Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na yarda da ke”

“Babu wanda zai taba jin wannan maganar daga gareni Leila, amman ina baki shawara ne akan abun da nake ganin zai zame miki masalaha”

“Yanzu dai bari na tafi Ali yana jirana”

“Okay”

Leila ta aje wayar sannan ta sauka saman gadon ta dauki wani karamin mayafi ta rufe kanta, sannan ta saka talkaminta ta nufi kofar fita idonta a kumbure saboda kukan da ta sha.
Ko da ta sauko falon babu kowa, dukansu suna bangaren Daddy, yan aikin Momy kuma Momy bata basu damar zama a falonta hakan yasa idan ba wani aikin zasu ba abu ne mai wahala ka gansu a main house din kullum suna BQ. A hankali ya bude kofar falon ta fita gabanta na faduwa, domin ji take kamar zata yi arba da Talba ne, domin a yanzu bata son ganin fuskarsa, ba dan bacin rai ba sai dan bata da amsar tambayar da zai mata. Tun kamin ta karasa gurin gate din police din ta bude mata karamar kofar ta fice, tana fitowa ta ga motar Ali fake sai ta nufi inda motar take. Ali na zaune cikin motar yana kallonta har ta karaso gaba daya sai ya ji tausayinta ya kama shi, a da can yana bata laifi kamar yadda yake bawa abokinsa sai dai a yanzu ya fahimci abokinsa ne mai matsala ba ita ba. Bude motar tai ta shiga sannan ta rufe ta kalleshi da idonta da suka kumbura.

“Ali”

Sai da ya sauke wani dogon numfashi sannan ya amsa mata.

“Na'am Leila, ya kike?”

Tambayar ya take da yai sai ta ji kamar ya tsokano mata kukanta, a take hawaye ya cika idonta.

“Ba Kalau ba Ali, ba Kalau ba”

“Na sani, abokina yayi rashin tunani, amman ban dauka zai miki magana ba, a thought ya bar abun a ransa ne kawai, sai dai faga lokacin dana kira ki na ji yanayinki, sai tausayinki ya kama ni, and now na fahimci irin halin da kike ciki”

Ya karasa yana kai hannu ya ciro tissue ya mika mata, sai ta karba ta share hawayenta.

“Sometimes ina kasa fahimtar waye Talba, abokinka yana da wahalar sha'ani Ali, taya wanda zaka aura zai zarge ka da kisa? How? And Why? Saboda na nuna kishina? Talba be dadin zama wani lokacin”

“Na sani, amman ban dauka abun zai kaishi haka ba”

Cewar Ali yana kallonta gaba daya zuciyarsa ta cika da tausayinta, domin gani yake Talba baya sonta ita ce kawai sonsa ke dawainiya da ita.

“And i respect your decision na cewar ba zaki auri Talba ba har sai ya canja”

Juyowa tai ta kalleshi da kyau.

“Dan Allah zaka fada min abun da ta faru da yarinyar?”

A takaice ya labarta mata komai na yadda aka samu yarinyar, sai dai be fada mata cewar Talba ya dauke ta daga asibitin ba, haka ma be fada mata cewar sun samu tsabani ba, domin yana ganin kamar sirrinsa ne da be kamata kowa ya ji ba.

“Amman me zai saka wani yai mata haka?”

“Ni ma ban sani ba, kuma a iya binciken da na yi wani be shigo ba, so dole dai sai ta farka zata iya fada mana yadda komai ya faru”

“Yanzu tana asibitinku?”

“No na canja mata asibiti, and i am here to apologize saboda ni na janyo komai, Talba be san yarinyar nan ba, ni na hada shi da ita da neman ya taimaka mata saboda yarinyar tana bukatar taimako, amman ban yi tunanin abun zai zama na rigima haka ba”

“Baka da laifi, na san ka yi ne da kyakkyawar niya, be kamata ka bada hakuri ba”

Yayi shiru na wani lokacin kamin ya kalleta ya ce.

“Amman Leila kin yi wani abun ne da zai saka Talba ya zargeki da taba yarinyar nan?”

“Ban yi komai ba, amman kasan a gurin abokinka kullum nice mai laifi, kawai dai na fahimci wani abu... Talba baya so na ni ce kawai na mutu da kaunarsa, wanda yake sonka ba zai maka haka ba, ko da gaske na aikata zai nemi hanyar kare ni ne, ba ya tunkare da wannan laifi mai girma ba, abun akwai ciwo”

Ta karasa wasu hawaye masu zafi na sauko mata, har cikin ranta tana fadawa Ali abunda ta fahimta ne akan zamantakewarta da Talba. Ali ya kawar dai yana jin irin tausayinta na kara kamashi.

“Ada can na dauka miskilancinsa ne ya saka yake min abun da yake min, amman a yanzu na fahimci kauna ta ce babu abunsa, kawai ya amince ne saboda ba zai iya cewa Daddy a a ba”

Ta runtse tana kokarin fashewa da kuka.

“Kabir yana da fada min gaskiya amman na kasa ganewa, saboda kaunar Talba ta cika min zuciya amman yanzu na fahimta...”

Ali yayi saurin daukar ruwan dake cikin motarsa ya mika mata.

“Please sha ruwa”

Sai kuma ya dauko tissue ya mika mata.

“Ki daina damuwa dan Allah, kukan nan yayi yawa idonki har ya kumbura, me yasa zaki damar kanki akan Namiji?”

Sai ta kalleshi hawaye na sauko mata

“Talba be taba min haka ba, na gode”

Ta fada sannan ta karba ya share hawayenta ta bude ruwan ta sha.

“Ki je ki huta, karki saka damuwar komai a ranki komai zai wuce, kin san idan ya fusata yana aikata abubuwa amman zai sauko and ina tabbatar miki zai baki hakuri”

Ta dan yi murmushi irin na bakinciki da kuma kin yarda da maganar Ali cewar zai bata hakuri domin ta san waye Talba, sai dai bata ce masa komai ta bude motar ta fita, Ali ya bita da kallo cike da tausayi har ta shige cikin gidan, sannan ya kai hannu ya dauki wayarsa dake carji a jikin motar ya kira Talba, wayar tai ta ringing har ta gaji ta katse be daga ba ya sake kiransa nan ma shiru, haka ya jera masa kusan 4 miss calls a na biyar ya ji wayar a kashe alamar ya gaji da kiran da yake masa kenan kuma ba zai yi picking ba.

“Talba....”

Ali ya fada yana jin kamar ace yana kusa da shi yai masa dan banzan duka a yau saboda kukan da Leila ta sha akasa.

‘Ina ka kai yarinyar nan?’

Shine sakon daya tura masa sannan yai reverse ya kama hanyar gidansa.


TALBA POV.

Be dawo gidan ba sai dare, domin bayan an gama diban jininsa sai ya fito asibitin ya koma gidan marayun, daman can yakan je idan yana cikin bacin rai ko damuwa ya wuni a can, sai ya ji damuwar tasa ta ragu saboda yara suna rage masa kewa, and ko ba komai zai ji cewar ba shi ne kadai a damuwa ba, su ma sun rasa iyaye da yan'uwa amman sun zaune a inda Allah ya tsara musu rayuwarsu kuma suna farinciki, balle kuma shi da Allah yai ma ni'imar aje su da ciyarda su, bayan tarin lafiya da ni'imar yan'uwa da kuma ta uba kamar Daddy da Allah yai masa.
A can yai sallah magaba a can yai isha'i, be dawo gida ba sai ba tara saura, wunin yau bayan abincin safe be sake saka komai a cikinsa ba sai ruwa. Yana shigowa ya faka motarsa kusa da entrance din Momy sannan ya fito ya nufi kofar falon cikin yanayin da ba zai iya fada ba, kawai misaltawa yake idan har da gaske Momy da Leila suna da hannu a mutuwar Baaba ko batanta ya iyalanta za su ji? Yayanta da jikokinta? And ya ma akai komai ya faru? Idan ma kasheta sukai ina suka kai gawarta. Sau biyu yana danna door bell din sannan Amal ta bude masa kofar.

“Ya Talba welcome”

Ya amsa mata ta kai fuska ba yabo ba fallasa, sannan ya shigo cikin falon, hakan ta nuna alamar baya cikin walwala. karasa yai kusa da Kabir dake zaune a sofa yana cin tuwon samun miyar gayye ya zauna. Kallo daya yai ma tuwon ya dauke kai domin shi ba ma'aboci cin tuwo ba ne, wayarsa dake aljihu ya ciro ya kunna sai ga sakon Ali ya shigo wayarsa.

‘Ubanta ne kai?’

Shine reply din da yai ma Ali sannan ya aje wayar ya busar da iskar bakinsa.  Kabir ya kalleshi sannan ya kalli Amal dake zaune tana kallonsu dama haka take idan ta lura da ba a zaune kalau, so that ta samu abun tseguntawa Daddy.

“Amal je ki yi bachi mana”

Kabir ya fada, sai ta make kafada.

“Bana jin bachi yanzu”

A take ya zare mata ido, hakan ke nuna ba da wasa yake ba, ya saba wasa da ita sosai sai dai a duk lokacin da yake serious magana da ita ta san yanayinsa. Mikewa tai tsaye tana kallon Talba.

“Ya sai da safe”

Ta murgudawa Kabir baki sai ya kyalkyale da dariya yai mata gwalo.

“Daddy's noy could we talk?”

Talba ya kalleshi.

“Leila ta fada maka ne?”

“Nooo Amal dai ta shinshino ta shinshina min”

Talba ya dan yi murmushi kadan yana kallon hannunsa.

“Na bada jinina yau”

Kabir ya duba shi duba na mamaki, ba zai ce ya san dukan abun da Talba yake yi ba, amman be taba jin yace zai bada jininsa ga kowa ba.

“Something new...”

Talba yayi murmushi.

“Yeah.... I feel like..... ”

Sai kuma yai shiru kamar mai tunanin abun da zai fada.

“I feel honour.. I mean it was a great joy.... to do....something like this”

A rarrabe yai maganar and he is very excited, he can't tell why amman yana jin yayi abu mai kyau.

“Yeah at least wani zai rayu da jininka, and mutumen nan ba zai taba manta ka idan ya sanka, idan kuma be sanka ba, kai zaka ji cewar wani yana can yana rayuwasa saboda ka taimaka masa da jininsa ko da kuwa siyarwa kai balle kuma ace kyauta ka bada, more especially ace mutumen nan yana cikin yanayi na bukatar jini tsakanin rayuwa da mutuwa...”

Talba yayi shiru yana sauraren kalaman Kabir, sai kuma ya soma tuna abun da ya faru a yau. Juyowa yai ya kalli Kabir.

“Idan mutum ya suma zai dauke ki awa nawa kamin ya dawo hayyacinsa?”

“Is depend on yanayin suman, ko kuma irin kulawar daya samu, but most wadanda tsoro yake saka su suma ko damuwa, ba su cika farkawa da wuri ba kamar wanda rashin lafiya ta saka shi suma, kuma ya danganta da kalar suman da mutum yai”

Shiru Talba yai alamar nazari sannan ya sake tambayar Kabir.

“Amman me ke saka mutum baya kuka da murya sai hawaye, kuma ba ya magana, baya cin abinci baya ma bude bakin”

Kabir ya aje spoon din da yake cin abinci da shi ya dauki ruwa ya sha.

“Depression... Damuwa tana saka wannan har fiye ma, tana saka hauka, rashin lafiya and so on, indai har ba wai mutum ya daman can haka aka haife shi ba, daga baya ne ya sauya gaskiya damuwa ce, tana tsoro tana saka mutum ya rika ganin abu yana imagination ko kuma zuciyarsa ta raya masa ya aikata ko ta saka shi hauka ko ya rika abu kamar mai aljannu, tana saka yawan mantuwa ko surutu ba akan abun da ake magana akai ba, you know komai n jikin dan'adam yana da limit din abun da yake iya dauka, so idan abun yai yawa ko yai kadan zaka tarar akwai irin illar da yake haifarwa”

Silently Talba ya sauke ajiyar zuciya.

“Idan mutum yana son yayi magana da mai irin wannan abu kamar ya tambaye shi wani abu ya zai yi?”

“Ya zai yi kuwa? Most important thing is ka yi kokarin cire wannan mutumen a damuwa, idan wani abu yake so ka sama masa, idan tsoron wani abu yake ka nuna masa babu abun da zai same shi kuma zaka bashi kula, ka sake jikim da shi kana bashi kulawa kana nuna masa far'a da walwala kana dauke masa hankali daga damuwar, kai ta kokarin ganin ka faranta masa rai, da haka da haka zaka ga ta saki jiki da kai, ka yi ta cusa kanka kana bata abinci tun bata ci har ta fara ci”

“Idan kuma ya ki fa?”

“Taki dai... Zata ma ci idan ta ji yunwa, idan ana saka mata maganine a ruwa na abinci ko kuma ana bata ta hanci a daina, as long as zata iya tashi zaune ko ta kwanta bata bukatar irin wannan maganin, a kyaleta ta wuni da yunwa idan ta ji babu komai a cikinta zata karbi abincin idan an bata, da haka zata saba ta rika ci, amman a yanzu ai an hanata jin yunwa ne, kuma ace ana son ta ci abinci?”

“But he cant walk fa”

“That one is different, maybe damuwar ce ta haifar mata da hakan ko kuma wani matsalar dabam, amman rashin lafiyarta ba zai zama da matsala a cin abincin ta ba, indai ba wai tana kan wani magani da aka dorata ba ne, shi ma kuma sai dai ace ba zata ci wani ba wani zata ci”

Talba ya yunkura da zimmar tashi sai Kabir ya kalleshi ya ce.

“Ita ce yarinyar?”

Da ido Talba yai masa alamar question mark, sai ya karansa tambayarsa.

“Yarinyar da kake zargin Leila tana kokarin kashewa?”

Talba be ce masa komai ba ya fara tafiya.

“And do you really think Leila zata iya wannan abun?”

Tsayawa Talba yai ya juyo ya kalli Kabir.

“Amal ta baka labarin Baaba?”

“No amman Momy ta fada mana yan'uwanta sun zo sun dauke ta right?”

“Yes amman dazun nan jikanta ya zo nemanta, so kai tunani akai”

A take Kabir ya cika da tsananin mamaki, Talba kuma ya juya ya fice daga falon. Bangarensa ya nufo kamin a karasa ya cire agogon hannunsa, sannan ya kai hannunsa na hagu ya bude kofar ya shiga, tafiya yake kamar baya son taka kasa ya karasa bathroom dinsa ya jefar da wayarsa saman gado, ya cire tufafin jikinsa ya daura tawul. Samun kansa yai da karasawa gaban katon madubin dake dakin wanda ke nuna iya tsayin mutun. Tsaye yai yana kallon kansa kamin ya kai hannu ya shafa kirjinsa zuwa cikinsa sai kuma ya dawo da hannun saitin inda zanen kirjinsa yake yana tabawa.
Motsin shigowar mutum da yaji ne yasa shi juyowa da sauri domin ya san ba kasafai ake shigowa bangarensa ba, Momy ba tai musu wannan tarbiyar ba, ta shiga dakin juna barkaita sai dai idan da wani dalilin. Takawa ya fara yi kamin ya isa bakin kofar Bathroom din Leila ta shigo, tsaye tai cak tana kallonsa daga kasa zuwa sama, wani irin bugawa zuciyarta tai da karfi a lokacin da idanuwanta sukai arba da faffandan kirjinsa. Tun da take a rayuwarta bata taba ganin Talba babu riga ba sai yau, duk kuwa da kasancewar a gida daya suka tashi sai dai baya bayyana mata siraicinsa kamar yadda ita bata taba nuna masa nata ba sai dai dan abun da ba a rasa ba, kamar saka damammen kaya ko wando da riga, sai dai rika hannunsa ko taba shi ba wani abu ba ne a gurinta kamar yadda shi ma be dauke shi komai ba.

“Ya akai?”

Ya tambaya yana kallonta, ba karamin jihadi tai ba na ganin ta daidaita natsuwarta, sai dai hakan be hana numfashinsa yin nisan kiwo ba na tsawon dakiku, ta dauken kai tana kokarin dawo da numfashin a hankali.

“Yarinyar ta fada maka wanda yai mata haka?”

“Kina da wata maganar ne bayan wannan?”

Juyowa tai ta kalleshi.

“Ita wannan maganar ba mai muhimmanci ba ce?”

“Mai muhimmanci ce a lokacin da ta fada min cewar ke ce ko ba ke ba ce, and kuma idan na gane gaskiyar komai a game da Baaba”

“Duka biyun ban aikata ba, miyasa baka yarda da ni ba? And me zai saka ka zarge ni da kisan yarinyar da kai ma basan san ta ba”

“She can't walk she can't talk, depression yana damunta, and now idan na gano da hannunki a ciki, i swear ba zan raga miki ba, you have no idea what she's going through”

Ta kara matsowa kusa da shi tana kallon idonsa.

“I don't care, she can't talk or walk is not my business, ta mutu ko ta rayu be dame ni ba, ina ta fito ina zata je me ya faru da ita duka ba matsala ta ba ce, all what i care is us....we... I mean us... Just us...”

Yanayin yadda tai maganar ya bayyana bacin ran dake tare da ita, shi ma kallonta yake ido cikin ido yana kokarin hana zuciyarsa tsanarta. Sai da ta gama yawo da idanuwanta a fuskarsa sannan ta juya ta fice daga dakin a fusace. Tana dawowa dakinta ta dauki wayarta ta kira Madina ta san is late amman tana son ta yi magana da ita mai muhimmanci.

“Hello Leila”

Madina ta yi picking.

“Madina fada yadda ake mantawa da mutum”

“Ban gane ba”

“So na ke na manta da Talba, na cire shi a raina gaba daya na manta da shi”

Wani irin murmushi ne ya kawata fuskar Madina, ta yi saurin aje kofin ruwan dake hannunta.

“Amman miyasa?”

“Na gaji ba zan iya ba, sai na nuna masa ni din mai tsada ce kuma na nuna masa he is nothing to me”

“Shikenan zan zo da safe, wannan maganar ba ta waya ba ce”

“Okay ina jiranki”

Leila ta katse wayar, sai Madina ta rike wayar tana kallo, rabuwar masoya ba abu ne mai kyau ko dadi ba, sai dai ita ya zo mata a dabam domin ta samu kanta cikin farincikin jin abun da Leila take kokarin aikatawa.



BATURIYA POV.

Kamar yadda Ramlee tai mata alkawarin kawo mata kayan mata da zata sha a jiya, ta kawo mata su cike kamar wanda zata sara ta kai su wani gurin, ita ma kanta ta yi mamakin tarin hakin mayen da Ramlee ta kawo mata, wanda za a hado da madara ko zuma a sha duka ta siyo mata madarar da zumar, yadda ta ware kudi ta siye mata kayan matan sai ka rantse da Allah yarta ce.
Hakan yasa ta bude wardrobe dinta ta saka su ta rufe da makulli, idan zata sha sai ta bude ta debo ta sha ta rufe, ko Sultan bata yarda ya gani ba balle kuma Faruq uban gayya.

Bayan ta gama gyara gidan yayi tsab ta dora girkinta da wuri, sannan ta shigo falonta ta dauki wayarta ta kunna data ta fara chat. Zata yi reply wani sako kiran Fahat ya shigo wayarta, da sauri tai picking ta kai wayar a kunnenta.

“Hello”

“Yan mata ya kike?”

“Lafiya kalau, sai marmarinka”

“Uhm mmn Marmari kamar gaske, ke da kin ki bari ma na zo mu gaisa, sai kwana kwana kike min”

“Ai na fada maka gidamu ba za a bar ni ba, ba a barin mu zance gaskiya”

“Amman ai kin yi girman da ya kamata ace ana barinki zance Fee'at”

Ta lumshe ido tana jindadin yadda ya kira sunanta, daman haka take so ba kamar yadda Faruq yake kiranta da Rafi'a ta yi complain har ta gaji, sai yace mata shi ba ba ta soyayya yake ba, ta neman kudi yake da abun da zasu ci.

“Ba zaka gane ba ne”

“Na gane, kuma suna da gaskiya, wasu iyayen basa barin yayansu su na kula samari barkatai, amman idan kin amince min zan iya sakawa a zo a nema min izinin magana da ke har mu fahimci juna”

“Da gaske?”

Ta tambaya tana tashi zaune daga kwance da take.

“Wallahi kuwa, Fee'at ni fa da gaske nake aurenki zan yi, ba da wasa na zo ba”

“Uhmm”

“Allah kuwa, Momyna ta dade tana min maganar aure, ansha kai ni gurin yan mata da yan'uwa amman wallahi ban taba jin wanda tai min ba, amman ke ina ganinki na ji wani abu akanki Fee'at you're different...”

Ba karasa maganar da yake ba ta yanke wayar ta kasheta gaba daya sakamakon jin ana kwankwasar gidan. Fitowa tai ta isa gurin kofar ta bude sai tai arba da Faruq yana dauke da Sultan.

“Har kun dawo”

Sai da yai kamar kar ya amsa mata sai kuma ya amsa.

“Eh, Sultan shiga ciki”

Ya karasa yana sauke Sultan dake rike da ledar kifi kasa. Sannan ya juya ya

“Zan tafi shago”

“Allah ya tsare”

Ta fada kamar ba ita ba har sai da ya juyo ya kalleta, rabon da tai masa addu'a har ta manta.

“Ameen”

Ya amsa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ita kuma ta maida kofar ta rufe taja hannun Sultan suka nufi cikin gidan tana tunanin maganar da Fahat yai mata.

‘Amman da gaske yake zai aure ni? Ko kuma dai wasa yake? Amman ai be san na taba aure ba, idan na fada masa gaskiya zai yarda ya auri bazawara?’

Ita kadai take ta haukanta ta saka wannan ta kwance wacan, gaba daya sai hankalinta ya tattara ya koma gurin Fahat tana ta ayyana irin rayuwar da zata yi, kasancewar sa mai kudi kuma dan masu kudin.

“Momy Mama tace a gaishe ki”

Sultan ya fada yana zaunawa ya bude ledar kifin.

“A hanya Dady ya siya min, yace na ci rabi na baki rabi”

Ba ta ma kula, gaba daya hankalinta yana gurin Fahat.

“Amman fa na masa karyar arziki, wata kila yana min kallon yar masu kudin ne”

Sultan ya kalleta.

“Momy waye?”

Sai a lokacin ta lura da a zahiri tai maganar ba a badini ba.

“Ba kowa ba ci kifinka, ga abinci can akan wuta idan yayi zaka ci kaji”

Ya fada mata kai ita kuma ta shiga uwar daka ta dauki wayar ta kunna, sai ga sakon Ramlee ya shigo mata.

‘Ki sha kayan nan da yawa, yace yana son ku hadu da gobe, na kira wayarki ban samu ba, idan kin gama karantawa ki goge sakon’

Dundundun ta ji gabanta yayi duka uku uku, ba dan bata saba haduwa da mazan da ba muharramanta ba, sai dai wata kila saboda wannan haduwar ta daban ce, saboda zata aikata sabo ne alhalin tana da aure da kuma da, ga kuma karamin ciki a jikinta.
Saurin goge sakon tai kamar yadda Ramlee ta bukata, sannan ta mike tsaye ta isa bakin kofar dakinta ta tsaya tana kallon Sultan dake ta aikin cin kifinsa hankali kwance, damuwa ce ta bayyana a fuskarta, duk wani dauki da take na son a bata kudi sai ta ji ya ragu, domin bata taba aikata alfasha ba, sai a wannan karon ne zata gwada. Juyawa tai ta koma cikin dakin tana busar da iskar bakinta.
18

*Khadeeja Candy*


Ko kin san kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin sa kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya domin siye ko sari ku tuntu Ramla incense ta wannan number +234 703 839 2576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

*Dan girman Zatin Allah karki karanta idan baki biya ba. Masu sharing Allah yai muku yadda kuke min! Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

LEILA POV.

Sam bachi ya gagari idonta saboda yunkurin da take a zuciyarta na naki da soyayyar Talba. Sai ta kasa samun hadin kan sassan jikinta ciki har da idanuwanta, da kuma zuciyar datai mata garkuwa da kaunar Talba. Sai yanzu ta gane ashe abun ba shi da sauki, daman taya zai zame mata mai sauki? Ta rayu da kaunarsa na tsawon lokaci a dare daya ta ce zata cireta?
A maimakon ta ji kuzarin cirewar ta karfafawa kanta guiwa, sai ta samu kasala tana jin kamar ba zata iya rayuwa idan babu Talba ba.
  Sai dai tana jin ajinta da martaba da kimarta ta wuce Talba yai mata haka kuma ta cigaba da sonsa ko waye shi kuwa?

“Na girmi wannan... Amman why?”

Ta furta tana jin kamar ba zata samu hadin kan zuciyarta ba.

“Allah karka min jarawa da kaunar mutumen nan”

Ta furta ta saka hanayenta biyu ta share hawayen da suka zubo mata. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin window ta bude window ta tsaya a gurin tana kallon taurarin da suka kawata samaniya.

“Do i deserve this? It's painful...”

Ta fada wasu hawayen na sauko mata, a rayuwarta bata san zafin rashin ba, bata san ta

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment