Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani sashi na ƙauyen sai koke-koke da harbe-harbe. Tsayawa ta yi tana kallon ko ina na ƙauyen.
Ƙafafuwanta ko takalmi babu, haka ta soma tafiya tana nufar hanyar barin gari. Can kuma da ƙwaƙwalwarta ta tariyo mata irin kisan gillar da aka yiwa ahalinta sai ta fashe da kuka ta fara gudu a kan ƙafafunta. Da haka ta fara kutsawa cikin daji. Babu abun da take so face ta bar ƙauyensu. Ta kutsa dajin nan, ko namun daji ne su cinye namanta ɗanye.
Ƙafafuwanta na taka ƙayoyi da kuma ciyayi masu kaifi, amma ko a jikinta. Raunikan da ke gangar jiki kan iya warkewa, ban da na zuciya.
Ba tare da ta ankara ba, ta taka wani abu me santsi. Kafin ta yi tuntuɓe da wani tubali. Ta faɗi ƙasa, har tana buga kanta a jikin bishiya. Ƙarar azaba ta saki tana dafe kanta. Kafin kum ta ji wani irin sara a ƙafarta. Raɗaɗin saran ya ratsa har ƙwaƙwalwarta. Daga haka kuma sai ji da ganinta suka yi nisan kiwo.

*No.675, 361 Stagg Street, Brooklyn, New York, USA.*

RAFEEQ POV.
Babu abun da za ka iya gani a shimfiɗeɗen filin Allahr face farin HASKE. Babu kowa a wurin sai shi ƙaɗai. Ko ina farin ne, daga sama har ƙasa. Cikin waige-waigen da yake, ya hango wata farar matashiyar budurwa hannunta riƙe da wuƙa. Hawaye take tana kallonsa. Cikin abun da bai fi ƙiftawar ido ba, setin inda take ya koma ja. Jini ya shiga malala a ƙasa. Hannunta na dama ta ɗaga tana faɗin.
“AL'AMEEN! Ka kawo min agaji! Ka taimakeni AL'AMEEN!...”
Sai kuma ta yi shiru. Saboda duwatsun da suka fara sauƙowa daga sama. Ƙaran harbe-harbe ya karaɗe ko ina, babu abun da ke gudana a ko ina sai jini. Sai kuma ya ga matashiyar ta durƙushe a ƙasa tana dafe kanta. Wasu muryoyi suka shiga kiran.
“SALMA!”
Wata muryar na faɗin.
“SALAME!”
Wata tace.
“SALAMATU CANDY!”
Wata ma tace.
“SALAME!”
“ADDA SALAME!...”
~~~
Kirrr! Kirrrr! Kirrrr!
Ƙaran alarm ɗin da ya seta ya karaɗe ɗakinsa. Amma ko motsi bai yi ba. Har Maa dake ƙasa ƙaran ya soma damunta. Hakan ya sa ta yi tunanin ko ya shiga wanka ne. Da ƙyar da fama ta hawo saman, dan ita bata son wannan benin, shi ya sa ɗakinta yake a ƙasa. Ƙofar ɗakin nasa ta buɗe. Ta sameshi kwance a kan gado. Mamaki ya kamata. Ta san Rafeeq Sam bai da nauyin bacci. To me yake faruwa.
Carbin dake hannunta na dama ta mayar da shi zuwa na hagu. Sannan ta nufi alarm ɗin ta kashe. Tsayawar ƙaran ta yi dai-dai da farkawar Rafeeq a razane. Rigar jikinsa ta jiƙe sharkaf da gumi. Idanuwansa sun firfito waje. Gaba ɗayansa a hautsine yake, kamar wanda aka koro. Ko kuma ya yi gudun abun da zai kasheshi.
Da ace agogon da ya saba auna adadin bugun zuciyarsa na tare da shi, da babu abun da zai hana ahi zuwa 100%. Da sauri Maa ta zauna kusa da shi tana tofa masa addu'a. Ba sai ya faɗa ba, ta san cewa irin mafarkan da ya saba yi su ne ya yi a yau. Tun yana ƙarami yake a haka.
Abu ne mayuwici ya yi mafarki ka ga bai faru a gaske ba. Akasarin abubuwan da zasu tunkareshi a gaba cikin ikon Allah yana ganinsu a bacci. Tun ɗanta na ƙarami ta riga ta san cewa shi ba kamar saura yake ba, yana da banbanci da saura. Hannunta kai ta goge masa gumin da yake. Har zuwa lokacin da ƙyar yake futar da numfashi.
“Maa! Wata yarinya ce!...”
“Shhhh! Ya isa, ya isa”
Ta faɗi tana ƙara goge masa gumi. Shiru ya yi mafarkin na ƙara dawo masa cikin tunani. Bai san wacece yarinyar ba, bai san a ina take ba. Bai san ta wace siga za ta shigo rayuwarsa ba, abu ɗaya ya sani kuma yake da tabbaci a kansa. Ko ba daɗe, ko ba jima sai wannan yarinyar ta wanzu a cikin rayuwarsa. Bai san ta yaya ? Yaushe ? Kuma a ina hakan za ta faru ba, shi de ya sani, kuma ya tabbatar da za su haɗu, za su haɗu ko a ina take!.
“Ka je ka yi sallah. Lokaci na wucewa”
Kansa ya gayɗa yana laluben agogonsa da glasses a kan side drawer. Ɗauka ya yi, ya fara da saka glasses ɗin, sannan ya ɗaura agogon a hannunsa na hagu kamar yadda ya saba ɗaurashi a wurin.
Sai da ya kunna agogon. Ya jira na wasu 'yan sakkani don ganin ma'aunin bugun zuciyarsa. Kafin agogon ya nuna masa 64%. Idonsa ya lumshe yana buɗewa. Kafin a hankali ya miƙe ya nufi banɗakin.
Sai da Maa ta tabbatar da ya shiga banɗakin, sannan ita ma ta fita ta shiga kitchen, ta saka Kiyara girka musu abun karin kumallo.

DEENA POV.
A fusace ta shigo babban falon dake ƙasa. Tsayawa ta yi tana bin falon da kallo, kafin ta ci gaba da takowa zuwa cikin falon. Ba ta tsaya a ko ina ba sai a sashen da su Abba suke. Ganin yanayinta ya sa Abba, Abby da Baffa miƙewa tsaye suna kallonta. Ban da Daddy dake zaune yana ƙara fantsamawa cikin duniyar tunanin da ya saba ziyarta.
“A gaskiyar magana Abba na gaji da abubuwan da Tauqeer yake min!”
Maganar tata ta fito babu wata girmamawa. Kamar ba wadda ke magana da yayan mahaifinta ba. Kuma maganar tata ce ta janyo hankalin sauran jama'ar falon. Har Saif ya miƙe yana nufo wurin.
“Me Junior ɗin ya yi Deena?”
Abby ya tambaya yana dubanta. Kanta ta riƙe tana hawaye.
“A gabana fa riƙe wata ƙazamar 'yar yarbawa. A gabana yake riƙeta Abby!”
“Ke da kike bawa ko wani kare da doki lasisin taɓa jikinki har kina da bakin da za ki kawo ƙarar Tauqeer akan yariƙe wata?”
Saif ya faɗi a fusace yana jin kamar ya mangareta. Wannan rashin kunyar tata da rashin sanin girman na gava da ita shi ne a ko da yaushe yake sawa ya ji baya son Deena.
“Ya isa Saiffudeen! Ba da kai take ba. Da mu iyayenta take. Ka barta ta faɗi abun da ke ranta!”
Abba ya faɗi yana jin ina ma ace yana da damar da zai hana auren ɗansa da wannan 'yar ɗan uwan nasa da bata gado komai na ahalinsu ba.
“Ban ƙaraso kan ka ba Saiffudeen Mas'ud Agha. Ba ni da lokacinka a yanzu!”
Deena ta faɗi tana kallonsa. Kasancewar Saif mutum ne mai jin maganar iyayensa, ya sa bai sake cewa komai ba, sai cika da batsewar da yake kamar wanda idan aka tsikar zai fashe.
“Abba na gaji da wannan jiran, ya kamata ace kun mana aure ni da Tauqeer. Ba zan saka ido wata ta ƙwace min shi ba!”
Babu wanda ya ƙara ko da tari, kallonta kawai suke suna jinjina rashin kunya irin ta Deena. Umma kam ji take ina ma ta sa Tauqeer ya fasa auren wannan mara ɗa'ar.
“Aure kike so?”
Abby ya tambaya. Cike da rashin kunya Deena tace.
“Eh Abby ina so a ɗaura mana aure ni da Tauqeer nan ba da jimawa ba, saboda na gaji!”
Abby ya gyaɗa kansa.
”Bari Tauqeer ɗin ya dawo to!”

TAUQEER POV.
A hankali ya faka motarsa a parking lot ɗin dake ciki Agha Mansion. Idan ka kalli tarin jerin motocin dake wurin cewa za ka yi kamfanin saida motoci ne ba gida ba. Fitowa ya yi ya na kallon ginin gidan. A lokacin da ya fara taka ƙafarsa ta faɗo masa a rai. Diya Shola! YAROBA GIRL!. Murmushi ya samu kansa da shi. Dan bisa ga dukkan alamu ɗaurin da ya yi wa zuciyarsa ne ya kunce.
Kwaɗon da ya saka ya kulle zuciyarsa ne aka buɗe shi a yau ɗin nan. Wannan feeling ɗin da yake dannewa a zuciyarsa a ko da yaushe shi ne ya ƙara motsawa a yau. Tabbas ya taɓa soyyaya. Ya san yanda ake yinta. Amma kuma sam bai sha da ɗi a hannun soyyayar ba.
Soyyaya ta bar masa tabo me girma a zuciya, ta yadda har ya yanke shawarar ba zai sake yinta ba. Amma a yau ya ƙaryata hakan. Shi kansa ya san cewa ya faɗa soyyayar wannan farar bayerabiyar me kama da fulani...
Tunaninsa ya katse, a sanda ya buɗe ƙofar babban fallo. Gaba ɗaya mutanen gidan ya gani tsaye a falon suna kallonsa. In ka ɗauke Hajiya da ya san i yanzu har ta kwanta bacci, Sai su Bobo da su ma ya san cewa suna bacci war haka. To kowa na gidan yana falon ciki kuwa har da Jamal dake tsaye a tsakiyar staris ya jingina da jikin stairs case ɗin yana kallon kowa na falon.
Yanayin kallon da kowa ke binsa da shi ne ya sa shi fahimtar cewa ba lafiya ba. Falon ya shigo yana gyara zaman jakar guitar ɗin dake goye a bayansa.
“Junoir zo nan!”
Muryar Abba ta kirashi a kaurare. Kuma yanda sautin muryar Abban ya fito ne ya sa shi sauron kallon inda suke. Abban ya haɗe girar sama da ta ƙasa, hannayensa rungume a ƙirjinsa yana kallonsa. Dan yau ji yake ina ma ace Deena ba jinin ɗan uwansa ba ce, da ya nuna mata iyakarta. Sun yi shiru sun ƙyaleta tana iskancin da take so da sunan film ba wai dan basu isa da ita ba ne.
Tauqeer ya haɗiye yawu, sannan ya sauƙe jakar guitar ɗin dake bayansa ya miƙawa Iqra. Da sauri Iqra ta karɓa tana rarraba ido. Dan su ba su saba ganin Abba cikin irin wannan fushin ba. Hajiya Zayya kuwa na tsaye a gefe tana kallonsu ɗai-ɗai. A cikin ranta take faɗin Wallahi ko kuna so ko bakwa so sai Deena ta samu abun da take so, Tauqeer na Deena ne ko sama da ƙasa za ta gaɗe.
Tauqeer ya tsaya a gabansu Abba yana sunkuyar da kansa. Sai da Abba ya juya ya kalli Deena dake daf da fashewa sannan ya kalleshi yana goya hannyensa a baya.
“Ɗazu Deena ta zo take sanar da mu cewa wai ka riƙe wata yarinya. Mi ye gaskiyar wannan zancen?...”
“Wato ni ba ku yarda da ni ba? Shi ya sa kuke tambayarsa. Shin ni zan muku ƙarya ne?...”
“Kar ki sake cewa komai. Ki rufa mana bakinki a wurin ko na bugeki. A sanda kika zo kika tsaya a nan kina mana rashin kunya akwai wanda ya dakatar dake a cikin mu? Babu, dan haka dole ki bari shi ma mu ji daga bakinsa!”
Cewar Abby a fusace. Daddy kuwa kallon Deena kawai yake. Shi tun da yake bai taɓa jin yarinyar a ransa ba. Bai taɓa jin wani abu irin na soyyayar uba da ɗa na gudana a tsakaninsu ba. Bai taɓa kallonta a matsayin 'yarsa ba, shi ya sa baya shiga duka sabgarta. Ita ma kuma ba ta jinsa a ranta, saboda duk damuwarta ta duniya Mommy take faɗawa. Ko me za ta buƙata sai dai ta sanar da Mommy tun tana ƙarama har yanzu.
Zayya ta rintse idonta ranta na mata zafi. Ko da ƙuda bata fatan ya taɓa Deena. Duk wani abu da zai ɓata mata rai bata sonshi. Ta buɗe idonta tana jin wai me ya sa ba ta kawar da Mas'ud ba ne tuntuni?.
“Muna jinka Junior!”
Baffa ya faɗa.
“Ba da niyya na riƙeta ba. Ta zo wucewa ta kusa da mu, shi ne takalminta ya yage ta gurɗe za ta faɗi. Hakan ya sa na yi sauri na riƙo hannunta dan kar ta faɗi... Shi ne kawai!”
Abba ya sauƙe wata ajiyar zuciya asirrance.
“Deena tace tana buƙatar ku yi aure nan ba da jimawa ba, dan haka sai ka shirya!”
Da sauri ya ɗago da kansa ya kalli Abby. Dan ji ya yi kamar ya buga masa guduma a tsakiyar ka. Aure da Deena? Kai ba za iyu ba. Fuskarta ce ta haska a cikin kansa hakan ya sa ya yi ƙarfin halin ture wani ƙaton dutse da ya danne harshensa wurin faɗin.
“A gaskiya Abby ba zan iya auren Deena ba!”

DIYA POV.
Tafe take a gefen titi. Tafiyar kawai take, dan hankalinta baya jikinta. Hankalinta da nutsuwarta sun yi cilli zuwa wata duniya me nisa. Kuma hakan ya samo asali ne sakamakon tashin hankalin da rayuwarta ke ciki. Babu abun da ya fi ɗaga mata hankali sama da maganar da MD ya zo ya mata ɗazu. Cewa ya bata nan da kwana huɗu. Idan har bata amince da ƙudirinsa ba, zai koreta a aiki, sannan ya tabbatar da ya kawo ƙarshen rayuwarta...
Tunaninta ya datse, a sanda wani abu ya bangajeta da ƙarfin da har sai da ta yi baya tana shirin faɗuwa. Da sauri ta kalli matar da ta bangajeta. Sanye take da wasu shuɗayen kaya. Yanayin fuskarta ne kaɗai zai nuna maka cewar ba a hayyacinta take ba. Hannayen Diya ta riƙe gam-gam tana faɗin.
“Ka da ki bari su kamani. Ki temakeni 'yata. Wallahi da hankalina!”
Sunan 'yarta da ta kirata da shi ne ya sa wani yanki na zuciyarta zaftarewa ya faɗo ƙasa. Kamar yadda manyan gidaje ke rugujewa a sanda aka yi girgizar ƙasa. Ba ta san me ya sa ba, amma haka kawai ta ji matar ta daki zuciyarta da ƙarfi. Fuskarta ta tsirawa ido tana kallon idanuwanta dake kama da nata idanuwan.
Da sauri Rahila ta koma bayan Diya ta ɓuya tana kuka, jikinta sai rawa yake. Ɗazu da aka buɗeta za'a bata abinci ne ta samu damar guduwa. Kuma masu tsaron asibitin sun lura da ita. Dan yanzu haka ma sun biyota.
Diya ta juyo ta kalleta tana kamo hannyenta. Sai a lokacin ita ma Rahilan ta kalli fuskarta.
“Su waye za su kamaki?”
Cikin zare ido Rahila tace.
“Likitoci ne. Kama ni suka yi. Kuma Wallahi da hankali na 'yata. Sun rabani da jajaririyata tun tana ƙarama. Yanzu kuma so suke ni ma su ga bayana. Ki temakeni!”
Ko kafin Diya ta fahimci zancen da matar take mata. Wata motar ambulance ta faka a gefen titin. Sannan cikin abun da bai wuce sakan biyu ba, ƙofar baya ta ambulance ɗin ta buɗe. Wasu nurses biyu suka fito suka nufosu.
Rahila ta ƙara fashewa da kuka tana komawa bayan Diya.
“Wannan matar ta bayanki majinyaciya ce daga asibitin masu fama da cutar taɓin hankali. A yanzu ta tsere ne ba tare da sanin mu ba, dan haka ki yi gaggawar matsawa daga inda take!”
Cewar ɗaya daga cikin nurses ɗin. Diya ta haɗiye yawu tana matsawa. Da sauri su kuma suka cafko Rahila sannan suka zirara mata ruwan allurar dake riƙe a hannun ɗayarsu. Tuni Rahila ta fara layi tana kallon Diya.
“Yata kada ki bari su tafi da ni! Ban aikata komai ba. Da hankalina. 'Yata! 'yata!...”
Haka ta yi ta faɗi har suka sakata a cikin mota. Har motar ta bar wurin Diya na tsaye a wurin kamar wadda aka dasa. Ita kanta da za'a titsiyeta a dai-dai wannan lokaci da ba za ta iya faɗar takakamen abun da take ji ba. Haka kawai ta ji bata kyauta ba da ta bari suka ɗauke wannan matar. Sannan har cikin zuciyarta ta yarda da abun da matar ke faɗi na cewar ita ba mahaukaciya ba ce!. To me ya kamata ta yi dangane da lamarin wannan baiwar Allahn?.
______________
_Dan dan dan dan! Ana dara, sai ga dare ya yi_
_Shin kun lura da tun kafin HASKE ya shigo cikin Agha Mansion ya fara kauda duhu?_
_Saboda Tauqeer fa ya furta cewa ba zai iya auren Deena ba_
_Wani mataki kuke tunanin Hajia Zayya za ta ɗauka a kan hakan?_
_Kuma Tauqeer ya tabbatar da yana son ɗiyar yarabawa!_
_Salame kuma ta bar gida. Ina kuke ganin za ta nufa?_
_Me ya sa Rafeeq ya yi mafarkin Salame?_
_Diya da Rahila ma sun haɗu fa!_
_Me kuke ganin zai faru?_
_Dan idan baku manta ba Na ce muku yanzu aka soma wannan tafiya_
A. ISAH CE✍️.
***
*Assalamu alaikum jama'a!*
*A zahirin gaskiya bani da wasu kalmomi da zan yi amfani da su wurin nuna muku irin godiyata gareku. Haƙiƙa ku abun alfahari ne a ko ina. Ina me matuƙar godiya zuwa ga duk waɗanda suke bibiyata a duk rubutun da zan yi... Na gode Allah ya saka muku da alkairi. Allah biyaku da gidan Aljannah.*
*Ina me farin cikin sanar da ku cewa daga wannan page ɗin, wato feji na goma zan dakata a free pages. Sauran pages ɗin dake gaban wannan kuma dukansu za su kasance paid. A farashin da nake da tabbacin duk wani Salmanian zai iya biya domin nuna min so da kuma ƙauna.*
*Salmanian ku yi sani cewa ku ne ƙwarin gwiwata a ko da yaushe. Ku ne ababen alfaharina. Kuma na san ba zaku bani kunya wurin biyan kuɗin paid pages ba.*
*Na gode Na gode sosai!...*
~~~
_Sauran fajin littafi HASKE za su zo muku a kan ₦ 300_
_Ga duk wanda zai biya zai tura kuɗinsa ta wannan account ɗin da zan rubuta a ƙasa..._
_Kuma daga zarar kun biya za ku fara samun update a kan kari. Dan ba dakatawa za mu yi ba_
_A har kullum, kun de san cewa SALMA A. ISAH taku ce_
_Na gode da so da ƙauna_
I LOVE YOU WUJIGA-WUJIGA❤️😘.
Biya ta wannan account ɗin:
5487270431
Monie point.
Salma Ahmad Isah.
Shaidar biyata wannan number:
08131549317
Kada ku manta ₦ 300 ne kacal.
#SalmaAhmadIsah
#Haske
#TaurariWriters.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment