Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafeta da ido.
“Ƙwarai, ka faɗa soyyaya, ina da tabbacin sonta kake”
Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauƙe yana ɗauke kai.
“Yanzu menene mafita?”
Hannunsa ta kama, hakan ya sa ya kalleta.
“Ka sameta... Ka faɗa mata...”
Sai ya yi shiru yana jujjuya maganar tata. Kamar kada ya yarda, kuma kamar ya amince...
“Wato ke da aka aiko ki kirashi, shi ne kema kika samu wuri kika darfe kamar bawan da aka aika garinsu ko?”
Cewar wata farar mata tana tsaye daga ƙofar ɗakin, a tare suka kalleta. Kafin Narjis ta dafe kanta.
“Wallahi na manta ma. Ka fito mu ci abinci”
Ta ƙarashe tana mikewa. Har zuwa lokacin matar nan na tsaye a bakin ƙofar,ta rungume hannyenta tana kallon 'yan'yan nata biyu rak da Allah ya azurtata da su. Shi ma Suraj ɗin miƙewa ya yi suka nufo bakin ƙofar, sai a lokacin matar ta juya ta fita. Narjis da Suraj na take mata baya sun ƙus-ƙus kamar yadda suka saba.
Da haka har suka sauƙa ƙasa zuwa katafaren falon gidan dake ƙasa. Daga nan suka zarce zuwa daninng area. Babu kowa a daninng ɗin sai wani farin datijjo dake sanye da farin gilashin da ya ƙara fitar da kammanin fuskarsa. Sai kuma tarin kala-kalar abincin da aka jere a kan daninng table.
Datijjon ne ya ɗago daga duban wayarsa ya kallesu, a lokacin da Narjis ke zama a kan kujera. Yayin da Suraj ya kewa zuwa setinsa, ya sunkuya yana masa side hug.
“Yaushe ka dawo Daddy?”
Suraj ya faɗi a sanda ya saki mahaifin nasa, ya shiga jan kujerar dake kusa da ta Daddyn nasa. Daddy ya aje wayar hannunsa yana faɗin.
“Ban jima ba... Mummyn ku ta ce kusan tare muka dawo da kai... Ya aka yi ka makara yau?”
Ya ƙarashe yana wurga masa tambayar. Suraj ya buɗe plate ɗin dake setinsa yana murmushi.
“Har na dawo gida, sai kuma na tuna da cewar na yi mantuwa a office ɗin... Shi ne fa na koma”
A lokacin Mummy ta shiga zuba musu abincin da ta girka.
“Aikin naku ba sauƙi Suraj”
Ya ɗan yi murmushi.
“To ya za ayi Daddy?. Tun da dan al'umma za ayi. So sai an daure”
“Ka aje aikin mana!”
Mommy ta faɗi a bakin gaskiyarta, dan ita dai kam bata son wannan aikin nasa na 'yan sanda. Shi da ya kasance magaji ɗaya tal na dukiyar Alhaji Ali Muktar, wai shi ne ya ɓuge da aikin ɗan sanda. Allah ya sani har cikin ranta bata san wannan aikin nasa tun sanda zai fara. Kuma sai da ta nuna masa ƙin amincewarta a lokacin, amma mahaifinsa ya yi uwa ya yi makarɓiya ya shige masa gaba har ya samu aikin.
“Haba Badi'a!? Wai sau nawa za mu yi wannan maganar ne, yaron nan ya na san aikinsa, baki san abun da Allah ya hukunta faruwar sa a cikin aikin nasa ba!”
Bakinta ta taɓe tana jan kujera, sannan ta ɗauke kai. Wayarta ce ta shiga ruri, hakan ya sa ta kalli screen ɗin. ‘TAYYAB AGHA!’ Shi ne sunan da ya fito ɓaro-ɓaro. Tsaki ta ja tana saka wayar a silent. Daddy ya dubeta yana tauna abincin bakinsa ya ce.
“Ki ɗaga mana”
Kanta ra girgiza ranta na suya na tunowa da 'yar uwarta ƙwallo ɗaya da ta yi.
“Me zai cemin? Ai ba na tunanin akwai wani abu da ya rage da zamu tattauna tsakanina da shi, tun da har ba zai iya ganomin inda ƙanwata take ba”
Ta ƙarashe muryarta na rawa. Nan take jikin yaranta ya yi sanyi, dan sun saba ganin mahaifiyar tasu a cikin irin wannan halin. Narjis ce ta dafa kafaɗarta.
“Dan Allah Mummy”
Kanta ta girgiza.
“Ba komai fa!”
Surja ya ci gaba da kallonta yana lissafa tazarar dake tsakaninsa da samawa mahaifiyarsa farin ciki. Tun tasowarsa ya fahimci cewar rabin farin cikin mahaifiyarsa na tattare da ƙanwarta Rahila. Kuma tun bayan da Rahilan ta ɓata rabin farin cikin mahaifiyarsu ya ragu, hakan tasa ya dage kan shi ɗan sanda yake san zama, ba dan komai ba sai dan ya nemo inda Ƙanwar mahaifyarsa take. Amma har zuwa yau bai samo komai ba.
_______________
_To fa, waye ya hango duhun dake tunkarar RAM?_
_Sannan ga Lazarus dake shirin ɓallo ruwa_
_Shin kun gane cewa Anti Badi'an da Tayyab Agha ke kira ita ce mahaifiyar Suraj!._
_Ga kuma Suraj ya kwarewa Diya Shola ɗiyar yarabawa..._
_A juri zuwa rafi dai_
A. ISAH CE ✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE...💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 07*
~~~

*Ƙauyen Wagini, Batsari Local government, Katsina state, Nigeria.*
*08:00 na dare.*

SALMA SA'AD (SALAME) POV.
Zaune suke a kan tabarma suna cin tuwon dare ita da Muja, yayin da Inna ke zaune a kan dakalin ƙofar ɗakinta tana saƙa hular sanyi ta yara, kasancewar saƙa sana'arta ce tun da can. Iya Abu kuma na zaune a cikin ɗakinta tana lazumi.
Sallamar Baba da Audu suka ji daga soro. Salame da Inna suka amsa a tare, yayin da Muja ya fita da gudu ya nufi Baba yana shirin rungumeshi, Baba ya riƙeshi yana faɗin.
“Bari bari bari Mujahid! Kar ka ɓatamin kaya”
Muja ya shiga yi wa Baba shagwaɓa irin tasu ta autanni. Yayin da Salame, Inna da Ya Audu suke musu dariya.
“Wasa nake maka Autana, zo nan”
Baba ya faɗi yana janyoshi. Muja na maƙale da ƙafarsa suka shigo cikin gidan.
“Sannu da zuwa Malam!”
Inna ta faɗa.
“Baba sannu da zuwa! Hamma Audu sannu da zuwa!”
Cewar Salame, suka amsa su duka. Hamma Audu na zama a kusa da Salame, yayin da Baba ya zarce ɗakinsa Auta maƙale da shi.
“Salma ga wannan!”
Hamma Audu ya faɗi yana miƙowa Salame wani abu a cikin baƙar leda. Hannu bibbiyu ta sa ta karɓa, haɗi da masa godiya. Kuma tun kafin ta buɗe ta san miye a ciki. Awara ce me ɗumi da fura me sanyi irin wadda ya saba kawo mata kullum ranar kasuwa, kasancewar tana san fura sosai.
“A kawo maka abinci?”
Inna ta faɗi ganin ya miƙe. Kansa ya girgiza.
“A'a tukkuna dai... Zan je wurin su Suma'ila ne”
“To sai ka dawo”
Ya gyaɗa kansa yana juyawa.
“Hamma zan kai maka abincin naka ɗakinka, dan wata ƙila sanda zaka dawo mun kwanta”
Cewar Salame tana kallon bayansa, juyowa ya yi ya kalleta yana murmushi, kafin ya gyaɗa mata kai ya fice, ta bishi da adawo lafiya. Tuni ta ture kwanon tuwon dake gabanta, ta buɗe ledojin da Hammanta ya bata. Inna ta fara miƙawa tana faɗin.
“Inna awara”
Inna ta girgiza kai tana miƙewa don ta kaiwa mijinta abinci.
“Na ƙoshi Salame”
“Furar fa?”
Inna ta yi dariya tana nufar rumfar da suke girki.
“Na ƙoshi na ce miki...”
“Muja! Muja! Muja!”
Salame ta shiga ƙwala masa kira. Da sauri ya fito daga ɗakin Baba, hannunsa riƙe da ledar kilishin da Baba ya siyo masa.
“Zo mu ci awara da fura, hamma ne ya kawomin”
Muja ya zauna kusa da ita yana nuna mata ledar hannunsa. A lokaci guda kuma yana tauna kilishin bakinsa.
“Ni ma Baba ya kawomin kilishi”
“To mu je ɗakin iya mu ci a can”
A tare suka miƙe suka shiga ɗakin Iya. Fitilar ƙwan dake ɗakin ta haska musu ita. Zaune take a kan darduma tana lazuminta na kullum. Hannunta na dama na jan carbin da ta saba jansa a kullum rana. Zama suka yi kusa da ita suna mata bismillah. Kanta kawai ta girgiza musu alamun ba za ta ci ba. Haka Salame da Muja suka cinye kayansu tas.
Kafin Salame ta fita zuwa gidansu Karime, bayan da ta kaiwa Audu abinci ɗakinsa. Yayin da Muja ya nufi wurin abokansa dan su yi wasa.
Kasancewar yankin nasu na fama da rashin tsaro. Dan ƙauyukan dake kusa da nasu duk an farmakesu, nasun ne kaɗai ba'a taɓa shiga ba. Hakan ta sa ba sa jimawa a waje idan dare ya yi. Da wuri Salame ta koma gida. Tana taka soron gidan za ta shiga ciki, ta tsinkayo hirar iyayenta dake zaune a tsakar gida.
“Ɗazu Malam Halliru ya zo ya sameni da wata magana a kan Salamatu!”
Jin hakan ya sa ƙafafunta cin birki a soron, ta tsaya tana kasa kunne dan jin batun da za ayi a kanta, duk kuwa da ta san maganar ba za ta wuce ta aurenta da ɗan gidan Malam Hallirun da ake shirin yi ba.
Aure! Ita tun da take ba ta taɓa ganin ko fuskar Haladun da aka ce za'a aura mata ba, dan ita ba yawo take ba. Daga gida sai makarantar boko sanda tana zuwa kenan, kafin ta yi candy, sai kuma ta Allo da suke zuwa ita da Muja da asuba. Sai gidan su Karime, sai kuma aike idan ya taso. Ko irin tallar nan da 'yan matan ƙauye ke yi ita ba ta yi, dan Baba ba zai bari ba, hakan ya sa ta zama kifin rijiya. Kuma auren nata irin auren nan ne na haɗi, dan ko shi angon me suna Haladu ba ta jin ya taɓa ganinta.
Iya dake zaune kusa da shi Sa'adu tace.
“Me yace?”
“Magana ce a kan bikin Salame da Haladu, ya ce ya na so a yanke bikin nan da sati ɗaya, dan su a shirye suke”
Inna dake zaune a ɗaya ɓarin nasa ta gyaɗa kai.
“To kai me ka ce masa?”
Iya ta kuma tambaya. Baba ya sunkuyar da kansa yana faɗin.
“To me zan ce da ya wuce to, kawai na amince da abun da ya zo da shi ɗin. Dan ban ga dalilin jiran ba, tun da mu ma a shirye muke...”
A lokacin Salame ta yi sallama sannan ta shigo cikin gidan. Ba tare da ta ce musu komai ba ta faɗa ɗakin Inna. Auta ta fara yi wa shimfiɗa, wanda ta iske kwance a kan gadon ƙarfen Inna yana bacci. Kafin ta yi tata shimfiɗar. Ta tashi Mujan ta ce masa ya je ya yi fitsari ya zo ya kwanta.
Yana cuna baki cikin magagin barci ya fice daga ɗakin, yayin da ita kuma ta shiga cikin nata gidan sauron ta kwanta. Tunani barkatai a kanta. Ita ba za ta ce bata son wannan auren ba, kuma ba za ta ce tana so ba, kawai dai tana tsaye a tsakiya ne, ba ta san ina ta dosa ba.
Tana nan kwance a wurin har Muja ya dawo ɗakin ya shiga tasa shimfiɗar. Har Inna ta shigo ɗakin ba ta samu bacci ba. Kuma ta rasa abun da ya hanata barcin!.
*A. Foods NIG LTD, 38 Eric Moore Road, Iganmu, Lagos, Nigeria.*

TAUQEER POV.
A hankali tayoyin gray color ɗin motarsa ƙirar Lamborghini Veneno suka tsaya a katafaren wurin aje motoci na kamfanin. Tun kafin ya fito daga cikin motar ma'aikatan dake kai kawo a wurin suka taho da sauri har su biyu suka buɗe masa ƙofar motar. Ya fito ya na ɗan jifansu da murmushi kamar kullum. Sanye yake cikin wata blue suit, wadda ta dace a fatar jikinsa, idanuwansa manne da baƙin glashi.
Tafiya ya soma yi, yana nufar ginin ma'aikatar, inda ofisoshinsu suke. Yayin da ɗaya daga cikin ma'aikatan da suka buɗe masa mota ke biye da shi yana riƙe da briefcase ɗinsa. Tun da ya shigo wurin kowa ke gaisheshi, shi kuma yana amsawa cikin mutunci, saboda shi ba ya ganin cewa ba ɗaya suke da shi ba, dan suna aiki a ƙarƙashinsu ba ya nufin cewa su sama suke da su ba.
Katafaren office ɗinsa ya nufa, yana shiga ya zauna yana aikawa Secretary ɗinsa kira. Cikin abun da bai wuce minti ɗaya ba sai ga ta ta shigo office ɗin bayan ta nemi izinin shigowa, tambayarta ya yi game da ayyukansa na yau, ta zayyano masa kaf ayyukan da zai yi a yau ɗin, duk da wasu ayyukan ba na yau ɗin ba ne, tafiyar da ya yi ce ta sa suka zama na yau ɗin. Sallamarta ya yi bayan ya bata wani File ya ce ta bawa messenger ya kai office ɗin Baffa Muzamill.
Yana duba wani file Asad abokinsa ya shigo. Asad abokinsa ne a harkar waƙa kuma tare suke aiki a kamfani ma. Ɗan kauda kai ya yi daga barin kallon file ɗin ya kalli Asad ɗin. A lokacin da yake zama a kujerar dake fuskantarsa.
“Ban san ka dawo ba ai”
Cewar Asad ɗin yana gyara zaman tie ɗin wuyansa. Tauqeer ya kauda kai yana ɗan guntun murmushi.
“Sai de idan mantawa ka yi... Amma sanda in airport na kiraka”
Asad ya ɗan yi shiru yana son tunowa. Saboda cutar mantawa dake damunsa a wasu lokutan. Kansa ya gyaɗa yana gyara zama.
“Na tuna yanzu... Magana ce a kan wata yarjejeniya da SSGF record leble...”
Da sauri Tauqeer ya dakatar da shi da faɗin.
“A office muke ba studio ba Asad, so ba maganar waƙa a nan, aiki kwai!”
Asad ya jinjina kansa. Kafin shiru ya ɗan ratsa na wasu sakkani, can kuma sai ya tuno da abun da ya shigo da shi office ɗin Tauqeer ɗin.
“Dan Allah Tauqeer so nake ka haɗani da RAM! Jiya da daddare aka yi hacking Facebook page ɗina!”
Tauqeer ya dubeshi.
“Garin yaya?”
Ya ɗan ɗaga kafaɗu cikin taɓe baki.
“Ban sani ba Wallahi, kawai jiya ina zaune na ga an yi hacking ɗinsa, kuma ko da na duba ta wayar Ummu Kulsum(Ƙanwarsa) sai na ga sunan wani a kai wai shi ‘Henry Samuel’”
Tauqeer ya ɗan yi dariya yana janyowa wayarsa.
“Sun kara maka kenan?”
“Wallahi! To ya zan yi da rayuwa?”
Tauqeer ya jinjina kai yana neman lambar babban abokinsa na jami'a, wato RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD a.k.a RANDOM ACCESS MEMORY, a.k.a RAM.
Da ƙyar ya iya lalubo lambar, ba wai don lambobin dake cikin wayar tasa suna da yawa ba, sai dan sukan jima ba tare da sun yi waya da Rafeeq ɗin ba, kasancewar shi Ram a duniya bai bawa waya muhimmanci ba. Saboda sai ya fi wata ba tare da ya san duniyar da wayar tasa take ba.
Sai da ya jera masa kira biyar, amma ba'a ɗaga ko ɗaya ba, kuma hakan ba sabon abu ba ne gareshi, dan wannan sababbe ne, haushin rashin samun Rafeeq ɗin a waya ya sa ya den kiransa, sai idan shi Rafeeq ɗin ya yi jajensa ya neme shi da kansa.
“Mtsww! Shi ai ka ji matsalarsa”
Ya faɗi yana ƙara trying. Cikin sa'a a wannan karon sai ya amsa.
“Kai kam Rafeeq ka ji jiki!”
Daga ɗayan ɓangaren Rafeeq ya yi dariya. Dan ya san faɗan abokin nasa na miye. Yanzun ma Allah ne ya temakeshi ya daga kiran nasa, dan yana duba wani abu cikin kayansa ne Allah ya sa ya ci karo da it, ya ga kiran Tauqeer ɗin, shi ne fa ya ɗaga. Tattoo ɗin wuyansa ya sosa yana faɗin.
“Da na yi me?”
“Ban sani ba, Ina Maa? Fatan tana lafiya?”
Ta jero masa tambayoyin. Sai da Rafeeq ya ɗan juya ya kalli ƙofar ɗakinsa sannan yace.
“Lafiyarta ƙalau Wallahi, sai godiya, jiya da na dawo daga aiki take tambayata kai”
Tauqeer ya ɗan yi murmushi.
“Ka ce mata ina lafiya”
Daga ɗayan ɓangaren Rafeeq ya gyaɗa kansa.
“Za ta ji da yardar Allah. Ya ya naka ahalin?”
Ya tambaya cikin sauƙƙaƙƙiyar jimla, dan idan har yace zai zauna yana lissafo tarin mutanen dake Agha Mansion za su cinye lokaci ne ba tare da sun gama ba.
“Kowa lafiya ƙalau. Wai kai yaushe za ka dawo?”
“Wata ƙila nan da wata uku, ban de tabbatar ba”
A lokacin ne kuma Asad ya ɗaga masa hannu alamun yana nan fa, kuma cikin son ya tunasar da shi dalilin kiran Ram ɗin. Dan idan Tauqeer ya haɗu da Rafeeq shi ne ke kamuwa da cutar mantuwar. Kuma ya manta ɗin, dan haka yace.
“Asad ne ya sa na kiraka, wai an yi hacking Facebook page ɗinsa... Shi ne yace na kiraka ko akwai yanda za ayi a dawo masa da shi”
Rafeeq ya nemi bakin gadonsa ya zauna tare da janyowa laptop ɗinsa ta kullum, wadda ke ɗauke da manyan rubutun sunan ‘RAM’ cikin manyan baƙi, manne a bayan screen ɗinta.
