Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin tsaya tsakiyar titi kar mota ta bigeki, people would get hurt people like my Uncle Zaid and Maalesh" tace "koma dai meye you care about the people you love, ba dole sai ni ba, dama ai ni ba kowa bace, amma su ka damu da damuwar su, ka kasa barina sabida su, ka ga kuwa wannan shine abunda nake so ka fahimta, you have a beautiful heart" "ke i dont care about anyone, Uncle Zaid is all i care about and maybe Maalesh,i can sacrifice anything for them" ta mai wani kallo tace "really? To tell me, har yanzu me kakeyi da Zoben hannunka? Me kakeyi da danuwa Zoben da ka ba Maminka? Saboda kana sonta, akwai 6angaren zuciyarka da ke sonta, akwai 6angaren zuciyarka da ke son sake ganinta, fushi da bak'ar zucciya suke hanaka, Rafeeq na girgiza kai yace " Ki min Shiruuu please, Ya isheni Nasiba" da sauri ta kallo shi, a iya saninta da shi ko Seebi bata ta6a ji yace ba, amma yau ita yake kira da Naseeba? Ya ilahi, yaba ta tausayi ama dole ta ya gane abunda yake yi ba me kyau bane, tace "kaga matsalar ka ko? Baka son gaskia, da an fara gaya maka gaskia sai ka tsaida mutum, ita gaskia kwara daya ce kuma daci gareta, Listen now, i am going to make this Straight to you, Incase you dont know, Aljannar namiji yana k'asan tafin Mahaifiyar shi, sai ya bita zai samu shiga, sai da Manzon Allah ya kira Uwa so uku kafin ya kira Uba so daya, ko kasan duk wanda ya sa Mahaifiyar sa kuka be ganin daidai? Ka san iyakar hawayen da tayi a kanka? Kasan zunuban da kake kwasa a ranar da tuna da kai ta zubda hawaye? Ya Illahi! i dont have to lecture you on this, kai kasan wannan abun amma fushi ya hanaka ganin hakan, ka ta6a tambayan kanka? Shin yanda nake ma Iyayena musamman Mahaifiya ta ina kyauta wa? Duk abunda ta mun tun ina cikin ciki har girmana ta chanchanci abubuwan da nake mata, kai ko me tayi, She's still your Mother, ko kisan kai tayi, she'll remain your mother, balle something you are not sure of, something no one is sure of, You didnt bother to find the truth, kai an maka laifi, ba wanda ya kuma isa ya ce kayi, ask yourself if this is the way you want your children to treat you when they're grown. Don abun da kayi shi zaai maka wallahi, fiye da ma wanda kayi, dole a maka, If you're not measuring up, it's not too late. You can make a change this very day. Uwa ta fi karfin wasa Wallahi, ka tashi ka fusknaci matsalar ka tun kan dare ya maka, tun kan ka wayi gari ace ba kai ko ita a duniya, Only then zaka higa damuwan da yafi wannan matsi i've said my peace" ta na kuka ta ciro paper da biro tayo rubutu, ta ajiye mai a cinya, tace "gashi this is her address, bance kaje ba, you decide what to do with it, ina so kayi tunani, ka tuna Who is your mother" ta share hawayenta ta bude motar ta fita tabar Rafeeq zaune kamar gunki.

Hannu ya sa a kai ya damk'i gashin kanshi, Jijiyar kanshi kamar ta fito, Nan ya soma tunanin halin da ya iske Mami a ciki, sai ya tuno ծaծծaծan lokuttan da sukayi da Mami Daddy and Rafee'ah ad a Family, Ya tuna wacece Mami, abunda be taba yi ba, kanshi ya hau sarawa, ya kusa Minti 30 bayan fitar Nasiba yana hawaye, hawayen da ya rasa na meye, ya kunna motar shi ya fita a guje kamar be shirin tashi Sama" Nasiba ta fito daga maboyarta tace "Allah ka sa yaji, Allah ya tsareka R- Lema".

_Malali Kaduna_

Shigowar ta kenan daga Gidan Ummin Anan, ta mik'a musu Coolern Danwake, don yau Danwake tayi, ta kalli agogo taga k'arfe 3:16, tace kaii bari inyi bacci kafin laasar tayi, kan kujera ta dan kishingiծa ji tayi motsin mutum tana dan kallo kofar ta ga Mutun tsaye, jiki na 6ari ta mik'e tsaye, ta kasa yarda da abun da idonta yake gane mata, baki na rawa ta nuna shi da yatsa tace " Rafeeeeeeq" A hankali yace "Mamiiiii" Da sauri ta runtse ido daidia digar hawayenta tana adduar kar ta farka da wannan mafarkin da takeyi, yau Rafeeq ne ke kiranta da Mami? Ba zata so ta ta6a tashi daga barcin nan ba, takowa yayi kusa da ita ya sa hannu ya share mata hawayen da ke zuba a idonta, jin an tabata yasa ta gane ba nafarki bane, a hankali ta bude idon ta fes kan fuskar shi da ta koma ja, girgiza mata kai yayi, da sauri ta rungumeshi tana kuka, "Rafeeq, Rafeeq my Child, Rafeeq ka yafe mini, Rafeeq na hallaka rayuwar ka, Rafeeq ka yafe mini DonAllah" shima kukan yakeyi sosai, kukan da be taba irin shi ba, yace "Mami meyasa? Mami Why? Why? Why?, Mami meyasa zakiyi haka?" ta dago da sauri tace "Wallahi bansani ba, bansani ba Rafeeq, ni nasan banda mafita, Allah kadai ne gatana shi kadai yasan me ya faru a wannan ranar, amma Wallahi bansan komai da ya faru a ranar ba i totally have no idea, please believe me my son" Zuciyar shi ta tambayeshi Wai kai dama tun farko meyasa ka yarda da Mamin ka zata iya aikata abu makamancin hakan, ita da kullum take maku Nasiha kan ku nissanci Zina, wata Zuciyar tace da idonka ka ganta" da sauri ya kawar da tunanin nan, ya sake rungume ta, yace "it doesnt matter anymore, ba zaki iya aikata hakan ba, i was blind to see, we all were blind to see the good in you, but not anymore, I swear on my Dead Sister whoever did this to you will pay" tace "Aa Rafeeq kadaina irin rantsuwar nan, be da amfani, ba kyau, kuma dont let anger have control over you, calm down" Yayi ajiyar Zuciya yace "Mami, whatever i said to you in the past, please forgive me, i dont mean any of it, i was stupid to forget who You are, someone said in har kina fushi dani ba zan taba ganin daidai ba ki yafe min" "Shhhh my baby, ba ka min komai ba, I got you, i always do" ta jawo hannun shi ta zaunar dashi ta dinga shafa hannun shi tana murmushi tana ganin komai kamar mafarki, tace "kasan me na dafa? Ya girgiza kai, tace "Danwake" yaui dariya yace kina son danwake har yanzu? Tace "kai ka koya min danwake" ya tashi yace barin zubo mana ko? Ya shiva kitchen ita kuwa ta dubi gabas tayi sujjada (Sujjudush Shukur) tana me godia ga Allah da ya dawo da danta gareta, saura Baban shi da take adduar Allah ya sa shima ya fuskanci gaskia, Rafeeq ya zubo musu Danwaken ya kawo parlor ya ajiye a kan Carpet, ya rik'o hannun Mami ya zaunar da ita a k'asa ya koma ya dibo mai da yaji a kwano yazo ya zauna, haka suka fara ci yana sa mata a baki tana sa mai a baki, hawayen farinciki sukeyi duka, har dai Rafeeq ya koma lallashin Mamin shi har suka gama, ya kwashe kayan ya shiga daki yayi alwala yayi Azahar ya ja su Jam'i sukayi laasar, nan suka hau labarin duniya.

"Allah sarki Nasiba, Nasiba Alheri Ce Rafeeq, Nasiba Alheri ce a garemu duka, ko ba ka fada ba nasan ita ce Silar zuwan ka Kaduna" murmushi kawai Yayi yace "Mami ke ina kika santa? tace "tashi muje gidansu yanzu" yace "aa i want to spend more time with you" tace ba nisa makota ne yanzu zamu dawo, suka nufa Gidansu Nasiba, Daidai shigowar Abbi, Rafeeq na ganinshi yaje ya rungume shi, Abbi ya bubbuga bayanshi, ya ji dadin ganin Rafeeq haka, Lallai in ciwo cuta ce to tabbas addua Magani ce, yace "Jiki yayi kyau Rafeeq, Allah ya sa a dace yayi murmushi" "ina Mutuniyar taka? Nenen ka?" guntun tsaki yayi chan kuma yayi murmushi ya kwashe labarin abun da ya faru jiya ya basu, Dukkansu dariya suke tayi, Abbi ya girgiza kai yace "nace ma Nenen ta daina biyewa yara ta ki ji, ita jinta takeyi kamar yar shekara 15" suka sa daria. Anan yazo ya hau kan Rafeeq, Rafeeq ya daure fuska beson yara, amma ganin idon Abbii da Ummi a kanshi ya sa shi yin yak'en dole, Anan na matukar kama da Nasiba, yace ka san Adda Seebin Nene? Kai kawai Rafeeq ya gyada, to ka tafi dani gurin su" Rafeeq ya mik'e tsaye yace "Idan anyi hutu kaji" ya kalli su yace "Ina so in koma Katsina yanzu" Mami ta zaro ido tace "Feeq 5 saura fa" yace "eh Mami" Abbii yace "da dai ka bari gobe" yace "Gobe zanyi test karfe 8" nan dai suka mai Allah ya tsare hanya, ya ja hannun Mami suka wuce Gida, sun dade suna magana, tace "R-Lema anya ba zaka bari sai gobe? 6 har tayi fa" yace "zan tafi dai, your prayer keeps me moving" bmya rungumeta kafin ya sake ta ya shige mota da sauri don ganin zata fara kuka. Nan ya dauki hanyar Katsina ta bishi da Addua "Rafeeq Allah ya tsare hanya ya kaimin kai lafiya, yasa ka iske su lafiya Amin"

_Layout Katsina_
11:45pm

A gajiye likis ya shigo Unguwar, duk ya gama gajia, ya wahala Mota ta tsaya mai gurin Dabai, Unguwar Shiru ba ka ganin kowa waje, abunka da Unguwanin yan gayu kowa na Gidan shi ya kulle, daga nesa ya ke hango hayak'i na tashi kan katangar wani Gida, yace "toufa, wannan hayakin daga ina, ko da ya kusanto gidan sai ya ga Gidan Nene ke ci da wuta, ai be san lokacin da ya fita daga motar ba, Gidan na ta ci da Wuta, ya rasa me zaiyi, da sauri ya dinga kiran wayar Nasiba, tana ringing baa dauka, duk ya bi ya damu, ya nufa k'ofar da niyyar ya bude ya ji wani irin zafi, ya ja da baya, ya fashe da kuka, Uncle Zaid ya fara kira, Zaid be dauka ba a lokacin yana toilet yana wanka, Yayi tsaki cikin kuka ya kira Maalesh, Maalesh ya daga " Guy howfa u never sleep?" cikin rudani yace "Nasiba, gidansu na ci da wuta" "What" inji Maalesh, gani nan zuwa, ya latse wayar, Rafeeq ya dinga kwankwasa ma makotan su Nasiba don suma Katangar ta hau ci da wuta, nan yayi tunanin yan kwana-kwana(Fire fighters), ai kafin ya samu taimako daga Makota k'ila gidan ya k'one kurmus, hannu na rawa ya latsa numbern Daddyn shi" a lokacin yana kwance ba dai bacci yakeyi ba, yana tunanin Wani abu ne da be san meye ba, ya ga kiran Rafeeq, ya daga da Mamaki "Ibn Zaid ya akayi da daren nan haka?" baki na rawa cikin kuka yace "Daddy, Daddy" Ya tashi a firgice yace "What isit son? Calm down and Talk to me" da k'yar yace "its Nasiba and Neh-Neh" zumbur Daddy ya mik'e yace "me ya samesu?" gidan su na ci da wuta, Daddy bansan me zanyi ba" Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Stay still son gani nan zuwa, i'll make some phone calls" ya tashi ya zumbura malummalum dinshi kan dogon wandon da ke jikinshi, ya dialo numbern shugaban Fire Fughters ya sanar dashi komai suka bashi tabbacin yanzu zaa su fito don ceton su"
Zaid ya kira Rafeeq bayan ya fito daga wanka, amma Rafeeq be dauka ba, a lokacin makocin su ya bude gida ya fito da yaranshi maza sun fara zuba ma Gidan Nene ruwa, amma kamar ana k'ara rura wutan, Maalesh ya kira Zaid ya sanar dashi, hankali tashe ya bar Hotel din ya nufo gidan Nene, a tare yan Fire fighters da Daddy suka iso, sai Maalesh, Rafeeq ya rasa sukuni, tuni Yan kwanakwana suka kuna injin suka kashe wutan Gidan Nene, Hankalin su a Tashe, Rafeeq ya dinga bubbuga gidan Nene amma ba alamun akwai me rai a ciki, Da K'arfi yace duk sun mutu kamar wani zautace, Maalesh cike da tashin hankali yace "Noo ba su mutu ba, we just need to get in" Rafeeq ya kalli yan kwanakwanan yace "Someone should break the Goddam Door" sai ya fashe da kuka, Zaid na fitowa daga motar ya nufo su, Rafeeq na ganinshi ya rungume shi, Zaid ya dinga bubbuga bayanshi yana kiran they'll be fine, Rafeeq yace "Noo Uncle, i cant loose them both, i cant" Daddy ya taba bayan Rafeeq yace "Rafeeq ka gani an 6alla kofar, yanzu zasu firdosu a kai su Asibiti, InshaAllah they are going to be fine" Rafeeq ya waiga ya ga Jamian sun 6alla k'ofar a sittin ya ruga gidan ana rirrikeshi yana fizgewa ya kutsa kai ciki, Zaid bi bayanshi Daddy da Maalesh suka rikeshi, Zaid cikin tashin hankali yace "No he cant get in there be da facial mask, Rafeeq ka fito please" Attishawa ya fara yi amma be fasa kutsa kai ba, ko da ya isa har ya ga sun dauke Nene kan Gadon marasa lafia sun saka mata Oxygen zasuyi waje da ita, sauran kuma suka nufa Nasiba, bangaje su yayi ya nufe ta yana Attisahawa da Tari ya Ciccibi Nasiba kamar jinjira, ba alamun numfashi a tattare da ita, fadi yake "Hey hang in there, i cannot loose you too, i lost Rafee'ah" kamar mahaukaci yake sunbatu ya fita da ita, be tsaya ko ina ba sai motar shi, baya ya sakata, ya shiga ya ja Motar, Maalesh na kwala mai kira amma ina sam baya ji, Officer yace da Daddy "ku tsayar dashi, she needs First Aid, Oxygen zamu saka mata, she needs it now, Daddy yace i'm sure Asibiti zai kaita" Officer yace "i'm afraid kafin a kaita Asibiti maybe ta mutu".

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Kin chanchanci Yabo a guna Masoyiyar Asali, Wannan page din naki ne Ag😘

Pg5⃣1⃣

Yana tuk'i yana kallon bayanshi hawaye na zuba, sambatu yakeyi, "DonAllah kar ki tafi ki barni, Rafee'ah ta yafi, kema kar ki tafi, bansan me zanyi ba in kika mutu, Ya Allah kar ka dauki ranta, Allah ka dauki nawa instead" ireiren maganganun da Rafeeq keyi kenan, Sanyi ACn Motar ya sa Nasiba farfadowa, tari ta hauyi ai da sauri ya juya ya kalleta, wani murmushin da be san lokacin da ta subulo ba ya sake tare da taka birki ya tsaida motar, fita yayi ya koma baya, hannunta ya rik'o Yace "Naseebah, Naseeba are you Ok?" tari ta shiga yi ba sassautawa ta zame hannunta daga nashi tace "I'm fine, ina Nene?" yace "Tana chan gurinsu Uncle Zaid" Nasiba ta shiga tuno abunda ya faru tiryan tiryan, tace "Hamma mu koma donAllah, Nene na chan ban san halim da take ciki ba" yace"karki damu nasan Asibiti zasu kawota, right now i need to take you to a hospital" tace "please mu koma, i'm fine now, i just need Water" da sauri ya dauko mata ruwa a gaban Seat, ya bude ya bata ta kwankwada" cikin sigar lallashi yace "Listen to me, zan kaiki Asibiti a duba ki, Neh-neh kuma is in safe hands, barin kira su in gaya musu kin farfado mu hade a Asibitin" Maalesh ya kira, "Maalesh kuna Ina?" cikin damuwa yace gata nan zamuzo "Alheri Clinic don ya fi kusa" "bata farfado ba?" Wallahi kuwa feeq, gatanan ko numfashi batayi" Rafeeq ya cije hak'oranshi, yace mu hade Asibitin ni na kusa ma" sukayi Sallama, Seebi tace ya jikin Nenen? Rafeeq ya fita ya koma matukin direba tare da cewa "gata nan zasu kawo ta wanchan Asibitin".
*****
Daidai isowar Ambulance, aka fito da Nene aka shiga da ita ciki already Daddy ya kira Dr aka yi da Nene Emergency, da kyar aka samu suka tsaya daga waje,Seebi kuwa ta k'i yarda a bata gado acewarta ba inda ke mata ciwo, Dr's suka buga nan suka ta6a nan ba alamun Nene Zata motsa suka dukufa da aikinsu a matsayinsu na Kwararrun likitoci.
Bayan 'yan mintoci Likitoci suka fito fuskar su ba Annuri.
Dr Sami yace "i'm so sorry, we couldnt save her" luuuuu Nasiba ta zame k'asa ta zauna dabas, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun inji Daddy, Zaid Ya dora hanayensa duka biyu akai, Maalesh ya fara matsar kwallah, Wtf? Inji Rafeeq, ya chakume shi, what do You mean by you couldnt, save her huh? Dr Umar yace "kuyi hakuri, kamar tana da Athma, kuma ta shaki hayak'in Sosai, kuyi hakuri Addua kadai take buk'ata" Bangaje shi yayi ya shiga dakin duk suka biyo bayanshi banda Nasiban da Hawaye ke ambaliya a fuskarta, Nene ta rasu? Nenenta? Inalillahi, Nan da nan ta chanza kammanni sabida kuka, tausayi Mahaifinta da Goggonta da ke Jigawa ya kamata, suna mugun son Nene (kamar yanda Iyalan Zailani keson Tsoho, lols) kuka takeyi sosai me hade da Sheshek'a, ta kasa yarda da Nene ta Rasu. Rayuwar da sukayi ya fara dawo mata, ta mik'e Zumbur ta shiga dakin.
Kwance ta ga Nene an rufeta da zanin Gado, Uncle Zaid ta fara kallo, har yanzu be sauke hannunshi daga kansa ba, yana kuka mara sauti, Alhaji habib be daina Salallami ba, Maalesh na kuka, Rafeeq na kwance kan jikin Gawar Nene yana kuka, Neh-Neh DonAllah ki tashi, DonAllah, Neh-neh kin zama wani Jigo a cikin Rayuwata, na k'i yarda kin mutu, in kika mutu bansan ta yanda Zan cigaba da Rayuwa ba ke a cikinta, Neh-Neh Ina sonki, ki tashi na yarda ki cigaba da cemin Dunkum, zan amsa sunan, ba zan k'ara miki tsaki ba, zan dinga shan Maganin nan, zanyi duk abunda kikeso, DonAllah ki tashi, Allah kar ka kashe min Neh-neh nah, Allah ka tada min ita I love you Neh-Neh. wani kukan me tsuma rai Nasiba ta fashe dashi, duk sun tausaya ma Rafeeq, Wai dagaske Nene ta Rasu? Shikenan ba Nene? Numfashinta taji ya kusa daukewa itama.
"kai ni Dallah daga ni,ka wani danne min kahon Zucciya, ko sai ka k'ara sani?" da mamaki ya dago ya kalleta yace"Neh-Neh??" tana yunkurin tashi Maalesh yayi saurin taimaka mata ya zaunar da ita, murna gun Rafeeq baa magana ya subuce da dariar murna "ku Bata mutu ba Wallahi bata mutu ba" Sujjudushukur Nasiba da Uncle zaid sukayi don godewa Allah, Alhaji Habib ya fita don kiran likita yana hamdala, daya bayan daya ta bi su da ido tace "wai ya? Ko cema ku akayi na mutu ne da kuke ta wannan abun? Dr Sami da Dr Umar suka shigo da mamaki, sun tabbatar da zuciyarta bata bugu kafin suka sanar da Yanuwanta, to ya akayi haka? Ikon Allah ne, Dr Sami ya soma dube dube a jikin Nene, Yace "Blood of Jesus has healed her, she is a strong fighter" Nene ta katse shi tace "wai gwajegwajen nan na meye? Kalau fa nike, zaka zo ka tasani gaba kana man turanci, Daga gani kai kace musu na mutu, haka kurun ka tada wa 'yan jikokina hankali" duk sai da sukayi Daria banda Rafeeq da ya daure fuska wai ba abun daria bane(ikon Allah ku ji min Rafeeq da ya gama fita hayyacinshi don ance ta Mutu) Dr Sami ya kalli abokin aikinshi yace "Dr Umar what is she saying?" Dr Umar yace "Shes thanking God that Shes still Alive, go to the Office i'll take it from here" Dr Sami ya fita daga Ofishin.
Ya kalleta da Murmushi yace "Sannu Mama, kiyi hakuri dogon Suma ne kikayi, Wallahi mun dade a kanki, Duk wata kafa ta sadarwa ta tsaya a jikin ki, saida muka samu tabbacin hakan kafin muka sanar dasu" tace "da kuka tabbatar kaine a zaune yanzu? Nace kaine a zaune? Toh ban mutu ba, bawai tsoron mutuwar nike ba, ku dai san aikin ku, ku san me zaku dinga fada ma mutane, yanzu da bakin labarinku ya sa Zuciyar Jikata bugawa ta shek'a lahira fa? Ni na mik'e ita ta mutu to me akayi kenan? Anyi ba ayi ba, ana muku kirari da likita bokon turai, to bokon kashi dai tunda ba ku san aikinku ba" nan ya shiga bata hak'uri tace su zaka ba hakuri, sai in yafe maka" yayi murmushi yace da su "Daddy suyi hakuri" murmushi sukayi sukace bakomai. Bayan nan aka fara diramar sama Nene Drip tace kwatakwata ita bata san Zancen ba sai dai a sallameta, Seebi tace "Wai Nene ki tsaya mana a sa miki drip din" tace "naki, ke ki zo a saka miki" Rafeeq ya daure fuska, "Uncle Zaid please talk to this Stubborn Old Woman" yayi daria yazo yace "Nenenmu kiyi hak'uri ki bari a saka miki drip din, kinga ko an sallameku yanzu ba inda zaku zauna a gidan don kusan komi ya k'one, da lallashi da lalama Nene ta yarda aka sa mata drip din.
"***
A dan tsorace Rafeeq yace "Ku tsaya ku tsaya? Ku tsaya! Ina Ayman? Nene tace sai yanzu ka tuna da ita? To kar ka damu tana gun Kakar ka, dazun Baban ta ya kaita kwana, ashe Soyayyar k'arya ake mata tunda sai da aka Neh-neh ta watsake aka tuna da ita, Rafeeq ya murtuk'e fuska, Zaid yace "kaii Nene, kinsan in ka rude abun da ke gabanka kawai kake gani, amma ba me tantaman Soyayyar Rafeeq ga Ayman, Nene tace sai ni don ya fi so na, yau naga tashin hankalin su O'eh, Maalesh yace "a fadi suna mana", tace "da Dunkum nike ai yasan dashi nike, tashin hankali yau Su dunkum har da su i lobi me Neh-neh, to nima i lobi you Dunkumeh, ai na rok'i Allah kar ya kasheni sai ya nuna mana auren mu" Alhaji Habib na daria yace "Aurenku ke dawa? Tace "yo ni da Dunkum mana, ai sai na Auri Dunkum" Duk suka fashe da Daria banda Rafeeq da ya hada gabas da Yamma kamar be ta6a daria ba.

"You cant sleep with them you know?" Cewar Maalesh, "Why cant i?" inji Rafeeq, Daddy yacei "Aa Rafeeq gida zamu tafi, ga Nasiba nan she cant look after her" yace "She's not well too, itama she needs someone to look after her" "Aa Hamma i can, i'm fine ba abunda ke damuna" Rafeeq yace "Shuttup you are not fine" Zaid yace "IkonAllah" Rafeeq be sake magana ba ya zaro wayar shi daga Aljihu ya latsa waya, ringing biyu ta dauka cikin magagin Bacci "Hello Mom" Mom din Maalesh tace "Son ya akayi ne da daren nan?" "sorry na tadaki, Hajjo fah?" ta kalli Agogon gefen gadonta tace for goodness Sake Rafeeq shes Sleeping, baka duba agogon bane kafin ka kira, this is 12:15am, guntun tsaki yayi yace "sorry mom, but you need to wake her up, an sake kwantar da Neh-neh kla Asibiti Maalesh yanzu zaizo daukanta, thanks Mom Love you bye" be jira ta amsa ba ya kashe wayan tare da kallon Maalesh, Maalesh kaje ka dauko Hajjo, Dad Uncle Zai ku tafi gida, I'll be here har sai Hajjo tazo". Kamar Shine Babba duk sukace Okay Maalesh ya fara tafiya, Kafin su Daddy, dama Nene Already tana bacci. A waje Daddy ke cema Uncle Zaid Rafeeq ya damu sosai, damuwar da yayi kan Nene da Seebi ya ban Mamaki, Zaid yace "ba wani abu bane kawai dai ya girgiza da Gobaran nan, na san Mutuwar Rafee'ah ta dawo mai Sabuwa, ya zata zai sake wani rashin ne, don kasan Ya dauki Nasiba kamar 'yaruwarshi, kuma duk da ba sa shiri da Nene, yana sonta Sosai" Daddy ya jinjina kai. A lokacin Zaid ke ba Daddy labarin abun da ya faru tsakanin Saude da Nene, yace " tohh abunda ya faru kenan, dazun naga bakinta ya kumbura da na tambayeta sai cewa tayi a tayi da bango ashe da walakin

Please Login or Register in order to submit comment