Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*Shimfiɗa...*
Akwai wasu ƙaddarorin da kan zo da wani irin duhu, wanda zai mamaye rayuwar ɗan adam, ta yanda ko da tafin hannunsa ba zai iya gani a cikin wannan duhun ba.
Kuma an ce HASKE ne kaɗai ke maganin duhu.
Ɗan adam kan shiga halin neman HASKEn da zai yi amfani da shi wurin gusar da wannan duhun dake bibiyar rayuwarsa.
Shin menene duhun?
Wasu tarin ƙaddarori ne waɗannan da ke tafe da matsanancin duhu?.
Shin a ina wannan HASKEn yake?
Sannan kuma menene wannan HASKEn?
*💡HASKE...💡*
_(Maganin duhu!)_
*©SALMA AHMAD ISAH*

TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
بسم الله الر حمن الر حيم*
*Page 01*
__(★★)__
*Shekara ta 2000.*
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*01:40 Na dare.*
Wata matace ke tafe cikin sassarfa, sanye take da atamafa kalar ruwan goro, wanda akewa laƙabi da me dalma. Hannunta riƙe da wani abu, wanda ke duƙunƙune cikin zani.
Kanta ta ɗan ɗaga ta kalli sararin samaniya, ta ga yanda hadari yake gangamuwa, ga kuma iska me ƙarfi da aka fara, sai cida da tsawa da ake har da walƙiya.
Ƙafafuwanta ne suka taka birki, a lokacin da ta kawo gaɓar ruwan shiga yankin Makoko. Tarin kwale-kwalen dake bakin ruwan ta kalla, sannan ta kalli abun da ke hannunta. Hawaye na bin fuskarta ta girgiza kai tana faɗin.
“Ba zan iya aikata haka ba!”
Sai kuma ta shiga juyawa tana kallon kewayen wurin da take, babu kowa sai gilmawar karnuka. haka ta nufi wani kwale-kwale dake cikin tarin kwale-kwalen dake wurin, ta shiga cikin kwale-kwalen ba tare da tsoro ba, ta tsuganna tana aje abinda ke hannunta.
Kafin a hankali ta kai hannunta kan zanin, ta buɗe shi, nan take fuskar jaririya sabuwar haihuwa ta bayyana, don da alama yanzu ta zo duniya, saboda ko jinin haihuwarta bai bushe daga jikinta ba. Fuskar yarinyar ta ƙara rufewa da zanin, ta ɗora wata sarƙar ƙafa a kan zanin. Sannan ta miƙe ta fita daga cikin kwale-kwalen. Ta dawo ta bayansa, ta shiga turashi cikin ruwan, har ta samu nasarar turashi gaba ɗaya. A kan idonta kwale-kwalen ya shiga yawo a kan ruwan. Ya na nufar gidajen katakwayen dake saman ruwan. Sai da ta share ƙwallar idonta tukkuna, sannan ta juya da gudu ta bar wurin.
Ma somin ƙaddarar kenan, a ganinta ta kawo ƙarshen matsalolin, tun da har bata kashe jaririyar ba kamar yanda aka umarceta. Tun da har yarinyar ta yi nesa da gidan, wata ƙila komai zai ƙare.
Tana wannan tunanin ne ba tare da sanin cewa yanzu ne komai zai fara ba, dan kuwa barin yarinyar da ta yi a raye, shi ne musabbabbin buɗewar ƙofofinsu wasu tarin ƙaddararo da ko ita kanta bata san da aukuwarsu ba. Saboda ta kashe maciji ne batare da ta sare kansa ba. A yanzu ne komai zai fara!.
*Present day...*
*Shekara ta 2024.*
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*06:30 na Safe.*
“Wai Shola ba za ki fito ki tafi wurin aiki ba?... Kin kusa makara fa!”
Cewar wata baƙar mata cikin harshen yarbanci, yayin da take zaune a kan dandaryar katakon da aka kafa ginin gidanta da shi. Daga can cikin ƙaramin ɗakin gidan, muryar wata matashiya ta bata amsa cikin faɗin.
“Takalmi nake sakawa Gigi!”
Matar ta girgiza kanta tana dawo da dubanta kan mijinta dake kwance a gefenta. Fuskarsa ta ɗan leƙa ganin idonsa a rufe, zatonta bacci yake. Amma a zahirin gaskiya ba baccin yake ba, idonsa biyu, tunanin rayuwa ne yasa shi a gaba.
Damuwar halin da gidansa ke ciki ita ce ta sako shi a gaba, ba dan 'yarsa ɗaya Shola ta duƙufa wurin nemo kuɗin da zasu ci abinci ba, da tuni gidan nasu ya jima da durƙushewa. A da shi ne yake kula da gidan, amma tun bayan iftila'in hatsari da ya afka masa riƙon gidan nasa ya koma hannun 'yarsa DIYA, wanda sukewa inkiya da SHOLA.
“Ga ni na fito”
Cewar Shola, bayan da ta fito daga tilon ɗakin gidan nasu, a tare suka dubeta, daga Gigin har mijinta da ya buɗe idonsa.
Sanye take cikin wani baƙin wando me faɗi, sai wata farar oxford shirt. Kanta yafe da baƙin gyale. Ƙafafunta sanye da fararen canvas da suka fara jin jiki. Wannan shi ne kayan da ta saba sakawa idan zata je wurin aiki. Fara ce sosai, tana da matsakaicin jiki, idan za ka mata adalci, a kallon farki idan ja mata za ka kirata da bafulatana.
Gigi ta yi murmushi.
“Ga guntuwar shinkafar jiya, ki ɗan taɓa kafin ki tafi”
Shola ta girgiza kanta tana sauƙowa daga kan mattattakalan katakon gidan nasu.
“A'a Gigi, ni idan na ci ku me za ku ci?, kawai ku ci, idan na je wurin aiki zan samu abun da zan ci”
Gigi ta miƙe tana fitowa daga gidan katakon nasu, ta tsaya kusa da Sholan dake kiran sunan Ekene, wanda yake zaune a gidan dake gaban nasu, dan ya zo ya fitar da ita bakin gaɓar ruwan unguwar tasu, dan ba'a zirga-zirga a unguwar sai da kwale-kwale.
“Ya kamata ki taɓa wani abun Shola”
Diya ta juyo ta kalleta.
“Karki damu da ni Gigi, ko biredi ne zan siya na ci, ke de ki kula, na bar miki ɗari biyar a ɗaki, wata ƙila za ku buƙace ta”
Gigi ta yi murmushi tana shafa kanta, tare da saka mata albarka.
“Shola ga ni”
Cewar Ekenen da take kira, bayan da ya fito daga ɗakinsu na katako.
“Na kusa makara Ekene! Ka zo ka fitar da ni”
Ta faɗi tana dubansa. Saida ya ɗaga busassun hannayensa ya yi miƙa, kafin ya sauƙe yana jan wata baƙar tsohuwar singlet da ke rataye a jikin wata gwafa ta gidansu. Sannan ya zagaya ta inda kwale-kwalensa yake, ya cinto shi daga jikin wani ƙarfe da ya ɗaureshi, sannan ya shiga yana ɗaukan marar kwale-kwalen, ya zagayo da shi har zuwa ƙofar gidansu Shola.
Shola ta yi wa Gigi sallama, sannan ta hau kwale-kwalen. Ekene ya fara tuƙasu. Diya ta ci gaba da kallon irin wahalar rayuwar da ake a yankin nasu. Kaf gidajen yankin na katako ne, kuma a saman ruwa suke, dan gaba ɗayan unguwar ma kanta malale take da ruwa, shi yasa ko ina zaka sai ka hau kwale-kwale.
Sosai ake shan wahalar rayuwa a yankin, yawancin mazaunan yankin masu zuwa cirani ne, sai 'yan gudun hijara, da kuma wanda ƙaddara ta zama silar zuwansu wurin. Yankin nasu ya haɗa tarin ƙabulu, da kuma mutane masu mabanbanta halaye. Kowa ta kansa yake a wurin, babu ruwan wani da rayuwar gidan wani.
“Mun iso!”
Cewar Ekene, sanda suka iso bakin ruwan. A hankali ta miƙe, hannunta riƙe da jakarta. Godiya ta masa tana fita daga kwale-kwalen. Hanya ta yanka ta so ma tafiya. Kafin ta samu isowa tashar bus ɗin da ta saba hawa.
Tafiyar munti 55 ce ta kaita cikin Victoria Island. A wani bus stop suka tsaya, ta fito daga motar bus ɗin, tare da sauran mutanen da suka shiga motar. A ƙafa ta fara takawa, har ta iso Cactus restaurant. Wurin da take aikin raba abinci kenan.
Memakon ta shiga ta ƙofar gaba kamar yanda kowa ke shiga, sai ta zagaya zuwa backyard ɗin ginin restaurant ɗin, ta shiga ta ƙofar kitchen ɗin restaurant ɗin dake baya.
“Shola sai yanzu kika iso?”
Ɗaya daga cikin masu girkin wurin ta tambayeta, yayin da take ƙoƙarin saka apron ɗinta dake rataye a jikin wani hook. Zaren apron ɗin ta gama ɗaurawa tana faɗin.
“Eh Wallahi, sai yanzu na samu isowa”
“Diya! Diya!”
Tun daga nesa suke jiyowa muryar Orisa cikin ƙwalla kiran sunan Diya. Kafin Diyan ta amsa, Orisa ta bayyana a cikin kitchen ɗin.
“Wai ya aka yi kika makara?.... MD ya zo yana ta faɗa!”
Orisa ta faɗa mata cikin harshen yarbanci, Diyah ta saka jakarta cikin wata loka tana amsa mata da.
“Yau ban farka da wuri ba ne!”
“Lalle kam, ke har wani lokacin miƙe ƙafa ki yi bacci kika samu?”
Orisa ta tambaya. Diya ta miƙe tana kallonta.
“Orisa mutum idan be huta ba ai sai ya samu matsala, mu yini muna aiki mu koma gida kuma a ce ba za mu yi bacci ba?”
Orisa ta gyaɗa kanta.
“To yanzu dai ba zan ce za ku tsaya kuna yi ba. Ga wani plate ɗin brown spaghetti can, ki ɗauka ki kai teburi na sha takwas”
Cewar Ifunaya, shugabar sashensu na masu kaiwa abinci.
“Ok”
Diya ta amsa tana raɓa Orisa, plate ɗin brown spaghettin ta ɗauka ta ɗora a kan wani tray me kyau, ta nufi ƙofar shiga cikin restaurant ɗin.
Da misalin ƙarfe tara na dare ta kamo hanyar dawowa gida, bayan da ta tashi daga aiki, hannunta na dama riƙe da wata farar leda. Kafaɗarta kuma saƙale da jakarta. Kasancewar a yankin nasu ba ko ina ne me wutar nepa ba, yasa take amfani da hasken wayarta, wurin haska hanya.
Kuma har zuwa lokacin akwai sawun mutane a waje. Ranta ne ya ɓaci asanda ta iso bakin ruwan yankin nasu, ta iske babu masu yin fito, sai de tarin kwale-kwale a bakin wurin. Ga shi Ekene tsabar talauci da ya masa kanta ko waya ba shi da ita, bare ta kirashi dan ya zo ya fitar da ita.
Haka ta duba ɗaya daga cikin kwale-kwalen da ta san me shi, ta fara tura shi zuwa cikin ruwan, kafin ta ɗale ciki tana ɗaukan marar fiton sa, ta fara tuƙa kwale-kwalen.
Ganin hasken fitila kunne a tsohon gidansu da ya kusa durƙushewa ya sa ta fahimci cewar har yanzu basu kwanta ba. A kan matakalar katakon ƙofar gidan nasu na ƙarshe ta dire,sannan ta ɗaure kwale-kwalen a jikin wani ɗan katako dake jikin gidan nasu.
Sannan ta ɗebi kayanta da ta aje su a cikin jirgin, ta fara taku a hankali, saboda yanayin jimawar da katakon ginin gidan ya yi, ya sa ba sa taku da ƙarfi, dan abu kaɗan ne zai iya sawa ya karye, saboda wasu wuraren ma sun karye ɗin.
A tilon ɗakin nasu ta tarar da su, Gigi na zaune tana wa Papi firfita, sun kunna mosquito coil, sai wata dundurusun fitilarsu mara haske sosai dake ci. Ɗakin babu komai sai wasu lamitssatssun katifu guda biyu, dake yashe a ƙasan ɗakin, sai 'yan wasu jakkukkunansu na kaya. Dan basu cika tara tarkace a ɗakin ba, gudun kada katakon gidan ya ɓalgace.
“Ba ku yi bacci ba?”
Ta tambaya tana cire viel ɗin jikinta, Gigi ta kalleta tana faɗin.
“Tukunna dai, zafi ne ya hana mu kwanciya”
Diya ta dawo bakin ƙofar ɗakin nasu, ta ɗauke labulen ɗakin, saboda iska ta ɗan samu ta shigo ciki. Ta dawo ta ɗauki kwandon soso da sabulunta, ta fita waje.
Ɗan siririn banɗakin gidan ta shiga, da wani ruwa rabin bokiti ta samu ta ɗan yi wanka, sannan ta fito, jikinta ɗaure da zani, ta dawo ɗakin ta saka wata doguwar rigarta. Sannan ta zauna kusa da Gigi, tana jan ledar da ta shigo da ita.
“Papi na samu kuɗin siyan maganinka, amma ɗaya aka samu, sai a yi maneji”
Papi ya kalli tilon 'yar tasa, ƙwalla na shirin taruwa a idonsa, a shekarun da suka wuce ya tsinceta, shi ya kula da ita har girmanta, sai ga shi a yau ita ce take kula da shi, rayuwa kenan.
“Allah ya miki albarka Shola”
Ta sunkuyar da kanta tana amsa masa da amin.
“Yau me kuka ci da rana?”
Ta faɗi tana fitar da sauran kayan da ke cikin ledar, Gigi ta aje muficin hannunta tana faɗin.
“Taliya muka ci”
Robar da ta zubo sauran abincin da ya yi saura a restaurant ɗinsu ta fitar, dan idan abinci ya yi saura su ake rabawa.
“Ga abinci na zo da shi, Papi ka tashi sai ka ci”
Kansa ya girgiza mata.
“A'a Shola, ke da Giginki dai ku ci... Amma ni na ƙoshi”
Shola ta ɓata fuska.
“Idan baka ci ba ni ma ba zan ci ba”
Da sauri ya yunƙura ya zauna.
“Yi haƙuri to, zan ci”
Ta ɗan yi dariya tana kallon Gigi, Gigi ta yi murmushi tana shafa kanta.
Haka suka gama cin abincin tana basu labarin abubuwan da suka faru da ita yau a waje, wani abu da tun tana yarinya take yi, duk inda zata je ta dawo, sai ta basu labarin abun da ya faru da ita a wurin.
Ko da suka gama cin abincin sai ta ɗauki katafarta ta fita da ita rumfar ƙofar gidan nasu, ta shimfiɗata, ta kawo wani jemammen bedsheet ta shimfiɗa. Kafin ta kawo wani fatattakkakken net ta ɗaura. Ta shiga cikin shimfiɗar tata ta kwanta.
Tana hasashen yanda ranar gobe zata kasance, wannan ita ce rayuwar da take gudanarwa tare da iyayenta, rayuwar tasu me wahala ce, amma kuma suna cikin farinciki. Shekaru uku kenan da fara aikinta, kuma a shekaru ukun da suka wuce ne, Papi ya samu hatsarin mota, sannan tun lokacin ƙafarsa ta samu matsala. Har aka buƙaci wasu maƙudan kuɗe wurin mata aiki, Kasancewar basu da su, ya sa suka dawo gida suka zubawa saratar Allah ido.
Ganin zaman ba zai kaisu ba ya sa ita Diyan shiga cikin gari neman aiki, kuma cikin nasara ta samu, da shi ne suke iya rayuwa a yanzu.
A. ISAH CE✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE...💡️*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
°°°
Akwai ɗaya daga cikin members ɗin gidan nan, da Allah ya yi wa mijinta rasuwa, ina so ku saka shi a addu'a, Allah ya ji ƙansa ya gafarta masa.
°°°
*Page 02*
~~~
*Coca-Cola Arena, Abu Dhabi, Dubai...*
_🎶When I look at you, I see a star, Shining bright, no matter where you are._
_My heart is full of love, it overflows,With you by my side, my joy it grows._
_Your beauty is like a work of art, My love for you comes straight from the heart._
_You're my one and only, it's plain to see, Forever yours, that's how it will be.🎶_
Maƙaƙaren hall ɗin cike yake da mutane. Babu abinda ke tashi a wurin, sai sautin mutanen wurin, suna rera waƙar dake tashi a hall ɗin. Daga can kan stage kuma wani kyakkyawan matashi ne tsaye, sanye cikin baƙar T-shirt, da baƙin khaki trouser. A saman T-shirt ɗin kuma ya ɗora red bomber jacket. Hannunsa na dama riƙe da microphone, sassanyar muryarsa ce ke rera waƙar dake tashi cikin sifikun wurin.
A dai-dai lokacin da kiɗan waƙar ya sauya, a lokacin masoyansa dake wurin suka sa ihu, har da masu tsalle, wasu na ɗaukarsa a hoto, wasu video wasu na ɗaga takardu masu ɗauke da sunansa.
Yayin da shi kuma ya dage wajen ganin ya farantawa masoyansa ransu. Su ma kuma suna jin daɗin show ɗin na yau, dan burin ransu ne ya cika, yau gasu ga babban masoyinsu, yana rero musu daɗaɗan waƙoƙinsa, cikin nutsatsiya kuma sassanyar muryarsa.
Daga baya kuma sai sautin koran sunansa ya cika wurin. Cike da jin daɗi da kuma farin ciki ya tsaya yana kallon masoyan nasa.
“TAUQEER AGHA!”
*
Tsaye yake a gaban katangar glass ɗin dake a ɗakin hotel ɗin da ya sauƙa, idonsa manne kan kyawawan gine-ginen dake garin na Abu Dabhi, shi kansa garin yana masa kyau, musamman da daddare. Duk da ya je ya yi rawa a kan stage, ya yi waƙa, ya yi ihu, amma baya jin gajiya a jikinsa, dan zuwa gobe zai koma ƙasarsa ta gado, wato Nigeria.
Ƙaran wayarsa dake kan gado da ya ji ne ya sa shi waigawa. Sannan a hankali ya soma taku zuwa jikin gadon, ya kai hannunsa ya ɗauki wayar. ‘Umma' shi ne sunan dake yawo a kan screen ɗin. Da wani ɗan guntun murmushi a kan fuskarsa ya ɗaga wayar. Sallama ya fara yi cikin daddaɗar muryarsa. Bayana an amsa masa sallamar ta cikin wayar kuma ya gaida matar cikin girmamawa.
“TAUQEER zuwa goben za ka dawo?”
Kansa ya gyaɗa a hankali yana juyawa.
“Insha-Allah Umma!”
“To Allah ya dawo da kai lafiya, Allah ya temaka”
“Amin”
Ya amsa yana sauƙe wayar daga kunnensa, dan wayar ta yanke, sumar kansa ya shafa daga gaba zuwa baya, yana fitar da wani hucin iska daga bakinsa.
A hankali ya zauna a bakin gadon yana jujjiya kansa, kafin a hankali ya kwanta a kan gadon, bacci yake san yi, amma kuma baccin ya ƙauracewa idonsa.
*Agha Mansion, No.854, Lekki pahse 1, Lagos State, Nigeria.*
Wani katafaren gida ne, wanda za'a iya kiransa da fada me zaman kanta, dan ko ginin gidan ya amsa sunan gida. Daga waje ma kawai gidan abun kallo ne, bare kuma ka saka ƙafarka a gate ɗin farko na gidan.
Tun daga kan maƙareren gate ɗin gidan, za ka fara cin karo da wata shimfiɗeɗiyyar kwalta, wadda zata sada ka da cikin gidan. Kyakkyawan garden ɗin gidan, shi ne a farkon gidan, kafin ka iske ainahin ƙofar shiga cikin gidan. Gidan ginin bene ne me hawa ɗaya.
Kai da ganin gidan ka san cewa wannan ya fi ƙarfin zaman mutum ɗaya, duk da ginin ba na yau ba ne, amma kayan da aka zube a cikinsa sabbbi ne, 'yan ya yi, hakan ke nuna cewar mammallakan gidan na kula da shi yadda ya kamata.
Agha Mansion kenan. Gida ne na iyalin mutum ɗaya. Agha Muhammad shi ne ainahin tushen kafuwar ahalin. Shi da matarsa Fariya. Daga Agha har matarsa Fariya dukansu fulanin Yola ne.
Allah ya albarkacesu da yara shida: Faruq Agha, shi ne babba cikin 'ya'yan nasu, shi ne mamallakim A. FOODS NIG LTD. Babban kamfanin da ya shahara a faɗin Nigeria, wurin sarrafawa da kuma shige da ficen kayan abinci.
Me bi masa kuma shi ne Mas'ud Agha, soja ne, me riƙe da muƙamin General.
Sai Tayyab Agha, shi kuma ya kasance likitan ƙashi, sannan ya mallaki asibiti tasa ta kansa.
Me bi masa shi ne Muzamil Agha, shi kuma ya bi sahun yayansa Faruq, dan tare suke kasuwancinsu.
Sai autarsu, kuma mace ɗaya tilo a cikinsu Abida, wadda ta yi aure, tun da jimawa. Kuma tana zaune a garin Abuja ita da mijinta da kuma yaranta.
Kuma duka waɗanan ahalin na zaune ne a cikin Agha Mansion. Domin kaf cikinsu babu wanda bai tara iyali ba.
Matar Faruq ɗaya, sunanta Maryam, yaran gidan kuma na kiranta da Umma, mace me kirki da sanin ya kamata, ga hange nesa, da jin ƙan talaka. Yaransa huɗu da ita, TAUQEER shi ne babba, suna masa inkiya da Junior, kasancewar ya ci sunan mahaifin Maryam ɗin ne. Sai Jamal. Me bi masa kuma ita ce Iqra, sai kuma autansu Aabis.
Mas'ud na da mata ɗaya shi ma, Hafiza shi ne sunanta, yaran na kiranta da Amma. 'Yar halin ko in kula kenan, dan ita babu ruwanta da sabgar gidan, ko me za'a yi tana gefe, dan bata damu da kowa ba. Yaranta huɗu cas, haihuwarta ta farko 'yan biyu ta haifa, Tajuddin da Saifuddin, sai kuma Muhammad, wanda sukewa inkiya da Hammad, sai auta Khabir.
Sau kuma Tayyab, matarsa ta farko sunanta Zayya, yaran gidan kuma na kiranta da mommy, Babban burin Zayya a duniya shi ne ta ga ta fi kowa, sam bata son a fita, shi ya sa komai nata da ban ne da na gidan, ta tsani ta ji an ce yau ga wani wanda ya ɗarata, kullum so take ta ji an ce ita ce on top. Haihuwarta ɗaya, ita ma bayan shafe shekaru masu yawa, Allah ya basu ita, sai matarsa ta biyu Rahila, wadda rana ɗaya aka wayi gari aka rasata ko sama ko ƙasa, ta yi ɓatan dawo, shi ya sa yanzu 'ya ɗaya gareshi, DEENA.
Muzamil ma na da mata ɗaya, Rahama yaran gidan na kiranta da Mama, komai da ruwanka kenan, duk wata kurɗa-kurɗa ta gidan babu wadda Mama bata sani ba, ko labarin abun da ya faru a gidan kake nema idan ka tambayi Mama ka samu. Ko zance ake ba da ita ba za ka ji ta saka baki, duk dan de ta samu labarin bayarwa, babu zancen da ba zaka ji a bakinta ba, ita fa tsabar gulmarta, har dustbin ɗin gidan take zuwa ta duba, ko an ci wani abun a gidan bata sani ba.
Tana da yara uku, Nasir shi ne babba, sai Abdullahi da suke wa inkiya da Bobo, autar cikinsu kuma ita ce Nimra. Ba ma a cikin 'ya'yan muzamil ɗin kawai ba, duka gidan ma Nimra ta fi kowa ƙananun shekaru.
Kaf cikin yaran gidan su goma sha biyu, huɗu daga cikinsu sojoji ne. Sojojin sun haɗa da; Saifuddin Mas'ud Agha, Tajuddin Mas'ud Agha, Jamal Faruq Agha, da Nasir Muzamil Agha.
Tauqeer kuma mawaƙi ne, wanda ya shahara a duniyar waƙa. Cikin gida da waje babu inda baya leƙawa dan harkar waƙarsa. Deena kuma actress ce, tana ɗaya daga cikin jaruman da ake ji da su a Nollywood.
Iqra da Hammad kuma suna University ne. Bobo da Khabir na secondary school. Yayin da Nimra da Aabis suke junior secondary school.
*
“Halima dan Allah ki gaggauta ku gama girkin nan, na san duk inda suke zuwa yanzu sun kusa ƙarasowa!”
Cewar Umma, yayin da take tsaye daga bakin ƙofar kitchen, tana duban masu aikin dafa abincin gidan. Halima shugabar madafan abincin ta risinar da kai tana amsa umarnin uwar gijiyar tasu.
Daga haka Umma ta baro kitchen ɗin ta nufo cikin falon gidan. Kai tsaye ɗakinta ta wuce.
“Wai ni me yake faruwa a gidan nan ne?”
Hammad da ya dawo daga makaranta ya tambaya yana zama a kan ɗaya daga cikin kujerun falon. Mama dake zaune tana sakatar haƙori ta gyara zama tana faɗin.
“Junior ne zai dawo yau”
Sai ya gyaɗa kansa yana buɗe wayarsa. Daga gefen Mama kuwa, Amma ce zaune tana latsa wayarta.
Daga can ɗayan ɓangaren na falon kuma Nimra, Aabis da Khabir ne ke home work. Yayin da Bobo ke zaune a kan kujera yana shirgawa cikinsa abinci, dan shi haka rayuwarsa take, shi da abinci five and six ne, rayuwarsa gaba ɗayanta ta tafi a kan cin abinci, shi ya sa ya haɗa wata uwar ƙiba. Tsabar ƙibar da ya yi cikinsa har zama yake a kan cinyarsa, ga luɓu-luɓu kumatu kamar yalo.
“Bobo! Kai ba za ka yi home work ɗin ba?”
Bobo ya sauƙe meat pie ɗin da yake shirin kaiwa bakinsa ya kalli setin inda Hammad ke

Please Login or Register in order to submit comment