Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an turawa kamfanin Almak kaya a satin nan”
Cewar Alhaji Muzamill Agha. Tauqeer ya gyaɗa kansa cikin faɗin.
“Eh, an tura musu kaya, kuma jiya aka sake sabon jadawali, ban san yaushe ka duba ba”
Muzamill Agha da yaran gidan ke kira da Baffa ya gyaɗa kansa yana so sa girarsa.
“Eh to da yake shekaran jiya na duba jadawalin, shi ya sa ban ga na satin nan ɗin ba”
Tauqeer ya gyaɗa kansa.
“An sake sabon jadawali, zan tura office ɗinka zu wa gobe”
“Ok sai na jika”
Baffa ya faɗa yana dubansa, Tauqeer ya juya ya barsu suka ci gaba da hirarsu da suka saba.
Daga nan inda iyayensu mata suke ya nufa, ya gaida su ɗaya bayan ɗaya, Hajiya Zayya ta amsa tana wani murmushi da ita kaɗai ta san na miye, Mama ta amsa baki washe kamar yanda ta saba, Amma kuwa kadaran kadahan ta amsa.
Ya miƙe ya bar sashen da suke yana nufar inda sauran 'yan uwansa suke. Gaba ɗaya yaran gidan suna wurin, idan ka ɗauke Deena da dama can ita bata zama a cikinsu kamar kowa, sai Jamal da baya gidan, kusan sati biyu.
Kusa da Saif ya zauna suna gaisawa, saboda kaf gidan babu wanda jininsu ya haɗu sosai da shi kamar Saif ɗin, duk da tsaurin halin Saif ɗin da kowa ke ga a gidan, ba ya nunawa Tauqeer, dan sosai suke shiri da shi.
“Hamma Taj ka ga makin da na samu a Homework ɗina da aka yi marking yau!”
Cewar Nimra tana nunawa Taj littafinta. Taj ya aje wayar hannunsa yana karɓar littafin nata.
“La la la la! Ai kuwa kin yi ƙoƙari mutuniyar”
Nimra ta ƙyalƙyale da dariyar jin daɗi.
“Nawa ta samu?”
Hammad ya tambaya yana matsawa kusa da su. Taj ya karkata masa littafin yana bashi amsa da.
“7 a cikin 10”
Hammad ya karɓi littafin nata yana ci gaba da dubawa.
“Suuuuu! Yarinya ta ciyo ta bayan Ronaldo!”
Gaba ɗaya suka kwashe da dariya, dan sak irin abun da Ronaldo ɗin ke yi a duk sanda ya yi nasara a wasansa ya gwada.
“Kai fa Aabis?”
Tauqeer ya tambaya. Da gudunsa Aabis ɗin ya miƙa masa littafin. Kuma tun kafin ya duba abun da ya samu, Aabis ɗin yace.
“9 over 10!”
“Give me five my friend”
Tauqeer ya faɗi yana miƙa masa hannu, Aabis ya ɗaga nasa hannun suna tafawa.
“Miƙomin ni ma na gani”
Cewar Nasir yana miƙo masa hannu. Tauqeer ya miƙa masa littafin yana faɗin.
“Next time ina so ka cin ye duka. Ni na san me zan baka”
Ya ƙarashe yana duban Aabis ɗin.
“Omoh! Wannan yarinyar fa tana wuta!”
Cewar Iqra, a sanda ta gama duba littafin Nimra dake zaune a gefenta.
Saif ne ya lura da Bobo da Khabir dake zaune a gefe suna zazzara ido. Zamansa ya gyara yana aje mug ɗin hannunsa.
“Bobo, Khabir! Ina naku homework ɗin?”
Khabir ya haɗiye yawu, yayin da Bobo ya ci gaba da cin meat pie ɗin dake hannunsa.
“Ba ku ji me nace ba ne?”
Ya faɗi yana tsaresu da ido, tuni suka shiga taitayinsu, dan da ma kaf gidan babu me zafin rai irin na Saif, kuma halin nasa shi ne ya banbanta shi da Taj.
“Nawa ku ka samu?”
Hammad ya tambaya, a sanda hankalin kowa ya dawo kansu.
“Ni... Ni... Ni 4 na samu”
Khabir ya faɗa.
“Kai kuma fa?”
Taj ya tambayi Bobo.
“2 na samu”
“Aikin kenan ai, har gwanda Khabir a kan kai Bobo, ban da ci babu abun da ka iya!”
Bobo ya turo baki gaba yana aje meat pie ɗin hannunsa.
“To yanzu Hamma Saif idan mutum bai ci abinci ba me zai ci?”
“Za ka ci duka!”
Haka suka ci gaba da yi wa Khabir da Bobo faɗa a kan rashin meda hankalin da suke a kan karatunsu.
A dai-dai lokacin Deena ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da wani bowl me ɗauke da vanilla yoghurt, ɗayan hannun nata riƙe da wayarta tana dannawa. Tana sanye da pyjamas. Kwatsam ta ci karo da mutum, hakan ya sa yoghurt ɗin dake hannunta zubewa a jikinta.
Nan take jikin 'yar aikin gidan me suna Aliya ya shiga ɓari, dan ta san wata ƙila yau tata ta ƙare, har ƙasa ta tsugunna tana bata haƙuri, tuni ta fara hawaye.
“Dan Allah Madam ki yi haƙuri, ki yi haƙuri dan Allah, na yi ta kauce miki, ke ce kika bangaje ni!”
Deena ta kalli jikinta, sannan ta kalli Aliyan dake durƙushe a gabanta jikinta na kyarma, hannunta ta ɗaga ta sharara mata marin da ya sa Aliyan ɗaukewa wuta.
“Shashasha talakar banza, ke har kin isa ki goga jikinki da nawa? Waye ibanki a Lagos? ”
Aliya ta share ƙwalla tana miƙewa tsaye, hannunta dafe da kuncinta.
“Ki yi haƙuri Madam, amma Wallahi ke ce baki lura ba!...”
Hannunta ta ƙara ɗagawa za ta ƙara mata wani marin, ta ji an riƙe hannun nata, ta juyo a fusace ta fisge hannun nata. Cikin matsanancin ɓacin rai ta ci gaba da kallon Saif da ya riƙe mata hannu, dan a duniyar Allahr nan, babu wanda ta tsana kamar Saif ɗin, dan shi ne wanda yake shige mata hanci da ƙudundune.
“Kai waye da za ka riƙemun hannu, SAIFUDEEN MAS'UD AGHA?”
Ta kira cikakken sunan nasa kamar yadda ta saba. Saif ya shiga goge hannunsa yana faɗin.
“Ni ne ya kamata na tuhumi kaina da na riƙe hannun mace mara sanin darajar kanta irinki!”
Deena ta yi murmushi tana ci gaba da dubansa.
“Saifudeen Agha kai ba sa'an yin faɗana ba ne, dan haka ba ni da lokacin ɓatawa a kanka, ka bari sai ka kai stage ɗin da nake tukunna”
Ta juya tana shirin barin wurin.
“A haka za ki ƙare babu mijin aure!”
Abba ne ya daka masa tsawa cikin faɗin.
“Wata irin magana ce wannan Saif? A matsayinta na 'yar uwarka kuma ƙanwarka ya zaka na faɗa mata haka? Memakon ka yi faɗa da duk wanda zai faɗa mata haka sai kai kana faɗa da kanka? Ku kenan kullum cikin faɗa kamar kaji!...”
Deena ko juyowa ba ta yi ba ta haye sama. Shi kuma Saif ya sunkuyar da kansa yana bawa Abba haƙuri.
Tauqeer dake zaune saɓanin sauran mutanen falon da suka miƙe tsaye tun bayan fara faɗan Deena da Saif ya dafe kansa, dan ya san da ma dole abun ya gangaro zuwa kansa. Damuwarsa biyu ce a duniya, auren Deena da baya so da kuma halin da ƙaninsa ke ciki!.
“Dare ya yi, kowa ya je ya nemi makwanci!”
Cewar Mas'ud Agha cike da umarni, ɗaya bayan ɗaya yaran suka shiga watsewa suna nufar ɗakunansu.
Sai da kowa ya watse a falon, sannan Hajiya Zayya da aka bari ita kaɗai, ta cije leɓenta na ƙasa tana jijjiga kai, dole ne ta yi wa tufkar hanci.
___________
_Hello!. Salmanians!_
_Shin da wa kuke ganin Fa'ee da Diya za su haɗu?_
_Kuma shin wani hali ƙanin Tauqeer wato Jamal ke ciki?_
_Me nene a ran wannan Hajjiya Zayyan?_
A. ISAH CE✍️.
08131549317
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡️HASKE...💡️*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 05*
~~~

DIYA POV.
Da gudu ta shiga cikin ofishin 'yan sandan dake yankin Makoko. Fa'ee ce biye da ita, gaba ɗaya hankalinsu a tashe yake.
“Yallaɓai! Yallaɓai! Ƙanina! Ƙanina Yallaɓai...”
Shi ne abun da ta shiga faɗi kenan tana hawaye.
“Me ya faru za ku zo kuna neman tada mana hankali?”
Cewar wani baƙin ɗan sanda me shirgegen ciki yana susar kunne. Diya ta share ƙwallarta tana faɗin.
“Ƙanina Yallaɓai, an kamashi ba tare da ya aikata laifin komai ba!”
Sheƙeƙe 'yan sanda dake bakin aiki su biyu suka kallesu.
“Me kike nufi da bai aikata laifin komai ba?”
Cewar ɗaya ƙyamurmurin ɗan sandan yana ƙarewa hallitar jikin Diyan kallo. A wannan karon sai ta kasa magana, dan haka Fa'ee tace.
“Yallaɓai ƙaninta ne aka kama ba tare da ya aikata laifin komai ba...”
“Ke! I mana shiru! Kuma da aka kama shi sai aka ce yana nan ko?”
Baƙin ɗan sandan ya faɗi cikin daka musu tsawa. Ekene Musa dake zaune a cikin cell ya ji kamar muryar 'yar uwarsa na kuka a waje, hakan ya sa ya miƙe daga inda yake zaune ya leƙo ta tskanin ƙarafunan cell ɗin ya kallesu, a lokacin da take ci gaba da yi wa ɗan sandan bayani. Nan take ƙwalla ta cika idonsa, shi da ma ya san cewa Diya ba zata barshi haka ba, babu abun da ya haɗashi da ita, amma ya san da cewa tana jinsa a ranta kamar ɗan uwanta na jini. A sanyaye ya kira sunanta.
“Diya!...”
Da ƙyar muryar tasa ta fito cikin kiran sunan, Diya data ke ci gaba da yi wa 'yan sandan bayani, ta kalli ƙofar cell ɗin da ta ji kamar muryar ɗan uwanta. Nan take hankalinta ya yi mugun tashi, ganin fuskar ɗan uwan nata da ta ci duka.
“Ekene!”
Ta kira sunan a iyaka kan leɓenta. Hawaye wasu na bin wasu, kafin ta buɗe baki da ƙyar ta kira shi.
“Musa! Musa! Musa... Yallaɓai wancan shi ne ƙanin nawa, shi ne ƙanina Yallaɓai!”
Ta faɗi tana nuna masa ƙofar cell ɗin, a tare 'yan sandan biyu suka kalli inda take nunawa, kafin suka juyo suka kalli juna, yanzu suka fahimci inda zancen ya dosa, a jiya aka kawo musu ƙarar wani ɓarawo da ya shiga gidan wani me kuɗi ya yi sata.
Kuma ta hanyar bayanan da masu kayan suka basu ne suka kamo me lefin, ama kuma me lefin sai ya basu kuɗaɗe, ya ce dasu su bar shi ya tafi. Kuma sun sake shi ya tafi ɗin. Sanin cewa su masu kayan ba shiru za su yi ba, ya sa su aikata kalar abun da suka saba, wato kamo waɗan da basu ji ba basu gani ba su jefasu a cin lefin. Kuma ko da suka je Makoko Ekene Musa suka kamo, duk kalar dukan da suka masa a jiya kan ya amsa lefin, ya ƙi, ama kuma duk da haka ba su saduda wurin dukan nasa ba.
“Kai ku fice ku bar nan!”
Baƙin ya faɗi yana miƙewa. Ran Diya ya soma ɓaci.
“A kan me za mu fice? Bayan ga ƙanina na ga kun kama, kuma sai ku ce mu fice?”
Haka baƙin ya shiga musu korar kare, yayin da ƙyamurmurin ya bada himma wurin ƙarewa Diya kallo.
Ba dan su Diya sun so ba haka Fa'ee ta jata suka fita, sai tafiyar ta gagari Diya, hakan ya sa ta zube gwiwoyinta a ƙasa tana risgar kuka, Fa'ee ta dafata tana faɗin.
“Dan Allah Shola ki tashi mu tafi, kin san halin 'yan sandan nan ba mutunci ne da su ba”
“Me ya sa zan tafi na bar Ekene a nan? Ki na ganin irin dukan da suka masa fa? Idan na tafi wata ƙila su kasheshi! Wallahi babu inda zan matsa daga nan, sai da ɗan uwana!”
Fa'ee ta goge ƙwallar tausayin ƙawarta, ta tsugunna ta ci gaba da bata haƙuri.
“Na ce ba?”
Suka ji muryar ɗan sandan nan a bayansu, hakan ya sa suka juya a tare, ƙyamurmurin nan ne ya ke tsaye a kusa da su yana musu wani irin murmushi. Da sauri Diya ta miƙe tana kallonsa, dan a ganinta, temakonta zai yi.
“Ki dena kuka, zan iya temaka miki”
Da sauri ta share ƙwallar idonta tana haɗiye yawu.
“Za ka iya fito min da shi ne?”
Ta tambaya idonta na hasko mata fuskar Ekene ɗauke da raunika. Ɗan sandan ya gyaɗa mata kai yana mata wani irin kallo, tuni Fa'ee ta ɗago jirginsa, banda Diya da hankalinta ya bar gangar jikinta.
“Yanzu ma kuwa, amma da sharaɗi!”
Ta kuma share wata ƙwallar tana gyaɗa kai.
“Menene sharaɗin? Faɗa mij in ji?”
Sai da ya haɗiyi miyau, ya juya ya kalli Fa'ee dake masa wani kallo me kama da harara, amma da yake bashi da kunya sai ya yi kamar bai gane ba. Ya dawo da jajayen idonsa kan Diya.
“Akwai ɗakina dake bayan layin can, za ki bini muje... Ai kin dai... gane ko?”
Ya ƙarashe yana taɓa botirin gaban rigarsa. Diya ta gyaɗa kanta.
“Ni kuwa na gane...”
Ba ta ƙarashe ba ta ɗauke shi da mari. Ba ɗan sandan kaɗai ba, har da Fa'ee sai da ta tsorata, kuma marin da ta masa ne ya jawo hankalin mutanen dake harabar wurin. Diya bata saduda ba ta nuna shi da yatsa.
“Kai a ganinka ni zan iya yarda da ƙazamar buƙatarka? Kun kama ɗan uwana ba bisa laifin komai ba, kuma yanzu ka zo kana buƙatar mutuncina?, Na gwammaci na je na tsaya a kan titi mota ta take ni, da dai na baka mutuncina!...”
Haka ta ci gaba da masa wankin babban bargo, har jama'a suka fara taruwa suna tambayart abun da ya faru, shi kuma ɗan sandan ya kasa furta komai.
***
A hankali wata farar mota ƙirar Audi Q6 ta yi parking a harabar ofishin 'yan sanda dake Makoko. Cikin abun da bai fi sakan huɗu ba, ƙofar motar daga ɓangaren direba ta buɗe, wani farin kyakkyawan matashin bafulatani ya fito, sanye cikin kayan 'yan sanda. Hannunsa riƙe da wayarsa da kuma hular kayan nasa na 'yan sanda, idonsa manne da baƙin glashi, wanda ya ƙara fito da farin fatarsa.
Tun daga jikin motar tasa ya hangi mutane na taruwa a kusa da ofishin 'yan sandan. Ya ɗan yamutsa fuska cikin mamaki, to me yake faruwa?, me zai haɗa ofishin 'yan sanda da hayaniyar faɗa?, Dan bisa ga dukkan alamu faɗa ake a wurin.
Hular kayan nasa ya sanya a kansa, sannan ya saka wayarsa a aljihun wandonsa, cikin takunsa na nutsuwa ya soma tafiya yana nufar inda mutanen ke taruwa, duk kuwa da ba shi da niyyar zuwa wurin, dan shi ba a nan ofishinsa yake ba. Kuma ba wai aiki ya kawoshi ofishin ba, saboda tun ƙarfe biyar na yamma ya tashi daga aiki, mantuwa ya yi, shi ya sa ya dawo domin ya ɗauka.
“Constable! Me yake faruwa ne?”
Saliha, kuma kamillalliyar muryarsa ta faɗi a sanda ƙafafuwansa suka tsaya daf da inda faɗan ke faruwa. Cikin hanzari Constable ya juyo, jin muryar chief inspector SAM. Shi ɗin ne kuwa tsaye a gabansu, nan take cikinsa ya yamutsa cike da tsoro, gumi ya shiga tsatsaffo masa, cikin daburcewa, ya ɗaga hannunsa na dama ya sara masa yana faɗin.
“Sir! Sir... Sir wannan yarinyar ce... Ta zo nan take neman tada mana hankali!”
A take ya shararo ƙaryar, idonsa na haskawa da matsanancin tsoron dake tasowa tun daga zuciyarsa, dan idan har Chief inspector SAM ya ji abun da suke aikatawa, tasa ta ƙare, dan SAM ba ya ɗaya daga cikin gurɓattattun 'yan sanda, akwai shi da tsayawa gaskiya duk rintsi.
Sai a lokacin idonsa ya sauƙa a kan yarinyar dake faɗa da Constable ɗin, nan take zuciyarsa ta buga da ƙarfi, jin wani abu me kama da tsinin mashi ya cakeshi a tsakiyar zuciyarsa, da za'a ɗora masa wuƙa a wuya a dai-dai wannan lokacin, a tambayeshi ya faɗi abun da yake ji a lokacin ba zai iya ba, dan shi kansa bai san sunan wannan abun ba, wani yanayi ne da tun da yake bai taɓa shiga ba.
Kuma daga wannan lokacin ne, wani babi na rayuwarsa ya buɗe, dan wannan yanayin da ya tsinci kansa a ciki shi ne zai yi wani tasiri a cikin rayuwar tasa. Ya iuma zama dalilin haɗuwarsa da HASKEn sa.
Diya ta yi murmushin takaici, dan Constable ɗin cikin harshen hausa ya yi maganar, a zatonsa ba sa jin hausa, dan tun da suka zo da yarbanci suke magana. Kuma lokaci guda ta kalli ɗan sandan dake tsaye a gabansu.
“Ƙarya yake yallaɓai!"
Ta faɗi idonta na cika da ƙwalla, chief inspector Sam ya kalleta da kyau, dan sai a sanda ta yi maganar ta dawo da shi zahiri.
“Menene ainahin abun da ya faru?”
Ya tambaya. Tun daga A har Z sai da Diya ta feɗe masa biri har wutsiya, kuma ta sanar da shi kalar zaluncin da 'yan sanda irin Constable ɗin ke yi a yankinsu. Cike da mamaki da ruɗani ya kalli Constable ɗin, dan wannan ɗin abu ne da bai taɓa cin karo da makamancinsa ba.
“Constable Adebayo! Me nake ji haka?”
Ya tambaya idonsa na shirin sauya kala, dan tun bayan fara aikinsa a hukumar 'yan sanda, bai taɓa cin karo da makamancin wannan zaluncin ba. Adebayo ya shiga sosa ƙeyarsa cikin tashin hankali, dan shi kam ta sa ta ƙare.
Jin shirun Constable Adebayo ya yi yawa ya sa SAM fahimtar cewa gaskiya matashiyar ta faɗa. Saboda haka ya kalleta, kuma sai a lokacin ya lura da cewar su biyu ne, akwai wata ma tare da ita.
“Ku shigo ciki Please”
Ya faɗi yana nuna musu hanya. Diya ta share ƙwallar idonta tana haɗe hannyenta alamun roƙo.
“Yallaɓai ni bani da abun da zan iya baku dan ku sakar min ɗan uwana, ba ni da komai, kuma bani da kowa, dan haka idan kai ma ba za ka iya temakonmu ba za mu kai ƙaranmu zuwa ga mahallicin samai da ƙasai, dan na san cewar babu wanda ya gagareshi”
SAM ya girgiza kansa.
“A'a, ni ba komai nake buƙata a wurinki ba, ku shigo ciki, akwai tambayoyin da nake so na muku”
Sai da Diya ta kalli Fa'ee, sannan ta dube shi, bayan Fa'een ta mata alama da su amince. Cikin ofishin suka koma, sannan SAM ya bi bayansu, a tsorace Adebayo ma ya shiga ya tsaya daga gefe yana kallon yanda asirinsu ke tonuwa.
Sai bayan da SAM ya yi wa su Diya tambayoyi ya fuskanci cewar gaskiya suke faɗa. Cikin wani irin tashin hankali da ɓacin rai, ya bawa su Adebayo umarni da a saki Ekene. Jiki na ɓari suka fito da shi.
Diya kuwa kasa daurewa ta yi da ganin ɗan uwanta, sai da ta ruga zuwa wajen ɗan uwan nata, ta rungumeshi tana kuka, ko tsayuwa me kyau ba ya iyawa, duka jikinsa shatin duka ne. Diya ta juya ta kalli SAM.
“Mun gode Yallaɓai! Allah ya saka maka da alkairi”
Kansa kawai ya jinjina musu, kuma suma daga haka ba su sake cewa komai ba, ita da Fa'ee suka kama Ekene suka fita da shi. Wani irin kallo SAM ya wurgawa Adebayo da Chibunna, sannan yace.
“Gobe da misalin ƙarfe takwas na safiya, ina so na ganku a ofishina!”
“Sir!”
Suka faɗi a tare suna sara masa, kuma har sai da ya fice daga wurin suka sauke hannuwansu.
“Tamu ta ƙare Chibunna”
Cewar Adebayo yana sharce gumi.
“Ai duk kai ne ka ja mana, akan dubu ɗari ga shi za mu rasa aikinmu, dan ina da tabbacin chief SAM ba zai barmu ba!”
Adebayo ya cire hular kansa yana firfita da ita. A idonsa yake hango tarin abubuwan da za su rushe a rayuwarsa idan aka sallame shi a aiki, saboda ya sani, babu ta yanda za'a yi su ci gaba da aiki bayan wannan lefin da suka aikata.
Kallo ɗaya za ka yiwa SAM ka tabbatar da ransa a ɓace yake, yanayin takunsa ma kaɗai zai tabbatar maka da hakan, duk da shi ba mutum ne me kwarafniya ba, komai nasa a nutse yake yinsa. Gaba ɗaya ji yake kansa na sara masa, duniyar na juye masa, ba ya san jalunci, ba ya so ya ga ana zalunci sam. Cikin wannan ɓacin ran ya nufi ofishinsa, ya ɗauko abun da ya zo dominsa, sannan ya dawo ya shiga motarsa ya bar station ɗin.
Su Diya na fita suka kama hanyar komawa Makoko, dan a lokacin magariba ta kawo kai. Ga shi Ekene ba ya iya yafiya da kyau, dan gaba ɗaya jikinsa ya yi tsami, kuma daga ita har Fa'ee babu wanda ya fito da ko asi, bare su hau abun hawa. Kamar daga sama suka ji horn ɗin mota, hakan ya sa su juyawa a tare. Duk da duhun magariba da ya kawo kai sun ganeshi, wannan ɗan sandan da ya temakesu ne a cikin motar, kuma ganin hakan ya sa suka dakata.
Shi ne ya fito daga motar yana nufar inda suke.
“Idan ba damuwa zan iya sauƙeku a gida?”
Diya da Fa'ee suka dubi juna. Wannan wani irin mutum ne me kirki haka?, bayan temakonsu da ya yi so yake ya sake temaka musu.
“Dan Allah?”
Ya faɗi a sigar magiya, da sauri suka dubeshi a tare, su da za'a temakawa akewa magiya?. Lalle wannan mutum akwai kirki. Ba musu suka amince, shi ne ya riƙe Ekene har suka saka shi a mota. Fa'ee ta shiga gidan baya tare da Ekene, yayin da Diya ta zauna a gidan gaba.
Haka ya fara jan motar har zuwa Makoko. Kuma ko da suka isa shi ya fitar musu da Ekene, kafin sauran abokansa dake wurin suka gansu suka taso suka riƙeshi, Fa'ee ta bi bayansu, yayin da Diya ta tsaya dan ta yiwa ɗan sandan godiya.
“Mun gode sosai da sosai, babu abun da zamu iya biyanka wannan abun da kamana da shi Yallaɓai!”
SAM ya girgiza kansa yana kallon cikin idanuwan Diya.
“Ban muku komai ba, kawai na yi abun da yake wajibi a gareni ne, sannan ki dena kirana da Yallaɓai, sunana SURAJ ALI MUKTAR!”
Diya ta gyaɗa kanta tana karanta abun da ke rubuce a jikin name tag ɗin rigar jikinsa ‘SURAJ A. MUKTAR’
“To Yallaɓai SURAJ, Sai an jima”
Ta faɗi tana juyawa, SAM ya kasa amsawa, sai bin bayanta da ya yi da kallo har ta shiga cikin wani kwale-kwale.
*Agha Mansion, Lekki phase 1, Lagos state, Nigeria.*

DEENA TAYYAB AGHA POV.
Tana fitowa daga bathroom ta ga mahaifiyarta Hajiya Zayya zaune a kan gadonta tana ƙare mata kallo. Kanta ta ɗauke tana nufar dressing mirror.
“Wanka kika yi?”
Hajiya Zayya ta tambaya ganinta ɗaure da towel, Deena ta ɗan dakata daga zaman da take shirin yi a kan stool, ta juyo ta kalleta.
“A tunaninki zan iya zama da wannan kayan da waccan shashashar ta zubamin yoghurt?. Ko kuma zan iya bacci ba tare da na yi wanka ba bayan da Saifuddin Mas'ud Agha ya riƙe min hannu?”
Ta ƙarashe tana zama a kan stool ɗin. Hjia Zayya ta girgiza kanta.
“Na san ba za ki iya ba...”
Deena ta gyaɗa kanta tana jan kwalbar man da ta saba shafawa na gyaran jiki, dan ita duk wannan wayer tata, bata yarda da wani abu ba wai shi bleaching, duk kuwa da yanda Mommy ke ta nuna mata cewar ta yi bleaching ɗin, saboda fatarta ta zama kamar ta sauran 'yan Agha Mansion.
Saboda kaf yaran gidan babu baƙi sai Taj, kuma shi ma ɗin ba baƙi ba ne, chocolate color ne. Sannan duka gidan ita ta fi kowa baƙi, amma hakan bai dameta ba, a ganinta zaman fatarta a baƙar shi ne burgewa.
Hjia Zayyata miƙe daga kan gadon, ta isa zuwa bayan 'yarta, sannan ta dafa kafaɗarta.
“Zuwa yanzu ya kamata ace kun yi aure ke da Tauqeer!”
Deena ta kalleta ta cikin mirror.
“A gaskiya Mommy bani da shirin yin aure a yanzu, bunƙasa carrer ta shi ne abun da ke gabana, idan baki manta ba na faɗa miki cewar a watan da za mu shiga za mu fara shooting sabon film ɗin nan... So ba na jin zan iya aure a nan kusa!”
Hjia Zayya ta ja guntun tsaki.
“Wai ke me ya sa a duk sanda zan ce miki yi gabar sai ki bauɗe zuwa yamma?...”
“Saboda haka nake son yi Mommy. Ni da kika ganni nan ban damu da ra'ayin wani ba, rayuwata nake a yanda nake so, kuma babu wanda ya isa ya hanani yin abun da nake son yi”
Ta faɗi tana kallon Hajia Zayya. Hajia Zayya ta ɗaga kanta sama, magana irin wannan ba baƙuwa ba ce tskaninta da 'yar tata, sun saba irin haka. Ta sauƙe kanta tana faɗin.
“Ya yi kyau, za ki gane cewa wannan hanyar da kika ɗauka ba me ɓullewa ba ce, a ranar da Tauqeer ya fara soyayya da wata ba ke ba!”
Ta faɗi a ƙokarinta na tunzura Deenan, ba wai dan za ta bar hakan ta faru ba, tun da dai har Deena ta furta cewar tana son Tauqeer to fa sai ta aureshi, dan ba ta ji ko ganin wani abu da zai iya dakatar da faruwar hakan.
A tunanita kenan, dan kuwa da ace ta san kalar ƙadarar dake tafe nan gaba, da bata yi Irin wannan tunanin ba. Saboda ƙaddarar da za ta kawo HASKE cikin Agha Mansion na nan tafe, ƙaddarar da za ta tarwatsa wannan alwashin nata har guntunsa.
Cak Deena ta dakata da shafa man da take, cikin abun da bai gaza sakan biyu ba, fuskarta ta sauya zuwa fushi.
“Tauqeer nawa ne Mommy, ba zan taɓa barin wata ta same shi ba, kin fahimta?”
“To tun da haka ne sai ki bi hanyar da zaki mallakeshi, ku yi aure, ta hakan ne kaɗai zai dawamma a matsayin naki ke kaɗai!”
“Auran Tauqeer da zan yi shi ne zai sa ya zama nawa na har abada?”
Hajia Zayya ta gyaɗa mata kai.
“Zan aureshi very soon”
Hajiya Zayya ta yi murmushi, kafin ta shafa kan 'yarta. Kuma kafin ta

Please Login or Register in order to submit comment