Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers please, idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -2️⃣

“Akwai abubuwa da yawa da rayuwa bata iya tafiya sai da su, a ciki akwai numfashi ci da sha, da kuma soyayya. Bana jin zan iya rayuwa idan babu kai a kusa ni, zan iya rasa ci da sha kuma na rayu da soyayyarka”

Ta nade wasikar da ta gama rubutawa da hausar azami, tana murmushi sannan ta mike tsaye ta maida biron da littafin cikin jakarta ta islamiya ta rataya a jikin kusar dake gurin sannan ta saka hijabinta ta fito.

“Inna an gama?”

“Auta tun dazun na gama, kin yi sallah dai ko?”

Ta saka wasikar a cikin jikinta tana murmushi.

“Inna ke ma kin san bana wasa da sallah fa”

“Haka ne, Auta Allah ya miki albarka”

Inna ta fada Baba da ke zaune saman tarbarma yana sauraren redio ya amsa da Ameen yana murmushi. Sanusi ma dake aikin auna tuwon dawo a bakinsa ya so ma zolayarta kamar yadda ya saba.

“Ku na fasa mata kai da wannan kafafuwan nata kamar itace”

Aiko kamar jira take sai ta fara kukan shagwaba, musamman ganin duka gatanta suna nan Inna da Baba.

“Baba kana jinsa ko?”

Baba yayi dariya tare da kai hannunsa ya kashe redio dake gefensa, ya tofar da goron bakinsa. Yai mata alama da ta zo da hannu, kamar jira take sai ta karaso inda yake tana ta turo baki ita ala dole an taba ta.

“Auta Mamana, ki daina biyewa Sanusi, shi da yake ragon maza, ke da kike Jaruma, ki daina nuna musu rauninki, kin ga shi kin ga Rilwanu ki daina bari suna saka ki kuka, da an miki aure sai kun yi ta marmarinki”

Ta rufe ido da sauri cike da tsantsan kunyar irin ta ya mace bahaushiya. Hakan da tai sai ya kara saka Baba murmushi.

“Allah ya miki albarka ya nuna mana lokacin Autata”

Kasa amsawa tai da ameen domin Aminatu irin yan matan nan ne masu kunya da kawarda ido ga wasu abubuwan. Sai kawai ta mike tsaye har lokacin bata janye hannunta daga fuskarta.

“Wai kunya take, kunya kike kika yarda kina fita zance”

Sanusi ya fada yana dariya, a cikin hasken farin watan Aminatu ta watsa masa harara. Ta nufi inda kwallar tuwonta take ta nada ganwo ta dauka ta dora a kai sannan ta mika dayan hannunta ta dauki miyar dake cikin bokitin roba.

“Ni na tafi gurin sana'a ta”

Ta fada tana kara murda masa baki, Inna dai bata ce komai ba bayan murmushin da tai. Har ta kai bakin kofar fita daga gidan sai Baba ya kirata.

“Mamana”

Ta juyo.

“Na'am Babana”

“Allah ya miki albarka”

Sai ta amsa tana kallon gefen Sanusi.

“Ameen, yan bakinciki sai dai su mutu”

Ba Inna da Baba da Sanusi kadai ba, har Rilwanu da Iro da suka shigo yanzu sai da suka saka dariya, domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, inda Aminatu ta yi habaici ko shagube to ba zai wuce Sanisu ko Rilwanu ba take yi ma.

“Mai tuwo a bani na hansin”

Ko kallon Rilwanu ba tai ba ta saka kai ta fice tana cinno baki gaba kamar zai zazzago ya zubo kasa. Kusa da Baba suka zauna ko wane ya aje bindigar maharba da manyan wukaken dake hannunsu. Kana ganinsu ka ga zaratan jarumai, tun daga kirarsu har yanayin shigarsu da muryarsu. Domin suna daya daga cikin manyan yan saka na yanki, abu ne mai wahala ka ga gidan da ke da maza uku ko hudu baka samu yan sakai a gidan ba balle kuma gidansu Aminatu da suke da maza bakwai. Ba wuka ba ko bindiga bata huda mahaifinsu balle kuma su da suke shiga dajijikan kauyen neman barayi da kansu.

Tana yin nesa da gida kadan sai murmushi ya wanke mata fuska, a cikin abubuwan da tafi kaunar a rayuwarta akwai yan'uwanta, musamman Rilwanu Sanusi da Musa, domin sun fi sauran sake mata, da kuma kyautata. Gashi basa yarda ko da wasa wani ya nuna mata yatsa a waje balle har a taba ta.
A natse take tafiya, tana ta mikawa mutanen data sani kuma suka santa gaisuwa cikin girmamawa, musamman abokan mahaifinta, sai da ta kusa dandali sannan ta rage saurin tafiyarta da alama akwai wanda take jira ko take son hangowa, can kuma ta ja ta tsaya ta juyo tana kallon hanyar data fito sai ta hango masoyinta tafe da saurinsa cikin shigar kananan kaya, murmushi ne ya cika fuskarta, sai ta sauke idonta kasa domin bata jin kunyarta zata barta tai ta kallonsa har ya karaso inda take.
Sai da yai wani gyaran murya ya waiga ya ga babu mai ganinsu sannan ya ce.

“Auta”

“Na'am barka da dare”

“Yau ina fitilarta?”

Sai da yai maganar ta tuna da zancen wata fitila, sam ta manta bata zo da ita ba, sai a yanzu ta suna ta bar fitilar a dakin Inna bayan ta gama rubuta wasikar.

“Wallahi na manta ta”

Ta fada tana dukawa ta aje bokitin miyar dake hannunta, sannan ta saka hannu a cikin zanenta ta dauko wasikar ta mika masa, ya karba da dayan hannunsa dayan hannun kuma ya mika mata tasa wasikar.

“Na je gida na karbo miki?”

Ta zaro ido.

“Kai Baba yana nan fa, ni ban saba aikin maza a gidanmu ba”

Yayi yar dariya yana kokarin magana suka ji muryar Sanusi.

“Auta...”

Ba karamin tsoro Aminatu ta ji ba, domin bata saba tsayuwa da maza har a ganta ba, duk kuwa da kasancewar ta kai munzalin da zata iya yin hakan, amman kunya da tsoron yayyunta ya hana ta yin haka, duk inda ta san idan ta tsaya da wani za a gani ayi mata magana ko fada bata yarda ta tsaya a gurin. Maniru ne ya soma wayancewa ya mikawa Sanusi hannu suka gaisa, Sanusi ya amsa yana musu dariya.

“Ka ce na zama yaya daga yanzu”

Maniru yayi dariya Aminatu kuma ta duka da sauri ta dauki bokitin miyarta daman tuwon yana saman kanta.

“Ga fitilar in ji Inna”

Ya mika mata yar karamar touch light din dake hannunsa, sai ta karba da sauri ta juya ta cigaba da tafiya cike da tsananin kunya gabanta sai faduwa yake. Sai da tai nisa sannan Sanusi ya kalli Maniru ya ce.

“Maniru idan kana son Aminatu ai gidansu ya kamata ka ta fi ba wai ka rika tare ta a hanya ba, amman irin wannan ai ba lallai ne kowa yai maka fahimta mai kyau ba”

“Wallahi Sanusi ina son zuwa, ita take hana ni, sai tace tana jin kunya kuma yayyunta za su iya mata fada”

Sanusi yayi dariya.

“Shirmen ta ne, ba a aure mu za mu yi, idan ka shirya kawai ka min magana zan sanar da Baba sai a komai cikin mutunci”

“Maa Shaa Allah, na gode sosai daman ni abun da nake nema kenan domin na gaji da zageye zageyen nan Wallahi”

“Inshallahu zan yi magana da Baba, duk yadda ake ciki zaka ji”

Sai da Maniru ya sake mika masa hannu suka gaisa sannan ya wuce yana ta jindadi abun nema ya samu.
Aminatu na daya daga cikin irin yan matan nan da suke da farin jinin siyarda sana'a musamman a dandali duk kuwa da kasancewar ba wani kula samari take ba, amman abu ne mai wahala ta je da tuwo ta dawo da shi sai ta saida kaf wani lokacin ma har ta karbi na wasu ta siyar musu, saboda tsabtarta da kuma dadin miyar Inna. Har ta gama sai da tuwon ta nade komai nata a guri daya Wasikar da Maniru ya bata tana cikin jikinta, a dayan bangaren kuma tana ta tunanin yadda zata shiga gida, domin ta san abu ne mai wahala ace Yayanta Sanusi be fada cewar ya ganta da Maniru ba, ba fada kadai ba wata kila har doka sai ta sha a gurin Yayanta Amadu. Da gangan ta ki yarda ta je gida da wuri duk kuwa da kasancewar ta siyar da tuwonta a cikin lokaci, sai ta zauna a gurin tana ta kallon mutane fuska ba yabo ba fallasa, ba zaka iya karantar damuwarta ba, sai dai hakan kuma be isa ka fadi cewar tana cikin farinciki ba.
Har kusan 11 na dare bata tafi gida ba tana zaune a gurin sai ta fakaici idon mutane sai ta matse yan kwalla da suke cika mata ido, sai kuma ta dan turo baki, sai kallon mutanen dandalin take sai ka rasa wa take turowa bakin. Ganin babu sarki sai Allah yasa ta mike tsaye ta dauki robar ta dora a kai tai ma abokan sana'arta sallama, ta fara tafiya kamar bata son zuwa, ta san inda bata je ba sai an aiko nemanta kamar yadda ake idan ta dade bata dawo ba, dan haka bata da wata mafita data wuce ta koma gida.





TALBA POV.

Yana shakimce cikin mota har Ali ya iso gurin motar ya bude front seat ya shiga ya zauna yana kallon abokin nasa

“Lafiya dai?”

Talba yaja wani dogon numfashi ya sauke sai huci yake, har ya bude baki zai yi magana sai kuma ya shiru ya maida dubansa wani gurin. Ali na ganin hakan yai dan murmushi.

“Leila ta tabo ka kenan?”

Talba ya kalleshi da idanuwan dake nuna bacin ransa karara kamar yadda fuskarsa ma ta kasa boye bacin ransa.

“Wai yarinyar nan ni zata wulakanta?”

Magana yake kamar wuta na fita a bakinsa. Ali ya masa kallon natsuwa.

“In I'm not mistaken ka sake mata maganar auren kenan?”

Shirun da Talba yai ne ya tabbatarwa da Ali eh ce amsar tambayar.

“Amman ta wace siga kai mata maganar?”

Talba ya watsa masa wani banzan kallo.

“Kamar wani karamin yaro zaka tambaye ni wace Siga nai mata maganar?”

“No baka gane ba ne Talba, su fa mata yan lalabawa ne, kai kuma sai kace komai da karfi da isa zaka yi ba haka ake ba”

Talba ya watsa masa wani kallo.

“Okay kamar ba baka san ni ba kenan? So kake na je na same ta ina lallashinta ta aure ni?”

“No kai baka gane ba, Talba wannan lokacin ya wuce da zaka dinga tirsasa mace ta yi maka abu any how, na san Leila tana sonka amman kai din ne wani iri”

“Kai Ali duk fa mace da zan aura alfarma zan mata, ba dai ita ta min ba, ina da kudi ina da kyau ina da ilmi ina da addinin da har a kasar waje za a iya bani aure balle a nigeria a nigeria ma a gidanmu”

“Ka ga matsalar ka ba, wani irin alfarma tun da har kuna son junanku? Kar fa ka manta Talba Leila a waje tai karatu kuma wayayyiyar mace ce mai son burgewa, Talba dan kalaman nan na soyayya baka san kai mata ba, dan morning text din baka tura mata, balle har ka kirata ku yi fira, ko ka dauke ta ku fita, mata suna son wannan”

“Ba zan yi ba, ina namiji zan wani zan wani rika lallaba mace, idan ma zan mata sai an yi aure, amman ba a yanzu ba ai sai ta raina ni, besides muna gida daya zan rika mata haka?”

“To miye a ciki, ai an san aurenta zaka yi tun da an muku baiko, kai komai sai kace na zafi zaka yi, idan ka sake mata ba shi yake nufin ka bata umarni ta ki bi ba, dan Allah ka kirata yanzu ka bata hakuri”

Kamar wanda aka cewa cire ranka ka bata haka Talba yai ma Ali wani irin kallo na mamaki da tsoro a lokaci daya.

“Ni Mu'azzam Auwal Shimkafi zan kira mace na ce dan Allah ki yi hakuri? Macen da ba uwata ba? Malam dan Allah fitar min a mota”

“Talba mata fa sai da haka, kuma ka canja hali dan Allah”

“Ita ma ai bata iya kalaman soyayya ba, bata san ta kira ni ta gaishe ni ba ko ta turon sakon soyayya, kai ni bana jin ma akwai ranar da Leila ta taba kallona tace kana da kyau simple word bata taba fada min ba, sai ni zan fada mata? Ba yi wannan macen da zan zauna ina bude mata sirrin zuciyata ba har ina rarrashinta”

“Wannan ji da kan babu inda zai kaika Talba, idan ka sake mata ka nuna mata kauna dole ita ma zata sauko fa”

“Malam na ce ka fitar min a mota...!”

Yanayin yadda yai maganar ya isa ya sanar masa ba da wasa yake ba, kuma ya san halin abokinsa idan ransa ya bace baya jin rarrashin sai dai hakan ba zai hana anjima ya kira shi yace yana son wani abu ba ko kuma su gadu a guri kaza. Salun alum ya bude motar ya fita yana murmushi da mamakin irin halin Talba.

“Ina fada maka matsalata kana wani kokarin ba ni laifi, an fada maka mata haka ake musu ne!”

Magana yake da kansa yana tukin cikin bacin rai, domin be san inda zai je ba a yanzu kasancewar yau weekend kuma gashi safiya ce be ma karya ba.



@12:44pm

Leila na zaune tool din mirror Momy tana zana mata abun da ya faru.

“Kawai sakonsa na gani a wayata wai na fito waje yana son magana da ni, Momy babu ko irin shaukin nan Wai Ke fito waje ina son magana da ke, haka dai na daure na fita, na same shi a balcony ya kusan 30 be ce min komai ba, sannan wai ki yi fixing date na auren mu, Imaging babu ko dan shauki sai wani ji da kai”

“Ke kuma kika ce masa me?”

Momy ta tambaya tana harararta.

“Na ce nasa ba zan yi ba, ni ban tashi aure yanzu ba”

“Ki ba shi hakuri”

Ta kalli Momy kamar tai magana sai dai ganin babu wasa a fuskar Momy yasa ta mike tsaye ba tare da tace komai ba ta fice daga dakin cike da bacin rai. Dakinta ta shiga ta dauki key din motarta da jakarta da wayarta, ta fito babu mayafi ta sauko kasa kamar zata tashi sama, daman ta saba fita babu mayafi abu ne mai wahala ka ganta da mayafi a jiki komai kankantarsa.
Tana fitowa ta nufi gurin da motarta take ta bude ta shiga tai yi warming dinta sannan ta danna horn da karfi mai gadin na ganin hakan yai saurin bude mata gate. Kamar wata mai gasar tsere haka ta fito daga cikin gidan da mugun gudu ta hau titi tana jin kamar ta fasa ihu. Sai da tai nisa sannan ta dauki wayarta ta kira Adam.

“Besty kana ina?”

“Ina gida ya akai? Kamar kina cikin damuwa”

“Ina ciki besty mun yi fada da Talba?”

“Mtssss wai me ke damun Talba ne?”

“Ina na sani, ban san abun da yake takama da shi ba, indai kudi ne ni ma ina da su, ilmin ina da shi kyau ba za a min gori ba, amman sai wani nuna isa da ji da kai”

“Wallahi kam yan kalaman soyayya ma ace ba zaka iya yi ma mace ba, idan an yi auren ya kenan?”

“Shine abun da nake magana a kai, ni kuma sai na nuna masa ina da tsada ni ba kamar sauran mata ba ne, dole na ja masa aji, yadda yake jin ba zai iya min kalaman soyayya ba ko ya dauke ni mu fita ko ba ni hakuri haka ni ma ba zan taba yi masa ba”

“Hakan shi ne daidai, kara ya san darajarki a dole ya sauko idan yana sonki”

“Shine ai, shi kawai abunda ya dauki mace ya mata umarni ta bi ya juyata yadda yake so, ni kuma sai na nuna masa na fi karfin haka Wallahi”

“Yanzu dai kwantar da hankalinki ki samu ruwa ki sha, ki fita waje ki sha iska zan zo na dauke ki mu fita”

“Har na ma fito gida amman bari na koma”

“Okay but ki yi murmushi pls”

Ta yi murmushin mai sauti kamar yadda ya bukata, sannan ta aje wayar, ta juya ta koma inda ta fito. Kamar yadda ta fito haka ta koma gidan da gudunta ba da damuwa da titi ko sauran motoci burinta dai ta aikawatar da abun da take so. Horn biyu tai kamin tai na uku Mai gadin ya bude mata gate ta shiga cikin gidan da mugun gudu ta faka motar a inda ranta ya so ta fito ta nufi kofar falon, door bell ta danna da karfi kamar zata balla shi sannan taja ta tsaya tana tsaki, shiru ba a bude ba har sai da ta sake danna door bell din sau biyu ta hada da knocking. Sannan Baaba ta bude mata.

“Wallahi tallahi kika sake barina a tsaye a waje ina knocking, abincin ki ya kare a gidan nan Baaba”

“Wanke wanke nake yi Leila shiyasa”

“Na dai fada miki”

Ta fada cikin tsawa, ba dan Baaba ta yi saurin kaucewa ba da Leila tureta zata yi ta wuce. Baaba ta maida kofar ta rufe sannan ta juyo cikin falon cikin rashin jindadi zata koma Kitchen din sai ta ji muryar Momy dake tsaye stairs.

“Baaba a rika kula mun dauke ku aiki ne kawai saboda mu huta, a daina batawa yarana rai”

Baaba ta daga kai ta kalli Momy sannan ta daga mata kai cikin da ladabi.

“To Hajiya Inshallahu za a kiyaye”

Sannan ta sadda kanta kasa ta nufi kitchen din cikin rashin kuzari.




FARUQ POV.

Kallonta ya tsaya yi da dayan biyu kamin ya amsa gaisuwar da tai masa, domin ba kasafai take gaishe shi da safe ba sai idan tana son wani abun ko kuma ta lura aljihunsa da dan nauyi.

“Lafiya Kalau an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah, sai yunwa da nake ta ji tun jiya”

“Toh Allah ya buda mana kofafin samu”

“Amin...”

Ta amsa tana kallon Sultan dake motsawa alamar zai farka daga bachin da yake.

“Na ce wai ba zaka kira abokin nan naka ba, ka roki shi dan wani abu?”

Ya girgiza mata alamar aa.

“Ba zan dauna kullum ina bin abokai ina rokonsu ba, bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi abun da zai ci ba, kuma ni ma na yi karatun idan mu kai hakuri komai zai wuce”

“Matsalar kenan Faruk girman kai, kana da girman kai, yanzu haka zamu zauna mu wuni da yunwa gashi idan ka fita baka dawowa sai dare? Ga ni da ciki ga Sultan?”

Yayi shiru yana jin yadda kansa yake sara masa saboda maganganun da Baturiya ta fara masa.

“Shiyasa na ce zubar da cikin nan zan yi na huta, kai ma ka huta domin na san ko ragon suna da wahala a samu a yanka masa wannan bakin talaucin da muke fama da shi”

Ta fada cikin kukanta na munafurci. Sai ya kalleta a raunane.

“Zubar da ciki ba zai kawo mana Mafita ba Rafi'a miyasa ba ki da tunani ne wai?”

“To ni dai gaskiya yunwa nake ji, tun jiya fa ban ci komai ba, kuma anjima na nan ga Sultan ma”

Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya mike tsaye ya fice daga dakin cike da damuwa. Binsa tai da harara.

“Ni dai Wallahi na gaji da wannan bakar rayuwa, Allah kadai ya san yadda masu kudi suke ji, su kwanta a mai kyau a ci abun da ake so, ni ko na kare a nan duk kyau na”

Ta fada tana mikewa tsaye tare da bin bayansa, sai da ta tabbatar ya fita sannan ta dawo ta dauki wayarta ta shiga contact list dinta ta kamo number da tai saving jiya. Maryam Dahiru Sokoto ta aika mata kira, ringing tai har ta tsinke ba a daga ba ta sake kira nan ma ba a daga ba.

“Ka ji yan gayu sai ayi ta kira basa dagawa...”

Whatsapp dinta ta bude ta shiga gurin numbers ta kamo number wanda ke dauki da hoton wani matashin da ba zai wuce sa'an mijinta hakimce cikin mota. Sai da ta gama kallon hoton sannan ta shiga aika masa sako.

‘Assalamu Alaikum, ranka ya dade fatar an tashi lafiya, ya aiki ya Madam da yara. Ranka ya dade sunana Fee'ah matar Faruq abokinka, na kira baka daga ba shiyasa na yanke shawarar turo maka sako. Wallahi muna ciki matsala, yau kusan kwana nan mu hudu ba mu girka komai ba, shi ma idan ya fita haka yake dawowa saboda shagon da aka bude sabon gurin ne cikin wata sabuwar unguwa ba kowa yake ta aski ba, yanzu haka Sultan kuka yake, ni kaina dauriya kawai nai saboda da na, Dan Allah ka taimake mu kamar yadda Allah ya taimake ka, na duba na ga a cikin abokan Faruk babu mai tausayinsa da son taimaka masa irinka, na so Faruq yai maka magana da kansa amman yace nauyi yake ji, yanzu haka be san na dauki number ka ba, domin idan ya sani ina ciki matsala. Ka huta lafiya Allah kara rufa asiri’

A rarrabe ta tura sakon har tana gadawa da emoji din rokon da kuka. Sannan ta duba last seen dinsa tun jiya da dare, tana jin motsin turo kofar gidan tai saurin aje wayar ta kwanta kasa. Faruq ne ya shigo dakin rike da bakar leda har biyu a hannunsa. Ya aje mata dayar a gabanta ganin hakan yasa ta tashi zaune tana kallon 200 dari biyun da ya mika mata.

“Ina ka samo?”

“Ke dai ka bar”

“Dan girman Allah Faruq ka daina mana cin bashi kana kara mana kanskanci a unguwa kamar kan mu farau talauci”

“Ba bashi na ci ba wayata na bashi jingina”

Bata ce komai ba ta karbi dari biyu kana ta bude ledar tana duba taliya da makaroni dake ciki sai maggi da mangyada.

“To wannan ledar fa?”

“Mama zan kaiwa”

Yana fadar hakan ya juya ya kalli dansa dake sharar bachi sannan ya fice ba dan ranta ya so ba.

“Mu ba mu wadatu ba amman sai dauka ka kaiwa wasu, mtchhhh”

Ta karasa tana jan tsaki.

“Kuma Wallahi sai na zubar da cikin nan haka kawai zan zauna ga talauci ga wahala da kurciyata da kyauna”

Ta fada tana mikewa tsaye ta dauki ledar taliyar ta fito waje domin sarrafawa. Kallo daya zaka masa ka karanci damuwarsa abubuwan duniya sun taru sun masa turr kamar ya zagi arziki kamar komai yake juye masa, gashi yayi degree amman aiki ya gagara duk inda yai applying shiru ba wani motsi. Da tunani kala kala mai achaba ya sauke shi unguwar Dallatu wato gidan mahaifiyarsa, sai ta ciro naira dari a mika masa sannan ya ratsa cikin gidanje har ya isa kofar gidan ya tura ya shiga da sallamarsa. Kanensu biyu mata da suke tsakar gidan suka amsa masa suna masa sannu da zuwa, bayan ya amsa musu ya nufi dakin Mahaifiyarsa ba karamin faduwa gabansa yai ba ganinta a kwance domin ba al'adarta bace yawan kwanciya musamman a irin wannan lokacin.

“Mama lafiya dai? Ko jikin ne?”

“Da sauki ai Alhamdulillah”

Ta amsa masa tana murmushin karfin hali.

“Wani irin da sauki ga ki kwance? Kai Innalillahi Wa'inna illahirraji'un”

Jin furuncinsa yasa ta yunkura ta tashi zaune tana kallonsa.

“Ina Sultan?”

Kasa amsawa yai sai kallon mahaifiyarsa yake, yana jin kamar ace yana arzikin da zai iya kaita Asibiti, domin ba yau ciwon ya fara ba.

“Mama ko dai maganar auren Aisha da akai ne jiya ya tada miki hankali? Idan ma fasa aurenta zai yi ai ba wani abu ba ne zata samu wani”

“Har aure nawa za'ayi ta fashi ne Faruq? Haka zamu ta zama ana fashin aure saboda talauci? Kuma yaran nan sai girma suke, sai gulma ake mana a unguwa”

Ta tambaya idonta tab da hawaye, Faruq yayi saurin kawarda nasa idon yana sauke ajiyar zuciya, domin kukan mahaifiyarsa na daga cikin abun da ya fi tsana a rayuwarsa.




________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment