Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye. Kuma kafin ya amsa shi, Nimra ta yi caraf tace.
“Cewa ya yi ba zai yi ba, kuma yau ma sai da uncle math ya masa horo!”
Bobo ya juyo da kansa ya kalli Nimra cikin harar. Ba tare da ya ankara ba, Hammad ya warce plate ɗin meat pie ɗin dake hannunsa yana faɗin.
“Gara uwar ci, ka tashi ka je ka ɗauko jakarka ka yi home work ɗin ko sai na mammake ka?!”
Miƙewa ya yi yana cillawa Nimra kallon za mu haɗu ɗin nan. Tiɓi-tiɓi ya nufi tagwayen stairs ɗin dake falon, har wani nishi yake idan yana tafiya, tsabar yawan da ƙibar tasa ta masa.
Kakarsu da suke kira da Hajiya ce zaune a kan wata kujera, Iqra kuma na mata tausa.
“Kakus ki na da goro ne?”
Saif da ya fito daga kitchen, hannunsa riƙe da mug ya tambaya yana kallon kakarsu. Hajiya ta wurga masa harara.
“Da za ka zo kana tambayata ka siyo ka kawo min ne?”
Ta tambaya tana wurga masa wata harar.
“Ka ji ni da tsohuwa, daga tambaya?, sai cibo ya zama ƙari? Ƙari kuma ya zama ƙababa?. Inde maganar goro ce Allah ya baki haƙuri”
Ya faɗa yana shirin wucewa, sai kuma ta fito da goron daga cikin aljihun doguwar rigar jikinta tana faɗin.
“Zo ka karɓa ba dan halinka ba!”
“Bana ci!”
Ya faɗa ba tare da ya ko waigo ya kalleta ba. Hajiya ta taɓe bakinta tana maida goronta aljihu. Iqra ta musu dariya. Kusan kullum sun saba irin wannan faɗan, ita Hajiya saurin faɗa, shi kuma Saif zuciya.
“Bar ni haka 'yar albarka”
Cewar Hajiyan tana janye ƙafarta daga hannun Iqran.
“Hajiya ai ni yau gani na yi ma ƙafar taki kamarta ƙara jagulewa”
Hajiya ta dudduba ƙafar tata tana faɗin.
“Ke de bari, wannan ja'irin yaron ne yake ƙara rikita min ita, sai ya zo ya yi ta jagula min ƙafa, wai a dole shi likitan ƙashi”
Iqra ta yi dariya tana miƙa mata kwajirinta, ganin tana shirin miƙewa.
“Dan girman Allah Taj ka dena taremana! Haba! Ka barmu mu yi kallon nan a tsinake mana!”
Cewar Nasir, ganin Taj ya hanasu su kalli film ɗin da suke kallo a tsinake, sai tare musu yake, wai film ɗin be yi kyau ba.
“Da waya zaunar da kai yace dole sai ka kalla? Idan ba ka so za ka iya tashi ka barmu mu kalla a tsinake!”
Nasir ya faɗi yana juyo da kan system ɗin gareshi.
Mommy da Deena ne suke sauƙowa daga kan stairs. Deena sai fara'a take, saboda dawowar masoyinta, farin cikinta, abun alfaharinta, wato Tauqeer, Mommyn ma sai kallonta take cike da alfahari kasancewarta 'yarta.
Saif dake ƙoƙarin hawa stairs ɗin ya tsaya yana kallon irin shigar dake jikin Deena. Wata mini dolman dress ce a jikin nata. Tsala-tsalan singalilanta masu kama da tsinken kwakwa bayyane a waje. Ƙafarta sanye da wedge booties me ɗan karan tudu. Kanta kuwa ya ji kitson attachment ya ƙoshi, baƙar fuskarta ta sha make-up. Ita gata wayyayye.
Ya ja tsaki a ƙasan numfashinsa yana kallon gefe, dan tsabar takaici. Haka kowa ya bisu da kallo ita da Uwar tata har suka fita daga falon, dan ita Deena tace zata je ta ɗauko Tauqeer daga airport.
Hajiya da ta taso dan shiga ɗakinta ta tsaya a setin Saif tana dafa kafaɗarsa.
“Sai haƙuri Saifu”
Ta bashi haƙurin dan ta san abun da Deena ke yi na ɓata masa rai. Ba ma shi kaɗai ba, kowa dake gidan ba ya jin daɗin shigar da take.
“Hajiya abun nata ya yi hawa Wallahi. Kar ki ga hoton da ta yi posting a shafinta na Instagram last week. Hoton ya jawo cecekuce a social media. Babban abun da yake ɓata min rai shi ne kasancewarta a cikin ahalinmu!”
“To yaya za ayi Saifu? Dole a yi haƙuri, tun da ka ga ita ma jinin gidan nan ce, kuma da ma irin haka na faruwa, duk inda aka samu yawan ahali ana samun gurɓattattu kamar haka, ku de kawai ku tayata da addu'a”
Kasa cewa komai ya yi saboda takaici, ya wuce sama, sai da ya yi nadamar sauƙowa ƙasan, dan da ace be sauƙo ba, da ba zai zo ya ga wannan abun takaicin ba.
*Murtala Mohammed International airport, Lagos.*
TAUQEER FARUQ AGHA POV.
Cike da mutsuwa ya fito daga terminal. Sanye yake da wata farar long sleeve tees, sai farin wandon rigar, ƙafafunsa sanye da fararen sneakers. Kansa sanye da p-cap. Fuskarsa kuma rufe da mask, ya rufe fuskar tasa ne, saboda ba ya son takurawar jama'a, duk da kasancewarsa me nuna so da ƙauna ga masoyansa, amma yau a gajiye yake, ba ya son kowa ya gane shi. Kansa a ƙasa yake tafe. Yayinda duffle bag ɗinsa ke riƙe a hannunsa na dama.
Daga can nesa ya hangi Deena ita da securities ɗinta biyu, sai wani yauƙi take kamar kuɓewa. Ita ga celebrity. Kuma tun daga nesan ya iya gano kalar shigar dake jikinta, hakan ya sa ya ja tsaki yana kawar da kansa.
Yau shi banda ƙaddara ma me zai yi da wannan abar, dan ba dan an cusa masa ita ba, babu yanda za ayi mutum kamar shi ya yarda da aurenta. Tsabar rashin kunya irin ta Deena ita da kanta ta kaiwa iyayensu maganar tana sonsa, hakan yasa iyayensu maza suka tambaye shi; shin ya na sonta?, be san ya aka yi ba, amma haka ya ji bakinsa ya masa nauyi a lokacin, ya kasa amsa musu da a'a, dan ko da ace zai amsa to amsarsa za ta kasane a'a ce. A rayuwarsa ya tsani mace mara kamun kai, ita kuma Deena rashin kamun kai shi ne adonta.
“Laaa! Momy! Deena Agha!”
Cewar wata yarinya cike da ɗaukin ganin jarumar dake burgeta. Mahaifiyar yarinyar da suke tafe tare ta kalli wurin da Deenan ke tsaye, sannan tace.
“Mu je ku ɗuki hoto mana”
“Ki na ga za ta yarda?”
“Me zai hana? Je ki gwada”
Cike da ɗoki yarinyar ta isa wurin. Bakinta har bayan kunne. Securities ɗin ne suka fara dakatar da ita.
“Ke! Ina za ki?”
Ɗaya daga cikinsu ne ya daka mata tsawa cikin garjejeyar muryarsa. Hakan yasa yarinyar tsorata, har wayarta na faɗuwa ƙasa.
“Ku... Ku yi haƙuri... Hoto nake so na ɗauka da... Da Deena!”
A tare securities ɗin suka juya suka kalli Deena. Wadda ta sauƙe sun glasses ɗin idonta, tana watsawa matashiyar kallon banza.
“Na miki kama da wadda za ta yi hoto da ƙazama irin ki? Dallah malama ja ƙazamin jikinki ki bar nan wurin!”
Nan take ƙwalla ta sauƙo daga idon matashiyar, dan duk sai ta ji ra muzanta, shin lefi ne dan ta nunawa wanda take so soyyaya?.
Deena ta ci gaba da taunar chewing gum, rashin mutunci da kuma muzanta ɗan adam hallayarta ce tun tana yarinya, bata ganin kowa da gashi, in dai kai ba wani ba ne, to baka isheta kallo ba, ta tsani wanda bai isa ba, musamman 'ya'yan talakawa, dan cewa take sun fiya tsiwa da iyawa, su ba 'ya'yan uban kowa ba, sai shegen ji da kai.
Matashiyar ta share ƙwalla tana tsugunnawa dan ɗaukan wayarta. Ta kai hannun za ta ɗauki wayar, ta ga wani farin hannu ya rigata ɗaukan wayar. Hakan ya sa ta miƙe tana kallon mamallakim hannun.
