Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma can kusa da gadon ta kwanta kasa ta takure kanta sosai kamar zata shige karkashin gadon. Bachi da bata farka ba kenan har sai da yai sallah asuba ya tashe ta. Sai ta farka a firgice duk da kasancewar a hankali yake tashinta.

“Tashi ki yi sallah”

Ta fara murza ido, sannan yunkura ta tashi ta nufi bandaki tana takawa a hankali kamar yadda take har ta shiga, bata sha wahala gurin kunna fanfo ba domin ta kula da yadda ya kunna mata fanfon jiya. Bayan ta gama alwala ta fito sai ta same shi zaune gefen gado yana karantu a alqur'ane da wayarsa, inda tai sallah jiya a gurin ta sake yin sallah asuba. Bayan ta gama ta daga hannunta ya yabi Allah ta miyar godiyarta a gareshi sannan ta yi salati fa Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wassalam, kana ta bijiro da bukatarta na naman gafara ga iyayenta, sannan tai ma maka na neman mafita da madafa, sai kuma ta rufe tana yi ma al'ummar Musulmi, ta dora da salati. Jinginawa tai jikin gado tana ta sauraren karatun da yake da muryarsa mai dadi saurare, sai ta lumshe ido kamar mai bachi alhalin ba bachin take ba. Sai da ya kai karshen suratul Ibrahim sannan yai addu'a ya aje wayar ya kalli inda take jingine jikin gadon idonta a rufe. Hakan nan kawai ya ji yana bukatar gyara mata kwanciyar kanta jikin gadon domin bata aje shi yadda ya kamata ba, wuyanta zai iya ciwo. Tashi yai ya karasa gefen gadon a haka ya kai kyakkyawan hannunsa ya kama fuskarta da zimmar kwantar da ita sai ta bude. Idanuwanta da na shi suka sarkafewa juna, ko wanensu ya kasa yin kawaicin dauke nasa, a zahirin kyaun idanuwanta yake kallo, a yayinda fuskarsa da idanuwansa suke mata kwarjini.

“Ina kwana... ”   “Ina kwana... ”

Suka furta a tare muryarsa ta muryarta sukai tarayya a lokaci daya, kamar yadda numfashinsu sukai auratayya da junansu, ta hanyar shiga da ita a tare. Ta kowace kusurwa a hancinta na shigar mata da kanshin turarensa, ya samu guri can kasan ruhinta ya kwanata. A yayin da shi shiga da fitar numfashin yake shiga tare da bugun zuciya mai tsanani. Ita ta fara dauke idanuwanta tana murmushi kadan, sai kuma murmushi ya cika bakinsa har ya kawata fuskarsa, mikewa yai tsaye yana kallon kofa.

“Kar mu yi latti, ki shirya sai mu tafi waje mu karya, sai mu kama hanyar”

“Toh Yallabai”

Ta amsa tana kokarin mikewa tsaye, sai ya nufi kofar dake kallon yana jin sunan wani iri wai Yallabai, sound so funny. A falon ya dawo ya zauna har sai da ta fito sannan ya juyo ya kalleta he thought ko zata yi wanka ne ta canja tufafin jikinta.

“Baki yi wanka ba?”

“Baka ce na yi ba”

Ya wara ido.

“Komai sai na ce ki yi? Come on ba ki bukatar komai sai na fada miki fa”

Juyawa tai ta koma ciki bathroom din ta shiga bata ga soso sai sabulu da shower gel kusan kala uku. Bata san abun da ake da shower gel din ba hakan yasa ba tai karanbanin tabawa ba, sai kawai tai amfanin da sabulun tai wanka, bata yarda ta fito ba sai da ta leko ta ga baya cikin dakin sannan ta nufi inda akwatinta yake da saurinta kamar ba mai ciwon kafa ba, ta bude akwatin ta dauko doguwar riga ta saka tana kokarin daura dankwalin ya shigo sai tai saurin juyawa ta bashi baya, shi kuma sai ya fice yana jin wani iri.
Be sake dawawo dakin ba har sai da ta saka hijabinta ta fito falon.

“Na gama”

Juyowa tai ya kalleta ita ma kallonsa take kamin ta kalli jikinta ganin yadda ya kura mata ido. Sai ya mike tsaye ya shiga bedroom din ya hada tufafinta har Wadanda ta cire a cikin akwatin sannan ya janyo akwatin ya fito da shi, yana gaba tana binsa a hankali har suka fita falon, cikin karfin hali ta karasa gurin daya faka motarsa shi ya fara bude mata kasancewar ya rigata isa gurin motar sai ta shiga gidan gaba ta zauna, bayan ya saka akwatin a mota ya koma ya rufe kofar falon sannan ya nufi gate ya bude ya dawo cikin motar yai mata key.

“Zan fara biya gida na yi wanka n canja tufafi sannan na tafi”

“Toh Yallabai”

“Talba, idan ba zaki iya ba ki kira ainahin sunana Mu'az”

Ya fada yana reverse sannan ya fita da motar gaba daya, ya dawo ya rufe gate din sannan ya sake komawa cikin motar ya ja suka dauki hanyar Shimkafi road.
  A lokacin daya isa kofar gidan sai ya faka motarsa daga waje, sannan ya fita ya nufi gate din yai knocking aka bude masa, ya shiga ciki suna ta mamakin ganin motarsa a waje kuma a jiya be kwana gida ba. Be shiga bangarensa ba sai da ya fara shiga part din Daddy ya gaishe shi sannan ya fito ya nufi part dinsa, a gaggauce yai wanka ya fito be tsaya shafa komai ba sai turaren daya zame masa jiki sannan ya dauki abubuwna bukatarsa ya saka aljihun shaddarsa ya saka agogon hannunsa sannan ya fito yana ta sauri kar Daddy ya riga shi fitowa ya ga Aminatu a motarsa, gashi yayi sa'a Daddy ya manta be masa maganar tafiyarsa kauye ba kamar yadda ya sanar masa a jiya, wata kila Daddy ya dauka ko sai da rana zai tafi ko kuma ya fasa ne, yana ta sake sake ya mai gadin ya bude masa gate ya fita. Sai ya hango motar Leila kusa da tasa motar rage tafiyar da yake yai yana nazarin a gidan ta kwana ko kuma yau ta dawo? Ta dade a gurin.

“Miyasa kike zargina da abun da ba ni na aikatawa kaina ba? Ke kin fi karfin Allah ya jarabeki ne?”

Aminatu ta tambaya cikin wani irin kuka marar misaltuwa.

“Me ke faruwa”

Talba ya tambaya a lokacin daya karasa kusa da su, Leila da ta baro motarta ta zo gurin Aminatu ta tsaya ta kalleshi.

“Babu, kawai na tambaye ta ne ya ta ji a lokacin da mutum fiye da goma suka keta mata haddi? Kasan me? Kai nake kokarin tunawa cewa wannan gwanjo ce, wadanda wasu suka gama amfani da ita suka jefar wasu man kuma wulakantaccin mutane da basa wanka sai sun ga dama, basa sallah kuma kashe mutum ba ya musu wahala, amman ka dauko ta kake kokarin motsa kishi na da ita...”

Tana kai aya Talba ya wanke mata fuska da mari cikin wani irin zafin nama da bacin rai.

“Taya kina mace zaki aikatawa mace yar'uwarki haka? Allah ya wadaran halinki Leila”

Ta dafe kunci hawaye na sauko mata, Aminatu kuma ta duka a gurin dafe da zuciyarta tana jin wani irin zafi da tukiki na kalaman da Leila tai mata, sai ta fi jin zafin kalamanta fiye da abun da mutanen suka aikata mata, ashe haka ake ji? Tabbas jawabi ba shi da dadi, yanzu bayan duk abun da ya faru har akwai wanda zata yi kokarin koranta mata a halin rayuwar da ba ta zaba ma kanta ba?

“Ka mare ni Talba saboda wata bare? Ka dauko ka kawo har kofar gida, ban kwana a gida ba, yanzu na dawo amman ina da tabbacin ita ma din a tare da kai ta kwana! Ko kadai ne namiji daya rage a duniya na hakura da kai Talba...!”

Ta fada kai tsaye hawaye na sauko mata, tana kallonsa ido cikin ido.

“Idan ka haihu ga ta uba da uba, ka auri yarinyar Talba...! Ka aureta sai na san son da kake mata na hakika ne, sai na san ka cika ka tumbatsa da tausayinta, sai na san ka amsa sunanka Talba”

Ta fada tana nuna shi da yatsa hawaye na sauko mata. Hannu ya kai zai kama hannunta sai ta kauce ta nufi motarta ta shiga ta fasa shiga cikin gidan ta juya ta koma inda ta fito tana fisgar motar. Sai ya ji babu dadi kamar be kyauta mata ba, not because of tace ta fasa aurensa but because of ya san kishi babu abun da baya sakawa ya kamata yai mata uzuri, and be kamata ya zo da Aminatu kofar gidan ba first place har ta gani, ba ita ba ko Daddy ya gani ya san ba zai jidadi ba.

“Shiga mota mu je”

Ya fada yana kallonta, sai ta mike tsaye tana kallonsa tare da girgiza masa kai.

“Aa dan Allah kai yi hakuri, ba zan iya ba, ka taimake ni iya taimakon da zaka iya kuma na gode Allah ya biyaka, be kamata na shiga tsakaninku ba, karka yarda ka rasa yan'uwanka ba zaka taba samun mai maye maka gurbinsu ba, dan Allah ka bar ni na yi tafiyata”

Be bi ta kanta ba ya kai hannunsa ya rika cinyar hannunta ya saka a motar da karfi ya rufe sannan ya zagaya ya shiga bangaren direba yaja motar suka kama hanya.
  Kuka take sosai cikin motar mai sauti, and what he hate the most is kuka, ko na yara ne baya so, yana tukin yana kallonta sai be ce mata yi shiru ba balle kuma ya tattara kalaman bada hakuri ya bata. Sai da suka kusa fita gari sannan ya tsaya gurin wani restaurant ya siya mata abinci domin shi dai baya jin zai iya cin komai a yanzu bayan ruwan sanyi da riko ma kansa.
A gidan baya ya aje ledar abinci ya dawo driver side ya zauna tare da ruwan gora a hannunsa, sai da ya fara sha sannan ya mika mata ba tare da ya ce komai ba. Sai ta karba ta kai bakinta ta sha kadan ta mika masa sai ya karba ya rufe gorar ya ajera a muhallin da aka tanada domin ajeta a cikin motar, sannan ya cigaba da tukin. Suna hawa babban titi zuwa sokoto sai ya kara ac ya kwantar mata da kujera, nan da bachi ya dauke ta.
  Har aka isa cikin garin maradun bata sani ba, har sai da ya faka gaban wani wadataccen gida dake unguwar gabas, ya kashe motar yana kallonta, sai kuma ya sake daukar ruwan ya sha ya rike gorar a hannunsa ya bude motar ya fita, kamin ya zagaya side dinta har ta bude idon ta tashi zaune tana kallon garin da yai yanayi da na su.

“Fito”

Ta fito tana kara kallon garin da take kyautata zaton ta taba zuwansa sau biyu zuwa sau uku a rayuwarta, sai dai ba zata iya kawo kanta ba. Rufe motar yai ya matsa key din hannunsa, shi kansa yana missing din garin da gidan da kuma mutanen da suke cikin gidan. Yalwataccen gida ne da itacen dogon yaro suka kawata shi ta ko'ina daga ciki kuma irin dogon itacen nan ne da ake cewa bedin turawa, ko'ina na gidan ya sha simimti kamar ba kauye ba. Tsaye tai sai da ya fara wucewa ya shiga ciki sannan ta bi bayansa tana ta karewa gidan kallo.

“Tsohuwa... ”

Ta furta tana ta kara kallon gidan, Talba ya kalleta sai dai be ce komai ba ya cigaba da tafiyar har suka shiga cikin gidan, abun ka da family house a take gidan ya dauki ihu suna ta murna da ganinsa, wasu kuma na dan kallon Aminatu suna ganin kamar sun santa ita ma haka take ganin kamar ta taba ganin fuskokinsu.

Sai da Talba ya gaisa da su, tabasansa suka hau tsokanarsa suna masa wasa da ce masa baya son zumunci.

“Wannan fa ko ita ce matar ta mu ka zo ka nuna mana?”

Ya kalli Aminatu yayi murmushi.

“Aa”

Shi ne kawai abun da ya fada sannan ya nufi bangaren Kaka. Kamin ya shigo murmushi da farinciki ya cika fuskarta, sai dai ganin Aminatu a bayansa ya saka ta manta da komai tana kallon Aminatu. Aminatu ma Kallonta take sai ta fashe da kuka ta karasa inda take da sauri domin ta manta da wani ciwon kafa, sai ta fada jikinta tana kuka.

“Tsohuwa...”

Kaka ma fashewa tai da kuka ta rumgume Aminatu tana kuka sosai, sai kara nerkewa take jikinta kamar zata shige cikinta.

“Auta... Laaa sai yanzu na gane ta”

Wata babbar mace dake tsaye kusa da Talba ta fada, sai Talba ya kalleta ya sake kallon Aminatu dake rumgume da Kakarsa tana kuka, mamaki ya hana shi cewa komai.

“Aka ce an kashe kowa, ashe ba gaskiya ba ne”

Matar da tai magana dazun ta sake fada, tana hawaye cike da tausayi.

“Kun santa ne?”

Talba ya tambaya.

“Eh jikar kawo Bala ce dake Galadi”

Talba yayi shiru yana mamaki, ya san kawo Bala dai dai ba kowa ya sani ba a cikin yayansa balle ya har ya sheidi jikansa, daman a familyn Mahaifiyarsa ba kowa ya sani ba, da dai na Daddy ne ko Momy sukan kusan zai iya shaidar kowa.




LEILA POV.

Da kuka ta shigo gidansu Madina, ko gaisuwar da ta saba yi ma mahaifiyarsu Madina bata iya yi ba a yau saboda kukan da take. Cewar da tai ta fasa auren Talba ya fi komai daga mata hankali miyasa ta fada masa haka? Bayan ta san har ga Allah ba zata iya rayuwa babu shi ba?
Madina na ganinta ta kama hannunta suka shiga dakinta ta zaunar da ita gefen gadonta hankali tashe.

“Subhanallahi, Leila mi ke faruwa?”

Leila ta kama hannun Madina ta dora saitin zuciyarta da take jin kamar zata fashe.

“Talba Madina Talba...”

Madina ta fisge hannunta tana jan tsaki.

“Ba ki taba ba ni haushi ba akan Talba sai yau, akan Namiji kike wannan kukan Leila? Me kuma ya faru?”

Haka nan cikin kuka ta labarta mata abun da ya faru. Sai hankali Madina ya tashi fiye da na Leila, jin cewar Talba ya kwana gida daya da Aminatu, kuma har ya mari Leila akanta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ta fada tana mikewa tsaye.

“Bana son na je gurin Momy ne na tayar mata da hankali”

Leila ta fada cikin kuka tana jin zuciyarta kamar zata nerke.

“Leila kar fa abun da muke gudu ne zai faru, miyasa kika masa wannan furucin, kin san halin Talba da zuciya”

“Ba zaki ga laifin abun da yai min ba? Sai nawa kike gani?”

“Ba wai ban ga laifinsa ba ne, mafita nake nema mana”

Ta dawo ta zauna.

“Kin san me? Zan iya rantsuwa Talba ba zai auri yarinyar nan ba, amman kar shedan ya rinjaye shi ya fada a halaka mu kuma mu fada a komar da na sani”

Madina ta rika Leila tana kokarin tashinta tsaye.

“Kin san me? Je ki wanke fuskarki wannan lokacin ba na kuka ba ne, idan kalaman da kika yi zaki iya kiransa ki bashi hakuri”

Leila bata musa ba, ta shiga bandakin tai wanke fuskarta domin ta san Madina bata dorata a shawarar banza. Bayan ta fito ta tararda Madina ta kawo mata ruwan sanyi da cup dai ta dauka ta zuba ta sha, ta sake zubawa ta sha sannan ta aje kofin tana kallon Madina.

“Me minene mafita? Ni ba zan iya bawa Talba hakuri ba, yadda yake ji da kansa haka nake jin kaina, kuma shi ya kamata ya ba ni hakuri ai”

“Ba ta wannan ake ba yanzu, kin san abun da nake ganin shi ne mafita? Ki lallaba Momy ta dawo gidan nan idan ta dawo sai ki sake lallabata ta saka Talba ya dawo da yarinyar nan gidan nan”

Leila ta yi mata kallon rashin fahimta.

“Ta dawo gidan kuma? Idan ta dawo ai sai abun ya fi haka ma, kin manta yadda ya fara yi ne akan wannan banzar”

“Ai inda yake tare da ita a can yana kara kusanci da ita ne, amman idan aka dawo da ita a nan komai zai faru kina gani”

“Wannan ba mafita ba ce, domin zai iya disgani a gabanta idan na yi mata wani abun”

“Ai ba haka zamu samu wanda sai aureta, sai mu biya shi kin ga mun huta, ke kuma sai ki biro masa da maganar aurenki”

Leila ta yi shiru tana nazari kamin ta kalli Madina da murmushi a fuskarta.

“Haka yayi, amman Talba zai iya zargin wani abu”

“Zamu yi abun ne cikin hikima ba tare da kowa ya gane ba, ke dai ki bar komai a hannuna, kuma ki bincike Ali domin mu san inda yake aje yarinyar”

“Zan yi hakan, amman kina ganin Talba zai yarda”

“Dole ma ya yarda, idan yarinya ta kamu da son mutumen me zai iya yi? Kin ga mun dauketa cikin rayuwarmu cikin sauki”

Leila ta yi murmushi tana kallon Madina wanda ita ma murmushin take.

“Yanzu ki kira Ali ki fada masa abun da ya faru cikin, kuka daga nan sai ki bincike inda yarinyar take”

“Okay”

Ta amsa tana ciro wayarta a jaka ta kira Ali fuskarta da murmushi kamar ba ita ce ta shigo dazun fuska sharkab da hawaye ba. Yana yin picking ta fashe masa da kuka.

“Subhanallahi Leila lafiya dai?”

“Ali ina cikin matsala kana ina dan Allah?”

“Ina gurin aiki”

“Gani zuwa, zan so na same ka yanzu”

“Okay sai kin zo”

Ta sauke wayar tana kallon Madina, sai su kai murmushi a tare.
32

Ko kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa


*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Tana daga waje zaune cikin mutanen gida, sai dai hankalinta ya tafi wani gurin dabam, domin kana kallonta ka san tana zaune a cikinsu ne kawai amman bata sauraren hiran da suke.

“Ai akwai makaranta mai kyau ko kaka?”

Kaka ta kalleshi tana jar carbin hannunta, idonta har ya sauya kala saboda kukan data sha na labarin da Aminatu ta bada.

“Akwai, akwai inda babu boko a yanzu? Ai sai dai idan mutum baya son saka dansa”

“Sai a sama mata makaranta mai kyau a saka ta, tun da gaki a kusa da ita”

“Karatu yana da kyau, amman ba karatu ne abun da Auta take bukata ba a yanzu, miji mai tsoron Allah wanda zai riketa da mana, domin a duk lokacin daka rasa uwaye, miji ne yake maye maka gurbinsu idan ka samu n gari, idan ni, ni ma ai ina kusa da mutuwa, wanda be tsufa ba ma ya jira mutuwa balle ni”

Kaka ta saka hannu ta share hawayen daya zubo mata.

“Mahaifin yarinyar mutumen kirki ne ga zon zumunci, ko dan'uwa be san shi ba shi sai ya san dan'uwa, zuwansa biyu da Auta zuwa na biyo ya dauke ni ya tafi da ni na ga iyalansa sannan ya sake dawowa da ni, ashe ganin karshe kenan na yi masa”

“Allah ya masa rahama, amman ya kike da shi?”

“Da ubansa da ni uban mu daya, ubanmu, ni an auro uwata daga nan aka tafi da ita can, a lokacin da Allah ya iyakance auren sai aka rabu, ta dawo a nan maradun tare da ni, shi kuma suka zauna can, wadannan Bandits sun hana yi kowa zaman lafiya, Allah ya isarwa yarinyar nan”

“Ameen, tana ba ni tausayi sosai, shiyasa ma na yanke shawarar kawo ta nan ta zauna tare da ke ashe ma yar'uwa ce”

“Ta fada min abubuwan da suka faru, ban jidadi ba mutum ko ba san inda ya fito ba ka ga yana bukatar taimako ai sai ka taimaka masa, balle har kai ka kawota, irin yarinyar nan ai bana jin ko bakar magana ta cancanci a fada mata”

Kaka ta sake share hawayenta.

“Ubanta be yi komai ba sai alheri, da shi ne da yanzu ya kame dan wani ya rumgume, amman ga tasa na watangaririya har ana wulakantata, mutane kwarai su ake ta kwashewa ana barin na banza”

Ta saka tsumman dake gabanta ta share majinar hncinta, sannan ta kalli Talba dake zaune kan gadonta.

“Da ace na isa da kai da na saka ka auri yarinyar nan...!”

Talba yayi saurin kallonta.

“Kaka ai... Ina da wanda zan aura kawai dai lokaci ne be yi ba”

“Ban sani ba, saboda ba a fada min ba, ni ai talaka ce shiyasa ba a sakawa da ni balle a kwance, ganina ma sai ka ga dama kake zuwa yi, yanzu ma ba dan kana neman inda zaka aje ta b ada ba zan ganka ba wata kila sai na mutu, saboda uwarka na haifa ba uba ba, shiyasa ban isa na saka ayi ba ko hana, ban isa na san komai ba”

“Ba haka ba ne kaka, idan kin kula Aminata ba aure take bukata ba a yanzu, kuma kin ga Daddy ya zaba min Leila taya zan zo masa da maganar wata kuma?”

“Ba aure take bukata ba? Saboda bata kai mizalin auren ba? Ko kuma saboda ita jinin talauchi ce kamar ni? Ko kuma saboda kana dan Boko ita tana yar kauye? Ko kuma saboda tsatsona ce? Ita wacan da yake bangaren ubanka ta fito ai ka aminta ko?”

“Ba haka ba ne Kaka kin yi min kuskuren fahimta, tun kamin yarinyar nan ta zo an tsayar da maganar auren mu da Leila, rana ce kawai ba a saka ba”

“Amman ai ba a taba fada min ba, saboda an maida ni talaka, wato da sau lokacin auren yayi sai a fada mana ka yi aure ko kuma zaka yi? Daman tun da aka haife ka suka saka hannu suka dauke ka, ba suke waiwayar inda muke ba, dangin ubanka ai babu wanda baka sani ba, amman na nan sai dai su suce sun sanka, ina matsayin mace data haifi uwarka amman sai ka share shekara biyu baka zo inda nake ba, na tabbatar da in da arziki da kullum sai ka ziyarce ni, Shi wacan uban daya dauke ka be nuna maka ka so dangin uwarka ba, balle ya nuna maka ka bisu”

“Ba haka ba ne, Kaka dan Allah karki fadi wata mummunar magana akan Daddy, ba shi da laifi a nan”

“Daman ai ba zaka ga laifinsa ba, ba zaka yarda ka bata masa rai ba, amman ni da nake uwar data haifi uwarka a baka gudun bacin rai na, kuma baka damu da ni ba, to ni ma babu ruwana daga yau duk wani abu naka babu hannuna a ciki, ba aure ba ko mutuwa kai kar a fada min, kuma ni bance idan na mutu ka zo gaisuwa ba”

Kaka ta karasa a fusace, tana dauke kafafuwanta daga dayan bangaren ta maida dayan. Talba ya mike tsaye da sauri yana furta

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ganin yadda karamar magana ta juye ta zame masa babba. Har ga Allah shi dai ba zai ce yana son Aminatu ba, ko a da can da yai yunkurin aurenta zai yi ne saboda gudun fadawa halaka da kuma tausayinta da yake amman ba dan yana sonta ba, a yanzu kuma yana ganin ta samu mafita na gaduwa da wasu daga cikin danginta yana ganin kamar komai zai zo masa da sauri ita ma ya zo mata, sai kuma Kaka ta zo masa da wani sabon zancen kamar saukar aradu.
Zuwa yai ya durkusa a gabanta ya dafa hannayensa yana kallon kakar tasa data dauke kai.

“Haba Kaka, ni ma ai abun tausayi ne, ina zan iya da mata biyu a yanzu? Kin san ni ba mai son rigima ba ne”

“Ban sani ba, ai baka tashi a gabana ba balle na sani, su isassu su suka san abun da kake so da wanda baka so, ni ba zan cilasta ka aurenta dole ba, daman ai ban isa na yi hakan ba, amman Wallahi Mu'azu wannan ne abu na karshe da zan roki ka yi min, har kasa ta rufe idona”

Ta karasa idonta na cika da hawaye. For the first time da Talba ya aikata wani abu ya ji ina ma be aikata shi ba, a yau kam ya ji kamar ace be zo garin nan da Aminatu ba.

“Amman kaka yarinyar nan bata dade ba

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment