Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

had'in Kai sosai, nice mace ta farko da aka fara haihuwa a gidan duk yayyina maza ne, hakan yasa na taso a sangarce saboda yadda kowa ke nan nan dani, Yaya Shahir d'ane ga wan Baba na kuma na farko a gunsa kamar yadda na kasance ta farko a gun iyayena, Yaya Shahir na matuk'ar kaunata duk cikin yayyi na yafi kowa nuna min k'auna duk da kowa na gwargwadonsa saidai ya Shahir ya musu fintinkau dan komai nace inaso sai ya kawomin shi, lokuta da dama Hajia Inna na masa fad'a akan hakanan take cewa kada ya sabamin da komai na nema a rayuwa saina samu dan kuwa mace ce ni kuma gidan wani zanje idan na saba da hakan wahala zansha nan gaba dan ba komai ake nema a samu ba a rayuwa.

Sai dai yay murmushi kawai yace "ai Hajia wannan bazai sangarta Mardiya kuma ma inshaa Allah nine mijinta ba zata wahala ba akan wannan Inshaa Allah" nikam a lokacin bamma san meye so ba, bare wani miji, amma dai nasan ina son Yayana saboda yanda yake kula dani da nunamin k'auna.

Duk ranar da Hajia Inna tayi irin wannan maganar fushi nake da ita na koma shashen mu, amma bazan iya kwana can ba nake dawowa saboda yanda na shak'u da ita, sai cewa take 'yar nema waya baki hak'uri kuma? Shima dai Yaya Shahir muddin yana gida to a sashen yake firar sa da komai nasa, mune dai tight friend na Hajia Inna, mune 'yan d'akin ta musammam ni da komai nan nakeyi wani sa'in sai in had'a sati banje sasan mu ba, saboda ban wani sakewa a can dan yadda mamata kemin kawaici irin na 'yan fari.

A haka mukaci gaba da rayuwar mu cikin jin dad'i da farinciki.

Kamar yadda kuka sani garin Kano garine da ya gadi kasuwanci inda mafi akasarin mazauna cikin 'yan kasuwa ne, to muma dai gidan mu abinda aka gadar mazajen mu kenan, duk wanda ya gama Karatunsa a maimakon ya tsaya jiran aikin gwamnati saidai su fad'a harkar kasuwan gadan gadan, dama tun suna yara sun San kan harkar dan suna zuwa kasuwar dama can...



*********



Yaya Shahir ya girman dani ne akan sonsa, koda na fahimci meye so to a kansa na tsinci tawa soyayyar, Wanda hakan ba k'aramin dad'i yayi wa iyayenmu ba musamman Hajia Inna da dama shine babban burinta musamman yanda taga Shahir na nunamin k'auna tun yarinta har girma...a cewarta shine kadai zai iya dani tun da dama can shiya b'ata ni.

Ganin wayoyi sun fara yawaita da yadda nakejin labarin social media irin yadda ake samun novel cikin sauk'i ba tare da ko sisin mutum ba yasa na gayama ya Shahir inaso ya siyamin waya, hmmm fad'a da cikawa a ranar Yaya Shahir ya kawomin wayar nan kirar gionee p5 da kanshi ya bud'e min WhatsApp da insta, Whtpp, Facebook yamin sub na monthly.

Samuwar social media a gareni itace stage na farko daya fara tab'arb'arar min da rayuwa, banda aiki kullum ina online Neman sabon novel, a insta kallon update pics da aka turo na *pre wedding pics* daga nan zuciyata ta fara kwad'aituwa Wad'annan fotunan da kowa keyi in zaiyi aure nima ma fara sha'awar yinsu ganin yadda mutane keta turo nasu ana yaba musu da zuzuta kyan su naga nima ai kyakyawa ce, shima ya Shahir haka dan haka nima sai nayi *pre wedding pics* kamar yadda kowa keyi haka na k'udurce a raina....

Sosai Hajia Inna ke fad'a akan wayar dan ta maidani busy always ina d'aki, dan aikin da nake mata ma na daina, 'yar haddata da islamiyya duk na watsar sai fa idan su Abba nanan nake zuwa ko kuma idan tamin Jan ido nake tafiya ina zumb'ura baki ala tilas an takura ni....

Yaya Shahir ne ya shigo yana nemana bayan sun gaisa da Hajia ya tambayeni ta ni "yo ni ka tambayeni wancen mashiriri ciyar yarinyar bayan kai ka b'ata ta da wannan abin nasarar wanda kullum tana tare da ita kamar ajali" tsaki taja "nidai ina jiye maka wannan tabatarar da kake biyemata kada ta zamar muku matsala nan gaba"

Yaya Shahir Sam baida hayaniya murmushi nan dai yayi "Hajia Inna ki kwantar da hankalink bafa abinda zai faru inshaa Allah, ai itama kuruciya ne data girma ta mallaki hankalinta zaki ga duk ta daina" ya fad'a yana shigewa cikin d'akina.......







Manage pls munata biki ne





๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜







```An karb'o daga Baban Amri ko Baban amrata sufyanu d'an Abdullahi assak'afi(R.D) yace nace da Manzon Allah (S.A.W) ya ma'aikin Allah ka gayamin wata kalma a cikin musulunci Wanda bazan tambayeni kowa ba face kai, sai yace kace kayi imani da Allah sannan ka tsayu akan kalmar(Arba'una hadith)```



๐Ÿ˜ _Namesake Maryam Ismael(muhphat) here is ur page I really appreciate ur love and care ur namesake love u too_ ๐Ÿ˜˜โค








*17*





Bashi ya fita gidan ba saida aka kira zuhr ya tasa d'ansa gaba suka wuce masjeed gwanin sha'awa, bayan fitar ce Safina ke gayama na wannan mutumin da yake yiwa yaransa tahfith ya Samar masa gurbin karatu a madina kuma har ita zasu wuce tare dan itama tayi nata a can bayan biki da sati biyu zasu wuce, sai a yanzu rayuwar Safina ke burgeni ada ina ganin ta cuci Kanta ina mata kallon bak'yauniya Ashe nice na cuci kaina gashi yanzu ta samu successful marriage sai alkhairai take gani a ciki saboda tun farko sun tsarkake zukatansu sun yadda da aure a amatsayin sunnah ce ta manzon tsira, kuma sun tsara abin su a turbar islama, nayi kaico da halina dama masu hali irin nawa....


Yau ma kamar kullum na taso daga islamiyya wacce na shiga a nan unguwar su Adda Ainau, ta rana ce ta matan aure hakan yasa na sayi nikaf nake b'oye kaina a ciki saboda yawan surutun mutane a kaina na killace kaina duk da hakan wasu sai sunyi, niko Sam basa gabana dan komawa ta islamiyya ba k'ara min dad'i yai min ba, na samu nutsuwa sosai dan nayi nadama ta gaskiya ga ilimi da wayewar kai irin na addini Dana samu sosai, sai a yanzu na fahimci ba abinda yakai shigar mutumci bada kariya da tsare mutumci kai kanka zaka fijin kanka safe idan ka killace jikinka ga kare lafia Jikinka daga rana da sauran abubuwa da ba zaka fahimci hakan ba sai ka zamo ma'aboci shigar kirki....

Dai2 zan shiga gida ne naji muryan wani a bayana yana min sallama, sanin muhimman cin amsata ne ya tilasta ni tsayawa na amsa, ba tare dana juyo ba, dan a tunani na irin 'yan cin fuskar nan ne, ina niyyar shigewa ya k'ara cewa.

"Malama dan Allah ki daure ki aramin kad'an daga cikin lokacin ki, na gaya miki abinda nazo miki dashi" k'irji nane ya hau bugawa ba abinda ya fad'omin a rai sai Aahil, shima anan gidan ya fara tarata, Allah da ya fad'a yasa na tsaya tare da Cewa ina jinka bawan Allah, amma da gaske hankali ba'a kwance yake ba..

A ido mutum ne cikakke mai kamala, baiyi kama da mutumin banza ba, koda yake mugu baida kama..."a gaskiya sonki nake kuma soyayya ta gaskiya ta aure " abinda naji kenan daga bakinsa, a dan tsorace na kallesa dan na gasgata shine yai maganar, murmushi yayi "kada ki tsorata dani Fateema bazan cutar da ke ba" mamaki ne ya k'ara kamani ko ina yasan sunana oho..

Naji na kuma gode saidai ni ban dace dakai ba kaje ka nemi dai2 kai nagode da k'aunarka, na fad'a hawaye taf idona sannan na juya da niyyan shigewa kuka na shirin sub'ucemin.

"Aa zuhrah kada ki juyawa ni'imar Allah baya mana, idan kika ce haka kenan, duk Wanda ya sab'awa Allah ya kuma yi tuba mai kyau bazai samu rayuwa mai kyau ba? Kada kimin haka pls ki bani dama nayi wannan aikin alkhairin..."




**********




Wannan shine tak'aitaccen tarihin had'uwata da Tahir mutumin da ya canja rayuwa ta ya soni a lokacin da nake ganin na rasa damar samun so na gaskiya, daga k'arshe ya aureni ya killace ni, Tahir mutumin kirki ne tsakanin sa da Aahil kamar ruwa ne da wuta, shine silar zuwana Kano, yana da mata da yara 4, muna zaune lafia dashi da matarsa da 'ya'yanmu masu tarbiya, na samu canjin rayuwa daga rayuwar k'unci zuwa ta jindad'i a gidan Tahir ya rik'e ni da amana da gaskiya, kamar yadda nima na rik'e aure a matsayin bautar ubangiji, nake iya k'ok'ari na gurin kyautata zamantacewa ta da kowa, ya samar mini gurbin karatu nayi karatu a yanzu haka ni nurse CE...

Daga k'arshe na fahimci ashe ba rayuwar da tafi rayuwar bin Allah da sunnah Manzon zama daidaitacciyar hanya, wacce ke cike da nutsuwa da albarkar Allah, dan rayuwa ta ta isheni buga misali, bawai dan mutum ya aikata kuskure ba shikenan rayuwar ta ta k'are, aa muddin zai tuba, tuba ta gaskiya rahamar Allah nada yawa sosai zai yafe masa kuma ya inganta rayuwar sa..

Kallon su tayi tana murmushi " me kuke tunani da Aahil Allah zai kyalesa hakanan? "

Duk jikin su ya gama yin sanyi qlau, suka ce meya faru dashi?

A jarida na gani duka ba'a wuce watanni biyu ba, Ashe Aahil dan wani senator ne, wannan 'yar tasa da yake matuk'ar so wasu bata gari suka yi reaping nata 'yar shekara biyar garade uku suka shige ta, tana asibiti rai kwakwai mutu kwakwai..

Kai tsaye nace Allah yayi gaskiya, zina bashi ce...ko a haka Allah ya nuna masa iyawarsa yafi abinda iyaye keji idan ya b'ata musu 'Ya'ya...

Tau kunji kalar tawa musiba *A dalilin pre wedding pics*



Mardiya ce ta taso tazo inda suke tare da dafa Zuhrah "lallai Zuhrah kinga rayuwa...to nima bari kuji tawa kalar musibar.....






_muje zuwa_ ๐Ÿ‡๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿป๐Ÿ‡๐Ÿป










๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜







```Wani mutum ya tambayi Annabi Muhammad (S.A.W) yace ya ma'aikin Allah, idan na sallaci sallolina na farillah guda biyar, na azumci azumin watan Ramadana, na halalta halal na kuma haramta haram, ban K'ara komai akan su ba shin zan shiga aljannah? Sai annabi yace "eh" ma'anar haramta haram shine ka nisancesa, ma'anar halalta halal shine ka aikata shi kanajin halalcinsa a ranka, (Arba'una hadith)๐Ÿ‘Œ๐Ÿป```





๐Ÿ“– *MARRAHA HOME OF NOVELLA* ๐Ÿ“– *ina yinku guys wannan shafin nakune dan soyayyar da kuke nunamin nida my dear raheenat da my parrot Hafsat muna sonku sosai guys, wannan shafin nakune duk wata member ta wannan gidan tana ciki ban cire kowa ba ๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜ #ILVYSM#โคโฃ๐Ÿ’*











*19*





Sam banji shigowarsa ba saboda yadda hankali ya tattara ya tafi gun kallon *pre wedding pics* d'in wata 'yar wani group d'inmu da ta turo Sai kalla nike ina maimatawa saboda yadda fotunan sukayi kyau, ina imaging namu yadda zaiyi chilling dan na fita diri da kyau haka ya Shahir yafi mijinta cikar halitta da haiba, sai murmushi nake ni kad'ai ina hango comments da like d'in da zan sha, lallai daraja ta zata d'aga a social media....

"Mardisha!" Sunan da Yaya Shahir ke kira dashi kenan, ya had'a suna na da nashi, "me kikeyi haka a waya tun dazu inata sallama bakiji ba?"

Da murmushi na diro daga bed d'in, ina fad'in sorry sweet Yaya, wallahi na shagala da kallon wannan ne, na m'ika masa phone d'in dan yaga pics d'in bayan na isa inda yake tsaye daga k'ofa.

Smiling yayi "sunyi kyau" ko kallon kirki baiyi musu ba ya mik'on wayata, nikam bamma kula da abinda yayi ba, sai wani murmushin jindad'i da nayi nace ai Yayana sai namu sunfi yin rocking dan mun fisu had'ewa..

"Namu me kenan? Badai wannan shirmen ba?"

"Haba Yaya *pre wedding pics* d'in ne shirme? Nidai wallahi inaso dan yanzu shi ake yayi kuma sai manyan yara keyi, na fad'a ina zumb'ura baki da b'ata fuska dan naji haushin maganar tasa..

" common Mardisha wannan fa duk shirme ne da tallan kai nikam a gaskiya ina kishin matata bana ra'ayinsa, kiyi hak'uri kinji 'yar k'anwata" wannan shine karo na farko da Yaya Shahir ya tab'a k'in ra'ayina a maimakon nayi lakari da maganarsa na yadda da zancen sa aa sai ma wani botsarewa da nayi INA fad'in.

Ai wannan zamani ne yazo dashi kuma mu 'yan zamani ne mezai hana mubi zamani, kuma da yake maganar kishi waye zai ganni har yace yana sona bayan yasan fotunan na aure ne, nidai wlh inaso kuma idan bai yadda nina san me zanyi(illar biyewa mutum akan ra'ayinsa kenan akan komai dan duk yadda kaso ka dawo dashi hanya daga baya da wuya ya gane hakan)

Duk yanda yaso ya fahimtar dani illar *pre wedding pics* naki ganewa saima fushi zazzafa Dana d'auka dashi..




*********





Tsawon wata d'aya muna zaman doya da manja duk da bashi kad'ai ke azabtuwa da hukuncin nawa ba, ni kaina ina azabtuwa amma na dake saboda kafiya irin tawa wacce Hajia Inna ke kirana da 'Yar takafiri unguwar 'yan mun kakkafe tun ina k'arama ta haka na tashi da wannan kafiyar.

Ganin na kammala secondary ne kuma su Yaya Shahir sun kammala gininsu yasa su Abba tsayar mana da ranar Aure, tare Dana Yaya Nasir da Basir ma'ana mu hud'u za'a aurar a gidan..

Duk da an tsayar mana da rana, hakan baisa na sauka da fushi na ba saima abinda ya k'aru, Hajia Inna ce kawai tasan halin da muke ciki amma data tambayeni Yaya Shahir b'oye mata yayi yace d'an k'ara min sab'anine kuma zai daidaita komai tab'e baki tayi tace "kana dai da aiki kam amma kowa yake ya iya guri ake bashi kuma kowa ya diba da zafi bakinsa" murmushi kawai yayi yace "Hajia kenan"

Duk da haka bata hak'ura ba saida ta tuntub'eni da har zan gaya mata sai na tuna 'Yar da ce itw zata iya b'ata min plan, yasa nace ba komai, bata wahalar da kanta da matsamin ba dan tasan ba fad'a zan ba..

Duk wata hanya da zata had'a ni dashi na toshe ta, dana jishi falon Hajia Inna zan shige toilet na kulle yazo yaita mitarsa ina jinsa yayi ya gama ya fice, kiransa kuwa dama ba d'aga wa nike ba, Text kuma bana dubawa gogewa Nike...

Yau kam mamayata yayi ya shigo min ina bacci zama yayi a gun nidai tashi kawai nayi na gansa a d'akin, d'aure fuska nayi sannan na Mik'e da niyyan shigewa toilet..

Shan gabana yayi "Haba Mardisha game d'in ta isa haka, pls ki Bari mu fahimci juna, kina ganin bikin nan sai matsowa yake amma ke sai k'ara nisan tata kike haba tawa Nine fa Yaya Shahir d'in ki" Kau da Kai nayi, ko gun da yake naki kalla duk da kuwa missing nasa da nake sosai.

Aini Yaya Shahir na fasa auren ka gara tun kaje ka gayama iyayenmu su janye wannan auren, dan bazan auri Wanda baya son farinciki na ba, cikin tsananin mamaki da firgici yake kallona "ya Allah kada kasa wannan mafarkin nawa ya zama gaskiya" ya fad'a yana murje idonsa..

Bafa mafarki kake ma Yaya da gaske na fasa auren ka.

Hmmm lokuta da dama so yakan zama musiba ga mai yinsa dan kuwa soyayyar da Yaya Shahir kemin ta wuce misali duk da yasan illar pics d'in amma saboda son da yakemin da gudun kar ya rasani yasa yace

"Aa love of my life kece rayuwa ta indai akan *pre wedding pics* ne zai sa ki k'i aure na tona amince ayi pics d'in, amma fa sai mun tambayi izinin Hajia Inna dasu Dady" da har na fara murmushi jin kalamansa na k'arshe ne yasa na tsuke fuska nace nikam duk ya gaya musu wallahi ko kasheni zasuyi bazan aure sa ba saidai nabi duniya..

Still dai azabar so da shedan sunyi aikin su "shikenan baby ur wish is my command I agreed wit ur said" aiko bansan lokacin da nayi wani irin tsalle na rungumesa ba inata sambatun murna.....






_still on biki manage_ ๐Ÿ˜˜๐Ÿ‘Œ๐Ÿป










๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜








```Annabi Muhammad (S.A.W) yace "mai kyauta ya k'arb'e ko mai kyauta ya amshe kamar karene yayi amai sannan ya koma ma aman sa ya lashe(husnul Muslim)๐Ÿ‘Œ๐Ÿป```




*_๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ‘Œ๐Ÿป oh๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€ to waini ta ina ma zan fara? In nake ke k'awata ce sai naga ai kin wuce k'awa? In nace ke 'yar uwata ce sai naga kin wuce hakan a guna, to wai ko Aminiya zance? Kai saidai Haniniya ko? To bari dai na tsaya a jinin jikina๐Ÿ™ kece fa dear 'Yar mutan niger wagga shafi nakine dear Raheenat Mahmud Niger, momyn khadija ina yinki 'yar uwata๐Ÿ’ž๐Ÿ’•โฃ_*








*20*






Kamar yadda na tsara hakan ce ta kasance munje munyi *pre wedding pics* bada sanin kowa ba, kuma sunyi kyau matuk'a kamar yadda nake tunani, a ranar jina nake kamar wata sarauniya dan kuwa na samu comments and like wuce yadda nake tsammani a duniyar media, sun saka kaina yayi k'ato har yana neman fashewa, duk group d'in da na duba ba abinda ake sai zuzuta novel d'in tare da zumayen shagalin biki, nikam burina ya cika girma na ya d'aga a social media, na burge mutane dama manufar kenan a *pre wedding pics* labarin aurena ya zaga media tare da nuna zubin halitta da kuma nuna nayi mijin nunawa sa'a...

Tau komai ya tafi yadda nakeso, banyi tunanin iya ina fotunan zasu kai ba, nasan kalar mutanen da zasu gani kuwa? Duk wannan baya cikin tunani na, Yaya Shahir kam bana tunanin ya tura a media, yo ma ko median Kanta ba damunsa tayi ba, inka ganshi kan net toko akan kasuwancinsa ne ko dan labarun duniya masu amfani, amma chat kam nama daina damun kaina akansa dan sai muna tsaka da magana zanga ya sauka, inna kira na tambayesa yake uziri ne ya rik'e sa tun ina jin haushi har na saba, shidai barshi a kira da love text lokaci zuwa lokaci....

Hajia Inna ce na fara nunawa fotunan aiko a ranar naji tsit a bakin tsuntsu dan kuwa tayi mana tatas dagani har Yaya Shahir d'in, inda take shiga banan take fita har yahudawa ta kiramu, to danma bata san an yad'awa duniya ba kenan...

Nice mai tare wa ina cewa ai mu ba irinsu bane 'yan da wad'anda sai ranar aure suke sanin mijin da suka aura ba soyayya ba komai tace "yo ai shiyasa auren mu yafi na yanzu k'ark'o saboda ba harkar yahudanci a ciki lamui ake aure kuma basai idonmu ya gama k'yank'yashewa ba, ba ruwan mu da bidi'ar nan, mu munsan wani hoto ma wai she mema kikace?" Ban Sani ba, nace "yo ai dole cike baki sani ba waike fitsararriya hadda wani mak'alk'ale masa shima sumui kamar na Allah Ashe duk kune ku yanzu ko kunyar d'aukar wannan foton bakuji ba? Koda yake ba laifinka bane nasan duk wannan iyayyar ce da bata laifi gunka ta saka yinsa nasan can wurin shegiyar wayar nan ta gano su" nidai tun ina biyeta har na gaji na tafi na barta nan dashi tanata zuba masa..

Hadda cewa zata nunawa iyayenmu suga abinda mukayi, ya akayi hak'uri ya bata ko tsohuwar mantuwar tata ce ta hana ta nuna musu oho...



*************



Anyi biki bidiri biki na 'yan fari shine biki na farko da akayi a gidan mu so ba laifi anyi rawar gani, kuma an d'an tab'a bidi'a saffa-saffa duk da ni ba'ama yimin yadda naso ba, dan naso a rak'ashe sosai, saidai iyayen mu maza sunk'i bada damar hakan..

Duk wani events da akayi Wanda yayi topping saida na d'auka na tura media d'an kara Jan girma kamar yadda naga wasu nayi musamman 'ya'yan masu fad'a aji a k'asar, banyi la'akari da cewa inda wani yayi rawa ya samu kari wani idan yayi duka zai sha...

Kamar yadda na gaya muku soyayya da Yaya Shahir nasan kun hango soyayyarmu a cikin gidan auren mu, 2 week muka d'auka a gida Yaya Shahir baije ko'ina ba sai gida shima dan gaisuwa kawai, yau kam cewa yayi zai fita gurin abokan sa kafin su iskoshi su mishi tsiya..

Dak'yar na barshi ya tafi dan kukan shagwab'a na tsira masa hadda dire diren k'afafu, sanda yamin wayo sannan ya tafi, bayan fitarsa da 'yan mintuna naji wayata na ring ganin new no ce yasa na mayar da ita kan center table d'in naci da kallona, abu kamar wasa sai kira ake ank'i a daina, ganin za'a dameni a katsemin jin dad'i yasa naja dogon tsaki tare da daga wayar cikin takaici nace wai waye dan Allah keta damuna haka.

"Haba kyakyawa ai fushi ba naki bane"6 mamaki ne ya kusa somar dani jin muryan wani gardi, cikin zafin rai nace kaiko wane irin dak'ik'i ne da zaka kirani ina matar aure, saboda rashin sanin hakk'in aure ko?

" Aa mai kyau mai yayi zafi haka nima fa mijin aure ne, kuma gaskiya nikam tunda naga fotonki na Aure naji na kyasa kinyi min dan haka ni sonki nake" wani irin ashar na dunk'ula na d'ura masa, tare da tsinke wayar..

Cire layin nayi gaba d'aya na jefa dustbin dama Yaya Shahir yace na cire nice dai na tsaya ganin gari, gashi wani banza gara yana so ya dama min lissafi a banza..

Na dad'e gurin ina tsaki da jimamin abin, dak'yar na daidaita kaina lokacin da Yaya Shahir ya dawo dan banason ya sani, dan nasan nice da laifi tunda nina bar layin...


*2 week later...*



Yau Yaya Shahir ya koma kasuwa, ina d'aki ina tsaka da bacci, naji ring d'in wayata cikin magani na d'aga ba tare dana duba ba, a tunani na ko Yaya Shahir ne amma me sai naji sab'anin haka.

"Mai kyau shikenan sai kika kashemin waya ina tsaka da jin sweet voice naki, kuma kika jefar da sim d'in kikayi sabo, saidai abinda baki sani ba garin masoyi baya nisa, gashi na sake laluboki, nifa sonki ne kawai nake ba komai ba kuma ni duk abinda nakeso saina samesa...ai tsabar rud'u da takaici kashe wayar naji gaba d'aya, tuni na wartsake daga baccin jikina sai rawa yake wannan wace irin musiba ce na fad'a a fili..

Hmm kusan me?

Mardiyah tace dasu tana zubar da hawaye, taci, girgikai sukayi kamar k'adangaru suna jiran jin me zatace .....Ashe wannan mutumin ba mutum bane..

" Haba masoyiyata ya za'ayi ki gujeni bayan ba zaki iya gujemin ba, tunda ina nan tare dake a duk inda kike hhhh hhhhh" amon muryansa ya cikamin d'aki gaba d'aya...

Wani irin ratsanannen k'ara na saki tare da zubewa akan bed d'in a some...........







_tofah ๐Ÿ˜ฒabin takai hadda aljannu๐Ÿ˜ณ๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿƒ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ‘ป_






๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜








```Daga cikin abubuwan da Annabi Muhammad(SAW) yake hakaitowa da Azza wa jallah yace "yaku bayina ni na haram ta zalunci a kan kaina, shiyasa na sanya shi Abin haramta wa a gareku kada kuyi

Please Login or Register in order to submit comment