Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi sa kallo. Kafin ta yunƙura da nufin tashi, amma sai ta ji hannayenta a ɗaure tamau, ta motsa ƙafafunta, suma ta ji su a ɗaure, hakan ya sa ta kalli jikinta. Ta ga cewa a ɗaɗɗaure take. Da ƙyar ta motsa bakinta cikin faɗin.
“Innalillahi wa inna'ilaihi rajiun!”
Saboda kanta da ta ji ya sara. Motsi ta ci gaba da yi da ƙafafuwanta da kuma hannayen. A ƙoƙarinta na kunce ɗaurin da aka mata.
Wata nurse ce ta zo wucewa ta ƙofar ɗakin, kuma ta cikin ƙarafunan da suka rufe ƙofar, ta hangi matar dake cikin ɗakin na jijjiga gadon. Idanuwanta ta zaro cike da mamaki. Dan abun akwai abun mamaki, idan ta canka dai-dai, yau kusan shekaru 24 tana asibitin, ba ta taɓa ko da motsa hannunta ba, amma yau sai ga ta tana jijjiga.
Da gudu ta juya ta nufi office ɗin Dr. Bashir. Tana zuwo ko neman izini ba ta yi ba ta shiga tana haki. Dr. Bashir dake waya ya sauƙe wayar daga kunnesa ya dubi nurse ɗin cikin ɓacin rai ya furta.
“Baraka wannan wani irin rashin hankali ne? Za ki shigo min office babu ko knocking”
Ƙirjinta ta dafe tana haki.
“Dr wannan matar dake cikin room No.36 ce ta farka!”
Cikin Dr. Bashir ya bada sautin Ƙuuuuuu!. Ba shiri ya miƙe tsaye waya riƙe a hannunsa, baki sake yake kallon Baraka. Nan take zufa ta fara keto masa dan tsabar tashin hankali.
Da gudu ya fita daga office ɗin nasa Barakan na biye da shi har suka kai ƙofar ɗakin. Ji ya yi yana shirin zamewa zuwa ƙasa. Saboda ƙafafuwansa da suka ɗauki rawa. A sanda ya ɗora idonsa a kan matar dake kwance a kan gadon tana ci gaba da jijjiga shi a ƙoƙarinta na ƙwatar kanta. Kai tsaye ƙwaƙwalwarsa ta hasko masa wani hoto da ya wuce shekara 24 baya.
Cikin wani dare ne da ba zai iya manta shi ba. Wata mata ta zo asibitin. Ta sameshi har office ɗinsa, ta bashi maƙudan kuɗaɗe, sannan ta ce masa akwai wata mata da ta zo da ita, tana so ya aje mata matar a nan asibitinsu, ita kuma ta masa alƙawarin za ta riƙa bashi kuɗaɗen da suka ninka yawan albashinsa duk wata. A lokacin sai da ya tsorata da tunanin idan matar ta farka ta ganta a gidan mahaukata alhalin ita da hankalinta me zai faru? Amma matar me suna Hajiya Zayya! Ta sanar masa da cewar har duniya ta naɗe matar ba za ta taɓa farkawa daga wannan doguwar suman da ta shiga ba. Buƙatarta kawai ya aje mata ita a nan asibitin nasu.
Kuma har a watan da ya wuce sai da Hajia Zayyan ta bashi kuɗaɗen da ta saba bashi duk wata. Yanzu kuma ga wani zance, matar da aka kawo ta farka, ba ma haka ba, tana cikin hayyacinta, dan a sanda ta lura da tsayuwar mutane a bakin ƙofar ɗakin ta kallesu tace su zo su kunce ta.
Juyowa ya yi ya kalli Baraka.
“Je ko kawo min allurar Midazolam”
(Midazolam allura ce da kan gusar da hankalin mutum ta saka shi bacci nan take. An fi yawan amfani da allurar lokacin da za'a yi surgery)
Da gudu Baraka ta bar wurin, har ta je ta dawo yana tsaye a ƙofar ɗakin yana kallon matar da bai san ko sunanta ba. Shi ne ya buɗe kwaɗon ƙofar, sannan ya shiga, Barakan na biye da shi, hannunta riƙe da allurar.
Ko da suka shigo sai Rahila ta dena ƙoƙarin kunce kanta, ta shiga rarraba idonta a kansu. Kuma sai da ta gansu ta tabbatar da cewar a asibiti take. Tun da kayan likitoci ne a jikinsu. Ganin namijin ya karɓi allurar yana haɗawa ya sa Rahilan faɗin.
“Likita! Likita! Ina 'yata?! Ina jaririyata take?! Dan Allah ka kawomin ita, ku bani 'yata na ganta...”
Da ido Dr. Bashir ya yiwa Baraka alama da ta kewata ta ɗayan ɓarin ta rike masa ita. Tuni Rahila ta fara hawaye tana kallonsu.
“Dan Allah ku bani 'yata! Ku... Ku... Ku bani jaririyata... 'yata ce! 'Yata! 'Yata!.... 'Yata...”
Sai kuma ta yi shiru, saboda allurar da ta soma aiki a jikinta. Tun tana gani dishi-dishi, har ganinta ya ɗauke duka, jikinta ya saki, bakinta ya buɗe, kanta ya koma gefe.
Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Dr. Bashir ya sauƙe, sannan ya juya ya fita, Baraka biye da shi. Ko da ya shiga office ɗinsa sai ya kasa sukuni, ya ɗauki robar ruwa ya sha, ya ja kujera ya zauna yana sharce gumi. Sannan ya janyo wayarsa ya lalubo lambar Hajiya Zayya, ya aika mata kira, ringing ɗaya... Biyu... A na ukun ta ɗaga.
“Hajiya akwai matsala!”
Shi ne abun da ya fara faɗi tana ɗaga kiran. Daga can Agha Mansion Hajiya Zayya ta miƙe tsaye cikin matsanancin tashin hankali. Da ma tun da ta ga kiransa jikinta ya bata akwai matsala. Wata busasshiyar iska ta haɗiye a maƙoshinta, sannan ta ce.
“Me yake faruwa?”
Gumi Dr. Bashir ya kuma sharcewa.
“Mara lafiyar nan ta farka!”
A hankali ba tare da ta ce komai ba ta sauƙe wayar daga kunnenta. Ta yi cilli da ita kan gado. Sannan ta shiga safa da marwa a ɗakinta. Me ya sa Rahila za ta farka yanzu? Me ya sa Rahila ba ta farka ba sai da ta ga tana daf da cika burinta?. Duk laifin Ƙundus ne, tun a waccan lokacin ta so a kashe Rahila gaba ɗaya, amma ya hanata, ya ce wai bai kamata ta mutu yanzu ba. 'Yar tata kawai ya amince da a kashe. Kuma a ranar ta dawo gida da jaririyar. Ta samu Kande, ɗaya daga cikin 'yan aikin gidan, wadda ta yarda da ita, ta kuma san dukanin surrukanta, ta bata jaririyar tare da umartarta da ta je ta binne jaririyar da ranta. Kuma Kanden ta karɓi jaririyar, har ma ta je ta aiwatar da abun da ta umarceta.
Komai ya tafi dai-dai a lokacin, ta gama da wannan matsalar, to me zai sa wata matsalar ta sake ɓullowa kuma? Dole ne ta yi wa tufkar hanci, ita ce Zayya! Zayyar da babu wanda ya isa ganin bayanta sai idan ita ta so, babu ma ta yanda za ayi ace ta saduda, dole ta nemawa kanta mafita. Wani murmushi ta saki, a lokacin da ƙwaƙwalwarta ta hasko mata mafita ɓaro-ɓaro.
Bakin gadonta ta samu ta zauna tana ƙirga biyar zuwa goma. Ba a haifi wanda zai kawo ƙarshenta ba har yanzu, ta sanda yadda za ta yi da Rahila, kamar yadda ta shafeta daga tunanin kowa na gidan, ciki kuwa har da Tayyab, haka za ta shafeta daga doron duniya!. Shi kenan kuma, wannan matslar ma ta zo ƙarshe. Ta kuma yin wani murmushin.
Tunaninta kenan, kuma tana wannan tunanin ne ba tare da sani zuwan wata ƙaddara me tafe da HASKEn da zai kawo ƙarshen duhun da ta mamaye makusantanta da shi. Duhun da ta fake a cikinsa tana cutar da makusantanta.
______________
_Ina tunanin daga wannan shafin za mu tsunduma cikin labarin_
_Dan duka wannan sharar fage ce_
_Mun riga da mun kamo bakin zaren labarin_
_To sai ku gyara zama, dan a yanzu ne za mu fara saƙa zaren labarin bi da bi..._
_Da fatan za ku kasance tare da ni_
A. ISAH CE ✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE...💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 08*
~~~
*Makoko, Lagos state, Nigeria.*

DIYA POV.
“Dan Allah Fa'ee ki yi sauri!”
Diya ta faɗi yayin da take tsaye a ƙarshen rumfar gidansu tana kallon gidansu Fa'een da take ta jira tun ɗazu, dan ta zo su tafi wurin aiki.
“Yi haƙuri Diya! Ga ni nan zuwa”
Muryar Fa'ee ta bata amsa daga cikin gidan. Cike da ƙosawa Diya ta juyo ta kalli Gigi, Papi da Ekene dake zaune a kan rumfar gidansu. Ekene na kwance a kan katifa, dan har yanzu jikinsa babu ƙwari, saboda ya doku ba ƙarya. Papi kuma na zaune a wurin da ya saba zama kullum, yayin da Gigi ke zaune a kan kujera ta yi tagumi.
Tun shekaran jiya da suka dawo daga police station, Diya ta lura da Gigi da kuma Papi suna cikin damuwa, musamman ma Gigi. Amma ko da ta tambaya sai tace mata babu komai. Sunkuyawa ta yi tana ɗaura igiyar canvas ɗinta da suka tsufa sosai tana faɗin.
“Gigi wai ba za ki faɗamin abun da yake damunki ba?”
Ta tambaya ba tare da ta kalli Gigin ba. Kuma tambayar da ta mata ce tasa Papi da Ekene kalon Gigin a tare. Gigi ta sauke hannyenta daga kan kuncinta tana kallon Diya. Ƙwalla na ciko idonta tace.
“Babu komai fa nace miki!”
Diya ta ɗago ta dubeta.
“Gigi...”
Ba ta kai ga faɗin abun da ke bakinta ba Fa'ee ta shigo rumfar a gaggauce tana faɗin.
“Muje Diya, na gama shiryawa!”
Kallon Fa'een ta yi, kafin ta juyo za ta yi wa Gigi magana, amma sai Gigin ta yi saurin cewa.
“Ya kamata ku tafi Shola, kun makara fa”
Shiru ta yi tana ci gaba da karantar Gigi ɗin, kafin ta juya tace da Fa'ee.
“Muje!”
Juyawa suka yi suka hau kwale-kwalen Lamu abokin Ekene dake jiransu tun ɗazu. Kuma shi ne ya fitar da su har bakin gaɓar yankin nasu. Bus ɗaya suka hau, kafin suka rabu a victoria island. Dan ita Fa'ee kamfanin da take aiki a can cikin victoria island ɗin yake.
Cikin hanzari Diya ta faɗa kitchen tana ƙoƙarin saka apron ɗinta. Dan ta makara ba kaɗan ba.
“Diya Shola!”
Cak ta tsaya da ɗaura apron ɗin da take. Zuciyarta ta buga sau biyu a lokaci guda. Sakamakon jin muryar MD ta kira sunanta. Yawu ta haɗiye, sannan ta juya ta kalleshi a tsorace. Wannan mayen kallon da ya saba binta da shi yau ma shi yake jifanta da shi. Kanta ta sunkuyar ƙasa tana ƙara matse jikinta da drawern da suke aje apron ɗinsu ta aiki.
MD ya lashi lips ɗinsa yana ci gaba da mata wani irin kallo. Kafin yace.
“Ki zo office ɗina, ina son ganinki!”
Da ƙyar ta iya gyaɗa kanta. Sai da ya kuma mata kallon sama da ƙasa, sannan ya juya ya bar wurin. Da ƙyar ta sauƙe wata ajiyar zuciya. Ƙara tsorata ta yi jin an kuma shigowa wurin. Amma sai ta ƙara sauke wata ajiyar zuciyar ganin Orisa ce, dan da farko ta yi tunani cewa shi ne ya dawo.
“Me yace miki?”
Orisa ta tambaya a sigar gulma tana ƙasa da muryarta. Diya ta ɗan kalleta kaɗan.
“Wai na je na sameshi a office”
Ta faɗi muryarta na karkarwa. Kamar me shirin fashewa da kuka. Orisa ta dafe ƙirji tare da zaro ido.
“Sai ki yi a hankali, tun da kin san halin mutumin nan, ba ɗan arziƙi ba ne”
Tsoro ya ƙara kama Diya. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ta shiga tafiya har ta kawo office ɗin nasa dake cikin restaurant ɗin. Sai da ta shaƙi iska ta furzar, sannan ta kai hannunta kan handle ta murɗa, sannan ta shiga da sallama a tsorace.
Tsaye ta sameshi jikin fridge yana zuba juice a cikin wasu wine guda biyu. Tana shigowa ya zubo mata ƙwalƙwalan idanuwansa yana mata irin wannan kallon da ba ta so. Kanta ta sunkuyar ƙasa a sanda ta ga yana tunkarota. A gabanta ya tsaya ya mika mata wine guda daya.
“Karɓi ki sha Baby!”
Wata ƙararrawa Shola ta ji sunan ya doka a cikin kanta. Ba shiri ta zazzaro idanuwanta tana kallonsa. Ido ɗaya ya kashe mata, sannan ya ƙara miƙa mata wine ɗin. Kasa karɓa ta yi, sai ƙwalla da ta fara silalo mata. Ba tare da ta ankara ba ya kamo hannunta ya danƙa mata wine ɗin. Ta ƙara ruɗewa, hannunta ya shiga karkarwa, har wine ɗin ya suɓuce ba tare da ta sani ba.
Kuma ƙarar tarwatsewarsa ce ta dawo da ita hayyacinta. Kusan a tare ita da shi suka kalli fasasshen wine ɗin dake ƙasa, wanda juice ɗin ciki ya zube a kan lallausan carpet ɗin dake ƙasan.
“Ba komai Baby! Za a zo a tsaftace, amma kafin nan, akwai maganar da nake so mu yi!”
Ta ƙara tsorata tana ja da baya. Kallonta ya shiga yi cike da mamaki. Ganin tana niyyar ficewa ya sa shi yin saurin cafko hannunta ya dawo da ita gabansa. Tazarar dake tsakaninsu kaɗan ce, dan hatta da fitar numfashinsa tana ji a kan fuskarta. Idonta ta rintse da sauri tana jan numfashi da ƙyar.
“Babu inda za ki iya guduwa Baby, na san da cewa kin san me cece manufata a kanki, zai fi miki kyau ki bani haɗin kai, komai ya tafi cikin ruwan sanyi. Ina me tabbatar miki da idan hakan ta faru sai kin fi kowa jin daɗi, domin zan wadataki da kuɗaɗen da baki taɓa riƙe kalarsu a rayuwarki ba, amma kuma idan kika ƙi, zan koriki daga aiki, sannan zan tabbatar da baki ƙara samun wani aikin a cikin garin Lagos ba!”
Ya ƙarashe yana sakinta. Da gudu Diya ta juya ta fice daga office ɗin, kuma ba ta tsaya a ko ina ba sai toilet. Ta shiga ciki ta kulle ƙofarsa tana sakin kuka me sauti. Ina za ta sa rayuwarta? Me ya sa wasu mutanen basu da imani? Yanzu ita menene laifinta dan tana neman abun da zata rufawa ahalinta asiri?. Ba zata iya amincewa da ƙudirinsa ba, kuma ba zata so ya koreta daga aiki ba, dan idan har ya koreta ba ta san inda za ta samo wani aikin ba, wannan ɗin ma sai da aka kai ruwa rana sannan ta sameshi.
Kuma ga shi yana faɗa mata cewar zai tabbatar da bata samu wani aikin ba. Ko dan magungunan Papi da suke da tsada da kuma abincin da zasu riƙa kaiwa bakin salati dole ta yi aiki. To yanzu ina za ta sa ranta idan aka koreta?. Silalewa ta yi ta zauna a kan wata kujera dake cikin bayin. Kafin ta kai hannu ƙafarta ta dama, ta ciro ankle bracelet ɗin dake kafar tata, ta riƙeshi a hannunta tana gani. Tun tasowarta abun yake tare da ita, kuma a duk sanda za ta tambayi Gigi na waye?, Sai Gigin tace mata nata ne, kuma abun yana da matuƙar muhimanci a gareta.

*Cactus Restaurant, No. 20 Ozumba Mbadiwe Abe, Victoria Island, Lagos, Nigeria.*

SURAJ POV.
Zaune suke shi da Narjis a kan kyawawan kujerun dake wajen Restaurant ɗin. Yayin da suke zaɓar abincin da za a kawo musu.
“Wallahi Hamma abincin nan wurin yana da daɗi, dan baka taɓa ci ba ne!”
Cewar Narjis ɗin tana ƙarewa kyakkyawan Restaurant ɗin kallo, bayan da suka gama zaɓar abun da suke buƙata. Suraj ya ɗan taɓe bakinsa yana jingina da jikin kujerar da yake kai.
“Haka kika ce dai!”
Ya faɗi yana kallon fitilun wurin da suka ƙara ƙawata wurin cikin duhun magaribar da ya fara shiga. Ga kuma daddaɗar iskar kogin dake bugawa zuwa cikin Restaurant ɗin, kasancewar daga gefen Restaurant ɗin akwai wani kogi.
“Wallahi da gaske nake maka, bari su kawo mana ka ji”
Kansa ya jinjina yana kallon agogon hannunsa. Shi ba dan ma ta takura tace sai ya tsaya sun shigo ba da ba shigowa zai yi ba, suna tafe a mota za su koma gida bayan da suka dawo daga National theatre, ta ce ya tsaya su ci abinci sai su wuce, shi ne fa suka tsaya ɗin.
Abincin aka kawo musu, kuma bayan sun ci suka kwashi kayansu dan su koma gida, kasancewar har magariba ta yi. Ko da suka fito motar Suraj ɗin suka nufa, inda Narjis ta shiga wurin me zaman banza, yayin da shi kuma yake ƙoƙarin buɗe driver seat, idonsa ya kai kanta, tana fitowa daga wata ƙofa.
Cak ya tsaya daga shirin buɗe ƙofar da yake, ya tsaya a wurin yana ci gaba da kallonta. Sanye take cikin kayan da ya ga waiters ɗin wurin na sakawa. Fitulun dake parking lot ɗin ne suka haske masa fuskarta dau. Zai iya cewa yau ma yanayin fuskar tata irin na ranar da ya fara ganinta ne, dan fuskar tata a kumbere take, kamar wadda ta yi kuka, haka kuma babu walwala ko kaɗan a tare da fuskar tata.
“Hamma shigo mu tafi mana, dare na yi fa...”
Narjis ta faɗa tana dubansa, ganin kamar ba shi da niyyar shigowa motar. Juyowa ya yi ya kalleta.
“Narjis kin ganta can!”
Narjis ta kalli inda yake nuna mata tana faɗin.
“Wa kenan?”
“Yarinyar mana”
Ya bata amsa yana rufe ƙofar motar. Kuma kai tsaye Narjis ta fahimci wata yarinya yake magana a kai.
“To ka je ka mata magana mana”
“Allah ko?”
Ya tambaya kamar wani soko, dan shi a irin waɗanan harkokin za a iya kiransa da sokon.
“Eh mana, wata ƙila gida za ta je, ka ga sai mu rage mata hanya. Ko ta ce maka no ka tabbatar ka sata tace yes”
Kansa ya gyaɗa yana nufar inda take, dan zuwa lokacin har ta kai gate. Da sauri ya bi bayanta ya na faɗin.
“Barka dai!”
Diya ta tsaya da tafiyar da take, kuma a hankali ta juyo ta dubeshi, nan take ta ɗan yi wani guntun murmushi.
“Yallaɓai Suraj”
Ta faɗi sunan nasa tana kallonsa, to ya ma za ayi ta manta da sunan wannan bawan Allahn da ya temaketa sosai.
“A'a Suraj dai”
Kanta ta sunkuyar tana faɗin.
“An ya kuwa zan iya faɗa?”
Goshinsa ya tattare cikin alamun kokwanto.
“Me ya sa?... Ai yanzu ba na sanye da kayan 'yan sanda”
Sai ta ɗan yi murmushin da ba ta yi irinsa ba yau, saboda tun zuwanta MD ya ɓata mata ranarta ta yau, sai ta gyaɗa kanta.
“Haka ne”
“Gida za ki je?”
Ta ɗago da kanta tana amsa shi da.
“Eh, lokacin tashina ne ya yi”
“Idan ba damuwa sai mu je na sauƙeki”
Ta yi saurin girgiza kanta.
“A'a Wallahi! Da ka barshi ma”
Shi ma nasa kan ya girgiza mata.
“Ka da ki damu, tare nake da ƙanwata, mu je sai mu sauƙeki Please!”
Ta yi shiru tana jinjina kirki irin na Yallaɓai Suraj, kafin ta gyaɗa kanta, hanya ya nuna mata yana faɗin.
“Za mu iya tafiya?”
Ta dan yi murmushi sannan ta fara tafiya, yayin da shi yake take mata baya. Ko da suka iso wurin da motar take sai ya ga Narjis har ta fito ta koma gidan baya. Ko da ya kalleta sai ta kanne masa ido ɗaya, murmushi ya mata yana buɗewa Diya ƙofar motar ta gidan gaba. Diya na ta mamaki ta shiga motar.
“Barka da yamma Anti!”
Diya ta juya baya ta kalli wadda ke gaisheta, ya ce tare yake da ƙanwarsa, kenan wannan ita ce ƙanwar tasa, da ɗan guntun murmushi a fuskarta tace.
“Sunana Diya Shola”
Narjis ta gyaɗa kanta.
“Wannan ita ce ƙanwata Narjis”
Cewar Suraj yana rufe ƙofar motar bayan da ya shigo, Diya ta gyaɗa kanta.
“Na ji daɗin haɗuwa da ke Narjis”
“Ni ma haka Diya”
Daga haka kuma babu wanda ya sake cewa komai har suka kai Makoko, zuwa lokacin duhun magariba ya gama mamaye ko ina, yayin da cikin garin Lagos ya yi kyau da kyawawan fitilun da aka kunna na manya-manyan ginninnikan da suka ƙara ƙawata birnin.
“Na gode sosai Yallaɓai Suraj”
Cewar Diya da ta fito daga motar.
“Nop I'm Suraj”
Ta dan yi murmushi. Kafin ta yi wa Narjis Sallama ta juya ta nufi cikin yankinsu. Narjis ta dawo gidan gaba tana faɗin.
“To muje gida, na san yau Mummy sai ta yi bandarmu, mun jima Wallahi!”
Suraj ya yi murmushi.
“Ya kika ganta?”
Ya tambaya yana wa motar key. Narjis ta yi murmushi.
“Tana da kyau sosai, ni da farko na ɗauka bafulatana ce, sai da ta faɗa min sunanta na ji cewar bayerabiya ce”
“Menene sunan nata?”
Ya tambaya, dan shi bai ji sanda ta faɗi suna nata ba.
“Diya Shola!”

TAUQEER POV.
Zaune yake a cikin motarsa, yayin da tayoyin motar ke tafiya a hankali a kan titi. Fuskarsa kawai idan ka kalla za ka san cewa a gajiye yake. Dan yau ya sha aiki sosai. Wayarsa dake aje a gefe ce ta ɗau ruri, ganin lambar RAM ce ya sa shi ɗagawa da sauri, dan tun ɗazu yake jiran kiran Rafeeq ɗin.
“Hello Agha!”
“Na'am Ram, ka gano inda yake?”
Daga ɗayan ɓangare Rafeeq yace.
“Eh, yana ɗaki me lamba 34, Maroko Bayshore!”
Tauqeer ya rintse idonsa zuciyarsa na masa ɗaci. Sannan ya buɗe idon nasa yana ci gaba da tuƙa motar da hannu ɗaya.
“Na gode Rafeeq, ka gaida Maa”
Ya faɗi da ƙyar.
“Dan Allah ka bi komai a hankali Agha”
“I will insha'Allah!”
“Ok ka kula da kanka, kuma ka gida su Umma”
Ba tare da ya ce komai ba, ya katse kiran, sannan ya lalubo lambar Saif.
“Saif kana gida?”
Daga ɗayan ɓangaren Saif yace.
“Eh ina gida, ban jima da dawowa daga barrack ba”
“Ka sameni a Maroko Bayshore yanzu!”
*Room No. 34, Maroko Bayshore Hotel, V.I, Lagos, Nigeria.*
Wani matashi ne zaune a kan gadon dake ɗakin, jikinsa sanye da 3qrt me ɗauke da kakin sojoji, sai baƙar T-shirt wadda ta kama jikinsa. A hankali yake furzar da hayaƙin sigarin da yake zuƙa. Idanuwansa a lumshe.
Ƙofar banɗakin dake cikin ɗakin ce ta buɗe, wata farar budurwa ta fito daga ciki tana tsane gashin kanta. Idonsa ya buɗe a hankali ya kalleta. Sanye take cikin orange skort trouser, da farar tube top.
“Babe ya kamata na tafi fa”
A hankali ya ciro karan sigarin dake bakinsa, ya gyaɗa kansa, sannan ya miƙa hannunsa setin side drawer, inda wallet ɗinsa ke aje. Buɗeta ya yi ya zaro kuɗaɗen da shi kansa bai san adadinsu ba, ya miƙa mata. Sai da ta masa wani farr da ido, sannan ta tako zuwa gareshi tana murmushinta na yaudara, ta sa hannu ta karɓi kuɗin tana jujjuyasu.
Sunkuyawa ta yi setin fuskarsa ta sumbaci kuncinsa na dama sannan tace.
“Na gode Babe, sai yaushe kuma?”
Hannunsa ya sa ya cire nata dake taɓa wuyan rigarsa.
“Zuwa gobe ki dawo”
Murmushi ta kuma yi, sannan ta ɗauki jakarta ta masa sallama ta fita. Kwalbar giyar dake gefe ya ɗauka, ya kafa a bakinsa yana sha.
Tauqeer da Saif wanda isowarsa kenan suka hawo hawa na ɗaya dake hotel ɗin, dan an sanar musu da cewar ɗaki me lamba 34 yana hawa na ɗaya. Idan ka kalli idon Tauqeer babu abun da za ka gani a ciki sai tashin hankali, Saif kuwa duk alhini ne ya mamaye fuskarsa. Duk da yanda mutane ke ta kallon Tauqeer ɗin bai damu ba, sai da Saif ya tuna masa ne ma ya sa ya fara rufe fuskarsa dan kada a ga halin da yake ciki.
A sanda suka shawo kwanar da ɗakunan suke, suka ga wata budurwa ta fito daga ɗaki me lamba 34. Tauqeer ya haɗiye yawu da ƙarfi, dan bisa ga dukanin alamu ita ce budurwar ƙanin nasa, ko ma de ya kirata da karuwar ƙaninsa, ji ya yi zuciyarsa na wani irin tuƙuƙi. Kamar wanda aka zabura ya ƙara saurin tafiyarsa. Haka suka wuce yarinyar tana lissafa kuɗin dake hannunta, ko ta kanta ba su bi ba, dan ba ita ce matsalarsu ba.
Tauqeer ne ya buɗe ƙofar ɗakin da ƙarfi, kuma abun da ya yi arba da shi shi ne ya sa ya ji kamar zai zame ya faɗi ƙasa. Ƙaninsa ne zaune a kan gadon ɗakin hotel yana shan giya!. Ganin kamar zai faɗi ƙasa ne ya sa Saif ya yi hanzarin riƙoshi.
“Haba Tauqeer ka kula mana!”
Maganar Saif ɗin ita ce ta dawo da hankalin Jamal kansu. Da sauri ya mike yana sakin kwalbar giyar dake hannunsa. Kallonsu yake ido waje. Kansa ya soma girgizawa a sanda Tauqeer ya soma takowa cikin ɗakin. Tauqeer da idonsa ya yi jajir ya kamo hannun ƙaninsa.
“Zo mu tafi gida Jamal”
Ya faɗa kamar wasu ƙananun yaran da suka tsaya wasa a gefen hanya. Jamal ya girgiza masa kai.
“No Tauqeer ba zan iya komawa gidan nan ba”
Tauqeer ya dubeshi yana jin kamar ya fasa ihu.
“Me ya sa?”
Ya tambaya.
“Saboda bana son rayuwar gidan. A duk sanda zan sa ƙafata a gidan sai naji na tsani kaina, ji nake kamar na kashe kaina na huta Hamma!”
Ya ƙarashe ƙwalla na fita daga idonsa. Tauqeer ya lashi lips ɗinsa da suka bushe, hannayensa biyu dafe da ƙugunsa. Wace iriyar jarabawa ce wannan?.
“I understand that you have a strong negative reaction to that house. It sounds like being there is causing you a lot of distress. I know it's not easy to deal with those feelings. I'm here to listen and support you however I can. You're not alone”
Ya faɗi a ƙoƙarinsa na tausar ƙaninsa, dan yana ganin kamar lamarin na Jamal ba lafiya ba. A da Jamal ba shi da wani wurin zuwa da ya wuce wurin aikinsa wato barrack, daga barrack kuwa sai zaman gida, kullum yana maƙale da Umma, kuma hakan da yake ne ma ya sa suke kiransa da Mama's boy.
Jamal ya zauna a bakin gadon yana dafe kansa tare da fashewa da kuka. Saif ne ya ƙaraso

Please Login or Register in order to submit comment