Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma ya siyar da wayarsa, yau ina cikin ukuba”

Ta kara fashewa da kuka.

“Baki da number kowa akanki”

“Akwai ta yayata da Mamana”

Sai da ta share hawayenta sannan ta karbi wayar ta saka number Mama tana shiga aka dauka.

“Hello Sallamu Alaikum”

“Mama ina cikin matsala Mama gani a Kano”

“Kano kuma Rafi'a? Gurin me?”

A nan ta labarta mata abun da ya faru, cikin labarin tafi nanatawa Mama cewar wayarta na cikin jakarta kuma ya tafi jakar, da alama ma batan wayarta yafi mata zafi fiye da ganin kanta da tai a Kanon cikin kankanen lokaci, yan kudinta ma duk suna ciki. Kamar wata sabuwar mahaukaciya haka Baturiya ta zama har wani yamutsar kai take.

“Wallahi Takauci be yi ba, daman ance idan mutum ya kwana arba'in be ci nama ba idan yai maka baki zai ya kama ka, gashi nan ai laifin Faruq ne”

“Wanene kuma haka?”

Sai tai shiru bata fada ba, domin bata son tace mijinta ace bata jin magana tun da har ya hanata fita kuma ta fita duk kuwa da kasancewar ba wannan ne karo na farko da ya hanata kuma ta fita ba.
Account din mai POS din unguwar aka karba aka turawa Mama ta turo mata kudin mota, aka ciro mata sai dai tafiyar ba zata yi a yau ba domin yamma ta yi gashi kuma hanyoyin nigeria babu kyau a dole ta hakura sai gobe da safe ta kama hanyar dawowa Zamfara.

Kamar kullum sai bayan sallah isha'i Faruq ya dawo gida. A bakin kofar gidan ya tsaya ya kwankwasa yana sauraren ta bude masa amman shiru bata bude masa ba, ya sake kwankwasa nan ma ba a bude masa ba, yayi haka kusan sau hudu sai a na biyar ya saka makullin hannunsa ya murda ya bude kofar daman can a tunaninsa ko ta rufe kofar ne daga ciki kamar yadda ta saba, sai dai tun a yanayin yadda ya tararda gidan ya tabbatar masa da matarsa bata nan. Yayi sa'a akwai wutar nepa sai ya kunna gulob din waje dana falo ya shiga daki ma ya kunna, tsaye yai yana karewa dakin kallo komai a watse kamar yadda ya fita ya bar shi, daman yana fita ta shirya ta fita bata tsaya gyaran komai ba. Gashi kuma be tararda ita ba, ajiyar zuciya ya sauke.

“Rafi'a Allah ya shirya ki”

Ya furta cikin yanayin dake nuna alamar be jidadin daya sami gidan a haka ba, babu abun da ya fi bakanta masa rai ma kamar tararda ita da be yi ba a gidan, ko da yake halinta ne ko da ba zuwa unguwa ba takan fita makota tai taje can tana hira ko ta rika musu aiki alhalin ga nata aikin na gidanta ta bari, sai dai shi ya kasa sabawa da wannan halin, domin duk mai mata baya son ya shigo gida ya tarar matarsa bata cikin gidan idan ba da wani dalili ba, babu irin fadan da be mata ba amman bata canja ba, har ya gaji ya saka mata ido.
  Gadon ya fara gyarawa sannan ya kwashe kayan data bari ya aje su a guri daya, ya gyara shimfidar Sultan ya dauko tsintsiya ya share dakin har zuwa falo, sannan ya zauna saman kujera ya daga kansa sama yana tunanin halin damuwar daya samu mahaifiyarsa a ciki, kusan kullum uwarsa bata rabuwa da damuwa domin idan babu na abinci akwai na rashin lafiyarta, sai dai a yanzu ta fi shiga damuwar fiye da koyaushe, a da tunanin na yadda zamu samu abun da za su sakawa bakinsu ne ko kuma na maganinta tsabanin yanzu da tunanin aurarda yarta wanda kanwace a gurin Faruq ya hanata sakat, ba Mahaifiyarsa kadai ba, idan aka fasa auren nan shi kansa zai shiga damuwa balle kuma ita kanwar tasa, domin mijin yace ya gaji da daga auren da ake ta yi, su kuma ba su da wani abun aurar da ita a yanzu, sadakin da suka karba da dadewa Mama ta saka shi a cikin kasuwancin da take ta zimmar zata dan juya ko zata samu riba, sai gashi ba wan ba kanen wato ba uwa balle kuma riba, daman sana'ar talaka sai Allah, balle kuma irin nata sana'ar da ake ci ciki.
Bayan matsalar kanwarsa ga matsalar kudin hayan da ke jiransa next week, gashi ba shi da mafitar kudin a halin yanzu, dan aikin da yake ta applying shi ma shiru kamar wanda ya zagi gobnati.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ya furta yana dafe kansa.

“Allah ka kawo min sauki Allah ka yi min mafita”

Ya fada yana mikewa tsaye ganin har goma ta kusa matarsa bata dawo ba, duk yawunta bata wuce tara na dare sai idan biki ake ko kuma wani abu ke saka ta kai dare, ko da makota ta shiga bata wuce 9pm.

‘Ina tunanin tafiya nijar zai fi min gurin ginar zinari, sai dai shi ma ai dole sai ka samu kudi, samun wanda zai baka rance ma a yanzu ai aiki ne’

Ya nufi kofa yana ta sake-sakensa da tunanin inda zai samu mafita. Babu waya a hannunsa balle ya kira ya tambayi inda take domin ya bada wayar jingina tun shekaran jiya ya karbo musu abinci, hakan yasa ya fara nufar gidansu Maman Amira makociyarsu domin Baturiya tafi zuwa can ta wuni saboda suna da rufin asiri daidai gwargwado, ba shi ma ko mutanen unguwar sun shaidi Baturiya da son shigewa masu kudi, idan ka ga tana shiri sosai da mutum to mai rufi asiri ne.
Cikin almajiran dake zama bakin kofar gidan ya kira daya ya aike shi cikin gidan ya kira masa Rafi'a, almajirin na shiga ya fito dauke da Sultan dake bachi ya mikawa Faruq.

“Ance wai bata nan, tun dazun da ta shigo bar Sultan tace zata je kasuwa bata dawo ba, kuma ta kira wayarta a kashe”

Cikin fargaba Faruq ya karbi dansa ya juya yana yi ma almajirin godiya ya koma gida, kwantar da shi yai ya fito waje zuwa gurin mai shagon daya bada jinginar wayarsa.


AMINATU POV.

Sai da yamma lis ta farka, ta dade da farkowa daga suman da tai sakamakon ruwan da suka zuba mata ga kuma zafi rana dake dukanta. Kana kallon kwayar idonta zaka karanci gajiya, da wahala dake tattare da ita. Gaba daya jin take kamar babu mararta zuwa kasan cinyoyinta, ko motsasu ta kasa yi, hakoranta kuma sun dantse gam kamar a hade aka haliccesu, a kwance take amman jiri sai dibanta yake tana ganin hadarin dake haduwa yana juyawa. Ba ita kadai ce a cikin wannan halin ba, sai dai wasu sun fita juriya domin suna da aure wasu kuma sun yi har sun fa ra warkewa. Kamar jira suke ta farko sai wani yaja hannunta ayayinda sauran jikinta yake kasa zuwa gurin turken da suke daure matan, a kafa duka daureta kamar sauran matan, sai dai har lokacin a kwance take ta lumshe ido tana sauraren yadda numfashinta ke fita a hankali, babu tunanin komai a kanta tana son tai tunanin amman ta kasa, tana tai kuka ta kasa sai a yanzu ta gane ashe yin kuka ma wani babban gata ne, yin tunani ma wata baiwa ce, yau ta rasa ta ina zata fara tunani balle ya gayyato kukanta.
  Sama sama take jin kafarta na mata zogi, saboda tafiyar data sha da kuma Ƙayoyin da suka taka, ba ita kadai ba kusan kowa yana fama da ciwon kafafuwan wasu sun taka kusa wasu kaya, sai dai basa jin zafi a lokacin sai a yanxu, wasu kuma daurin da akai musu ne yake musu ciwo, domin na da wasa suke daure mutum ba.
Kamar dazu da safe haka aka biyo su ana ba su abinci a hannu cibi biyu wasu uku, kowa aka zubawa sai yai sauri ya cinye saboda yunwa ta ci su har ta galabaitar da su, daman idan suka ci cibi biyu ko uku da rana ba za su sake ci ba sai kuma dare, wani lokaci ma ci daya ake a rana.
  Komai tsananin zafin rana ko sanyi ko ruwa ba a basu abun rufa ko gurin fakewa, sai dai sanyi ya kare akansu, haka ma idan ruwa ne sai dai ayi ruwa a gama ya jika musu kaya kuma tufafin ya bushe a jikinsu, idan rashin lafiya ta same su sai dai su mutum domin babu zancen basu magani balle kuma akai su asibiti.

“Dan Allah ku kwance mu yi sallah magariba ta yi”

Daya daga cikin mutanen dake daure ya fada, kusan wannan shi ne karo na barkatai da yake rokon su barshi yai sallah. Sai wasu kananan samari suka nufo inda yake suka kwance shi suka ware shi gefe suka saka bulala mai kyau suna dukanshi.

“Wato kai shege ko, baka daddaraba”

Duka suka masa ba na wasa ba, daman jikinsa da sauran bulala da suka masa dazun saboda yace su bar shi yai sallah, a kullum sai yayi magana kuma a kullum sai sun masa duka.

(As I'm  writing this mutumen da yake cewa su bar shi yai sallah is no more, Wallahi sun kashe shi neighbor din mu ne, and they sent his friend wanda aka kamasu tare ya fadawa iyalinsa bayan an biya kudin fansar karbo shi)

Bayan sun gama dukansa suka maida shi gurin da yake suka sake daure shi yana ta kuka, ga wahalar yunwa ga na dukan dazu dana jiya ga shi yanzu kuma sun kara masa da wani.
Ana gama sallah magariba ruwa ya fara sauko, ta yanayin garin suke iya gane magariba ko azahar da la'asar domin babu masallaci balle su ji kiran sallah balle kuma agogo. Yan bindigar ne suke ta gudu suna neman gurin fakewa, mutanen da aka ma kuma suna daure aka fara ruwan kama da bakin kwarya yana sauka a kansu, iyakar abun da suke shi ne su dukar da fuskarsa saboda kar ruwan ya taba fuskarsu, wasu kuma su saka hannu su kare fuskar tasu, sai dai hakan be hana ruwa ya jika su.
A cikin mutanen da ruwan saman ya jika har da Aminatu, dake kwance galabaice kamar sauran matan da basa da kuzarin yin komai, abincin da aka bata ma bata karba ba, komai ganinsa take kamar ba shi ba, har yanzu bata yarda mutanen da suka kashe mata uwaye da yan'uwa suka kawota daji suka keta haddinta yan'adam ne masu zuciya da jini a jikinsu ba. Ta kasa yarda a duniyar da ta sani take, gani take kamar daukarta akai aka jefata a wata duniyar ta dabam mai cike da azzalumai, kuma marasa tausayi da tsoro Allah.
  Haka suka kwana a cikin sanyi cikin kwabon ruwa har safe, sam ita ko yunwar bata ji, sauran da suka dade nan kuma suna fama da yunwa domin sun sabu da gurin ya zame musu kamar gida, wasu sun yi wata uku wasu biyu wasu hudu har biyar ma.

                  ***       ***        ***

MONDAY MORNING 9:21am.

“I wonder what wrong with our country? Kashe mutane ya zama kamar abinci?”

Cewar Kabir yana kallon hotunan da aka turo na harin da aka kai a garinsu Aminatu, abun ya kazanta kuma yayi muni sosai, musamman harin nan na biyu yafi na farkon ma, domin a yanzu an bar garin ba kowa, tun a lokacin da abun ya faru suka kashe na kashewa suka tafi da wasu, sauran da sukai rai suka gudu zuwa wasu garuran gudun Hijira!
Talba ya kalleshi yana kokarin gyara agogon hannunsa. Ba al'adarsa ba ce yin breakfast a bangaren a week days sai dai weekend, idan har zai karya to sai dai ya karya bangaresa ya sha tea ko kuma ya tafi office dinsa ya karya, sai dai ya zame masa al'ada shigowa ya gaisa da Momy kamin ya tafi aikin, sanadin hakan yasa suka sabu da Baaba idan ya shigo tana masa kirari ko da ba zai amsa mata ba zai mata murmushi ya gaishe ta sannan ya fita.
Yau sai ya ji dabam domin ya saba idan ya shigo zai tarar ita take shirya abun karyawa sai idan weekend ne Momy take tayata su hada komai a tare.

“Wai ya ake son talaka yayi ne? Su fa suke noma, yanzu an hana su noma wadanda sukai kuma a kone kuma a ashe su a dauke matansu kai jama'a wannan abun yayi yawa, nan gaba abinci ma sai yayi wahala”

Momy ta kalle tana kokarin aje flakes din ruwan zafi a dinning.

“Shiyasa ga su nan sun bi sun cika mana gari da bara kamar za su kwata da karfi”

“Haba ai dole Momy, ki duba yadda mutumem kauye yake alfahari da noma amman su bar komai nasu su dawo inda babu kowa suna bara, abun tausayi ne Wallahi”

“Su ma ai sun so, tun da su suka fara kashe Fulanin”

“No wannan ba hujja bace Momy idan ma da gaske ne”

Tabe baki tai ta cigaba da abun da take, har suka ci suka shude Talba be ce komai ba, daman shi ba komai ke saka shi magana ba, ko da kuwa abun ya dame shi.

“Momy zan tafi aiki”

“Yau da wuri?”

Ya daga mata kai.

“Allah ya tsare”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya fito daga bangaren yana wani irin kamshi turare mai jan hankali yan mata da saukar da natsuwar mai shakarsa. Kai tsaye bangaren Daddy ya nufa sai da yai knocking sannan ya tura kofar sai ya jita a rufe, door bell din ya danna sannan yaja ya tsaya. After few minutes aka bude masa kofar. Sai da suka gaisa da Amal da ta bude masa kofar sannan ya karasa can ciki gurin Daddy. Sai ya same shi zaune rai a bace yana kallon wayarsa, domin labarin harin da aka kai ya karadi kafofin sada zumunta musamman Facebook.

“Wa'alaikassalam”

Daddy ya dago yana amsa masa sallamarsa, Talba ya zauna kusa da shi yana karantar bachin ran daya bayyana a fuskarsa.

   >>>>>><<<<<<
Sauran page daya mu gama free page, if you want to subscribe pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank and sent the evidence via 08036126660. Yan nijar kuma za ku biya ta wannan number +227 90 16 59 91 sai na yi adding dinku a group.

________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
  Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -1️⃣0️⃣

Talba ya mikawa Daddy wayar bayan ya gama dubawa.

“Daddy ku da kuke kusa da gobnati ya kamata ace kuna fada musu halin da ake ciki mana, mutanen nan suna cikin bala'i, kamar ni ne, kana zaune kana rayuwarka sai a iskoka a koreka daga gidanka a akashe yayanka kuma a keta haddin matanka, Wallahi tausayi suke ba ni matuka”

Cewar Talba cikin wani irin bacin rai da jin zafin abun da yake faruwa. Daddy yayi murmushi yana gyara zamansa.

“Mu'az kenan, waya fada maka gobnati bata san halin da ake ciki ba? Sun san komai, wannan matsalar tsoro tana kawo kudi sosai, fiye da yadda kake tunani, duk jihar dake fama da matsalar tsaro kudin da ake ware mata dabam, idan har aka magance matsalar to abinci wasu zai tsaya, kuma duk jihar da kaga suna fama da matsalar tsaro to suna da cigaba da ake bukata”

“Amman Daddy basa tsoron hakkin rai?”

“Wannan kuma ai sai lahira, Allah dai ya kyauta kawai amman matsalar tsoro a yanzu abu ne mai wahalar magancewa, domin an fi samun kudi ta gurin tun daga manya har kanana, na mu dai addu'a ne, da kuma taimaka musu da abun da Allah ya ba mu”

A hankali Talba ya busar da iskar bakinsa ya kalli Amal data doso inda suke sanye da uniform dinta na makaranta.

“Na yi magana da PA zai yi list din abubuwan da zamu siya mu kai musu soon”

“Maa Shaa Allah, hakan na da kyau”

“Wa za a kaiwa? Baaba?”

Amal ta tambaya tana aje fular abinci. Daga Daddy har Talba kallonta su kai, ta san ba maganar Baaba ake ba, kawai ta dauko maganar ne saboda tana son fadawa Daddy abun da ya faru ne, daman ita ce yar gulmar gidan komai akai a bakinta za aji.

“Wace Baaba kuma? Yan gudun hijira ake magana”

“Au na dauka Baaba za a kaiwa, Allah yasa dai ta ji sauki”

“Miya same ta?”

Daddy ya tambaya, a nan Amal ta zauna gefensa ta labarta masa irin abun da ta fadawa Talba.

“Taya Doctor zata yanke wannan hukunci bs tare da sani na ba? Tafi ki kirata”

Daddy ya fada rai a bace. Sai ta mike tsaye gabanta na faduwa.

“Ya sai ka ce ni kai ka fada”

Talba yayi murmushi, ita ma murmushin tai ta fice, bayan ta wuce Daddy ya kalli Talba.

“Ka san da maganar ne?”

Talba yayi shiru ba tare da ya amsawa Daddy da eh ko aa ba. Wanda hakan ya tabbatarwa da Daddy cewar ya sani kenan, domin idan be sani ba kai tsaye zai fadi cewar be sani ba.
Daddy be sake cewa komai ba har sai da Momy ta shigo dauke da wasu manyan kulolin abinci ta aje a gabansa, sai da Momy ta kalli Talba sannan ta kalli Daddy tana karantar yanayinsu.

“Lafiya dai engineer?”

Daddy ya kalleta irin duban da ke fassara mata bacin ransa.

“Baaba ta fado, har kun kaita asibiti amman baki sanar da ni ba”

Dagowa Momy tai ta kalli Talba da kansa ke kasa.

“Ina ganin kamar karamin abu.... ”

“Karamin abu? Da gaske? Amina kin san abun da kike fada kuwa? Mutum ya fado daga sama zuwa kasa ki kira shi karamin abu? Idan har karamin abu ne yayanta zasu dauke ta su tafi da ita ne? Ko da ma karamin ciwo ne tun da har a nan ta samu matsalar ai ya kamata ki sanar da ni, kuma be kamata a bar yayanta su tafi da ita ba, a nan ya kamata a dauki nauyin komai na ta, shekara biyu tana aiki tare da mu”

“Ranka ya dade, ba wani ciwo ne sosai ba, kuma na kaita asibiti sun bata magani sai ta kira yayanta tace zasu tafi da ita, babu yadda ban yi ba amman suka ki yarda, kuma ina da niyar fada maka anjima da dare idan ka natsu”

“Yanzu idan wata ce a cikin yayanki ta fado zaki mata haka ne? Balle tsohuwa? Sometime kina abu kamar damuwar wani ba damuwarki ba ce”

“Allah ya huci zuciyarka Engineer, amman be kamata damuwar wani ta dame mu ba, mu ma yanzu idan muka shiga cikin wata matsalar babu wanda zai damu da halin da muke ciki”

“Okay, yayi kyau daga yau ba zan sake biyan mai aiki ba, indai zan dauki mai aiki ta taya yaranki aiki ne ba za a sake ba, idan har damuwar wani be kamata ya dame mu ba, karki sake gabatar min da wata matsalar yan'uwanki balle kawaye”

Yana kaiwa nan ya mike tsaye a fusace ya nufi hanyar dakinsa. Momy ta rutse ido ta bude ta kalli Talba da shi ma kallonta yake domin ya san shi zata dorawa laifi.

“Karamin abu ma, sai ka tasa mahaifinka a gaba kana tsegunta masa? Talba wacce irin rayuwa ce wannan? Mun yi fada hankalinka ya kwanta? Kuma zai fita be karya ba, ina tunanin haka kake so ai? Kai na ya fara kwnacewa da lamarinka”

Uffan Talba be ce ba, har tai ta gama ta mike tsaye ta fice, mikewa yai tsaye ya ciro wayarsa dake ringing.

“Ali”

Ya fada bayan ya danna picking.

“Talba ka fita office ne?”

“No ya akai?”

“No ina son magana da kai ne, na dauka kana office na biyo”

“No yanzu zanje, yau da wuri zaka je aiki kenan?”

“Eh muna da patients da aka kawo mana, kasan sojoji sun samu kwato wasu daga cikin wadanda yan bindiga suka tafi da su, akwai wadanda suka samu rauni sosai an kawo mana su”

“Eh na ji an kai hari abun ba dadi Wallahi”

“Sosai an kawo wasu shekaran jiya wadanda suka harba abun ya kazanta”

“Allah ya kyauta, We can talk later”


Ya sauke wayar, sannan ya nufi kofar fita yana kiran Jahid.




AMINATU POV.

Labarin harin da aka kai ya karade ko'ina a Nigeria, gidanjen jaridu da kuma kafofin sada zumunta. Hakan yasa aka turo jirgin sojijin tun daga jihar Lagos har zamfara.
Kwashe gari aka bi su da danyen dankalin hausa a hannu duk wanda aka gutsawa sai yai sauri ya cinyewa, bayan sun gama ci kuma sai a bisu duka musamman wadanda aka akai maganar kudi da yan'uwansu ba su kawo ba. Sun fi dukansu fiye da kowa, duk abun da ake Aminatu na kwance bata iya komai ba, har yanzu bakinta a nauyaye yake, idanuwanta ne kadai abun da suke aiki a jikinta sai numfashi. Tana kwance galala ta daga kanta sama tana kallon jiragen sojoji guda biyu da suke shawagi a sama, kararsu kadai ta isa ta kurmantar da mutu, sun yi kasa kamar zasu saki wuta sai dai ba su saki wutar ba suka gangara can nesa da damarsu suka saki wutar a inda babu mutane.
Bayan ya wuce barayin suka fito daga gidanjensu na bukka dake can nesa da inda aka daure su Aminatu, suna da yaya da mataye a cikin bukokin sai dai akwai tazara mai yawa a tsakaninsu.
Suna isowa inda suke mutunen jiya ya sake rokon su bar shi yai sallah, sai suka hau shi da zagi.

“Kawo shi nan”

Dayan ya fada, sai sauran suka kwantoshi daga inda yake suka nufi wata bushiya inda mutunen yake, suka daureshi jikin icen suka sako kansa kasa kafafuwansa a sama yana ta lilo.
Tun yana kuka yana rokon su kwance shi har ya gaji ya fara kalmar shahada, majina ta fara fitowa ta hancinsa tana zazzagowa kasa tare da hawayensa.
Ba su kwance shi ba sai da su suka tabbatar rai ya bar jikinsa, sannan suka sauke shi kasa, lumshe ido Aminatu tai wasu hawayen suka cika mata ido.
Bata sake bude idon ba sai da ta sake jin karar jirgin, wannan karon da fatan mutuwa take kallon jirgin burinta ya sako wuta kowa ya kone har ita, domin tana da tabbacin babu wata rayuwar jindadi a tare ita ko da rayu! Ta ina ma zata rayu? Taya zata fita a nan? Idan ma ta fita gurin wa zata je? Da wa zata zauna? Wa zai rike ta? A kashe mata kowa, yayyu da iyaye, idan zata nemi yan'uwan uwa ko na uba ta ina zata fara nemansu? Ina zata gansu? Zata fita a nan ma?

‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’

Ta maimaita a cikin ranta, domin bakinta ya mata nauyin da bata iya saka komai ta tauna balle har ta furta wani abu, wata kila kalamanta sun kare wata kila kuma har da rayuwarta, farinciki kam ta tabbatar da ya barta. Bayan sallah isha'i ta dan unkura ta tashi zaune tana jin kamar ba zata iya zaman ba kuma gashi ta gaji da kwanciyar. Hannunta ta kai ta damki kasar gurin ta junke a hannunta da wani irin karfin zuciya, sai dai na jiki kam babu shi ko kadan a kusa da ita, a galabaice ta dago kai tana kallon mutanen da suka doso inda suke da manyan fitulu suna haske su, matasan yan bindigar ne suka kwance matan kusan shiri maza takwas, a cikin mutanen da aka kwance har da Aminatu.

“To ku fadawa sauran dabobi an yi diyya kar sai mun kama hanya su bude mana wuta”

Wanda yai maganar fuskarsa a nade take da rawani babu ta inda zaka iya ganinsa balle ka shaida shi, sauran yan bidigar kuma wasu na sanye da rigar soja wasu kuka wandon suka saka wasu kuma duka biyu sai dai dukansu suna dauke da manyan

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment