Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, idan son samu ne ma tafiyar nan da zan yi China naje dake, kin taba zuwa china?”

“Aa Wallahi”

“To ki shirya dake zamu je”

Ta yi murmushi tana jin wani kalar dadi ya sakota gaba, duk kuwa da bata da tabbacin zata amince ta bishi din ko kuma aa, saboda aure da kuma Fahat.
Wayarsa ya mika mata..

“Saka min number ki a nan, ya kamata ace muna da number juna, ba dole sai mun biyo ta bangaren Ramlee ba”

Ta karbi wayar ta saka masa number, sannan ta dauki kudin ta saka a jakarta ta fito falo ta dauki wayarta ta saka mayafinta tai masa sallama ta fice tana mamakin yawan kudin daya bata, wannan karom bata yi shakkar saka gyaren ba saboda dare ne kuma a yanzu bata da kwaliya kamar dazun.



FARUQ POV.

Sai da ya fara biyawa gurin Mama ya gaisheta suka dan taba hira sannan ya kama hanyar zuwa shagonsa. Ba su karasa ba wani mai mota ya bugu babur din da yake kai, shi da mai achaban suka fadi gefen titi. A take mutane suka yo kansu da gudu mutumen daya buge su ma faka motarsa yai gefe ya fito yana dubasu. Kana ganinsa ka san babban mutum ne, domin shaddar jikinsa ma kadai abun kallo ce balle kuma bakar motar data buge su, a tare da shi a akwai direba sai kuma wata jar mota dake bayan tasa da alama take masa baya take ko kuma a tare suke. Daga mai achaban har Faruq daya ji ciwo a kafa zaune sukai mutane na musu sannu.

“Akwai asibiti nan kusa?”

Mutumen ya fada yana kallon direbansa, sai saurayin dake tsaye kusa da shi ya amsa masa.

“No Abba ba kace kana uzuri ba, ka tafi kawai ni ni zan kai su”

“Okay Muhammad idan an dubasu ka samu abun aka basu, idan mun hadu gida anjima zamu yi magana, yanzu jirana ake”

“Okay”

Dan nasa ya amsa sannan ya rika Faruq da yafi jin ciwo ya mikar da shi tsaye.

“Muje ga motana can”

Ya nuna masa jar motar da take bayan ta mahaifinsa, kamin su karasa gurin motar har mahaifinsa ya shiga tashi motar direban yaja motar sun kama hanya. A front seat ya zaunar da Faruq sannan ya bude back seat din ya ce da mai achaban ya shiga.

“Aa kaje ka kai shi, ni ban ji ciwo ba”

“Ka tabbata?”

“Inshallah”

Sai ya rufe motar ya rufe inda Faruq yake zaune, ya zagaya mazaunin direba ya kirga dubu biyar ya mikawa mai achaban, sai ya karba yana godiya daman haka tafi masa dadi. Ya hau achabansa ya kama hanya shi kuma ya shiga motar yaja Faruq suka isa asibiti.

“Sannu ko kana da asibitin da kake zuwa?”

“Aa”

“Okay bari muje ta nan kusa, ai zaka iya jurewa ko?”

“Haba sai kace ba namiji ba”

Faruq ya fada yana murmushi, shi ma murmushin yai ya cigaba da tukin har suka isa asibitin, aka duba kafar aka bashi magani suka rufe ciwon. Sannan ya sake daukoshi a motarsa suka suka nufo unguwarsu, suna tafe suka hira kamar daman can sun saba, be yarda ya bar Faruq a bakin titin ba duk kuwa da kasancewar mota bata shiga har kofar gidansu, sai ya fito ya taka masa har kofar gidan yana masa wasa wai kar madan tace sun buge mata miji, Faruq murmushi kawai yai ya kai hannu ya taba gidan sai ya ji shi a rufe, key dinsa ya dauko ya bude ya shiga ciki.

“Ina jin bata nan, daman tace min tana da biki zata je”

Fada a kokarinsa na kare matarsa duk da kasancewar mutumen be san Rafi'a balle har ya munana mata zato.

“To a gaishe ta, kuma a bata hakuri ga kuma wannan ayi cefane”

Ya fada yana mikawa Faruq dubu goma.

“Aa haba ai abu ne da Allah ya kawo...”

Kamin Faruq ya karasa Mutumen ya saka rantsuwa.

“Wallahi sai ka karba, kai shedan kadai ke maida kyauta”

Murmushi Faruq yai a karo na barkatai ya karbi kudin yana masa godiya.

“Na manta ban tambayi sunanka ba”

“Faruq”

“Ni kuma Muhammad Fahat na gode sosai Allah ya tsare gaba”

“Ameen”

Daga haka Faruq ya karaso cikin gidan shi kuma ya juya ya kama hanyarsa. A falo Faruq ya zauna yana kiran Baturiya a waya domin jin inda take, sai dai bata dauka ba daga baya ma sai yaji wayar a kashe, hakan kuma ba karamin bata masa rai yai ba, ba yau ta saba fita ba tare da izininsa ba sai dai ya fi jin zafin fitarta fiye da koyaushe. Cikin karfin hali ya shiga uwar daka ya tube tufafin jikinsa yai wanka ya canja wasu kayan sannan ya kwanta, nan da nan bachi yai gaba da shi. Kiran Allah azahar ne ya tashe shi, ya tashi yai alwala ya fita masallaci a can ya hadu da dansa da yabi yaran makotansu suka tafi masallacin a tare. Kusan kowa da ya gaisa da shi sai ya masa sannu da fatar Allah ya tsare gaba, shi kuma ya amsa da Ameen bayan ya labarta musu abun da ya faru.

Sultan na ganin mahaifinsa ya rike shi suka dawo gida tare. Abun ka yaro yana shigowa ya fara tambayar Faruq ina mamansa.

“Dady Momy bata dawo ba?”

“Ina ta tafi?”

“Bata fada min ba, amman na ji tana ta waya da yawa tana ta waya har ta ce ummouy”

Ya nuna yadda tai kiss din da bakinsa. Faruq ya hade yawu yana jin wani bakinciki na taso masa. Haka ya wuni a gidan daga shi sai dansa girkin rana ma shi ya girka duk da kasancewar akwai ciwo a kafarsa, tun yana tunanin zata dawo da la'asar bata dawo gidan ba sai bayan magariba ana daf da kiran sallah isha'i wani gurin ma har an fara kiran. Sannan ta shigo da dan faduwar gaba, ganin cewar Faruq ya rigata dawowa, ta shigo falon da sallama, ya amsa mata ya mike ya fice ya bar mata falon, sai ta bishi da kallo kamin ta kalli danta.

“Sultan yaushe Dadynka ya dawo?”

“Tun da rana har ma ya ji ciwo a kafarsa”

Bata sake cewa komai ba ta nufi dakinta ta aje jakarta a inda ta saba ajewa sannan ta fita tsakar gidan da saurinta saboda kashi ya matseta. Ko da ta fito ta dauki buta ta shiga bandakin yana tsakar gidan yana alwala, bayan ta shiga bandaki ya shigo falo daga inda yake tsaye ya hango Sultan na ciro kudi mai yawa a jakar Baturiya, da sauri ya karasa ya kara bude jakar da kansa yana duba kudin. Bandir din yan dubu daya ne har guda hudu sai kuma karamin canji dake kasan kudi.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Ya furta cikin wani irin yanayi na tsoro da bakinciki. Kamar an dasashi haka yai tsaye a gurin har ta fito daga bandakin ta shigo dakin, tana ganinsa tsaye kusa da jakarta sai ta yi tsaye a bakin kofar tana kallonsa. Tsayin da tai ya bashi damar kare mata kallo, lace din dake jikinta tsadadden lace ne da karfinsa be kai ya siya mata shi ba, sai dai ba zai munana mata zato ba saboda tana da yayyun dake auren masu rufin kudi, sai dai bata saka irin wannan tufafin sai zata je guri na musamman.

“Ina kika samu wannan kudi?”

“Ajiya aka ba ni”

Ta amsa kai tsaye kamar da gaske, sai ya watsar da kudin ya daka mata tsawa.

“Karki raina min hankali mana, wa ye zai baki ajiyar kudi mai yawa haka? Ina kika je?”

“Gida gurin Umma”

Ta amsa tana hade fuska.

“Rafi'a kin wuce gona da iri, ban taba tunani zaki iya aikata abun da kika aikata ba, kuma abun bakinciki da jinani a jikinki”

“Faruq.. Zarkina kake yi kuma? Zargi fa yana kashe aure”

“Waya baki ajiyar wannan kudin?”

“Ba zan fada ba, tun da zargina kake ai sai ka cigaba kuma Allah sai ya saka min, ka cutar da ni kuma yanzu ka fara bina da kazafin zina”

Ta fashe da kuka.

“Juya ki koma inda kika fito

Ya fada yana nuna mata kofa.

“Wallahi ba inda zan je sai idan sakina kai”

“Tafi na sake ki saki daya, kuma duk kika cutar min da yaya Allah ya isa tsakanina da ke”

Ta dora hannu biyu akai tana zaro ido kamar za su fado.

“Faruq ka sake ni fa kace...?”

Be bi ta kanta ba ya rika hannunsa dansa ya ratsa gefenta suka fice a fusace zuciyarsa na masa zafi.
Zaune tai a bakin kofar dakin tana kallon kudin, ba kuka take ba, bata jin ma kuka ko bakinciki yana kusa da ita, farinciki kudi data samu sai ya koma mata ciki.



AMINATU POV.

A tsakar falon aka barta babu wanda ya sake bi ta kanta Mairo ta koma kitchen bayan ta karbi brush din da Kabir ya kawo mata ya fice, Leila kuma ta haye sama ta shige dakinta ya sauki wayarta ta kira Madina ta labarta mata abun da ya faru.

“Leila wata mace da ba yar kowa ba, ba zata taba samun gurbi a zuciyar Talba ba, saboda yana ji da kansa sosai ba zai yarda ya auri wanda ba yar kowa ba, balle kuma yar gudun hijira”

“Ni ma ai ban ce sonta yake ba na san ai ba zai taba sonta ba, amman ina jin zafin abun da yake mata, taya zaka tsinci yarinyar ka kawota gidanku shi yafi kowa tausayi ne”

“Yanzu yarinyar tana nan gidanku?”

“Eh, tana nan yace Mairo tai mata wanka ta bata abinci ni kuma na hana, kuma ko ban hana ba Momy ma b zata bari tai ba”

“Gani nan zuwa yanzu, zan zo na ganta”

“Okay”

Ta kashe wayarsa sannan ta kira Ali tana fada masa abun da ya faru.
Ba'ayi minti talatin ba, Madina ta iso gida, tana faka motarta ta nufo entrance din da saurita, kamin a bude mata kofar ta danna door bell din kusa sau uku, sannan Zulai ta bude mata.

“Sannu da zuwa”

“Yauwa sannu da gida, ina Momy?”

“Tana sama”

Ta shigo cikin falon tana rabon ido, sai ta hango Aminatu zaune a wheelchair kanta a kasa, karasa tai kusa da ita ta duka tana kallon fuskarta, wannan karon ba kuka take ba sai dai idonta a rufe yake ba kuma bachi take ba.

“Hey...”

Madina ta fada, sai Aminatu ta bude idonta a hankali ta kalli Madina. Sai Madina ta sakar mata murmushi.

“Sannu Sunana Madina ke fa?”

Aminatu ta maida idon ta rufe. Sai Madina ta mike tsaye ta kalli Zulai.

“Ina Mairo?”

“Tana kitchen Mairo”

Ta karasa tana kwala mata kira. Sai ta fito tana amsawa. Sai da suka gaisa da Madina sannan tace.

“Ba a mata wankan ba?”

“Leila tace kar na yi, har buroshin da Kabir ya bani ban mata ba”

Madina ta yi murmushi.

“Amman Mairo baki san waye Talba ba, da zai baki umarni ki bini ki bi na Leila, ina brush din?”

“Na aje shi a dakin da daya ce a ware mata?”

“Wane daki?”

Mairo ta nuna mata hanyar corridor dake kasa inda dakunan uku suke.

“Na farkon”

Zagayawa Madina tai ta fara tura wheelchair din, ta nufi corridor da ita, suna isa ta tura kofar dakin ta sannan ta sake turata suka shiga ciki. Bandaki ta nufa da ita ta kunna fanfo ta zuba makilin din ta a brush ta cire karamin gyarenta ta aje gefe tare da jakarta ta fara wanke mata baki, bayan ta gama ta taimaka mata ta cire tufafin jikinta ta daura mata tawul ta murza nata inda zata iya a jikinta ta bar mata ragowar ta karasa wankewa sannan ta dauraye mata jikinta. Ba tare data raba ta tawul din dake jikinta ba, bayan sun gama ta fito da ita, sannan ta fita dakin ta nufi kitchen abun da ya rage na safe ta dauko ta dawo da shi dakin ta dora saman karamin gadon ta fara bata.

“Zan iya ci da kaina”

Aminatu ta fada ganin tana kokarin kai mata abincin a baki, sai ta girgiza mata kai tana murmushi.

“No bari na baki da kaina”

Ta shiga bata abincin a hankali, kamar daga sama Talba ya shigo dakin Zulai na biye da shi rike da jakar Candy Collection, tsaye yai bakin kofar yana kallon Aminatu dake kan Wheelchair Madina kuma na zaune a bakin gado suna facing din juna tana bata abinci ga tawul din jikinta a tsike, wani irin dadi ne ya lullube Madina daman abun da take nema kenan Talba ya shigo ya sameta tana aikin da bana Allah ba.
22

*Khadeeja Candy*


Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

*Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Ta yi saurin aje abincin ta mike tsaye tana kallon Talba.

“Sannu da zuwa”

Aminatu ta juya a hankali ta kalleshi, sannan ta kalli Madina, yadda ta ga yanayinta ya sauya tana kokarin shiga natsuwarta kadai ya isa ya saka ta fahimci cewar Madina tana tsoro Talba sosai. Shigowa yai cikin dakin fuska babu annuri, ba dan komai ba sai dan ya san irin amintar dake tsakaninta da Leila. Juyawa yai ya kalli Zulai.

“Ba na ce Mairo tai mata wanka ba?”

“Eh ranka ya dade, Leila ce ta hana ta”

A take yaji ransa ta bace domin ya tsani ya saka mutum wani abu be yi ba, musamman ma ace wani ya hana shi, wanin ma wanda shi ma zai iya controlling dinsa kamar dai yadda Leila tai.

“Ya kai tawul din jikinta ya ke da ruwa?”

Ya tambaya yana kallon Madina.

“Na taya ta wanka ne, to bata yarda ta cire tawul din ba shi yasa ya jike, kuma bata da wani tufafin da za a canja mata, kuma a san idan na tambayi Leila ba lallai ne ta bata ba”

Talba ya kalli Aminatu sai kuma ya sake kallonta.

“Waya ce ki mata wanka?”

“Babu, ko da na shigo tana falo ne, sai na tambaya Mairo ta fada abun da ya faru, sai na yanke shawarar taimaka mata, amman ka yi hakuri idan hakan ya bata maka rai ba zan sake ba”

Ta karasa tana risinawa a gabansa kanta a kasa, kamar wanda take a gaban sarki tana neman yafiya. Da hannu Talba yai mata alama data tashi tsaye, sai ta mike tsaye.

“Zan iya cigaba da bata abinci?”

Ta tambaya cike da ladabi kamar mai tsoronsa, Talba ya kalleta da duba na mamaki irin da gaske? Kamin ya kalli Aminatu da idonta ya cika da kwalla tana girgiza masa kai.

“No”

Ya amsa mata still yana kallon Aminatu. Kamin ya juya gurin Zulai.

“Aje tufafin a can, ki taimaka mata ta saka”

Da sauri Aminatu ta sake girgiza kai hawaye na sauko mata. Hakan ya saka Talba yai saurin dakatar da Zulai dake kokarin bude kayan.

“Bar shi kawai tafiyarki”

“To ranka ya dade”

Ta amsa sannan ta fice da sauri, kana ya kalli Madina dake tsaye tana kallonsu.

“Excuse me”

Murmushi ta sakar masa alamar okay sannan ta fice da saurinta. Sai Talba ya karaso gurin Aminatu.

“Idan kina son wani abu, ko kuma baki bukatar wani abun, ba sai kin yi kuka ba zaki iya yin magana ko ki yi alama da hannu ko da ido ko da kai, ba wai kullum ki yi ta kuka ba”

Ta saka hannu ta share hawayenta.

“Ki ce to zan yi haka”

Ta maimaita abun da ya bukata da muryar kasa kasa kamar mai rada, hakan yasa shi risinawa ya kai kunnensa kusa da bakinta.

“Fadi na ji”

Ta sake maimaitawa saitin kunnensa.

“Good, ki dai kuka ba komai ake yi ma kuka ba”

“Ni ma ji nake kuka ya zo min”

Ta fada a nan sai da ya sake kai kunnensa sannan ya ji abun da ta fada.

“Okay na fahimta, yawan kuka zai iya zame miki matsala ne shiyasa, zaki iya canja tufafin da kanki?”

Ta daga masa kai.

“Okay ki duba tufafin da kike so sai ki canja”

Nan a kan ta daga masa. Sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin yaja mata kofa, hannu ta kai ta dauki jakar ta bude ledar sama ta fara daukowa ta budewa sai tai arba da doguwar rigar abaya ash color, warware rigar tai ta soma sakawa daga zaunen da take, sannan ta cire tawul din ta aje a gefe ta daga kadan ta ja rigar zuwa kasa. ta daura mayafin ayabar a kanta sannan ta maida hankalinta gurin kofar tana sauraren shigowar wani, kusan kamar ta yi sara akan gaba ne, domin a tsakanin lurawa kofar ido da kuma kwankwasa kofar da akai ba zaka iya fadar wanda ya riga wani ba. A hankali ya turo kofar dakin ya shigo idonsa a rufe alamar ba kallonta yake ba, domin bashi da tabbacin ta gama kintsawar ko akasin haka, duk da kasancewar ya bata mintuna daya kamata ace ta gama, ba kuma zai iya kiranta daga can wajen kofar ba ya tambaya idan ta gama.

“Na gama”

Ta fada kamar ta san manufarsa, sai ya bude idon ya sauke su akanta.

“Ki karasa cin abincin, Zulai zata fitar da ke waje ki sha iska, ni zan tafi gurin aiki”

Ta gyada masa kai, sai ya juya ya fice, ido kawai ta kurawa abinci ta kasa kai hannu ta dauka balle ta ci, ko dazun ma saboda yunwa ta matsa mata ne kuma Madina ta dage sai ta bata abincin.

Ko da ya fito falon Madina na zaune a kan sofa, Leila kuma na saukowa downstairs. Kallo daya yai mata ya dauke kai ya maida gurin Zulai.

“Idan ta gama cin abincin ki fito da ita ta sha iska”

“To ranka ya dade”

“Mairo da Zulai ni suke yi ma aiki, idan kana son a kula maka da wacan kazamar sai ka dauki mai aiki”

Ya juyo ya kalli Momy dake tsaye dinning tana maganar, sai dai be ce uffan ya sa kai ya fice. Madina ta bishi da kallo cikin rashin jindadin furucin Momy, sannan ta kalli Leila.

“Yar gari”

“Kin ga abun mamaki a gidanmu ko?, gaba daya gidan nan neman hargitsewa yake”

Madina ta kama hannu Leila ta zaunar da ita kusa da ita tare da rage murya.

“Kina daina bari Momy tana ma Talba fada ko nuna be isa akan abu ba a gaban yan aiki, saboda kar su raina shi, ke ma kuma ki daina pls?”

“Raini kuma na nawa? Ai ni na dade da raina wayonsa Wallahi, duk yadda yake ji da kansa yana wani mazurai ace zai dauko wata ya kawo a gidan nan har yana mata yar muryar mtsss”

Ta karasa tana jan tsaki, sai Madina ta yi murmushi.

“Leila kenan ba zaki gane ba, idan kan son mutum, lallaba shi kake kana nuna masa kauna, musamman Talba daya zama watsentsen mutum, yadda ya dauko yarinyar nan ya kawo sai ki nuna masa kin fi shi sonta, idan Momy tai masa abu ki nuna kin fi jin zafin abun...”

“Uhmmm Madina kamar baki san wacece ni ba, kina tunanin zan iya wannan bautar? Ai ko aurensa nake sai ni na juya shi ba wai shi ya juya ji baki daina fada min magana kamar kin fini wayo”

Madina ta sake yin murmushi a karo na biyu tana kallon Leila.

“Ai na fiki wayo! Kuma very soon zan baki mamaki, ina fada miki gaskiya saboda baki da kawa kamar ni, nima kuma bani da kawa kamar ke, amman ba zan haramtawa kaina abun da Allah ya halattamin ba, kuma ba zan zabi cutar da zuciyata akan abun da nake ganinsa magani a gareta ba, ni da ke yake ne muke tsakanin zuciya da zuciya waye zai ci nasara? Allah shi ya bar wa kansa sani”

Leila ta yi mata kallon rashin fahimta.

“Ban gane ba?”

“Ina yakar zuciyata ne ta fada miki gaskiya kuma ta nuna miki ita, ke kuma kina yakar zuciyarki ki hana ta daukar gaskiya”

Ta karasa tana mikewa tsaye tare da daukar jakarta ta rataya.

“Baki shiga kin ga yarinyar ba”

Har ta yi kamar tace mata ai na ganta, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, domin ko da suka sauko sun same ta zaune, babu wanda yaga shigarta ko fitowarsa a dakin.

“Okay muje na ganta”

Leila ta nufi hanyar corridor Madina ta bi bayanta dakin kofar suka fara budewa sai suka hangota zaune a kan wheelchair din ta juyo tana kallonsu.

“Kin ga musakar can, daya dauko ya kawo mana”

Leila ta fada tana yamutsa fuska, sai Madina ta karasa kusa da Aminatu tana mata murmushi, sai da ta kawar da murmushi a fuskarta sannan ta juyo ta kalli Leila.

“Ki daina haka, ke ma baki wuce Allah ya jarrabe ki ba, abun da Talba yayi abu ne mai kyau, kamata yayi ki taya shi sai ku ci ribar tare, taimakon maraya abu ne mai kyau ni kaina ba abun da nake so kamar wannan”

Leila taja tsaki ta saki kofar dakin ta juya ta fice domin ta fahimci Madina ba zata gane abun da take nufi ba. Sai da ta fice sannan Madina ta rage murya ta kalli Aminatu.

“Idan Talba ya dawo ki fada masa abun da Leila tace miki, da kuma wanda nace kin ji?”

Uffan Aminatu bata ce mata ba, kuma bata nuna wata alama dake nuna ta ji ko bata ji ba. Madina ta mike tsaye tana sakar mata murmushi.

“Zan dawo gobe na gyara miki kanki, wata kila ma anjima na sake dawowa, Allah baki lafiya”

Ta fada sannan ta juya ta fice. Ko da ta fito Leila na zaune a inda suka zauna dazun tana tabin wayarta.

“Ina Momy?”

“Ta hau sama”

Ta amsa mata ba tare data kalleta ba.

“Tana sama”

“Idan ta fito ki fada mata na tafi”

Leila ta mike tsaye ta bi bayanta, rakata tai har gurin motarta, Bayan Madina ta bude motar ta shiga ta zauna ta kalli Leila ta ce.

“Ina ganin kamar Talba ba zai iya son yarinyar nan ba, amman komai zai iya canjawa”

Leila ta bushe da dariya.

“Madina baki da hankali”

“Really? Ai tausayi ne silar soyayya tun da har ya fara tausayinta, ba ki ga yadda yake son a kula da ita ba?”

Wani irin zafi zuciyar Leila ta fara yi, ba dan ta yarda da maganar Madina ba, sai dan danganta alakar so da tai da Talba.

“Madina kamar baki san waye talwba ba, yaran masu arziki basa aure sai masu arziki, amman duk wanda ya gaji arziki ya taso a cikinsa ya ginu a cikinsa ba zai taba son rabar talaka ba, a littafai ne ake wannan ko a fina finai, amman talaka sai talaka mai arziki sai dan arziki kaddara ma yana sonta kina tunanin Momy da Daddy za su saka masa ido yana aureta? Ni kuma yayi ya da ni?”

Madina ta yi dariya.

“Waya ga Leila da kishiya”

“Har abada ba zan taba zama da kishiya ba”

“Ko da ni ne?”

Ta fada tana dariya, sai ita ma tai dariya.

“Kin san wani abu? Taimako daya zan miki, ki yi yadda zaki iya yarinyar nan ta dawo karkashin kulawata”

“Ya za'ayi haka ta faru? Kin san yanzu Talba ba yarda yake da ni ba, balle na bashi shawarar ya kai ta gurinki, tsaya ma me zai saka ya kaita gurinki?”

“Saboda ya nisanta da ita, ki kuma ki samu kusanci da shi, amman idan tana gidan nan, kullum sai kun samu matsala da shi, hakan kuma zai ta lalata alakarku ne har ya kai inda ba a so”

Leila ta yi shiru tana nazarin maganar, ta san gaskiya Madina ta fada sai dai tana ganin hakan kamar a dabara ba ne.

“Kawai ki bari sai ina nan shi m yana nan, ki yi mata wani abun da zai zama na magana, daga nan sai ki yi rantsuwa ba zata zauna ba, sai ki bar min sauran aikin”

Ta karasa tana kanne mata ido daya, Leila dai ta bita da kallon badan ta gamsu ba, har ta rufe motar tai reverse ta bar

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment