Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalaman so mtsss..

Ni zan shiga ciki kada Abba ya samemu na fad'a, "ba komai princess nagode da lokacin ki da kika bani thanks much baby" kud'i ya bani nak'i karb'a sosai ya nuna b'acin ransa akai hadda cewa inban ansa ba hakan na nuna baida muhalli a zuciyata kenan ya hak'ura kawai, hakan yasa na amsa tare dayi masa godiya yace ba komai saina ji daga garesa.

Ban tsure da lamarin ba saida muka k'irga 50k nan fa muka rud'e nida Umma, tace yanzu dai nayi miji amma me za'ayi da ya sayyadi a d'auri kashi ko ab'ata igiya...tace duk juyin da Abba zaimin na dage Aahil nakeso, nima ko batace ba hakan ne raina dan bazanbi tsiya ba ga Arziki.....






****************




Bayan kwana biyu ina d'aki kwance Abba ya aiko kirana bayan Na gaidashi yace "fad'ima wani yaro yazo gurina yace yanason aurenki kuma ke kika turoshi gurina hakane?" Girgiza kai nayi alaman eh "tau ya maganan Ahmad d'in bakya sonsa ne?" Nan ma kai na girgiza alaman eh.

"Kin tabbatar wannan yaron kikeso bakyason Ahmad?" Zan girgiza kai Yace "Aa bud'e baki kiyimin magana" nace eh Abba Aahil nakeso.


"Tau kije zanyi bincike akansa" daga haka na tashi na naje na gayama Umma yadda mukayi da Abba, naso naji daga Aahil amma ba dama dan ko number juna bamuda gashi kuma bai sake dawowa ba kaddai Abba ya koresa ne? Haka naita tunane tunane barkatai ga ya sayyadi naci gaba da zuwa gurina haushinsa sai k'ara ninkuwa a raina yake......



*A week later....*

Abba ya kirani nida Umma yace yayi bincike game da Aahil da zan hak'ura dashi da zaifi dan a cikin lamarinsa akwai rud'u, kuka na sakawa Abba akan ya barni ni shi nakeso indai baya sab'on Allah yanzu haka sharrin mak'iya ne, mamakine ya kama Abba ganin yanda na dage bako kunya abinda bai sanni dashi ba, itama Umma cewa tayi wasu 'yan suka ne suke son b'atasa a gunsa, ganin shima baida tabbas game da abinda aka fad'a saidai ransa bai kwanta da yaron ba sam duk da sigar ladabi da biyayya da yazo da ita.....

Shiru yayi na tsawon lokaci sannan yace "yi shiru Fad'ima tun da dai shi kikeso bazan hanaki ba kuma ni banda tabbas akan abinda aka gayamin a kansa kije kiyi istikhara akai, idan kinyi kikaji still ranki shi yakeso to zan baki shi kuma Ahmad na bashi hak'uri.

Umma tace "wai malam me akace ne game dashi?"

"Hmm magan ganune dai wasu suce bad'an garin bane wasu suke mayaudari ne amma a unguwarsu an bani tabbacin yaron kirki ne" tab'e baki tayi "yo malam ai dagaji kasan 'yan hana ruwa gudu ne"........


Washe gari naje gurin Abba nace nayi amma nidai shi nakeso, nayi istikhara amma babu niyya mai kyau kuma dukkan Abu yana tafiya ne da niyyar da akayi sa, yace tau naje zanyi yadda akayi...


Bayan sati biyu Abba ya sake kirana tare da duka mutan gidan da basu san wainar da ake toyawa ba sai yanzu, yace ya bawa iyayen Aahil damar fitowa kuma sunce gobe zasu kawo kayansu, dad'i kamar ya kasheni, sai murmushi nake bako kunya, sannan yace Ahmad kuma ya bashi hak'uri amma ya nuna yana sha'awar Safina in har tana sonsa kuma na tuntub'i Safina tace ta amince, Safina k'anwatace ita ke bina, nanfa Umma ta shiga Auna mata harara dan bata gayamata zancen ba sai yanzu da takeji, k'asa tai da kanta, Abbanmu murmushi kawai yayi daya ga abinda ke faruwa, nan dai kowa ya fad'a albarkacin bakinsa da nuna farincikinsu Wanda Umma tace munafinci ne dan basu da yadda zasuyine.......


Hakan ce ta kasance washe gari aka kawo kayan baiko kayane na fitar hankali dan ban tab'a gani ko jin anyiwa wata irinsu ba, nan fa kaina ya kara k'ato na k'ara jin feeling a raina na fara tunanin yadda zan fara fasawa...

Da dare sai Abba yayi kirana yace naje falonsa ga Aahil can na jirana, aiko farinciki na bazai misaltu ba.

Amma dan jan girma saida naja lokaci sannan naje bayan nasha make up na fitar hankali...

"Wow princess a gaskiya am d lucky of d would world, nayi kewarki sosai princess sai naji kamar na shekara 100 ban ganki ba" a gaskiya Aahil ya iya zance ya had'u d most ga uwa uba kawai Masu gidan rana..

Hmmm a ranar Aahil ya shayar dani mamaki bayan ya cikani da kalaman k'aunarsa sannan ya cilani da kayan more rayuwa ga kud'ad'e sannan ya bani gift d'in iPhone 5 mai shegen kyau wow a ranar munyi tsallen murna nida Umma, Safina dai na gefe sai bak'aken maganganu Umma ke yad'a mata hadda ce mata duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka....


A ranar kwana nayi muna chat da Aahil yana k'ara kasheni da kalaman k'aunarsa niko ina feeling akan no one like me........










🤤 _sorry my fans Ku kara hak'uri dani sanyi ne baya shafamin lafia ya kowanne ciwo tonomin yake, gani kuma masakiya ce so abubuwa sunmin chaa saidai ina manage kawai_ #1one love# 😍








💄Meryerm Abdool💄
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍









```Manzon Allah (S.A.W) yace "naga wani mutum yana yawo a cikin gidan aljannah, saboda wata itaciya daya d'auke akan hanya wacce ta kasance tana cutar da mutane(mahma'ul Bahrain) ```

*kawar da Abu mai cutarwa daga kan hanya sadaka ne, kuma kyakkyawan dabi'a ce wacce zatayi mana jagora gurin dacewa da rahamar Allah, Allah yasa mudace👏🏻*





💗 _Mom sultan novella ga naku shafin, Nabeela zaga where r u kin boye 2days?? #ana tare#_ 💓

















*11*



A school ma ba abinda nake sai swagg dan Aahil ya rik'emin kan maciji sai wasa da bindi nake, tuni na watsar da islamiyya na daina zuwa sai nake fakewa da aiki nake taya su Umma dan na k'ara gogewa a girki..

Ba kalar chat d'in da banayi dan banda matsalar data cos wayata Kullum cike take da kud'i kuma shi kemin sub so banda matsalar komai sai aikin chat har tsakiyan dare groups kala-kala na bude na big gurls wanda ake harkar manyas a ciki imma baki isa ba bana sakaki ciki, wuni ake aka VN and video chat muna tsula iskancinmu son rai, a school ma har gangs gareni karatun ma na daina sai shashanci...

Ina tsaka da chat ranar sai jin k'anwata Safina nayi tace "Adda Zuhrah niko meyasa kika zabi wannan rayuwar? Kin zubar da islamiyya a bokon ma kin daina maida hankali sai wata rayuwa da kika d'orawa kanki wacce a ganina ba mai b'ullewa bace, Adda Aure zakiyi ki zamo uwa mai bada tarbiya anya wannan hanyar itace dai2, kuma kina tunanin in Abba ya sani zaku wanye lafiya?"

Wata irin tsawa da Daka mata har sai da har saida ta razana, duk da ba wata tazarace a tsakaninmu ba dan shekara ce a tsakaninmu hakan bai hanani Jan girma gunta ba duk da dama can ita mai sanyi ce kamar Abba, ke har kin isa kiyimin wa'azi? OK saboda kina ganin k'anmu d'aya kuma aure zakiyi kamar yadda zanyi shiyasa kike dai daita kanki dani ba har kike tunanin kin isa shaa? To bari kiji imma kina min bak'in ciki ne saboda zan auri mai kud'i keko kin bige da ya sayyadi tun wuri ki daina dan ni dama ba sa'arki bace, kaina a waye yake ba kamar ke ba da duhun kai ya mamayeki bakisan me duniya ke ciki ba daga karatu sai karatu kika sani, to kije and kada ki k'ara sakamin baki a lamari rayuwa tace ba taki ba kin gane? Nace cike da fad'a da jan kunne hak'uri ta shiga bani sannan ta wuce dogon tsaki naja naci gaba da abinda nake ina mitar abin a raina...

Ni itama ke bani tausayi yarinya ta zabi rayuwar k'unci da wahala ana wa gani.....


A haka iyayen Aahil sukazo tambayan rana, Abba ya tsayar bayan mun kammala secondary hadda na Safina aka tsayar dan yace yafi son ya aurar damu a tare tunda ba wata tserayya ce a tsakaninmu ba dama ajinmu d'aya kuma shima ya sayyadi yace a shirye yake dan dama yayi NCE yana teaching a wata primary.....


Sati biyu tsakani aka kawo lefena da sadaki 100k, hohoho zo kuga hura hanci da daga Kai dan kuwa lefene na nunawa sa'a nunawa sa'a set had'u kuma ba shege daga sama har k'asa duk tsadaddu ne, tuni na d'auka na watsa media nan fa suka shiga santi da kod'a kayan kaina ya k'ara girma feeling ya k'aru, yan zuwa gani kuma ba'a magana kamar gidan suna gidanmu ya dawo Umma kuwa sai d'aga kai take ma kishiyoyinta tana sakar musu magana, duk diyansu mata k'anana ne amma basu tsira ba..

Akwati uku da kit ya sayyadi yayima Safina, nan fa Umma ta shiga kushe kayan da renawa amma fa ba gaban Abba ba dan duk abinda ake baida labari, itakam bai Abu sai murna take tana yabawa gwarzon nata dan itakam sunyi mata, nima dai na rena kayan dan har fad'a mata nayi ta cuci Kanta, sai cewa tayi "nikam Adda banga abin cuta anan ba sai dai2 ruwa dai2 gari, wallahi yayi k'ok'ari sosai" ganin zata sakamin ciwon kai yasa naja tsaki tare da kyaleta.

Adda Ainau ma mai hali take aure sai ita ta bige da ya sayyadi mai lifan a fad'a ta, da Adda Ainau tazo ganin kayan itakam ta yabawa kowa da irin bajintarsa itama dai kamar Safina tace k'arfi ne kowa da irin nasa, halayyarta ta sanyi da fad'an gaskiya yasa bama sakata a komai daga ni sai Umma na muke abuwanmu, Safina ma bata ciki dan daga fad'a sai harara ke had'ata da Umma...




*************



Muna chat wani group namu na classic lady suke tambaya basu ga *pre wedding pics* ba lokaci nata matsowa kuma ya akama nayi yadda nake chilling din nan, aiko a take nama Aahil magana akan fotunan.

Yace abinda yasa bai magana ba yaga kamar Abba na bazai yadda ayi ba dan yaga yanada ra'ayi dan ko kayan da aka kawo da sadaki cewa yayi a rage sunyi yawa saida fa iyayensa da yan uwana suka matsa sannan ya amsa badan yaso ba...

Sai cewa nayi Aa wallah nikam ai wajibi ne nayi *pre wedding pics* a yadda ake yayin yinsu yanzu in ban ba ai sai girmana ya fad'i a gaban k'awayena su renani, ya manta da zancen old man kawai...

Dariya yayi yace "my princess ke babba ce fa, shiyasa nake k'ara sonki toya za'ayi kenan"? Kada ka damu my love zanyi ma Umma maganan ka zamo ready kawai ka tsara mana komai dan Allah so nake na k'ara Jan girma na, nace Ina hango yadda zamu had'e watakil sai an bamu award..

" OK babe dana dawo da daga yafiya shine next Abu da za'ayi gimbiyata ai maganarki umarni ce dole na cika shi..".

Hmmm Aahil na kasheni da kalamansa duk da bayamin maganan banza bai tab'a koda tab'a hannuna ba, iya maganarsa na zama matarsa na Haifa masa yara kyawawa uwa ni, zai shayar dani mamaki ta hanyar mayar dani abar kwatance a mata...

Lokacin da gayama Umma maganar pic d'in cewa tayi "Hiri maddin hic kuma meye su d'in?" Dariya sosai nayi sannan na d'auko wayata na nuna mata pics d'in wasu da sukayi tace "ayyo cewa zakiyi abunku na 'yan boko ni ina nasan wani Abu hiri maddin hic" dariya na k'ara yi dan yadda ta dage iya gaskiya fad'a tace, nace Umma bada haka ake cewa ba *pre wedding pics* akace.

"Um nidai barni ban iya ba, amma kam zakiyi kyau dan kinfi wancen yarinyar kyau, sai naku yafi kyau" ina jin dad'i nace Allah Umma na.

"Sosai ko 'yar Umma, ita wancen matar malam nasan ba tayi ai" cewa da Safina, hmm Umma ai da wuya amma zan tuntub'eta in tanaso sai Aahil ya had'a dasu...

"Wancen uwar 'yan sani yanzu saita fara yi miki wa'azi, amma ki gwada ki gani, kuma kar Bari malam yaji dan nasan yana iya hanawa, ke ko yayyinki kada ki gayama bare wad'ancen matan" ai Umma kowa bazaiji ba saidai su gani kawai daga baya.....

Dana tunbub'i Safina sai cewa tayi "Adda ai wannan saiku nikam banaso, dama zakiji shawara da kema bakiyi ba wlh dan kin sani ko a makaranta ana fad'a..." Dakatar da ita nayi ta hanyar d'aga mata hannu ke rik'e guntun wa'azin kinji, na wuce ina tsaki dan ta b'atan rai.............








🤷🏻‍♀ _Dubara ta rage ga mai hawan kura babu takunkumi_ 🤤











💄Meryerm Abdool💄
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍








```Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa, idan ba zakaji kunya ba toka aikata abinda kakeso ma'ana idan ba zakaji kunyar Allah idan baka tsoron sa to ka aikata abinda kakeso(Arba'una hadith)```👌🏻









*13*






*_wishing speed, quickest, blink, jet recovery my half Abdool😘😞👏🏻_*









Bayan hankali na ya gama dawowa jikina, na tabbatar abinda ya faru ba mafarki bane da gaske ne, saboda yanda nakejin jikina kad'ai ya gasgatamin abin ya faru, wani irin kuka na saki mai tsuma rai cikin tausayin kaina dan nasan na cutar da kaina.

Aahil dake fitowa da toilet towel a kansa yana tsane ruwa da alama wanka yayi, da sauri ya iso gareni, tare da k'ok'arin rungume ni, kada ka tab'a ni Aahil, shine abinda na fad'a cikin k'araji da tsawa.

Gefen gadon ya zaune tare da rausayar da kai cikin yaudara yace "sorry baby is out of our control ke kanki kinsan bazan aikata haka gareki da gangan ba kiyi hak'uri kinji, don Allah ki yafemin hakan ba zata k'ara faruwa ba kinji my wife" ko inda yake ban kalla ba bare nayi tunanin tankashi.

Amma da yake Aahil dan duniya ne na k'arshe ya iya bakinsa hakan ya kalallameni da kalamansa har da fad'ar ai shine zai aureni kuma na sani so hakan bazai tab'a soyayyarmu ba saima abinda zai k'aru da dai kalamai makamantarsu na dad'in baki.

Da haka har na yadda da zantukan shi na hak'ura da taimakon shi na gyara jikina sannan ya mayar dani gida cike da kayan kwalam da mak'ulashe kamar kullum.

Iya d'auriya na yita don kada kowa ya fahimci halin da nake ciki, Nayi sa'a Umma bata fahimci komai ba dan kayan kwalamar sun tafi da hankalinta, saima Safina ce ta bini da kallon tuhuma har ta kasa daurewa tace "Adda lafiyarki kuwa naganki sukuku ga idonki kaman kinyi kuka" ras gabana ya fad'i amma na dake nace ba komai sannan na wuce dan kada ta tutsiyeni...

Sanda na nunawa Umma fotunan sai zuzuta kyansu take, sannan tace na b'oye kada ma muna fukai suga su ga yawa Abba na, hakan kuwa akayi, wad'anda aka turomin ta waya kuwa, turasu nayi on net kamar yadda akeyi nan fa comments and like Mara adadi sukaita shigomin a groups d'in mu kuwa ba abinda ake sai tattaunawa ake game da pics d'in suna fad'in yadda sukayi rocking har da bani award, dad'i ya mantar dani abinda ya faru Sam ban wani damu ba tunda ba abinda ya canja cikin soyayyata da Aahil saima wata kulawa da yake bani..

Saidai me tun da wannan abun ya shiga tsakanina da Aahil sai nakanji feeling sometimes mai tsananin gaske, dak'yar nake dannewa, kai in tak'aice muku haka wannan sha'awar tayi rinjaye dani wannan yaba Aahil damar mayar dani matarsa dan haka zaizo kullum ya d'auka ni muje gidan sa muyi abinda mukeso ya murjeni son ransa kamar ya samu matarsa ta Sunna..

A haka muka d'auki months muna sheke ayar mu dan na fahimci ni mace ce mai k'arfin sha'awa nasan cewa ba dai2 muke aikata wa ba amma kuma na kasa danne zuciyata da sha'awa ta, duk wannan abin dake faruwa Abba baya gari yaje Saudia, Umma kuwa ba ruwanta cewa take Ai mijina ne, ko kullum zaizo yaita zuwa tunda soyayyarmu ce ta zama ni, dan ita batasan muna fita ba, koda yake wani sa'in a cikin gidan mu yake danneni saboda tsabar rashin tsoron Allah..


*************


Lokacin da muka fara NECO ne Aahil yace min zasuyi tafiya Scotland shida Dadyn sa, banji dad'in tafiyar ba dan ina tunanin yadda zan iya jure rashin sa gashi yace sai gab da bikinmu zai dawo, rarrashina ya shiga yi da dad'in baki sannan ya cikani da kud'i sosai yace "ki kula da kanki sosai sai wata rana" ban kawo komai a raina ba a lokacin, a ka'ida daya isa wata k'asa yake kirana da sabon layinsa amma shiru shiru har akayi sati bashi ba dalilinsa, nan fa hankali na ya fara tashi amma sai na danne, na maida hankali gun exam d'in da muke zanawa...

Sai kuma me? Canji na faraji a jikina yau ciwo gobe lafia, ga yawan bacci ga kasala, ban k'ara shiga rashin hankali ba saida lokacin yin period d'ina yazo naji shiru, har na k'ara sati 2, nan fa na tsorace, sace jiki nayi naje chemist din unguwar mu na siyo abun gwajin ciki, positive na gani b'aro, b'aro a jiki, wayyo Allah na anan na sulale jamgwan ba damar nayi kuka Safina taji ta dameni da silly questions, kaina k'ullewa yayi gaba d'aya, ga rashin Aahil ga ciki ga exam nama rasa da wanne zanji, wani tunani ne nayi nace bari na gwada number Aahil ta naija naga ko zataje cikin mamaki na sameta a bud'e, saida nayi masa kira kusan goma a na sha d'aya ya d'aga dan na d'auki alkawarin ko zan kwana ina kiransa bazan daina ba saiya d'auka..

"Zuhrah baby..hhhh..dama nasan zaki nemeni soon shiyasa na bar miki layin a bud'e" Aa..Aahil dama kana k'asarnan amma kamin k'arya kace zaka tafi wata k'asa? Y? Y Aahil meyasa zakamin haka meyasa??

Wata irin dariyar mugunta ya sheke da ita saida yayi mai isarsa sannan yace "ke dakata! Ke a tunanin ki zansha mangwaro ne in tsaya rik'e k'wallon? Me zaimin? Yarinya na d'ana miki tarkona kuma cikin sauk'i ya kamaki hhhhh saboda kwad'ayin ki, a gaskiya I really enjoy wit u a duk matan da nake mu'amala dasu babu kamar ki, shiyasa na tsaya dake na mori kud'i, nasan zakice kinsan gidan mu kinsan iyayena wannan duk plain d'ina ne, kada fa ki d'auka kece ta fari..no kunada yawa danni haka nake zan kashe ko nawa ne danna d'and'ana mace, kada ki damu fa maganar *pre wedding pics* nayi da mata da yawa dan na fahimci kunfi yarda za'a aureku idan akayi fotunan daku, amma fa kece da abun kunya bani ba ko? Hhhhhhh...kada ki damu duk abinda kika samu hannuna naki ne, keda mayyar Uwarki, ladan jiyar dani dad'i ne....take heart bye silly girls,. Shoot u" kit naji wayar ta katse...

Rufe ido nayi da ba a kwance nike ba, to tabbas nasan k'afafuna ba zasu d'aukeni ba, wayyo na kasa gasgata abinda kunnuwana suka jiyomin, nafi yadda da bacci nake ina cikin mafarki ne, kuma mafi munin mafarki, jikina ba abinda yake sai b'ari dakyar na iya bud'e idona na naga tabbas ba mafarki nike ba, wayar na sake d'auka na duba kodai ba Aahil d'ina bane, tabbas no d'in sa CE, kira na kara yi amma a kashe..

Wani irin ihu na zunduma Wanda saida d'akin ya amsa, aiko rige-rigen shigowa ake tsakanin Umma da Safina da sauran mutanen gidan.....







_manage pls_









💄Meryerm Abdool💄
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍








```Manzon Allah (S.A.W) yana cewa "karatun yaro kamar rubutu ne a saman dutse amma karatun babba idan ya girma kamar rubutune a saman ruwa (majma'ul Bahrain)```


*mu dake muyi karatu tun da kuruciya basai girma yazo ba, mu d'aure mu nemi ilimi don gyaran lahirar mu tabbataccen gida, duniya ba komai bace face Abu mai wucewa, bata da daraja a gurin Allah dan yace fiffiken sauro ya fita k'ima, to idan hakane lallai mu daure mu gyara gidanmu na gaskiya, Allah yasa mudace👏🏻*

Small quote👌🏻








🤝❣ _Aminan juna group ban manta daku ba kuna raina abokan arziki musamman my Qwllytah, Malama ubaida, my shamcy, Nuwaira, Meenat, umcee, khadija, Fatima, Rukie ina kika shige muna kewarki😢😘 #Ana tare iya wuya🤝#_











*12*






Ana haka muka fara rubuta WAEC hakan tasa dole na nutsu na maida hankali na ga karatu don ina tsoron na fad'i Abba ya tasani gaba musamman idan Safina taci, naga kuwa ta dage sosai, successfully muka kammala WAEC d'in, wanda yayi dai2 da dawowar Aahil daga Thailand wanda yace sunje tare da Dadyn sa ne da yake dan kasuwa ne a yadda ya gayamin nida iyayena....

Tsaraba sosai ya jibgomin kai hatta 'yan gidan mu ba Wanda bai samu ba ga gift daya kawomin na taya murnar kammala WAEC sannan gana wishes din NECO, bazan iya misalta irin dad'in da nakeji ba yadda Aahil kemin hidima kamar baisan zafin neman kud'i ba, duk abinda na furta inaso haka zai kawo min shi jiki na rawa kuma wanda yafi wanda na buk'ata, har k'awaye na nake sawa yana ma hidima, bare kuma Umma na har kud'i ya bata ta canja komai na d'akinta amma sai aka b'oyewa Abba kada yai fad'a tace kiwon ta ne ta sayar....

Bayan mun gaba shan soyayyarmu ne yace na zama cikin shiri gobe zaizo mu tafi gurin *pre wedding pics* aiko tuni na fesawa k'awaye na wad'anda ke zugani nan suka shiga bani gurguwar shawara tare da cewa na tabbatar na bada show yadda zaiyi cilling nayi na wayis sosai, aiko hakan yasa na b'ata daren ranar gurin tunanin irin style d'in da zamuyi da yadda foton zai kasance wato shedan yana k'ara kawata min abin a raina tare da ingizani akan nayi duk abinda nakeso shine wayewa....



********



*Washe gari.....*



Tun da sassafe na farka sabanin kullum da sai ta hantse nake tashi, wanka nayi sosai tare da fesa kwalliya ta fitar hankali, 10:00am Aahil yamin wayar cewar ya iso ba b'ata lokaci nayi ma Umma sallama, gashi munyi sa'a Abba baya nan....

"Wow princess kinyi kyau sosai, kin ganki kuwa kamar ace kawai daga nan sai gidana an d'aura.." Ya fad'a yana kashemin ido.

Murmushin jindad'i nayi nace nagode my Prince kaima kayi kyau sosai...

Direct muka wuce studio Wanda ake ji dashi a Gombe wata side bag naga ya d'auka sannan muka shiga ciki, make-up suka k'ara yimin na irin na amare sannan Aahil ya bani wannan jakar kayane na rashin arziki a ciki na tsiraici da rashin kunya, a maimakon naji haushin kayan saima murna da nayi dasu dan nasan zan burge mutane, banyi tunanin martaba da mutumci irin na 'ya mace ba, banyi tunanin kariyar mutuncin gidan mu ba, ba abinda nake hange a lokacin sai yadda zan burge mutane ba tunanin makomata ba...

Tunda uwata ta kawoni duniya Wani namiji bai tab'a koda rik'emin hannu ba, amma gashi yau ba inda Aahil bai tab'a a jikina ba da sunan *pre wedding pics* which is haram Wanda kowa ya sani amma son zuciya da son burge wasu yasa mun manta Allah, mun manta addini da al'ada mu ta malam bahaushe, mun d'auki ak'idar yahudu mun mayar tamu Wanda dole ne muga ba dai2 ba tunda mun shure hukuncin Allah mun zabi son ranmu..

Sanda aka kammala fotunan suka tura mana a waya nidai kam haka nakejin jikina wani iri sai tsigar jikina ke tashi idanuna har sun canja launi inajin

Please Login or Register in order to submit comment