Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



*_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*PML*


( We don't just entertain and educate we also touch the heart of the readers)






ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…




*YABO*

```Dukkanin kirari, yabo da godiya su tabbata ga sarkin sarakuna, Wanda bai haifa ba, ba'a kuma haifesa, Allah mad'aukakin sarki, Wanda ya adaidaita akan al'arshinsa mai girma, tsira da aminci su tabbata ga d'an gatansa, sha lelensa sayyidina Muhammadur rasulillah, dashi da sahabbansa da iyalan gidansa gabaki daya```


*GARGAD'I*

_Banyi niyyan rubuta wannan littafi ba don cin fuska ko cin zarafi ga kowa ba, nayi ne d'an fad'akarwa da nuna akan wannan bala'in daya kunno a cikin k'asar musulunci, k'asar bahaushe, Wanda yaci karo da addini da al'adar malam bahaushe kai tsaye, wanda a yanzu wannan nower day da muke ciki Wanda bayayin sa an d'auke sa bagidaje, bak'auye hmmm ita kuma dokar Allah ba haka take ba, duk Wanda yayi mata k'aran tsaye to tabbas zai had'u da fushinsa wasu tun anan duniya wasu kuma zaiyi musu talala har sai anje can a had'u๐Ÿคท๐Ÿฝโ€โ™€ Allah ya kiyashemu ya bamu ikon kiyayewa yasa wannan ya zama izina a garemu Ameen๐Ÿ‘๐Ÿฝ_


*A duk lokacin da akace tubarrij(tsiraici)na mata ya yawaita tofa musiba zata yawaita, ya Rahman musiba takai matuk'a kije dake da wani namiji Wanda ba muharraminki ba Ku d'auki foto na fitsara Ku yad'a a duniya, shin kinsan iya adadin wad'anda zasu kalleku, wai nan da sunan mijinda zaki aura ne kuke tallata kanku, anya akwai kishin juna anan? Annabi yace duk ma'auratan da basa kishin junansu to su da dabbobi basu da banbanci, Allah ya gyara*๐Ÿ˜‚

Wannan littafin wani bangare ya kasance gaske ne, sauran kuma duk dai abinda ke faruwa ne a wannan gabar, ina rokon Allah ya bani Ikon isar da sak'on yadda ya kamata ya bani ikon gamawa lafia Ameen.


Noteโœ๐Ÿป

_pls my true friends, don Allah in kinsan zaki karanta rubuta ki fara tun daga yanzu, kar sai nayi nisa a fara bina PC wallahi abubuwan da Yawa akwai takura, kuma bazan iya share mutum ba dan yanada daraja ko a gurin Allah, pls Ku taimaka min da wannan alfarmar, nasan me sonka ke son abinka nagode da soyayyar ku a gareni๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜˜๐Ÿค_



Dedicate 2 ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜







*01*






*QUEEN MIEMIE CLASSIC SALOON*


Abin da na gani rubuce kenan, gaban wani katafaren gurin salon da aka kawata shi da salon zamani, wow na fad'a a raina dan gaskiya ba k'arya gurin ya d'auki hankali na saboda yadda ya had'e, abinku da 'yar rahoto ganin nayi bazan iya wucewa ba har sai na isa gurin naga kwaf, watakil ma na dace da abin kawo muku, tsallaka titin nayi na isa gurin tare da shiga kai tsaye.

Mashaa Allah readers ashe banga komai ba kallo na ciki, guri ne mai girman gaske, ba abinda ba'ayi a ciki daya shafi mata, tun daga saloon, henna design, Kitso, gyaran k'afa, gyaran jiki, kai har kayan k'yale-kyalin mata ba'a barsu a baya ba, abinda zaifi d'aukar hankali da burgewa, yadda duk mata ne masu aikin cikin uniform na kamala Wanda ke nuni da gurin na musulmi ne.

Gefe d'aya na kalla, mata ne kusan su shida, Mashaa Allah, kyawawa dasu, kowacce da abinda ake mata.

Phone d'in d'aya daga Cikin su tai rings sunan *Shona* ya bayyana b'aro-b'aro akan faffad'an screen d'in wayar, wacce ake tsantsarawa henna design na gani na fad'a dan ubansu just like bride, Cikin yanga ta d'aga wayar tare da fad'in "yadai Shona!"cikin Jan hankali mai sauraro.

Banjin me yake cewa nadaiji tace "wow shona, dat y nake Matuk'ar sonka, nima ganin nan ana cancad'ani wlh so nake *pre-wedding pics* namu yayi rocking d best of d year, so nake su eshart su tabbatar nayi musu nisa, so nake a bani award a group namu na best bride of d session" fad'a tana kashewa wacce ke gefanta ido da alama k'awar ta ce.

" *Pre-wedding pics!*" Sauran matan hud'u suka fad'a da k'arfi, Fuskokinsu k'unshe da tashin hankali da kad'uwa Wanda zanyi iya cewa duk sanadin jin wannan kalmar ce ta jefasu ciki, dan sanda na shigo kowacce hankali a kwance yake.

Itama wacce ke wayar, katse wayar tayi jin yadda suka fad'a Kalmar da k'arfi, ta bisu da kallon tambaya da tuhuma da son Karin bayani ita da k'awar tata, suma dai kallon juna suke cike da mamaki, gashi dai basu tab'a had'u wa da juna ba sai anan gurin kuma a yau amma Kalmar d'aya ta jefasu a rud'u su duka me kenan?.........





๐Ÿค” _Tau nima dai da nake shirin ficewa dan ma'aikatan sun fara tambaya ta me za'ayi min, ni kuma banzo da shirin yin komai ba, saidai wannan al'amarin yasa dole zan tsaya a warware zaren a gabana dan bamu rena tsegumi๐Ÿคฃ_











Sabon salo๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€โ›น๐Ÿพโ€โ™€โ›น๐Ÿพโ€โ™€โ›น๐Ÿพโ€โ™€










๐Ÿ’„ Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜







```Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa yace "Ku riskar da bak'in cikinku da b'acin ranku dayin sadaka, Allah mad'aukakin sarki zai yaye muku cutar Ku, kuma ya d'ora Ku akan mak'iyanku(majma'ul bahrain)```




_๐Ÿ‘Œ๐ŸปMom ussey where r u, this is ur page u mean a lot to me๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐Ÿ‘๐Ÿป_



*03*







Da nayi da wata kyakyawar halitta wacce tunda uwata ta kawo ni duniya ban tab'a ganin kyawu irin nasa ba, bawai a kyawun kad'ai ya tsaya ba, kwalliyarsa kad'ai abar dubawa ce, k'amshinsa kuma abin shakane, wasu gangs ne a bayansa suma cikin shigar k'asaita, saidai tauraruwar wannan guy ta dosashe tasu.

Duk a cikin seconds na fahimci wad'annan ababe daga garesa, gasa nai da kaina yayin da k'irjina ke duka da sauri-sauri kamar ya fito.

Sake jin sautin daddad'ar muryarsa nayi wannan karon daf dani " yes ke kyakyawa ce, in fact kece sarauniyar kyakyawan duniya" a maimakon naji haushi kamar yadda na saba ji idan wani namiji yamin irin wannan kalaman dana d'auka na yaudara, na kuma yi masa warning amma duk sai na k'asa aikata komai, saima k'ara d'ago ido nayi dan yadda zuciya ta ke azalzalata da son k'ara kallonsa.

Subhanallah na shiwai wannan komai nasa mai kyau ne na fad'a a zuciya ta, da wani daban ne ya samar da wannan kusancin a tsakaninmu nasan tsaf zan iya marinsa, amma shikam na kasa, kashe min ido d'aya yayi tare da kyakyawan murmushi "can I be a friends?".

Ban iya cewa komai ba saidai martanin murmushin da na mayar masa " wow I like ur style" ya k'ara fad'a.

"Can u help me wit ur digit?" Bance komai ba still saima k'asa da nayi da kaima dan Allah yasan kyawun sa ba kad'an yake fisgata ba, a yau na rena kyawuna da mutane ke zuzutawa, Wanda ni kaina nasan kyakyawa ce ni a yanda nake ganin kaina a madubi.

Banyi aune ba sai ganin nayi ya duka ya d'auki phone d'ina dake gefena, in style yake operation phone d'in, abin bai wuce 2mnt ba ya saka no nashi ya kira yaga nawa.

"Till we meet next buddy" yace bayan ya aje phone d'in inda ya d'auka, "bye" ya k'ara fad'a tare da juyawa ya fara tafiya, tafiyar ma abar ayi kallo Ce, wad'annan gangs nasa suka take masa baya, wad'anda duk wannan bidirin da ake ba Wanda Yace tak, da alama dai yaransa ne.

Dafe kaina nayi tare da cewa ya ilahi maike shirin faruwa dani ne? A fili.

Dafani naji anyi da sauri na d'ago dan na d'auka shine ya dawo, murmushi tayi mini sannan ta zauna gefena, na ganeta tare mukayi lectures da ita dazu.

"Duk abin da ke faruwa a gaban idona nasan kina cike da tambayoyi ko" ta fad'a.

Kallon mamaki na bita dashi "kada ki damu, *Amir* kenan king of ATBU more than big boy, classy guy wanda Mata ke rububi a ATBU, ban tab'a ganin Amir yaje gurin wata ba saike, shi ake bibiya yana sharewa wannan na nuna ke mai sa'ace, nasan Amir sosai dan nasanshi ne a dalilin yayana he's his best friends, but yana yanzu yana Italy a can yake karatu, amma a yanzu haka kamar suna tare ne, na dad'e ina nacin son Amir amma bai taba kulani ba koda a minutes ne, dole na hak'ura dashi, duk had'uwar da zamuyi dashi a school d'in nan baya tab'a nuna ya sanni, hmm Amir ya wuce duk yanda kike tunani"

Nidai kallon ta kawai nike yanda take zuba to meye nawa da take bani wannan labarin, kamar tasan abinda ke raina tace.

"Ni fad'a miki ne saboda naga alaman wata alaka Amir keson kullawa dake, kiyi hankali ki iya takunki Amir nada matuk'ar had'ari shida Yayana nabarki lafia" ta Mik'e zata tafi, murmushi nayi mata nace nagode, duk da ban yaba da labarin nata ba....




************



Wasa-wasa, tunanin wannan gayen da aka kira Amir ya sakoni gaba ya hanani sukuni, a take na gane na kamu da sonsa, dan a gaskiya tun farko barina shine na auri kyakyawa abin Ajin farko na nunawa sa'a to wannan gayen ya zarce mafarkina da burina ya wuce mijinan da nake mafarkin mallaka..

Bai kirani a ranar ba sai can 12 After, dama Allah Allah nake ya kirani, bana d'aukar new no normally amma yau duk sabuwar no data kira shi nake hasashe hakan yasa nake K'asa runtsawa ina tsumayen kiransa, har barci ya fara d'ibana naji wayata na ring.

Zaune na tashi a lokacin da muryan sa ta daki dodon kunnena, wacce nayiwa lak'ani da golden voice.

"Sarauniyata bakiyi bacci ba" abinda ya fad'a kenan.

Aa banyi ba na fad'a a tak'aice, "meyasa hanaki bacci? Kaddai abinda ya hanani ne?" Ya jehomin da tambaya.

Um kawai na fad'a, dad'i duk ya gama mamayemin zuciya, wai nice wannan tsadadden guy ke riritawa, hmmm in tak'aice muku wannan shine farkon Had'uwata da mijina Amir farkon soyayyar mu kenan.

Wata d'aya Amir ya d'auka yana b'atamin hankali da tunani da zazzafar soyayyar sa, bayan Jan aji irin namu na mata da nayi tuni na bada kai bori ya hau.

Yan uwa soyayya bala'i ce kuma illa ce sometimes dan takan makantar da mai yinta ta hanashi hango laifin masoyinsa komai girmansa, soyayyar da mukeyi da Amir ta wuce ta addini da al'ada saidai a kirata ta yahudawa amma haka kullum korafin ban waye ba yakeyi, a maimakon naga laifin sa saima k'ok'arin wayewar nakeyi.

A ATBU kuma ba Wani d'alibi da bai samu labarin soyayya ta da Amir ba, haka ake turuwa azo kallona ana fad'in wace mai sa'ar ce, wasu su yaba wasu su kushe, nidai ba abinda ya daman da yabawan ko kushewan, nakan doka hassada ce kawai saboda ni na ciri tuta.

Sameera kuwa k'anwar Abokin amir tuni na sakata a sahun mahassada, na yadda da yadda tace akwai aminci sosai tsakanin Amir da yayan ta dan kuwa da wuya magana ta had'a mu komai k'ank'antar ta bai sako Sameer ba, tuni mun saba dashi ta waya.

Mami ce ta kula da yadda karatuna ya tabarbare sakamakon result dana kawo na first semester, baiyi kyau ba sabanin secondary da nake topping, to dole dan a makarantar bamu da aiki sai soyayya da amir, mune cafe, mune bin shadows da sauran gurin shakatawa.

Gaba Mami ta sakani akan na gayamata damuwata dan ta lura hadda zaman d'aki na fiyeyi yanzu, bud'ar bakina sai cewa nayi aure nakeso, dan da gaske auren nakeso a lokacin gudun kada Amir ya had'u da wacce ta fini kyau ya guje ni, banyi tunanin indai har akan kyau ne yake sona ba, to ko bayan auren ne yaga wacce ta fini zai iya juyamin abinda yafi baya ma.

Mamaki ne ya kama Mami jin Kalmar aure a bakina bako kunya, bayan tasan ada banason ko maganar saurayi ayimin balle ta Aure, b'oye mamakinta tayi tare da tambaya na tayi na samu Wanda nakeso ne, eh na bata amsa Kai tsaye.

Cewa tayi naje zatayi tunani akai, haka na tafi na barta da mamakin canja wata lokaci d'aya.

Dana gayawa Amir cewa yayi "so soon Queen".............






*labarin Suhaila ne dai take bamu, Niko nake zuk'o maku* ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€








๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



*_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*PML*


( We don't just entertain and educate we also touch the heart of the readers)


Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜





*_Da zaki had'a shekaru 99 kina faranta masa/mata a rana d'aya idan kika Kuskure musu duk alkhairanki na baya zasu shafe a zukatansu basa hango halacci da kyautata, sai wannan kuskuren da kika yi na rana d'aya, wannan shine dan Adam mai manta baya, duka haka muke 'ya'yan Adam, sai kad'an ne daga cikinmu ke tuna baya, akwai mu da manta alkhairi munfi bada himma gurin ganin laifin d'an uwanmu amma bamu damuwa da alkhairansa๐Ÿคท๐Ÿฝโ€โ™€ nidake dasu mu gyara tsakaninmu da mahaliccinmu bada wani/wata ba dan bazaka iya musu ba, d'an Adam sai Allah._*

Small quote๐Ÿ‘Œ๐Ÿป



_This page goes 2 u my Charming, careful, lovable sisters ๐Ÿ˜˜ Iya Amima, mom sultan, Aunty Khady, fannah, miss hafsy, indon kauye๐Ÿน#one love#๐Ÿคž๐Ÿผ













*02*






"Kaddai kema kin shiga musibar *Pre-wedding pics* " d'aya daga cikinsu tai k'arfin halin fad'a tana kallon wacce ke gefen ta da tuni idonta ya kawo kwalla.

Girgiza mata kai ta shiga yi alaman eh, bakinta na motsi amma ta kasa magana, a tare biyun sukace "kenan duk munyi tarayya a matsala d'aya, mun shiga musibar *Pre-wedding pics*"?

" and u again"? wacce ta tambayi wancen ta sake tambayan su cikin rud'u da son jin meke faruwa ne haka.

"Nifa kun sakani a duhu wacce irin musiba kuka shiga *A dalilin pre wedding pics*? Wacce aka kira ta fad'a tana zare ido dan ta tsorata da yanayin da tagansu ciki, itama k'awar ta cike da son jin wannan murdadden al'amari, tadaiyi cooling ne kawai.

( _nima dai mutuniyar taku na kame gefe nayi ready da pen dina na fara zuk'o maku d'umi-d'uminsa_ ๐Ÿคฃ )





***********



" pls kuce wani Abu mana, dan Allah kar kuyi shiru" eh pls Ku fiddamu duhu" yarinyar da k'awar ta suka k'ara fad'a a karo na biyu, suna kallon yadda kwalla kebin fuskokinsu.

Tattaro nutsuwarsu sukayi sannan daya daga ciki tace "sunana Suhaila" ni kuma Zuhra"

"I'm Mardiyya" and Na'ima" su duka hud'un suka gabatar da Kansu wa juna sannan wacce ta kira Kanta da Suhaila tace "ba tambaya mun fahimci mu duka 4 mun had'u da musibar Pre-wedding pics, ga kuma wata 'yar uwarmu tanason jefa Kanta a ciki" dafa yarinyar tayi tace "K'anwata pre weeding pics yana daga cikin mata'ul hayat, kuma yana daga Cikin sharrin yahudawa na yiwa musulunci zagon k'asa, shin zafi iya gayamin amfanin *pre wedding pics* kwaya daga bayan burgewa da nunawa jama'a?" Girgiza kai yarinyar tayi alaman batasan amfaninsa ba, murmushi Suhaila tayi Wanda yafi kama da yak'e "to Bari kiji musifar da ya jefani a ciki.....



*Labarin Suhaila*

Kamar yadda na gaya muku sunana Suhaila, 'yar asalin jahar Adamawa/yola, anan na tashi na ganni ina rayuwar k'ark'ashin kulawar iyayena, na tashi ni kad'ai ce a gidan mu, wato ni kad'ai iyayena suka Haifa, hakan yasa na samu gata matuk'ar gata, kowanne daga Cikin su baida abin roro sai farinciki na, amma hakan bai hanasu bani ingantacciyar tarbiya ba, boko kam ba'a magana dan da alama ya ratsasu shiyasa nima nayi shi da gaske.

Bayan na kammala secondary school, a lokacin ina bisa tsinin budurcina duk wata halitta ta kyawu ta gama bayyana a gareni, kamar yadda kukasan Fulanin yola da kyau, koma nace kamar yadda kuka gani yanzu a zahirance...

Bani da wani buri a rayuwa daya wuce nayi karatu mai zurfi, sam soyayya da saurayi basa gabana, duk da dinbin samari da sukayi min caa kamar suci babu, saidai banda lokacin su, kuma nayi nasara burin iyayena kenan.

Akwai rufin asiri sosai a gidanmu dan mahaifina babban ma'aikaci ne wanda ya taka muk'amai da dama a gwamnati, so babu abin na nema na rasa, kud'i Sam ba matsala bace, a haka Dady ya samarmin gurbin karatu a ATBU b'angaren business/administration, dan na nuna matuk'ar soyayya akan b'angaren, tun nursery up to now k'awayena 2 ne Khadija Sadis, Zahira Yunus, d'an bana sha'awar Tara k'awaye, sune dai tight friends d'ina, sauran dai a had'u a gaisane kawai, Khadija cousin dita ce and childhood friend, Zahira kuwa a Secondary muka had'u.

Ranar da na fara zuwa ATBU a ranar Dady ya bani sabuwar mota ta k'irar BMW latest, normally ni 'yar gayu ce, gayu bana maku up ba Aa na fashion, saidai duk da haka nakan rufe tsiraicina ta hanyar saka hijab ko gyale, yauma sanye kamar haka ne a ranar nayi gayu na Cikin wasu fakistan da Dady ya zomin dasu daga India, kalar lemon green and light orange ne,Kasancewar suna da babban mayafi wadatacce yasa banji nauyin saka su ba, sunlight glasses na maka sannan na manna hills a k'afata.

Addu'a da nasiha Mami tayi min kamar kullum idan zan fita, godiya nai mata tare da sallama kamar kullum sannan ta Bini da fatar alkhairi.

A lokacin da nayi parking a parking space, na fito "wow" naji wasu gangs sun fad'a, nasan ba mota ta ce ta d'auki hankalinsu ba, duba da motoci na kece reni dake birjik a gurin wad'anda suka dama tawa suka shanye, nafi tsammanin kyawuna da kwalliya ta ce ya d'auki hankalinsu, niko ko a jikina dan ko inda suke ban kalla ba, nayi wucewata faculty namu.

Zaune nike a k'ark'ashin inuwar wani Shadow dake bayan department d'in mu, ina duba handout d'in da aka gama mana lectures nasa yanzu, ina jiran internal d'in da garemu ya cika mu shiga next lecture.

Daga sama naji ance "hi Queen of beauty" cike da tsiwa na taso domin naci wa ko wane mai shishhigin ne mutunci, saidai me, kasa koda furta a nayi sanadin tozali da...............






๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚muje dai๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€







๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜






```Annabi Muhammad (S.A.W) yace "abubuwa uku duk Wanda ya kasance yana aikatasu munafuki ne, koda yana azumi da Sallah, koda yayi hajji da umrah, koda yace shi musulmi ne, idan yayi magana yakan fad'i k'arya, idan yayi alk'awari ya saba, idan aka bashi amana sai yaci(majma'ul Bahrain) Allah ya kiyashemu๐Ÿ‘๐Ÿฝ```


๐Ÿ“–MARRAHA HOME OF NOVELLA๐Ÿ“– ga shafinku saboda jin dad'in ku ana tare iya wuya๐Ÿค

*Mom Zee taki gaisuwar ta daban ce kishiyas๐Ÿ˜ k'awar Iya Hari ta amana๐Ÿ˜œ*









*04*







Tome ya rage ne my king yanzu, ina sonka kana sona kuma mun isa auren nan tome za'a jira? Murmushi mai sauti yayi " hakane my Queen, dama na fad'a ne kawai na auna mizanin sona a ranki Ashe kema kin kamu da yawa, amma fa baki kamani ba dan son da nake miki baki yayi kad'an ya furta shi, hankali yayi k'ank'anta ya k'ididdigesa, inasonki much Suhaila, dan haka duk lokacin da iyayenki suka buk'aci na fito a shirye nake beauty na".

Tunda ya fara kalaman nan nasa masu tsumani nai lahu a pilo ina saurarensa dad'i na ratsa jini da b'argo na, dan a lokacin yadda nakejin Amir a raina rana iska basu isa su rabamu ba.

Bayan kwana ina zaune a d'akina ina chat dasu Khadija duk dai hirar bata wuce akan Amir ba, dan yanzu ko wane motsi na Amir ne, kiran Dady ne ya na gani, ina dagawa yace nazo na sameshi a falonsa.

Tare na sameshi da Mami, bayan na gaida su Dady yace "Suhaila naga result d'in ki is too poor, shine Maminki, take gayamin kince Aure kikeso, wanene yaron"

Kaina a k'asa dan a gaskiya inajin nauyin Abba nace Amir sunan sa dan gidan Alhaji Mas'ud ne, a ATBU yake karatu shima.

"Aa kaddai Mas'ud kwangila nawa?" Dady ya fad'a, nace eh shine Dady "to ai tazo gidan sauk'i nasan Alhaji Mas'ud mutumi nane sosai, dan haka kicema yaron yazo zan ganshi, tashi kije kinji Allah yayi miki albarka" Mami dake zaune gurin mamaki ne ya kashe ta ita da take tunanin fad'a zaiyi, sai taga ba haka ba.

Kasa daurewa tayi "Alhaji ya haka, kada fa ka manta Suhaila yarinya ce, batasan me take so, karatu yafi kyau da ita a yanzu"

Murmushi yayi "Asiya kenan, ai duk kika ga yaro yakai ga furta yanason Aure tofa yin shine maslaha, kuma ai wanda takeson nasan mahaifinsa sosai" jim tayi sannan tace "hakane Alhaji amma duk da haka kai bincike sosai akan yaron Kafin a tsaida magana kasan yaran yanzu sai a hankali"

Amsa mata yayi da zaiyi, bayan Amir ya

Please Login or Register in order to submit comment