Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa, yau yau muka zo sai kuma ki dauki min wata maganar aure? Ina laifin ma ki barta ta kwana biyu?”

“Yanzu nake da wannan damar, idan ka saka kafarka ka tafi ba zan sake ganinka ba sai nan da wasu shekaru, wata kila sai na mutu. Ka yi hakuri Allah zai bata wani ai ba kai ne kadai dan'uwanta ba, zata samu miji na gari inshallahu”

Gaba daya sai ya ji kalaman bakinsa sun kare, ya zai yi ya fahimtar da kaka sai ya rasa. Mikewa yai tsaye ya nufi kofar fita cikin yanayin damuwa. Fitowa yai daga cikin gidan gaba daya bakin kofa ya fara tsayawa sai kuma ya fara takawa ya nufi gurin daya aje motarsa, be karasa ba ya juyo yana kalle kallen neman mafita sai ya hango Aminatu zaune gindin wani icen dogon yaro, ta bashi baya. Sai da ya sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya juya ya doshi inda take, ta bayanta ya fara tsayawa jin motsin mutum yasa ta kai hannu ta share hawayenta. Sai ya zagaya gabanta ya zauna kusa da ita a saman dutsen dake gurin, akwai hasken gulub a gurin amman haka be hana shi ciro wayarsa ya kunna fitilar ya haska fuskarta, arba yai da hawayen da take.

“Kuka dai? Bayan na kawo ki gurin Kakarki har kina neman ki fini gata”

Kallonsa tai wasu hawayen na sauko mata.

“Baka san yadda nake ji ba”

“Na sani, ni ma ai na rasa uwa da uba kin tuna?”

“Ka san yadda ake ji idan an rasa uwa, da uba, amman baka san yadda ake ji ba idan an rabaka da su a gabanka, baka san yadda mace take ji ba idan aka ci zafinta.. Shi ma na kasa mantawa... ”

Ta fashe da kuka. Sai jikinsa yai sanyi shi din ba mace ba ne, amman kalmar daya fi tsana ita ce fyade. Shiru yai yana sauraren kukan da take rerawa a hankali can kuma ya dauke kai.

“Shi ma zaki manta nan gaba kadan”

Daga haka yai shiru yana ta kallon wani gurin zuciyarsa kuma tana masa wani iri saboda kukan da Aminatu take, a kokarinsa na dauke mata hankali ya ce.

“Kina son karatu?”

Ta kai hannunta ta sake share hawayen da suka ki tsaya mata.

“Da can, ina so ina da wannan mafarki”

Sai ya kalleta

“Yanzu fa?”

Ta girgiza masa kai alamar babu.

“A yanzu ina tafiya ne a yadda rayuwa ta zaba min na tafi, duka burina da mafarki ya ruguje”

“Idan na miki alkawarin wani abu zaki yarda?”

Ta daga masa kai tana kallonsa still hawaye na sauko mata.

“Na miki alkawarin farinciki, kuma na miki alkawari zan cika miki wannan burin na karatu da duk wani buri naki da be fi karfina ba”

Shiru tai bata ce masa komai ba, a yanzu kam tana ganin kamar cikin burinta ba shi da amfani, Domin an baro kyau ne tun a gurin wanka, ta rasa farincikinta dawowa da shi kuma ba zai yiyu ba.

“Akwai sanyi ki shiga ciki”

Ya fada bayan ya daga kansa yana kallon hadarin dake haduwa a samaniya. Ita ma kallon hadarin tai sannan ta mike tsaye.

“Kaka ta ce idan ka tafi zaka yi shekara baka dawo ba, gobe zaka tafi ko?”

Daga zaunen da yake ya sakar mata murmushi sannan shi ma ya mike tsaye.

“Haka dai take gani, amman fada min kin saba da ni ne, za ki yi marmarina idan na tafi?”

“Me zai saka ba zan yi marmarin mutum mai karamci da sanin darajar dan adam kamar kai ba? Yallabai wani ya taba fada maka kai mutumen kirki ne? Kana daya daga cikin mutanen da suke wahalar samuwaa wannan zamani, mutumen da baya duban dukiyarsa ko kyaunsa ko asalinsa yake nemawa wani musulmi dan'uwansa mafita!”

Wani irin kallonta yake cike da shaukin kalamanta.

“Wani ya taba fada maka zuciyarka mai kyau ce?”

Ya girgiza mata kai alamar aa.

“Ban taba haduwa da wani mutum mai karamci da mutumci da sanin darajar dan'adam kamar kai ba”

Yayi murmushi yana sanda kansa kasa.

“Da ace ko wane namiji zai zama kamar kai, da rayuwar mutane da yawa ta inganta, baki yayi kadan ya gode maka, ina fatar Allah ya tsare gabanka da bayanka ya shiga gaba a lamarinka ya zama gatanka ya haska lamurranka”

“Ameen”

Ya amsa yana mata wani irin kallo da shi kansa be san na minene ba, tun da yake a rayuwarsa ba a taba tsaya a gabansa a yabe shi kamar yadda Aminatu tai masa ba.

“Allah ya tsare hanya”

Ta fada tana jin babu dadi, dan zaman da tai da shi sai ta ji kamar ta saba da shi, ji take kamar kar ya tafi ya barta. A nan shi ma kasa amsawa yai sai ya bita da kallo har ta isa bakin kofar gidan ta shige ciki.

“Oopss”

Ya furta tare da busar da iskar bakinsa, sannan ya zauna baki dutsen. Ma'adanar lambobi ya shiga neman number Ali sai ga kiran Daddy ya shigo wayarsa. Da sallama ya amsa yana mikewa tsaye ya nufi gurin motarsa.

“Ranka ya dade idan zaka kwana a can ai sai ka fada mana, da zaka tafi ma baka fada mana ba, kuma ka san yadda hanyoyin nan suke”

Talba yayi murmushi yana shafa kansa.

“Ayi hakuri Daddy, ni ma ban dauka zan kwana ba, sai dai ganin na dade ban zo ba yasa na ce bari na kwana saboda Kaka”

“Hakan na da kyau amman a rika addu'a, Allah ya tsare, tana kusa da kai ka bata wayar mu gaisa?”

Sai da ya kalli kofar gidan sannan ya amsawa Daddy.

“Aa ina tunanin ta yi bachi”

“To a gaishe ta pls”

“Inshallah thank you”

Ya sauke wayar, sai kuma ya sake maida ita kunnensa bayan ya aikawa Ali kira.

“Hello”

Ali ya daga sai ya ji muryar yaransa a kusa da shi, da alama yana gida tare da iyalansa.

“Kana gida ne?”

“Yes gwaro kana da magana ne?”

“Yeah”

“Okay Ina jinka”

Ya fada yana tashi ya fita daga falon, sai da Talba ya daina jin hayaniyar yaran sannan ya biro masa da abun da ya faru tsakaninsa har zuwa abun da Kaka tai masa. Ba karamin mamaki Ali yai ba jin cewar Aminatu da Talba yan'uwan juna ne.

“I'm happy for her yanzu ta huta da rabe rabe”

“Seriously? Bayan kana ta hanani?”

“No bana son kana samun matsala da Leila ne, kuma ya zama ni ne sanadi, ba zan jidadi ba, kuma duk wani abu da zai taba mutuncinka ya zubar da kimar ka bana sonsa ka sani”

“Yanzu miye abun yi ina cikin matsala Wallahi”

“Kana da wata mafitar data wuce ka amince ka auri yarinyar ne?”

“Wasa dai kake, na yi yaya da mata biyu”

“Can da kai yi niyar aurenta ya zaka yi da ita?”

“Wannan ai dabam ne, daman zai aureta ne saboda gudun abun da zai je ya dawo, kuma ni ada niyata idan ta samu wanda take so zan rabu da ita ta aure shi, daga baya kuma tunanin kawota gurin kaka ya zo min ashe wani sabon fitina ce zata bullo min, kuma ka san ban isa na ce zan yi auren sirri na munafucin Kaka ba, idan na yi haka zai zama akwai zalinci a ciki”

“Ka lallabata idan ta fahimta shikenan idan kuma bata fahimta ba, kawai a auri yarinyar nan Talba, tsakani da Allah kai kanka kana bukatar aure, kuma ga Leila bata shirya ba a yanzu, kuma kai da Leila kun kasa fahimtar juna, dazun ma ta zo nan tana bincikar gurin da ka kai yarinyar, abun nan fa ya dame ta, tana son ka kai da ita girman kai ya hana ku fahimta, amman yanzu na fi yarda kana son yarinyar nan fiye da Leila”

“Ali baka da hankali, miya kawo maganar nan?”

“Haba Talba ka damu da damuwarta, ka dauke ta ka kaita gidanku har ka yi fada da Leila a kanta, sannan ka kaita gidanka yanzu kuma ka kaita gurin kakarta domin kawai ka sama mata mafita, zaka iya yi ma Leila haka?”

“Me zai hana indai har zata shiga a halin da yarinyar nan ta shiga?”

“Bari na fada maka gaskiya Talba, idan ka auri yarinyar ba zan jidadi ba, saboda zaku samu matsala da Momy da kuma Leila, kara ma Daddy na san yana son abun da kake so, kuma yana da saukin fahimta zai maka uzuri. Abu na biyu wanda nake ganin shi ne mafita a gareka shi ne auren yarinyar nan, saboda ka farantawa Kaka rai, kuma ina da tabbacin yarinyar nan zata samu kulawa yadda ya kamata, saboda ka san halin da take ciki ba zaka yarda ta shiga wani hali ba, tsakani da Allah yarinyar nan ta shiga damuwa da yawa a yanzu farinciki kawai take bukata idan kasan zaka aurenta ta zo ta samu matsala karka yi”

Talba ya sauke ajiyar zuciya.

“Tsofun nan rigima ce da su Wallahi”

“Wata kila kuma lokacin auren ne yai, ka san komai yana da lokaci, ni yanzu ai ba za shiga tsakaninka da yar'uwarka ba, duk dai bana son a shiga hakkin Leila, ka fara fahimtar da ita idan ta ki sai ka yi magana da Daddy ka ji abun da zai ce, idan ya amince shikenan idan kuma ya nuna akwai matsala sai mu sake neman wata mafitar”

Talba ya sauke ajiyar zuciya.

“Ban dauka abun nan zai zame min haka ba, and ni dai ba sonta nake ba, ita ma bana jin tana so na”

“Karka damu da sai ta soka, kai ma kuma na san kana sonta, ka kai level din da ya kamata ace ka aje yaya Talba”

“Let me talk to Daddy first”

“Okay, Allah ya zaba maka abun da yafi alheri, kai ta addu'a”

“Abu kamar a film”

Ali yayi dariya.

“Haka Allah yake ikonsa, kaga zak taimaki yarinyar ta samu rayuwa mai kyau”

“Ko ban aureta ba, na mata alkawarin rayuwa mai kyau, zan yi duk abun da zan iya na ganin na faranta mata rai”

“Yanzu dai zabi ya rage naka”

Be sake cewa komai ba ya kashe wayar ya rumgume hannayensa yana tunanin kalaman da Ali yai masa. Ba zai ce yana son Aminatu ba, haka ma ba zai sheidi tsanarta a zuciyarsa ba, tausayinta ya bi jini da jikinsa ya tsaya masa a rai. And of course idan ya aureta ba zai cutar da ita ba, amman ya zata ji? Aurensa ma wani sabon kalubale ne a gurinta.

“Kaka...”

Ya furta yana runtse ido, cike da rashin samun mafita.

AMINATU POV.

Tana baro gurin sai ta tsaya a zauren gidan ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba, wata kila saboda Talba zai tafi gobe ya barta ne, gashi kuma Kaka tace idan ya tafi sai ya shekara yake dawowa. Dukewa tai a gurin ta dafa kasa tana ta kuka sai bakincikin ya dawo mata sabo. Sai da tai kukanta mai isarta sannan ta share hawayenta ta shiga cikin gidan, kanta a kasa tana ta boye fuska har ta shiga dakin Kaka. Tun daga yanayin sallamarta da tai da muryar kuka Kaka ta gane kuka tai.

“Wa'alaikissalam Auta”

Yanayin yadda Kaka ta kirata sai ta ji kamar Inna ce ta kirata, kallonta tai sannan ta karasa kusa da ita ta zauna.

“Kin ci abinci?”

“Bana son komai, Tsohuwa na kwanta a jikin dan Allah”

“Kwanta auta”

Kaka ta fada cike da tausayi, sai ta kwanta a gurin ta dora kanta a cinyar kaka ta lumshe ido kamar mai bachi.



BATURIYA POV.

“Wai yanzu can ba a bar masa Sultan?”

Babban Yayansu ya tambaya, sai Umma tai karaf ta ce.

“To me zamu yi masa? Daman idan aka saki mace ai uba ne yake rika yayansa, ni Wallahi bana son ma rika yayan Faruq”

“Aa Umma kar a zafafa, dan'uwa ne fa, kuma abun da ya faru baki san mai gaskiya a tsakaninsu ba, tun da shi dai be fadi laifinta ba yace ki minene zamu gani, ita ce kawai ta fadi na shi”

“Ita ma dai ai ba zata masa karya ba, bayan duk hakurin da tai da shi, ga talauci”

“Allah ya sauwake, wannan ai na Allah ne, ba ku san arzikin da Allah zai masa ba nan gaba”

Duk maganar da ake Baturiya bata saka bakinta ba, har sai wayarta tai ringing sannan ya mike tsaye tana fadin.

“Ranar Monday zan je asibiti Umma”

“Allah ya kaimu, idan an rubuto magani sai mu kai masa ya siya”

“A kawo dai na siya”

Ya fada yana kallon wayar dake hannunta, sai dai be ce komai ba har sai da ta shiga ciki.

“Waya siya mata wannan wayar?”

“Tace adashe tai”

“Wanda ke fama da talauchi ina zai samu kudin yin adashe? Idan har zata samu yin adashe a gidansa to karya take masa kenan na cewa yana barinta da yunwa!”

“Dan Allah ka daina ma wannan maganar, mace ai tana da hikima kuma talauchi ba ita kadai ta fada ba, jikinta ma ai ya nuna haka, ko zuwa yai gidan nan haka zai fita sisin kwabo ba zai ba ni ba, rabon da yai min alheri har na manta”

Mikewa yai tsaye yana sauke ajiyar zuciya.

“Allah ya sauwake, ni zan tafi idan an rubuta maganin sai a aika min da takardar”

“Toh Allah ya maka albarka, ya kara rufa asiri”

Sai da ya amsa da amin sannan ya gyara babbar rigarsa ya fice daga falon yana yi ma Umma sallama.
Mai da kofar dakin tai ta kulle sannan tai picking.

“Yan mata...”

A take ta ji gabanta ya fadi, domin muryar babban mutum ta ji ba saurayi ba, gashi bata san ta bawa wani number ta ba.

“Wake magana?”

“Nine dai da ake ta yi ma rowa bayan a lasa min zuma”

Murmushi tai domin ta gane mai maganar.

“Aa waya isa? Sai idan baka bukaci ganina ba”

“Aa wacan karon ma ni kadai na san wahalar dana sha kamin na samu ki amince min, yanzu kuma kin fara guduna, Ramlee tace wani saurayi ne yake dauke miki hankali, shiyasa na ce ta turo min number ki na yi rokon iri, ko za a laba ni na sha miya”

Ta yi wata shu'umar dariya.

“Alhajina kenan, ko dai a laba wasu su sha miya ba, kai ai ka wuce nan”

“Anya dai, gani sai bibiya nake, ko maganar zuwa chine da na miki, ba ki ce min komai ba, ko da yake haduwar ma ta yi wuya balle zuwa wata kasar”

Ta sake yin dariya sai dai wannan karon bata ce komai ba.

“Yanzu dai a fada min yaushe za a sake labani?”

“Fitar ce tana min wuya yanzu, amman dai ranar Monday za mu hadu”

“Zan iya jira har Monday? Na zaku fa”

“Haka nan dai zaka yi hakuri har Allah a kai mu, sauran kwana hudu ai”

“To ya na iya tun da abun ya zama na manya, ina saurarenki Gimbiyata”

“To yayi Alhajina zan maka shiri na musamman kuwa”

Dukansu dariya suka yi sannan ya kashe wayar, ita kuma ta zauna bakin gado tana nazari, kamin ta kai hannunta ta saka cikin riga ta fara shafa cikin tana jin tausayin cirewar da zata yi, wata zuciyar na raya mata karta aikata, a yayinda dayar take ayyana mata rashin mafita a al'amurranta matukar bata yarda da zubar da cikin ba.

‘Idan na zubar shikenan na gama idda, zan samu damar auren Fahat, amman kuma zai yarda ya aure ni as bazawara? Idan kuma na boye dole a gaskiya zata fito za a ji’

Haka dai take ta sake sakenta, ta kulla wannan ta kwance wacan. Sam zuciyarta bata kawo mata Sultan kusa balle har tai tunanin a wane hali yake ciki a yanzu, gaba daya ta shagaltu da soyayyar Fahat.

“Wallahi da na san zan hadu da shi, da ban auri Faruq ba”

Mikewa tai tsaye tana jin wani kalar bakinciki ina ma ace ita din budurwa ce ba bazawara ba, da yanzu burinta ya cika.
33

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

A dakin Kaka Aminatu ta kwana, kaka na kan katifa ita kuma tana kan gado, asubar fari ta farka ita da kaka sukai sallah. Kaka na jan carbi ita kuma tana azakar din data manta when last ta yi saboda rashin kwanciyar hankali da natsuwa. Bayan ta gama ta daga hannayenta ta mikawa Allah bukatar ta kuka kai kukanta.

“Tsohuwa ina kwana?”

Sai Kaka ta amsa masa da murmushi a fuskarta.

“Lafiya kalau Auta, an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

“Maa Shaa Allah, fatar dai idan kika yi sallah kina yi ma iyayenki addu'a domin mamaci babu abun da yake bukata kamar addu'a”

“Ina yi tsohuwa ina yi sosai”

“Toh Allah yai miki albarka, ya baki miki na gari”

“Amin ya rabb”

Ta amsa tana yin kasa da kanta, ba laifi tana jin sakewa a gurin tsohuwa fiye da ko'ina wata kila saboda tana jininta ne ko kuma saboda ta santa ne, ko kuma dai dan bata da kyara ne amman Madina ma ai bata da kyara sai da bata jin sakewa a can, duk kuwa da kasancewar kwananta daya a nan.
Misalin Bakwai na safe aka shigo da kunu da kosai. Kaka da kanta ta dauki karamin kofi ta zubawa Aminatu nata sannan ta dauko mata sugar dake cikin wani bowl mai murfi.

“Ki saka wanda ya isheki, anjima zaka kawo dumame sai ki ci, idan kuma indomie kike so ko kwai akwai a dakin ajiya sai a dafa miki”

“Aa wannan ma ya isa”

Ta fada tana jin marmarin kunun a ranta, rabon da tasha kunu tun lokacin da tashin hankali ya fara samunsu, daman mutumen kauye ba ka raba shi da kunu ko fura ba. Sosai ta zuba surgan ta motsa da karamin ludayin da Kaka ta saka mata sannan taja kunun gabanta ta fara ci tana cin kosan.
Kaka ta janyo radio ta kamo bbc sannan ta aje radio kusa da ita ta cigaba da jan carbin.

“Assalamu Alaikum”

Talba ya shigo da sallamarsa, sai Aminatu ta dago ta sauri ta kalleshi tana shan kunu, Kaka ma juyowa tai ta kalleshi sai ta dauke kai ba tare da ta amsa ba.

“Wa'alaikassalam”

Aminatu ta amsa masa, sai ya zauna kusa da ita can Center carpet din da take zaune yana sakar mata murmushi. Kallonsa kawai take cike da shauki tana jin kamar tace masa kar ya tafi, daman jiya da tunanin tafiyar ta kwana a ranta, kasa dauke mata ido yai har sai da ita ta kawar da nata idon tana sannan shi ma ya dauke nasa yana kallon Kaka zai mika mata gaisuwa a yayinda ita kuma ta dago zata mika masa nata gaisuwar.

“Ina kwana” “Ina kwana”

Sun fada a tare, shi yana kokarin gaishe da Kaka ita kuma tana mika masa nata gaisuwar, sai suka kalli juna ita da shi murmushi ya biyo baya, wanda ya karawa kowanensu kyau da haiba.

“Lafiya Kalau an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

Ta amsa sannan tai kasa da kanta, shi kuma ya juya ya saka gaishe da kaka, kamar dazun yanzun ma bata amsa masa ba sai ta daga masa alamar amsawa. Murmushi yai ya kalli kunun da Aminatu take sha.

“Kaka ni ba za a bani kunun ba? Saboda ni ba dan gida ba ne ko kuma me?”

Kaka ta yi kamar bata ji shi sai jan charbinta take. Aminatu ta mikawa Talba nata.

“Ka sha wannan”

Ya mika hannu ya karba ba dan yana son sha ba, kusan zai iya cewa be taba shan kunu ba a rayuwarsa idan ma ta taba to ya manta, tashinsa Momy ta saba masa da tea ba kunu. Babu kyama ya kai kofin bakinsa ya kurba, sai yai saurin runtse ido, ba dan dadi ko rashin dadin kunun ba, sugar da Aminatu ta zuba ne ya ji shi har cikin kansa, saboda be saba shan suga da yawa ba, wani lokacin ma ya kan iya jika Lipton kawai ya sha ba tare da suga ba, idan ma zai saka sugar baya wuce one or two to three cube.

“Shalele haka kike shan zaki ko Kaka ce take son bata ki?”

“Ni na zuba”

Daukar kunun yai ya kara a cup din ya motsa sai zakin sugar ya ragu, sai dai hakan be hana shi jinsa har cikin kansa ba, haka dai ya daure yana shan kunun idan yayi ludayi daya sai ya mika mata ta sha daya a haka har suka shanye kunun.

“Idan baki koshi ba ki kara ki cika cikinki, sai ki kwanta kamin a kawo dumame”

Kaka ta fada tana janyo kwanon da take ajiyar goro ta bude ta balla kadan ta saka a baki tana taunawa.

“Na koshi”

Aminatu ta fada tana lashe baki.

“Kaka ni ban koshi ba”

Talba ya fada yana kallonta, sai tai masa banza kamar ma bata san da zamansa a gurin ba. Murmushi yai ya tashi ya kuma kusa da ita ya zauna ya kai hannunsa ya dafa ta.

“Haba Uwargida kin taba ganin matar dake son aljanna kuma tana fushi da mijinta”

“Kai Mu'azu babu wani abun da zaka min ka wanke kanka, kar nake kallonka, kuma ka gwada min yan'uwan ubanka sun fi na uwarka, ba zan manta da wannan ba, ka nuna wasu dangin sun fi wasu”

Saurin dauke hannunsa yai yana jin wani irin, har ga Allah ba manufarsa kenan ba, amman kaka ta kasa fahimtarsa. Kallon Aminatu yai.

“Shalele zaki iya zuwa waje? Zamu yi magana da Kaka”

“Toh”

Ta amsa tana kokarin tashi sai Kaka tai karaf ta ce.

“Babu inda zata je, ni ce uwarta ni ce ubanta a yanzu, bata da wasu dangin sai ni, idan zaka yi maganar kai a gabanta ko kuma ka je can gurin naka dangin kai magana ai kai kana da gata”

“Haba Kaka wannan wace irin magana ce kuma?”

Ta furta cikin rashin jindadi, sannan ya mike tsaye ya ciro kudin dake aljihunsa ya aje masa a gabanta.

“Gashi nan a ci goro ni zan kama hanya, kuma zan aiko mota a daukeki saboda ciwon kafafuwan a kai ki asibiti”

“Ai daman idan ka zo garin nan kamar ana tsikararka kake, shiyasa kowa baka sani ba na dangin uwarka, idan ka zo baka san kaje ko'ina ba, idan kuma ka tafi sai an sake ganinka. Ka dauki kudinka sisin kabo bana so naka Mu'azu, ai baka gan ni a wahala ba, komai bana so naka, kuma karka sake takowa garin nan da sunan zuwa ganina na yafe maka har na mutu”

Sai a yanzu ya tabbatar da gaske kaka take, domin babu alamar wasa a fuskarta sai ma fushin dake kara bayyana a maganarta. Kallon Aminatu yai wanda ita ma kallonsa take tana mamakin yadda Kaka take masa magana da fushi, be ce komai ba ya dauke kai ya fice daga dakin cikin rashin jindadi.

“Auta dauki kudin nan ki kai masa”

Kaka ta fada tana nuna mata kudi, kamar marar kuzari haka Aminatu ta isa gurin kudin ta dauka ta fito daga dakin tana jin kamar ta tambayi kaka dalilinta na kin karbar kudin.
Ko da ta fito waje yana zaune cikin motarsa ya bar kofar a bude yana kallon kofar gidan kamar ya san zata fito, tafiya take kamar wata hawainiya har ta isa gurin motar ta ja ta tsaya, ya dade yana kallonta ita kuma ta kasa daga ido ta kalleshi saboda kukan dake son zuwa mata.

“Shalele ya akai?”

Ta mika masa kudin da hannu biyu. Sai yai murmushi.

“Kin ga na kawo ki nan amman kin fini fada, saboda ke Kaka take fushi da ni”

“Ko dai tana jin an dora mata lalura ne?”

Ta tambaya hawaye na cika idonta.

“Aa wani abun ne dabam”

Ta hade yawun bakinta.

“Zan koma Gusau”

Bata ce masa komai ba, kuma ta kasa daga idon ta kalleshi.

“Ba zaki ce min Allah ya tsare ba?”

Ya furta yana kallon yadda yanayinta ya sauya, shi kansa yana jin kamar kar ya tafi ya barta. Sai a lokacin ta kalleshi hawaye a sauko mata.

“Da gaske idan ka tafi sai bayan shekara zaka dawo?”

Ido ya kura mata sannan ya fito cikin motar ya tsaya a gabanta still yana kallonta.

“Ba ki son na tafi?”

Samun kanta tai da daga masa kai.

“Kina son na dawo?”

Nan ma kan ta daga masa.

“Zan dawo”

“Yaushe?”

Ta tambaya cike da shauki da kuma zakuwar ta ji yace mata gobe ko jibi.

“Yaushe?”

Ta sake tambaya.

“Ba da dadewa ba”

“Yaushe?”

Ya shafa kansa zuwa hancinsa.

“Cikin satin nan”

“Ya za'ayi na yarda zaka dawo”

“Saboda nace zan dawo, idan na ce zan yi abu, zan yi”

Ta dauki idonta hawaye na sauko mata sosai, sai take jin kamar shi ma din idan ya tafi ba zai dawo ba. Ya kara matsowa kusa da ita cike da tausayinta.

“Kina son na zauna ne?”

Ta daga masa kai sai

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment