Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nemi wani abu ta rasa, wata wani abu painful irin na wannan daren ba, a damuwarta akan halin Talba ne, amman a yanzu abun ya ninku tana jin kamar ba zata iya yakar kaunarsa a zuciyarta ba, kuma ba zata iya barin kaunar ta zauna ba then me zata yi?
Ta yi kasa da kanta wasu hawaye na sauko mata, ta fashe da kuka marar sauti, sai kuma ta soma murmushi.

“Ni Leila ina kukan namiji? Wannan ba ajina ba ne, at least na san Talba be isa yace ba zai aureni ba, amman ni din ai be kamata na aure shi bayan duk wannan abun da yai min ba, be kamata na damu ba”

Ta share hawayenta, sai magana take da kanta tana kallon harabar gidan kamar wani bakonta. Can kuma ta rumgume hannayenta tana tuna kalaman Kabir cewar Talba yana son ta, sometimes akwai kamshin gaskiya maganarsa, amman idan har Talba baya son ta waye zai so? Dole dai ita din ce.

“Akwai maza da yawa da suka fi Talba komai a duniyar nan, kudi, kyau, aji da komai ma, idan zan ba wa maza da yawa dama zan samu wanda zan so fiye da Talba ma”

Wannan karon with full confidence tai maganarta tana jin cewar zata iya. Ba laifi ta dan samu karfin guiwa da dakiyar zuciya, hakan yasa ta rufe window ta dawo saman gadonta ta hau ta kwanta ya rumgume filo ta lumshe ido tana son bachi ya dauke ta.
A nan ne bachi ya ce mata fir ba dai shi ba a yanzu, tunanin abun da Talba yai mata sai ya dawo mata a rai ya zauna, idonta zuciyarta kuma a bude, har kusan karfi uku na dare, Leila ba mace ce ma'abociyar karatu ba balle ma har tai tunanin raya daren da nafila.
Bata yarda ta bude idon ba duk kuwa da kin bata hadin kai da bachin yai. Sai kusan asuba bachi yai gaba da ita.
  Washe gari Sunday kamar jiya kowa ya hadu a gurin cin abinci ban da Leila, sai dai a yau bangaren Momy aka zauna ba kamar jiya ba da aka karya bangaren Daddy.
Daddy ya gama duba kowa be ga Leila, hakan ya saka ya kalli Momy.

“Doctor ina Leila?”

“Tana dakinta i think”

Daddy ya yi mata wani kallo da kyau.

“So you think? Lafiya take na lafiya tana dakin ma ko bata ciki baki da tabbaci?”

“Uhm wani lokacin kana bani mamaki Alhaji, yaran nan fada wayansu ya kamata idan muka gan su a wani yanayi da suke son kebancewa mu bar su a yanayin da suke ciki”

“Amman idan suna da damuwa fa? Har kullum wanda ka haifa kana masa kallon yaro ne ko da kuwa ya girmi duniyar nan, irin wannan abun shi yake haifa da depression mutum yana da damuwa kuma a kasa maganance masa ita ko a ki kula da shi, wannan be dace ba, ko jiya bata ci abinci safe tare da mu ba”

Momy ta tabe sannan ta kwalawa Mairo kira, Mairo dake kitchen tana wanke kayan da sukai amfani da su, ta amsa tana fitowa da sauri.

“Shiga dakin Leila ki kirata”

“Hajiya Wallahi ko dazun dana shiga gyara dakin fada tai tayi tace idan a sake shiga dakinta ba tare data fito ba ko kuma na tashe ta bachi sai ta mare ni”

Mairo ta fada a ladabce. Sai Daddy ya kalleta.

“Ta mare ki? Yarta ce ke?”

“Wata kila fada dakin ne ba sallama ko knocked”

Momy ta amsa.

“No wannan ba dalili ba ne, at least ai ta girmamasu sun gurme ta nesa ba kusa ba”

“Wallahi Daddy haka take musu, ko magana cikin tsawa take yi”

Amal ta dora da nata, sai Daddy ya kalleta sai dai be ce komai ba ya cigaba da cin abincinsa, Daddy mutum ne mai matukar son yayansa, ko kadan baya son ya ga wani abun bacin rai ko n damuwa ya same su, sai dai hakan be taba saka shi ya kyalesu a inda ya kamata ya gyara musu ba kuma ya saka musu ido.
Sai da Daddy yai rabin cin abinci sannan ya kalli Momy ya ce.

“Yawan fushi ko tsana yana nuna akwai abun da yake damun mutun ne, musamman a kwana biyun nan da bata fitowa cin abinci, idan akwai wani abu da yake damunta ki sama mata mafita, akwai abun da ke ya kamata ki yi a matsayinki na uwa, zata fi sakewa da ke kuma ta bude miki cikinta ta fada miki damuwarta, and to you my friends idan akwai wanda yake mata wani abu da zai sakata a damuwa ko bacin rai dan Allah ku daina, ya zama tsintsiya madaurinki daya, idan dayanku yana cikin damuwa ku yi kokarin ganin kun kawar masa Allah ya hada kanku yai muku albarka”

Duk suka amsa da Amin, sannan Daddy ya mike tsaye yana fadin.

“idan kin yi magana da ita, ki fada mata ina son ganinta”

“Okay”

Momy ta amsa tana watsawa Talba harara kasa kasa domin har ga Allah yanzu haushinsa take ji, saboda yana kokarin wuce gona da iri. Sai da Daddy ya fice daga falon sannan Momy ta dakawa Amal tsawa

“Amal... Wallahi idan na sake jin bakinki akan fadawa Daddy magana any how sai na baki mamaki, sai na miki hukuncin da baki taba mafarkin zan miki ba, cigaba karki fasa”

Momy ta karasa tana dukan burin dinning din sannan ta mike tsaye ta bar gurin a fusace. Amal ta bata fuska kamar zata fashe da kuka, Kabir ya saka mata dariya. Talba ya kalleshi.

“Kabir?”

Ya sake bushewa da dariya yana yi ma Amal gwalo.

“Sai a hana ni dariya? Yarinyar tafi kowa iya gulma, bata gidan amarya bata gidan ango ai maganinki kenan”

Dariyar ya cigaba da yi mata yana cin abincinsa, ita kuma ta kara bata fuska kamar zata fashe da kuka.

“Karki biye Kabir kin san halinsa ai, daman so yake ki yi kuka, karki yarda ki masa kuka”

“Ai ba zan masa kuka ba, na fi karfin na yi masa kuka”

Ta fada tana matse hawayen dake son fito mata. Kabir kam ban da aikin dariya babu abun da yake mata, daman shi haka yake gurin dariya da keta shine a gaba gaba.
Talba be bar dinning din ba sai da cikinsa ya cika, sannan ya tashi yana handala da muryar da shi kadai zai iya jin kansa ya nufi bangarensa.
Tufafin jikinsa ya cire ya saka gajeren wando sannan ya hau gadonsa ya kwanta, da zimmar bachi amman ya ji kamar ba zai iya bachin ba, hannunsa ya mika ya dauki wayarsa dake gefen gadon, sai ya tararda miss calls har hudu daga Ali. Ganin kiran na Ali ne ya tuna masa da Aminatu, sauka yai saman gadon ya nufi bandakinsa, ta bata minti talati yana jika jikinsa sannan ya dauki man wanka ya zuba ya soma gogawa a jikinsa. Bayan ya gama wankan ya fito daure da tawul dayan kuma a hannunsa yana goge jikinsa da shi, gaban madubin ya zo ya tsaya da alama dai kallon kansa a madubi abu ne daya zama masa al'ada, domin yana jindadin tsaya a madubin yana kallon kansa.
Sai da ya tsane jikinsa sannan ya dauki wani mai ya shafa a jikinsa ya feshe jikinsa da turare, ya murza wani a shafa a jikin, sannan ya shirya cikin kananan kaya ya dauki turaren tufafi ya saka sannan ya murza wani a hannunsa, sai ya juya ya nufi gurin da yake aje agogonsa ya dauki wanda yake ganin ya fi dacewa da tufafin jikinsa ya saka, ya saka talkaminsa sannan ya dauki wayarsa ya da wallet dinsa ya saka aljihu ya dauki wata Jacket milk color ya dora sama. Sannn ya fice dakin rike da makullinsa na mota. Sai da ya isa gurin motarsa sannan ya daga kansa yana kallon windows din dakin Leila, bakinsa ya cika ma iska sannan ya bude motar ya shiga. Ko kamin ya juya motar har sun bude masa gate, kamar dominshi kadai aka shimfida titi, haka ya fige mota ya hau titi yana driving. Kiran Ali ne ya sake shigowa wayarsa, sai ya saka hannunsa ya dauko wayar daga aljihunsa yai piciking.

“Hello”

Ali ya fada daga dayan bangaren sai Talba ya amsa masa kamar baya son magana.

“Ya akai?”

Ali yayi dariya.

“Kar kace min har yanzu fushi kake, Ni da n kira na fada maka ka ya kamata ka bawa Leila hakuri, sai kuma na ji ka a fushi har yanzu”

“Ali taya na kusa da ni zai wulakanta dan adam ya muzanta shi kuma ka tsammaci abun nan zai wuce da sauri? Kawai fatan da nake ya zama na babu hannun Leila a taba yarinyar nan, and zan binka matsalar Baaba na tabbar idan akwai hannunta ko babu”

“Wace Baaba kuma? Talba are you in sense? Miya samu Baaba and why za kai blaming Leila? Ban taba yarda baka son ta sai...”

Ali be karasa Talba ya yanke kiran ya aje wayar ya cigaba da tukinsa, ya san idan zai bata lokaci yana ma Ali bayani a yanzu ba zai fahimta ba saboda yana ganin tausayin Leila kuma yana ganin kamar Talba yana mata haka saboda baya sonta.
  Be sake bin ta kan wayar ba har ya isa asibitin ya faka motarsa a inda aka tana domin aje motoci, sannan ya dauki wayar ya bude motar ya fita.
  Kai tsaye ya dauki hanyar da zata sada shi da dakin da aka kai Aminatu, so kawai yake ta farka ya tambaye ta, idan ta amsa masa da eh zai dauki mataki akan Leila idan kuma ya zama tsabanin haka zai bata taimakon da take bukata be kuma zama lallai ta sake ganinsa ba. Ba dan wannan abun daya faru ba wata kila ma da ba za zai sake sakata a idonsa ba har abada.
A hankali ya kai hannunsa ya tura kofar dakin, sai kuma ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta, kwance take idonta a rufe hawaye na sauko mata, an cire mata robar jinin an saka mata ta ruwa, sai kuma ledar pure water dake saman dan karamin tabur din dake kusa da gadonta. Silently ya shiga cikin dakin ya maida kofar ya rufe, sannan ya isa gurin gadonta yana kallon fuskarta, ko kadan bata ji motsin bude dakin ba balle kuma shigowarsa ba, sai dai kamshin turarensa ya dawo da ita duniyar tunanin da tafi, hakan yasa ta bude idon a hankali a karo na biyu ta sake saka idonta cikin nasa, bayan wacan karon da suka zo tare da Ali, sai dai yanayin fuskarta sa ya tsorata, da alama ba mutum ne alaka da sakin fuska da murmushi ba. Sai dai kallonta yake kamar yadda ita ma take kallonsa hawaye na cigaba da sauko mata.

“Can you talk?”

Ta tambaya domin burinsa ta amsa masa da eh ko aa. Sai ta maida idon ta rufe.

“Keeee.!!!”

Ya daka mata tsawa, sai ta bude idon a zarane ta tashi zaune jikinta na rawa ta fara dube dube, domin ta tsorata matuka, abu kadan sai zuciyarta ta fara bugawa tana ganin kamar abun da ya faru ne a baya zai sake faruwa.

“Mi na yi, kashe ni za ayi?”

Tsayawa yai kallonta a ransa yana jinjina irin tsoratata da Leila tai. Be ankaro ba ya ji ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya, hakan ya saka shi matsowa kusa gadon.

“Ba komai za a miki ba tambayarki kawai zan yi”

Ta kalleshi jikinta na cigaba da rawa hawaye na sauko mata kamar ba gobe.

“Me zaka tambaye ni? Inna? Ko Baba? Ko kuma yan'uwana?”

Shiru yai yana kallon yadda idonta yai ja tsabar kukan da take, ya hade yawun bakinsa tare da maida numfashi a hankali.

“Ki kwantar da hankalinki babu abun da za a miki, kawai ina son na tambaye ki ne ko akwai wanda yai kokarin kasheki kamar makura, saboda an samu hannunta yana zubar da jini kuma roba zagaye a wuyanki”

Kokarin natsuwa take tana son tuna abun da ya faru, sai ta daga kanta tana kallon dakin, sai a yanzu ta tuna akwai banbanci tsakanin wannan dakin da wacan.

“Zaki iya tunawa?”

Ya sake tambaya.

“Ban manta komai ba, komai yana cikin kaina, idanuwana suna ganin komai har yanzu”

Ta amsa masa cikin rashin kuzari.

“Good fada waya kika gani kamin su suma?”

Ta kalleshi.

“Ban ga kowa ba”

“Wa yayi kokarin kasheki?”

“Babu”

“Amman an tarar da hannu da jini...”

Be karasa ba ta bashi amsa, bakinta a bushe kana ganinta kasan yunwa da ciwon sun mata mugun kamu.

“Ni ce ni na aikata”

Kallonta yake irin kallon nan dake nuna so yake ya gano idan tana cikin hayyacinta ko akasin haka. Sai ya ware mata hannunsa.

“Miye wannan”

Ta kalli hannun nasa, sai kuma ta koma zata kwanta.

“Keeee!”

Sai ta zaburo masa kamar ba ita ba.

“Miye? Me kake so? Me zan maka? Dan Allah ka bar ni da damuwata, ka bar na ji da abun da yake damuna”

“Ni ma ba damuwa ba ne, i just want to ask miyasa kike son ashe kanki..”

Shi ma a tsawace yai mata tambayar zuciyarsa na bugawa da karfi yana jin kamar ya dake ta saboda ta masa tsawa.

“Saboda na mutu, na huta, na tafi inda yan'uwana suka tafi na tararda mahaifiyata da mahaifina, ta tafi inda ba a zalinci inda ba a danne hakkin kowa, na tafi inda....”

Ta kasa karasawa sai numfashinta yai sama ta fadi kwance saman gadon wuyanta a lankwashe, da sauri ya kai hannunsa ya rikota ta gyara mata wuyanta.

“Baba.... Baba.... Baba.... Baba...”

Shine kawai abun da take ta fada tana kallon Talba da idanuwanta da suka fara rufewa. Fita yai dakin da sauri ya nufi inda likitoncin suke ya fada musu sai likita da nurse uku suka taso a guje suka nufo dakin, zai shiga wata nurse din ta dakatar da shi.

“Malam ka tsaya a waje...”

Sai yaja ya tsaya gabansa na faduwa, kalamanta sun ratsa shi ga tausayinta, a yanzu kan ya tabbatar tana da babba damuwa wanda zata iya haifar mata da matsala kamar yadda Kabir ya fada. Yana tsaye a wajen har suka fito. Likitan ne ya tsaya yana tambayar Talba yayin da nurses din suka wuce.

“Ya kake da wannan mai rashin lafiyar?”

Talba yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada.

“Kanwata ce”

“Dan Allah bismillah akwai bayanin da zan maka”

Likitan na fadar haka ya wuce gaba, Talba ya bi bayansa har suka shiga cikin Office. Talba ya zauna ba tare da jiran likitan yai masa izini ba.

“I'm sorry ban sani ba, ko an maka bayanin cewar yarinyar nan an mata fyade, fyaden da ya wuce na hankali, da alama ba mutun daya ba ne ko biyu, domin abun yayi effecting kwakwalwarta, tana jin tsoro gaskiya, so ya kamata ka kiyaye bacin ranta damuwa, kuma kai kokarin kwantar mata da hankali, and karka dame ta da tambaya ko son sai ta tuna abun da ya faru, domin a yanzu ta kai matakin da zuciyarta zata iya bugawa, kuma be zama lallai idan ta buga ta rayu ba, za a iya rasa ta”

Ya karasa tare da mika hannu ya dauko wata takardar yai rubutu akai, ya mika masa.

“Ka siyo wannan maganin ba mu da shi a nan”

Talba ya kai hannu ya karba yana kallon takardar maganin.

“And zata fara cin abinci daga yanzu, domin na ga a file dinta an rubuta cewar bata ci, sai dai jiya na gwada bata ruwa ta sha kuma ta sha, so from now on zata fara cin abinci”

Talba ya gyada masa kai. Sannan ya juya ya fice daga office din jikinsa a mace, tafiya yake yana tuna kalaman da tai masa da kuma na likitan, and the most important part is fyade. Kamar marar kuzari haka ya bude motar ya shiga ya zauna.

“She's too young for this, maybe sun ashe Mamanta Babanta and su kai raped dinta... Wow.... ”

Ya furta yana runtse ido, yana ayyana yadda abun yake da mugun ciwo. Wayarsa ya ciro ya nemi number Kabir ya kira shi.

“Ranka ya dade”

“Kabir wane chemist ko pharmacy zan samu magani ko wane iri a yanzu?”

“Wa zaka siya wa?”

“Kai... ”

Kabir yayi dariya. Sannan ya fada masa, Talba ya kashe wayar ba tare da sake ce masa komai ba, sannan yai ma motar key yai reverse ya fice daga asibitin. After ya siye maganin ya siyo ayaba da kankana da lemu a hanya sannan ya dawo asibitin, kamar wani barawo haka ya shiga dakin without making a sound, har gaban gadonta ya karasa ya aje ledodin.

“Waye kai?”

Ta tambaya a hankali idonta a rufe, kallon mamaki yai mata a zatonsa bachi take but maganar da tai ya tabbatar masa da tsabanin haka, sai dai idonta a rufe yake.

“Talba, you can call me Talba...”

Ya samu kansa da amsa mata yana kallon fuskarta. Sai ta bude ido a hankali ta kalleshi, ta sake maida idon ta rufe.

“Idan kina bukatar wani abu ki fadawa likitan zai sanar da ni, kuma idan zaki iya fada zamu so sanin inda yan'uwanki suke sai a bincika so that su san kina raye kuma ki samu mai kula da ke”

“Da rayuwata da mutuwa ta duka daya ne, saboda ba ni da kowa a yanzu”

“Shiyasa kike kokarin kashe kanki? Ko kuma dai wani ne yake kokarin kasheki?”

Ta bude idon ta tashi zaune cikin rashin kuzari tana kallonsa, idonta har ya yi baki yayi ja kamar tsabar damuwar da kuka.

“Idan baka ci abinci ba akwai mai damuwa? Wani yana damuwa idan baka da lafiya? Idan ka shiga damuwa akwai mai kokarin faranta maka rai? Akwai wanda zai so abun da kake so, ya guji abun da zai bata maka ra?”

Yayi shiru yana kallonta, kamin ya hade yawun bakinsa, ya daga mata kai alamar eh akwai.

“Ni duk na rasa wannan, a cikin dare daya rayuwata ta sauya, a tsakanin awannin da dakiku aka min katanga tsakanina da iyayena, farincikina yana tare da yan'uwa kuma duka an kashesu, a ciki wuni guda aka juya duniyata, aka nesanta ni da farinciki, a kusanto da bakinciki, a cikin daren nan aka raba ni da martaba da, na kasa manta komai, hoton komai ya gagara goguwa a idanuwana, a tsakanin wacan daren da dararen da suka biyo bayansa bakinciki ne da tashin hankali, sum rusa duniyata, sun tarwarsa shirina...”

Kallonta Talba yake a tsakanin hawayenta da duniyarta da take labarta masa sai ya rasa wane ne yafi tsaya masa a zuciya. Kujerar dake gefen gadon ya ja ya zauna yana kallonta.

“Likita yace ki daina damun kanki, saboda yanayinki yawan tunani da damuwa zai iya haifar miki da wata matsalar...”

“Akwai matsalar data wuce ta rashin uba da uwa? Rayuwata ta riga ta sauya, bana tsoron mutuwa....”

“Amman baki yi tunanin miyasa mutuwa take gudunki ba? Na san kin shiga a gurin da za a iya kasheki amman ba a yi ba, kika samu kanki a nan kuma kika yi kokarin kashe kanki, still hakan be faru ba, rayuwata tana ta zabenki ke kuma kina neman mutuwa baki yi tunanin ya kamata ki rayu ba?”

Ta lumshe ido tana jin bachi na son daukarta saboda allurar da akai mata.

“Na rayu a inda ba a rufa idan akwai sanyi, ba a fakewa a idan ana ruwa, ba a gusawa idan rana ta kawo, a hannu ake raba mana abinci, idan an bada da safe ba za a sake ba badawa ba sai da dare, na ga wa ana dukan wasu, kuma a kashe da yawa a gabana, sun keta haddin mahaifiyata a gabana, sun yanka yan'uwana, sun kona abincin mu, suka akashe babana saboda ya ki yarda ya keta haddin ni, sanadin tafiyar da muka yi kafafuwana basa iya komai a yanzu, sun yanka yan'uwana sun fasa kan wasu da dutse, a haka kuma kake ganin rayuwata tana zabata? Wata kila saboda tana son na yi taraiyya da bakinciki ne”

Hawaye ya sauko mata sai bachi yai baga da ita, ido ya sakar mata kalamanta na taba zuciyarsa, misali yake da kansa idan shi ne ya zai ji? Yana rayuwa cikin jindadi lokaci daya ace komai ya tarwatse! Shi kansa maraya ne, amman be san zafin rashin iyaye ba, be san zafin rashin yan'uwa ba, idan wani abun ya same shi da gudu za a kawo masa agaji, tsabanin it. Takurewa tai gurin daya ta jikinta na dan rawa alamar tana jin sanyi ga kuma hawayen har yanzu ba su daina zuba ba, murmushi mai sauti ne ya biyo bayan hawayen.

“Inna....”

Ta furta tana cigaba da murmushi, sai kuma tai fuskar kuka wasu sabbin hawayen suka zubo mata. Mikewa yai tsaye ya cire Jacket din jikinsa zai lulluba mata sai jikimta ya fara, tana numfashi da karfi ta kara rumgume kanta kana ganinta kasan a tsorace take, a hankali ya lullub mata jacket din sai kuma ya tsaya yana kallonta har lokacin hawayenta zuba suke, wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya juya ya fara tafiya a hankali zuwa gurin kofar.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Taya zan tafi na barki? Ko na gudu harbina zasu yi, ba zan tafi ba tare da ke ba...”

Juyowa yai ya kalleta, kana ganinta ka san wani tashin hankalin ne take mafarki, da alama abun da ya faru ya shiga ranta sosai ya zauna, ya kusan minti biyar a tsaye yana kallonta sannan ya fice yaja mata kofar a hankali ya rufe.
19

*Dan Girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*



Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa


FARUQ POV.

Mama ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina lamarin Rafi'a.

“Faruq ka saka mata ido, duk abun da take tana yi saboda ta bata maka rai ne, kuma komai na rayuwar duniya jarabawa ne, ko da arziki ne Allah ya baka ya ga yadda zaka iya rike su, balle kuma talauci, da muguwar mata”

“Wallahi Wani lokacin Rafi'a tana bani mamaki, ita kamar bata san Allah ke yi ba? Shi zai yi ma kansa arziki ne? Sai ta rika abu kamar ba yar'uwa ba?”

Aisha ta dana da nata. Sai Faruq ya kalleta.

“Wani lokacin ina jin kamar na sake ta na huta, sai dai idan na tuna irin wahalar da mahaifinta yai da ni a karatuna kuma ya dauki yarsa ya aura min duk da a lokacin bana da komai, sai na kamar idan na sake ta ban kyauta masa ba”

“Haka ne, wani abu dole a daga mata kafa saboda mahaifinta, domin mutumen kwarai ne, kuma na tabbatar da yana raye Rafi'a ba zata maka wani abun ba, kasan Umma daman ba son auren take ba tun farko shiyasa komai tai bata ganin laifinta, amman kai hakuri Inshallah sauki yana tafe”

Ya ja wani dogon numfashi ya sauke.

“Ni da har na yanke shawarar na bi Yusufa mu tafi nijar gurin ginar zinarina nan”

“Nijar kuma?”

Cewar Mama ciki damuwa.

“Eh kin ga masu zuwa suna samowa ba laifi, kuma ba kasan inda rabonka yake ba, amman zama haka ba zai yi Mama, hausawa sun ce idan hagu ta ki sai a koma dama”

Mama ta girza kai.

“Wallahi bana son tafiyar nan nesa Faruq, da dai ka hakura mu ga abun da Allah zai yi”

“Mama duk inda rabonka yake sai ka tararda shi, ko kuma ya nemeka, kuma abun da Allah ya rubutawa bawa ko a ina yake zai same shi, na san dai ba zai wuce ki ce kina jin tsoron hanya ba ko abunda zai faru da ni, kawai ki min addu'a”

“To Allah ya zaba mana abun da yafi zama alheri, idan tafiyar Alheri ce Allah ya shige maka gaba”

“Ameen idan Allah

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment