Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake cewa wani abu Deena tace.
“Ki bani wuri zan kwanta”
Hajiya Zayya ta ɗan yi murmushin yaƙe, kafin ta saketa tana faɗin.
“Ki yi bacci me daɗi”
Daga haka kuma ta juya, ranta na mata ba daɗi, a da bata damu da kalar renin da Deena ta mata ba, hasali ma ganinsa take ba a bakin komai ba, amma zuwa yanzu ta fara shiga damuwa a kan hakan, dan idan Deena za ta mata magana, yi take kamar wadda take yi da sa'arta.
Deena ta ci gaba da shafa manta, kafin ta miƙe ta shiga closet, ta fito sanye cikin farar night gown, ta kwanta a kan gadonta ba tare da ta kashe wutar ɗakin ba, tunani Tauqeer shi ne kaɗai abun da zuciyarta ke yi, eh ƙwarai ta san da cewa tana sansa, kuma ba ta jin za ta iya barwa wata ahi, dan Tauqeer nata ne ita kaɗai.
Cak Hajiya Zayya ta tsaya a ƙofar ɗakin Iqra dake kusa da na Deena, jin kamar tana dariya. Cikin sanɗa ta matsa zuwa jikin ƙofar ɗakin, ta kara kunnenta tana sauraron abun da Iqra ke faɗi.
Daga cikin ɗakin kuma, Iqra ce kwance a kan gadonta tana waya da sabon saurayin da ta sake, wanda take ga kamar shi ba zai gujeta ba irin sauran samarin da ta sha yi a baya.
Daga saurayi ya nuna yana santa, ta amince suka fara soyayya za ta nemi shi ta rasa. Tun abun ba ya damunta har ta zo ta fara damuwa, amma cikin ikon Allah sai shi wannan Jawad ɗin ya tsaya, kuma a yanda yake nuna mata soyyayarsa a makaranta tana jin kamar shi ba zai kufce ba kamar sauran.
“Dare na yi Babe, zan kwanta”
Ta faɗi idonta manne a kan agogon ɗakin, daga cikin wayar, muryar Jawad ta ce.
“Ok Queen, ki kwanta sai gobe, ai za ki shigo school ba?”
Ta ɗan yi dariya.
“Insha-Allah!”
“Okay I love you!”
“I love you more!”
Daga haka wayar ta ƙare. Ta ƙanƙame pillow tana murmushi.
Hajiya Zayya ta yi murmushi kamar yadda ta saba. A ranta take faɗin; wato ta yi sabon saurayi kenan?. To ayi mu gani, idan tusa za ta hura wuta. Daga haka ta nufi ɓangaren da ɗakinsu ita da mijinta yake a cikin gidan.
*
Kamar Kullum, Tayyab Agha na tsaye a balcony ɗin cikin ɗakinsa, wayarsa riƙe a hannunsa yana kallon hotonta. RAHILA matarsa da yake matuƙar so da ƙauna, matarsa da rana tsaka ya nemeta ya rasa. Har zuwa yau ciwon rasata bai bar ransa ba, don ɓata ta yi ba tare da ya san inda take ba, da ace ma mutuwa ta yi, ya ga gawarta to da zai haƙura, amma har zuwa gobe bai cire ran sake ganinta ba.
“Har gobe ina sanki matata, kuma ba na jin zan dena sanki har zuwa fitar nunfashina na ƙarshe... Ko a ina kike? Shin kin haifi cikin jikinki ko a'a?...”
Kamar wanda ya zautu, haka ya ci gaba da yin sambatunsa da baya ƙarewa. Kafin ya fita daga wurin hotuna, ya shiga wurin kira, ya shiga neman lambar yayar Rahila matarsa, wato Anti Badi'a. Ko da ya samo lambar sai ya shiga aika mata da kira, amma kamar kullum, haka ya yi ta gwadawa amma ta ƙi ta ɗauka.
“Tayyab!...”
Ya ji muryar Zayya ta kira sunan, nan take gabansa ya faɗi, ya ji kamar ana dauɗe ƙwaƙwalwarsa daga tunanin Rahila. A hankali ya juyo ya kalleta, tana tsaye daga cikin ɗakin tana kallonaa, fur ya ƙi yarda su haɗa ido, dan ba ya so ta gane cewa ya ga hotunan Rahila, balle ta gane cewar ya kira Anti Badi'a.
“Me kake a nan?”
Ta tambaya kamar uwa da ɗanta.
“Na... Na... Zan... Zan..”
Ya kama inda-inda.
“Lokaci na ƙurewa, ka zo ka kwanta!”
Ta faɗi jajayen idanuwanta a kansa. Kamar wanda ake controling da remote haka ya dawo zuwa cikin ɗakin da sauri, ya nemi bakin gado ya kwanta ya lumshe idonsa.
Hajiya Zayya ta ɗau muntuna a tsaye a wurin, har sai da ta tabbatar da ya yi bacci, kafin ta juya zuwa ga lokarta, ta buɗe ta ɗauko wata doguwar jar riga. Ta tuɓe kayan jikinta sannan ta saka rigar. Ta dawo ƙarƙashin gadonta, ta sa hannu ta janyo wata ƙwarya dake lulluɓe da baƙin ƙyalle.
Miƙewa tsaye ta yi, ta buɗe ƙwaryar, wani baƙin ruwa ya bayyana a cikin ƙwaryar. Idonta ta lumshe tana karanto wasu abubuwa da ba zaka iya tantance da wani yaren take magana ba. Bayan ɗan wani lokaci ta buɗe idonta. A hankali-hankali hayaƙi ya turnuƙe ɗakin. Kuma a cikin hayaƙin Hajia Zayya ta ɓace ɓat. Kamar almara.
***
Durƙushe take a gaban wani yamushasshen tsoho dake zaune a kan wata baƙar kujera. Fuskarsa baƙin ƙirin, ga wani farin gashi da ya baibaye jikinsa, sanye yake da wasu tufafi na ganye irin na mutan da. Hannunsa na dama rike da tsabga yana kaɗawa.
“Yau da wace buƙata kika zo GAMANDI!”
Zayya ta ƙara risinawa kamar me shirin yin sujjada tana faɗin.
“Ƙunduns abun dogaro, girma naka Ƙundus, babu me bamu bayan kai, a gurinka kaɗai muke nema mu samu, yau ma na zo da tarin buƙatu, kuma ina fatan za'a biya minsu”
Tsohon ya yi wata dariya mara daɗin sauraro.
“An baki dama Gamandi, faɗi abun da ke tafe da ke”
“Ina so a shiga tsakanin Gudaliya da SAIFUDDIN, idan da hali a kawar da shi Ƙundus. Sannan Iqra ta yi sabon saurayi, ina so a rabata da shi kamar yanda aka rabata da sauran. Sai maganar Tayyab, har yanzu bai mance da Rahila ba. Akwai kuma batun Jamal, ina so a ƙara hargitsa rayuwarsa fiye da da ya me girma Ƙundus!”
Ta ƙarashe tana kifa kanta a ƙasa. Tsohon ya ɗan yi shiru, kafin yace.
“Gamandi wata ƙila kin mance lokacin da na ce miki 'yayan Hafiza ba za su taɓu ba, dan a tsaye take a kan 'ya'yanta, saboda haka Saifuddin ba zai iya taɓuwa ba. Ita ma Maryam ɗin dan ba ta tsaya a kan yaran nata ba ne shi ya sa ake iya taɓasu. Game da Iqra kuwa wannan me sauƙi ne, ki ɗauka an gama miki da wannan buƙatar kamar sauran, batun Tayyab ma ba me wahala ba ne, zan masa abun da zai sa ya ji kamar zai ruga da gudu ko da sunan Rahila aka kira. Haka Jamal ma baki da damuwa”
“Godiya nake Ƙundus”
Tsoho Ƙundus ya gyara zamansa yana faɗa mata kalaman da ta jima da haddace su a cikin kanta, saboda a duk sanda za ta zo masa da buƙata sai ya faɗa nata su, kuma har wa yau ita ta rasa takamemen ma'anarau.
“Amma fa Gamandi ki sani cewa akwai ranar ƙin dillanci, akwai ranar da duk abun da aka binne a ƙasa zai fito, akwai ranar girbi. Sannan akwai ranar karɓar sakamako!”
______________
_To ka ji, Salmanians, an ya kuwa kuna ganin duhun dake mamaye da Agha Mansion?_
_Waye wannan Suraj a.k.a SAM ɗin, dan da alama akwai wani abu gagarumi dake shirin faruwa tsakaninsa da Diya da kuma Fa'ee._
_ Kuma wani hali Jamal ke ciki?_
_To mu je de zuwa, dan ba ayi komai ba ma_
A. ISAH CE ✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE...💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 06*
~~~
*No.675, 361 Stagg Street, Brooklyn, New York, USA.*
RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD POV.
A hankali ƙafafuwansa ke takowa zuwa down stairs. Sanye yake cikin baƙar suit, wadda a ƙasanta ya saka farar high neck shirt. Ƙafafunsa sanye cikin fararen sneakers. Bayansa goye da backpack, wadda ke ɗauke da laptop ɗinsa.
Da murmushinsa ya ƙarasa zuwa wurin Maa dake tsaye a falon. Ta baya ya rungumo kafaɗunta.
“Sakeni mana! Sai ka karya ni?”
Maan ta faɗi tana juyowa, ta dubeshi.
“Zan tafi wurin aiki Maa, ki sakamin albarka”
Ya faɗi yana kama hannayenta, Murmushi ta yi tana ƙara dubansa. Yau ya samu ya ɗan rage tsayin gemun da ya tara, amma bai aske shi duka ba, duk kuwa da ta san cewa shi ba ya tara gemu da yawa, a wasu lokutan ma askeshi yake gaba ɗaya.
“Allah ya maka albarka, ya bada sa'a!”
“Ameen Maa”
Ya amsa yana sumbatar hannyenta. Kafin ya saketa yana ɗaukar doguwar trench coat ɗinsa, kasancewar ana cikin yanayin sanyi ne, dan a wasu wuraren ma snow ce ke sauƙa, ya sakata, sannan ya fita.
Kekensa dake jingine a jiki balcony ya ɗauka. Ya juya kansa yana nufar ɗan gajeren gate ɗin gidan.
Kuma tun kafin ya fito daga gidansu ya hangeta ta fito daga nata gidan. Saboda katangun dake gaban gidan basu da tsayi. Kamar kullum, sai da zyciyarsa ta doka sau biyu a lokaci guda. Kuma ko da ya ɗago da hannunsa na hagu dan ya tabbatar da ƙaruwar bugun ziciyar tasa sai ya ga ya ƙarun, har da kashi 7. Setin zuciyarsa ya dafe a ransa yana faɗin; Da alama yarinyar nan kasheni take son yi.
Ita kuma sai a lokacin ta lura da shi, duk da ya ɗan sauya mata yau, kasancewar ya rage gemun da ya saba tarawa. Baki washe ta ɗaga masa hannu. Hakan ya sa keken dake hannun Rafeeq ƙoƙarin suɓucewa, ya yi sauri ya ruƙoshi yana mata murmushin yaƙe.
Kafin ya turo keken zuwa jikin gate, ya buɗe gate ɗin, sannan ya fita, sai da ya kafe keken a gefe, ya dawo ya rufe gate ɗin. Kuma har zuwa lokacin tana tsaye a ƙofar gidanta, da titi ne kaɗai ya rabashi da nasa gidan.
Keken nasa ya fara turawa yana tafiya, duk da jikinsa na bashi cewar har yanzu kallonsa take. Kuma sai ya ƙara tabbatar da hakan a sanda ya ji muryarta a kusa da shi.
“Hey BLACK INDIAN!”
Abun da ta faɗi kenan, wanda ya haddasawa zuciyar Rafeeq tarwatsewa a ƙirjinsa, ya dakata da tura keken da yake ya juyo ya kalleta. Ita wai nan kallon ba'indiye take masa?.
“Ni Nigerian ne, ba indian ba”
Ya faɗi cikin harshen hausa, ido waje take kallonsa, dan a zatonta shi ɗin ɗan indiya ne, ba wai dan ya na da farin fata ba, sai dan yana yanayinsu, kuma ko da bai kasance ba'indiye ba, zai iya kasancewa ɗan Asia.
“Wai kai ɗan ƙasarmu ne?”
Ta tambaya idonta na haskawa da zallar mamaki. Kansa ya gyaɗa nata yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo, dan shi a kallon farko da ya mata ya gane cewa 'yar nigeria ce.
“Amma kai shuwa arab ne ba?”
Ya girgiza mata kai yana gyara riƙon keken hannunsa.
“Ni bafulatani ne”
Mamaki ya ƙara kamata. Ita fa Wallahi ba ta taɓa danganta shi da Nigeria ba ma, balle har a ce mata bafulatani ne. Keken hannunsa ta kalla tana faɗin.
“Keken waye wannan?”
Rafeeq ya kalli keken, sannan ya kalleta.
“Nawa ne”
Ya bata amsa, nan take kaso tamanin na burgeta da yake ya ragu, wai da ma duk wannan haɗuwar tasa keke yake hawa?. Tun bayan data hasasowa kanta alaƙa da shi, ta ke ta dudduba cikin gidansa, wai ko za ta ganshi da mota, amma bata taɓa gani ba, ƙarewarta ma wai keke gareshi.
Tun da kuwa keke yake hawa hakan na nuna cewa ba shi da ƙumbar susa. A ganinta, duk saurayin da bashi da kuɗi, duk haɗuwarsa sunansa sifili. A duniyarta, kuɗi shi ne komai, in baka da su, baka da ƙima a idonta. Da har ta fara hasasowa irin kuɗin da za ta tatsa a wurin wannan ba'indiyen, ashe duk kanwar ja ce, shi ma dai ɗan Nigeria ne, wata ƙila ma talauci ne ya koroshi daga gida. Kuma de ta na ganin cewar gidan da yake ciki ba nasa ba ne, haya yake kamar dai ita.
“Helloo!”
Ya faɗi yana ƙyasta yatsunsa, a ƙoƙarinsa na dawo da ita hayyacinta, dan ya lura da ta lula zuwa duniyar tunani. Ta yi firgigit ta kalleshi.
“Mu je?”
Ya faɗi yana nuna mata hanya, a ƙasan numfashinta ta ja tsaki, dan kuwa dai ɓaro-ɓaro take hango rushewar shirinta a kansa. Ta soma tafiya gefensa.
“Sunana Rafeeq! Ke fa?”
Ciki-ciki ta amsa masa da.
“NADRA!”
Kansa ya gyaɗa yana haddar sunan a cikin kansa.
“Aiki ne ya kawoki nan?”
Ta juya ƙwallon idonta cike da ƙosawa.
“Eh”
“A ina kike aiki?”
Sai da ta ɗan kalleshi, sannan ta furta.
“Kamfanin ƙera kayan sawa na OP”
Ta shararo ƙaryar ba tare da ta ji komai a ranta ba. Dan a zahiri ne take aiki a can ɗin, amma a baɗini ba a can take aiki ba, hasali ma ba wannan aikin ba ne ya kawota USA.
“Ni kuma a GroTech AI center nake aiki!”
Ji ƙarya! In ba ƙarya ba yana aiki a GroTech ɗin zai zauna ba shi da mota?. A yanda ta san babbar ma'aikatar, babu ta yadda za ayi ma'aikacinsu ya zauna ba shi da mota, dan ba ƙaramin kuɗaɗe ake samu ba. Wata ƙila ma shara yake musu, maƙaryacin banza!. Ta ƙarashe zancen zucin nata tana hararsa a fakaice.
Rafeeq ya tsaya a sanda suka iso kwanar da zai yi wadda za ta sada shi da inda ya nufa.
“Ni zan yi nan”
Ya faɗi yana duban yanayin fuskarta da ta sauya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ba ya ce ga dalili ba, amma tun bayan da suka yi zancen keke ta sauya. Kallonsa ta ɗan yi sannan ta kalli hanyar da take da niyyar bi.
“Ni kuma zan yi nan!”
Naman goshinsa ya tattare alamun kokwanto.
“Ai nan ce hanyar da za ta sada ki da kamfanin OP”
Ya faɗi yana nuna mata hanyar, kasancewar wurin mararraba ne, hanyace da ta kasu kashi huɗu.
“Akwai ƙawata da zan biyawa, shi ya sa zan bi ta nan”
Ta faɗi tana mamakin yadda ya san kan garin New York. Kansa ya jinjina. Kafin ya laluba aljihunsa, ya ɗauko wallet ɗinsa, yana duba mata kuɗin da zai bata dan ta yi kuɗin taxi, bus ko jirgin ƙasa idan ta so.
Nadra ta shiga leƙa cikin wallet din nasa a fakaice tana mamakin yawan kuɗin dake ciki, ka da fa ta yi sake reshe kama ganye, ko da bashi da mota ai yana samun kuɗaɗe, za ta yi manage a haka, ko ba komai ta samu wani ATM machine ɗin.
“Ki yi kuɗin abun hawa”
Ya faɗi yana miƙa mata kuɗin, ko kunya babu Nadra ta miƙa hannunta ta karɓa tana ayyana yawan kuɗin.
