Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

had'u da Dady sai Dady ya bashi izinin turo magabatansa, ba bata lokaci magana ta kan kama, akayi baiko da komai na al'ada aka tsaida rana, haka mukaci gaba da soyewar mu da Amir kamar mu had'iye juna ba dare ba rana ba'a school ba ba gida ba, saidai Dady ya tabbatar min dole zan maida hankali na a karatun dan aure baya hana karatu kamar yadda karatu baya hana Aure, da yake su Amir suna ending ne lokacin hakan yasa muka saurara juna mukaci gaba da karatu, wannan karon result d'ina da d'an dama, hakan ya farantawa su Mami, itadai Mami bata wani murna da aurena Wanda a lokacin bansan dalilin ta ba, da badan tana ita ta haifeni ba da zan iya cewa bak'in ciki takemin dan a lokacin duk Wanda yace ba Amir ba ko zaginsa zan iyayi.

Ana saura one month Amir yace na shirya muje muyi *Pre-wedding pics* tsallen murna nahau dan dama inason duniya taga tsadadden mijin da zan aura.

Lokacin da na gayama Mami watakil tasan kota hana ba lallai na hanu ba, dan ta kula da yanda kaina ke hayak'i, sai cewa tayi Allah ya kiyaye na kula da kaina...


**************



Studio ne na gani da magana duk Yola ba kamarsa, duk wani mai jin ya isa nan yake zuwa ya d'auki photo.

K'walla ne ya zubo a idonta, saurin sharewa tayi, suma matan gaba d'aya hankalinsu ya tafi gareta sun k'agu suji ya aka kaya(nima dai da readers mun k'agu Allah).lol


Ci gaba tayi, Hmmm fotuna muka d'auka na fitsara to na fitsara mana, dan kowane lungu da sak'o na jikina Amir ya tab'a, nima ya sakani na tab'a nasa, amma a lokacin banji komai ba saima a tunani na burgewa ce, kusan kala 20 akayi mana ba d'aya Wanda bai bayyanar da surar jikina ba dan shigace ta fitsara munyi mukayi ko nace nayi dan shi namiji komai yayi ado ne, mace ce ke kwasar kunya, Wanda duk amir ne ya tanadar mana tufafin.

Anan on d sports aka bamu su sannan aka zuba mana sa a wayoyinmu, Sameer shine mutum na farko da Amir ya fara turawa, ni kima su Zahira, sannan muka watsa a yanar gizo-gizo, tun anan studio.

Sannan muka wuce ya saukeni gida, lokacin da na nunawa Mami Sam abin bai burgeta ba a yanda ta nuna a fuska, harta kasa daurewa tace amma dai abin yayi tsiraici da yawa, nikam haushi naji nace to ai Mami haka yayi yanzu, Allah ya kyauta ta fad'a...

Lokacin da na isa d'akina na kunna data, nan na dinga ganin like da comments shares sunfi millions, tun daga Facebook, Twitter, IMO, insta, WhatsApp, kowa sai zuzuta kyan fotunan yake, kai ranar dad'i kamar ya tafi dani, haka su Khady sukace suma da suka tura sai yabawa aka wai hadda cewa ba'a taba match couples kamar mu ba, kai naga mutane ranar hadda masu kirana, ni kuma sai feeling nake nayi miji na numawa a ko'ina ba kunya.

Tau yan uwa ina gaya muku, haka lokacin Auren mu yazo aka sha biki na kece reni dan kud'i ne suka had'u da kud'i, anyi events sunfi ashirin Wanda duk bidi'a ce da k'arya, walima ce kad'ai akayi abin kirki a ciki ita din ma Mami CE ta shirya.

Amir yaso ace anyi bikinmu Sameer na nan, amma da yake yana zana final exam ne dole muka hak'ura saidai a waya ake gayamai komai daya gudana, ga wani kulawa na musamman da yake bani harma yafi Amir yawan kirana, a chat ma haka duk ba ban fiye hawa ba, saina d'auka a matsayin yanayi ne saboda abokinsa.

Anyi biki lamui an murji bidi'a matuk'a, an watsa lafia, abin ya fara bani mamaki da Amir shine a daren farkon mu, ba wani sallah ko Addu'a, ko Neman albarkar ubangiji duk babu sai soyayya aka raya a wannan daren.

Wani abin haushi da asuba, abinda ya kamata ace shine ya fara tashi ya tattaleni da bani kulawa a matsayina na amaryarsa daya jigatar amma saini ce ta tashi na gyara kaina, har nayi sallah asuba, ko motsi bai ba sai bacci yake kamar matacce.

Nayi tada shi harna gaji yak'i tashi to kodai wannan bai saba sallah a jam'i bane, tunanin da yazo min arai kenan, saurin kawar wa nayi a raina dan soyayyar da nake masa ba zata bari naga aibunsa ba(wannan so ya zama musifa)

Bashi ya tashi ba saida rana ta fito K'iri-k'iri a gaggauce ya shiga toilet yayi wanka tare da d'auro alwala, tashin sa zuwa sallarsa duka bai wuce 10mnt ba, nan ma maimakon naga baiyi dai2 ba saima uzurin rashin dalili da nake bashi.

"Queen morning, hw was ur last night?" Yace yana shafa gefen fuska ta tare da kashe min ido d'aya, samun kaina nayi da sakar masa murmushi na amsa da lafia, sannan nace ka makara yau, ko duk gajiyar CE?

"Eh wlh kinsan ke d'in ce kin rud'ani ga gajia biki gata musamman" yace yana Shafo k'eyarsa tare da kashe min ido ya jani gaba d'aya zuwa jikinsa....







_banyi alkawarin Baku 2page a kullum ba, Indai kun samu to alhmdllh in kuma bai samu ba, to ayi hakuri_ ๐Ÿ‘Œ๐Ÿป








๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜






```Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace "duniya kurkukun musulmi ce, aljannar kafiri ce``` (majma'ul Bahrain)




*๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜ Real PML writers, this is ur page, heart u so muah๐Ÿ’‹guys ana tare iya wuya๐Ÿค*


*Hip!*๐ŸŽˆ
*Hip!!*๐ŸŽˆ
*Hip!!*๐ŸŽˆ
*Hurray๐ŸŽŠ๐ŸŽ‰*

๐Ÿ˜˜ _Happy womb escape Fatyy Azland_๐Ÿ˜˜


๐ŸŽ *_May Allah's noor and Rahman, khair be wit u 2day and after, Allah ya raya mana ke Antynah๐Ÿ˜๐ŸŽ_*


๐Ÿ›Happy birthday๐Ÿ›







*05*




Haka mukaci gaba da gudanar da soyayyarmu cikin kwanciyar hankali, saidai wasu abubuwa dake d'aure min kai game da Amir, Sam bai damu da addini ba, dakyar yake tashi yaje masjeed Shima saina dage, ban tab'a ganin ya d'auki Qur'an da sunan ya karanta, baya kallon tashar addini, idan na saka kuma bazai ce na cire ba saidai ya maida hankalinsa ga wayarsa ko kuma ya danne kunnensa da ear pieces, ke in tak'aice muku rayuwar Amir gaba d'aya batayi kama da rayuwar islama ba yahudanci ne kawai ya saka a gaba.

Sai wani Abu daya keyi duk zai kwanta dani sai yayi amfani da wani cream Wanda bansan na miye ba, ranar da na tambayesa kai tsaye ya gayamin na hana d'aukar ciki, planning yake mana dan gaskiya bai kamata mu haihu yanzu ba, Allah yasan ina matuk'ar son yara, amma saboda son da nakewa Amir yasa na kasa yi mishi musu ko na nuna b'acin raina saima goyon baya dana basa dan dai ganin farincikinsa.

Ranar da ya fara kawo min abokansa yace Nazo mu gaisa, hijab na saka har kasa a ganina na kare masa mutuncinsa Ashe ban burgeshi ba sai harara yake aikamin, bayan sun wuce ya shiga mita wai na wani zubu hijab har k'asa kamar matar liman, ni Sam ba waye ba ke ta inda yake fita ba tanan yace shiga ba, waishi Ashe yaso na matse yadda abokansa zamu gane ya auro kyakyawa wayayyiya, (wayewar banza da wofi ba, wayewar yahudawa).

A ranar Amir ya shayar dani mamaki banyi tunanin hakan daga gareshi ba a yadda yake zuzuta son da yakemin ban d'auka baya kishi na ba, dan iya sanina duk inda akace so tofa za'a samu kishi, a k'arshe ma ficewa daga gidan gaba d'aya yayi waishi nan fushi yake dani.

Haka rayuwar auren ta fara samun matsala, miyagun halaye Kala-kala Amir yake b'ullomin dasu, yanzu ma zaman gidan sa k'alilan ne, inya fita tun safe sai can rana yake dawowa daya ci abinci ya danyi bacci, ya tashi zai sake tsantsara ya d'auki ado as usual da k'amshin nan nasa, wad'anda suka rud'eni, amma baiyi donni ba dan ficewarsa zaiyi bazan k'ara sakashi a ido ba sai can sulusin dare, wani sa'in ma sai nayi bacci yake dawowa saidai na ganshi da safe, mamaki na shiga dama wannan ne Auren? Soyayyar iya wajene daga an shigo ciki ba ita, wato shiyasa Mami take cemin sai nayi hak'uri dan shi Aure d'an hak'uri ne ina ganin me kuma zanyi hak'uri dashi tunda Wanda nakeso yake kuma sona na aura Ashe ba haka abin yake ba.

Duk wannan halin da muke ciki ban tab'a gayawa kowa ba, even Mami, a tunani na zan iya magance matsalar da kaina, lokacin da na tunkareshi da maganar sai cewa yayi ai ni naja saboda ban waye ba komai nawa saina saka k'auyenci, ina kuka nace don Allah yayi hak'uri ya gayamin abinda nake na rashin wayewa na gyara, dan Allah yasan har a lokacin sonsa na nuk'urk'usan zuciyata, shiyasa na jigata da halin ko in kula da yake nunamin, a ranar dai muka k'ara shiryawa muka koma kamar da.

Hakan nake fitowa cikin matsu gaban abokansa ayita fira suna k'aremin kallon mayata, shiko sai dad'i yakeji yanda suke zuzuta kyawuna suna fad'in duk ya fisu dacen da kyakyawar mace, Allah yasan abin baya min dad'i dan kad'a'an nasan haram ne, amma dan son ganin farincikin Amir nayi biris da hukuncin Allah nake biyewa Amir, akwai ranar da Amir yaje dani club, Ashe dama can ne yake zuwa duk dare, ya ilahi a ranar naga ta kaina, na kuma yi dana sanin binsa da nayi, acan na barshi na dawo gida abina cike da tashin hankali, Ashe Amir shaye-shaye yakeyi? Amma ban tab'a sani ba, amma ban tab'a ganin alama ba, koda yake in style yakeyi dan ko yanzu baiso na sani ba girshi na mishi dan ya barni gurin matan abokansa ne, ganin yadda maza ke kawomin hari yasa na nemi shi acan na gansa yana shak'e kwayoyi, ranar na kwana kuka ba mai rarrashi na, sai safe ya dawo duk da yaga halin zazzabi da nake ciki Wanda a sanadin kukan da nayine ya jamin baisa ya tausayamin ko kulani ba saima fushi da ya hauyi dani, nima dai cikin fushi na nuna masa abinda yakeyi ba kyau meyasa yake shaye-shaye, dariyar rainin wayo yayi min tare da fad'in "kaji rashin wayewa ba" daga haka ya wuce abin sa ya barni nan.

Wannan karon kam nima d'auke wuta nayi na fita harkarsa, ba ruwana da sabgarsa, amma kuma still ba tare da kowa ya sani ba tun daga gidansu har namu zuwa k'awayena, chatting na koma yi a matsayin d'ebe kewa duk da ada ba wani damuna yayi ba, su Zahira har sunamin tsiyar wai Amarci ya k'are kenan.

B'angaren Sameer kuwa dawowa chat ba k'aramin sha kuwa ya Samar a tsananin mu ba, nidai na d'auka ne yanayi ne akan Amintar da ke tsakaninsu da Amir da yake dama can mun saba tun kafin auren mu, gashi har yanzu bai dawo ba so baisan halin da muke ciki ba.






************



Wata rana muna chat yake cemin "Queen" kamar yadda Amir ke kirana "ina matuk'ar sha'awarki, kusan kullum sai nayi mafarkin ki, inaso kimin alk'awarin zaki bani had'in kai idan na dawo, tunda mun kusa dawowa" na karanta text din yafi sau biyar inason na tantance shidin ne ko wani kodai wasa yake nace a raina, hakan ya bani damar ke masa yabar irin wannan wasar ba kyau.

Bayan 2mnt saiga kiransa ba kunya ba tsoron Allah, yake gayamin shi wallahi tun ranar da Amir ya tura masa Pre-wedding pics namu yaga yadda surar jikina take ya kamu da matsanciyar sha'awata kullum sai yayi mafarkin yana tare dani, dan Allah na taimaka na bashi had'in kai idan ya dawo dan wallahi ya kwad'aita dani.

Tsabar tashin hankali kasa koda motsi nayi wannan wace irin musiba ce, daga k'arshe sai ma kashe wayar nayi gaba d'aya saboda yadda kunnuwana suka k'asa d'aukar miyagun maganganunsa.

Jagab na fad'i a gado nama rasa kalar tunanin da zanyi, ba abinda ya fad'omin a rai sai tunanin adadin mutanen da suka kalli fotunan namu nake, Indai har amininsa zai fad'i haka a gareni, kenan mutum nawa na jefa a kogin sha'awata *Adalilin Pre-wedding pics* dinmu, dafe Kai nayi tare da sakin kuka mai cin rai ina kiran sunan Allah, lallai a yau na gane dalilin da na kasa samun nutsuwar Aure............





*ayi hak'uri da jina shiru da akayi na shiga busy ne* ๐Ÿ‘๐Ÿฝ






๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



ยฎ โ€‹PURE MOMENT OF LIFE WRITERSโ€‹
โ€‹ษฏษ› ษ–ฦกล‹'ลง ฦกล‹ูณแƒง ษ›ล‹ลงษ›ล™ลงฤ…ฤฑล‹ ล‹ษ– ษ›ษ–ลณฤ†ฤ…ลงษ›, แƒชลณลง ษฏษ› ฤ…ูณลžฦก ลงฦกลณฤ†ษง ษ– ษงษ›ฤ…ล™ลง ฦกส„ ล™ษ›ฤ…ษ–ษ›'ลžโ€‹


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
โ€‹#IG PML WRITERSโ€‹
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜






```Manzon Allah S.A.W yana cewa "kashedinku da zato domin shi zato k'aryan labari ne(husnul Muslim)```





๐Ÿ˜ _Ahalin duniya Makaranta 2 ga shafinku domin jin dad'in ku nagode sosai da encourage, musamman Aunty Baraka I really appreciate๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐Ÿ˜_






*06*





Sai can dare Amir ya dawo guraren 2Pm ina zaune na tallab'e kumatu na da hannayena, nayi kukan har na gaji, sai saka da warwara nake, shin na gayama Amir, wata zuciyar tace ba lallai ya yanda ba saima yaga kina son had'a shi da abokinsa ne, towa zan gayama nace Mami, ita naga bai kamata na tayar mata da hankali ba, nace su Khady naga innai hakan na tona sirrina ne, daga k'arshe dai na yanke shawarar blocking nasa kawai, hakan kuwa akayi koda na bud'e wayata sai text d'insa suka ringa shigo min masu cike da shed'anci irin nasa, ko karanta wasu banyi ba na goge tare da blocking nasa.

Inajin Amir a parlour yana kallon sa koya shigo ya duba lafia ta, kai bak'in ciki kan bak'in ciki, a maimakon na tashi nakai kukana ga mahaliccina sai na k'asa yin hakan saboda ban saba ba, hasalima bansan matsala ba a rayuwa ko tashin hankali sai wannan karon, haka dai na kwanta cike da tunane-tunane har bacci yayi gaba dani..


*********


Ina tunanin na yadda kwalon na huta da k'uda Ashe ba anan gizon ke sak'a ba, dan kuwa Amir layi ya saye kala- kala da yayi min magana na gane shine nayi blocking zai canja wani ya sake yimin magana haka ya takura rayuwa ta ya sakoni gaba da maganganun b'atanci, har ikirarin cewa yana lallab'ani ne badan nafi k'arfinsa ba, sai don yafison ya sameni yadda ya kamata wato da son raina, niko nace har ya mutu bazai samu wannan damar ba, kuma saina gayama amininsa tunda shi baisan mutunci da amana ba, kunsan me dariya ya kwashemin da ita tare da cewa yafi buk'atar hakan, daga haka na katse wayar tare da cire sim d'in na jefa dustbin na aje wayar gaba d'aya.

Kamar yadda nace zan gayawa Amir, hakan akayi dan a tunani na shine last stage da zanbi na rabuda wancen shed'anin koda kuwa abokin nasa bazai yadda dani ba.

Lokacin da na tareshi da maganar kunsan me? Suhaila ta dakata tana share hawaye wasu nabin wasu, zuwa lokacin ba Wanda baya hawaye a cikin su, (nikam sai matsar hawayen nake sunk'i fitowa) lol.


Taci gaba bayan ta goge hawayen.

Sai cewa yayi "to shine meye? Kin kuwa San matsayin Sameer a gurina? Zan iya mallaka masa abinda yafiki ma, kedai wallahi anyi bak'auyiya, bakisan yanzu muna global time ne ba, wannan abin is nothing" ya fad'a yana daga k'afad'a alaman ko a jikinsa ya fice ya barni dask'are a gurin.

Bantab'a sanin Amir d'an akuya bane jahili sai yau, Ashe har wayewarsa ta wuce sanina? Lallai na tsumduma kaina a musiba nan na wuni kuka da dana sani Mara adadi.

Gaba d'aya na d'auke wuta, a yau fuskar Amir danake ganin tafi ta kowa kyau ta dawo kota kare tafita kyau a gurina, na tsaneshi matuk'ar tsana ko muryar sa bana buk'atar ji, gashi kuma na kasa gayawa kowa wannan musibar da nake ciki wacce na had'u da ita a dalilin son zuciya da *Pre-wedding pics*.

Saida muka had'a sati bamu saka juna a ido ba, ranar ina zaune a falo sai gashi kamar an jefo shi ba sallama ba komai, ko kallon inda shike banyi ba, na tashi da niyyan shigewa d'akina dan na tsani ganin mummunar fuskarsa dan a yanzu tafi komai muni a idona saboda munanan halayensa "ke!" Naji ya fad'a cike da gatsali ban juyo ba kuma banda niyyan juyawar, koya fahimci hakane yasa ya k'ara cewa " Sameer fa ya iso yau"

Wani bak'in ciki ne ya turnik'eni ji nake kamar nahau kan shi da duka har sai ya daina numfashi, dan wallahi a yau ko bindiga aka bani zan iya harbesa tsaf, wani dogon tsaki naja tare da wucewa, can na jiyoshi yana wata dariyar rainin wayo, tun inajin motsinsa har barji Alaman ya fice, ji nayi kamar na tashi na fice gidanmu dan yanzu kurkuma tafimin shi Wallahi, amma kuma na k'asa aikata hakan to naje nace me a tawa wautar..


Bayan kwana biyu ina kwance d'aki da dare bayan isha nayi nisa da tunani, sai muryan amir na jiyo a falo ina mamakin mai ya dawo dashi wannan lokacin, ban gama mamaki ba naji ganshi tsaye gabana tashi nayi zaune da sauri dan son jin da wacce yazo dan nayi alkawarin bazan kara had'a jiki dashi ba "dude shigo mana" itace Kalmar da ya fad'a saiga wani saurayi ya bayyana a d'akin shima dai mai kyau kamar dai amir da kyalekyale irin nasa, cikin firgici na mik'e tsaye tare da cewa wannan wane irin rashin sanin h'akkin addini ne da hauka ya zaka shigo min da gardi har d'aki.

"U see na gaya maka bagidajiya ce ka nace, well gaka gata sai kayi abinda kakeso da ita kota k'arfin tsiya ne" zaro ido nayi cikin kid'ima ina kallon Amir da wannan gayen bakina na rawa nama kasa motsi shi kuma saurayin sai kallon mayata yake bina dashi da murmushin mugunta, Kafin nace tak har Amir ya fice daga d'akin ya barni da gayen.

"Hi Queen" shine abinda ya fad'a a tace na gane Sameer ne, ciki na ya fara dosowa ni kuma ina ja da baya ina fad'in Waiku wasu irin marasa imani ne meyasa bakwa tsoron Allah ne dan Allah kayi hak'uri kada ka ketamin haddi nifa matar abokinka ce?

Ko jina bayayi saima k'ok'arin hugging d'ina yake, yaje kamani na duk'e tare dayin baya can saman fridge na hango kwalbar cook dana sha dama nafison drink na kwalba, aiko ko shawara ban tsaya ba na jajubeta na rotsa mai aka da duka k'arfina, ba zato yaji saukar ta a ceyarsa aiko wani irin ihu ya saki sai jini sha ihunshi ne yasa Amir shigowa d'akin yana fad'in lafia ganin halin da yake ciki yasa yayi kansa yana fad'in "Kai ta fasama" shiko yakai k'asa sai juyi yake baisan inda kemai ciwo ba, ni kaina na rud'e na k'asa koda kwakkwaran motsi, cikin fushi Amir ya taso tare zaro bell "kika illatashi? Wallahi yau a gidan nan saidai adau gawa biyu wato keda shi" ganin yayo kaina yasa na kwasa da gudu na fice rude wa nayi na rasa hangar fita sai na fad'a kitchen.

Ashe yaga shiga na jin takunsa yana zuwa yasa na rasa yadda zanyi, a can gefe na hango tabaryar da Mami ta sakomin akayana ada har ina mitar mezanyi da ita Ashe ranarta na zuwa.

D'auka nayi na rik'e sosai tare da b'oye wa bayan ganbu, yana shigowa yana fad'in "ina kike 'yar iska yau nidake ne" saida na daidaici k'eyarsa na sauke mishi ita, shima anan ya zube yana ihu, aiko da gudu na tsallakesa na nemi hanyar barin gidan....





๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿ˜‚ _wayyo maza anji jiki, wallah dariya ta hanani ci gaba, to kuma ku dara amma kad'an fa, dan ba ruwana in cikin mutum ya kulle ehe๐Ÿคท๐Ÿฝโ€โ™€_











๐Ÿ’„Meryerm Abdool๐Ÿ’„
[12/6, 5:12 PM] maryam Abdul: ๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ
*_ADALILIN PRE WEDDING PICS_*๐Ÿ’
๐Ÿคฆ๐Ÿฝโ€โ™€๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ
( _Mun shiga musiba_ )
๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ๐Ÿ™†๐Ÿพ



```Written by```
*By*
๐Ÿ’„ _Meryerm Abdool_ ๐Ÿ’„



*_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
*PML*


( We don't just entertain and educate we also touch the heart of the readers)




Dedicate to ๐Ÿ˜M_M๐Ÿ˜







```An karb'o daga Abu huraira(Abdurrahman bin sahri) R.D yace :-

Naji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa "duk abinda na umurceku dashi ku aikata shi gwargwadon iyawarku abinda kuma na haneku dashi Ku nisanceshi iya nisanta, domin yana daga cikin abinda ya halakar da wad'anda suka gabaceku yawan tambayoyin su da yawan sab'awarsu ga annabawansu(arba'una hadith)๐Ÿ‘Œ๐Ÿป```





โค *Wannan shafin nakune Real PML writers fans, Shamsiya Umar gaisuwarki ta daban ce Suhaila na godiya da kulawarki๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜˜*





*07*








Cikin sa'a na isa gate ban samu gateman ba, hakan yasa na fice da sauri, dan a yadda nakeji koda na samesa bai isa ya hanani tafia koda takai na turesa ne zan aikata, gudu nake iya k'arfina ina waiwayo bayana kar su biyoni duk da nasan sun bugu da wuya in zasu iya tashi yanzu, har na isa babban titin unguwar mu banci karo da kowa ba dayake unguwar reserve area ce so kowa ya rufe gidansa, ko rana haka take sai can kake ganin mutane tsilli-tsilli.

Maida numfashi na shiga yi sannan ina d'aga wa motocin da ke wucewa hannu, Saidai ba alaman zasu tsaya, duban jikina nayi a lokacin ne na gane dalilin rashin tsayawar tasu su taimakeni, dagani sai wata gown ta material ba d'ankwali bare takalmi ga gashina a yamutse kamar sabon kamun hauka, watakil ma kallon mahauciya sukemin.

Ashe kuka ma ni'ima ne, dan gashi na kasa yi, duk inda hankali na yake ya gama hargitsewa ganin yadda motoci ke wuceni ba niyyan zasu tausayamin, aza hannu aka nayi ina fad'in yau na shiga bala'i da musiba wayyo Allah na, ga tsoro ya gama cikani dan a tab'a sanin haka dare yakeI bapks inya Lula sai yau dan lokacin da nake gida bana fitar dare Dady ya hana, kuma ko ranar da mukaje club da Amir koda na dawo dare bai lula haka ba, kuma da mota na dawo, tsoron kada su Amir su biyo sahuna ya cikani ga tsoron yan iskan gari kada su illatani, a tak'aice dai lokacin nama rasa wane tunani zanyi, in nace naje da k'afa bansan yaushe zan isa ba, and bansan wane bala'i zan had'u dashi ba, in nace na koma gidan Amir nasan na kashe kaina kawai, ganin ba mafita yasa na koma kiran sunan Allah da Neman agajinsa, kamar a mafarki naga wata mota ta tsaya, hmm aiko shawara ban tsayayi ba ko sauraran naga mai ita na afka ciki.

"Are you OK" shine ma mallakin motar ya fad'a yana zuba min ido da alama nazarina yakeyi, dan Allah ka taimaka min kabar nan gurin dani na fad'a cike da d'okin mubar gun duk da shi bansan ainihin abinda yasa ya tsaya ya d'auke ni ba.

Ba musu yaja motar, saida muka fita da unguwar sannan hankali na ya fara dawowa jikina, wata tambaya naji ya jefomin "meya sameki kika fito a haka da daren nan? Sannan da kika shigo motata kinsan wayeni?"

Nan fa tsoro ya fara dirar min amma saina dake nace wlh mijina ne yayi niyyan kasheni shine na samu na sab'eshi da tabarya na gudo, dan Allah kada kutar dani ka taimaka ka kaini gidanmu nace cikin raunin murya, yanayin fuskarsa naga ya canja zuwa na tausayi yana kallon kwayar idona dan ya gane in gaskiya na fad'a.

"Meyasa zaiyi yunk'urin kasheki me kika masa?" Ban masa komai ba, nan na gaya mishi kad'an daga abinda ya faru a ranar, ya jinjina lamarin a ransa dan ya dan ya dad'e Kafin ya iya cewa "Allah ya sawwak'a, toni kinga banma san garin nan ba dan hanya ce kad'ai ta biyo dani ciki, lokacin da na ganki na d'auka ko

Please Login or Register in order to submit comment