“Ba shi wayar”
Ya faɗi yana tare wayar da kafaɗarsa.
“Hello! Rafeeq”
“Na'am Asad... Faɗomin lambar da ka buɗe facebook ɗin da ita”
Cikin sauri Asad ya karanto masa lambar, yayin da shi kuma yake rubutawa a laptop ɗinsa. Ya ɗan yi wasu 'yan danne-danne na minti ɗaya, har zuwa lokacin kiran na tafiya.
“Akwai wasu lambobi da za su shigo ta layinka, buɗe ka karonto min su”
Rafeeq ya faɗa bayan wani lokaci. Daga ɗayan ɓangaren Asad dake kare da wayar Tauqeer ya lalubo wayarsa. Kuma an turo lambobin, saboda haka ya karantawa Ram su. Cikin minti ɗaya yace.
“Shiga ka duba”
Hannu na rawa Asad ya shiga dubawa. Bakinsa ya buɗe cikin dariya yana kallon Tauqeer da ya ci gaba da duba file ɗin gabansa.
“Ya dawo Wallahi...”
“Ok saika kula saboda gaba, na saka maka matakan kariyar da babu wanda zai ƙara hacking ɗin page ɗin... And one more thing, ba da niyya Henry ya sace maka account ba, account yake son buɗewa a instagram. Sai ya danna join facebook account, alhalin bashi da account a Facebook, su kuma da suka tashi sai suka bashi account ɗinka ya buɗe... To ka ji”
Asad ya jinjina kai yana ƙara girmama basira da hazaƙar Ram. Tauqeer ya miƙawa waya wanda ke tambayarsa shin account ɗin ya dawo? Cike da murna Asad ya amsa shi da Eh yana barin office ɗin. Sai da Tauqeer ya tabbatar da Asad ya yi nisa daga office ɗin nasa sannan damuwa ta maye fuskarsa.
“Feeq ina so ka min wani temako”
Rafeeq ya gyara zamansa.
“Faɗi ko menene Bro, ni me iya maka ne, in har bai fi ƙarfi na ba”
Ya faɗi, idonsa na hasko masa tarin alkairan Tauqeer gareshi a sanda suke karatu. Sai da Tauqeer ya haɗiye yawu, sannan ya goge bakinsa da tafin hannunsa. Kamar me shirin furta wata ƙazamar kalma.
“Ka dai san halin da Jamal ya shiga a shekarar nan... To yanzu abun ya yi ƙamari, dan yanzu ba ya kwana a gida. Yanzu haka zancen da nake maka kwanansa takwas bai kwana a gida ba, kuma ba mu san inda yake ba. Shi ne nake so ka bi diddigin layinsa, dan mu san inda yake, Habibty na cikin damuwar rashin ganinsa a gida!”
Rafeeq ya yi shiru.
“Wallahi Agha sai ka sa na ji kunya, yanzu dan kana so na yi tracking numbern Jamal shi ne sai ka marairaice murya kamar me roƙon guntun buredi?”
Tauqeer ya shafa sumarsa ya na ɗan murmushi kaɗan.
“Ka fara ba?”
“Kawai ka turo min lambarJamal ɗin”
Tauqeer ya gyaɗa kansa.
“Okay!”
*Federal Neuro, Psychiatric Hospital, Yaba, Lagos, Nigeria...*
A cikin madai-daicin ɗakin kwantar da marasa lafiya na asitin, kwance a kan gadon marasa lafiya na ƙarfe irin na asibitocin masu fama da cutar taɓin hankali. Wata mata ce, sanye cikin shuɗayen kaya. Idonta a rufe. Kanta babu ɗankwali, hakan ya bayyana kyakkyawar sumar kanta da ta fara sirkawa da fari. Ba wai dan shekarunta sun kai na tsufan ba, sai dan azabar rayuwa da take sha.
Hannayenta da ƙafafuwanta kuwa ɗaɗɗaure suke a jiikin ko wani saƙo na gadon, ta yanda babu damar guduwa. Kuma bayan wannan gadon da take kwance a kai, babu komai a ɗakin face ƙarfen saƙala drip. Daga waje kuwa ƙofar ɗakin kulle take da wani garƙamemen kwaɗo.
A dai-dai lokacin da rana ta hasko cikin ɗakin daga taga, ta hasko fuskar matar, a dai-dai lokacin, yatsan tsakiya na hannunta ya motsa. Kamar almara kuma sai ta motsa ƙafarta. Da aka ƙara jimawa kuma sai ga ƙwalla ta silalo daga gefen idonta na ɓarin dama. Ƙwallar ta ci gaba da gangariwa daga kwarmin idonta har zuwa cikin kunnenta. A hankali bakinta ya buɗe. Ta furta “‘Yata!” kawai a kan laɓɓanta.
A dai-dai lokacin, babu abun da take gani a cikin kanta face yadda aka rabata da ‘Yarta sabuwar haihuwa.
___________________
*Shekara ta 2000.*
_Tafe suke ita da Hajia Maryam matar Faruq Agha. Yayin da Maryam ɗin ke riƙe da ita, saboda tsohon cikinta da ya girma, haihuwa yau ko gobe._
_“A hankali!”_
_Cewar Maryam ɗin tana buɗe mata ƙofar ɗakinta. Rahila na murmushi ta ci gaba da taka kumburarrun ƙafafuwanta zuwa cikin ɗakin. A bakin gadon ɗakin Maryam ɗin ta zaunar da ita tana faɗin._
_“Babu abun da kike buƙata?... Dan ina so na je na ɗorawa su Tauqeer abincin rana, saboda na ga lokacin tashi daga makaranta ya yi”_
_Ta ƙarashe tana kallon agogon bangon dake ɗakin. Rahila ta girgiza kai._
_“Babu komai Antina, ki je kawai”_
_“Kin tabbatar?”_
_Rahila na murmushi ta gyaɗa kai. Ita ma Maryam ɗin kanta ta gyaɗa tana nufar ƙofar ɗakin tace._
_“Zan bawa Hafiza apple ta kawo miki!”_
_Rahila ta yi murmushi tana shafa tsohon cikinta. Ba jimawa sai ga Hafizan ta shigo, hannunta rike da plate me ɗauke da yankakkiyar apple. Kuma duk halin shariya da nuna halin ko in kula na Hafiza a gidan, suna shiri da Rahila, dan ko yanzun da ta kawo mata apple ɗin, sai da ta tabbatar da ta cinye, sannan ta ɗauke plate ɗin ta fita, bayan ta ce mata ta kwanta ta huta._
_Kwanciyar ta yi, ba jimawa ta ji wayarta ƙirar Motorola irin ta wancan zamanin ta shiga ruri, hakan ya sa ta janyota. Ganin yayarta Anti Badi'a ce me kiran ya sa ta ɗauka da sauri._
_“Ya jikin naki?”_
_Shi ne abu na biyu da Anti Badi'a ta tambaya bayan Rahila ta gaisheta._
_“Jiki Alhamdullilah. Ina Suraj!”_
_“Ya tafi makaranta, amma duk inda suke na san sun kusa dawowa gida”_
_Hira suka ɗan taɓa, kafin suka yi sallama. Wayar tasu na yankewa, kamar me jira sai ga kiran Tayyab ya shigo wayar tata._
_Dariya ta yi, kafin ta ɗaga kiran da sallama a bakinta. Cike da kulawa irin ta mijin dake tsantsar son matarsa ya shiga tambayarta halin da take ciki. Ita kuma tana bashi amsa cike da ladabi. Kuma wannan ladabin nata shi ne yake ƙara sama mata gu a zuciyarsa. Dan a aurensa na farko bai samu hakan ba._
_Har suka yi sallama yana ƙara jaddada mata kada ta yi aikin komai, ta kwanta ta huta kawai. Yankewar wayar tasu ba ɓata lokaci, ta ji ciwon bayan da ta fara yi tun jiya ya tsikareta, da ciccije baki da komai ta samu ta dafa ta zaune._
_Miƙewa ta yi da niyyar shiga banɗaki ta ji mararta ta yi wani irin juyawa. Ta dafe wurin da sauri tana karanto ‘Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un’._
_Kamar daga sama ta ji ana kiran sunanta da ƙarfi. Hakan ya sa ta dafe kunnenta, tana ci gaba da faɗin abun da take faɗa. Ji ta yi kamar ana janta zuwa waje, kamar ana cewa ta fita zuwa waje. Ba tare da ta sani ba ƙafafunta suka juya zuwa ƙofar ɗakin. Bayanta da mararta na ci gaba da amsawa._
_Ko da ta fita daga ɗakin nata bata tsaya a ko ina ba sai tsakiyar ɗakin Hajia Zayya. Hajia Zayyan na ganinta ta jefeta da wani mugun murmushi. Kuma daga wannan murmushin, ba ta ƙara sanin inda take ba, sai farkawa ta yi ta ganta a cikin wani ɗaki me matsanancin duhu. Ga mararta dake ƙara ƙullewa, bayanta ya ci gaba da mata ciwo. Haka ta shafe tsawon awwanin da bata sansu ba a ɗakin, ita kaɗai ta yi naƙuda, har Allah ya bata ikon haihuwa._
_A sanda kukan jaririn ya baza dakin wani irin HASKE ya mamaye ko ina. Kuma ta cikin HASKEn ta ga Hajia Zayya da wani yamushasshen tsoho, tsaye a gabanta suna kallonta._
_Da ƙyar ta iya zama a kan dandaryar ƙasar dake wurin da bata san ina ne ba. Jini mamaye a ƙasan inda ta yi naƙuda. Da ƙyar ta iya ɗaukar jaririn da ta haifa ɗin, ta dudduba jikinsa har ta fahimci cewa mace ce._
_Kuma har zuwa lokacin Hajiya Zayya da wannan tsohon na tsaye a gabanta suna kallonta._
_“Zayya me kika yi?”_
_Ta tambaya da ƙyar. Saboda numfashinta dake sama-sama._
_“Abun da na miki alƙawari a kansa shi nake yi”_
_Hajiya Zayyan ta faɗa._
_“Dan Allah Zayya ki ƙyalemu mu tafi. Kada ki cutar da mu dan Allah...”_
_“Ai tun da kika auri mijina na riga da na yanke cewar mutuwarki a hannuna take, waye ya faɗa miki cewar Zayya tana haɗa miji da wata? Ba'a haifi me zama lafiya da mijin Zayya ba!”_
_Cikin raɗaɗin ciwo Rahila ta yi murmushi._
_“An haifeta mana, gani nan zaune a gabanki, kuma ko ba komai na auri mijinki, na yi zaman farin ciki da shi har na tsawon shekaru biyu, ga kuma ribar aurenmu kina gani da idonki!”_
_Ta ƙarashe tana rungume sabuwar jaririyarta dake kuka har zuwa lokacin. Cikin fusata Hajiya Zayya ta rarumi wani katako, ta yi kan Rahila da shi, kuma tana isa gabanta ba ta yi wata-wata ba wurin ɗaga shi sama tare da buga mata shi a tsakiyar ƙwaƙwalwa. Daga nan kuma bata ƙara sanin komai ba, ba ta sake gane komai ba, ba ta sake jin komai ba sai a yau!._
______________
Idanuwanta ta ci gaba da motsawa, har ta samu damar buɗesu tar. Bin ɗakin da take ciki ta

Please Login or Register in order to submit comment