Ko kafin zuciyarta ta faɗa mata cewar bata san shi ba, mutumin ya kai hannunsa ya cire mask ɗin fuskarsa. Idanuwanta ta zaro waje tana kallonsa, nan take ta nemi ƙwallar tata ta rasa, dan ganin babban masoyinta, wanda ya fi Deena matsayi a zuciyarta.
“Password?”
Wannan sassanyar muryaryar tasa ta tambaya yana buɗe wayarta.
“Ummm?”
Ta tambaya idonta a kansa, dan ta kasa gane ma'anar password ɗin.
“Ina nufin password ɗin wayarki”
Bakinta na rawa ta ƙifta idonta.
“4457”
Password ɗin ya buɗe, ya lalubo camerar cikin wayar, kafin ya shiga, ya matsa kusa da ita yana ɗaga wayar sama. Tsabar mamaki da farin cikin da take ciki, sai ta kasa kallon cameran, ta ci gaba da kallon fuskarsa, kuma a haka ya ɗauki hoton.
Ya sauƙe wayar yana miƙa mata, kamar wata doluwa haka ta ɗago da hannuta ta karɓi wayar. Ido ɗaya ya ƙifta mata yana murmushi, sannan ya barta tsaye da baki a sake.
Mask ɗinsa ya mayar yana murtike fuska, bayan da idonsa ya sauƙa a kan Deena, wadda ita kuma take masa nata murmushin, kansa ta iyo zata rungumeshi ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. Ba ta ji daɗin hakan ba kamar kullum, ita har yanzu gani take wayewar Tauqeer ta banza ce, tun da har ba ya irin halayenta. Duk wanda baya hallaya irin tata ganinsa take wawa.
Ya raɓata ya wuce ya nufi motar da ta zo da ita, ɗaya daga cikin securities ɗin ne ya buɗe masa motar, ya shiga ba tare da ya jirata ba. Haka ta zagayo ita ma ta shiga ta ɗayan ɓangaren. Kuma har suka kai gida bai ko ƙara kallonta ba, dan daga zarar ya kalleta sai ya ji kamar zunubi yake aikatawa.
A. ISAH CE✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE...💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 03*
~~~
*GrowTech. AI centre, No. 10, 23rd street, Astoria, NewYork, USA.*
Cikin sassarfa wani farin dattijon bature ke tafe, sanye yake cikin baƙar suit, bayan sa kuma biye da wasu matasa wanda yanayin biyyayar da suke masa ko a tafiyarsu ke nuna cewa shi ne gaba da su. Ganin kamar inda suke san nufa ya yi masa nisa ya sa dattijon fara gudu, hankali a tashe ya kutsa kai cikin babban ɗakin kula da computers na tsaron ma'aikatar.
“Sir! Sir!, All of our computers have been hacked by an unknown hacker!”
Cewar wata matashiya tana miƙewa tsaye daga kan kujrar da take. Cikin halin ruɗu, baturen ya kalli babban allon glass dake manne a jikin wata katanga dake ɗakin, wanda yake ƙunshe da hoton gaba ɗaya fuskokin computers ɗin ma'aikatar.
Kamar wanda be yarda da abun da idonsa ke gane masa ba, ya rarumi keyboard ɗin wata desktop dake wurin, ya shiga dannawa a kiɗime, idonsa manne da babban allon glass ɗin. Sai de kuma duk dannawar da yake a banza, don kuwa dannawar tasa bata hana madatsin na'urar kwasar bayanan da ya fara ba.
Ɗagowa ya yi daga kallon desktop ɗin, gumi na tsatssafo masa, hannu ya sa a aljihun suit ɗin jikinsa ya ɗauko hanki, sannan ya shiga goge gumin.
“Did ram RAM arrive today?”
Ya tambaya, idonsa na hango masa mafita a tare da bayyanar RAM ɗin ɓaro-ɓaro.
“No sir, he didn't appear today” wannan macen ta amsa masa.
“Get in touch with him, now!”
*No.675, 361 Stagg Street, Brooklyn, New York, USA.*
Abu na farko da za ka farra kalla a ɗakin shi ne, computers, domin kuwa kusan computers biyar ne ke kunne a cikin ɗakin, haka zalika ɗakin babu haske sosai, sai na wata shuɗiyar fitila dake ci daga can wani ɓangare na ɗakin, idan kuma ka ci gaba da wilƙita idonka a ɗakin za ka iya hangowa ƙarafunan robot da ake haɗawa, wasu an haɗasu, wasu kuma ana kan haɗasu.
Daga can jikin wata babbar desktop kuma, wani matashi ne zaune kan kujera, ya jingina bayansa da kujerar, yayin da hannyensa biyu duka ke kan keyboard, kuma cikin sauri-sauri yake daddadanawa, sannan idonsa manne kan screen ɗin desktop ɗin, kai ka ce bai ma san madannan da yake dannawa ba. Hannyensa duka biyu na sanye da agogo. Sanye yake cikin wando jeans, da Oxford casual shirt a sama, kasancewar maɓallayen casual shirt ɗin ba a ɓalle suke ba, ya sa za ka iya ganin ash T-shirt ɗin dake ƙasanta. Sumar kansa na da tsayi sosai, don daga baya ta sauƙo har zuwa wuyansa, yayin da daga gaba kuma ta sauƙo kan goshinsa. Sumar kan nasa na da kyau da kuma santsi, don tsabar santsinta har wani kannaneɗewa take. Dogon gemun da ya tara a fuskarsa ne ya ɓoye fiye da rabin kammaninsa, idonsa sanye da farin glashi, yayin da gefen wuyansa ta ɓangaren dama, ke ɗauke da wani zanen baƙin tatto, wanda aka rubuta ‘RAM’.
“Feeq! Feeq!...”
Tun daga waje yake jin muryar sanyin idaniyarsa na kiran sunan, amma sai ya ƙi amsawa, dan gani yake kamar idan ya kauda idonsa daga kan screen ɗin na sakan ɗaya duk tarin tilin aikin da ya yi a ranar zai ruguje.
“Feeq!”
Ta kuma kira tana buɗo ƙofar ɗakin. Matar ta kalleshi tana girgiza kai.
“Wai ba ka ji ina ta kiranka?”
Ta faɗi tana duban bayansa. Ba tare da ya juyo ya kalleta ba, salihar muryarsa ta furta.
“Na ji Maa, wani abu nake son ƙarasawa”
“Ka aje abun da kake ka fito ko sai na ɓata maka rai?”
Ta tambaya ranta na shirin ɓaci. Kamar wanda aka cewa tana ganinsa, ya shagwaɓe fuska yana faɗin.
“Maa tun safe nake tsara sashen magana na AI humanoid robot ɗina, amma ban gama ba, Wallahi daga na gama zan fito”
“Kada Allah ya sa ka fito ka ci abincin, ai cikinka ne ba nawa ba!”
Ta ƙarashe tana rufowa ƙofar ɗakin. Ba dan ya so ba, haka ya dakatar da komai, sannan ya ɗaga hannyensa sama yana miƙa. A hankali cikin natsuwarsa ya miƙe tsaye, sannan ya nufi ƙofar balcony yana gyara rigarsa da ta tattare daga baya saboda zaman da ya sha.
A hankali ya buɗe ƙofar, sannan ya kutsa kai. Tsayawa ya yi a jikin ƙarfen balconyn, ya kafe windown ɗakinta da ido. Don ya san za ta iya fitowa a lokaci irin wannan. Kuma kamar da ya auna. A dai-dai lokacin, aka buɗe tagar gidan dake facing nasu. Sannan fuskar wata matashiya ta bayyana. Kallo ɗaya ya mata,zuciyarsa ta buga, kamar wadda take shirin fitowa daga allon ƙirjinsa.
Yawu ya haɗiya yana gyara tsayuwarsa, tare da duba agogon hannunsa na hagu, ganin bugun zuciyarsa ya ƙaru da kashi 5 ne ya sa ya sauƙe hannun ya ƙara maida dubansa kan tagar gidan. Zuwa lokacin ita ma ta fito zuwa nata balconyn. Kallonta ya ci gaba da yi, zuciyarsa na rawa.
Wata biyar da suka wuce ya fara ganinta, lokacin da ta kama wannan gidan dake kusa da nasu gidan, kuma tun a ganinsa na farko da ita zuciyarsa ta faɗa cikin wani irin yanayi mara fasaltuwa, shi kansa ba zai iya cewa ga abun da yake ji a kanta ba, amma de ya san a duk sanda zai ganta sai bugun zuciyarsa ya ƙaru...
Tunaninsa ya katse a sanda ta ɗago masa hannu tana murmushi, hannayensa ya sauƙe, waɗanda ke harɗe a ƙirjinsa ya ci gaba da kallonta yana murmushi.
“How is your day going?”
Ta tambaya cikin ɗaga murya, dan akwai 'yar tazara a tsakanin gidajen nasu.
“Good, Alhamdulillah”
Sai ta gyaɗa kanta tana ƙare masa kallo. Ita dai kam yana burgeta, duk da ba ta taɓa ganin fuskarsa duka ba, saboda gemun da ya rufe masa rabin fuska, amma a haka kawai idan ka kalleshi za ka san cewa yana da kyau. Ita ba ta san ɗan wani ƙabila ba ne, amma yana mata kama da baƙaƙen indians, yanayin fatar jikinsa da take Chocolat color, da kuma sunar kansa da take da laushi ko a ido, shi ne yake sawa a kallon farko da mutum zai masa ya ɗauka cewar ba'indiye ne, duk da shi ba fari ba ne.
Jin ƙarar wani abu na tashi a ɗakinsa ya sa shi juyawa ya kalli ƙofar balconyn. Sai kuma ya juyo ya kalleta.
“Bye!”
Ya faɗi yana ɗaga mata hannu. Ita ma hannun ta ɗaga masa tana murmushi.
Ɗakin binciken nasa ya koma ya shiga duba computers ɗin nasa da yake da tabbacin sautin daga su yake fita. Daga cikin system ɗinsa sautin kiran ke tashi, dan haka ya zauna kan kujerar dake gabanta yana duba kiran. Duk da ya san babu me iya masa kutse kamar haka idan ba daga CrowTech ba, wato ma'aikatar da yake aiki, ya san cewa wata ƙila kiran wayarsa suka yi ba su samu ba, shi ya sa suka datsi na'urarsa don su aiko masa da kiran.
“Ram, ana buƙatarka a center, yanzu-yanzu!”
Abun da wani matashin bature ya faɗi kenan, bayan da Ram ɗin ya ɗaga kiran. Sai da ya ɗan juya kansa, sannan yace.
“Ok, on my way”
Ya faɗi yana katse kiran. Miƙewa ya yi, ya nufi inda backpack ɗinsa take, ya ɗauka, sannan ya saka laptop ɗinsa a ciki, ya goya a bayansa ya fita daga ɗakin. Ƙasa ya sauƙa, inda yake da tabbacin Maansa na can.
Ilai kuwa, Zaune ya sameta a kan kujerar danning tana cin abinci. Harara ta maka masa tana kawar da kai. Shi kuma sai ya mata murmushi yana takawa zuwa gareta. Peck ya mata akai yana zama kusa da ita.
“Ga ni na fito fa”
“Ina za ka je?”
Ta tanbaya ganinsa da jaka, ya ɗan yi shiru yana kallon abar son nasa. A kallo ɗaya idon ka musu za ka shaida wannan kalmar ta 'dangantaka' ita ce ke a tsakaninsu, duk da tarin gemun da ya rufe masa fuska bai hana kammaninsa da nata fitowa ba, banbancinsu ɗaya ne, kalar fatarsu, ita ta kasance fara ce sosai, yayin da shi kuma tasa take brown colour,kamar ta baƙaƙen indiyawa.
“Daga wurin aiki ne aka kirani, suna buƙatata”
Ya amsa mata yana ci gaba da kallon kyakkyawar fuskarta.
“Lami! Lami!”
Ta shiga ƙwala kiran Lami tana kallon ƙofar kitchen. Ram ya dafe kansa yana girgiza shi, be san yaushe Maan nasa za ta iya faɗin sunan robot ɗin dake girka musu abinci a gidan ba.
“Maa Kiyara,! Kiyara ne sunanta ba Lami ba”
Ya faɗa mata abun da ya saba faɗi a duk lokacin da ta yi rafkanuwa wurin kiran sun robot ɗin. Maa ta taɓe baki tana aje cup ɗin hannunta.
“Ni fa ba zan iya da wannan kiyare-kiyaren naku ba, na riga da na saba da sunan Lami, don haka Lami zan ce ehe...”
Ya yi murmushi yana tuno da Lami ɗin. Lami ta kasance 'yar aikin da take taya Maa aiki a gidansu dake Nigeria, ta jima tana aiki a gidan,kafin suka kamata da lefin sata, shi ne suka sallameta, kuma bayan sun sallametan ne Ram ɗin ya haɗa mata Humanoid android robot, wada ya ƙirƙireta akan girki da gyaran gida kawai, kuma tun daga lokacin ita ce take girki a gidan, har zuwa yau. Ita kuma Maa ta riga da ta saba da kiran sunan Lami a duk sanda take buƙatar a mata wata hidima, shi ya sa ko bayan da ya ƙera Kiyara robot bata dena kiranta da sunan ba.
“Maa!”
Wata murya sak irin ta Maan ta faɗi daga kitchen, kafin suffar silver humanoid robot ɗin ta bayyana a gabansu, a yanayin jikinta macace, kasancewarta macen, amma kuma jikinta babu kaya, da zallarƙarfen silver kawai aka yita, yanayin ƙirarta irin mutum ce, tafiya ce kawai ba ta yi, sai wasu tayoyi da ya saka a ƙasan ƙafafunta. Kuma cikin tafiyarta ta tayar ta iso gabansu tana kallonsu.
“Ki sakawa Feeq abinci a filas, zai tafi wurin aiki”
“Ok Maa!”
Har ta juya Ram ya kirata, jin muryarta ta fito kamar ganga ta fashe.
“Kiyara wait”
Kiyara ta tsaya kana ta juyowa. Miƙewa ya yi ya isa gareta.
“Me ya samu muryarki?”
Kiyara ta ci gaba da kallonsa da idanuwanta da suka kasance haske kamar tocila.
“Sashen magana... Na jikina... Ne... Ya lalace!”
Ta faɗi muryarta na ƙara hargitsewa.
“Bolbo kawo min screwdriver!”
Ram ya ƙwalla kiran sunan. Bayan shuɗewar wasu sakkani, sai ga wani abu ya fito daga ɗaya daga cikin ƙofafin dake falon, abun de gajere ne, kuma ba normal tafiya yake ba, gangarawa yake a ƙasa kamar ball, a kallo ɗaya de ba za ka iya fasalta yanayin suffar abun ba. Tsayawa ya yi a kusa da Ram, sannan fitar da wani dogon abu me kama da hannu, ya miƙawa Ram screwdrivern da ya buƙata, Ram ya karɓa.
“Thanks Bolbo1”
“You got it, Ram!”
Muryar abun me kama da ta kiriku ta faɗi yana komawa ɗakin da ya fito daga cikinsa.
Ram ya zagaya zuwa bayan Kiyara, sannan ya danna wani switch a bayan nata. Nan take hasken idon Kiyaran ya ɗauke, kanta ya sunkuya ƙasa, saboda switching off ɗinta da ya yi. Wani murfi ya buɗe a bayanta, ya yi amfani da screwdrivern hannunsa ya gyara wurin da ya samu matsala a jikinta, ya mayar da murfin ya rufe, sannan ya danna switch.
“Hello Kiyara H178rs9Q12!”
Ya faɗi yana kallon fuskarta.
“Hey RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD!”
Muryar Kiyara da ta dawo dai-dai ta faɗi. Ram ya yi murmushi yana aje screwdrivern a kan danning.
“Yi sauri ki kawomin abincin”
Kiyara ta juya a kan tayoyin ƙafarta, ta shiga kitchen. Jim kaɗan ta dawo ta kawo masa wani flask me ɗauke da abincin da ta girka a ranar, Ram ya karɓa yana mata godiya, sannan ya saka a backpack ɗinsa ya yiwa ma Maa sallama, ya fita.
A ƙofar entrance ya tsaya yana kallon kekensa dake ake a gefen ɗan ƙaramin compound ɗin gidan. Kasancewar keke yake hawa idan yana USA, dan motarsa tana Nigeria, jakarsa ya goya a bayansa, sannan ya isa wurin keken, ya ɗauka, ya buɗe ƙofa ya fice, ya hau kan titi ya fara tsuga gudu.
Kuma bai dakata ba sai da ya iso GrowTech, haɗɗaɗɗen kamfanin sarrafa na'ura me ƙwaƙwalwa, Kamfanin ƙirƙirar robot, kuma Centre ɗin AI (Artificial Intelligence) da ake ji da shi a kaf faɗin USA. Ginin kamfanin ya kasance na beni me hawa 13, yanayin kyan ginin kaɗai ya isa ya tabbatar maka da muhimmancin ma'aikatar.
A parking lot ɗin dake ƙasan kamfanin ya aje kekensa, sannan ya nufi ƙofar entrance. Yana tura ƙofar wani abu ya zo ya wuce ta saman kansa yiffff, hakan ya sa ya kaucewa abun yana binsa da kallo.
“My bad Ram!... Sorry!”
Muryar Henry dake riƙe da remote control ɗin drone ɗin ta faɗi yana kallonsa. Ram da ya juya yana kallon dron ɗin da ya wuce shi, ya juyo ya kalli Henry ɗin. Kafin ya sakar masa murmushi yana faɗin.
“Ba komai”
Kafin ya raɓa Henry ɗin ya wuce. Shi kansa reception ɗin ma'aikatar abun kallo ne, robotics da harkar AI ce kawai za ka yi ta gani a wurin iya ka ganin idonka. Ko da Ram ya isa elevator shiga ya yi, sannan ya danna hawa na 10, inda office ɗinsa yake.
“Kai tun ɗazu ake ta jiranka amma sai yanzu ka zo?”
Abu na farko da Abdulrahman babban abokinsa a ma'aikatar ya fara faɗi kenan lokacin da suka haɗu. Ram ya sosa wuyansa setin inda tattoo ɗin sunansa yake, sannan yace.
“Wai me yake faruwa ne?”
“Wani tantirin aka samu ya datsi babbar na'ura!”
Ram ya kalleshi na wasu 'yan sakkani. To wai duk akan an datsi na'ura shi ne ya ga ma'aikatar ta rikice?, shi ai a nan bai ga abun tada hankali ba.
“Ram! Mr. Rafeeq!”
Aka ƙwala kiran sunayen biyu daga bayansu, hakan ya sa su duka suka kalli wurin, Isabella ce ta iso wurin tana ta haki saboda gudun da ta yi.
“Sir Thomas yana jiranka a control room”
Ta faɗi tana juyawa, ba tare da Ram da Abdulrahman sun ƙara cewa komai ba, suka bi bayanta har zuwa control room ɗin.
“Na gode Allah da ka zo Ram!”
Cewar Mr. Thomas yana kallon Ram ɗin da ya shigo wurin. Ram ya shiga bin ƙaton allon glass ɗin dake sama.
“Gaba ɗaya na'urorinmu aka datsa, sannan ana ɗaukar bayanan mu na sirri zuwa wata computerr”
Cewar Isabella, Ram ya ja kujera ya zauna yana sauƙe jakar bayansa.
“Dan Allah Ram ka san abun yi, sun kusa kwashe duka bayananmu”
Cewar Mr. Thomas hankali tashe. A nutse Ram ya fito da laptop ɗinsa dake cikin jaka, sannan ya aje ta akan wani table yana buɗeta. Danne-danne ya shiga yi yana duba allon glass ɗin nan. Kowa ya yi shiru, ana jiran ganin warwarewar matsalar, saboda tun da ha Ram ya zo, komai ya zo ƙarshe. Cikin abun da bai fi muntuna uku ba, ya cire wani flash drive daga jikin laptop ɗinsa ya miƙawa Isabella.
“Ki yi sauri ki saka a jikin babbar na'urar”
Ta karɓa da sauri tana nufar wurin babban system ɗin, buɗewa ta yi, sannan ta saka flash ɗin. Daga nan kuma sai kallon kowa ya koma kan babban allon glashin nan. Sakan ɗaya... Biyu... Uku...
A sakan na uku ne, komai ya tsaya cak, duka naurorin suka ɗauke. Mr. Thomas ya buɗe baki zai yi wa Ram magana, na'urorin suka kawo wuta. Komai ya dawo dai-dai, na'urorin suka dawo under control ɗinsu.
Sauran ma'aikatan wurin suka sa ihu, har da masu tafi. Ram ya miƙe yana rufe laptop ɗinsa. Mr. Thomas ya dafa kafaɗarsa cike da alfahari, don zai iya cewa kaf ma'aikatar tasu babu wanda ya kai Ram fasahar sanin kan na'ura me ƙwaƙwalwa, haka robot.
“Ina alfahari da kai Mr. Rafeeq”
Ram ya yi murmushi yana sosa gemunsa.
“Godiya nake”
“Kwana biyu na lura da baka zuwa, fatan dai lafiya?”
Mr. Thomas ya tambaya, a sanda suka fito daga control room ɗin. Ram ya gyara zaman backpack ɗin

Please Login or Register in order to submit comment