Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mahaifiyarta Hajiya Yana.

“Hajiya ni fa ba kamar ke bace, ni kam kaza ce mai son yayanta, ba zan iya yi ma yayana abun da kike mana ba, na nuna mana kin fi son yayan yan'uwa fiye da mu, yanzu fa zamani ya canja, Wallahi kowa kansa ya sani”

“Allah ya wadaran wannan canji na zamani Amina, mu kam a da ko dan makoci dan ka ne balle kuma dan dan'uwa na kusa da nesa”

“Hajiya ai ni ban hada jini da Talba ba”

“Ban ga ta inda Talba ya babanta ki da mahaifiyarsa ba, bibiyar da yake miki ko Kabiru da kika haifa be fishi yi miki bibiyaya ba”

“Babu wannan damar ne ai, da ace zai samu hanyar nuna min zai yi, ai ruwa be taba zama jini ba”

Hajiya Yana ta girgiza kai.

“Na yi tunanin sakin nan da Alhaji yai miki zai saka ki natsu ki gane kuskurenki domin yayi abun da ya dace, ya nuna miki jini ba abun wasa ba ne, ke kam dai halinki ya fita dabam dana yan'uwanki, ba ki dauko ni ba kuma baki biyo halin mahaifinki ba, sam wannan ba rayuwa bace”

Mikewa tai tsaye tana dariya.

“Hajiya idan kina min wani abun kamar ba ke kika haife ni ba, ni saki be tashi hankalina ba, amman ya saka na kara nazari da tunani da kuma fahimtar abubuwa, ina mai tabbatar miki sai Engineer yayi nadama sai ya zo da kansa yana neman afuwa yana kuka da hawayensa, abun da be min a kurciya ba yanzu zai min shi da tsufana? Da yaya? Ai duk wanda ya zama silar mutuwar aurenka a gidan mijinka da kake kauna kuma da yayanka manya ba kakana ba, ba masoyinka ba ne Hajiya...Hmmm”

Ta karasa tana kashe ido daya, sannan ta kai hannu ta dauki wayarta tare da plate din data gama cin abincin ta nufi bedroom, Hajiya Yana binta tai da kallo tana mamaki yadda zamani ya lalace har zaka fifita danka akan son zuciya, domin a iya abun da ta fada mata bata hango Talba ko Daddy da wata matsala ba, duk abun da ya faru ita ta janyo komai, ba tun yau ba halin Amina ya fita dabam a cikin yayanta.

“Allah ya kyauta ya shirya ki”

Addu'ar da Hajiya Yana tai kenan ta cigaba da jan carbinta, tana gama tasbihin jikanta Kabir ya turo kofar falon ya shigo, juyows tai ta bishi da kallo har ya zauna, bata ce masa uffan ba domin ta lura yana cikin yanayi na bacin rai, domin ba haka ya saba shigo mata ba. Idan zai shigo ya kan yi sallama kuma ya shigo yana wasa da ita tsabanin yau da ya shigo kamar wanda akai wa dole.

“Hajiya Yana Ina Momy?”

“Bacin ran da ubanku ya saka muku shi ne zaka zo ka sauke a kaina?”

Ya kalleta sai kuma ya hade yawu yana ta kokarin danne bacin ransa.

“Hajiya ki yi hakuri, ina Momy?”

Da hannu tai masa nuna da kofar dakin, har ya mike tsaye sai ta kira shi.

“Kabiru... Zauna”

Bayan ya juyo tai masa umarnin zama, sai ya koma ya zauna.

“Karka dorawa mahaifinka laifi, karka kuskura ka biyewa mahaifiyarka abun da tai da kai da ita Leila duk ba ku kyauta ba, hakan da kuka yi kun nunawa Talba rashin gata ne da galihu, domin na tabbatar idan kai ne Amina ba zata maka haka ba”

“Son da Daddy yake yi ma Talba yayi yawa Hajiya, ni ma sai yanzu na lura da haka, kuma da Talba ya dauki Momy a matsayin uwa ba zai tana yarda ta kawo yanzu a gidan nan ba, duk yadda zai yi ya saka Daddy ya maidata gidanta zai yi, saboda Daddy yana jin maganarsa kuma yana gudun bacin ransa, amman be yi komai ba, saboda ba mahaifiyarsa ba ce”

“Aa Kabiru kar fushi ya rufd maka ido, ka rika ganin daya a matsayin biyu, baka san abun da yake kasa ba, kuma ka san halin Mahaifinka sani murdanden mutum ne, ba lallai ne wani ya iya saka shi abun da be tashi ba, yanzu kuma Amina ta gama waya da Talba”

Kabir ya mike tsaye.

“Ke ma kina goyon bayansa kenan? Akan mahaifiyata bana ganin kowa da gashi Hajiya, ya sha saka ta kuka saboda Silly abu Daddy zai rufeta da fada har sai ta yi kuka ranta ya bace, amman yanzu mai gaba daya Daddy yai, be dubi ni ko Leila ko Amal ba, abun da be yi da kurciya zai aikata da tsufa saboda Talba? Ya duniya zata kallemu da girmanmu ace iyayenmu sun rabu”

Hajiya ta nuna shi da yatsa.

“Kabiru me mahaifiyarka ta fada maka? Ka zurfafa abun nan”

“Babu zancen zurfafawa Hajiya, ina fada miki gaskiya ne, har yanzu Talba ne kira ya min magana ba, kuma be saka kafarsa ya shigo gidan nan ba, that's mean ya jidadin abun da Daddy yai kenan? Yanzu na fahimci dalilinsa na kin nunuwa Leila kulawa wato baya son ta kuma ba zai iya cewa baya son ta ba, ai ya san kulawa tun da gashi nan yana nunawa yarinyar, and now da Leila ta kamu da kaunarsa ta saka a zuciyarta shi ne yake kokarin broken heart dinta and i won't let that happen, i will teach him a lesson”

Yana fadar haka ya nufi dakin da Hajiya Yana ta nuna masa sai wani cika yake fushinsa yana kara hauhawa.

TALBA POV.

Kallonta yake yana ta tunanin ta inda zai fara mata bayanin, zata fahimta? No wait ya ma dace yai haka? Amman idan be yi ba yana da wata mafitar ne? Idan yace zai kaita wani gurin zata zauna? Zata jidadin rayuwa? Idan kuma ya zauna da ita anya zai iya rike ba tare da shiga hurumin da Allah ya haramta masa ba?
Ta dan sakar masa murmushi ganin kallon yayi yawa har ta soma tsarguwa, sai shi ma yai murmushi yana cigaba da kallonta.

“Kin san me?”

Ta girgiza kai alamar aa.

“Ina ganin kamar muna da mafita daya ni da ke? Ita kadai ta rage mana”

Kamar ya san ba zata tambaye shi minene mafitar ba, sai ta ya cigaba da maganar yana kallon cikin idonta.

“Idan muka zauna a haka zamu iya sabawa Allah, ba ina nufin mu aikata wani abu ba, no zan iya kula da kaina, amman rika hannunki taba jikinki ko taimaka miki da yin wani abu da zai saka na kai hannu a jikinki, idan kuwa har zamu zauna a gida daya a tare dole ne sai hakan ta faru, tsakani da Allah ban saba mu'amala da mata ba, taba mace kallonta ba halina ba ne, and duk abun da zan yi ina kokarin ganin ban shiga hurumin da ya haramta a gareni ba, ina kokari sosai wajen ganin n tsare mutuncina da na iyayena da yan'uwana, idan babu yan'uwa da iyaye kuma akwai Ubangijina, ban ce na fi karfin sheidan ba amman duk inda mace da namiji suka kebe na ukunsu sheida ne, haka ne?”

Ta daga masa kai, sai ya zauna gefenta yana kallon gefen fuskarta a yayinda take kallon kofar bedroom din.

“So ina son na yi wannan shawarar kuma na yanke wannan hukuncin akan yardarki da amincewarki, bana son na cilasta ki ko kadan bana son ranki ya bace akan komai, bana son ki cilasta zuciyarki ta karbi abun da baki bukatarsa a yanzu, ni kaina idan nace miki ina bukata na yi karya, domin zan jefa rayuwata a hadari ne da kuma na matar da zan aura Leila, kuma zamu yi wannan abun ne a bisa sharadi”

Ta juyo ta kalleshi.

“Minene?”

“Shalele...”

Sai kuma yai shiru yana tunanin dacewa da rashin dacewar aikata hakan, ita kanta ya zata kalli abun?

“Ina son mu yi aure ni da ke....”

Duk wani abu dake motsi a jikinta sai ya tsaya cak na tsawon dakika uku.

“Aure...”

Ta maimaita a raunane tana kallon wani gefen.

“Yes... Aure ba saboda ina son ki ba, ba saboda kina so na ba, kuma ba saboda mun dace da juna ba, zamu yi wannan abun ne a karkashin sharadi guda daya”

Ta sake kallonsa sai dai wannan karon hawaye har ya fara sauko mata.

“Zan aure ki ne saboda gudun aikata abubuwan dana fada miki a dazu, amman Wallahi ba dan ina son ki ba, sai dan ina tausayinki, kuma saboda hakan zai zame mana mafita ni da ke, domin na san ke ma ba sona kike ba! Amman na miki alkwari ni Talba zan sakeke da zarar rayuwarki ta inganta, ma'ana kin gane yan'uwanki ko kuma kin samu wanda zai aure ki, kuma wannan auren zai kasance ne kawai a tsakaninmu, babu wanda zai san da wannan sirrin har mu rabu”

Dauke kai tai tana jin abun wani iri, an taba aure ba yan'uwa ba kowa? Daga ita sai shi?

“Zamu yi ne saboda tsare mutunci da gudun fushin Allah, kuma na rantse miki da Allah zan sake ki a duk lokacin da dayan biyun nan ya faru! Ko dai kin gane wasu daga danginki ko kuma kin samu wanda ke sonki tsakani da Allah zai aureki, karki damu da tunanin babu yan'uwa ko naki, zamu yi wannan auren ne saboda ke, domin ni ina da wanda zan aura, kuma mu yi wannan abun ne a rubuce kuma akan yarjejeniyar saboda ki samu natsuwa”

Ya fada kamar ya san abun da ke ranta. Da gaske aurenta zai yi saboda abun ya fada ko kuma dai saboda wani dalilin ne na dabam?

“Momy...”

“Karki damu da ita, ba zata taba sani ba na miki alkawari”

“Leila...”

“Taya zan barta ta sani bayan kuma ita zan aura? Ya kike ganin zata kalli abun? Wannan abun zai zama sirrine a tsakaninmu”

Ta girgiza masa kai.

“Ba zan iya ba”

Ya cikama bakinsa iska ya busar kana ya kai hannu ya shafa kansa.

“Daman bana son cilas ta ki, yanzu dole mu nemo wata mafitar ta dabam, zan memo miki wani gurin da zaki zauna tare da wasu mutanen, amman kamin na samu wannan dole ki zauna a nan kamin mu samu wata mafitar”

Sai ta rumtse ido wasu zafafan hawaye na sauko mata.

“Inna ta yi gaskiya, ta fada min zan yi kuka a gaba, sabowa da wata rayuwar ba abu ne mai sauki ba, fuskantar kalubale bayan wani kalubalen abu mai wahalar gaske, ina a tsakankanin rayuwa da mutuwa, farinciki da sabo sun min nesa, samun sukunin na zuciya da ruhi ya min tsada”

Har ya kai hannu ya kama hannunta, sai kuma ya maida hannun a cikin dayan hannunsa ya rike.

“Miyasa ba zaki yarda da kaddara ki karbi duk abun da ya zo miki da hannu biyu? Wata kila idan kika bi rayuwar a yadda ta zo miki sai ki samu sukuni da walwala a gaba?”

Ta bude idanuwanta da suka soma yin ja ta kalleshi.

“Kana ta karfafa guiwa a inda babu karfi, taya kake ganin komai zai zo min da sauki? Na rasa uwa a gaban idona suka kashe mahaifina, aka kashe yan'uwana a dare daya na rasa komai, a tsakanin wadancan ranaku da na yau na rasa wacece ni, ina jin zafin abun a raina ina jin kamar zuciyata zata fasa kirjina ta fito babu abun da yake da sauki a gareni...”

Ta karasa tana ta shesshekar kuka jikinta na rawa, hawaye na sauko mata kamar an yi su ne kawai saboda wannan ranar. Gaba daya jikinsa yayi sanyi sai tausayinta ya kara kama shi, ba tare da ya so ba ya kai hannunsa ya kama hannunta ya jimke sosai, sai kawai ta kara fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya.

“Za ki iya yarda da ni?”

Ta daga masa kai tana kuka.

“Na miki alkawarin zan dawo miki da farinciki a rayuwarki, ban ce zan dawo da iyayenki da yan'uwanki ba, amman da yardar Allah sai na samo miki wadanda za su maye miki gurbinsu? Zan dawo miki da farincikin da kika rasa Amina i promise you this! Kin yarda da ni?”

Ta sake daga masa kai, sai ya sauke numfashi a hankali yana jin kamar ya rikata ya saka ta a kirjinsa ya rarrasheta. A hankali ya zare hannunsa ya mike tsaye yana nuna mata gadon.

“Kwanta”

Ta kalleshi daker tana kokarin tsayar da kukan da take.

“Ta.... Tafiya... Zaka yi....”

Kamar ya ce mata eh sai kuma wata zuciyarta ta hana shi, wata kila idan ya amsa mata da eh zata iya cewa ba zata zauna ba, idan kuma ya ce mata aa ta kwanta ta tashi bata tararda shi ba zata dauke shi makaryaci. Be ce mata komai ba ya nufi inda bargon yake aje gefen gado ya dauka ya rike.

“Kwanta, ki samu bachi”

Ta hau saman gadon gaba daya ta kwanta sai ya dauki filo ya mika mata ta karba ya rumgume, sannan ya lullube ta. Baka jin komai a dakin sai saukar numfashinta da karfi, gefen gadon ya samu ya zauna yana kallonta, zaman da yai sai ta ji natsuwa har ma ta samu damar lumshe idonta, ta kai hannunta a baki tana cizawa a hankali. Kallonta yake for so many reasons, na farko rayuwarta yake hangowa, da kuma tasa ta ina zai sama mata duka abubuwan da take bukata? A dayan bangaren kuma yana tunanin Momy. Lokacin lokaci take sauke ajiyar zuciya da karfi tana shakar numfashin a hankali. Sai da ya tabbatar bachin nata ya nina sosai sannan ya mike tsaye ya karasa inda take ya kai hannunsa ya janye hannunta daga bakinta ya kara jan bargon ya lulluba mata har gurin wuyanta, sai kuma ya tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarta, samun kansa yai da murmushi kamin ya juya ya fara takawa cikin izza ya nufi kofar dakin, hannunsa ya kai ya kunna ac dakin sannan ya juyo ya sake kallonta, kamin ya sa kai ya fice ya ja kofar a hankali ya rufe, this is the first time da yake taba kofa a hankalin saboda gudun katsewa wani bachi, after Daddy. Fita kofar falon ma a hankali ya jata ya rufe saboda kar karar rufe kofar ya tashe ta, sannan ya saka key ya rufe kofar daga waje, sai da ya fara isa ya gurin gate din ya bude sannan ya dawo ya fita da motarsa sai kuma ya dawo ya rufe gate din ya koma cikin motar. Kamin ta fita unguwar aka soma kiran sallah magariba, a kusa da wani masallaci ya faka motarsa ya fita yai alwala ya shiga masallacin yai sallah sannan ya dawo cikin motarsa yai mata key ya dauki hanyar gida.
Kamin ya isa ya kira Daddy a waya, sai dai har wayar tai ringing ta gama be daga ba, hakan ya saka shi rike wayar a hannu ya cigaba da tukin da hannu daya har ya isa gida, yana danna horn sai ya ji babu dadi tunawa da Momy bata cikin gidan, har yake jin kamar ya juya ya koma domin shiga cikin gidan yana masa nauyi a yanzu, ya kasa daina ganin laifin Daddy na yanke irin wannan hukuncin kuma yana ganin shi ne silar komai, tun da yake da Momy ko fushi be tana ganin ta yi ba, balle kuma har saki ya shiga tsakaninta da Daddy, idan ma an taba ta an yi ta sigar da su ba za su gane ba. Har ya isa harabar aje motocin ya faka motarsa be lura da Kabir dake jingine jikin mota yana waya ba, duk da kasancewar ko'ina na gidan haske ne irin hasken nan da ko allurarka ta fadi zaka iya gani, ko da yake hausawa sun ce hankali ke gani ba ido ba.
Sai da ya bude motar ya fito sannan ya kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar Kabir, rufe motar yai ya karasa inda Kabir yake jingine ya tsaya tare da zuba hannayensa aljihu yana kallon harabar gidan kamar bako.

“Ya akai?”

Kabir ya bukata ganin ya tsaya a inda yake da alama jiran yake ya kare wayar, kallonsa Talba yai jin wata bakuwar kalma da be saba furta masa ba ga fuskarsa a gade kamar bakin hadari.

“Come on.. Karka ce min ka zo nan ne saboda ka yi magana akan abun da ya faru? Kai da baka san zafin uwa ba? Taya za ayi ka ji wani abu?”

Talba ya kalleshi da mamaki.

“Kabir magana fa kake fada min kai tsaye”

“Yes ko ni ma zaka saka Daddy ya kore ni ne? But I'm grown up now ba yaro ba ne ni”

“Kabir me ke damunka?”

Talba ya tambaya da mugun mamaki.

“Babu abun da yake damuna, kawai ina fadar gaskiya ne da ace ka san wacece uwa da baka bari komai ya faru ba? And you won't be here standing in front of me, Momy ta raine ka for so many years amman a yau ka nunawa duniya cewar kai ba danta ba ne, and Thank you....”

Yana fadar hakan ya bar gurin ya nufi hanyar falo, Talba binsa yai da kallon yana mamakin kalaman da Kabir ya fada masa kai tsaye! Ta dayan bangaren kuma sai ya ji kamar an caka masa wuka a kirji, how could someone like Kabir zai ce masa be san zafin uwa ba? For the second time after wacan karon da Daddy ya ba shi labarin komai ya samu kansa da jin wani yanayi irin na Aminatu.



BATURIYA POV.

“Na kira ne kawai na yi miki barka da safiya”

Ta yi murmushi tana kara gyara kwanciyarta kan gadon Umma.

“Na yi fushi baka kira ni da wuri ba har rana ya fito sosai”

Ta fada tana ta zuba masa shagwaba kamar yana gabanta. Sai ya marairaice murya daga can cikin wayar yana bata hakuri.

“Haba Babyna kin san bana son bacin ranki fa, amin afuwa ba zan sake ba, kuma ina tafe da wani katon albishir”

“Na me?”

“Sai kin ba ni goro zan fada”

“Me kake so?”

“Komai ma kika ban ina so, ai ni komai ni so nake”

“To na baka kaina”

“Wow na gode ko da yake ke ma din ai tawa ce”

“To yanzu fada min”

“Abbana ya amince, zai fada min lokacin da yake free sai na fada miki ki duba idan na ki Abbah yana free sai su hadu su ga juna”

Ta dafe kirjinta gabanta na faduwa, ga wani irin tsoro da fargaba da suka rabeta a lokaci daya.

“Da gaske?”

“Haba ana wasa da irin wannan maganar ne?”

“Wow Alhamdulillah, amman ka san me? Ni fa a gidan mu ba a san da maganar ka ba”

“Yeah ai na fadawa Abbana, shiyasa ma nake son aje nema min aurenki so that na samu izinin magana da ke”

“Kana ta maganar Daddy ban ji ka tabo Momy ba?”

“Kin san Momy tana son na auri wata a familynsu ne, amman ita ma ta yi na'am saboda tana son abun da nake so, kuma Abbah ya bi bayana yace matukar suka yi bincike suka tabbatar babu wata matsala za su nema min aurenki”

“Alhamdulillah Allah ya amince mana”

“Amin kin san fa ni na gaji da wannan boye boyen da kike min kin hanani zance da ke, da na yi magana sai ki ce ana fada a gida, kuma ya kamata ace muna haduwa saboda mu kara fahimtar juna da kyau”

“Haka ne, ni kaina ina son haduwa da kai, idan na samu free time zan kiraka sai mu haduwa akwai abubuwa da yawa da ya kamata ka sani akaina ni ma kuma na sani akanka”

“Haka ne, idan kin samu sa'ar fita sai ki fada min inda zamu hadu”

“Inshallah, i love you so much”

Ta fada da muryar dake nuna farinciki take, sai dai a zahiri ba farincikin take ba, tsoron abun da zai je ya dawo ne a ranta.

“Na'am Umma gani zuwa”

Ta yi amsawar karya kamin ta ce.

“Ina zuwa Umma tana kirana”

“Okay i love you”

Tun kamin ya aje ya yanke wayar ta tashi zaune tana dudu da hannayenta.

“Kam uban nan, zubar da cikin nan ya zame min dole, amma...”

Bata karasa ba Umma ta daga labulen dakin ta shigo tana fadin.

“Rafi'a, ta so ga yayanki can yana nemanki”

“Toh”

Ta amsa sannan ta sauko saman gadon a ta dayan bangaren tana ala ala idan ba Faruk ya fada masa tsabanin abun da ta fada musu ba. Kamin ta karasa falo har ta fara tunanin irin karyar da zata yi ta kare kanta. Gabanta na faduwa ta zo ta zauna a kasa kanta a kasa Umma dake bayanta ta zauna kan kujera.

“Yaya ina wuni?”

Ta gaishe shi tana dan kallon yanayinsa, sai ya amsa mata fuska ba yabo ba fallasa.

“Umma ta fada min abubuwan da suka faru, na kira Faruq har gida domin ji daga bangarensa, sai dai be fada min komai ba, kawai dai ya ce min ya gaji ne, yayi iya hakurin da zai iya da ke, yanzu kuma Allah ya kare abun, sai dai yayi ta jaddada min cewar ke yar'uwarsa ce kuma uwar dansa, ba zai fadi mummunna abu akanki ba, amman mu zamu fahimci komai da sannu, ina fatar babu abun da kike boyewa”

Ta dago kai ta kalli Yayanta idonta cike da hawaye.

“Haba yaya! A hannunka fa na tashi idan akwai abun da ba halina ba ai kai zaka fara sani”

Umma ta tabe baki

“Ai ni ba haka na so ba Wallahi, da ka biye ta tawa da police station zaka kai shi a lakada masa shegen duka kamar yadda shi ma yayi mata”

“Ai an daga kafa wani gangaren ko dan zumunci, shiyasa na kira shi a gida na yi magana da shi”

“Shi ai be duba zumuncin ba a lokacin da zai wulakantata haba”

“Yanzu dai ayi hakuri komai ya wuce, Allah shi zai saka mata ai”

“Aiko ya saurari abun da zai same shi domin hakkinta sai ya kama shi, kuma gobe gobe zan aika a kwashe mata kayanta duka da yardar Allah, daga ma ta huta da talauci da rashin abincin, kuma ba zamu rika masa dansa ba”

“Yace ma zai rika aiko mata abinci duk wata saboda cikin da take da shi, Allah ya sauwake”

“Ameen”

Ta amsa a tare da Umma sannan ta taso ta baro musu falon da dawo dakin Umma ta zauna tana ta tunanin maganar da Fahat yai mata! Da sauri ta kai hannu ta dauki wayarta ta kira Ramlee ringing daya ta dauka cike da far'arta.

“Yar gari yanzu fa nake son kiranki”

“Lafiya?”

“Lafiya sai alheri, Wallahi Alhajin nan ne ya fara damuna da maganar ki jiya, har yana ce min yana son ya leka chine da ke, bayan shi ma na samo miki wani Alhajin”

“Uhmm ai yanzu fita ma sai ta min wahala Ramlee, Faruq ya sake ni”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya sake ki fa kika ce Fee'ah”

“Wallahi kuwa yau kwana biyu....”

Daga can cikin wayar Ramlee ta sauke ajiyar zuciya bayan Baturiya ta gama labarta mata komai.

“Wato sai yanzu na gane kin ci ubana da iya makirci Fee'at”

“Uhmmm ni ma ai ba ta wasa ba ce, ni yanzu kin san ma miyasa na kira ki?”

“Sai kin fada”

“Cikin nan nake son zubawar kin ga ina zubar da shi na gama iddata”

“Haka ne, amman kar ki yi gaggawa Fee'at, saboda zai taba lokacinki a yanzu, maganar ba zai yi a waya ba, ina son mu hadu if possible”

“Karki zo gida, zan kira ki idan na samu sararin fita”

“Okay ”

Ya sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya.
29

*_MATAYEN ƘWARAI SARAKAN ADO DA ƘAWATA JIKI DA KWALLIYA KUNA INA NE?._*

_Maza ku garzayo da gudunku ga mutunuyar taku maida tsohuwa yarinya ta sake dawo muku da sabon salo, sabon sunfarin kayan gyaran jiki na mayika da sabulai ƴan gaske💃🏻._

*Kayan kwalliya na mg's skin care zasu maidaki shalele ƴar ƙwalisa tamkar wata ɗan daren sha biyar koda kina da kishiya ƴar Morocco bata girgizaki ba, balle saurayi ɗan son ƙyale-ƙyale da ƙawa ga burwallensa😂💃🏻*.

_Kayan mg's skin care nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai.

*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻

Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?
Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki
Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

1 year ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment