Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bindigogi.

“Ai dai hanyar da suka biyo zaku bi karku kuskura sauya hanya, idan ba haka ba zaku hadu da wata dabar, kuma za mu aika musu”

Dayansu ya fada, sannan aka fara dukansu da bulala aka korasu kamar dabbobi.

“Ku wuce yan iska, ni na tsani kado Wallahi”

Cewar dayan yana dukansu, masu kuzarin cikinsu suka tashi suka fara tafiya ban da Aminatu da sauran da akai ma fyade kamar ta, ganin hakan yasa mutumen ya roki a dorasu akan babur, a fitar da su sauran da suke iya tafiya a kafa kuma a korasu a kasa. Wadanda aka kora a kasa suna tafe suna jin tsoro saboda daukin ba dadin da ake da babbar daba, daman can sun fi kowa dauka da zafi, karama daba kudin fansarsu ba su da tsada kuma ba da taurin kai kamar babbar daba, kasancewar karamar daba matasa ne masu tasowa wasu ma duk yara ne, babbar daba kuma manya ne wadanda suka dade a cikin harkar.
Su Aminatu sun riga isa kusan da bakin dajin saboda an dauke su a babur, sai dai zubesu akai a kasa suka zauna a gurin har sai da na kasan suka karaso sannan aka hadasu aka nuna musu hanya. Sauran wadanda sukai musu rakiya kuma suka juya suka koma ana kusan kiran sallah asuba suka fiton daga dajin, Aminatu na tafiya daker tana hawaye, idan ta gaji da tafiyar sai ta zauna a kasa ta yi rarrafe idan ta gaji sai ta unkura ta mike tsaye ta fara tafiya.. Da haka har suka iso bakin gari a inda motocin sojojin suke. Da farko sun tsorata duk kuwa da kasancewar an fada musu akwai sojoji a gaba, sai dai ganin a cikin barayin ma akwai masu uniform din sai ya saka wasu suka tsorata, sai dai kana ganin wadandan sojojin kasan zaratan sojoji ne ba kamar yan bindigar ba. Karasowa sukai suka dauki mutanen a mota, Aminatu kuma da ire irenta suka daukesu suka saka a motarsu, suka kama hanyar gari da su.
Ko da tara na safe ta yi, labarin nasarar da sojojin suka samu a kokarinsu na kwato mutanen da akai garkuwa da su ta kwarade ko'ina, labarin barin wutar da akai ya shiga lungu da sako na nigeria, ya leka gidan jaridu ya cika social media.
Masu lafiya aka tafi da su inda za a buka fuskarsu ayi ado da su a jaridu, marasa lafiyar kuma aka wuce da su asibiti a sirrance.
A tsakanin iskar dake dajin dana cikin gari zuwa na asibitin da aka wace da su Aminatu ko wane dabam, na dajin na tawaya ne da damuwa da bakinciki, shigowa garin kuma samun iskar yanci ne, sai dai shiga asibiti kuma na fata ne, wata kila ta rayu wata kila kuma rayuwar ta zaba mata mutuwa.
Mutanen da suka zo da gudu suka karbeta a hannun sojan daya dauko ta, sai su ka yi mata kama da wata halittar da taban kasancewar suna cikin farin uniform ne na aikinsu. Lumshe ido tai tana sauraren yadda aka dagata sama aka dorata saman gadon asibiti ana turata.



FARUQ POV.

A gurin mai shagon ya karbi wayarsa, ya saka line sa ya kira number Baturiya ya jita kashe. Hakan ya saka ya kira ta kanwarta sai da ta kusa tsinkewa sannan ta yi picking.

“Hello Raliya ya kike?”

“Lafiya Kalau Ya Faruq”

“Yayarki ta zo?”

“Aa, tana Kano fa”

“Kano?”

Ya maimaita cikin tsananin mamaki.

“Eh Napep ta hau shi ne...”

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama sauraren abun da Raliya ta fada masa, sannan ya sauke wayar yana jin babu dadi. Ya sani ba dan komai Baturiya take masa haka ba sai dan talauci, da yana da arziki da bata isa ya mata umarni ta saba ba, daman ai ta fada idan yana da kudi ba zata taba gujewa umarninsa ba, tabbas da yana da arziki da iyayenta sun nemi inda yake sun fada masa halin da matarsa take ciki, sai dai ba su yi hakan ba saboda ba kowa ba ne a idonsu, wannan dalilin ya saka a duk lokacin da ya kai kararta akan abun da take masa sai du bata gaskiya su goyi bayanta. Cire line yayi ya ya mika masa wayar ya juyo ya dawo cikin gida cikin yanayi na rashin dadi ya maida gidan ya rufe.


BATURIYA POV.

Washe gari mutanen gidan suka bata wani tsohon Hijab ta saka ta talkami, Bayan ta karya suka rakota har bakin titi suka tara mata Napep zuwa tashar mota. Su suka biya mata na napep din, tana ta musu godiya, idonta har yanzu be warware daga kukan da tasha ba, babu abun da take ji kamar wayarta, domin samun wata wayar a gareta yanzu abu ne mai matukar wahala a halin da suke ciki, har kara ma a gidansu wata kila mahaifiyarta zata iya taimaka mata da wani abu, yayanta ya cika mata sauran ta siye wata wayar, amman ba daga bangaren Faruq ba kam.
Tun daga yanayin hausarta suka gane yar zamfara, abun ka da kanawa sai dariya suke mata ita kam bata ma bi ta kansu ba gaba daya hankalinta yana kan wayarta data bata yadda zata samu wata wayar kawai take tunani, gashi hanyar samun kudinta ta facebook ne inda take yaudarar maza, yanzu kuma babu wayar yaudara ma.

“Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ta furta wasu hawayen na cika mata ido.

‘Dan Allah aljanuna idan kuna jina ku taimaka min da wayata ku dauki kudin na bar muku’

Wannan karon a cikin zuciyarta tai maganar hawaye na sauko mata.

“Malama Lafiya dai?”

Wani matashin saurayi dake kusa da ita ya tambaya yana kallonta. Banza tai masa ta ta juya masa fuska, sai yai murmushi ya cigaba da danna wayarsa. Sai da motar ta cika sannan suka kama hanyar Zamfara suna tafe suna addu'a saboda yanayin hanyoyin nigeria kowa ya san yadda tafiya take a yanzu. Sai da tafiya tai nisa sannan aka kira saurayin a waya, Baturiya ta kashe kunne tana sauraren yadda yake amsa wayar a cikin har da amsar da yake fadawa cewar motar haya ya shigo saboda motarsa ta tsaya ya barta a nan Kano.
Baturiya na jin haka sai ta juya ta kalleshi sai a lokacin ma ta lura da shaddar jikinsa babbar shadda ce, haka zalika wayarsa ma.
Tun da suka kama hanyar direban be tsaya ba har suka iso Zamfara.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Baturiya ta fada da muryar kasa kasa tana fashewa da sabon kuka. A nan ma kallonta yai ya tambayeta.

“Lafiya...?”

Kai ta girgiza ta share hawayenta ta fada masa abun da ya faru da ita, sai dai ta canja cewar tana da aure, sai ta fada masa cewar mahaifitarta ta aiketa.

“Subhanallahi, ki gode Allah ma be kai ki wata kasar ba”

“Haka yan gidanmu suka ce, ni daman Allah ya sani gidanmu bama hawan Napep duk inda zamu je a mota ake kai mu yanzu ma tsautsayi ne”

Ta fada kamar gaske, kallon lace din dake jikinta yai kamin ya kalli kyakkyawar fuskarta.

“Allah ya tsare gaba”

“Amin”

“Amman miyasa kike kuka?”

“Haba Malam dubi tufafin dake jikina fa? Ban taba kwana a irin gidan dana kwana ba sai jiya, yanzu kuma motar haya na biyo tun daga Kano har Zamfara abun da ban saba ba”

“Ba dadi gaskiya, ni ma ban saba hawan motar haya ba sai dolen dole”

“Ba dadi ai”

“Gaskiya”

Daga haka be sake cewa komai ba sai da suka isa cikin tasha. Bayan sun fito ta jero ita da shi suka fito titi, fitowarsa tai daidai da fakawar wata bakar mota mai kyau har wani sheki take tsabar sabuntaka.

“If ba wani matsala zan iya sauke ki a gida ai”

“Aiko da naji dadi Wallahi domin tsoron Napep nake yanzu.”

Murmushi yai ya bude mata baya ta shiga, shi kuma ta bude front seat ya shiga ya zauna.

“Ku gaisa da abokina”

Ya fada yana juyowa ya kalleta.

“Sannu ya aiki”

“Alhamdulillah ya hanya”

“Da godiya”

Ta amsa sai ta maida dubanta gefen titi tana kallon motocin dake kai kawo.

“Wace unguwa ma?”

“Gada biyu”

Ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba, ko kadan tsoro be kamata ba balle ta ji faduwar gaba, ta saba shiga motar maza duk kuwa da kasancewar tana da aure, sai dai bata barin wanda ya santa ya ganta, wannan karon ma bata haufin ganinta ne saboda ta san yayanta ya san labarin bata tan idan ya ganta da wani ba zai mata fada ba.
Har kofar gidan yayanta suka sauketa, kato gidan mai kyaun gaske, sai da tai musu godiya sannan ta bude motar zata fita.

“Ga katina maybe zamu iya gaisawa”

“Okay thank”

Ta fada tana karbar katin sannan ta fice ta maida motar ta rufe sannan ta tura gidan ta shiga.

“Ina ka hadu da wannan?”

“Ta sha kuma ta min”

Ya fada yana murmushi.

“Tana da kyau gaskiya”

Dukansu dariya sukai sannan abokin nasa yaja mota suka juya.




LEILA POV.

Tsaye take jikin windo tana kallon garden din dake cike da itatuwa, fuskarta dauke da hawaye, haka ma zuciyarta babu dadi ga rashin natsuwa da samun sukuni da take.
Hannu ta saka ta share hawayenta tana jin wani irin nadama da bakincikin abun da ta aikata.

“Why? Sometimes I'm very selfish”

Ya fada tana kai hannunta ta shafa wuyanta, bakinta ta cika ma iska ta busar sannan ta juyo ta baro jikin window ya nufi kofar fita har yanzu jin take babu dadi, tsaye tai tana kallon bakin kofar dakin a daidai inda Baaba ta tsaya sannan ta dauke kai ta fara tafiya, sai da ta leka dakin Momy ganin bata ciki yasa ta sauko kasa gaba daya sai ta same ta zaune akan sofa tana amsa waya. Wucewa tai dinning taja kujerarta ta zauna tana ta kallon abincin dake gabanta kamar mai wani nazarin.

“Leila...”

Momy ta kira sunanta bayan ta gama wayar, sai Leila ta juyo ta kalleta da idanuwanta dake nuna alamar bata samu bachi da yawa ba. Tasowa Momy tai tana karantar damuwar yarta, a take ta nemi bacin ran dake tare da ita ta rasa, hannu ta kai ta rika fuskar Leila.

“Dear ba ki bachi ba?”

“Wallahi Momy na kasa bachi kamar yadda na saba, Wallahi dana rufe ido matar nan nake gani”

Momy taja kujera ta matsa kusa da yarta sosai ta zauna.

“Leila ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru, babu wanda zai san wannan abun even if ma sun sani ba su isa su yi komai ba, they're poor ba su isa su ja da mu ba, kuma wannan abun ai kaddara ce, ki dauka haka Allah ya rubuta”

Ta gyada kai cike da gamsuwa. Sai Momy tai mata murmushi ta share mata hawayenta.

“Ko kadan bana son na ganku a damuwa, ku kenan uku Allah ya bani bana son kuna samun kanku a damuwa, wannan matsalar ma ta Talba zata wuce inshallah sai ya sauke duk girman kan nan”

“Anya Momy Talba zai ce?”

“Dole ya canja, sometime lamarinsa har daure min kai yake, yanzu maganar nan ta Baaba har ya kai ta gurin mahaifinki, simple abu Talba ya rika yinsa kamar wani mace ko karamin yaro, gashi na je Mahaifinku yace ba zai sake biyan mai aiki ba”

“Ba zai rika dafa abinci kenan?”

“Dole a aljihu zan rika biyansu, ai na yi magana da Hajiya Samira ta nemo min wasu yan aikin, a dole mu dauki wasu amman da ni zan biya su”

“Ban san miyasa Talba ya fita dabam a gidan nan ba, ni na rasa gane wane irin mutum ne”

“Shiyasa nake son ki kwantar da hankalinki, domin bana son ya fara zarginki, ni kam ba dan kin matsa kina son Talba ba....”

Kamin Momy ta karasa Leila tai saurin tare numfashinta tana rike hannunta.

“Wallahi Momy ina son Talba, ina mugun sonsa, Wallahi idan ba shi ba ba zan iya auren kowa ba”

“Shikenan ai ba zamu bari ya dauko mana bare ba, amman halin nan nasa ina ganin kamar zaki wahala idan akai auren nan”

“Momy ba zan aure shi ba sai ya canja, zan canja shi inshallah na san yana son mu yi aure ai zan yi amfani da wannan damar na canjan shi”

“Allah yasa yanzu dai sai ki karya”

Ta daga mata kai ta kai hannu zata fara bude kular akai knocking, kusan a tare ita da Momy suka kalli kofar falon sai dai ta riga Momy mikewa tsaye ta karasa gurin kofar ta bude.

“Madina...”

Suka sakarwa juna murmushi, sai kuma Madina ta juya tana kallon Talba dake kokarin shiga mota, kamin ta juyo ta kalli Leila.

“Fita zai yi?”

“I think”

“Kamar ya you think zai fita baki sani ba”

“Kina abu ke ma kamar baki san Talba ba”

“Ke ce ya kamata ki canja ba shi ba”

Madina ta fada tana sake juyawa ta kalli motarsa, ajiyar zuciya ta sauke a sirance sannan ta shiga cikin falon gabanta na mugun faduwa, irin faduwar gaban da take yawan samun kanta a ciki a duk lokacin da tai arba da Talba.


Alhamdulillah a nan na kawo karshen free page duk page din da zai biyo bayan wannan na kudi ne.

If you want to subscribe Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660. Yan Nijar zaku biya ta wannan number +227 90 16 59 91.



_____________


Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria.

11

Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle I'm on Instagram as ramla_incense. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa


_____________________

“Madina ce”

“Eh Momy ya gida?”

“Lafiya Kalau ya Maman ki?”

“Lafiya Kalau take”

Ta amsa tana murmushi, sai Momy ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta dake kasa. Daga Leila har Madina binta su kai da kallo sai da ta shige sannan Madina ta kalli Leila.

“Wai da gaske baki san inda Talba za shi ba?”

“Ba zai wuce Office ba”

“Amman ya karya kamin ya fita?”

Ta daga fadunta alamar bata sani ba.

“Sometime a office yake karyawa wani lokacin kuma a bangarensa”

“Wani lokacin kina bani mamaki Leila, idan an yi magana ki ce kina son Talba, amman baki san abun da yake so ba, da wanda baya so, ba ki kokarin kiyaye bacin ransa”

“Shi yana kokarin kiyaye nawa ne? Yana son a rika masa sakon soyayya ana tambayar Lafiyarsa an damuwa da shi, amman shi be damu yai min ba, ni fa macece be kamata na zubar da kai a kansa ba”

“I know amman idan kin kula haka rayuwarsa, then why ba zaki bishi ku tafiyar da rayuwarku a haka ba, I'm sure idan kuka yi aure komai zai canja”

“Zamu yi aure, amman sai na gasa masa gida a hannu tukuna, and kina bukatar sanin wannan, Talba wanda zan aura ne ba wanda na aura ba, me yace me zai ci rayuwarsa for now bata dame ni ba”

“Haka dai kike gani, amman matakin kulawa daga yanzu ne, ni ina ganin ya kamata ma ki fara aiki ta haka zaku samu fahimtar juna sosai”

Rausayar da kai Leila tai.

“Madina, miyasa kike yawan damuna da maganar Talba ne? Ban shirya aiki yanzu ba sai na yi masters”

“Ina tsoron kar ya kubuce miki ne!”

“Really....”

Leila ta fada tana dariya.

“Ke a tunaninki akwai abun da zan nema na rasa a rayuwata? Haba Madina, ai Talba ko daga wani tsatson ya fita Daddy da Momy za su tsaya min na same shi, ballr kuma a jinina Talba ya fito, ba wai rasa shi ba, soyayyata ma ya hada da ta wata ma be isa ba, balle har ya hada ni da kishiya, haufi daya ne akan halayyarsa”

Madina ta yi murmushi.

“Leila kenan, na san kina da gata ta ko'ina, amman Talba yafi gaban yadda kike tunani, kar fa ki manta shi namiji ne”

Leila ta juya ido.

“Please My friend mu aje maganar Talba a gefe, kin san wai ko jiya na yi mafarki matar nan?”

Madina ta zaro ido.

“Da gaske?”

“Wallahi, ina ganin kamar ko yawan tunaninta da nake ne yasa nake mafarkinta”

Madina ta yi shiru tana kallonta kamin ta ce.

“Amman kin san fa hakkin jini...”

“Hakkin jini Madina sai kace wanda na kwantar na yanka? Kamar yadda Momy tace mistake ne, kuma kowa yana iya yin laifi ai dan adam ajizi ne ko?”

“Yeah.. Amman wannan kamar da banbanci Leila... ”

Ganin Leila zata yi mata wata maganar ta daban yasa Leila kawarta maganar ta hanyar dauko wata maganar.

“Ya aikin ki?”

“Alhamdulillah, ni aikin ma ya fara isata Wallahi”

“Kamar ya?”

“Ayukan ne basa karewa kuma gashi bama tashi da wuri, kuma zuwa kullum ne, ni da zan samu wani aiki ai da na aje wannan”

“Kamar ya zaki samu? Kin fa yi karatu ne Madina”

“Na sani amman idan ba irin kamfaninku ba ne da suke biyan ma'aikata da kyau kin san ba ko wane aiki zan iya ba”

“Idan kina son aiki a kamfaninmu ai zaki iya samu”

Madina ta wara ido tana murmushi.

“Da gaske?”

“Haba dai kina kawata ki nemi abu a gurina kuma ki rasa samu? Ki kawo takardunki kawai zan yi ma Daddy magana”

Da sauri Madina ta bar inda take zaune ta rumgume Leila tana wani irin murna. Leila ta yi dariya.

“Are you kidding me? Ai ko mahaifinku kika yi ma magana zai canja miki aiki domin su ne manya a gobnati, amman kina ta kewaye kamar wanda bata da kowa”

“Ba haka bane, Leila na dade ina mafarkin aiki a kamfaninku Wallahi”

“Amman shi ne baki fada min ba? Haba dai Madina ina ganin kamar mun zama daya ni da ke?”

“Ai da nauyi, amman dai yanzu komai ya wuce na gode sosai zan kawo takardun anjima ko gobe Inshallah na gode sosai dear ina kaunarki”

Leila ta yi murmushi.

“Karki damu, i trust you”

“Bari na tafi kar na yi latti”

Ta fada tana daukar jakarta ta rataya, sai Leila ta rakota har gurin motarta sai da ta shiga ta bar gidan sannan Leila ta juya ta koma ciki.



BATURIYA POV.

Har ta huta ta ci abinci yayanta be dawo ba, daman idan ya fita gurin kasuwancinsa baya dawowa sai dare. Batan ta yi wanka ta fito ta tari Napep ta nufi family house dinsu.
Tana shiga cikin gidan kannenta da mahaifiyarta suka hau murna kamar su hade ta. Ko minti talati ba ta yi da zama ba, Sultan ya shigo cikin gidan da gudunsa, kanwarta ta fara tare shi ta daga shi sama yana dariya.

“Sultan kaga Mama ta dawo?”

“Tace a daina cewa Mama sai Mommy”

Ya fada da yar siriyar muryarsa yana kallon Baturiya dake zaune falon.

“Kai da wa ka zo nan?”

“Daddy yana waje”

Wani tsaki taja ta dauke kai.

“Zuwa zai yi ya fara min bakar masifar nan Ko?”

“Aa ya isa? Ai Raliya ta fada masa halin da kike ciki, ko ma haka be faru da ke ba tun da ya ga baki dawo gida ba ai ya san ba lafiya ba, dole ya daga miki kafa”

“Uhm Umma baki san halin Faruq ba, Wallahi ni da nake tare da shi kawai na san ukubar da nake sha a gidansa, zai iya zuwa a nan ya nuna babu komai sai mun koma gida ya fara min masifa”

“Bayan duk hakurin da kike da shi? Cikin yan'uwanki ke kadai ce baki dace da daki ba Rafi'a, ba mu yi zaton haka ba”

Wannan maganar da Umma tai sai ya saka Baturiya ta kara bata fuska.

“Wallahi Umma ni kadai na san azabar da nake sha a gidan Faruq, bayan yunwa ga rashin sutura da kwadayi, ga masifarsa kamar ni na dora masa talauci”

Umma ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yarta cike da tausayawa.

“Shiyasa tun farko ni bana son auren nan na zumunci, mahaifinku ne ya dage sai an yi gashi nan ya tafi ya barki da wahala, haihuwa daya kenan nan gaba idan an tara yara me kike tunani”

“Ni ma tsorona kenan Umma, haihuwa daya, rayuwa tana ta mana haka balle nan gaba, kullum dai dai tai ta min karyar aikin zai fito amman shiru”

“Ni abun nasa har mamaki yake ba ni, wai ko dai be yi karatu mai kyau ba ne”

“Ni ina na sani, tun da ba fada zai yi ba, ni Wallahi makaranta ma nake son komawa, kar na bata nawa future na zama irinsa”

“Aiko da kin yi ma kanki abu mai kyau, sai ayi ma yayanku magana ya biya miki”

A take murmushi ya cika fuskarta.

“Da gaske Umma?”

“To miye a ciki idan ma be biya miki ba, ai ni zan biya miki”

Umma ta fi tausayin Baturiya fiye da kowa a cikin yayanta, domin ita kadai ce take auren matalauci talaucin da abun da zasu ci ma sai ya gagaresu wani lokacin. Ba wasu masu arziki ne can sosai ba sai dai suna da rufin asirin irin na yayan da suka dace da daki, domin kusan duk abun da ake ci a gidan yayyun Baturiya ne dake aure suke kawowa, sauran dawainiyar kuma babban yayansu ne yake yi, domin yana da rufin asiri irin na wanda kasuwanci yai ya aura.

“Sultan je kace Daddy ya shigo kar ya ce an barshi a waje”

Baturiya na fadi hakan Sultan din ya sauka daga kafafuwan kanwar mamansa ya nufi kofa da saurinsa, ko da ya fito Faruq na tsaye bakin karamin gate din gidan rumgume da hannayensa.

“Daddy ance ka shigo”

Faruq ya sakar masa murmushi sannan ya kama hannun dansa suka shiga cikin gidan, cike da nauyi ya shiga kasancewar baya samun riko musu komai idan zai zo, ba kamar sauran surukan ba da har mararin zuwansu ake saboda suna da rufin asiri, Baturiya ma ta sha fada masa shi kadai ne baya kawo komai idan ya zo, hakan yasa idan ba da wani babban dalilin ba baya son shiga cikin gidan duk kuwa da kasancewarsa dan'uwa, shi kansa ya san baya samun sakin fuska a gurin mahaifiyarta yadda ya kamata.
A bakin kofar falon ma tsayawa yai sai da aka matsa iso, sannan ya shiga cike da kunya ya nemi guri kusa da matarsa ya zauna bayan ya gaishe da sarakuwarsa kuma matar Kawunsa.

“Yanzu kika iso ne? Na dauka gida zaki wuce ai”

“Ko naje gida me zan yi tun da ba abinci ke akwai ba, yunwa kawai zan sha”

Juyowa yai da kyau ya fuskance ta.

“Rafi'a wannan wane irin magana ce? Idan ma kasa kike ci naga ai gidan aurenki ne”

“To karya na fada? Ni yanzu ga shi na rasa waya da sauran canjina”

“Rashin jinki ne yaja miki ai”

“Kaji ba bakar fata kawai yake min, shiyasa ai baka ma damu ka san inda nake ba sai yanzu”

Uffan be sake cewa ba ya kama hannun dansa yana wasa da shi.

“Ya kira ni ai ya tambaye ni”

cewar Raliya kanwar Baturiya. Sai mahaifiyarsu ta tashi ta nufi dakinta tana fadin.

“Allah ya kyauta”

Bayan ta wuce, Faruq ya kalli Baturiya.

“Tashi muje gida”

“Yanzu yanzu fa na shigo, sai na huta zan tafi gida”

Ta fada tana turo baki gaba tana hararsa kasa kasa.

“Rafi'a me ke damunki, sai ki rika min abu kamar ba mijiki ba, danki ne ni?”

“To idan naje gidan me zan maka? Yanzu fa na dawo ai sai ka bar ni sai na huta sannan anjima zan koma ai ban ce nan zan zauna ba”

Sanin cewar idan ya biye mata za su siyar da hali ne a gidan da ba a ganin mutunsa da kimarsa ne yasa be sake ce mata komai

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment