Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sabuwar haukace duba da yanayin ki shine nayi deciding na taimaka maki ta hanyar kaiki gidan mahaukata, Ashe da hankalinki yanzu saiki kwatanta min ta inda zamubi muje gidan naku" a hankali yake maganar cikin sanyin murya da alama zaiyi lafia.....




************




Da kwantance na muka isa gidanmu, godiya sosai nayi masa, yace ba komai yiwa Kaine, sai bayan ya wuce ne naji inama na tsayar dashi ya gana dasu Dady amma kuma dare ne gashi yace a hanya yake.

Saidai ko sunansa ban tambaya ba bare no nawa oh duk a rikice Nike da k'arfi na shiga knocking gate d'in dan unguwar tsit sai kukan karnuka kakeji, jin muryata yasa gateman din bud'ewa da sauri yana bina da kallon mamaki "lafia dai ranki ya dad'e da tsohon daren nan?" Hmm da sauk'i Baba daga haka nayi ciki.

Nan fa k'ofar falon knocking nayi Sosai sannan Mami da Dady suka zo suka bud'en da mamaki suke kallona, jikin Mami na fad'a tare da sakin kuka mai cin rai, nan fa hankalinsu ya k'ara tashi sai fad'i suke "menene, meya faru, Amir ne ya mutu, ko gidanmu ne ya k'one?" Nidai sai kuka Nike, jana Mami tayi zuwa seat, suna rarrashina, sai da nayi kuka mai isata sannan na samu na zayyana musu komai from A-Z.

"Innalillahi wa'inna ilairrajiun" itace Kalmar da suka shiga maimaitawa a tare "dama ni shiyasa ni tun farko yaron bai kwanta min a rai ba, wayewar sa tayi yawa kaga yadda yake magana ba tarbiya, amma a lokacin in da nayi magana da nayi baki a gun Suhaila da Kai, a yanda idonta ya rufe akan soyayyar sa, ko lokacin da nayi magana akan fotunansu da Event d'in da akayi ta nunan b'acin ranta, nidai na biku da fatar alkhairi kawai amma nasan tunda baku gina auren Ku akan turbar musulunci ba dole Ku had'u da musiba, Allah ya kiyaye na gaba" Mami ta fad'a, duk a maganar ta nasan ba k'arya dan komai ya faru nina jawa kaina, ban bi karantarwa d'aya da Manzon mu ya koyar a zaben miji ba, sai son zuciya.

"Hakane amma muma munada namu laifin musamman ni dan banyi bincike yadda addini ya tanadar ba, a ganina nasan mahaifinsa sosai, kuma mutumin kirki ne, ashe albasa batayi halin ruwa, Alhaji Mas'ud mutumin kirki ne kowa ya sani, banyi tsammanin haka daga d'ansa ba"

"Alhaji ai shiyasa ake cewa Allah na fitar da rayayye daga matacce kuma yana fitar da matacce daga rayayye, yanzu dai mai faruwa ta gama faruwa fatar Allah yasa wannan ya zama darasi a gareki"

Wallahi Mami na d'au darasi na fad'a cikin kuka, mun dad'e a gun ana jajanta lamarin da kuma k'ara nunamin rayuwa, sannan daga karshe muka nufi makwanci.

A ranar raya dare nayi first time in my life, nayi kukan tsoron Allah da Neman gafararsa da godiya a garesa daya kub'utar dani daga hannun azzalumai............







๐Ÿ˜ *kuyi hakuri my fans, missing chat d'ina nayi all, shiyasa kukaji shiru#1love#* ๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ˜
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



*_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*PML*


( We don't just entertain and educate we also touch the heart of the readers)




Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜







```An karb'o daga Abu huraira R.D yace
Naji manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a garesa yace "yana daga cikin kyawun musulunci, mutum yabar abinda bai shafesa ba.(Arba'una hadith) ```










*08*





Washe gari bayan Azahar saiga sak'on Amir mai gadi ya kawomin, saki uku tare da kalaman b'atanci da cin mutunci had'e da tsora ta ni akan idona idonsa sai ya d'au fansar abinda nayi musu, sai fotonan wata daya turomin yana gayamin ya samu wacce ta fini komai, kyau, wayewa da komai, ganin sakin ba k'aramin dad'i yayimin ba dan ji nayi kamar an rabani da k'aya, ko kad'an banji zafin rabuwa da Amir ba, dan abun kwarai ake burin zama dashi ba cuta, ita kuma yarinyar tausayi ta bani dan ta shiga mugun hannu, inko da gaske itama irinsa ce ina musu fatar shiriya...


Sakin kawai na nunawa su Mami ban nuna musu sauran tarkacen ba dan banaso Dady yace zai d'auki wani mataki, Mami kam sanyi jikinta yayi nasan hakan baya rasa nasaba da mayar dani k'aramar bazawara da Amir yayi, nikam da auren Amir gara tabbata a zawarci, Dady yace zai jira yaji daga mahaifin Amir kafin ya taresa da zancen.

Ganin har anyi sati baiji daga garesa ba, koda Dady yaje wa Baban Amir da zancen mamaki ne ya rufesa dan baisan da zancen ba, kuma baiji ko a cikin gidan ba, koda ya shiga gida suma hakan ce basusan zancen ba, har mamarsa tace gaske dai aka had'a sati banzo ba kuma ban kirata Ashe ba lafia ba kuma ta kirani taji kashe amma batayi hausan kiran Amir ba kota tura k'anninsa su duba mata a nata tunanin muna lafia.

Sosai Baban Amir ya nuna b'acin ransa dan baisan Amir ya lalace har haka ba saboda rashin zamansa bai kuma damu da saka ido a 'ya'ya ba a ganin sa sun mallaki hankalinsu, Ashe ba haka bane ( 'ya'ya a koda yaushe sai ana kula da lamuransu dan komai na babba yafi na yaro, Allah ya shirya mana zuria damu baki d'aya)

Koda suka bincikesa yabar k'asar shida Sameer da sabuwar budurwarsu duniya sabuwa, nan dai Abban sa ya bawa Dady hak'uri akan al'amarin, Dady yace ai wannan ya Riga ya wuce yanzu shine da gyara dan rayuwar Amir na buk'atar gyara.

Sanda su Khadija sukaji sukazo sun girgiza da lamarin kuma sun d'auki izina daga abin da ya sameni, a haka naci gaba da zama a gidanmu bana fita ko'ina har na kammala iddata, makarantar duk ta fita raina, hakan yasa na nemi su Mami su barni naje Kano gurin k'anwar Dady nayi karatuna a can dan duk yola ta fita a raina saboda bak'in fentin Amir yanzu koda mai irin sunansa na tsani ji kamar yadda nake kad'uwa da shiga tashin hankali idan naji ance *Pre-wedding pics* dak'yar na samu su Dady suka barni shima saida saka bakin Aunty Salma(k'anwar Dady) nasan zanyi missing iyayena sosai kamar yadda zasuyi missing d'ina saidai hakan shine kwanciyar hankali na....




***********




Zamana a Kano yamin dad'i sosai dan Aunty Salma irin mutanen ne ce masu barkwanci kuma dama na saba da ita dan dama ina zuwa Hutu, ga yara a gidan masu debe wa mutum kewa, hakan yasa hankalina ya kwanta na samu nutsuwa, saidai abinda ba'a rasa ba na yanayin rayuwa.

Cikin sa'a na samu gurbin karatu a BUK b'angaren computer science, sosai na mayar da hankali akan karatuna, ba ruwana da kowa a school d'in, duk wani saurayi dazai kawomin Hari kar nake kallon sa dan Amir duk ya batasu a idona, banda lokacin soyayya da makamancinta, muna second semester a 1st year namu, akace wani lecture na department d'in mu, dayaje course wata shida daya wuce ya dawo, zaici gaba da d'aukar mu course d'in da wani copper ke d'aukar mu dama na shine aka bawa copper d'in, yanda naga students nata murnar dawowar sa ya tabbatar min da suna sonsa da alama yasan kan aiki.

Kunsan waye? Suhaila ta fad'a...

Girgiza kai gaba d'aya sukayi alaman Aa, nisawa tayi tare da sakin murmushi cikin hawaye....


Wannan bawan Allah ne Wanda ya taimakamin a ranar ya kaini gida, nayi farincikin ganin sa dan ina so na k'ara gode masa kuma na had'a shi dasu Mami suyi masa godiya dan suma suna burin hakan.

Bayan mun gama lectures ne, da sauri na fito dan ganawa dashi a bakin motarsa na samesa yana shirin shiga Sir na fad'a cikin sanyi, juyowa yayi ganina yasa mamaki ya bayyana a fuskarsa ni a tunani ma bazai ganeni ba, sai jin nayi yace "u again, from yola 2 Kano how comes?" Dan murmushi nayi tare da gaidashi, bayan ya amsa ne yake kara tambaya ta ya akai ya ganni a Kano kuma da alama ni students ce anan.

Amsa masa nayi hakane anan nake karatu nazo gun k'anwar Dady na ce, nace na manta a ranar ko sunanka ban tambaya ba, bare no ka har fad'a Dady yayi yaga wautana yace ya kamata su gode ma, murmushi yayi yace ba komai ai, nace to zan iya samun no sa dan na bawa Dady na, ba musu ya bani sannan mukayi sallama, cikin zumud'i na kira Dady na gayamusu sannan na tura musu no sa suka kirasa sukayi masa godiya.

Sannu-sannu sha kuwa ta fara shiga tsakanina da Sir Imran students har mamaki suke dan Sam ba ruwan sa da Mata, gashi baida hayaniya komai nasa very cool and simple, har tambaya suke hala dan uwa nane nikam eh nake ce musu dan banson silly question, yana taimaka min sosai a harkar karatuna wani sa'in har office nake iskoshi ya gayamin inda ban fahimta ba, har Aunty Salma saida tasan da Sir Imran.

Ranar muna zaune bayan ya gama min explanation yake cewa "Suhaila Niko ya kika kare da mijin naki?" Nan na shiga bashi labarin yadda akayi da har ma yadda mukayi auren ban b'oye masa komai ba, dan inajin sa ne kamar d'an uwana Yayana, ya jajantamin tare da nunamin kuskurena a ciki sannan yayi min fatan alkhairi.

A ranar muna lectures nakejin wata na fad'in Sir Imran na burgeta tayi nisa a sonsa da zata samu ya sota data more, sai naji Abu ya tsayan a wuya naji inajin haushinta, har na koma gida abin na raina, tambayan kaina na shiga yi me hakan ke nufi kenan na fad'a sonsa? Aiko nayi kuskure dan nasan bazai tab'a aurena ba, da wannan tunanin na fara janye masa, sannu-sannu dan samawa kaina sauk'i.

Ranar ina zaune d'aki saiga kiransa wai gashi yazo biko sannan nazo yaji laifin me yayimin nake gudunsa, gashi na tayar masa da hankali na hanashi nutsuwa.

Da mamaki na fita aiko sai ganinsa k'ofar gidan nayi sai naga yad'an fad'a da tsawon sati d'aya kenan rabona dashi, jagora nayi masa zuwa falon gidan, bayan mun gaisa na kawo masa abin tab'awa ya kalleni yace "kekam naga ko a jikin ki, kiga yadda na rame akan rashinki" nikam kaina ne ya k'ara daurewa tome zaisa ya damu dani har haka "na damu dake mana tunda zuciya na k'aunar ki, ban sani ba ko zaki iya Auren mai marayun yara har biyu" yace kamar yasan me nake tunani, d'ago wa nayi da sauri dan na gasgata shidin ne ko mafarki nake, murmushi ya k'ara yi "da gaske ina sonki kuma nayi alk'awarin mantar dake Amir inshaa Allah zan rik'e ki amana"......


Allah mai yin yadda yaso a lokacin da yaso ga Wanda yaso gashi ya bani Imran a lokacin da nake ganin banda damar samunsa, nayi masa kuskure nayi tuba, tuba mai kyau gashi ya amshi tubana ya inganta rayuwa ta ya had'a ni da Imran masoyin gaske Wanda yasan darajar Addini da hak'ok'insa.

Ba bata lokaci akayi bikina da Imran, banbancin Imran da Amir kamar duhu ne da haske, Imran ya mantar dani Amir ya d'auka ka ni ya girmama ni ya bani dukkanin jin dad'in rayuwa, na gane idan mutum ya gina rayuwar sa domin Allah zaifi jin dad'in rayuwa, nayi tak'aicin fotunana dake yawo har yanzu cikin media *A dalilin pre weeding pics*.

Wannan labarin da nake gaya muku tsawon shekara 4 kenan,na rik'e yaran Imran da gaskiya da amana gashi yanzu har na mallaki nawa inada 'ya daya mai sunan Mami muna kiranta Amal, gani ina shekara ta k'arshe a , Sir Yayimin komai a rayuwa, saidai nace Allah yayi masa mafificin sakamako.

Tau k'anwata kinji bala'inda *Pre-wedding pics* ya afkani.

Hmmm kunsan meya faru da Amir??


_mun baza kunne muna saurara_ ๐Ÿ‘‚๐Ÿป๐Ÿ‘‚๐Ÿป๐Ÿ‘‚๐Ÿป





๐Ÿ˜kuna raina a kullum my dear Raheenat & my parrot Hafsat mai Sharif๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜







๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



*_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*PML*


( We don't just entertain and educate we also touch the heart of the readers)




Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜








*_daga gareta muka samar daku, daga cikinta zamu maidaku, kuma a cikinta zamu tayar daku, tayarwa ta biyu, dan haka ba wata tak'ama da nuna isa suk d'aya muke ba Wanda yafi wani a gurin Allah sai Wanda ya fika tsoronsa, Allah ka kara masa tsoronka dayi maka biyayya Amin_*๐Ÿ‘๐Ÿฝ




๐Ÿ’“ _Sumyn bash Novell, ga shafinku don kun cancanta_ ๐Ÿ’“







*09*



Last year da naje Adamawa nake samun labarinsa daga gurinsu khadija, Ashe tunda suka bar kasar, India suka wuce suke sheke ayarsu tare da wancen yarinyar daya turomin fotonta ta zame musu kamar matarsu, haka suke shearing nata ba k'amk'ami bare kunya ko tsoron Allah.

Hmmm ashe basu sani ba wuka suka dab'awa kansu da Kansu, dan sun d'auki ruwan dafa Kansu, tunda suka je garin basu k'ara tuna iyaye da 'yan uwansu ba, sai duniya suka saka a gaba, haka sukaci gaba da zama Ashe yarinyar 'yar damfara ce, da haka ta kwashe duk wani Abu da suka mallaka sannan ta basu tukucin AIDS, ta gudu ta barsu a can, basu Ankara ba sai bayan kwanaki suka fahimci ta damfaresu ne, anan kuma ta bark'e a tsakaninsu suka shiga blaming juna, at d end suka rabu kare jini biri jini, kowa ya kama gabansa, ganin zaman garin ya fara masa zafi ne yasa ya yanke shawarar dawowa gida, bayan ya dawo da yaje gidansu iyayensa cewa sukayi su basu sanshi ba sai yanzu yasan dasu, yaje sun yafesa, abunku da marar ilimi marar tarbiya a maimakon ya basu hak'uri sai yayi fushi shima ya kyalesu yaci gaba da Neman aikinsa a ganinsa yana cikin matsala suna son k'ara masa wata, kunji tab'ewa da rashin rabo, meyakai tab'ewar fushin ubangiji dana iyaye ya tabbata a gun mutum, yana tsaka da wahalar nema ne ciwo ya kwantar dashi koda aka kaishi hospital sai aka gane ya kamu da HIV har ya zama chronic to AIDS nan ya k'ara shiga tashin hankali, a maimakon ya koma ga Allah sai ya tayar da hankalinsa ya hanama kansa nutsuwa so pity ya haukace a halin yanzu yana gidan mahaukata,ga mugun ciwo ga hauka kuma duk sab'on Allah ne ya janyo masa, iyayensa ne still yanzu a kansa suke bashi kulawa dan kunsan jinkai da tausayi irin na iyaye musamman uwa, Sameer kuwa ya rasu, lokacin da na samu wannan labarin na girmama Allah.

Sai nayi tunani wato ita rayuwa ba aikata sab'o ne matsala ba, sab'o is common kowa na aikatawa abinda yake matsala kana aikata sab'o ka kasa yadda da sab'on kakeyi bare har kayi tunanin gyarawa, sau da yawa muna kuskure to indai zamu karb'i kuskuren namu, mu gane yes munyi kuskure sai muyi darasi daga garesa mu gyara da mun dace, to waima meke kawo hakan wato rashin gane kana aikata kuskure?

Nidai a tawa fahimta son zuciya ne da girman kai da karamcin ilimi da rashin fahimta, kamar yadda ta faru ga Amir, na k'ara samun darasi daga rayuwar Amir, na k'ara tsorata da lamarin sab'awa ubangiji kuma na gode wa Allah daya sa na gane kuskure na, dan rahamarsa gareni badan wayo ko dubarata ba....

Dafata tayi "k'anwata kinga a cikin labarina da Amir ba tsantar tabawa ubangiji ne kawai ba hadda son zuciya wacce ita ke leading zuwa ga sab'on Allah, Allah yasa mu dace duniya da lahira" Suhaila ta fad'a, Ameen suka amsa, jikin kowa dake gurin ya gama yin sanyi kuka kam ba Wanda bai zubar da hawaye ba, wacce ta kira kanta Zuhra ce ta taso ta dafa Amaryar da Suhaila, sannan tace "tabbas Suhaila kin had'u da musiba irin taki, hmmm to bari kuji tawa kalar musibar......







*LABARIN ZUHRAH*



Fatima Ismail shine cikakken sunana amma Umma nah na kirana da Zuhrah saboda sunan kakata dana ci, dama sunan da uwa ta kira 'yarta dashi shike binta hakan yasa Zuhrah ya kwace, ni 'yar asalin Gombe ce, muna zaune a buhari estate, na ta taso na ganni a gidan taro dan mahaifina yana da matan aure har uku mahaifiya tace ta farko, sannan biyun suka biyo baya mu 16 muke a gurin Babanmu maza 10 mata 6 nice ta biyu a cikin mata sannan 4 ke biyo ni.


Ba laifi akwai rufin asiri a gidanmu mahaifinmu ba wani babban ma'aikaci bane amma yana iya k'ok'arinsa a kanmu bai tab'a bari mu gani ga wasu yana iya yinsa gurin hanamu hangen na wasu, muna karatun islamiya sosai haka na boko munayi mata daga secondary muke tsayawa, Allah yayi mini baiwar kyau dan naji ana fad'a nafi kowa kyau a gidanmu, hakan yasa na d'auki dogon buri na saka a raina tun ina aji uku a secondary na fara kula samari saidai iyaka ta naci kud'insu amma ko hannuna baka isa ka tab'a saboda har tsoratar war da Umma na ke mana da kuma islamiya sunyi tasiri a kaina....


A haka akayi auren Adda Aina'u ganin yanzu tauraruwa ta ke haskawa ta d'aga ta Bani gu, duk wannan abin da nake Abbanmu baida labari sai Umma ce ta Sani dan itama ta d'ora buri a kaina kuma ina kawo mata 'yan canji, ana hakane wani ya sayyadinmu yazo gurin Abbbanmu ya nemi izinin aurena in har ba'a tsayar min da miji ba yana sona, sanin halin kirkin ya sayyadi Ahmad yasa Abba ya bashi damar neman soyayya a gareni.

Lokacin da Abba yazo da maganar ba k'aramin tashi hankalina yayi ba, nan take naji tsanar ya sayyadi ta dirar min a rai wato shiyasa yake wani kwantar min da murya, yana wani shigemin dan yaga ina mishi murmushi to daga yau na daina tunda abin nasa bana girma bane, kuma zaisan dawa yake zancen zai gane ya d'auki ruwan dafa Kansa, yo in banda renin wayo mena sama yaci bare yaba na k'asa kuma ni mezanyi da ustaz da baisan komai ba sai k'alallahu k'ala rasulu, nida naci burin soyewa in bige da ya sayyadi ga talauci ga mita abin da naita sak'awa a raina kenan.

Inda na k'ara samun dama Umma ma batayi na'am da zancen ba, saidai bamu Nuna masa a fili ba, daga haka na shiga gara ya sayyadi Ahmad ya kasa gane gabana bale bayana....


Duk iskancin da nake masa, bai tab'a gayawa Abba ba, kullum cikin lallab'ani yake da nunamin gaskiya niko hakan ya bani damar ci masa mutumci da wulak'antasa, idan shike dauk'armu a aji saidai na fice waje nayi ta danne-dannen wayata wacce Abba baima San da ita ba dan a nashi tsarin bama rik'e waya sai munyi aure idan mazajenmu sun aminta dan haka akayi da Adda Ainau...

Daga k'arshe ma na gane islamiyyar takura ce a gareni, saina fara tsallaken ranakun zuwa sai Tamin suger, barni dai da yawon gidan k'awaye masu kud'i ina d'aukar pics ina d'orawa a dp na ko a groups irin big gurl d'innan ba raini...

Wata Rana naja wanka as usual na d'aukar magana na fito da marece zanje gidansu Adda Ainau, ina cikin tafiya kan titi saiga wata jahilar mota wuce bak'a sidik sannan glass d'inta duk bak'ine wow na fad'a a raina duk da bansan motoci ba a lokacin nasan wannan motar ba k'arya ta had'u kuma da alama bata wasa bace ma'ana taja naira.

Ina cikin tunani game da motar sai jin horn nayi a dai2 ni, ina daga ido naga motar ce da nake santi akemin horn da ita, abinku da son jan girma saina basar naci gaba da tafiyata cikin solon yaudara da jan hankali, nak'i kulasa a haka naci gaba da tafiya yana biye dani har na isa gidan Adda Ainau da yake dama na kusa.......

Ina cikin gidan amma hankalina naga motar can, har na fara hango wautata nak'in tsayawa na sauraresa gashi har yanzu banji ance ana nemana a waje ba, har saida Adda Ainau ta tambayeni meke damuna naketa zuba tsaki, sai CE mata nayi ina tunanin exam dinmu ce.

Sai bayan magrib na baro gidan, hmmm wai kusan me???










*mun shigo shafin Zuhrahriyyah 'yar gayu๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ˜‰*





_kuyi hakuri da jina shiru ina fama da ciwon hak'ori ne๐Ÿคง๐Ÿ˜–_








๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜










๐Ÿ’–Mom ihsan novels here is ur page๐Ÿ’– just for u my fans๐Ÿ’ž ana tare๐Ÿค









*10*











"Saurauniyar mata, barka da fitowa" abinda naji an fad'a kenan a bayana, da d'an mamaki na jiyo dan ganin waye hmm subhanallah na fad'a dan a gaskiya na razana da ganin cikar halittarsa ya had'u iya had'uwa yana kama da fulani kai tsaye dan har maganarsa kamar tasu, motar ce tasa na gane wannan saurayin ne daya biyoni kenan naki saurararsa Ashe ba kud'i kawai yakeda ba hadda cikar halitta kai wannan shine dai2 ni na fara rayawa a raina dan ya had'a komai da nake buk'ata a tare da namiji duk da nasan bai kamo Ya sayyadi Ahmad a kyau ba, saidai ya fishi tunda yanada masu gidan Rana.

Tsayawa nayi chak tare da cewa wai me kake nema a guna ne daka ke bibiyata? "So da k'aunarki kawai nake buk'ata ma'ana ki zamo matata uwar 'ya'yana" ya fad'a yana dirowa daga motar.

Cikin nuna ko in kula nace naji saidai ban aminta ba kuma ni a hanya nike, na juya da niyyan ficewa, shan gabana yayi yai k'asa da murya cike da magiya "haba keko gimbiya ai kya tausayamin ki duba tsawon lokacin da na d'auka anan gurin saboda ke, kada ki manta mai sonka ya gama maka komai"

Meya hana ka aika a kira maka ni, waima da ban fito ba a yanzu da zaka ganni ne? Na fad'a cikin k'osawa duk da ina yine dan na auna son da yakemin inna gaske ne, a tawa wautar da k'uruciya.

"Bazan iya katse miki jindad'i ba ko uzurinki na gwammace na kwana anan har sai ranar da kika fito da kanki da ace na aika a kiraki na b'ata maki rai, and nasan lallai zaki fito kodon school" ya fad'a still cikin yaudara irin tasa wacce ada na d'auka gaskiya ce tayi masa yawa.

Tau yanzu dai kaga nan ba gidanmu bane gidan yayata ne kuma yanzu gida zanje ina sauri dan nayi dare Abbana zaiyi min fad'a, so zaka iya biyoni in har kana sona da gaske saika je gurin Abbana da zancen.

"Why not na saukeki tunda dare ne?" Aa bazan shiga motarka ba, in zaka iya bina a haka well.

"Ai dolena tunda na had'u da matata abar sona ur wish hajia" ya fad'a yana murmushi, nikam mamaki nake yadda nake bashi umarni yana bi duk girma da matsayinsa dan da gani d'an Baban gidane, hakan yasa zuciyata ta k'ara narkewa sonsa.

Ban sake cewa komai ba na fice, a maimakon ya shigo motar ya bini saiya barta nan ya biyoni a k'afa sai babban titin muka samu napep na shiga kud'i masu yawa ya bawa mai napep d'in 'yar tafiyar da in tayi tsada a kaika a 100 aiko mai napep sai washe baki yake yana zuba godiya, niko dad'i ne ya mamayeni dan nasan lokacin bud'awa nane yazo nayi babban kamu, daga haka muka wuce.

Muna isa shima mai achaba na isowa dashi kallon mamaki na bishi dashi, murmushi ya sakar min "u deserve more than dis princess, a kanki nasan so, princess I love u wit all ma heart, hmm love at first sign ashe haka so yake?" Murmushi nayi dan a gaskiya magan ganunsa sunyi tasiri a raina sab'anin ya Sayyadi da bai iya komai ba sai zan kula dake zan kula da addininki da zan kyautata mu'amalar mu shikenan zancensa ba wani

Please Login or Register in order to submit comment