Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa da shi ya zauna yana dafa kafaɗarsa.
“Ƙwarai kuwa Jamal ni da Tauqeer duka muna tare da kai”
“I dislike that house Saif...”
“To a ganinka wannan rayuwar da ka ɗaukawa kanka ta yi dai-dai? Saboda kawai baka san gidanku sai ka ɗauki wannan rayuwar?”
Saif ya tambaya, ba tare da ya amsa shi ba ya ci gaba da kukansa. Kafin kuma numfashinsa ya fara sama. Ɗif kukan nasa ya ɗauke tare da numfashinsa. Hankali tashe Tauqeer ya shiga kiran sunansa. Saif da ya taɓa jijiyar hannunsa da ta wuyansa yace masa.
“Ba mutuwa ya yi ba, damuwa ce ta masa yawa, mu ɗaukeshi muje gida kawai”
Kansa ya gyaɗa yana cicciɓar Jamal ɗin da kansa.
*Agha Mansion, Lekki phase 1, Lagos, Nigeria.*
*Da misalin 09:40 na dare.*
“Wai ni ina Saif ne?”
Taj ya tambayi sauran 'yan uwansa, yayin da yake jan kujerar daninng.
Mama da bakinta ke ƙaiƙayi wurin furta labarin da take ta dakonsa tun bayan fitar Saif ta dubeshi tace.
“Junior ne ya kirashi ɗazu yana dawowa, shi ne ya fita”
“Junior kuma? Wai shi ma bai dawo ba?”
Abba ya tambaya yana duba agogon dake a sashin katafaren danning area ɗin gidan. Umma dake zuba masa abinci tace.
“Ɗazu da na kirashi yace min yana hanyar dawowa gida, ban san me ya sa bai dawo ba kuma”
Jin ana danna door bell ne ya katse maganar.
“Aliya! Aliya!”
Umma ta ƙwalawa Aliya kira tana zama a kusa da mijinta.
“Gani Madam”
Cewar Aliyan tana risina mata.
“Ana danna door bell, je ki duba waye”
“Ok Madam”
Ta faɗi cikin girmamawa tana nufar hanyar da ƙofar gidan take. Deena dake zaune a kan danning ɗin ita ma ta wurga mata harara.
Tun kafin ta kai bakin ƙofar aka buɗo ƙofar, Tauqeer ya shigo, kafaɗarsa ta dama ɗauke da Jamal, Saif kuma na biye da shi.
*
A hankali ya kwantar da ƙanin nasa a kan gadon dake ɗakinsa. Blanket ɗin dake kan gadon ya janyo, sannan ya rufeshi da shi. Kallon fuskarsa ya ci gaba da yi yana nazarinta. Kamar me son gano halin da yake ciki. Jin sauƙar hannun Abba a kafaɗarsa ne yasa shi sauƙe ajiyar zuciya.
Miƙewa ya yi a hankali, sannan ya juya suka fuskanci juna shi da Abban.
“A ina kuka samoshi?”
Abba ya tambaya yana kallon fuskar Jamal. Shi ma Tauqeer ɗin kallonsa ya yi.
“A Maroko Bayshore!”
Abba ya dubeshi.
“Tun satin da ya wuce na yanke shawarar kaishi Rehab... Na yi shiru ne kawai dan Ummanku”
Tauqeer ya dube shi.
“Rehab kuma Habiby?”
Abba ya gyaɗa kansa.
“Ka sani kuma ni ma na sani Junior. Duka waɗanan abubuwan da Jamal ke yi ba yin kansa ba ne, dole da akwai wani abu a ƙasa. Sau nawa yake mana alƙawarin ya dena aikata komai. Ya taɓa denawar ne?”
Tauqeer ya girgiza kansa.
“A'a Habiby ba ya denawa”
“To shi ya sa nake son kaishi can ɗin, ko ba komai idan yana can akwai tsaron da ba zai barshi ya aikata waɗanan abubuwan ba, bayan wasu wattani sai ya dawo gida”
“Amma Habiby kana ganin cewa Habibty Za ta yarda?”
Abba ya sauƙe numfashi yana haɗe hannyensa waje guda.
“Wannan shi ne abun da ya dakatar da ni daga zartar da hukuncin da na yanke... Ban san wani irin hali za ta shiga ba”
Tauqeer ya ɗaga kansa sama, wuyansa da kafaɗarsabda ya ɗauko Jamal a kai na masa ciwo.
“Shi kenan. Yanzu ka je ka huta, ka samu abinci ka ci, na san a gajiye kake”
Kansa ya gyaɗa yana sauke shi ƙasa, kafin ya kalli fuskar Jamal.
“Ka da ka damu da shi, zan kula da shi har sanda zai farka, ka je kawai!”
Abba ya faɗa. Tauqeer ya gyaɗa masa kai.
“Sai da safe”
“Ka tashi lafiya Habiby”
Ya faɗi yana juyawa. A bakin ƙofar ɗakin Jamal ɗin ya haɗu da Hajiya.
“Tsohuwa ina zuwa?”
Ya tambaya cikin zolaya, duk da ba ya cikin irin yanayin. Hajiya ta ci gaba da leƙa ƙofar ɗakin Jamal ɗin kamar wadda aka cewa Jamal na tsaye a bayan ƙofar.
“Tsohuwa magana fa nake!”
Ya faɗa a ƙoƙarinsa na dawo da hankalinta kansa.
“Na'am tsoho ya jikin Jamalun?”
Ta tambaya kamar wadda ta dawo daga duniyar tunani. Kallonta ya ci gaba da yi, kafin yace.
“Bacci fa yake tsohowa, kada ki tada hankalinki mana!”
Kanta ta girgiza.
“Bari tsoho, lamarin na Jamalu sai dai addu'a”
“Shi ne abun da ya kamata ki masa, dan Allah kar ki saka kanki a damuwa”
Kanta ta gyaɗa.
“Bari na shiga na duba shi to”
Ya matsa mata ta shiga cikin ɗakin. Kuma bai bar ƙofar ɗakin ba Abby ya zo. Shi ma tambayoyi ya masa kan inda suka samoshi, sannan ya shiga ɗakin Jamal ɗin.
Me makon ya nufi ɗakinsa, sai ya nufi ɗakin Umma, dan a yadda ya ga yanayinta sanda ya shigo gidan da Jamal ya san yanzu tana ɗakinta tana kuka.
Umma na zaune a bakin gadon ɗakinta tana kuka, wayarta kare a kunnenta tana faɗawa yayarta Halima halin da take ciki.
“Ni fa ba na ganin lefin kowa bayan naki Maryam. Tun yaushe nake faɗa miki cewar akwai wani a bayan lalacewar Jamal? Amma kika ƙi yarda, daga ƙarshe ma sai kika ce wai ke baki da maƙiyin da zai iya miki haka... Shi yanzu Jamal an lalata masa rayuwa, shi kuma Tauqeer za'a lalata masa rayuwa ta hanyar aura masa wannan balamar!”
Umma ta dafe kanta.
“Wallahi Anti Halima ni kaina bana son auren Tauqeer da Deena, amma ya zan yi, iyayensu maza sun nuna suna son haɗin, kuma shi ma Tauqeer ɗin da aka tambayeshi amincewa ya yi, kin ga kuwa babu abun da zan iya a kai”
“Ai sai ki yi ta zama a haka, kina ji kina gani a sabauta miki rayuwar yara!”
“Zan iya shigowa?”
Muryar Tauqeer ta tambaya daga bakin ƙofar ɗakin, Sallama ta yi da yayar tata, ta goge hawayenta, sannan tace.
“Shigo!”
Shigowar ya yi, memakon ya ƙaraso cikin ɗakin, sai ya tsaya a jikin ƙofar yana kallonta. Yayin da ita kuma ta ƙi yarda su haɗa ido. Cikin ɗakin ya shigo, sannan ya zauna a kusa da ita yana kamo hannyenta.
“Habibty!”
Da ƙyar ta iya kallon fuskarsa. Ƙwalla na cika idonta.
“Jamal fa na cikin ƙoshin lafiya”
Ba tare da ta sani ba wani kuka me ƙarfi ya kufce mata, ta kwantar da kanta a kafaɗarsa tana ci gaba da kukan nata. Kanta ya shafa yana faɗin.
“Dan Allah ki kwantar min da hankalinki Habibty, ba na son kina kuka irin haka, ni da Iqra da Aabis da kuma Habiby hankalinmu zai iya tashi”
Shiru ta yi, amma ba ta dena hawaye ba, ɗagota ya yi daga jikinsa, sannan ya ƙara kama hannunta.
“Habibty mun yi magana da Habiby a kan za'a kai Jamal Rehabilitation center!”
Ya yi shiru yana kalon reaction ɗinta. Kallosa kawai ta ci gaba da yi, ta kasa furta komai.
“Ba na son ki yi wani mummunan tunani Habibty, za'a tabbatar da yana cikin ƙoshin lafiya, sannan na miki alƙawarin babu wani abun cutarwa da zai sameshi a can ɗin. Kuma a yadda Habiby ya faɗamin za'a kaishi ne domin a ya dena wannan halayen da yake yi”
Ba ta ce komai ba, saboda zuciyarta dake mata zullo, dan ji take kamar za ta fashe lokaci guda. Hanci ta ja tana goge ƙwallar da ta ƙi tsaya mata.
“Na amince Junior. Ku kaishi can ɗin, in dai har kuna da tabbacin zai dena abubuwan da yake!”
Rungumeta ya yi, ganin tana shirin sake fashewa da wani kukan.
“Insha'Allah Jamal zai dena komai, zai dawo Mama's boy ɗinsa kamar da... Yanzu dai ki dena wannan kukan”
Ya faɗi yana ɗagowa da kanta. Tare da share mata ƙwallar.
“Habibty an ya Habiby ya taɓa faɗa miki cewar idan kina kuka muni kike...”
Ya ƙarashe yana yamutsa fuska, ta yadda dole sai da ya sata dariya cikin kuka, ta ɗan daki damtsen hannunsa.
“Ki dena kukan ba ya miki kyau”
Ta yi murmushi tana goge ƙwallar, dan kaso sittin na damuwarta ya ɓace. Kuma hakan ya sa a ko da yaushe Tauqeer yake a sahun na biyu a cikin ranta. Saboda Jamal shi ne kan gaba, dan ta fi kowa kusanci da shi.
“Kar ka so ka ga yanda Abbanku yake shiga damuwa a duk sanda zan yi kuka, sanda ina budurwa babu kalar wahalar da ban bashi ba. Ko ka san sanda ina da cikinka tsakar dare nake tashinsa na ce ya fita ya nemo min muruci?!”
Ya ƙyaƙyale da dariya, ita ma ta shiga tayashi tana tuno zamanta da mijinta a shekarun baya.
“Ki ce shi ya sa na zama dogo!?”
Suka kuma yin dariya.
“Har yanzu ma yana damuwa da kukanki”
“Zan iya shigowa”
Iqra dake tsaye a bakin ƙofa, hannunta riƙe da tray ta faɗi. A tare suka dubeta. Tauqeer ne ya mata alama da ta shigo.
“Wai baki ci abinci ba?”
Ya tambaya a sanda Iqran ta dire trayn dake hannunta. Umma ta sunkuyar da kai tana motsa yatsunta.
“Ta zauna za ta ci abincin kuka shigo, shi ne ba ta ci ba, ta dawo ɗaki ta zauna tana kuka”
Iqra ta bashi amsa tana zuba mata abincin.
“Ya kamata ki ci abinci, ni zan je na ɗan watsa ruwa”
Ya fadi yana miƙewa.
“Kai ma ai baka ci abincin ba. Iqra ki je ki kai masa abinci...”
Ta ƙarashe tana duban Iqra.
“A'a Umma, ba yanzu ba, sai na fara zuwa na yi wanka tukkuna, idan na yi wanka zan kiraki, sai ki kawo min”
“Ok”
Iqra ta amsa tana zama kusa da Umma.

HAJIYA ZAYYA POV.
Cike da farin ciki ta shiga ɗakinta ta zauna a kan sofa. Haƙiƙa yau tana cikin matsanancin farin ciki, dan na ɗaya daga cikin ɗabi'unta, shiga farin ciki yayin da ta saka wani baƙin ciki. Tana samun farin ciki daga ƙuncin wanda ta zama sanadiyyar shigarsa cikin halin damuwa. Babu abun da ya fi faranta mata rai kamar yanda Maryam ta koma ɗakinta tana kuka. Wayarta ta ɗauka, ta aikawa Dr. Bashir kira.
“Barka da dare Hajiya!”
Abun da ya faɗi kenan bayan ya amsa sallamarta. Cike da jin kai ta gyara zama.
“Ina ajiyata?”
“Ajiyarki tana nan, yau ma sai da aka mata allurai uku. Sannan muka samu ta suma”
“Hmmm! Ya yi kyau, kana ji na ko? Ina so a haɗata da sauran masu taɓin hankali na asibitinku, a kuma ƙara saka mata matakan tsaro!”
“Amma kuma ai tana da hankalinta Hajiya, har magana ma fa tana iya yi”
Hajiya Zayya ta turɓune mummunar baƙar fuskarta cikin faɗin.
“Ai na san cewa tana da hankalin. So nake ka sakata a cikinsu, ta yadda ita ma za ta haukace ɗin, ka yi abun da nace kawai, za ka ga saƙo ya shigo maka”
Jiki na rawa ya amsa da.
“To Hajiya!”
Ta sauƙe wayar, ranta fes.
_________________
_Me kuke ganin zai faru da tsakanin Diya da MD?_
_Me zai faru ifan Rahila ta koma cikin masu taɓin hankalin dakw wacxan asibiti?_
_Mu je zuwa!_
A. ISAH CE✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE...💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER'S ASSOCIATION.
*Page 09*
~~~

SALAME POV.
Zaune suke a kan tabarma ita da Iya, yayin da takewa Iya Abun kitso. Inna kuma na daga madafa tana girkin dare, kasancewar me girkin tana kitso. Muja kuwa tun ɗazu da rana ya fita wasa wuri abokansa, Baba da Audu kuwa tun safe ba sa gidan, hakan ya sa daga ita sai Iya Abu sai kuma Inna.
“Salamatu Candy uwar riga!”
Ta kirata da sunan da ta saba mata waƙa da shi tun tana jaririya.
“Na'am Iya!”
Salame ta amsa tana duban saman goshin Iyan, dan bata iya ganin fuskarta gaba ɗaya.
“Wai me kika shirya a auren nan ne?”
Gabanta ya buga da ƙarfi ba tare da ta san dalilin bugwar ba. Yawu ta haɗiye, sannan ta sunkuyar da kai. Ganin Inna ma na kallonta, alamun dai ita ma ta ji tambayar, kuma su duka suna jiran amsarta ne.
“Me... Me kuma zan shirya Iya, babu abun da zan shirya ai”
Ta basu amsa kanta a ƙasa. Iya Abu ta juyo ta kalleta.
“Salamatu ko ba kya son auren nan ne?. In de har ba kya so ba za mu taɓa miki auren dole ba!”
Da sauri ta girgiza kanta ƙwalla ta rashin dalili ta silalo mata.
“Wallahi Iya ba haka ba ne, kawai de... Kawai ina jin ba daɗi ne na rabuwar da zan yi da ku... Shi... Shi ne kawai!”
Ta ƙarashe tana goge ƙwallar da ta sauƙo mata. Iya ta yi murmushi tana kamo hannunta.
“Ka da ki damu Salamatu Candyna, ai rabuwar aure ba ta mutuwa ba ce, a garin nan fa za ku zauna, idan kin yi kewarmu za ki iya zuwa ki ganmu idan har mijinki ya barki!”
Tunowa da ta yi da nan da wasu 'yan kwanakin zata rabu da su ne ya sa ta ƙara fashewa da kuka tana faɗawa jikin Iya. Iya Abu ta riƙeta tana lallshinta. Inna ta fakaici idonsu ta goge ƙwallarta.
“Kada ki damu Salamatu, muna nan tare da ke!”
Cewar Iya tana ci gaba da lallshinta.

*No.675, 361 Stagg Street, Brooklyn, New York, USA.*
* Da misalin 06:30 na safiya.*
RAFEEQ POV.
A hankali ya miƙe tsaye daga zaunen da yake. Hannunsa na dama riƙe da jar me ɗauke da hot chocolate. Idonsa manne da screen ɗin desktop ɗinsa dake kan desk.
Jin jikinsa yake duka babu daɗi. Saboda sammakon da ya yi na fara yin aikin nasa. Ga kuma makarar da ya yi a daren jiya, dan bai kwanta da wuri ba. Ga kuma tarin ayyuka dake jiransa. Saboda abu biyu ne ya sako shi gaba, haɗa AI humanoid robot ɗinsa, da kuma haɗawa kamfanin motocin nan device ɗinsu. Sauƙinsa ɗaya, yana da matemaka, da bai san yanda zai yi da ayyukan ba. A jiya ne ma ya yanke shawarar aje haɗa humanoid robot ɗin nasa, idan ya kammalawa kamafanin motoci aikinsu sai ya ɗora daga inda ya tsaya.
Bakinsa ya kai kan straw ɗin dake jikin jar ɗin, ya ɗan yi sipping kaɗan, kafin ya sauƙe da sauri yana kallon windown office ɗinsa.
Ya kamata ya ɗan yi jogging. Wata ƙila jijiyoyin jikinsa su ɗan miƙe, kuma ko ba komai ya samu sabon tunani. Kuma ya kamata ya kirata su fita tare. Amma kuma ai shi ba shi da lambarta. Murmushi ya yi a sanda ya tuna da:
_“Kamfanin ƙera kayan sawa na OP”_
Abu ne me sauƙi gareshi samun lambarta. Dan haka ya kuma yin murmushi, sannan ya nufi desktop ɗinsa, ya datsi na'urar kamfanin OP. Ta hanyar da ko su kamfanin kansu ba za su san an datsi na'urar tasu ba. Bayanan ma'aikatan dake aiki a kanfanin ya shiga dubawa. Kuma a ciki ya samo nata. ‘NADRA’ Shi ne kawai a rubuce, bayan shi kuma babu komai a gaba. Mamaki ya ɗan kamashi, amma kuma sai ya ture ya nemi lambarta. Ya kwafe a wayarsa da baya bawa muhimmanci. Sannan ya aika mata kira.

NADRA POV.
Kwance take a jikin sabon saurayin da ta yi a daren jiya, sanda ta je nightclub. Sigari suke sha a tare, idan ya zuƙa ya furzar, sai ya miƙa mata ita ma ta zuƙa ta furzar. Ainahin gaskiyarta kenan! Ainahin aikin da ya kawota New York kenan. Karuwanci ita ce sana'arta ta gaskiya, aikin kamfanin OP kuwa tana fakewa da shi ne domin kauda idon mutane a kanta, duk da nan ƙasar waje ne, duk rayuwar da za ta yi babu me saka mata ido.
_“Ki iya takunki Nandra!”_
Waɗanan su ne kalaman mahaifiyarta gareta a ko da yaushe, a ko da yaushe LANTANA mahaifiyarta na nusar da ita hanyar samun kuɗi a hannun samari da mutuncinta. Tun da ita kyakyawa ce, kuma ta iya jan hankalin maza, shi ya sa mahaifiyar tata ta turota nan ƙasar waje, don ta samu kuɗaɗe masu yawa.
Ainahin LANTANA mahaifiyar Nadra karuwa ce wadda ke zaune a garin Lagos. A sanda ta samu cikin Nadra babu yadda ba ta yi dan ta zubar da shi ba kamar sauran cikin da ta saba zubawa a harkar karuwancin nata. Amma cikin wani ikon Allah sai cikin ya ƙi zubewa. Hakan ya sa ta bar shi har zuwa lokacin da ta haifeshi. Kuma tun a lokacin da ta ɗora idonta a kan jaririyar tata ta yanke hukunci kafa jari da ita a sanda za ta girma.
A lokacin da harkar karuwancin Lantana ya shahara sai ta bar garin Lagos ta dawo garin Suleja ta siyi wani gida ta fara kawalci. Ba wa 'yayan mutane ba kaɗai, har da 'yarta ta cikinta. Idan ka ga yanda Lantana da Nadra ke mu'amala sai ka ce ba 'ya da uwa ba ne, dan kamar yanda kowa yake kiranta da Lantana haka ita ma take kiranta da Lantana nan.
Wayarta ƙirar iPhone 'yar ya yi ce ta hau ruri, ta miƙa hannunta ta ɗauka, kamar ba za ta ɗaga ba ganin baƙuwar lamba, sai kuma ta ɗaga.
“Hello Nadra!”
Abun da ya fara faɗi kenan, kuma tana jin muryarsa ta gane cewa shi ne. Da sauri ta miƙe zaune, sannan ta lalubo rigarta dake yashe a ƙasan gadon, ta saka kana ta sauƙa daga kan gadon, ta fita daga ɗakin, kuma har lokacin bata furta komai ba.
Ram da ya fara tunanin ba za ta yi magana ba ya ji tace.
“Black indian!?”
Murmushi ya ɗan yi jin muryarta. Ya sosa wuyansa yana faɗin.
“Eh ni ne... Zan je tattaki ne, shi ne na ce bari na faɗa miki idan za ki iya zuwa mu tafi”
Sai da ta waiga ta kalli ƙofar ɗakinta, sannan ta gyaɗa kanta cikin faɗin.
“Zan iya zuwa, bari na fito”
Cike da farin ciki Rafeeq yace.
“Ok, sai na ganki”
Daga haka ya sauƙe wayar. Ɗakinta ta koma ta yi wanka, aannan ta sauya kaya. A lokacin saurayin nata me suna Liam ya dubeta yace.
“Baby ina za ki je ne!”
Kallonsa ta yi ta mudubi tana saka canvas a ƙafarta tace.
“Zan je na dawo yanzu, ka kwanta ka yi baccinka ka ji?”
“Ok sai kin dawo”
Abun da ya faɗi kenan yana kara jan bargo. Ko da ta fita daga gidan a bakin ƙofar nasa gidan ta ganshi tsaye. Sanye yake cikin baƙin sweat pants. Da farar shirt wadda ya ɗorawa bakar hoodie a sama, kasancewar a gaba ɗaya rayuwar Rafeeq ba ya saka kaya ba tare da jacket ba, dan shi ba ma'abocin saka manyan kaya ba ne.
Murmushi yake jifanta da shi, yayin da ita ma ta mayar nasa da martani tana tsayawa kusa da shi.
“Mu je ba?”
Ya faɗi yana nuna mata hanya. Kanta ta gyaɗa a sanda suka jera ita da shi suna tafiya. Sun zaga sosai a unguwar, kafin suka tsaya a wani coffee shop, ya siya mata ta sha ita ɗaya. Sun jima a wurin suna hira, kafin suka dawo gida, ita ta shiga gidanta, yayin da shi ma ya shiga nasa gidan, ransa cike fal da farin ciki.

DEENA POV.
Zaune suke a inda suka yi shooting yau ita da ƙawarta Bilkisu. Coffee suke sha, dan ba su jima da kammalla shooting ɗin sabon film ɗin Deenan na yau ba.
“Mommy ta ce min aure tsakanina da Tauqeer shi ne abun da zai sa na mallakeshi a hannuna... Amma ni ban aminta da hakan ba”
Deena ta faɗa tana kallon mug ɗin dake hannunta. Bilkisu ta kalleta tana kurɓar coffee ɗinta.
“Ai Mommy tana da gaskiya Deena, aure tsakaninki da Tauqeer shi ne zai sa ki mallakeshi na har abada!”
Deena ta girgiza kanta.
“A'a Bilkees, a halin yanzu ba na jin zan iya auren Tauqeer. Saboda har zuwa yau bana jin Tauqeer yana sona kamar yanda nake sonsa. Ƙwarai na san ina sonsa, kuma na kan nuna masa hakan a aikace, amma to me ya sa shi ba ya ganin wannan son?”
“Wannan kuma laifinki ne Deena, ta ya za ayi ace kina da sauri, amma ba kwa yin wata wayar soyyaya, irin ɗan fita yawon nan ma na masoya ba kwa yi, hirar masoya ba ta haɗaku, kin ga kuwa ai dole ba za'a samu shaƙuwa tsakaninku ba”
“Bilkees Tauqeer fa ba ya kirana kwata-kwata, rabon da na ga kiran Tauqeer ya shigo wayata har na manta. A ganinki ni ce zan kirashi? Hmmm jin kaina ba zai sa na yi hakan ba. Bilkees ina da matsayi me girma, kuma ina son a riƙa ba ni girmana. Tauqeer ba ya yin hakan, so kike na riƙa binsa ina neman ya soni?”
Bilkees ta girgiza kanta tana murmushi.
“Deena look. Tun farko ke ce kike son Tauqeer. Kuma sai da kika kawo zancen aurenku tukkuna ya amince. To me zai hana ki sauƙe jin kanki, ki bi shi sau da ƙafa ki gani idan bai soki ba”
Murmushi ta yi tana aje mug ɗin hannunta.
“Ba ki san Tauqeer ba ne Bilkees, Tauqeer yana da taurin kai fiye da zatonki. A da yace ya dena soyyaya soboda wata budurwa ta taɓa yaudararsa sanda suna University. Ko amincewarsa da auren nawa ya bani mamaki. Ban san ya aka yi ya amince ba. Da farko na ɗauka cewar har zuciyarsa ya amince ɗin, sai daga baya na gane cewar ba haka ba ne. Mts lamarin Tauqeer sai a hankali Bilkees”
“Kin ga, ki kirashi ki ce ya zo ya ɗaukeki a nan, motarki ta lalace, idan kuna tafiya a hanya sai ki ce kina jin yunwa, ya tsaya ku ci abinci, a wurin cin abincin za ki faɗa masa cewar zuwa yanzu ya kamata ku yi aure”
Deena ta kawar da kanta tana kalon crew ɗin dake aikin tattara kayan aikin da aka yi amfani da su wurin yin aikin shooting ɗin, ta girgiza kanta.
“Wai ba ki ji me na ce ba ne? Ba na shirin yin aure yanzu”
“To sai ki zuba ido, kina ji kina gani wata ta zo ta ƙwace shi!”
Da sauri ta dubeta tana haɗe rai.
“Me kike nufi?”
“Idan har baki maida hankali kun yi aure da Tauqeer ba, to kina ji kina gani zai fara soyyaya da wata, har su yi aure ba tare da ke kin iya taɓuka komai ba!”
Deena ta yi shiru tana hango rashin yiwuwar hakan. Tauqeer ya auri wata ba ita ba?. Ai wannan gaibu ne Wallahi, matsawar tana da rai ba za ta taɓa barin hakan ta faru ba.
Tana wannan tunanin ne ba tare da sanin ƙaddarar dake shirin faruwa cikin wasu 'yan kwanaki ƙalilan ba. Wata kalar ƙaddara da za ta zo da HASKE. Wanda zai HASKA ko ina a cikin Agha Mansion, har ya kaisu ga ganin tarin abubuwan da suke ɓoye a cikin duhu.

*Agha Studio, No. 86, Orchird road, Lagos, Nigeria.*

TAUQEER POV.
“Gaskiya Asad ya kamata a ƙara kiɗan piano a kai!”
Cewarsa yana daga zaune a kan kujera, yayin da Asad ke zaune a gefensa, hannunsa riƙe da rubutacciyar waƙar da Tauqeer ɗin zai saki. Daga can jikin kayan kiɗan studio ɗin kuma, DJ Odunola ne ke zaune, bayan da ya haɗa kunna musu kiɗan da ya kamata a ɗora da waƙar.
“A'a beats ya kamata a ɗora ba piano ba”
Asad ya faɗa yana jinjina kai.
“Idan ka duba waƙar za ka ga ba ta buƙatar beats a kiɗanta, wurin zai fi kyau idan aka ƙara ko da busar sarewa ne!”
Cewar Odunola.
“To tun da haka ne, me zai hana mu ƙara sautin guitar a kai?”
Faɗin Tauqeer.
“Ƙwarai kuwa guitar sait ta fi hawa... A saka kiɗan guiter ɗin kawai”
Faɗin Odunola.
“Asad bani guitar ɗin nan!”
Asad ya miƙe ya nufi inda instrument ɗin studio ɗin suke, memakon ya ɗauko guitar kamar yadda Tauqeer ya buƙata, sai ya ɗauko piano keyboard.
“Asad! Guitar! Guitar ba piano keyboard ba”
Tauqeer ya faɗi a ƙoƙarinsa na tuna masa.
“Oh sorry. Guitar”
Ya faɗi yana juyawa, ya aje piano keyboard ɗin, sannan ya ɗauko guitar da ake buƙata. Tauqeer ne ya karɓa ya shiga kaɗawa suna shawarar yanda ya kamata ace kiɗan ya tafi.
“The sun may set, the moon may rise,The seasons change, before our eyes. But through it all, our love will stay, A constant truth, from night to day. The years will pass, our love won't fade, A flame that burns, it won't be swayed. Our hearts are one, our souls as one, A love so true, our story's done...”
Rera waƙar ta dakata tare da kiɗan guitar da kuma wanda ke tashi ta cikin sifikun studio ɗin. Saboda wayar Tauqeer ɗin da ta shiga ruri. Guitar ɗin ya aje yana kallon screen ɗin wayar. ‘DEENA’ Abun da sunan me kiran ya nuna kenan. Fuska ya yamutsa yana miƙa hannunsa tare da ɗaukar wayar.
“Hello!”
Ya faɗi yana miƙewa tsaye, tare da fita daga cikin studio ɗin, ya nufi office ɗinsa.
“Am hello Junior!”
Muryar Deena ta faɗi daga ɗayan ɓangaren. Ƙofar office ɗinsa ya buɗe yana shiga, sannan yace.
“Na'am”
“Na je shooting ne, sai motata ta lalace, shi ne na ce idan ba damuwa za ka iya zuwa ka ɗaukeni?”
Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba yana faɗin.
“A halin yanzu dai akwai abun da nake, bari na turo ko Hammad ne ya zo ya ɗaukeki!”
Da sauri ta girgiza kanta tana faɗin.
“Da ace za ka zo da kanka da sai na fi jin daɗi, dan Allah ka zo!”
Sai ya yi shiru yana sauraronta,

Please Login or Register in order to submit comment