Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zalunci```👉🏻 _Allah ya da kansa ya haram ta zalunci kada muyi zalunci babu kyau, babban zunubi ne kuma addu'ar Wanda aka zalunta bata da hijabi da Allah madaukakin sarki_😢 muyi kokari mu kiyaye.










*21*




Ruwa naji an yayyafamin, firgigi na tashi ina raba ido, wani irin tsoro ne ya mamaye ni duk da kuwa taurin da dakiya irin tawa, tunawa da nayi da abinda ya faru minti kad'an da suka wuce.....


Banga Wanda ya yayyafamin ruwa ba, amma ga sanyin ruwan a jikina, tunanin in bar gidan ne yazo min a rai, aiko ban tsaya dogon tunani ba na mik'e ko ta mayafi banbi ba...

" Aa masoyiya ta ina zakije mai kyau na, ina tsaka da kallon kyakyawar surarki.." Muryan wannan aljanin ta cikamin kunne kamar farko, cikin tsoro na shiga raba ido dan ganin da inda maganar ke fitowa hmmm ni kaina naga k'arfin halina ba kad'an ba..

"Hhhhh hhhhh so kike ki ganni ne mai kyau? Tau gani gefenki juyo ki ganni, ina tare dake a duk inda kike masoyiyata" naji muryan nan tasa mara dad'in amo ta sake fad'a, saboda ganin kwaf juyawa nayi dan tabbatar wa....

Aiko anan idanuna sukayi tozali da wani mummunan halitta, duka tsawon sa bai wuce zira'i biyu ba, bak'i sidik dashi sai uban kai da yafi gangar jiki girma, idanunsa jajir kamar jini, bakinsa ya kuwa kunne, da wasu hak'ora manya manya, ya bud'e su yana dariya....

Sai dun faroni yake yana dariya, ihu na saka tare da fita d'akin da gudu tsiya inata zunduma ihu da kiran sunan ya Shahir..

A k'ofar fita parlour naci Karo da Yaya Shahir, ban tsaya wani mamakin ganinsa ba, tun da dan mai ceto nake nema...

Da gudu na fad'a jikinsa, tare da k'ank'amesa, ina kuka sosai nace Yaya pls d'auke ni mubar gidan nan wallahi zan haukace yaya, wallahi na shiga musiba yaya tafiya zaiyi dani, dan Allah yaya muje da sauri, jin duk sambatun nan da nake Yaya Shahir baiko motsa ba bare yace wani abu yasa na d'aga idona don ganin me yakeyi...

Mezan gani ba fuskar wannan aljanin ba a gangar jikin Yaya Shahir, ihu na k'ara k'walla wa tare da ja da baya da k'arfi ina kuka sosai ina fad'in wai me nayi maka ne? Menayi maka da zaka takura rayuwata, meye laifina dan na zama mai kyau? Meyasa zaka soni ina mutum kana aljani meyasa? Duk cikin tsananin tsoro da matsanancin kuka nake wannan magana inayi baya baya dan tunkaro ni yake yana wannan dariyar tasa mara fasali da rashin kyan gani..

"Ke kika ja na soki dan ke kika tura *pre wedding pics* d'in ki a group d'in da Nike, niko surarki ce ta jani, kina da kyakyawan zubi mai lokaci d'aya sonki ya harbemin zuciyata, ina sonki kuma kema dolenki ki soni dan komai nakeso to dole na mallakesa" ya fad'a cikin wata murya mai kama data tsoffin da sukaji duniya.

Wayyo Allah na na shiga musiba *A dalilin pre wedding pics* dan Allah kayi hak'ura kaga bata alaka tsakanin mutum da aljan, dan Allah kai hak'uri ka kyaleni wlh ni matar aure ce, duk ji nake kamar na saki fitsari a wando jikina sai rawa yake naga tashin hankali yak'azatan ido da ido, dana sani kuwa tuni ya dirar min, ina ma naji maganar Yaya Shahir da ban shiga musiba irin wannan ba..

"Ke! Ya fad'a da k'arfi, kinsan waye ni? To bari kiji dan ina sonki ne nake lallab'aki da ba dan haka ba d'akin gane waye Mahboob dan sarki Markaz" ya fad'a yana zare jajayen idanun nan nasa, aiko saijin fitsari na bin k'afata naji sannan naji hannuna a k'ofa, cikin sauri na shige d'akin tare da murza ke a k'ofar toilet na fad'a nan ma na murza key wai ni na tsere masa...

Wannan karon a dogo tsalala ya fitomin mai d'an k'aramin kai, fari Kamar zabaya, idonsa kuwa bak'i k'irin, hak'oran sa jajir yana dariya yana fad'in "ai ba zaki iya gujemin ba duk Wani motsi naki a kusa dani zakina yinsa, kinzama tawa, kin zama mallakina ni kad'ai" yana ta dun faroni Yana k'ok'arin kamani ya washe jajayin hak'oransa, ihu na k'ara kwallawa tare da silalewa a gun...



************



Sanda na farka a d'akin Hajia Inna na ganni ga 'yan uwa da iyayenmu duk sun zagayeni kowa fuskar sa d'auke da jimami, Yaya Shahir gefe yayi jigum, yunk'urawa nayi don tashi Hajia Inna ta kamani tare da sakamin filo na jingina, tanamin sannu, nan kowa ya shiga yimin sannu Da gai na shiga ansa musu...

Ina kowa da kallo, gefena na k'ara ganinsa wannan dariyar, nuna gurin na shiga yi cikin zare ido inaso nayi magana amma bakina ya k'asa cewa komai...

Da sauri Yaya Shahir ya taso ya kamani yana fad'in "menene Mardiya? Waime ke faruwa dake ne Mardiya, yi magana dan Allah Mardiya" so nake nayi magana amma na kasa, sai bakina dake motsi na kasa furta komai, ga wannan mugun abun da ko rufe ido nayi shi nake gani, gashi dai inajin maganar kowa amma ni na k'asa magana, kuma da alama ba mai ganin wannan aljanin saini dan gashi ina nuna musu shi suna fad'in me nakeso ne, menene..

Komawa nayi na kwanta a filo tare da lumshe ido hawaye na bin fuskar ta, ga ba abinda nake gani sai wannan mummunan halittar...


Tabbas na had'u da musiba *A dalilin pre wedding pics*...ni Mardiya..









_sai kuna hak'uri dani abubuwan ne ba guda ba🤗_












💄 Meryerm abdool💄
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍









🤗 *Jan hankali........*

👇🏻

*_akwai wani abu da mukeyi a yanzu Wanda bamu a bakin komai ba Wanda a zahirin gaskiya zunubi ne mai girma, wato yanke wa mutum hukunci best on ur opinion or others opinion, 'yar uwa idan kinga wani/wata yana aikata wani zunubi ko barna a maimakon ka yanke masa hukunci da ra'ayinka ko fahimtar ka ko ra'ayin wasu ko fahimtar wasu, gara kaje direct ka tambayesa meyasa yake aikata aiki kaza? Idan ba zaka iya hakan ba to zai fi ka nema masa shiriya kawai idan ba zaka iya nema masa ba to kayi shiru(falyak'ul khairan au lih yasmut) 🤗 pls sisters don't judge a book by it cover📗_*


*Small Quote👌🏻*










*22*








"Mardiya meke faruwa dake nikam, dan Allah kiyi magana d'iyarga" Hajia Inna ta fad'a cike da rauni, idona na bud'e tare daci gaba da hawaye dan na gama tabbatar da bazan iya magana ba, nikam tawa ta sameni, da kai da hannu nayi mata alaman bazan iya magana ba, taslima tayi cike da tausayi duk Wanda ke d'akin jikinsa ya gama yin sanyi...

Juyawa tayi ta kalli Yaya Shahir Wanda zuwa yanzu shima hawayen yake "Muhammadu wai meye ainihin abinda ya faru? Handcart yasa ya share k'wallar da ta zubo masa " Hajia wallahi bansan komai ba, kamar dai yadda na gaya muku tun farko, dawowa nayi ban sameta a parlour kamar yadda na saba ba, har d'aki bata sai toilet na sameta a some shine na rud'e na kwasota nayo nan" yace yana k'ok'arin fidda wata k'wallar...

Jim inna tayi na d'an lokaci sannan tace "anya Muhammadu kunyi saukar Al-Qur'an da addu'o'i a gidan nan?"

Girgiza kai yayi "duk anyi Hajia" momy ce(mamar yaya Shahir) tace "to addu'a fa kunayi?" Tabbas bamayi ko d'an irin karatun Qur'an d'in nan da ake sakawa a sabon gida bamayi iyakar mu soyayya da kallon fina-finan soyayya irin na India, Chinese, american da sauran tashoshi na fina finai, har ma gara yaya Shahir yana karatu Qur'an duk safiya, nikam tun da naje gidan ban tab'a d'aukar Qur'an da sunan na karanta...

Bazan tuna when nayi azkar ko istigfari, hailala da hamdala ba, nafi maida hankalina da chat ko kallo idan yaya Shahir bayanan idan kuma yana nan haka zan kalalla mesa da soyayyar da na koya da novels, karatun da nake na novel soyayyar kawai na koya ba wani darasi da nake d'auka nidai naga love kawai na kwafa na gwada ga nawa mijin, nasan sosai nake tauye Yaya Shahir gurin ibadar sa amma son da yakemin ya hana ya gane ina nisanta shi da mahaliccinsa, bare ya gyara yayi tunanin gyara ni nima, lallai na cutar da kanmu, gashi yanzu ina son nayi addu'ar amma na kasa yi...

Jin shirun nasa yayi yawa ne yasa Hajia Inna cewa "basayi gashi nan yayi shiru ba amsa, ba wai wannan 'yar gamo tayi" nan fa kowa ya k'ara tsorata tabbas wannan yanayi nawa na mai mutan b'oye ne, "to ya za'ayi yanzu Hajia?"

"Malami za'a nema yanzu kam, yanzu dai Kai ke lmamu kira muna su Abdullahi su San abinda ake ciki" tace Ya Imam k'anin yaya Shahir, ba musu ya kira Dadyna dama shine ke gari Abba da Baba sunje kwatano..

Lokacin yazo damuwa ce k'arara a fuskar sa, amma yayi k'ok'arin dannewa sosai a matsayina na 'yar fari, nidai da ido kawai nake binsu ba um ba uh um, Dady ne ya bada shawarar a kawo biro da paper na rubuta abinda ya faru saidai abin mamaki na kasa rubutun shima hannuna sai sawa yake yi, nan fa aka tsurewa da lamarin, Umma na duk yanda taso ta b'oye Hawayenta saida suka zubu, lallai na jawa Kaina musibar da bata tsaya iyani ba har 'yan uwana ta Shafa tunda duk na hargitsa musu kwanciyar hankali..



************





Dady da Yaya Shahir da ya Imam ne sukaje sukazo da wani malami, bayan yayi dube-duben sa yace tabbas iska ne kuma mugun iska, wasu magagunguna ya kawo yace can dare zuwa k'arfe 1 dare zan tashi nayi turare dashi....

Hmmm tashin hankali kunsan me?

Ina tashi dan yin turaren bayan ta nayi kamar yadda malam yace na saka a rushi zan lullub'e sai naji muryarsa...

"Hi mai kyau na gani nima Zan tayaki shan hayakin" wannan aljanin dai wato Mahboob ne shima da rushinsa a gabansa kamar ni zaiyi hayaki........








*don't scare my sweet friend👾👺👹*






Manage👏🏻









💄Meryerm Abdool💄
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍




```cikin fad'ar Allah mad'aukakin sarki, yace "yaku bayina dukannin ku b'atattu ne face wad'anda na shiryar Ku nemi shiriya ta na shiryar daku, yaku bayina dukannin ku mayunwata ne face wad'anda na ciyar Ku nemi ciyar wata in ciyar daku, yaku bayina dukannin Ku huntaye ne face wad'anda na suturta ku nemi suturta wata na suturtar daku(Arba'una hadith)👌🏻```


💋😍 _my sweetheart, my Darling, my sweet namcy ever_ 💋😍


*Earth may stop rotating*
*Birds may stop flying*
*Candles may stop melting*
*Fishes may stop swimming*
*Heart may stop breathing*
*But i will never stop Loving you my true friend*

~❣Ur d best Darling Maryam Yusuf Zango❣~









*23*





Jikina ne ya shiga bari, gashi ba bakin ihu, sai matsoni yake yana fad'in "Ku dena wahalar da kanku dan auren mu ba fashi, wani d'an shiri nake dana kammala sai a sha biki, muah!muah!! Kai lallai zan more da wannan lafiyannen jikin naki mai kyau" Yana k'ok'arin tab'a jikina, baya nayi da sauri sannan na kwasa a guje na shige d'akin Hajia Inna, dariyar sa kawai nake jiyowa duk ta cikamin kunnuwa, hannu nasa na toshe kunnen hawaye na bin fuska ta cike da tausayin kaina na fad'a jikin Hajia dake lazumi kan carpet, "menene kuma mardiya har kin gama hayak'in?" Hajia ta fad'a fuskar ta d'auke da tsantar tausayi na, hawayen naci gaba dayi ina nuna mata waje tare da girgiza kaina..

"Oh ni Hauwa! Wannan 'ya Allah ya yaye maki wanga musiba da kike ciki" sannan ta jani zuwa gadonta tana tofamin addu'o'i sannu a hankali barci ya d'auke ni mai cike da mafarkin wannan aljanin, gashi yaje wata masarauta yana cikin shigar sarauta ya fito da kyakyawan sifa yana nuna gun 'yan uwansa a amatsayin matar da zai aura, haka naita ganin ababen tsoro da firgici naita cin karo dasu, gani a wata duniya cikin wasu halittu da ba jinsi ba, ana haka ne, sai ga wata kyakyawan budurwa ita cikin shirin sarauta amma babu annuri a fuskarta tazo tare da barorinta inda muke tace "dama akanki ne Mahboob ya FASA aurena? Ke! Bil adama ki saurara dakyau ni nan Marshufa, saina zama ajalinki middin kika yadda kikayi yunk'urin rabani da masoyina...

Tass ya sauke mata mari a fuskar sannan ya fara magana cikin fushi da wani kalar yaren da tun da nazo duniya ban tab'a jinsa ba, fad'a suke sosai nidai ina gefe a tsorace sai zare ido nake, ta fad'i ya fad'i har takai ga sun fara dambe, nuni ta yiwa bayinta akan su kamani, aiko ganin sunyo kaina yasa na k'walla wata irin k'ara wacce tayi sanadin farkawa ta ina zuba uban gumi kamar wacce tayi gudu...

Gefena na ganshi yana kallona " kin tsorata ko kada ki damu zanyi maganin abin bazan tab'a Bari ta cutar da ke ba" hannayena na had'e guri d'aya cikin mamaki naji bakina ya bud'e nace dan Allah ka taimaka kamin rai ka barni na huta wlh na gane kuskure na, bazan k'ara ba, zan kiyaye dan Allah ka barni na zauna da mijina lafia ka fita rayuwa ta cike da kukan dana sani wacce take k'eya CE...

"Ke! Saurara baki da wani miji daya wuce ni nan" ya fad'a cikin tsawa yana nuna kansa, duk wannan abun da ake Hajia Inna ko motsi batayi ba hakan ya tabbatar min bata jin komai dan nasan bata da nauyin bacci da taji data farka, "ki kwanta kiyi bacci zanje naji da wancen ki zama cikin shiri dana kammala da ita zan dawo na d'aukeki" daga haka ya wuce yana min smiling, wasu zafafan hawaye, gashi inaso nayi addu'a amma na kasa yi, lallai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka, yau na ta kaina ni mardiya....



*****************



In tak'aice muku dai aka shiga kawo malamai suna kawo magungunan su amma koda zanyi amfani da maganin zan samu yana yin irinsa ko yazo da irin maganin ga badar na kwanta, zan ganni a duniyar su ya kaini, nidai gani a raye cikin mutane amma ba um ba uh um muddin nayi magana to da shine ko a duniyarsu ne, yan uwa da iyayena na k'ok'arin yimin addu'a musammam Hajia Inna da Yaya Shahir shima duk ya rame yayi bak'i...

A haka nayi wata cikin matsanancin hali, ni kaina na kasa gane kaina, shin mutum nike ko aljana? Na fita cikin mutane iyaka dasu ido, haka yaya Shahir zai sakani gaba yana kuka akan nayi masa magana, amma bazan iya ba, tausayinsa da kaina kad'ai ya isheni Wanda duk son zuciyata da taurin kaina ne ya kaimu ga wannan, hmmm abokanaina na social media ba mai nemana, ashe media abar banza ce Dana barta itama ta barka, duk inda iyayena sukaji labarin Malami mai fidda iskoki zasu kirashi ko su kaini haka sukayi ta spending money a kaina amma ba nasara, shi kuma b'angaren aljanin nawa har yanzu yana kan fafatawa da wannan budurwar tasa da taci burin kasheni..

Kwatsam ranar aka samu wani malami, Malamin Sunna ne na sosai Wanda ke aiki da ayar Allah dan k'ona aljanu, tunda yazo ya ganni yace lallai na had'u da mugun aljani mai wuyar sha'ana amma ba abinda ya gagari ayar Allah, yace a cire duk wani foto dake cikin d'akin, da duk wani Abu mai janyo aljanu, karatu ya shiga yi da gaske saida yayi tsawon awa biyu yana yi sannan aka samu yazo, amma yak'i magana, yayi-yayi ya kafe aiko nan ya shiga k'onasa sa, saida zafin k'unar ya ratsashi sannan yace zaiyi magana, nan ya fara bayanin duk yadda akayi har ya shiga jikina, da yadda nake sakaci da addu'a, da yawan jin kid'e-kid'e da wak'e-wak'e duk yayi bayanin sannan yace shi sona ne yake kawai dan nayi mishi kuma ba wanda ya isa ya raba mu, dan yana matuk'ar sona...

Tsantsar mamaki ne ya kama iyayenmu dan su duk basu san yaushe akayi fotunan ba har aka yad'a, zasu rufe Yaya Shahir da fad'a dan duk sun d'ora laifin a kansa, meyasa bai gayamusu ba in har shi tsorona yakeji baison b'acin raina, Hajia Inna tace "duk ba yanzu za'ayi wannan ba ku bari mu fara samun kanta a rabata da wannan bala'i tukun, malam yanzu ya za'ayi" ta tambayi malamin.

"Kada ki damu Hajia tunda har yayi magana, ai yazo da sauki, ya gudu yanzu amma kada Ku tada hankalinku da kanshi zai dawo yace zai fita inshaa Allah" ruwan zam-zam da man zaitun habbatus sauda, da hantiti, ganyen magarya, da sauran magunguna na shafawa dana wanka, ya basu tare da bayanin yadda za'ayi amfani dasu, Sannan yace a kiyaye sakamin karatun Qur'an duk inda nike koda kuwa bacci nike sannan a nisanci tashoshin banza na shaidanci in so samune a ma daina kallon gaba d'aya, ya zamana duk gidan Qur'an ne kawai, ayi haka zuwa sati d'aya...sannan ya kawo ayoyin waraka yace ana ringa karanta min a zam-zam ina sha ana shafamin a jiki...

Haka kuwa akayi, yanzu Sam bai iya zuwa inda nike saidai na ganshi nesa yana kuka yana fad'in kar na Bari a rabamu inna rabu dashi mutuwa zaiyi...

Sati na cika malam yazo, wannan karon baisha wahala ba yazo yana kuka tare da fad'in zai fita, dan Allah kada ya kona sa, cikin ikon Allah da yardarsa aka rabani da wannan aljanin, attishawa na shiga yi wata na bin wata, saida na d'auki lokaci inayi sannan na gama, Alhmdllh itace Kalmar da ta fara fad'a cike da godewa Allah yau gani ina magana bayan tsawon lokaci dana zama kurma......












😂🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀ _an sha dak'yar su Mardisha iyayen *pre wedding pics* ga Mahboob nan ya dawo, amma wannan Karon gurinki zaizo sis lubabat 👹😆 #1love deae#💋_









💄Meryerm Abdool💄
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: 🤦🏽‍♀😭😭
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*💏
🤦🏽‍♀😭😭

🙆🏾🙆🏾🙆🏾
( _Mun shiga musiba_ )
🙆🏾🙆🏾🙆🏾



```Written by```
*By*
💄 _Meryerm Abdool_ 💄



® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to 😍M_M😍






```daga cikin abin da Allah mad'aukakin sarki yake cewa "yaku bayina Ku kun kasance kuna sab'amin dare da rana ni kuma na kasance mai gafara a gareku, ku nemi gafarata in gafarta muku```👌🏻


*👏🏻 Allah _gafurun rahimun ne_ a kullum k'ofar tuba a bud'e take babu makara, mu daure mu koma gareshi mu nemi gafararsa ta hanyar istigifari, hailala, hamdala, da nisantar miyagun dabiu da umarni ga kyawawan dabi'u, muyi tuba, tuba mai kyau wacce ba zamu komawa sab'on da muka tuba dominsa ba, Allah yasa mu dace👏🏻*








*24*


Gaba d'aya falon kowa sai hamdala yake cike da farinciki ganin yau gashi na bud'e baki nayi magana, yaya Shahir gefe ya kame tare da rungume hannayensa a k'irji yana kallona tare da murmushi cikin hawaye, nima hawayen ke fita a idona tare da mayar masa martanin murmushin, gyaran murya malam yayi hakan yasa kowa ya nutsu ana sauraronsa...

"Tabbas wannan 'yar taku ta auna arziki saidai muce Allah ya kiyaye gaba, dan sai dace ake samu aljani ya shiga jikin mutum ya kuma fita kai tsaye, amma duk da haka taci gaba da amfani da wad'ancen magungunan sannan a kiyaye addu'a, da azkar da kuma karatun Qur'an a kuma nisanci kallace-kallacen banza da rubuce-rubucen banza, a kiyaye aje abubuwan da zasu nisanta mala'ikun Allah zama a wuri kamar, fotunan banza dana tsiraici, kare, toys na yara da dai makamantansu..

Littafin husnul Muslim malam ya bani sabo fil yace " kinga wannan shine garkuwar musulmi ta hanyar addu'a, Allah da kansa yace _Addu'ah saiful Muslim (addu'a takobin musulmi CE)_ muddin kika kiyaye addu'o'in cikinsa baki ba matsala a rayuwa, addu'ar komai daya shafeki na sha'anin duniya da lahira duk zaki samu a ciki kuma sahihai ne bisa k'aulin malamai gaba d'aynsu, Allah ya baki lafia ya kiyaye gaba" godiya sosai na shiga yi masa haka iyayenmu dasu Hajia da kuma su yaya Shahir..

Bayan sun rakashi har mota tare da cika shi da abin arziki dan yace shi baya jinga a bashi duk abinda ya sawwak'a...


Abba nane ya fara magana "Yanzu fisabillah abinda kikayi kin kyauta kenan mardiya? Koda yake bakida laifi, Hafsat ta fiki laifi cewa da momma na, dan tana sane kikeyi" Dadyn yaya Shahir ne yace.

"Taya zaka d'aura musu laifi bayan ga babban mai laifin nan, Shahir da bai amince da hakan ba aida duk haka bata faru ba, koko so yake yace Mardiya ta fishi wayo da sanin dai dai" Hmmm yanzu dai duk kowa ya tsaya" Hajia Inna tace sannan taci gaba...

"Duk mai faruwa ta Riga da ta faru kuma Hafsatu bata da laifi ko d'aya dan batama San anyi ba, kaganta sarkin kafiyar nan itace silar faruwar komai saboda taurin Kanta, itace can wurin gane-ganenta ta hanyar salular nan da suka saka kansu ta gano wad'annan fotunan, ta kuma CE sai tayi, itama kai har fad'a sukayi dashi Muhammadu akan fotunan, ni duk ban san meye dalilin fad'an ba sai bayan sunyi fotunan su ne na gane ashe akansu ne, shidai imma yana da laifi to baifi biyemata da yake akan duk abinda takeso ba amma bayan haka komai ya faru itace taja" cikin fushi Abba yaje zai dakeni...

"Wai kai Hamza ba nace abar zancen ba ai wannan musibar kad'ai data shiga ta isheta darasi basai ka k'ara mata da duka ba, ai taga ishara ganin idonta" Hajia Inna tace, zamewa nayi kan gwiuwata ina hawaye tare da had'a hannayena guri d'aya Abba, Dady, Baba, Hajia, momma, Umma, Aunty, Yaya Shahir, da duk Wanda ke gurin nan dan Allah Ku gafarceni komai ya faru nina ja kuma na gane kuskure na, dan Allah Ku yafemin inshaa Allah bazan k'ara kwatanta irin wannan ba, wlh na azabtu na gane son zuciya b'acin ta...

Nan dai aka k'ara yi mana nasiha da k'ara nuna mana rayuwa ita duniya ba komai zuciya ceso yake zamo wa alkhairi ga mai ita ba, sau da yawa takan jefa mai ita a halaka ba tare daya sani ba sai ya ganshi ya afka a ciki, sannan aka jama yaya Shahir kunne shima akan ya daina biyemin akan son raina dan bazai gane ba gata yakemin ba sai zama yayi zama, sannan kuma halin rayuwa ne yau samu gobe rashi, yau Kaine gobe wani, aini kam ko basu ce komai ba na gane kuskure na bazan kara kwatanta irin abinda nayi ba dan naga izaya...

Saida na k'ara sati a gidan nad'an murmure na tada komad'a sannan Hajia ta k'ara min dabarun zaman aure da rayuwa ma gaba d'aya kacokam...



**************



Ashe ma rayuwar 'yanci tana cikin inuwar bin koyin sunnar Manzon Allah, yanzu da gidan ya dawo gidan karatu da addu'a kullum cikin karatu muke da safe sai rana ta fito muke gamawa bayan mungama tilawa Qur'an nakan d'auko littafaina yaya Shahir ya d'orana, azkar na safe da rana basa kub'ucemin saida ciwo ko sha'afa, social media kuma inayi har yau saidai na iya kaina yanzu na iya takuna, sai ina free nake log in, karatun novel ma inayi saidai masu ma'ana nake karantawa kuma na d'auki right nabar wrong, da taimakon yaya Shahir na fada North-west uni, inda na karanta b'angaren poultry mashaa Allah yanzu na kware a harkar kiwon kaji na zama expert, Allah ya azurtamu da yara biyu twins mace da namiji Arif da Amrah mun gina rayuwar a turbar islama...


"Tau sister kunji tawa musibar nida Aljani, na had'u kuma daga lokacin da na koma ga Addu'a da Qur'an, na rabu dashi lallai ba abinda yafi k'arfin Addu'a" mardiya ta

Please Login or Register in order to submit comment