Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta nufi wayarta dake ringing ta dauka.

“Hello”

“Madina ya kika?”

“Lafiya kalau, kamar Kabir”

“Ni ne baki da number ta, ni ai ina da taki”

“Uhm Ya aikin?”

“Alhamdulillah, Yarinyar nan tana gurinki?”

“Wai Shalele? Eh tana nan”

“Shalele kuma?”

“Eh haka na ji Talba na kiranta, na dauka haka kuke kiranta ne ai saboda tana da sunan Momy”

“Aa zan zo na dubata yanzu”

“Momy ta sauko kenan?”

“No tana da ciwo a kafarta, zan duba ciwon ne, kuma ga maganinta nan kin manta”

“Okay sai ka zo”

Ta sauke wayar tana kallon Aminatu.

“Shalele wai haka Talba ke kiranki ko a gida?”

“Aa”

Aminatu ta amsa mata a takaice cikin rashin sakewa. Tsayawa tai tana kallonta sannan ta fice tana kiran Leila a waya.
Harabar gidan ta fito tana labartawa Leila abun da ya faru.

“Yau fa be ma shigo nan ba, ko Momy ta waya ya gaishe ta, be leko bangaren nan gaba daya, kuma na san duk saboda na ce ba zata zauna a bangaren ba ne”

“Ni abun har mamaki, taya zaka hadu da yarinya a titi kace zaka fifitata sama da yar'uwarka kuma matar da zaka aura”

“Daman kin san bama sha inuwa daya, idan ba ganin yai raina ya bace ba hankalinsa ba zai taba kwanciya ba”

“Jiya fa bata kwanta ba sai da ta ji muryarsa”

“Da gaske?”

“Wallahi kuwa, kin ji yadda yake kiranta Shalele”

“Madina sai na ci uban yarinyar nan, me take nufi?”

“Me yake nufi dai shi, idan bata ga fuska ba ai ba zata soma ba, amman fa karki ce ni na fada miki”

“Ai ba zan fada ba, amman dole na dauki mataki?”

“Matakin me zaki dauka? Har a bada, Talba ba zai taba auren yarinyar nan ba, ko da yana sonta, Wallahi ba zan bari ba, sai dai ina ganin yana yi ne saboda ya musguna miki, shiyasa na baki shawarar ki kulla soyayya da Ali, so that ya ji yadda kike ji, amman ko dan rashin sanin asalinta da kuma fyaden da akai mata ai ba zai aureta ba, besides ita fa ba yar kowa ba ce”

“Na san da wannan, amman ko zai yi dan ya bata min rai be kamata yai da wannan yarinyar ba”

“Zan kira ki anjima”

Ta yi saurin katse kiran hango motar Kabir da tai, tana tsaye har ya iso kusa da ita ya faka motar ya bude.

“Hajiya Madina...?”

“Yau dai sai gaka gidanmu kamar wasa”

Yayi dariya.

“Na zo na goge laifina ne, kin san jiya ba mu kyautawa Talba ba, shiyasa na zo na goge laifina”

“Hakan ya kamata gaskiya, bari na fito da ita”

Ya mika mata maganin ta karba ta shiga ciki ba dadewa ta fito tare da Aminatu ta kawo masa har gurin motar.

“Tashi tsaye”

Ta girgiza kai.

“Ni bana ita tashi yana min ciwo”

Fitowa yai motar ya duka gabanta yana duba kafafuwan, sannan ya koma ciki ya dauko safa ya saka a hannunsa ya fara latsa kafafuwan.

“Akwai zafi fa”

Ta fada a shagwabe. Rikata ya mikar da ita tsaye, sannan ya saka dayan hannunsa ya janye kujerar yana kokarin sakinta.

“Aa aa aa akwai zafi”

“Haka zaki hakura ki tsaya idan baki tafiya ya za'ayi ya warke? Kin yi gudun daya wuce kima ne shiyasa amman kina fara takawa zai warke tun da an saka miki magani”

Ya saketa sai ta fara rawa can kuma ta kasa tsayuwar ta fadi, tsakanin Madina da Kabir aka rasa wanda zai rika ta har ta kai kasa.

“Kar a sake bari tai zauna, ku rika barinta tana tafiya”

“Ton”

Ya koma cikin motar ya dauko takardar yayi rubutu akai ya mikawa Madina.

“A nemo mata wannan maganin duka na shafawa ne”

“Okay”

Ta fada tana karba sannan ya rufe motar ya juya ya fice daga gidan. Sannan Madina ta nufi inda take da keken ta rikata ta zauna.

“Karki takura kanki da tafiya, idan ba zaki iya ba ki yi zamanki a nan kin ji?”

“Toh”

Ta fada idonta tab da kwalla. Suna shiga ciki Madina ta kalleta tace.

“Anjima zan kaiki gurin gyaran kai, kuma zan muje da ke ki zabo tufafin da kike so, amman kamin mu tafi zan kira Talba ki fada masa inda zamu je, sai ki ce masa kina son ya raka mu okay?”

“Toh”

“Good, kuma idan yace zai je aiki ki ce masa kina son zaman a gurin aikinsa kamin na dawo daga nawa aikin, saboda ni ma aiki zanje yanzu”

“Tohm”

Kamar hadin baki Madina na daukar wayar da zimmar kiran Talba sai gashi ya kirata, murmushi ne ya kawata fuskarsa tai picking call din ranta fes.

“Hello”

“Shalele na kusa”

“Eh”

Ta amsa tana hade abu mai daci na kiran Aminatu da yai da Shalele sannan ta mika mata wayar.

“Hello”

“Shalele kin tashi lafiya?”

“Lafiya kalau, yanzu zamu je gurim siyen kayan sakawa da kuma gyaran kai, idan kana nan ina son mu tafi tare”

Ya dan yi jimmm kamar mai sauraren wani gurin, har sai da ta dauke wayar daga kunnenta ta duba sannan ta sake maida wayar.

“Hello”

“Already ina Office, ba zan samu zuwa ba kuje tare da Madina ki zabo duk abun da kike so”

“Ita ma aiki zata je yanzu, ko ta kawo ni a nan idan ta tashi sai ta zo mu tafi tare”

“Miyasa kike son zuwa inda nake ne?”

Tayi shiru sai kuma ta ce.

“Ka yi hakuri”

“No ba zan cen na yi hakuri ba ne, bata wayar”

“Gashi yace a baki wayar”

Ta mikawa Madina.

“Ki kawo ta nan idan zaki je aikin, idan kin dawo sai ki zo ki dauketa kuje siyayyar”

“Wata kila zata fi sakewa idan muka je tare da kai, tun jiya bata da magana sai taka, tun safe take son na kiraka, ni kuma bana son ka ga kamar ina takura maka ne, and you know her situation duk abun da zai sakata farinciki shi ya kamata mu yi”

Tana kawai nan ya yanke wayar, sai tai murmushi.
25

Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

Kamin su sai da ta kira ta fadawa Leila cewar zata je yi mata siyaya ita kuma tace sai anje da Talba kuma yana gurin aiki yace a kawo masa ita kamin ya tashi aikin. Sannan ta shiryawa Aminatu cikin atamfa mai kyau duk da kasancewar ta yi mata yawa domin tsawo da jikin Madina ba daya dana Leila ba, sai dai hakan he hana atamfar karbarta ta mata kyau sosai sannan ta saka mata hijab.

“Ba zamu je da kujera ba, daurewa zaki yi ki rika takawa”

“Ba zan iya ba akwai zafi”

“Zaki iya ma”

Madina ta rikota sai ta fara takawa a hankali da dan tsoro, tana jin zafi sai dai ba irin zafin da zai hanata takawan ba, wata kila dai da tsayin ne ba zata iya ba. Da taimakon Madina suka fito falon har da gaisa da Hajiya sannan suka nufi kofa ba laifi ta yi kokari domin da kafafuwanta ta isa isa gurin motar Madina, ta bude mata ta shiga ta zagaya bangarenta, dadi gurin Aminatu ba a magana, saboda ta taka da fafuwanta a zatonta ba zata iya ba. Sai da suka yi tafiyar rabin awa sannan suka iso Kamfani, wani irin shuki ne ya kama Madina ace wai mijinta ne ke da iko da katon kamfani kamar wannan, bayan kyau da cikar kalama da Allah yai masa.

“Hmmm Leila kina wasa da damarki”

Ta furta tana karewa kamfanin kallon, kalaman da ta yi ne suka saka Aminatu ta kalleta. Sai tai hade yawu ta ciro wayarta ta kira Talba ta mikawa Aminatu.

“Hello”

Jin muryar Aminatu ya saka ya amsa.

“Shalele”

“Na'am mun zo muna waje”

“Okay, zan aiko a shiga dake yanzu nan”

“Toh”

Ta mikawa Madina wayar, Madina ta kai wayar a kirjinta ta rumgume tare da lumshe idonta bude. Ba jimawa wata mace sanye da suit kanta babu mayafi tana sanye da sarkar cross ta nufi inda suke ta gaisa da Madina sannan ta nunawa Aminatu hanya.

“Malama Bismillah”

“Ba zata iya tafiya ita kadai ba, sai kin taimaka mata”

Matar ta rika Aminatu suka fara tafiyar a hankali har suka shiga ciki, sannan Madina ta koma motar ta tana ayyana irin kulawar da zata bawa Talba idan mafarki da take ya tabbata, sam bata hangowa kanta yadda taraiyar da Leila zata lalace idan har soyayya ta kullu a tsakaninta da Talba.
  Aminatu na rike da hannun matar suna takawa a hankali har suka hau sama, daman kamfanin mai hawa biyu ne. Yadda take ganin mutane sai ya saka ta dan tsorata abun ka da bakauye, kamin su isa gurin office din Talba ya fito hannayensa duka biyu a aljihu, yana sanye da suit kala daya dana matar dake rike da ita, wato black color. Murmushi ya sakar mata sannan ya kalli matar ya ce.

“Chidima sake ta, tafiyarki”

“Okay Sir”

Ta sake ta kamar yadda ya bukata ta juya ta bi wata hanyar, har lokacin murmushi yake yi ma Aminatu.

“Tako ki zo nan”

“Akwai zafi idan wani be rika ni ba ba zan iya tafiya ba”

“To ni zan koma ciki idan ba zaki zo ba”

“Wash.. Wash... Wash... Akwai zafi”

Nan da nan har ta fara hawaye tana takawa a dolenta tana ta raki, hannunsa daya ya ciro ya miko mata alamar ta kama.

“To ka matso”

“Aa ki zo dai, Madina ta kyauta, ta gyara min ke kin yi kyau, kuma gashi har kina takawa”

Daker ta karasa inda yake ta rika hannunsa suka karasa shiga karamin office din mai dauke da wata macen bahaushiya, da alama sakatariyarsa ce, sannan ya wuce office dinsa dake hannun dama. Yana shiga da ita ta fara rabon ido sanyin ac na ratsata, har gaban kujerar dake taburinsa ya kaita ya zaunar da ita.

“Duk wannan katon office din naka ne?”

Ya daga kai yana kallon office din kamar yadda take, sai ya dan tabe.

“Ba Office dina ba ne”

Ta nuna masa hoton Daddy sai ya juya ya kalli katon haton dake manne.

“Abokin Daddyn ne mai kamfani shiyasa ya saka hotonsa, kuma yanzu yayi tafiya shi ne yace yana son na zauna a nan kamin ya dawo”

Ta yi murmushi sai shi ma yai murmushi.

“Murmushi na miki kyau, jiya ma kin yi shi da muna gidan marayun nan”

Sai tai kasa da kanta.

“Fada min me kika ci yau?”

Ta daga hannunta tana taba teburin shi kuma ya zauna a kujerar dake facin din ta yana kallonta.

“Da safe mun sha tea da birede kuma mun ci waina kwai, wannan kanenka ya zo ya duba ni, yana ta latsa min kafa yace wai Madina ta daina bari ina zaunawa, wai sai dai na yi tafiya”

Tana fadar hakan Talba ya gane Kabir take nufi.

“Ya kyauta, me kike son ki ci? Tea ko lemu”

“Bana jin yunwa”

Ya mike tsaye ya nufi firgin din ya bude ya dauko lemu ya zuba mata a lemu ya mika mata, sai ta karba da hannu biyu ta sha kadan ta rike raguwar.

“Mai office din nan fada yake idan wani ya sha masa lemu ya rage”

“Da gaske?”

Ta yi saurin kai ragowar bakinta ta shanye da sauri ta mika masa cup din.

“Na shanye duka”

Ya karbi cup din ya juya yana dariya ba tare da ta gani ba. Sai da ya aje cup din sannan ya juyo ya dauki wasu takardun yana kallonta.

“Mai office din nan baya son ayi masa bachi a office”

“To ai ba bachi zan yi ba”

“Ni ma ai ban ce bachi zaki yi ba, zan yi wani meeting ne kar na tafi ya shigo ya tarar kin yi bachi”

“Ba zan yi bachi ba”

Ya daga mata kai sannan ya dauki takardun ya fice a office din ya barta yaje meeting ko da ya dawo tana zaune tana kallon tv.

“Ba ki yi bachi ba?”

“Ai kai ce mai kamfanin bayan son ayi masa bachi, ban yi ba”

Yayi murmushi.

“Me kike son ki ci yanzu?”

“Bana son komai”

“To ni yunwa nake ji, bari mu kira Madina ta zo mu tafi siyayyar mu dawo na kaiku gida sai na je gida ni ma na ci abinci”

Ta daga masa kai sai ya dauki wayarsa dake nan ya kira Madina, ringing daya ta daga.

“Hello”

“Baki tashi aikin ba?”

“Ban gama ba, amman zan iya fitowa yanzu, tana bukatar wani abu ne?”

“No ina son na tafi gida ne”

“Okay gani nan zuwa”

Ya aje wayar, sannan ya zauna a kujerar dazun yana kallon Aminatu.

“Shalele, fada min me kika fi so lokacin da kina gida?”

Ta fara bashi labarinta da yadda take rayuwar a kauye da yadda yayanta Sanusi yake yawan tsokanarta har zuwa abubuwan da suka faru sai gata tana ta kuka hawaye na sauko mata.

“Ya Sanusi ai yana da gaskiya, ke raguwa ce abu kadan sai kuka, ungo wannan ki share hawayenki”

Ya mika mata tissue, sannan ya tashi ya dauko mata ruwa ya zuba mata a wani kofin ya mika mata, ta karba ta sha wasu hawayen na sauko mata.

“Shikenan komai ya wuce”

Ya fada yana jin wani irin tausayinta ma kara kamashi. After like 30 minutes  Madina ta kira wayarsa ta sanar masa tana waje.

“Ta so muje ta iso”

Yana fadar hakan yai gaba sai ta ce.

“Yallabai ba zan ita tafiya da kaina ba”

“Raguwa”

Ya fada sannan ya dawo ya rika suka fita tare, yana rike da ita har suka sauka kasa yana fitowa direbansa ya janyo mota ya iso inda suke tsaye, sai Talba ya budewa mata front seat ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya kalli Madina dake tsaye.

“Bismillah”

Ta bude motar ta shiga duk kuwa da kasancewar ba haka ta so ba, a zatonta zai barta ta shiga front seat din ya saka Aminatu a baya, shiyasa ta bar motarta a gurin aikin ta hau Napep zuwa nan. Key din ya karba ya shiga motar yaja suka kama hanya. A hankali yake driving har suka isa Wani babban super market dake cikin garin gusau, yana yin fakin Madina ta bude ta fito ta zagaya ta sauri saboda ta samu rika Aminatu kamin Talba ya rika ta, har ga Allah bata son rikon da yake mata zuciyarta tana sosuwa ba kadan. Ta bude side din Aminatu ta rikota ta fito, yana gaba suna baya suka shiga super maket din.



LEILA POV.

Har wani huci take tana fadawa Momy abun da Madina ta fada mata.

“Leila baki da wayo baki da tunani, yarinyar so take ta dora ki a keken bera, idan ba haka ba mi zai saka ta rika kiranki tana fada miki abun da yai ko yace? Ni fa gani nake kamar so take ta hada ku”

“Haba Momy kamar baki san Madina ba, Wallahi ba zata yi haka ba”

“Aman yadda take fada, ni na san Talba ba zai aikata hakan ba har da wani kiranta Shalele tana karawa abun gishiri kawai, zan dai iya yarda tace a kira mata shi, dan haka ki yi hankali da ita”

Har Leila ta bude baki zata yi magana sai ga Amal ta shigo sanye da uniform din makarantar boko har dan gudunta.

“Momy Daddy yana falo yana jiranki”

“Yana jirana? Kamar ya? Wani abun kika fada masa ne?”

Amal ta yi shiru tana kallon Momy, kamin Momy tai wani yunkuri har Daddy ya shigo dakin kana ganinsa kasan ransa a bace yake.

“Amina kina ji kina gani Mu'az ya fita da yarinyar nan gidan nan?”

Momy ta hade yawun bakinta ta kalli Amal.

“Wallahi ban dauka abun zai kai haka ba, ban dauka Daddy zai dauka da zafi ba, Momy ki yi hakuri ba zan kara ba”

Daddy ya kalli Amal sannan ya kalli Momy rai a bace ya ce.

“Okay hakan yana nufi hanata kike ta fada min idan wani abun ya faru ko? Taya Mu'az zai dauko yarinya ya kawo ta a gidan nan sannan ke da yayanki ku wulakantata ki saka ya fitar da ita gidan nan? Ni kuka wulakanta ba shi ba ko ita, a tunani ko kare Ma'az ya dauko ya kawo a gidan nan ya kamata ki mutuntashi”

“Ban ce ya fita da ita ba, Leila ta yi rantsuwa yarinyar ba zata zauna a gidan nan ba, tace sai dai ya zaba ita ko yarinyar, kuma ka san babu yadda za ayi na bar Leila na zabi yarinyar da ban san asalinta ba”

“Miyasa baki tura Leila waje ba kin bar yarinyar? Ke har kullum ba zaki nuna cewa danki ba na ki bane dan wasu shi ne naki? Idan kin tozarta Mu'az kin ci mutuncin ribar mika ce? Akan Mu'az zan iya batawa da kowa, kuma ba zan dauki raini akan jinina ba, ba zan taba yarda a nuna masa isa ko rashin galihu ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Engineer wannan soyayya da kake nunawa Talba ta yi yawa, idonka ya rufe ruf baka ganin komai sai shi, ko yayanka baka so yadda kake son yaron nan, tsintacciyar mage bata taba zama mage ba, ni fa matarka ce amman idonka ya rufe akanTalba kana fada min magana son ranka dan Allah ka...”

Momy bata karasa ba Daddy ya nuna kansa a razane.

“Amina? Ni kike fadawa Tsintacciyar mage bata mage? Mu'az ne tsintacciyar mage? Yaron da ubansa ne sanadiyar arziki da nake ci a yanzu? Yaron da dan'uwana ya yafe karatunsa saboda ni na samu ingantaciyar rayuwa? Yaron da soyayyar mahaifinsa ta saka ya saka shi barin wasiyar idan an haifi masa da a saka masa sunana? Saboda uban yaron nan na samu ilmi har na zama abun da na zama a yanzu, karki manta babu abun da Mu'az yake nema a duniyar nan, dan'uwana be mutu ba sai da ya bar masa abun da zai isheshi kula da rayuwarsa, yaron da ba uwa ba uba? Ai ko da dan'uwana yana raye ba zan dauka a musgun ma dansa ba balle kuma ba shi da rai, dan'uwana yayi min komai Amina, dan'uwa na zame min uwa ya zame min uba, a lokacin da kowa ya kyare mu, dan'uwana shi ne ci na shi ne sha na, idan ina ciwo shi ne, saboda ni dan'uwana ya rasa rayuwarsa, yanzu kuma kike kiran dansa da tsintacciyar mage? Saboda ni dan'uwa na rabu da matansa biyu amman yau kin aibanta dan dan'uwana a gabana”

Hawaye ya cika idon Daddy.

“Na gode, indai maganar dana da nake ne ya zame miki fitina da tashin hankali, to na sauwake miki ki tafi inda zaki zauna ki samu kwanciyar hankali da natsuwa, ni kuma zan kawo wanda ke son dana wanda zata so abun da ya ke so, domin na tabbatar da Kabir ba zaki yarda ki masa wannan wulakancin ba, ba zan jure ko maganar banza a fadawa Mu'az ba, Wallahi ka bata masa rai kara a bata min rai, kuma har a bada ba zan wulakanta jinina ba...”

Momy ta daki kirji da karfi tana fadin.

“Engineer sakina kai?”

Amal ta dora hannu akai ta fashe da kuka, Leila kuma ta yi sauri girgiza kai tana kallon Daddy daya juya zai fice daga dakin.

“Daddy no please be kamata kai haka ba, abun da ba ayi da kurciya ba be kamata ka yi shi a yanzu da girma ya kama ma...”

Juyowa Daddy yai ya kalleta.

“Ba ke kika ja komai ba? Akan dana, zan iya batawa da kowa you too should be very careful...”

Tsayawa tai cak tana kallon yadda ransa ya bace har wani huci yake irin ma su na manya. Sai da ya fice sannan ta juyo ta dawo gurin Momy dake tsaye tana ganin komai kamar a mafarki.

“Momy dan Alla... ”

Tassss Leila ta wanke fuskar Amal dake maganar da mari.

“Dan ubanki ba ke kika ja komai ba? Duk abun da akai a gidan nan yana bakinki, komai aka yi sai ki je kin fadawa Daddy, yanzu ai kin ga ribar abun ko?”

“Ya Kabir ne ya fada min, ni ban dauka abun zai saka a saki Momy ba..”

Momy ta zauna tana nuna kanta.

“Yau ni Alhaji zai saki saboda Talba? Abun da be taba min ba? Saki? Ni Aminatu?”

Leila ta yi saurin dafata tana hawaye.

“Momy dan Allah ki yi hakuri, zafin zuciya ne da bacin rai nasan anjima zai sauko ya gane cewar yayi kuskure”

“Kar ma ya sauko, awa daya ba zan kara a gidan nan ba, je ki kira min Mairo ta zo ta hada min kayana ke da Shi sai kun dandana zafin rashina”

Momy ta fada tana kallon Amal dake kuka.

“Momy idan kika tafi mu zaki bari a damuwa dan Allah ki yi hakuri”

Leila ta fada tana kuka.

“Duk bakar yarinyar nan ce taja komai, duk ita ta haddasa mana fitina a gida”

Amal ma ban da kuka babu abun da take, bata aikata wani abu taji ta yi nadamar aikata shi ba irin fadawa Daddy abun da ya faru. Momy ta mike tsaye a fusace ta sauka kasa ta nufi hanyar kitchen inda Mairo da zulai suke suna aikin hada abun karyawa.

“Mairo Zulai ku shiga dakina ku janyo akwatunana ku zuba tufafi da yake wardrobe”

“To Hajiya”

Suka bar kicin din da sauri suka nufi upstairs, sai ta sake nuna kanta.

“Ya sake ni? Lallai Engineer...”

Ta girgiza kai tana jingina lamarin.



FARUQ POV.

Ko kadan sakin da Faruq yai ma Baturiya be yi ma Mama dadi ba.

“Saki ba shi da dadi, amman halin yarinyar nan ya wuce inda muke tunani, sai dai bana son wannan abun ya taba zumuncin mu”

“Inshallahu babu abun da zai samu zumuncin mu Mama, gobe zan je na kwaso tufafina na dawo da su anan, zan bar Sultan a nan ni kuma nan da kwana biyu zan bar garin nan na tafi nijar, idan Allah ya buda mana sai na samo a can idan na dawo sai na ayi wani auren, ita kuma zan cigaba da kula da ita saboda cikin dake jikinta”

“Yaya ba za'a gyara ba?”

Cewar Aisha cikin damuwa sai Faruq ya girgiza mata kai.

“Bana son na yi uku, na riga na yi biyu kuma na riga na cire Rafi'a a raina, ba zan iya zama da ita a wannan sabon halin da ta fara ba, kuma duk wani cin mutuncin daya kamata ta yi min, ba ta inda ta raga min, nan gaba ban zan yadda abun zai zama ba”

“Allah yasa haka shi yafi alheri ya baka ta gari, ita kuma ya shirya ta”

“Amin, ranar alhamis din nan nake son tafiya inshallah, tare da Malam Sirajo”

“To Allah yai maka fatahi a tafiyar, mutane na samowa, ko dan gidan Amadu ya samu yana dawowa ya siye gida da babur, amman tafiyar ce abun tsoro gashi ance ramen yana rusgawa da mutane”

“Kawai ki min addu'a Mama dacewa kawai ake so”

“To Allah ya datar da mu”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya kwantar da Sultan dake jikinsa yana bachi kan shimfidar Mama.

“Baka nan kenan za'ayi bikin Aisha”

Mama ta fada tana kallon danta cike da tausayawa.

“Bana son na kara sati a garin nan kam”

Ba dan neman halal kawai yake son tafiyar ba, har da gujewa Baturiya saboda abun da tai masa da kuma sakin da yai mata ya tsaya masa arai yana jin babu dadi musamman idan ya tuna cewar saboda talauci tai masa haka. A dakin ya bar Sultan saboda Mama ta kula masa da shi, shi kuma ya nufi dayan dakin da ba a karasa ginewa ba ya shimfida tabarma da zane ya shimfida, sannan ya kunna maganin sauro ya kwanta, sai dai ko kadan bachin be ziyarce shi ba, sai tunani yake kala kala har safe.

BATURIYA POV.

Bata bar gidan ba sai da safe, sannan ta saka wasu tufafin ta saka Hijab ta rufe gidan ta tafi gidansu.
Tun a Napep ta fara kirkirar kuka, sai dai kukan be zo mata har sai da ta sallami mai Napep din ta shiga cikin gidan, sannan ta fashe da kuka tana faduwa tana tashi hankali kowa sai da ya tashi a gidan. Cikin kuka ta fadawa Umma irin abun da ta fadawa makontata, a take ran Umma ya ace ta

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment