Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar me shawarar kada ya je ɗaukan nata.
“Dan Allah Tauqeer!”
Ta marairaice murya.
“Ok gani nan zuwa”
*Cactus Restaurant, No. 20 Ozumba Mbadiwe Abe, Victoria Island, Lagos, Nigeria.*
A tare suka shigo restaurant ɗin, Deena sai faɗi take ita yunwa take ji. Tun bayan da ya bar studio ɗaukarta ya je. Kuma bayan ya ɗaukota suna tafiya a mota tace tana jin yunwa dan Allah ya tsaya su ci abinci a Cactus Restaurant. Ba haka ya so ba, dan de kawai ta nuna tana so ne.
“Na gaji sosai yau!”
Ta faɗi tana jan kujer, tare da zama, shi ma zaman ya yi yana kallon yanda hankalin mutane ya dawo kansu, dan ya san cewa ba shi kaɗai ake kallo ba, har da Deena.
“Barka Tauqeer Agha!”
Muryar wata budurwa ta faɗi a kansu, kallonsu suka yi a tare, su biyu ne tsaye a wurin suna ta jifan Tauqeer da murmushi. Shi ma murmushin ya musu.
“Ko za mu iya ɗaukar hoto?”
“Why not”
Ya faɗi yana miƙewa. Deena da ta cika ta yi fam, ta bisu da kallo tana jin kmar ta shaƙesu ta hut. A tsakiya suka sashi, sannan suka ɗauki hoton selfie.
“Mun gode”
Suka faɗi a tare suna barin wurin. Kujerarsa ya ja ya zauna yana murmushi. Idonsa ne ya kai kan Deena dake cika tana batsewa.
“Menene?”
Ya tambaya cikin halin ko in kula, dan shi bai ga aibun hoton da suka yi da 'yan matan ba. Su fans ɗinsa ne, dan sun yi hoto da ahi ba komai ba ne, tun da ba cewa suka yi suna sonsa ba.
Kanta ta kawar tana faɗin.
“Junior! Ya kamata ka gane wani abu guda ɗaya, ba'a kishin mutum sai ana sonsa, ka san cewa ina sonka, kuma akwai maganar aure tsakanina da kai, to me ya sa kake tunanin ba zan ji ciwo i idan na ganka da wata ba?”
Tauqeer ya yi shiru kawai. Dan shi har ga Allah ya kan manta wanan batun auren dake tsakaninsa da Deena, dan abu ne da ba ya cikin lissafinsa. Tun shekarun baya da suka wuce ya jingine babin soyyaya. Ko shi kansa bai san me ya sa ya amince da aurenta ba. A batun gaskiya shi bai taɓa son Deena ko da da minti ɗaya ba ne. Ba wai ya tsaneta ba ne, a'a, shi yana mata kallon 'yar uwarsa ne ba masoyiyarsa ba.
Batun tana kishinsa kuma wata magana ce da ban. Tun da take baɗalancinta da sunan Film bai taɓa nuna mata ƙin abun da take ba. Sai shi dan ya yi hoto da 'yan mata za ta ji haushinsa?.

DIYA POV.
“Ki kai wannan trayn teburi me lamba 16!”
Umarnin ya fito daga bakin shugabarsu. Diya da kanta ke sunkuye ta gyaɗa shi. Sannan ta ɗauki trayn. Damuwar da take ciki a ko da yaushe ƙara girmama take. A kullum kwanan duniya mastaloli na ƙara tunkarar rayuwarta. A jiya jikin Papi ya ƙara tsanani, ga kuma Ekene da har zuwa yanzu bai gama warkewa ba, ga kuma Gigi dake ɓoye mata wani abu da ta kasa gano menene shi. Ga kuma MD da ya uzzurawa rayuwarta. A daren jiya har kiranta ya yi a waya. Ya na ƙara nanata mata mummunan ƙudirinsa a kanta... A lokacin ne kuma abun ya faru. Matakin farko na wanzuwar ƙaddarar dake tafe da jirkitattun al'amura.
Tunaninta ya maƙale a iska, sakamakon tsohon canvas ɗinta da ya yage, hakan ya haddasa mata gurɗewa, ta yi gefe zata faɗi. Amma cikin ikon Allah sai ta ji an riƙo hannunta, an fisgota da ƙarfi. Kuma ƙarfin da aka saka wurin janyotan ne ya sa trayn dake hannunta suɓucewa ya faɗi. Ita kuma ta faɗa ƙirjin wanda ya janyota. Idanuwanta a rufe gam-gam. Yayin da hannun mutumin da ya temaka mata ke riƙe da kunkuminta, ita kuma nata hannayen na dunƙule a kan ƙirjinsa. Daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya fara dawowa da ita hayyacinta. Kafin sassanyar muryarsa ta doki dodon kunnenta.
“Kina lafiya?”
Sai ta kasa gaskata abun da kunnuwanta ke jiye mata. Ta saba jin muryarsa cikin waƙa, ta saba jin muryarsa idan ana masa interview. Ta saba jin muryarsa a tallace-tallacen da ake bashi na kamfanunuwa. Ko a barci ta farka babu abun da zai hana mata gane muryarsa. Babban mawaƙin da ke burgeta TAUQEER AGHA!
“Kan bala'i! Junior miye hakan?... Akan me za ka riƙeta irin haka a cikin jama'a?”
Wata murya ta dawo da ita daga duniyar kokwanton da ta lula. Da sauri ta buɗe idonta tana kallon setin inda muryar ta fito. DEENA AGHA ce.
Kuma ganin Deenan ne ya tabbatar mata da wanda take cikin jikinsa a yanzu Tauqeer Agha ne. Cikin jikinsa! Kalmar ta nanata kanta a cikin ƙwaƙwalwarta. Da sauri ta matsa daga jikinsa tana kallon fuskarsa. Ji ta yi zuciyarta ta daka tsalle. Abun kamar a mafarki, yau ita ce tsaye a gaban Tauqeer Agha?.
Tauqeer kuwa kallonta kawai yake. Suna cikin magana da Deena ta zo za ta gifta su, da yake hankalinsa na a setin inda ta zo wucewa ne ya sa ya ankara da gurɗewar da ta yi. Shi ya sa ya yi hanzarin miƙewa ya ruƙota. Kuma a sanda ya kalli fuskarta ya ji wani abu na bi ta kan zuciyarsa da bai san sunansa ba.
Bai taɓa ganinta ba, bai santa ba, ba ya jin ya taɓa ganin ko da me kamar ta ne balle ita ɗin kanta. Amma haka kawai sai ya ji kamar ya santa. Kamar ya taɓa saninta a wani wurin bayan wannan. Sai ya samu kansa da kasa dena kallon fuskarta har yanzu. Har zuwa yanzun da Deen ta ɗauki glass cup me cike da ruwa ta watsa mata a fuska.
Hakan ya sa ta yi saurin rintse idonta. Shi kuma Tauqeer ya yi saurin kallon Deena.
“Deena mi ye haka?”
Ya tambaya ransa na shirin ɓaci. Dan hankulan tsurarun mutanen dake Restaurant ɗin ya dawo kansu.
“Au tambayata ma kake? A kan me zaka riƙe wannan ƙazamar yarinyar a gaban mutane? Ko hannuna ba ka son ka riƙe amma a gaban idona ka riƙe wannan ƙazamar oloshi oloddo, opola ɗin?”
Tauqeer ya lumshe idonsa yana so ya hana ransa ɓaci.
“Deena ki bata haƙuri!”
Deena ta yi dariyar renin hankali.
“Wow! Ni ce zan bata haƙuri? Har wannan ƙazamar talakan ta kai na bata haƙuri? To bata isa ba, daga kai har ita baku isa ba!”
Tana kaiwa nan ta finciki jakarta ta fice tana harar Tauqeer. A hankali Tauqeer ya matsa kusa da Diya da har zuwa lokacin idonta ke a lumshe tana hawaye. Mutane da dama kan ce Deena Agha bata da mutunci, ta iya wulaƙanta mutane, ba ta taɓa gaskatawa ba sai yau. Ba zato ba tsammani ta ji sauƙar wani lallausan hanki a kan fuskarta, sannan muryar Tauqeer ta biyo baya.
“Ki yi haƙuri...”
Sai kuma ya yi shiru yana karanta sunan dake rubuce a jikin name tage ɗin rigarta.
“DIYA SHOLA!”
Yanda ya furta harufan sunan nata ɗaya bayan ɗaya cikin daddaɗar muryarsa ya sa ba shiri ta buɗe idonta ta kalleshi. Tsaye yake kusa da ita, hannunsa na dama riƙe da hanki yana goge mata fuskarta da Deena ta watsa mata ruwa. Idanuwanta ya ci gaba da kalla, yana jin kamar su dawwama a haka yana kallonta.
“I'm truly sorry!”
Ya kuma faɗi idonsa cikin nata. Diya ta zama daskararriya dan mamaki! Ita fa Wallahi ta kasa yarda da cewar wai yau ita ce tsaye a gaban tauraron duniya lamba ɗaya. Ba haka kawai ba, har sunanta ya furta, a lokaci guda kuma yana bata haƙuri. Hannunta na dama ya kamo, sanyin hannyensa sune suka kunna wuta a cikin jijiyoyin jikin Diya. Dan ji ta yi kamar ya kara mata ƙanƙara. Hankin hannuna ya aje mata a hannun nata. Sannan ya ƙara furta.
“Ki yi haƙuri”
Ta kasa motsi, ta kasa magana, ta kasa dena kallonsa, ta kasa komai, babu ma wani abu dake aiki a jikinta face zuciyarta dakw kaikawo daga maƙogwaranta zuwa ƙirjinta. Sai kuma idanuwanta da ta kafeshi da su ba ta ko ƙiftawa. Har ya fice a kan idanuwanta bata dena kallonsa ba.
Ko da Tauqeer ya fita bai iske Deena ba, dan haka ya shiga motarsa ya koma studio. Kuma ya jima a can. Dan har bayan magariba yana can ɗin.
______________
_LANTANA! Ina so ku samu wani ɗan ƙanƙanin space a cikin ƙwaƙwalanku, ku aje min wannan sunan, dan wannan sunan zai taka tasa muhimmiyar rawar a cikin wanga tafiya._
_Lalle Rafeeq yana lalube ne a cikin duhu, dan da alama zuciyarsa na shirin saka shi ɗaukar dala ba gammo._
_Akwai ƙura fa, dan na lura da Salame ba ta son wannan auren, dannewa kawai take._
_Na lura kamar Tauqeer ya fara son Diya._
_Ga kuma matsalolin dake tunkarar Diya Shola._
_Mu de je zuwa, kun san na ce muku ba fa mu yi komai ba har yanzu... Yanzu aka soma._
_wannan zai kasance feji na kusa da na ƙarshe a free pages... Wai na manta ban gaya muku ba?. Haske fa paid book ne_
_To ku yi maza-maza ku biya tun kan free pages su ƙare.._
A. ISAH CE ✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE...💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 10*
~~~
*Federal Neuro, Psychiatric Hospital, Yaba, Lagos, Nigeria...*
Wata nurse ce ke tura wheelchair. Wadda Rahila ke zaune a kai. Idonta kawai idan ka kalla za ka san cewa ba ta cikin hayyacinta. Dan da ƙyar take iya buɗesu.
“Ka buɗe ƙofa. Sabuwar majinyaciya ce”
Cewar nurse ɗin a sanda ta iso sashen adana maau taɓin hankali na aibitin. Me gadin ƙofar wurin ya buɗe mata yana faɗin.
“Okay”
Ci gaba ta yi da tura wheelchair ɗin. Har ta iso ƙofar wani ɗaki baƙinƙirin da shi. Da kantata buɗe kwaɗon ɗakin, sannan ta shigar da wheelchair ɗin, ba ta tsaya ɓatawa kanta lokaci wurin sauƙe Rahila ba, ta hankaɗata ta faɗi ƙasa har tana fasa kanta. Tsabar a galaɓaice take ko damar ihun azaba bata samu ba.
Babu imani haka nurse ɗin nan ta juya ta fice daga ɗakin, sannan ta kulle. Haka Rahila ta yi ta murƙususu a ƙasan ɗakin da yake baƙinƙirin kamar sauran sassan ɗakin. Ta shafe sama da awa ɗaya cikin wannan hali, kafin hayyacinta ya dawo jikinta. A daddafe ta miƙe zaune. Sannan ta jingina da bango tana ƙarewa ɗakin kallo. Babu komai a cikinsa sai wata latsatssiyar katifa guda ɗaya.
Jikinta ta ƙanƙame waje guda, sannan ta saki kuka me ban tausa.
“Ya Allah kana gani! Allah ka ga halin da nake ciki! Ka kawo min mafita ya Allah! Ya Allah ka kawo min mafita”
Haka ta faɗi ƙasan ɗakin tana kuka me sauti. Kamar daga sama ta ji an daki ƙarafunan ƙofar ɗakin. Ba ta kai ga fahimtar komai ba wata tsawa ta biyo baya.
“Ke! Kukan ub*n me kike mana! Ki ja bakinki ki yi shiru, in ba haka ba jikinki ya gaya miki, mahaukaciyar banza... Ɗauki ki ci!”
Lutetiyar matar dake ta bala'in daga bakin ƙofar ɗakin ta ƙarashe tana garo mata wani kwanon silver ta ƙasan ƙarafunan ƙofar ɗakin. Har kwanon ya iso gaban Rahila binsa kawai take da kallo. Sai da ta yi da gaske sannan ta iya gane menene a ciki. Wata cakuɓɓaɓiyyar shinkafa ce, wadda ba ta da maraba da tuwo, saboda ruwan da aka tsula wurin dafata, sai wata baƙar miya a kai. Kallon abincin kaɗai ya sa Rahila jin cikinta na yamutsawa, ta ji amai na shirin fito mata. Dan haka ta yi saurin kawar da kanta daga barin kallon abincin.
Ko da dare ya yi kasa bacci ta yi, saboda koke-koke, bige-bige da doke-doken da masu taɓin hankalin dake kusa da ɗakinta ke yi. Haka ta yi ta firgita tana kuka. Kuma gashi ta kasa cin abincin wurin. Dan ko da daddaren ma an kawo mata wani baƙin tuwo da ta kasa gane na miye, da wata miyarsa me kama da ruwan wankin kai.

SURAJ POV.
Kasancewar yau laraba akwai aiki, kuma bayan ya je ya taso ya yanke shawarar kaiwa Diya Shola ziyara. Cikin wani ikon Allah yana zuwa bakin gaɓar yankin nasu ya hangeta ita da wannan ƙawar tata suna shigowa yankin. Da sauri ya faka motarsa ya fita yana nufarsu.
“Kalli can ki gani Diya!”
Cewar Fa'ee da ta hangi Suraj na tunkarosu. Diya da ta shagala wurin bawa Fa'ee labarin haɗuwarta da Tauqeer Agha a yau ta juyo ta kalli inda take kallo ita ma.
“Da alama fa officer yana ciki”
Da sauri Diya ta bigi hannunta tana mata alama da ta yi shiru, ganin Suraj ɗin ya ƙaraso inda suke.
“Barka da yamma officer!”
Cewar Fa'ee tana ƙunshe dariyarta, ganin yanda Diyan ke tsilli-tsilli da idonta, kamar ɓera a buta.
“Lafiya ƙalau”
Suraj ya amsa a mutunce.
“To bari ni na wuce. Diya! Sai kin iso”
Ta ƙarashe tana barin wurin.
“Ƙawarki ce?”
Suraj ya tambaya yana kallonta. Diya ta sunkuyar da kanta tana faɗin.
“Eh, sunanta Fa'iza”
Suraj ya ci gaba da kallonta. Shi kam yana mamakin ɗabi'unta, ko a hali ko a kammani ba ta da haɗi da yarabawa, tashin farko idan ka kalli kyan fuskarta da kuma yanayin ɗabi'unta da bafulatana za ka kirata.
“Kame ka zo yi a yankin namu ne!”
Ta tanbaya jin shirun ya yi yawa. Suraj ya ɗan yi murmusa yana cire hular kansa.
“Ko kaɗan kawai de na zo wucewa ne, shi ne na ce bari na tsaya mugaisa da ke!”
“Ka kyauta kuwa tun da gashi ka sada zuminci”
Ya jijina kansa yana ci gaba da kallonta.
“Ni zan koma... Sai an jima”
Sai a lokacin ta ɗago da kanta ta dubeshi.
“Na gode sosai Yallaɓai Sur...”
“Suraj kawai”
Ya yi saurin katseta, murmushi ta yi tana kawar da kai. Ba za ta yi wa kanta ƙarya ba, ita dai kam ta san yana burgeta, amma ba za ta kira hakan da so ba.
Dan so na nufin haɗuwar zuciyoyi biyu wuri guda. Kuma idan ta yi la'akari da matsayinta da na Suraj sam ba ɗaya ba ne. Akwai tazara me tarin yawa a tsakaninsu, duk da ba ta san waye shi ba, amma ta faɗawa kanta cewar ya fi ƙarfinta, dan haka maganin bari kar a fara.
“Suraj!”
Ta kira sunan kamar yadda ya buƙata. Suraj ya tsaya ya ci gaba da kallonta kamar kar ya tafi.
“Ka fasa tafiyar ne?”
Ta tambaya. Da sauri ya girgiza kansa yana juyawa. Har ya kai jikin motsar ya dawo. Ya zaro katinsa, ya miƙata yana faɗin.
“Wannan lambar wayata ce, ki kirani idan buƙatar hakan ta taso!”
Sai da ta kalli katin sannan ta kalli fuskarsa. Hannunta ta kai ta karɓa, sannan ta masa godiya ta juya. Yana tsaye a wurin har ta sha kwana.
Murmushi ya yi yana nufar motarsa ya isa gida ransa fes. Wanka kawai ya yi ya fito ya nufi ɗakin Narjis, ya sameta ya zayyana mata kaf abubuwan da suka faru.
“Da kyau Hammana na kaina, a hankali a hankali za ka ci gaba da kusantarta, har zuwa lokacin da zaka bayyana mata sirrin zuciyarka”
Murmushi ya yi yana gyara zamansa.
“Wacece yarinyar?”
Suka jiyo muryar Mummy na tambaya daga bakin ƙofar ɗakin. Dan haka suka juya suka kalleta a tare. Ganin ba su da niyyar bata amsa ya sa ta shigo ɗakin, ta zauna a tsakaninsu. Tana binsu da kallon tuhuma.
“Ai kana iya zuwa ka faɗawa ƙanwarka damuwarki, ni ce ba za ka faɗawa ba?”
Da sauri Suraj ya girgiza kansa.
“Ba... Ba haka ba ne Mummy. Har zuwa yanzu ban faɗa mata ba, na fiso na sanar mata da farko, kafin na kawo maganar gareki!”
Shiru ta yi tana kallonsa.
“Waye mahaifin yarinyar!”
Yawu ya haɗiye yana faɗin.
“Ban... Ban san ba Mummy, kawai de na san a Makoko take!”
“Makoko?”
Ta maimata sunan mamaki kwance kan fuskarta. Kansa ya gyaɗa yana taoron jin abu na gaba da zai fito daga bakin nata. Shiruu na tsawon minti ɗaya. Ban da bugu babu abun da zuciyarsa ke yi. Tsoro yake ji, yana jin tsoron kada Mummy ta ce bata amince da yarinyar ba tun kafin ta ganta. Ga shi kuma ta ƙi yin magana, sai kallonsa kawai da take.
Har ya riga da ya fidda rai, sai ya ga ta yi murmushi tana ɗora hannunta a kansa. Murmushin nata ne ya sanyaya zuciyarsa har ya sa shi shi ma ya yi murmushin.
“Ka yarda da tarbiyyar yarinyar?”
Da sauri ya gyaɗa mata kai.
“Eh Mummy”
“To Allah ya tabbatar mana da alkairi”
Kwanciya ya yi a jikinta yana murmushi.
“Ameen Mummy!”
“Auta fa?”
Cewar Narjis a shagwaɓe. Suraj ya saki Mummy yana dungure mata kai.
“Lokacin firstborn ne yanzu”
Suka yi dariya suna rungume mahaifiyar tasu.

DIYA POV.
Tana shan kwana ta samu Fa'ee zaune a cikin kwale-kwale tana jiranta. Murmushi ta yi tana nufar kwale-kwalen.
“Allah sarki tawan, ashe jirana kike”
“Eh mana, jira nake ki gama soyewar sai mu tafi”
Diya ta zauna a cikin kwale-kwalen tana hararta.
“Bana son shari Fa'ee”
“Wani irin shari kuma? Bayan daga nan ma ina jiyo ƙaurin soyewar da kuka”
“Sai ki yi kuma ai”
Ta faɗi tana ɗauke kanta. Fa'ee ta yi murmushi.
“Allah Diya na lura da ɗan sandan nan yana sonki!”
Diya ta juyo ta kalleta da sauri.
“Dan Allah Fa'ee kada ki fara abun da ba zai ƙarasu ba. Tskanina da Suraj mutunci ne kawai, ba na jin wata alaƙa me kama da ta soyyaya za ta iya shiga tsakani”
Fa'ee ta yi shiru ba tare da ta sake cewa komai ba. Don ko me za ta faɗa Diya ba yarda za ta yi ba, amma dai ita ta san cewa ta hango abun da ita Diyan bata hango ba. A ranta ta musu addu'ar Allah tabbatar musu da alkairi.
Kuma har suka iso gida babu wanda ya sake cewa komai. Ko da Fa'ee ta sauƙa a rumfar gidansu Diya sai ta tsallaka zuwa tasu rumfar. Kafin kuma ta shiga cikin gidansu. A ƙwallin ɗaki ɗayan dake gidan nasu ta iske mahaifiyarsu na zaune tana dama koko. Ƙaramin ƙaninta kuma na kwance a gefen mahaifiyar tasu.
“An dawo?”
Mahaifiyar tata ta tambaya tana dubanta.
“Eh Mama, na dawo, kuma Wallahi a gajiye nake gaba ɗaya!”
Ta faɗa tana zama kusa da mahaifiyar tasu.
“Sannu to!”
“Yauwa... Ina Aliyu?”
Ta tambaya saboda ba ta ganshi a gidan ba. Mama ta miƙa mata koko a kofi tana faɗin.
“Sikari na aikeshi ya siyo min”
Fa'ee ta gyaɗa kanta tana karɓar kofin.
Ai nahinsu mutanen garin Kano ne, ci rani ne ya kawo mahaifinsu Lagos, kuma ko da ya tashi tahowa sai ya taho da su, a lokacin Fa'ee tana ƙarama. Sannan a nan Makoko aka haifi Aliyu ƙaninta na farko, sannan aka haifi Sadiq autansu. Wanda bayan haihuwarsa ne mahaifinsu ya rasu. Shi ya sa kula da nauyin gidan ya rataya a wuyata.

*Ƙauyen Wagini, Batsari Local government, Katsina state, Nigeria.*
*11:40 na dare.*

SALAME POV.
Fitsarin da take ji ne ya tasheta a bacci. Da ƙyar ta miƙe zaune tana mitsikka ido. Fitowa ta yi daga gidan sauronta. Sannan ta laluba kan shimfiɗar Inna, ta ɗauko tocilan ɗinta. Ko da ta kunna fitilar sai ta ƙi kawowa. Hakan yasa ta ɗan bigi kan tocilan ɗin. Hakan ya bawa fitilar damar kawowa haske dal.
Kasancewar ɗazu Inna ta saka mata sabbin batura. Kuma ta cikin hasken da fitilar ta bayar ta kalli jan lallen da aka mata a hannayenta. Jan lallen aurenta da wanda bata sani ba. Jan lallen da ya zauna a kan farar fatarta ya yi kyau.
Ture zancen wannan auren ta yi daga kanta, sannan ta lallaɓa ta fita daga ɗakin ba tare da ta tada kowa a bacci ba. Ko da ta fito sai ta tsaya a tsakar gida. Kunnuwanta ne suka fara jiyo mata ƙaran babura a cikin shirun daren. Bakinta ta taɓe tana nufar randa dan ta je ta rage mararta. Buta ta ɗauka ta cika ta da ruwa, sannan ta nufi banɗaki.
Ko da ta yi fitsarin ta gyara jikinta ta miƙe tana shirin fita daga banɗakin. A lokacin abun ya faru, a lokacin mukullin buɗe ƙofafin ƙaddararta ya wanzu a doron duniya. A ranar a kuma lokacin ne ƙaddararta ta farko ta auku. A lokacin ta saka ƙafarta cikin wani irin duhu dake mamaye gaba ɗaya rayuwarta.
Ƙaran baburan da take jiyowa a nesa ne ya matso kusa. Bayan ƙaran baburan akwai wani sauti me razanarwa sautin harbin bindiga. Tuni ƙwaƙwalwarta ta hasaso mata irin abubuwan dake faruwa a maƙotan ƙauyukansu. Da alama 'yan bindiga ne suka shigo musu ƙauye.
Nan take jikinta ya soma kyarma, har fitilar dake hannunta ta suɓuce ta faɗo ƙasa. Sabbin baturan dake cikin fitilar suka fice da ƙarfi, hakan ya haddasa ɗaukewar hasken fitilar. Duhu ya mamaye ban ɗakin. Wani irin duhu dake kamanceceniya da ƙaddararta. Tsoro ya hanata motsawa. Tuni ta soma hawaye, bakinta banda rawa babu abun da yake.
“Inna! Salma! Iya! Baba! Muja!...”
Ta jiyo muryar Hammanta na ƙwala musu kira a tsakar gidan. Baba ne ya fito daga ɗakinsa, dan shi ma ya ji ƙaran Iya ma ta fito haka Inna, duka suka tsaya a tsakar gidan suna tambayarsa abun da ya faru.
“Baba 'yan bindiga ne suka shigo Wagini!”
Zuciyar Salame ta ƙara dokawa da ƙarfi, a sanda ta jiyo ihun matan gidan dake maƙotaka da nasu. Ƙaran bindiga ya cika ko ina. Zabura ta yi za ta fita daga banɗakin ta ji an banko ƙofar gidansu da ƙarfi.
Hakan ya sa ta sandarewa a cikin banɗakin. Ta tsaya ƙiƙam tana kallon 'yan uwanta da ke rafka salati. Fitilun da 'yan bindigar suka haskesu da su shi ne ya haska mata kalar tsoron da ko wannensu ke ciki. Kafin ta yi wani tunani na biyu, sun buɗewa kowa wuta a gidan.
Tana ji kuma tana gani suka harbe kowa! Kowan ya haɗa da Inna, Baba, Iya Abu da Hamma Audu. Ƙarar harbin ne ya tashi Muja daga barci, ya fito yana murza ido. Ko kafin ya ce komai shi ma suka harbeshi.
Tsoro ruɗani tashin hankali da ɗimuwa suka riftowa Salame a lokaci guda. Ƙafafunta suka gaza wurin ɗaukarta. Hakan ya bata damar zama a ƙasa daɓas!. Bakinta a buɗe, ta kasa furta komai sai ‘Innallilahi wa inna'ilaihi rajiun’ A kan idonta 'yan bindigar suka gama zaga gidan, ba tare da sun lura da ita ba suka fice daga gidan.
Ta cikin hasken farin watan da ya haska duniya take kallon gawwawwakin ahalinta yashe a ƙasa cikin jini. Daga nan inda take tana iya jiyo sautin harbe-harbe, da iface-ifacen jama'ar ƙauyen. Amma ta kasa motsawa. Ji take kamar zuciyarta za ta fashe lokaci guda. Ta kasa janye idanuwanta daga kan gawarwakin danginta. Farin cikinta. Ababen alfaharinta. Rayuwarta. To yanzu ita me ya kamata ta zauna ta yi a duniya? An kashe mata kowa, kowa ya mutu, babu kowa, sai ita kaɗai. Cikin ƙasa da muntuna goma rayuwarta ta rugurguje tun daga farko har zuwa tsakiya. To yanzu me za ta yi.
Kamar wadda aka cillo daga sama ta miƙe da gudu ta iyo cikin gidan. A kan gawar Baba ta fara durƙushewa.
_“Ina so ki yi karatu Salamatu. Mace me ilimi ita ce abar alfaharin ko wace al'uma... Allah ya miki albarka”_
Ire-iren kalamansa gareta kenan. Hannunta na dama ta ɗora a kan ƙirjinsa dake zubar da jini. Ta ɗan jijjiga shi idonta na zubar da hawaye kamar an kunna famfo.
“Baba... Babana... Baba...”
Da ƙyar ma sautin muryar tata ke fita. Hannunta ta ɗauke daga kansa, sannan ta ɗora a kanta tana rushewa da kuka. Idonta ne ya sauƙa a kan Inna. Da rarrafe ta isa gareta. Hannunta ta riƙe bakinta na rawa wurin faɗin.
“Inna! Innata!...”
Sai kuma ta kwantar da kanta a jikin Innan tana tuna kalaman Innar gareta yau, sanda ana mata lalle.
_“Sai haƙuri Salame. Shi zaman aure ɗan haƙuri ne, ki bi mijinki sau da ƙafa, ki masa biyyaya. Idan kika yi hakan, ina me tabbatar miki da za ki ci riba a nan gaba!”_
“Innaaaaaa!”
Ta furta da ƙarfi cikin kuka. Sai kuma idonta ya sauƙaba kan Muja. Da sauri ta miƙe ta isa inda yake, kamoshi ta yi tana rungumeshi a ƙirjinta.
_“Adda Salame idan na girma zan siya iki ƙatuwar mota irin ta gidan Alhaji Maude!”_
A lokacin da ya faɗa mata hakan dariya ta yi tana cewa santi yake, dan abinci suke ci a lokacin.
“Mujahid!”
Ta kira sunan da bata saba kiransa da shi ba. Haka ta saki gawarsa ta isa kan ta Iya Abu.
_“Salamatu ko ba kya son auren nan ne?. In de har ba kya so ba za mu taɓa miki auren dole ba!”_
Kuka take sosai tana tattaɓa fuskar Iya Abu. Haka ta koma kan Audu tana kuka. Ta jima a zaune a wurin tana kalon gawarwakinsu. Kamar wadda aka tsikara kukan nata ya tsaya cak. Ta miƙe tsaye tana kallon gawarwakin 'yan uwanta. To yanzu tun da kowa nata ya mutu me za ta yi? Ya kamata ace ita ma ta mutu...
Ba tare da ta sani ba, ƙafafuwanta suka fara takawa suna nufar ƙofar gida. Har zuwa lokacin babu abun da ke tashi a ko

Please Login or Register in order to submit comment