“Na gode”
Ta faɗi tana ƙarawa gaba. Tsayawa ya yi a wurin duk da ya san cewa ana jiransa a wurin aiki. Amma ba ya son ya tafi ba tare da ya ga tafiyarta ba. Traffic ne ya dakatar da ita daga tsallaka titin da take san isa. Hakan ya sa ta tsaya a gefen titin ita da waau fararen yara guda biyu, suna jiran A basu hannu kafin su tsallaka.
Rafeeq na ganin haka ya samu wata kujera dake gefen hanya ya zauna yana sauƙe jakar bayansa. Duk da yau ana sanyi fiye da kullum, haka ya zauna yana daddana laptop ɗinsa a wurin. Kafin ya rufeta yana mayar da ita cikin jaka.
Ba zato ba tsammani Nadra ta ga an basu damar tsallaka titin ba tare da lokacin tslallakawar tasu ya yi ba, ba ita kaɗai abun ya bawa mamaki ba, har da masu abeben hawan dake tafiya a kan titin. Haka Nadra da yaran suka tsallaka titin suna ta mamaki a ransu.
Sai da Rafeeq yaga tsallakawarsu, sannan ya yi murmushi yana hayewa kekensa. Ya nufi inda yake son zuwa.
“Wai a ina ka tsaya ana ta jiranka?”
Abdulrahman ya tambayeshi a sanda ya iso ma'aikatar.
“Wani uzuri ne ya ɗan riƙeni a hanya...”
Ya amsashi yana shiga kyakkywan office ɗinsa dake hawa na shida. Abdulrahman ya biyo bayansa yana faɗin.
“Ina Maa?”
Rafeeq na cire trenchcoat ɗin jikinsa ya bashi amsa da.
“Lafiyarta ƙalau”
Abdulrahman ya gyaɗa kansa yana ci gaba da kallon abokinsa. Rafeeq ya nufi jikin mirror yana gyara sumar kansa.
“Kowa ya hallara a meeting room ɗin?”
“Eh, kowa ya iso, kai kawai ake jira”
Ya kuma gyaɗa kansa yana raɓa Abdulrahman ɗin, hannunsa riƙe da wannan laptop ɗin tasa ta amana, dan duk tarin computers ɗin da yake da su, ba su da anfani kamar wannan me ɗauke da zanen suna nasa a bayan screen ɗin.
Meeting room ɗin suka nufa a tare yana faɗawa Abdulrahman.
“Ina buƙatar hot chocolate, yanzu!”
Abdulrahman ya gyaɗa kansa, dan ga duk wanda ya san Ram, ba shi da abun sha da ya wuce Hot chocolate. Babu ruwansa da coffee ko tea, shi dai a bashi hot chocolate. Kuma a take a wurin Abdulrahman ya kira waya ya ce a haɗawa Ram hot chocolate, sannan kada a sa masa gishiri a ciki kamar yanda aka saba haɗa masa, saboda ciwon zuciyar da yake ɗauke dashi, dai-dai lokacin da suka iso ƙofar meeting room ɗin.
Ram ɗin ne a kan gaba, ya shiga yana bada haƙuri game da makarar da ya yi. Sannan ya samu wuri ya tsaya daga jikin farin board ɗin dake cikin meeting room ɗin. Bayan ya danƙawa Abdulrahman laptop ɗinsa. Wani switch Abdulrahman ɗin ya danna a jikin taga, nan take curtains ɗin dake sama suka sauƙo zuwa ƙasa, suka rufe ko wace katangar glass dake ɗakin, ya rage sai hasken projector dake haska farin board ɗin tare da Ram dake tsaye a gefensa.
“Good morning everyone! I'd like to introduce you to my self-driving car device. It uses sensors, cameras, and artificial intelligence to navigate roads and avoid obstacles. It's still in development, but it has the potential to make our roads safer and our lives easier...”
Haka ya ci gaba da kwararo bayanai a kan device ɗin da ya ƙera da hannunsa, dan hatta da matarsa tana amfani da device ɗin. Yana bayanin yana nuna musu hotunan dake playing a jikin bord. Yayin da masu kamfanin motar da Sir Thomas suka nutsu suna sauraronsa.
“How does the car know when to stop at a stop sign?”
Ɗaya daga cikin masu kamfanin motar ya wullo masa tambayar. Ram ya sosa tattoo ɗin wuyansa yana murmushi. Wani abu da ya kasance ɗabi'arsa.
"The car's sensors detect the stop sign and send that information to the car's computer. The computer then compares that information to a database of road signs and recognizes the stop sign. It then calculates the car's speed and distance from the sign, and it instructs the car to slow down and come to a stop”
Ya amsa cikin murmushi. Haka suka ci gaba da wurgo masa tambayoyi yana amsa su ɗaya bayan ɗaya. Ko da aka kai karshen tattaunawar tafi suka shiga masa suna jinjina baiwa irin tasa, ba a banza ya ci sunan nasa na RAM ba.
“A gaskiya ka burgeni, kuma mun karɓi wannan device ɗin hannu bibbiyu, sannan muna so mu fara gwadashi da motocin mu daga nan zuwa wata uku...”
Cewar shugaban kamfanin motocin, Rafeeq na murmushi irin wanda ya saba ya lumshe idonsa alamun ya amsa. Dan abu ne mawuyaci ka ga Ram na dariya, ba wai dan bai iya ba, sai dan ya fi yin murmushi.
Kuma murmushin ya fi dace da kamillalliyar fuskarsa. Kuma wani abun burgewa game da shi shi ne, a duk sanda zai yi magana ba'a iya ganin haƙwaransa sosai, ko zaka gansu sai dai samansu kawai, amma wai ka ga haƙwaran Ram duka sai idan ya yi dariya.
Kamar kullum haka Sir Thomas ya shiga faɗa nasa irin alfaharin da suke da shi. Sai da suka fice, kafin Rafeeq da Abdulrahman ma suka fita.
“Wai ina hot chocolate ɗin?”
Rafeeq ya tambaya yana buɗe ƙofar office dinsa.
“Ga shi nan”
Muryar ɗaya daga cikin ƙananu ma'aikatansu ta faɗi tana shigowa. A lokacin da yake zama a kan executive chair ɗinsa.
“Mrs Matilda kwana biyu?”
Ya faɗi yana kallon tsohuwar, Matilda ta ɗan yi dariya.
“Na je ƙauye ganin yarana ne, shi ya sa baka ganina”
Ya yi murmushi yana sipping hot chocolate ɗinsa.
“To ya yaran naki?”
Daga haka suka shiga hira da Matildan kamar yanda ya saba da kowa, dan duk ƙaryarka a wurin ba za ka ce ga abokin faɗan Rafeeq ba, kowa nasa ne, shi ma na kowa ne.
Sai da Matilda ta fice Abdulrahman yace.
“Da alama fa bamu ba komawa Nigeria kwana kusa”
“Ni kaina ban so hakan ba, amma babu yanda za mu yi, dole mu tsaya zuwa wata ukun!”
“To Allah ya kaimu”
“Ameen”
*Makoko, Lagos state, Nigeria.*
Gigi ce zaune kusa da Papi tana risgar kuka. Shi kuma Papin sai aikin lallashi yake.
“Kin ga Khadijatu, da yardar Allah Ekene zai fito lafiya!”
Papi ya faɗi a ƙorinsa na kwantar mata da hankali. Gigi ta fyace hanci tana faɗin.
“Ya za ayi na kwantar da hankalina? Sanin kanka ne idan 'yan sandanan marasa imani suka kama matasan yankin nan ba'a ƙara jin ɗuriyarsu... Wata ƙila shi ma hakan ce za ta faru da shi, na shiga uku ni Khadijatu! Me ya sa rayuwa ba ta min adalci? Ɗan marayan Allahn ma ba za'a ƙyale ba...”
Ganin mutum tsaye a kansu ya sa ta yi shiru, suka dubi wanda ke tsaye a kan nasu a tare, tashin hankali ya sa sam ba su ga shigowarsa cikin gidan ba. Cike da razani Gigi da Papi suka dubi juna. Lazarus me gidan hayar da suke ciki ne, sun san halinsa, ba shi da mutunci. Hakan ya sa Gigi dubansa tana goge ƙwallar idonta.
“Sannu da zuwa Lazarus... Ga wuri zauna!”
Ta faɗi tana miƙa masa wata kujera a kusa da ita. Gabjejen mutumin me sunan Lazarus ya musu wani banzan kallo yana zuƙar karan sigarin hannunsa, ya furzar musu da hayaƙin yana faɗin.
“Ba zama ne ya kawoni ba, ina 'yarku take?”
Cikin inda-inda Gigi ta kalli Papi kafin tace.
“Yan sanda ne suka kama Ekene, shi ne ta je ta yi belinsa...”
Ba ta ko rufe bakinta ba, Lazarus ya bushe da dariya.
“'Yar wahala kawai, na faɗa mata cewar wannan abun da take wahalar da kanta take a banza, amma ta ƙi fahimta, ina so ku fahintar da ita, ta aureni, zan hutar da ita”
Gigi ta goge ƙwalla.
“Dan Allah kayi haƙuri Lazarus, Shola ba ta san aurenka, ka yi haƙuri ka ƙyaleta”
Ta faɗi wata ƙwallar na ƙara silalo mata. Lazarus yay musu wani wulaƙanttaccen kallo.
“Okay, ba damuwa tun da haka kuka ce, ku shirya barin gidan nan, nan da sati ɗaya, sati ɗaya na baku, ka da ku kuskura ku haura hakan”
Yana kaiwa nan, ya juya ya daka uban tsalle ya faɗa cikin kwale-kwalen da ya zo gidan da shi. Gigi ta kuma fashewa da kuka tana ɗora hannunta a ka.
“Wayyo Allahna ni Khadijatu na ga ta kaina”
Papi ne ya ɗan muskuta kusa da ita yana dafa kafaɗarta.
“Ki dena kukan, ga su Ekene nan sun dawo, duba can ki ga!”
Da sauri ta ɗago da kanta ta kalli ƙofar gidan, inda ta hango Shola, Ekene, Fa'ee da abokan Ekenen guda biyu.
Har ta miƙe Papi ya riƙo hannunta, ta kalleshi.
“Ka da ki faɗawa Shola abun da ya faru”
Ta san a kan me yake magana, dan haka ta gyaɗa masa kai tana ƙara miƙewa. Zuciyarta cike fal da tashin hankalin da ba ta san ranar ƙarewarsa ba, don da a ce sun bar Shola ta auri mutum kamar Lazaru, gwanda su bar masa gidan nasa. Kuma yin hakan ma ba mafita ba ce, saboda ba su san inda za su je idan sun bar nan ɗin ba.
*No. 811, Poka, Epe, Lagos state, Nigeria.*
SURAJ ALI MUKTAR (SAM) POV.
Zaune yake a ɗakinsa, ya kafe balcony da ido, kamar me ƙirga adadin iskar dake shige da fice ta wurin. Tunani ne fal ransa, tunaninta, ita ɗin da bai ko san sunanta ba. Kyawawan fararen idanuwanta sune suka manne a cikin tunaninsa.
“Hamma Sam! Hamma Suraj!”
Ya jiyo ƙanwarsa Narjis na ƙwala masa kira tun daga ƙasa. Kuma har ta shigo katafaren ɗakin nasa bai amsa ba. Mamaki ya kama Narjis ganin yayan nata zaune a kan sofa ya kafe balcony da ido. Ƙarasowa cikin ɗakin ta yi, ta zauna kusa da shi tana bangazarsa da kafaɗarta.
“Ya dai officer, tunanin me kake?”
Ya juyo ya kalleta. Sai ta shiga ɗaga masa gira cikin alamun tambaya. Zamansa ya gyara yana kallonta da kyau.
“Narjis!”
Ya kira sunanta, ita ma nata zaman ta gyara tana miƙa masa hankalinta kacokam.
“Na'am Hammana”
Ya lashi lips ɗinsa yana so ya kwatanta mata irin yanayin da yake ciki, dan duk wani sirrinsu tare suke tattaunashi, bata ɓoye masa komai, shi kuma ba ya ɓoye mata komai.
“Wani abu nake ji yana yawo a zuciyata. Tun bayan da na ga wata yarinya a station yau. Zuciyata ta buga da ƙarfi, na ji ina son na kalli cikin idanuwanta, kuma na ji ina son na ci gaba da kasancewa da ita, ban... Ban ma san ya zan kwatanta miki abun ba”
Narjis ta lumshe idonta ta buɗe.
“Bro!”
Ta kira.
“Na'am Narjis!”
Ya amsa.
“Ka san menene sunan wannan halin da kake ciki?”
Ya girgiza mata kai da sauri, dan bai sani ɗin ba, bai ma san halin da zuciyarsa take ciki ba, bai taɓa tsintar kansa a cikin hali makamancin wannan ɗin ba.
“Love at first sight... You're in love Bro!”
“Da gaske kike?”
Ya tambaya yana

Please Login or Register in order to submit comment