Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukaje a duniyar media da sunan zamuyi aure haka suka koma da sunan angon ya rasu, nasha ta'aziyya a wannan lokacin Wanda har yanzu wasu nakan yi....wasu kuma sai cewa suke aiga irinta nan Allah ya nuna mana Isar sa, kai kowa ma da yanda yake cewa....

Yauma kamar kullum mun fito daga schools Real Fareedat ta isheni da naci akan bana zuwa gidansu mitar ce ta isheni dan yanzu na dawo silly girl ko yawan surutu banaso, ko a schools kallon miskila ake min dan ba ruwana da kowa....

Ke nidai muje amma fa dan my son dan ina missing nasa, kema da k'eta shine bakya zuwa dashi, na fad'a bayan mun shiga motar, a car d'ina ce so nike driving, shima slowly kamar mai tsoron sitiyarin...

"Tab lallai yau Hanif ya taimaka mana za'a je mana saboda shi, whatever mun gode a hakan ma" nidai ban tanka ta dan banajin maganan hakan yasa itama taja nata bakin tayi mui(shiru).

A harabar gidan muka samu Yaya Khaleel tare da wani mutum da alama friend d'insa ne a yanayin yadda naga suna fira kad'ai ya nuna, aiko Hanif dake hannunsa yana ganin mu ya sheko yana mana oyoyo, sama na d'aga sa ina masa wasa yana dariya tare dayin gwarancinsa, sosai nakeson yara shiyasa yaron ya shiga raina sosai, haka 'ya'yan su Aunty khadija musamman mu'azzam Wanda nake ganin kamar sa da ya Sadeek d'ina......


Gaisawa mukayi dasu Yaya Khaleel sannan muka isa ciki, dan yanzu sosai muke shiri da Yaya Khaleel tun rasuwar Yaya Sadeek yake tausaya min da Jana a jiki, but still in nayi misbehave zai min fad'a ya nunan banyi dai2 ba sai yanzu na gane Ashe ko acan baya bawai sona ne bayayi ba son kenan Ashe, gashi kullum naga fotunan mu da yaya Sadeek sai naji ba dad'i ban kyauta masa ba dan nice na nace sai munyi....

Bayan magrib zan wuce Yaya Khaleel yace yana son magana dani, falonsa na samesa "Na'eemah dama maganar akan wancen friend d'ina da kika ganmu dashi dazu ne" dumm k'irjina ya amsa tun bai fad'i komai ba game dashi, k'asa nayi dakai ba tare da nace komai ba, yaci gaba.

"Sunan sa Umar amma anfi sanin sa da Farook, a zahirin gaskiya na dad'e da sanin sa, tun da na fara lecturing yanzu kinga 3years banda abokin da ya wucesa kaf school d'in nan ke har ma cikin gari tunda na rasa Sadeek" hawaye ne suka zubomin dan ya tunamin da Yaya Sadeek d'ina, Wanda kullum naji an kira sunansa saina zubar da hawaye, ina nema masa gafarar Allah..

"Baida matsala Na'eemah nasan halinsa sosai, sonki yake kuma na gaya masa komai game dake in har kin amince saina bashi damar ya ganki kinga in yayi miki alhmdllh in bai miki ba saiya hak'ura, amma fa ki sani dole zakiyi aure ko ba yanzu ba dan shine kimarki, kuma ki sani Sadeek ya riga ya tafi bazai tab'a dawowa ba, kiyi tunani mai kyau sannan ki nemi shawarar momma, ki kuma yi addu'a kinji k'anwata?" Tau zanyi inshaa Allah, abinda na iya fad'a kenan sannan na tashi na tafi jiki ba kwari...

Kamar yadda Yaya Khaleel ya bani shawara haka akayi, nayi addu'a Sosai sannan na nemi shawarar Momma, bayan sati biyu yaya ya Sake tuntub'a ta da zancen, ba nida option daya wuce na bashi damar zuwa...

Ta'aziyya itace abinda Farook ya fara yimin Wanda hakan yamin dad'i, a yanda na fahimceshi yana da barkwanci da saurin sabo, kuma yanada kirki kamar yadda Yaya Khaleel ya fad'a, ba laifi kyakkyawa ne mashaa Allah.

Hakan yasa naji zan iya sonsa zan iya auren sa, koba komai nima hankali ya kwanta, aiko ba b'ata lokaci akayi komai aka gama aka saka time dama abin kowa ke jira kenan..

Lokacin da nayi masa maganar yin *pre wedding pics* kai tsaye yace wannan ai bidi'a ne kuma shi yana kishin matarsa, in fact dai bai amince ba, ban son fitina hakan yasa nima na hak'ura.....


*Rana bata k'arya........*


Anyi biki cikin aminci na tare gidan mijina, dake unguwar hotoro Muna zaune cikin aminci, soyayya ba kalar wacce bana gani gurin Farook tarairayata yake kamar kwai...

Saidai Abu biyu da nayi la'akari yanada sune zafin kishi, da kuma zuciya amma akwai gaskiya dan komai nasa gaskiya da gaskiya ne, zai fad'a maka ita koda zaka kashe shi ne, fita kuwa kota mak'ota ce saina sanya nik'af sai gani nida nake kiran Real Fareedat matar ladan nina zamo ta liman gaba d'aya ....

Ina cikin kitchen dawowa ta kenan daga school inata sauri na had'a abinci dan nasan habibty na ya kusa dawowa...

"Na'eemah!"
"Na'eemah!!"
"Na'eemah!!!"

Saida na tsorata da kiran har ina rikicewa ina saka ludayin miya cikin dustbin, har nakai k'ofa na dawo rikice na kashe gas d'in, duk na rud'e jin yadda Ya Farook ke kwala min kira cikin tsawa, na manta when ya kirani da Na'eemah saidai baby Nah, lallai akwai abinda yake faruwa, cike da tunani na isa parlon...

Tsaye yake rannan had'e kamar an aiko masa da sak'on mutuwar uwarsa, sai kai da komo yake yana huci, lafia dai habibty? Nace jiki a sanyaye..

Wata uwar harara ya watsa min saida hantar cikina ta kad'a sannan ya mik'omin wayar sa tare da fad'in "meye wannan?"

Zaro ido waje nayi, jikina na rawa nace

Um...am.. *pre wedding pics* d'in mu ne da mukayi da Yaya Sadeek kafin ya rasu..........













_🤦🏽‍♀ sai kuna hak'uri dani wlh am too busy on process, ga kuma patients da nake da, pls Ku tayani addu'ar samun nasara da kuma samun lafiyar Mamana, nima am eager to finish it Allah🤸‍♀🤸‍♀🤸‍♀#1love guys😍#_












💄Meryerm Abdool💄
[12/16, 9:50 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍










*Hattara mata* ❗

*Daga lokacin da kika ga namiji yana Neman ya yi shashanci da ke iskanci ko maganganun wofi ko ya rika Neman yaga wani Abu na jikinki ki tabbata karya yake ba sonki yake ba yana boye wata manufa a ransa*

*Malam Ahmad Tijjani yace cikin wani karatunsa "Babu soyayya ga duk wanda Zai nemi Neman ganin tsiraicin ki, wallahi babu soyayya bazai ta6a yadda ayiwa kanwarsa ba haka".*

*Duk lokacin da namiji ya gurbata miki tarbiya to illar da Dana Sani tafi yawa akanki ke aka fi cuta*

*Mata Ku yi hattara, Ku ji tsoron Allah Ku tsare mutunci ku,don samu rayuwa me albarka da zuri'a masu albarka.*







*_Allah sarki su Abdool 'yan kaciya😆☺ Allah ya fitar lafia ya baka lafia mai amfani👏🏻#love u much son😍❣# Abdulmajid_*👌🏻






*Going 2 close d chapter...one more 2 go....*🤗






*29*







Kallon renin wayo yamin tare sake zubamin harara " imaging ke yanzu ko kunyar fad'a bakiji ba, kin rungume wani k'ato can daban wai kuma kuka nunawa duniya da sunan zakuyi aure! To kunyi auren yanzu dashi? Hmm a naki tunani wannan shine wayewar?" 'Yan yatsun hannunsa ya tank'wasa da k'arfi yana cije lip nasa na k'asa, tare da girgiza kai idanunsa har sun fara canja launi "kin cuceni wallahi, na d'auka ke wayayyiya ce nutsattsiya ashe ke limamiyar kwararo ce, barauniyar hanya, ashe saida kuka gama sheke ayarku, Allah ya nuna maku abinku ya amshi abokin shashancin naki, shine nina d'auka a tunani na na d'au abin kwarai ashe gaibu ce, mai wayewar zamani irin ta yahudawa" cikin razana na d'ago idanuna dake cike tab da hawaye, dan da zafi yake maganganunsa ransa ya riga da ya gama b'aci gayamin magana yake son ransa, zuciyata sai k'una take musamman ma yadda yake had'a wa da ya Sadeek da baiji bai gani ba, komai ya faru nice sanadi niya kamata na d'auki komai bai kamata yana had'a wa dashi ba Wanda ko duniya bashi a yanzu gashi akan son raina dana sakashi a ciki ana dangantashi da d'an iska, mutumin da koni bai cika so ina tab'a shi ba ko shiga jikinsa.....

Murya na rawa cikin kuka nace amma dai kasan a budurwa ka sameni kafi kowa sanin haka, kuma nina yi laifi ni kad'ai ya kamata ka zaga dan nice keda alak'a dakai amma ka dena saka Wanda baya raye dan shi baisan komai akai ba...

"Hehehe!" Yayi wata dariyar takaici wacce tafi kuka ciwo, dan shima sosai idanunsa suka kad'a dan dai yanada zafin zuciya ne yasa bai zubu k'walla ba "taya zansan haka kuwa, waya sani ko anyimin surkulle ne, tunda dama idanunki a bud'e suke, Ai dole na sako abokin shedanar naki dan dashi kuka had'u kuka cutar dani" yana gama maganar ya shige bedroom d'insa kamar iska.

Innalillahi wa'inna ilairrajiun kawai nake maimaitawa tare da silalewa na zube a carpet tare da dafe kaina mai neman rabewa gida 2, wannan wace irin musiba ce, abinda ban d'auka a matsayin komai ba gashi yana Neman tarwatsamin rayuwa ta...

Nan na dab'e tsawon lokaci har aka kira magrib ina gurin ina saka da warwara, shima sai lokacin ya fito da alwala zaije masjeed ko inda nake bai kalla ba bare yasan Allah yayi wata ni a nan, ya wuce abinsa, jiki a sab'ule nima na mik'e don gabatar da sallar, na roki Allah sauk'i dan dai abin ya bani tsoro dan a gaskiya yanzu ina matuk'ar son Farook dan yana da qualities na aso shi don su, dan lokacin nan dai har naji na damu da abinda ya faru, musamman ganin yadda ya d'auke wuta nasan ba k'aramin fushi yake ba dole na kawo gyara a wannan lamarin tunda nice mai laifi...

Addu'a sosai nayi sannan na fesa wanka tare da sheka kwalliya, dinning na gyara tare da feshe gidan da k'amshi kamar kullum...

Saidai me ina zuwa Zan kirashi naji yasa ma k'ofar tasa key, turus na tsaya ina mamakin wannan sabon salo, daya b'ullo dashi, nayi knocking har na gaji yai banza dani, dole na hak'ura na koma d'aki nayi kuka har na gode Allah, dan ban sab'a ba, tunda na shigo gidan kullum cikin tarairaya ta da sakani a jiki yake yasa nayi sabo dashi matuk'ar sabo, amma yau *A dalilin pre wedding pics* mijina yayi min kaura ya barni da kewarsa, ganin kuka bazai min maganin komai ba yasa na Mik'e na d'auro alwala tare da komawa gurin mai duka....


Wasa-wasa saida muka had'a sati kafin na samu na shawo kansa, da ban hak'uri da kwantar dakai da ban baki da nuna nadama na da komai sannan ya hak'ura muka dawo normal, shima dai ba kamar da ba, da dama dai.....





*************





"Wow! Lailah Mar'uff?" Wata matashiyar budurwa ta fad'a cike da zumud'i tana tunkaro inda nake tsaye, fitowa ta kenan daga cikin mota ya Farook ya kawoni bikin wata cousing d'inmu, ina shirin zagawa ta gefen sa na bashi bye peak wannan yarinyar ta katse ni da kirana da wannan sunan Wanda bansan mai shi ba....

Da kallon mamaki na bita, ita kuma sai wasar baki take tana k'ara tunkaro inda Nike...

"I can't even know how I feel happy Allah, wallahi even in dream banyi tsammanin zan ganki ba sai gaki a fili na ganki wayyo am so glad" ta fad'a tana k'ok'arin rungumeni cikin zumud'i bayan ta iso inda Nike..

D'an zamewa nayi tare da cewa ya haka baiwar Allah? Murmushi ta k'ara yi "am so sorry wlh tsabar farin ciki ne, Ashe marubuciyar nan da gaske ne dama take littafin true life story ne Ashe gaske ne gashi kuwa Allah ya nuna min ke, ina hubbyn naki Mar'uff, gaskiya soyayyar Ku ta burgeni zanzo miki har gida ki kowaya min pls accept me" ta sake fad'a tana had'e hannayenta alamar begin...

Nidai tsaye nayi gun kamar wacce aka dasa dan ban fahimci abinda take magana akai ba, amma da alama abun nada alaka da novel dan naji tace marubuciyar littafi tace true life story ne, da sauri k'irjina ya harba kaddai novel cover akayi da pics d'inmu, aiko in hakane da an cuceni, cikin sanyi nace mata kiyi hak'uri sister bansan me kike magana akai ba, niba Lailah sunana ba ban kuma San wani Mar'uff ba..

"Haba kece Allah, Bari kiga" ta sake fad'a tana d'auko phone d'inta a jaka, cikin mintina kad'an ta kamo pics d'in tare da nuna min "kiga kina nufin kice ba kece wannan ba?" Ya Farook dake tsaye gefe ya rungume hannunsa a k'irji, yana kallon mu, takowa yayi zuwa inda muke, tare da amsar wayar a hannuna ya duba pics d'in, nice tabbas, *pre wedding pics* d'inmu ne da Ya Sadeek akayi editing anyi novel cover nice a matsayin Lailah ya Sadeek a Mar'uff, hawaye ne suka zubomin inata addu'a a raina tare Neman tsari da wannan musibar daketa kunnu kai a gareni, ganin yanayin fuskar Farook tuni hanta ta ta kad'a dan yau nasan na kad'e har ganye sai abinda Allah yayi kawai...

"Kin gani ko? ai kece, dan Allah malam ba ita bace? Ta tambayi Farook, nidai ina tsaye sai zarar ido nike, duk addu'ar da tazomin a baki yi nake, dana sanin d'aukar foto kuwa nayi yafi cikin kwando...

Smiling irin na yake yayi " itace amma abinda nakeso ki gane shine wannan foton nata ne da saurayin da sukayi niyyan aure shine sukayi *pre wedding pics* to sai Allah yayi masa rasuwa, yanzu dai nine mijinta, sannan wannan da kika gani had'a wa kawai akayi amma is not Real, anyi editing ne kawai ita sunanta Na'eemah ba Lailah ba kin gane just it a fiction" sororo nayi ina kallon yadda yake mata bayani kamar ba abinda ke damunsa..

"Ayya sorry, wlh na d'auka abin is real but pls accept my apologies, and gaskiya ke kyakyawa ce, INA sonki Am Nusaiba by name" ta fad'a tare da mik'o min hannu, nima yak'en nayi ur always welcome dear..

"Muje ko?" Yace nan mukayi sallama da Nusaiba bayan ta amshi no ta, bikin da ban isa ciki ba kenan, muka juya muka koma, a mota sai kame-kame Nike, shiko gefe ya maida kansa tare da shan toka sosai inason yin magana inajin tsoron mai zai biyo baya da k'yar nace dan Allah kayi hak'uri, wlh ba laifin na bane, kuma wallahi Allah ya isa na da wannan writer ko wacce tayi editing d'in, sai lokacin ya watsomin mugun kallo.

"Kanki ya kamata kima Allah ya isa ba writer ba ko wacce tayi editing, da baki d'auki foton kin d'ora a media ba, da akwai Wanda ya isa ya sameki har gida ya d'auki foton ki yayi editing? Mtssss ashamed of ur self nonsense" nan dai yata fad'an sa Niko dole na daure zuciyata na shiga bani hak'uri nan ma da k'yar da lallami na samu ya hak'ura....


*********



Jingine nake da motar mu dake bakin shopporite mun yi provisions ne yace naje bakin mota na jira shi kafin a gama total...

Sai kallon yadda mutane keta harkokin gabansu nike, can gefe gurin soft drinks na hango wani guy cikin shigar gayu irin on top dinnan har da sarka da 'yan kunne, yana sipping fanta cikin kwanciyar mind, girgiza kai kawai nayi nace a raina yanzu haka idan aka bibiya musulmi ne, kai wannan rayuwa...karaf idanun mu suka had'u, saurin d'auke idona nayi.....

"Najwa beauty!" Naji an fad'a daf dani, wa zan gani ba wannan guy d'in ba, dan razana nayi tare da duba gefena ko zanga Najwar, ba kowa a gun..

"Am so glad 2 meet u Najwa, ba yadda ban ba da writer of that novel akan ta had'a ni dake tak'i wai ita wallahi bata sanki ba had'a wa kawai fans d'inta sukayi Ashe k'arya ne ta sanki k'i kawai tayi" ya Rahman itace Kalmar da na fad'a wannan wace irin musiba ce..

"Pls Najwa took 2 me, wlh I really love u for d very first day I saw ur picture.."

"What do you said! U love her? "Naji muryan Farook ta fad'a, shikenan anyi an k'are anyiwa mai zane d'aya sata, na fad'a cikin raina tare da juyawa na kallesa a razane..

" yes our Bros, I truly love her wit all my heart pls help me, wlh tun ranar da naga pics d'inta am not in d mood" yace da Farook..

"Tassss!" Farook ya wanke masa fuska da mari" my wife! Zakace kanaso dan ka kai dan akuya wawa." Ur wife Sir, am very sorry wlh ban sani ba" yana gama fad'a ya there..
Dafe kansa yayi da duka hannayensa biyu , pls habibty kayi..... "Shut up!" Ya fad'a cikin tsawa idanunsa jajir yana huci "am tired wit ur trouble, ur a always try to make me angry, kije gidanku saina nemeki.." Pls....."shiit! No more word na gama magana.... "

Yana gama fad'ar haka ya shige motar sa tare da janta da gudun tsiya, ya bad'eni da kura...

Hannu na Dora aka nace wayyo yau naga ta kaina naga bala'i *a dalilin pre wedding pics.........*





















💄Meryerm Abdool💄
[12/19, 1:33 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍









*_TSOKACI....._*




*Kamar yadda wasu ke ganin naja ragamar littafin nafi d'aura laifin kacokam akan mata, to abinda nakeso Ku gane idan akace magana ta son burge wa da nuna na isa da son k'yale-k'yali tofa mata ne kan gaba dan kowa yasan yadda dama su mata an haliccesu da son k'yale-k'yali, so indai akan _pre wedding pics_ to zakaga majority daga mata yake samun asali sune masu k'arfafa wa akan sai anyi, kuma idan akazo aka samu matsala sune zasu kwana a ciki, dan ita mace 'yar kunya ce yayin da shi kuma namiji komai yayi ado ne, misali zaku had'u Ku aikata b'arna keda namiji, ko ma shi ya yaudareki amma sunan ki ne zai b'aci, kece zaki zama abin k'yama ki kasa auruwa, shi kuma ko gobe yaga wacce yake so da gudu za'a bashi dan shi komai yayi ado ne, amma abin takaici ko yanayin d'aukar foton muka kalla, namiji zaiyi shigar kamala ya suturce jikinsa, amma ita mace ta matse ta fitar da duk wata sura ta jikinta, ita da akace komai nata al'aurace amma itace kan kaga gurin tubarruj(tsiraici) to ta ya bala'i bazai yawaita ba b'anna taci gaba da faruwa, a social media fa za'a zuba fotunan inda kashi 70% cikin 100% na mutanen duniya duk suna nan, Allah d'ai yasan iya adadin wad'anda zasu kalla suyi sha'awarki to ta yaya bala'i bazai sameki ba tunda kinyi karan tsaye akan dokar Allah🤦🏽‍♀ Mata! Mata!! Mata!!! Kuyiwa girman Allah mu daure mu tsare mutuncinsu mu da kada mu manta fa mune masu tarbiyar al'umma idan mace d'aya ta gyaru tamkar wasu masu yawa daga al'umma sun gyaru ne, pls mu daure mu cire son zuciya, da kwad'ayi, Allah yasa mudace duniya da lahira👏🏻*





*_Alhmdllh komai yayi farko tofa zaiyi k'arshe in banda ikon Allah, masoyana masu bibiyar rubutu na bansan da wane baki zan gode muku ba, dan abin alfahari ne ka zauna kayi d'an rubutu wasu su karanta ina fatar kun d'auki darasin ciki kun yasar da kurakuran ciki☺ nagode sosai my true friend, Allah ya barmu tare har abada🤝 cikin aminci🤗_*#double love #👌🏻❤❣












*Last Page 30*











Na dad'e tsugune a gurin ina kuka, mara sauti, ganin hankalin mutane ya fara zuwa kaina ne yasa, na tashi na isa bakin titi ga kaina dake barazanar rabewa gida biyu tsabar ciwo da yakemin ga juwa dake d'ibata, cikin sa'a na samu adaidaita, gayamai nayi sai munje can zan bashi kud'i, dan ko bag babu a hannuna tana motar....

A parlour na samu momma jikinta naje na zube tare da sakin wani marayan kuka "ke lafiyarki? Keda waye? Ina Umar d'in?" d'agowa nayi da niyyan yi mata magana naji kaina ya matuk'ar sarawa, tare da ganin wani irin duhu luuu na koma jikinta na zube....

Ban k'ara sanin abinda ya faru ba sai farkawa nayi na ganni gadon hospital ana min K'arin ruwa, ashe suma ne nayi, ana haka ne wata nurse ta shigo tare da tambayan kona farka, ganin na farka ne yasa tamin sannu tare da komawa ta kira doctor...

Bayan ya gama dubani ne yace ya Khaleel ya same shi office yai mishi bayani, minti kad'an sai gashi ya dawo yace ma momma "Ashe shigar cikine sannan yace tana cikin damuwa tana yawan samun bugun heart, Wanda a halin yanzu yake barazana ga rayuwar ta data babyn" kallona yayi "Na'eemah me yayi zafi haka meye damuwarki?" Tunda naji batun cikin na samu kaina cikin farinciki nasan inshaa Allah zai zamo samun maslaha tsakanina da masoyina a yadda yake son yara nasan zaiyi farinciki, maganar bugun zuciya kuma, aini na d'auka za'a same ni da hawan jini ko fiye da haka.... "Aa Khaleel mubar wannan maganar har mu koma gida yanzu dai kira Umar d'in ka gaya masa halin da ake ciki in yaso daganan in yazo sai a zauna gaba d'aya" momma ta katse sa.

Nan take ya shiga kiransa amma wayar bata zuwa a kashe take, haka yayi ta kiran layukan sa duk a kashe, nan take hankali na ya k'ara tashi nasan ba k'aramin fushi Farook yayi ba, tun da har takai ga ya kashe wayoyinsa.....




*************



"Na'eemah meye ainihin abinda yake faruwa ne wai"? Momma ta tambayeni, k'asa nayi dakai sannan na shiga gaya musu duk abinda ya faru tun daga ranar da Farook ya fara zuwa da *pre wedding pics* d'inmu a wayar sa har zuwa yanzu da yace naje gida sai ya nemeni...

" u see! Ai kinga irinta shiyasa tun farko nayita gujemata hakan amma tak'i ji, haka kuma kuka goya musu baya, to yanzu wa gari ya waya, Sadeek dai ya riga tafi, dama da mai rai ake rigimar duniya, kuma ni bansan baki gayama Farook game da fotunan ba, aida nida kaina zan gaya mishi" yaya Khaleel ya fad'a...

"Wallahi Khaleel ban tab'a tunanin haka abin zai zama ba aida nida kaina zan hana, yanzu dai kuskure an riga an yishi yanzu kawai a nemi hanyar sulhu" momma tace cikin jimamin abin..

"Hakane momma bari yanzu naje can gidan nasa, sai azo a zauna a fahimci juna" tau kayi maza, bari na kira Dadyn ku, sannan na gayama su Hajia halin ake ciki(cewa da mommyn su ya Sadeek) nidai ina zaune inata addu'ar Allah yasa ya hak'ura yazo d'in a sasanta...

Haka su mommy sukazo anata jajanta abin, hadda su aunty khadija na gidan, har su Abba sukazo yaya Khaleel bai dawo ba, sai can zuwa dab da magrib ya dawo yace yaje gidan a kulle, hakan yasa ya wuce family house d'in su, yayi musu bayani, anan ne suke gaya masa cewa tafiya yayi amma bai gaya musu komai ba game da wannan lamarin, dan basu nan ma yace naje gida ba, amma zuwa gobe zai dawo inshaa Allah zasuzo sai a zauna akan zancen, hak'uri suka bayar akan abinda yayi dan sun san zafin zuciyarsa...

Haka muka hak'ura, kowa ya tashi yaje yai Sallah, ranar dai ban samu na runtsa ba, Allah kawai nake kaiwa kukana tare da Neman yafiyarsa da gafararsa...

*Washe gari....*


By 12:00pm babban parlour mu ya cika, da dimbin jama'a iyayena iyayen yaya Sadeek, iyayen Ya Farook, da kuma yaya Khaleel, bayan an gaggaisa ne, kawun Ya Farook yace "Muna k'ara Baku hak'uri game da abinda ya faru abin Farook Yayi, shima dai in banda yana dawainiya da zuciya, yarinyar nan ta nuna mishi tayi kuskure ta bashi hak'uri to mai zai hana ya hak'ura, ai yama yi sa'a da 'yar arziki wasu yaushe ma zasu gane sunyi kuskure, bare su gane suna cikin musiba su nemi yafiyar Allah, wlh ka rage zuciya da wannan zafin kishin sai kana hak'uri zaman aure saida hak'uri"

"Ai babu komai Alhaji, shima yana da gaskiya dan gaskiya irin haka ba dad'i, wannan wani bala'i ne daya b'ullo mana a wannan zamanin ya kuma zama ruwan dare, yaran

Please Login or Register in order to submit comment