Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayansa.
“Ka san ina tsara ɓangaren karɓar bayanai na AI humanoid robot ɗin nan nawa, shi ya sa ba na fitowa”
“Shi ya sa na ga ka tara gemu?”
Ram ya yi dariya yana shafa gemun nasa. A lokacin kuma Mr. Thomas ya tsaya, hakan ya sa Ram ɗin ma tsayawa suka fuskanci juna.
“Zuwa gobe baƙin da muke jira za su zo, sun ce za su zo su ga device ɗin, kuma suna so su yi testing ɗinsa, idan har ta musu za a iya ƙera musu wasunsu, dan haka ya kamata ka zo”
Ram ya gyaɗa kansa, don ya gane wasu mutanene za su zo ɗin, mutanen da saboda su aka ɗauko shi daga branch ɗin GrowTech na Nigeria aka kawoshi na USA, don kawai ya haɗa musu device ɗin ake amfani da shi yasa mota tuƙa kanta da kanta, wato self-driving car. Kuma a zamansa na wata huɗu da ya yi a garin, ya samu nasarar haɗa musu device ɗin da yake saka mota a self-driving mode, duk da ba shi ne karo na farko da ya fara ƙera device ɗin ba, saboda ko motarsa tqna tafiya a kan tsarin self-driving ne. Kuma yanzu shi ne masu kamfanin motar za su zo don su duba device ɗin.
“Sai goben”
Mr. Thomas ya faɗi yana miƙa masa hannu, alamun su gaisa, shi ma miƙa masa hannun ya yi, suka gaisa sannan ya juya yana kiran Abdulrahman.
*
RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD, wanda aka fi sani da RAM haifaffen ƙasar Nigeria ne. A asalin sunan mahaifiyarsa shi ne Salamatu.
Salamatu ta kasance ɗaya daga cikin fulanin tashi na rigar Shariga. A cikin yawon kafa rigarsu ne suka sauƙa a wani daji dake kusa da garin Nguru dake jahar Yobe. Saida nono ya kasance sana'a ga duka matan aure da 'yan matan rigar. Hakan ya sa bayan sun sauƙa a dajin suka fara kaiwa tallar nono cikin garin Nguru.
Kuma a nan ne Allah ya haɗa Salamatu da wani buzun Niger me sunan Ahmadu. Tun farkon haɗuwarta da shi ya sanar mata da cewar shi maraya ne, kuma ci rani shi ne abun da ya kawoshi ƙasar Nigeria. Kan ka ce me soyyaya me ƙarfi ta ƙullu tsakanin Salamatu da Ahmadu. Har ta kai ga Ahmadu ya fara mata zancen aure. Hakan ta sa Salamatu turashi zuwa ga mahaifinta.
Ahmadu da limamin masallacin unguwar Hausari da Ahmadun ya sauƙa a gidan dake maƙotaka da nasa suka shirya domin zuwa nemawa Ahmadu auren Salamatu ɗiyar fulanin rifar Shariga.
Ko da suka je ba su samu tarbar girmamawa dag mahaifin Salamatun ba, don korar kare ya musu, tare da faɗa musu cewar shi ba zai aura wa 'yarsa kaɗo ba ma bare a je ga wata ƙabila da babu irinta a Nigeria wai su buzaye, don haka kada ya ƙara ganin ƙafarsu.
Haka Ahmadu da limamin nan me sunan Zakar suka kwaso ƙafafunsa gwiwoyi a sanyaye suka dawo Nguru. Ba don Ahmadu ya so ba, sai dan ya zame masa dole haka ya haƙura da soyyayar Salamatu, ya ci gaba da gudanar da sana'arsa ta kayan miya a kasuwar Nguru.
Kwatsam rana ɗaya sai ga Salamu a rumfar saida kayan miyan nasa, ganinta da kaya ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, ko da ya tambayeta me yake faruwa sai take sanar masa da cewar ita ta gudo daga rigarsu ne don su yi aure, a lokacin sai ya shiga yunƙurin ganar da ita kuskuren aikata hakan amma saboda soyyaya ta rufe mata ido sai ta nuna masa cewar ita fa ta riga da ta yanke hukunci, idan yana sonta su yi aure kawai, idan kuma ba ya sonta zata shiga duniya.
Gudun rasata ya sa ya amince da cewar za su yi auren, ya ɗauketa ya kaita gidan Kawu Zakar, sannan ya tsara masa halin da ake ciki, hatta da shi kansa kawu Zakar ɗin sai da ya yi ƙoƙarin ganin ya nunawa Salamatu kuskurenta, amma ta ƙi yarda da abun da yace.
Washe garin ranar da Salamatu ta gudo daga rigarsu, aka ɗaura aurenta da na Ahmadu, a ka sakata a gidan da Ahmadun ke haya, wanda yake kusa dana kawu Zakar. Tun kafin aurensu, Ahmadu ya riga da ya sanar mata da matsalar ciwon zuciya da yake fama da shi, wanda ya yi gadonsa daga wurin mahaifinsa.
Kuma bayan aurensu da shekara ɗaya ciwon nasa ya fara ƙamari, tun yanayin ciwon a tattafe, har ta kaishi ga kwanciya, a lokacin suna da shekara uku da aure, kuma a lokacin ta samu ciki. Bayan doguwar jinyar da ya yi fama a ita ta tsawon shekaru Allah ya amshi ran Ahmadu.
Ba ƙaramar damuwa mutuwarsa ta saka Salamatu ba, don har sai da aka bata gado a asibiti, ga tsohon cikinta haihuwa yau ko gobe, bayan an tasota daga asibitin, kawu Zakar yace ta dawo gidansa da zama. Ta ci gaba da zama da matarsa da kuma yaransa biyu. Bayan wasu wattani Salamatu ta haihu, ta haifo kyakkyawan yaronta na miji, wanda yake tsananin kama da ita, a lokacin sumar kansa ce kawai irin ta Ahmadu.
Bayan haihuwarta da wata uku, kawu Zakar ya tisata a gaba suka tafi zuwa rigar Shariga, domin ta je ta nemi yafiyar mahaifinta. Sai de kuma kash, sun makara, don kuwa ba su tarar da kowa a rigar ba sai wani mutu ɗaya, kuma shi ne ya sanar musu da cewar ai mahaifin Salamutu ya rasu shekara ɗaya baya, mahafiyarta kam da ma ta daɗe da rasuwa. Ƙawarta Dija ce kaɗai ta rage. Kuma sauran mutanen rigar sun tashi, ko shi ma ya saida wasu daga cikin shanunsa ne yana jiran a bashi kuɗin, daga an bashi zai bi bayansu. Amma kuma ya sanar musu da cewar mahafin Salamatun bai rasu ba sai da yace ya yafe mata. Haka Salamatu ta sha kukanta ta gode Allah, kafin ta ɗauki ɗanta ta bi kawu Zakar zuwa Nguru.
Haka ta ci gaba da zama a gidansa, tana renon ɗanta me suna Rafeeq. A lokacin da Rafeeq ya fara tasawa ta fuskanci cewar nauyi ya yiwa kawu Zakar yawa, hakan ya sa ta shiga yin sana'o'i da ban da ban, duk domin ganin goben ɗanta ta yi kyau.
Rafeeq na da shekara biyar a duniya suka fara fanin alamun ciwon mahaifinsa tare da shi, kawu Zakar da kansa ya ɗauke shi ya kaishi asibiti, kuma a asibitin ne suka sanar musu da cewar ciwon zuciya yake ɗauke da shi,wanda suke kyautata zaton gadarsa ya yi. Haka suka jera musu tarin ƙa'idojin da ya kamata ace sun kiyaye ganin ɗan nasu ya samu sauƙi, don babu batun warkewa gaba ɗaya a ciwon nasa.
Salamatu da Rafeeq ke kira da Maa tun yana yaro, ta ci gaba da fafutuka wurin ganin ɗanta Rafeeq ya taso cikin gata da kuma turba ta gari. Tun Rafeeq na ƙarami alamun baiwa da hazaƙarsu suka fara bayyana.
Domin shi ba kamar sauran yara gama gari yake ba, akwai shi da wata irin ƙwaƙwalwa me kaifi da kuma saurin haddace abu, ga shi da sanin makamar ƙirƙire ƙiren abubuwa. Yana ss2 a makaranta ya ƙera wani jirgin helicopter na kwali, hakan ya sa malaman makarantarsu suka ɗauki jirgin zuwa local government secretaria, daga nan ya tafi zuwa government house, kuma a nan ne aka saka sunansa a jerin ɗaliban da za su tafi ƙasar America domin yin karatun gaba da sakandire.
A lokacin ba ƙaramin farin ciki suka shiga ba shi da mahaifiyarsa, don Maa har da hawayenta. Bayan Rafeeq ya kamlla secondary kai tsaye ya wuce ƙasar USA domin ci gaba da karatunsa na matakin jami'a, inda ya fara karantar fannin mechatronics engineering. Kuma ko bayan da ya gama degree be dawo ba sai da ya haɗa da masters. Ko a lokacin da ya na Universityn babu wanda bai san RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD ba, kuma tsabar ƙoƙarinsa da sanin kan computer ne ya sa aka laƙabamasa sunan RAM, wato (Random Access Memory), wasu kuma kan kirashi da sunan ne domin su rage yawan sunansa, don idan ka kira sunan nasa a taƙaice RAM ɗin zai baka. Ƙwazonsa da hazaƙarsa ne ya sa bayan ya kammala makarantar manyan kamfanonin ƙere-ƙeren robotics da na software suka riƙa kawo masa dammamaki na yin aiki a ƙarƙashinsu.
Amma haka ya toshe kunnensa ya nuna sam shi ba ya buƙatar zama a ƙasarsu, ya fi so ya koma tasa ƙasar,domin su amfana a baiwar da yake da ita. Su kuma sam ba sa so su yi asarar ɗan baiwa kamar sa, hakan ya sa wani kamfani me sunan ‘GrowTech’ da suke da branch a Nigeria suka ba shi aiki. Kuma sai suka yi sa'a ya karɓi aikin. Daga nan ya tattara nasa ya nasa ya antayo Nigeria.
Sosai Maa ta yi farin cikin ganin tilon ɗan nata bayan shafewar tsawon shekaru, don tun bayan tafiyarsa ko sau ɗaya bai leƙo gida ba. Satinsa biyu a garin Nguru, ya ɗauki Maa suka shilla garin Abuja, a inda branch ɗin GrowTech ɗin yake, kuma da kuɗaɗen da suka ba shi ya sai musu wani madaidaicin kyakkyawan gida.
Sai de kuma a sunane yake ya bar USA, don har wa yau idan wani aiki ya tashi sai ya koma can ya je ya yi, hakan ta sa a can ɗin ma ya siyi gidan da zasu riƙa zama idan sun sauƙa a can US ɗin.
________
_Kun dai ji yanda tafiyar ta soma_
_Kun tuna da RAM ma'aikaci a ƙarƙashin KULIYA da ZAID?_
_To shi ne wagga_
A. ISAH CE✍️.
08131549317
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡️HASKE...️💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 04*
~~~
*Ƙauyen Wagini, Batsari local government, Katsina state, Nigeria.*
*07:00 na safe.*
A cikin wani madaidaicin gidan ƙasa, wanda ya ƙunshi ɗakuna huɗu, uku daga cikin gidan, ya yin da ɗaya ya kasance a soron gidan, wata farar mata da a ƙiyasin shekaru ba zata wuce shekara 44 ba, ta fito daga wani ɗaki ta na hama tare da miƙa, ɗankwalin kanta da ya since ta kai hannu tanan gyarawa, a lokancin da idonta ya. Kai kan tilon 'yarta dake zaune a rumfar da suka saba girki tana hura wuta. A lokaci guda ta saki murmushi.
“SALAME!”
Ta kira sunaun tana kallonta. A hankali matashiyar ta juyo tana aje maficin hannunta.
“Har kin tashi Inna?... Ina kwana”
Matar ta ƙarasa. Kusa da rumfar tana amsa gaisuwarta.
“Yayanki ya dawo?”
Salame ta ɗauki maficin tana amsawa da.
“Eh to, na ji motsinsa sanda na fito, amma ban sani ba ko ya ƙara fita”
Inna ta juya ta kalli hanyar soro, kasancewar ɗakin yayan Salamen a soron yake.
“Audu! Audu!”
Ta ƙwala kiran sunan yayan Salamen.
“Na'am Inna, gani nan”
Suka ji muryar Audu ta faɗi daga soro, kafin kuma ya shigo cikin gidan, har ƙasa ya tsugunna yana gaida mahaifiyar tasu, sai da ta amsa shi, tukkuna ya miƙe tsaye.
“Hamma Audu ina kwana”
Salame ta. Faɗi tana duban yayanta, da murmushinsa yace.
“Lafiya ƙalau Salma... Fatan kin tashi lafiya?”
Ya kirata da sunanta na gaskiya, kamar yadda ya saba kiranta da shi. Amsashi ta yi tana ɗora tukuyar ɗumamen dake aje a gefenta a kan murhu.
“Yau Muja lafiya?, Dan ban ga ya je masallci ba”
Cewar Audu yana duban mahaifiyarsu.
“Ah-ah, bai je masallaci ba kuma?. Sai da na tasheshi fa”
Inna ta faɗi tana duban ƙofar ɗakinta, inda ta san autan nata na ciki yana bacci.
“Ai kuwa bai je masallaci ba”
“Mts! Ba ri na je na taso shi”
Ta faɗi tana nufar ɗikinta. Yayin da Audu kuma ya nufi ɗakin babansu dake wani sashi na gidan. Salame kuma ta ci gaba da firfita wutar murhun dake gabanta.
“Inna na yi sallah fa”
Cewar Mujan da Inna ta samu nasarar koro ƙeyarsa daga ɗakinta. Ya fito sai murza ido yake. Salame ta kalleshi.
“Banda ƙarya auta, na san ba ka yi sallahr nan ba fa”
Salamen ta faɗi tana ci gaba da dubansa. Kuma a lokacin Inna ta fito daga ɗakin, ta ɗaga carbin da ta saba lazimi da shi ta cauɗawa autan nata a bayansa tana faɗin.
“Ai Wallahi Muja sai kowa ya ji kan mu ni da Kai a cikin gidan nan, in dai a kan Sallah ne, sai na yi maganinka, saboda iskanci irin naka, na tasheka dan ka je ka yi sallahr sai ka koma ka kwanta dan ka raina ni?!”
Tun bayan da ta samu nasarar cauɗa masa carbin ya finciki buta ya shiga banɗaki da gudu. Salame da Audu me za su yi in ba dariya ba.
“Ah-ah, ke Dija! A kan me za ki dakar min jika da safiyar Allah ta'ala!”
Cewar kakarsu Iya Abu tana ɗage labulen ɗakinta, tare da leƙowa kanta.
“Sallah ce fa be yi ba ”
Salame ta bata amsa tana dariya. Iya Abu ta ƙarasa fitowa daga ɗakin tana yatsina fuska.
“Kuma dan be yi sallah ba shi ne zata dake shi? Ai har yanzu Mujahid yaro ne, da sauransa, sai ana ɗaga masa ƙafa”
“Ban da abunki Iya, Muja fa ya kai shekara goma, idan be fara yin salah tun daga yanzu ba sai yaushe kenan?”
Inna Dija ta tambaya. Iya Abu na bata amsa, Baba ya fito daga ɗakinsa yana kallon Audu dake tsaye a bakin ɗakin. Audu na dariya suka ƙara gaisawa da maihaifin nasu, kasancewar tare suka je sallahr asuba.
“Iya kuma ma fa na yi sallahr, masanllacin ne kawai ban je ba”
Muja ya faɗi yana fitowa daga banɗakin, sai cuno baki gaba yake.
“Zo nan ɗan jikkallena, ai na san za ka yi sallahr, su ne ba su sanka ba”
Iya Abu ta faɗi tana miƙa masa hannu, a ɗarare ya gifta Inna ya isa zuwa ga Iya Abu, duk kuwa da ya san ba lalle Innan ta sake dukansa ba, tun da ga Iya abu da Baba a wurin.
“Ka zo ka siyo mana koko a gidan Marka”
Cewar Inna tana miƙa ma ɗari biyu. Iya Abu ta kai hannu ta fisge kuɗi.
“Kai Sa'adu! Wai ni kai ne ka ɗaurewa Dija gindi take bautar mi da jika?”
Baba dake tsaye a ƙofar ɗakinsa ya girgiza kai.
“Ni a wa? Kare da gudun layya, Wallahi Iya ban san zancen ba”
Iya Abu ta yi ƙwafa.
“Ke Salame sai ki tashi ki je ki siyo kokon, jikana bai ƙoshi da bacci ba, dan haka zai koma”
Ta ƙara she tana miƙawa Salame kuɗin. Salame ta miƙe, ta ja hijabinta na yadin tayabo yalo, dake rataye a jikin igiyar shanya. Ta saka hijabin, sannan ta karɓi kuɗin. Ta fita tana dariya.
Tana fita daga gidan suka haɗu da ƙawarta Karime.
“Salame in zuwa haka?”
Salame ta tsaya tana kallonta.
“Siyan koko zan je, yanzu Iya Abu ta tada balli da sassafen nan, wai auta ba zai je siyan koko ba”
Karime ta yi dariya yayin da suka ci gaba da tafiya, dan ita ma gidan Markan ta nufa.
“Iya Abu hoo... Yau za ki je yin ice?”
Salame ta gyaɗa mata kai.
“Kin san yau ranar kasuwa, baba da hamma za su je kasuwa, shegiyar ƙiwar auta ba za ta barshi ya je daji ba, dan haka babu me zuwan sai ni...”
Haka suka ci gaba da hira har suka kai gidan Marka me koko. A tare suka dawo bayan sun sai kokon, Salame ta shiga gidansu, yayin da ita ma Karime ta wuce nasu gidan dake ɗan gaba da na su Salame.
________________
*11:04 na rana.*
“Zo ka raka ni auta”
Cewar Salame tana zura hijabinta dake riƙe a hannunta. Auta dake zaune yana haɗa dokin kara a tsakar gidan, ya ɗago da kansa ya kalleta.
“Ina?”
Ya tambaya.
“Yin ice”
Ta bashi amsa tana dubansa. Inna dake zaune a kan tabarma tana tsintar shinkafa ta dubesu tana faɗin.
“Ba tare da Karime kika ce zaku je ba?”
Salame ta dubeta.
“Eh, ina so na yi itacen da yawa, kin ga ai sai ya tayani da ɗauka ko?”
“Kuma haka ne”
Inna ta faɗa tana meda hankalinta kan tsintar da take.
“Ko ba zaka je ba?”
Salame ta tambaya ganin Mujan ba shi da niyyar miƙewa.
“Idan ba zai je ba kar ki takurashi mana”
Cewar Iya Abu da ta fito daga banɗaki, hannunt riƙe da buta.
“A'a, zan je”
Cewar Muja da ya miƙe tsaye. Salame ta sashi a gaba suka fita.
“Kukula fa Salame!”
Cewar Iya Abu.
“In Allah ya yarda!”
Salame ta amsa suna ficewa daga gidan. Sai da suka biya ta gidan su Karime, kafin suka nufi daji dan yin ice. Ko da suka iyo icen Muja be bar Salame ta ɗauka da kanta ba, duka ya loda a kansa yana faɗin.
“Muje Adda”
Salame ta yi murmushi, duk ƙiwar Muja a kan Salame ba ta aiki, dan zai iya yi wa kowa ƙiwa, amma ban da ita.
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*06:44 na yamma.*

DIYA SHOLA POV.
Tana dawowa daga wurin aiki ta shiga wanka, bayan ta fito ta sauya kayanta, a 'yar rumfar dake gaban gidansu ta iske Papi zaune a kan tabarma kamar kullum, ya miƙe ƙafarsa me lafiya, yayin da guntilalliyar ƙafar tasa ke nan a yanda take. Ɗaki ta shiga, inda ta iske Gigi tana zuba musu eba da stew ɗin da ta girka.
“Yauwwa Diya, zo ki miƙawa Ekene nasa”
Cewar Gigin tana miƙa mata kwanon dake ɗauke da anbincin Ekene. Shola ta saka ɗan ƙaramin farin hijanbin data saba sakawa, sannan ta ɗauki kwanon tana faɗin.
“O dara (To)”
Fita ta yi daga ɗankin, ta wuce Papi dake zaune a kan tabarma.
“Ina zaki je?”
Ya tambayeta.
“Ekene zan miƙawa abinci”
Ta amsa masa tana juyowa, kansa ya gyaɗa mata sannan ta juya ta tsaya a jikin rumfar gidan kwanan su Ekene ta shiga ƙwala masa kira.
Asalin sunan Ekene shi ne Musa, musulmi ne kuma ɗan ƙabilar igbo, haifaffen wani ƙauye ne dake can Enugu. Tun yana ƙarami iyayensa suka rasu, kuma ya girma ne a hannun wani kawunsa da matarsa da yasha wahala a wurinsu, bayan ya girma ne ya gudo daga ƙauyensu ya iyo garin lagos.
Kuma tun bayan zuwansa Makoko Allah ya haɗa jininsu da Gigi da kuma Diya, hakan tasa ya zama kamar ɗan gidan, dan har kwanan gobe ba shi da 'yan uwan da suka wuce su Gigi, sai abokansa da suke kwana tare.
“Musa! Musa!...”
Shola ta kira sunansa na gaskiya, jin har yanzu bai amsa ba balle ya fito.
“Mu kin cika mana kunne da kiran Ekene, ni ba kya nema na?”
Diya ta juya ta kalli gidan dake manne da nasu, dan ta san muryar babbar ƙawarta ce, FA'IZA. Kuma kamar yanda ta sani, ita ɗin ce ta leƙo daga tagar ɗakinsu. Sai wani murmushi take mata.
“Ni ban sanki ba”
Cewar Diya cikin harshen yarbanci. Fa'ee ta wurgo mata harara.
“Wata gulma ce kuma ta sauya harshen?. Malama ina za ki min hausa ki min, ni bana san gulma ehe!”
Fa'ee ta ƙarashe tana ƙara manna mata harara. Shola ta yi murmushi.
“Wasa nake miki fa, ina nemanki Allah, ɗazu kafin na fita ma sai da na tambayi Mama ina kike, tace min wai kin je aiki”
Ta faɗi cikin harshen Hausa, kamar ita kaɗai ce yaran da ta iya.
Fa'iza ta fito daga ɗakinsu tana taka katakwayen da suka haɗa gidansu da na su Shola tana faɗin.
“Wallahi, kin san ogan namu ne ba sauƙi, kana kuskurewa zai seta maka hanya”
ta ƙarashe tana tsayawa a setinta.
“Wai ina Ekene ne?”
Fa'ee ta tambaya tana kallon ɗakinsu Ekene. Nan take fuskar Shola ta rikiɗa zuwa damuwa.
“Yau da safe ma fa banganshi ba, sai Oliver ne ya fitar da ni, ban sani ba ma ko ba shi da lafiya...”
Ta ɗan dakata da maganar, ganin Lamu abokin Ekene ya fito daga ɗakin kwanansu, fuskarsa ɗauke da damuwa yake dubansu.
“Lamu ina Ekene?”
Diya ta tambaya, ko kafin ya bata amsa, Gigi dake zaune a rumfa ta fito ta tsaya kusa da su hankali tashe, dan duk abun da suke faɗi tana ji, haka Papi ma kallonsu yake, dan ya ji me ke faruwa da Ekene.
Lamu ya sunkuyar da kansa yana sosa hannunsa. Sannan ya furta abun da ya zama sannadiyyar haɗuwarsu da dalilin sauyawar rayuwar ɗaya daga cikinsu.
“Jiya da daddare muna zaune a rumfarmu ta 'yan fito, 'yan sanda suka zo suka rufamu da duka, daga bisani kuma suka ɗauki Ekene suka tafida shi!”
Nan take kwanon Ebar dake hannun Diya ya suɓuce ya faɗo ƙasa. Bakinta a buɗe hankalinta a tashe take duban Lamu. Ita ta san cewa Ekene bai aikata wani lefin da za'a kamashi ba, dole abun da aka saba yi wa sauran matasan Makoko ne ya faɗa kansa.
Wannan abun sababbe ne a yankin Makoko, gurɓatattun 'yan sanda dake kusa da yankin Makoko, kan karɓi cin hanci daga hannun manyan masu lefi idan sun kamasu, daga nan sai su sakesu, su zo yankin makoko su kama matasan yankin, sannan sun jefa musu lefin. To bana kuma kan ƙaninta abun ya faɗo?!.
*Agha Mansion, Lekki Phase 1, Lagos State, Nigeria.*

TAUQEER POV.
“You're like a ray of sunshine, Brightening my every day... You're like a breath of fresh air, Filling my lungs with glee... You're like a warm summer breeze, Making me feel free... You're like a song that never ends, Always making me grin... You're my everything, my dear, The joy that I live in...”
Waƙar da yake rerawa kenan. Waƙar me sunan Sunshine, na ɗaya daga cikin waƙoƙinsa da ya fi so. Tsaye yake a jikin dressing mirror yana taje sumar kansa irin ta asalin fulani, wadda ba ta cika tsayi ba, kasancewar tana cikin askin buzz cut.
Sanye yake da khaki trouser milk color, da kuma baƙar T-shirt, me ɗauke da makeken hoton fuskarsa a gaba, daga ƙasan hoton fuskar tasa kuma sunansa ne a rubuce 'TAUQEER AGHA' yayin da bayan rigar kuma ke ɗauke da rubutun 'GOAT' (Wato Greatest Of All Time). Rigar na ɗaya daga cikin kayansa da ya fiso a duniya. Ba wai dan rigar na da tsada ba, sai dan matsayinta gareshi. Ɗaya daga cikin masoyansa daga ƙasar south Africa ne ya turo masa ita, ranar da ya ƙara yake wani Birthday partynsa. Hakan ya sa yake matuƙar son rigar.
Juyawa ya yi ya ɗauki wayarsa bayan da ya gama taje sumar tasa. Sannan ya fita daga ɗakinsa yana nufar babban falon gidan dake down stairs. Yana karyo kwanar da ɗakunan samarin gidan take ya hangi mahaifiyarsa ta fito daga ɗakinta, hannunta riƙe da kwalbar zuma. Wadda ya san a shayin mahaifinsa za'a saka shi. Dan a lokaci irin wannan, mahaifinsa da ƙannensa sukan zauna su sha shayi. Da sauri ya ƙarasa kusa da ita yana rungumarta ta baya.
“Ya kike? Habibty”
Ya faɗi yana sumbatar gefen fuskarta. Umma ta yi murmushi tana kallonsa yayin da ya saketa.
“Lafiyata ƙalau Junior, ya gajiyar hanya?”
“Gajiya ta bi jiki Habibty”
Ya amsa mata yana karɓar kwalbar hannunta. Tare da ita suka jero har suka sauƙo ƙasa, inda ya iske mutanen gidan gabaki ɗayansu nan zaune. Daga can wani ɓangare na falon iyanyensu maza ne ke zaune suna shan shanyi kamar yanda ya sani, yanyin da a ɗayan ɓangaren kuma, iyayensu mutane ke zaune, kowa yana sabgarsa, daga wani ɓangaren kuma gabaki ɗaya yaran gidan ne ke tasu sabgar. Ɓangaren da iyayensu maza suke ya nufa, yayin da Umma ta nufi inda matan gidan suke, dan daman a wurin take zaune, Abba ya mata magana kan ta ɗauko masa zuman da ya saba sakawa a tea.
“Ya kake Habiby?”
Tauqeer ya tambaya yana ma Abba side huge. Murmushi kwance a kan fuskar Abba ya amsa masa da.
“Lafiya Junior”
Abban ya amsa kamar yadda ya saba, kafin Tauqeer ɗin ya shiga gaisawa da kawunansa dake wurin.
“Daddy!”
Ya kira sunan Daddy da ɗan ƙarfi, ganin ya kirashi har sau biyu bai amsa ba, kuma dama can shi haka yake, sau tari za ka ganshi ya zauna ya yi shiru yana tunani, kuma hakan ya samo asali ne sakamakon ɓatan matarsa ta biyu.
Firgigit Alhaji Tayyab Agha ya dawo duniyar zahiri ya dubi Tauqeer. Da ƙyar ya ƙaƙalo murmushin yaƙe ya yafa a kan fuskarsa, kamar yadda ya saba jifan sauran jama'a da irin murmushin. Saboda murmushin kan tsaya a kan laɓɓansa ne kawai, dan tun bayan ɓatan matarsa Rahila ya shiga yin irin wannan rayuwar.
“Tauqeer!”
Ya faɗi yana kallonsa. Tauqeer ya girgiza kansa yana murmushi, hakan ba wai sabon abu ba ne game da kawunasa.
“Na'am Daddy”
“Ashe ka dawo?, ya Abu Dhabi?”
“Wallahi Baffa, yau da yamma na Samu isowa”
Baffan ya gyaɗa kansa yana ƙara yin nitso a cikin kogin tunanin da ya saba linƙaya. Alhaji Muzammil Agha ya girgiza kansa yana murmushi.
“Hamma kenan”
Ya faɗi yana aje newspapern dake hannnunsa. Tauqeer na murmushi ya miƙe zai bar ɓangren nasu, maganar Abba ta dakatar da shi.
“Junior”
“Na'am Habiby”
Ya amsa yana juyowa.
“Fatan Munira (matemakiyarsa) ta faɗa maka meeting ɗinka da kamfanin GU Industry a gobe?”
Tauqeer ya gyaɗa kansa.
“Eh, ɗazu take sanar da ni, kuma insha-Allah zan halarta...”
“Tauqeer! Ɗazu na duba jadawalin shige da ficen kaya na watanan, amma ban ga na satin nan ba, kuma Yahaya ya ce min

Please Login or Register in order to submit comment