshi, yace "eh Yaya, Rafeeq is somehow changed, naga chanji wallahi, ashe akwai silar chanjin shi" Nene tayi magana, tace "ai da Mahammadu yazo ne ya mishi wuriwuri har ya amso mai magani ya kuma tilasta mai sai ya sha, yanzu ms zai dawo in bashi na yau" Daddy yace "abunda bangane ba, shine Zaid dama kun san su Nasiba? Ya abun yake?" Nene ce taba Daddy labarin daga farkon haduwan su Zaid har zuwa yau, Daddy ya jinjina kai dama akwai irin mutanen nan? Masu maida damuwar wasu nasu? Kuma tsakanin su da Allah? Ba don wani abu ba? Kai su Nene ba abun yadawa bane, mutanen Arziki ne, ashe sune Silar saukowan da Rafeeq keyi yanzu, Allah ya musu Albarka, Lallai su Nene *ALHERI NE* a rayuwar su.

Daddy yace "Inna Mungode k'warai da wannan karamci naku, ba abunda zan iya biyanku dashi, amma ina so in dauki Nauyin karatun Nasiba, wallahi a sanda na fara ganinta na fara Sonta, irin So din da na ke ma diyata Rafee'ah, donAllah ku bani wannan damar" Nene tayi darian murna tace "Ai jahili ke maida kyauta, an baka dama,Allah ya bar zumunci" duk suka amsa da "Amin" ya cigaba da cewa, "My daughter, ke kuma daga yau if you ever need anything, come straight ahead and tell me, dont hesitate to tell me, zan baki number na, you can easily reach me" tayi godia Sosai. Nan Rafeew ya shigo da Sallama, suka amsa mai, Akwatin Ayman ne sai kayan wankan ta, sai kwandon Abincin ta, Seebi ta taimakeshi ta shiga da kayan cikin dakin Nene, tana jerawa bayan ta kwantar da Ayman kan Gado ta sakar mata Net don kar soro su cijeta. Nene ta kalli Rafeeq ta tuburne fuska tace "ai sai kaje ka dauko maganin ko?" bakin shi ya turo ya mik'e yana gunguni, dakin ya shiga saman wardrobe inda ake ajiyewa ya dauko ya kalli Nasiba da take ta ririita Ayman tana bacci ya ta6e baki ya fita da robar maganin, kitchen ya shiga ya zaro chokali, Daddy da Uncle Zee suka bishi da ido, yanda yakeyi kamar yaron da ke tsoron magani, duk sai ya basu daria suka gumtse. Kawar da kai yayi ya mik'a mata, ita ma ta kawar da kanta ta amsa, su a dole basa shiri, ta bude ta tsiyaya mai, kamar kullum ta toshe hancin shi ta dura mai, tare da gumtse bakinshi har sai da ya hadiye, guntn tsaki yayi yace "kina da matsala" ai ko igiyar chajin radion kusa da ita ta wawuro ta shauda mai a baya "Ouuuuchhhh!" ya fada yana sosa baya, da Daddy da Uncle Zaid suka tuntsire da daria, ya kallesu yace "Its not funny it hurts" Nene ta mik'e tace kana so in k'ara ma ne? Ba na hanaka turanci a gabana ba? Tsaki yayi ya kalle su duka yace "I'm outta here" ya juye ya fita, tana daria tace "ai da ka tsaya mana, kai karatun ka iya Najiriya, da ka tsaya nasa Zaidu bawan Allah shi da yaje Ingila ya turance min kai, ya kafirce min kai da turanci" ai kam Daddy dariya harda rik'on ciki, Zaid ya kalli Nasiba da ke daria k'asa k'asa, yace "are they always like this?" tace "Yesss, they are always like this like all the time" Nene tace "Au kuma turancin ne?" duk suka sa Daria, Daddy ya mik'e yana daria yace "Nene da jikokinta baza ku kasheni ba, nayi Gida" Sukayi Daria har Gate suka rakashi, suka mai Sallama, a waje suka ga Rafeeq zaune kan mota au ashe be tafi Ba inji Nene "kema dai ki barshi donAllah" Daddy yace "R-Lema, mu tafi kaji kar Nene ta sake dukkanmu kai" Rafeeq ya lura duk daria suke mai, to meye abun daria, guntun tsaki yayi ya murtuk'e fuska, ya sauko daga kan motar, ya mik'a ma Zaid mukullin motar shi ya bi bayan Daddynshi, Nene tace "Guznight gaye" kallonta yayi ya buga tsaki tace "Auu, Dunkum dangin Tsaka". Duk suak fashe da daria.

"Seebin mu, zo ki tayani kwasan kaya" tayi murmushi ta biyo shin gun booth, Nene kuwa tayi shigewar ta ciki tana murmushi, Manyan Ledoji guda 3 ya kwaso a booth din, yace "muje ko?" tace "Uncle Zaid cewa fa kayi inzo in tayaka" yace "kuma nagode muje" sukayi daria suka shiga ciki, Nene na nan kan tabarma, ya dire ledojin gabanta yace "Nenenmu ga tsarabarki ta Ingila ga kuma na Seebi" Nene ta bude ta na murna, Seebi kuwa kasa taba ledar tayi, tace "Allah ya saka da Alheri, Nene ta ciro Dogayen riguna marasa nauyi, tana murna, tace kamar kasan ina son dogayen riguna, sai dai kawai na zumbula su, kai madallah madallah da Zaidu dan Albarka, kai ALHERI NE, Allah ya biyaka ya raya Zuri'a, ta dinga shatato mai Adduoi, yaji dadin adduoin ta yace " Amin Ameen" Nene tace ke baki bude taki ledar ba, sadda kai tayi k'asa Nene tace "ke tafi chan shashasha, mik'o min ni in bude" kwalin waya ta fara cirowa, Iphone 6s, sai doguwar Riga mai wando, da dan jacket dinshi me kama da boyfriend jacket, sai takalma, sai kuma kwalin turare, sai kuma chocholates. Nene tace "Anya Zaidu BawanAllah kayan nan basuyi yawa ba?" Nasiba ta kalli kayan ta wutsiyar ido da sauri ta zabura ganin kwalin Apple, tace Uncle Zaid, i cant accept these, they are too much wallahi" ce mata yayi "Shhhh, they are not, they are all yours, and you are accepting all" Nasiba ta girgiza kai tace "Nene kingani ko, ki ce mai sunyi yawa, bazan iya amsa ba donAllah" Nene tace "gaskia ne kayan sunyi yawa, daga gani zasuyi tsada, amma ya zaayi aikin gama ya gama, Ingila ne balle a ce zaa maida su, ya zakiyi dole ki karba, amma nesitym(next time) kar ka k'ara irin wannan kaji? Zaid na daria yace " toh Nene ba zaa k'ara ba" Yauwa danAlbarka, ke kwashe kayan ki kai daka zamuyi hiran yaushe gamo da Zaidu dan Albarka.
*****
"Zaidu gaya min kana Son Seebi ne ko? Don wannan kayan sun fi kama da na toshi" cewar Nene ta na me daga mai Gira, Zaid ya daburce ya fara in ina, Nene da ta dago jirgin shi tace "kai kar ka wani damu, naji ka harda su in-ina, ai tuni na dago Jirginka, Son Seebi kakeyi" Zaid yayi murmushin jin kunya ya shafe k'eya yace "Nene taya kika sani?" tace "kai Zaidu na fa kwan biyu, ko kallon da kake binta dashi ai ya isa in gane, balle ni nan da saurin dago zance nikeyi, kaga ko Maalush sonta yakeyi" Zaid ya dan kallo ta yace "Mahmud dai? Tace shifa, shima kallon da yake binta dashi ne yasa na gano shi, kaga kar ka damu, kar kace baza kayi takara da Maalesh ba, bana zato ya ma sanar da ita, hikima ta ce ta dago min shi, Kayi saurin isar da sak'on zuciyarka gareta, don bana tunanin tana kula wani da namiji" Zaid ya share gumi yace "Nene kina ganin zata soni? Ba za tace na mata tsufa ba?" "Kai dallah tafi chan, kai tsoho ne? Duk tsufan ka ka kai Aminene Mamman? Ko ni zaka aura eyi? Ka manta kai Hadadden mutum da duk mace zata so samun ka? Kai ka kai da ba macen da zata guje ka, ko tace ka mata tsufa, ko da ka kai tsufa na, kaga Zaid, irin Ka nike ma Seebi adduar fatan samu, kaga mu ba makwadaita bane, Mu muna da rufin Asirin Allah, munfiso ayi Aure cikin rufinAsiri da so da k'aunar juna, kagane? Gwara ta aurei wanda ya san darajarta da kimarta, kuma ni Wallahi kai nikeso da Jikata, shawara daya zan baka, ka nemi So gurin Seebi" ya jinjina kai yace "InshaAllah Nene, zan nemi So Gurinta, in kuma Allah ya yarda, Zan auri Nasiba" Nene ta tafa hannayenta, tace yo Seebi zata zama sirikata don ni fannin Ango nike" yayi daria. A bangaren Nasiba ta gama jin komai don Nene ba a yi sirri da ita, ta rasa ganewa murna zatayi ne ko kuwa? Tabbas Uncle Zaid ya kai a So shi, don bai da makusa ko kadan, bata damu da tsufan shi ba, amma ta kasa yarda, Namiji kamar Uncle Zaid yace zai aureta, ai kam ta dace, ta nuna kanta da Yatsa, Wai ni Uncle Zaid keso?. Ba ta ankara ba taji yana kiranta, yace ta dauko mai wayarta zai saka mata Sim a sabon wayarta, duk ta kasa fita, Nauyi da k'imar shi suka k'aru a idonta, da k'yar ta fita tana susuna kai, Nene ta shige ciki bayan sunyi bakwana da Zaid, yanda takeyi ne ya bashi tabbacin taji su, hakan ma daidai ne, ya samu saukin wani abun, ya lura ta kasa daina murmushi, da kyar ta mik'a mai wayar, cikin muryar shi me sanyi yace "Seebin mu ni da Nene yadai? ta dago a hankali ta kasa hada ido dashi don kunya, yace " so you've been eavesdropping? Kinji tace gobe zaa daura auren mu ko? Shine kike ta kunya" da sauri tace "laaahh ba haka tace ba fa, cewa tayi ka nemi So a gurina" da sauri ta toshe bakinta, shi kuwa yayi daria yace "ashe dai kinji komai, so tell me, Zaki iya Auren Tsoho kama na? Ta rufe fuskarta da hannunta biyu ta tura kanta cikin cinya, yace " Magana fa zakiyi 'yanmata na, I love you Seebi, right from the first Day, i want you to give me chance and experience 'the Old School' love" da sauri ta tashi ta shiga daki ta barshi zaune don ya cika ta da kunya, kalaman shi sun mata nauyi, Zaid yayi murmushi, yace "i take that as a Yes" ya kwashi wayoyin duka ya fita dasu, saboda zai kai a yanka Sim din ta window take lek'en shi, ta na Murmushi, muryan Nene ta ji a sama "Hegiya ana so ana kaiwa Kasuwa" da sauri ta murtuke fuska ta fita zuwa kitchen.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg4⃣9⃣

7:45am

"Ayman Zauna kici Indomie kinji?" Ayman ta k'ura ma Nasiba ido kamar me son gane Wani abu chan kuma sai ta fashe da kuka, Nasiba tayi saurin Rungume ta tana cewa "yi shiru kinji babyna in kaiki gurin Mami?" gyada kai tayi, tace ''to kici sai muje gun Mami a Motar Daddy ko?" nan ta shiga bata Indomie din tana ci har ta fara fiddoshi idan ta bata alamun ta k'oshi, Nasiba ta fita da plate Ayman a binta a baya duk inda taje, Nasiba ta sata a baya ta juye ruwan Zafi cikin bokiti ta tu6eta ta mata wanka, ta zo ta mata shafa ta sa mata wasu riga da dogon wando, sai ta sa mata Sweater sabida sanyi, tana cikin haka ne sai ga Zaid yayi Sallama, ai ko Ayman na hango babanta ta ruga a guje gunshi, ya dagata ya chafe, yace "Baby Good Morning" ita ko sai daria takeyi, Nasiba ta fito tana dari-dari ba tare da ta kalleshi ba tace "Ina kwana" cike da k'auna ya amsa mata gaisuwar, yace "Ya Bak'uwa, halan ta hana ku bacci?" Nasiba ta girgiza kai tace "Ai tunda ta kwanta bata tashi ba sai yanzu" a ranta tace "zai so ya san me taci" tace "yauwa taci Indomie kawai, ko akwai abunda zaa k'ara bata? Ya ta6e baki yace " Oho, ku kuka san in ta k'oshi, but ai nasanta bata da juriyar yunwa, da ta ji yunwa za tace miki "Friso" duk sukayi daria, yace "ina Nene?" tace "Nene taje siyan K'osai tun dazun, k'ila akwai layi ko suna chan suna Gardama da Maigadin gidan Lema" dariya yayi yace "wai kullum sai taci k'osai?" tace ai kuwa harda koko da ta dawo zata dama koko, wai idan bata ci K'osai ba ji takeyi kamar mara lafia" Zaid yayi daria yace "Nene Ikon Allah", ya sa hannu cikin Aljihu ya ciro wayarta ya mik'a mata, yace "gashi an yanko sim din" cike da kunya ta amsa tayi Godia. Suka yi dan shiru na wani lokaci sai chan yace "yau ba Lectures ne?" tace "Akwai" yace "to ya? Banga an shirya ba?" tace "ai bazan je ba" ya kalleta yace "saboda me?" tace "Ayman mana" yace "No No No, bamu yarda ba ko Ayman? Jeki ce ma Mummy ba mu yarda ba ta shirya yanzu mu kaita mu jirata ta gama lectures ko baby? Mummy ta maimaita a ranta, tirkashi, yace " Oya Madam, je ki shirya, hubbynki da babynki zasu raka ki Makaranta. Mun baki 30mins to dressup, Oya make it fast" ta tashi cikin jin kunya, bata so ta mishi gardama, haka ta shige dakinta" Daidai nan Nene ta shigo gidan da Sallama hannunta dauke da bakar Leda. Ahh Zaidu BawanAllah har ka iso kenan, yayi daria suka gaisa, ta shiga kitchen ta juyo K'osai din a plate ta shek'a Koko, ta fito inda su Zaid suke dauke da Jug da kwanon ta dire gaban Zaid da ke ta wasa da Ayman, ta koma ta dauko Kofi da teaspoon, ta dauki k'osai daya ta ba Ayman a hannu, Zaid yace "anya kuwa zata ci?" Nene tace bari ka ga ku yaranku sai indonie ko? To bari ka ga" Cikin saa yarinya ta hau cin k'osai, Nene ta fashe da daria tace "Yarinya is know K'osai" Sosai Zaid yake daria, harda k'warewa, tace "maza muci na san bakayi kalaci ba, ka zuba kokkon" ba musu ya sa hannu cikin plate din yana mai kara son Nene har ranshi bata da matsala wallahi (Anya Zaid? Tambayi Rafeew ka sha labari) chan yace "Nene ina na Seebi?" tace ce maka tayi zataci? To bata ci nai" ita sai Tea da biredi, ko indomie.

"Dallah ki saka sabin kayan da yayi maki tsaraba mana jiya, kinga harda mayafi, ai gwara ki sa yaji dadi" Cewar Nene, "Anya Nene?" "mtssw, in za ki sa ki saka, in ba zaki sa ba ke kika sani" Seebi tace "zan saka" nan ta sa Doguwar riga da ya kusa zuwan mata idon sahu, da dogo. wandon kayan, ta dauko mayafin gyalen ta yafa, yiriri inji Nene, Wallahi jikata son kowa kin wanda ya rasa, wanga kyau haka, wanda be sanki ba yace kamar kin sa A cuci maza, ni ko da na sanki nace Gashi ne, takawar ki lafia Jikar Aminene Mamman, daria ta bata Sosai, ji take kamar ta sa Hijab, anma Nene ta rantse ba za ta sa ba wai ita da tsiya yau sai Seebi tayi shigar Miemee Yar gayu. Maza ki fita Zaidu na jiranki a mota yace, ta dauki Jakkar Makarantar ta, Nene ta ciro dari 2 ta bata sukayi Sallama ta fita.

Wasa yake ma Ayman cikin Mota, ji yayi kamar ana kallon shi, waigawan da zaiyi ya Nasiba cikin shiga ta Alfarma, Sosai tayi kyau, ya fito ya zagayo gunta, ita kunya ma ya hanata shiga motar shisa ta choge tana kallonsu cikin k'auna, muryar Zaid ta dawo da ita duniyar da suke inda yake cewa "You look beautiful Seebi nah, Ayman tell mummy she looks Beautiful" kunya ya sa ta rufe ido, ya bude mata k'ofar gaba ta shiga, duk ta bi ta tsargu, haka suka kama hanya, ta amsa Ayman suna tafiya kamar wasu Maaurata, yana kallonta jefi jefi yana mata magana irin ta masoya ita kuwa Allah Allah take a iso School, coz taji maganganun Bambarakwai, har gaban Faculty ya kawo ta yace zasu jirata tace "Aa Uncle Zaid, donAllah ka tafi, ina nan har 2 a School ka tafi please, yace to in kun kusa tashi ki kirani kinji?" tace "to shikenan" ta shafa kan Ayman ta juya ya kira ta "Seebi" ta juyo tace "Naam" yace "I love you" ai kuwa duk ta daburce ta rasa me zatayi, daria yayi kawai ya ja Motar shi yayi gaba ya barta tsaye, Ji tayi an dafata, a firgice ta waigo ganin Miemee ya sata sauke ajiyar Zuciya, tace "Seebi waye wannan ya sauke ki? In ina ta farayi, tace "Uncle Zaid ne" Miemee tace "Uncle dinki ne?" kai kawai ta daga ta wofintar da maganar da tambayar Ushee, ta shaida mata cewa bata k'araso ba amma tana hanya.

12:45pm (Hikma Restaurant)

Miemee ta kallesu a karo na biyu, ta lura da maganar da sukeyi k'asak'asa tun a aji, yanzu ma sunzo CAF sun cigaba, da alamu Seebi bata so inji labarin da take ba Usheey, don sunfi kusa, ganin hakan ne ya sa Miemee ta tashi ta basu wuri tace bari taje tayi musu ordering abinci don gudun zuciya, suka cigaba da labarinsu harda kashewa a tafa. Miemee na hangensu, ranta a 6ace it hurt Sosai, yanda ta dauke su ba haka suka dauke ta ba, amma bakomai tunda haka ne she will keep her distance tunda clearly sun nuna mata they dont want her among them.

"Anee Lema, kamar wata nike gani da irin kayan ki" Aneesa da ke cin Dankali ta kalli k'awarta Meesha tace " na lura Kayan nan nawa sun tsole miki ido, to kina ganin su Nikadai ke dashi duk fadin Katsina, jiya Uncle dina ya kawo min Tsarabar, daga England so idon ki ne" Meesha ta girgiza kai tace "Wallhi wanchan da ke zaune tare da me Red veil irin kayanki ta sa, komai harda gyalen" da sauri Aneesa ta juya idonta ya hango mata Nasiba, ta bi jikinta da kallo taga irin kayan ne, Meesha tace "Ko 'yaruwarku ce, Uncle dinku ya siyo muku komai iri daya don kuyi Anko?" Cikin masifa tace "No, wallahi ba 'yaruwata bace, Allah ya sauwake wanchan middleclass girl din? Ko jiya Mum dina sai da ta tambayi dad dina idan suna da Relation, ya kuma tabbatar mata da cewa ba 'yanuwa bane, Aneesa tace " Yariska ce, jiya har gidan mu tazo neman Dad dina" Tabdijam k'ila ma tayi seducing Uncle din naki ya muku siyayya iri daya" Anee tace "Lallai kuwa zan koya maya hankali" ta mik'e tsaye ta nufi Seebi da Ushee da ke zaune.

Tun daga nesa Seebi ta hango Aneesa hanjin cikinta suka kada, ta mik'e tsaye, ai kuwa Aneesa na zuwa ta kamtse Seebi da Mari lafiyayyu har kala biyu, tare da nuna ta da yatsa "stay away from my Family" Seebi dafe da kuncinta, tana hawaye, Ushee tace "haba baiwarAllah me ta miki ne zaki ci zarafinta?" Aneesa tace "ko zaki rama mata ne?" Usheey tayi shiru don ta fi Seebi tsoro, Aneesa yarinya ce ko shekara 18 bata rufe ba, amma girman jiki ne da ita, girmanta zai sa ayi zaton Babba ce shiyasa ake jin tsoron ta, "kuma Wallahi kije ki cire kayan nan, duk randa na sake ganinki da su sai na wulakanta ki" hankalin mutane ya dawo kansu, sunsan Aneesa Lema da Masifa, wani yace "kema kije kiyi yanda tace mana" da sauri Seebi zata juya ta tafi taji an rik'o hannunta tana dagowa taga Miemee tsaye, tace "Ba inda zaki, in Uban wani yace ta sa irin kayan da kika sa sai taje ta cire tunda tafi k'arfin a ga ta sa irin kayan ki" "Ke kuma wacece yar shiga sharo ba shanu?" inji Meesha, kallon Ke gara Miemee tayi mata, tace "Rama marinki" Seebi ta girgiza kai, Miemee cikin daga murya tace ki rama Marinki Nasiba Muhammad" Aneesa da mamaki ya gama kashe ta tace ke banza ke wacece? Ba zata rama ba ko zaki rama mata ne?" kafin ta sake wani magana taji an kaure da mari kala 2, Miemee ce da k'arfin halin nan, Usheey da Seebi da kowa na gun na mamakin Miemee, Miemee ta nuna ta da yatsa tace "She's my Friend, f**k her up, and i'll f**k u down" Aneesa cikin borinkunya tace "We'll meet again, this is not the end of this, Meesha get my bag" tafita ,Meesha taje ta dauko jakkar ta bi bayan Aneesa.
*********
Usheey tace "Seebi me ya hadaku da ita ne?" Seebi na kuka Miemee ta tashi zata bar gurin, Usheey tace "ahh Miemee ina zaki?" tace "i'm giving you two space, ai naga kamar maganan Sirri zakuyi" Seebi ta dago kai idonta sunyi Jaaa tace "wace irin magana kikeyi wannan? Miemee tace " Seriously? Ai naga sirri kuke tayi tun dazun, kuna magana K'asa k'asa, ba kwa so in ji maganar da kukeyi, to tell you the truth it really hurts me, yanda na dauke ku ba haka kuka dauke ni ba, nice me bakin Reza, da idan abu ya sameni na Sharri ko na Alheri ku nake fara sanarmawa, because i love you two like my sisters, Amma ku kwatakwata ba haka kuka daukeni ba, a ganin ku ni ballagaza ce, da naji zanje fesa ma mutane, i'm not worth sharing your secrets, kuna wareni a cikin ku, ai gwara in fidda kaina" zata wuce Seebi da Usheey sukayi saurin kamota, Usheey tace "haba Miemee is not like that wallahi, ba abun da kike tunani bane, kin tsargu ne kawai, dazun cikin aji nine ma ke bata labarin Usman(Saurayin Usheey) kuma kinsan da labarin, kuma abunda ya sa muke magana a hankali kar Mallam ya fitar da mu yace mun isheshi da surutu, yanzu kuma a CAF ne ta fara bani labarin, tace a bari sai kinzo nice na matsa mata coz

Please Login or Register in order to submit comment