Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to DON ADNAN'S destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV

Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi ta timmus salihat 🥺🥰 Allah ka qarawa Annabi daraja 🤲


Bismillahir rahmanir raheem


Free page_1

..........Garin a lumshe yake kasancewar lokacin damuna ne kuma ga yanayin safiya, iska ce me dadi take kada duk mutumin dake a waje harma da wanda yake a daki dan sosae ake iska, safiya ce sosae bayan asuba kenan wanda se a lokacin garin ya fara haske, mutane jefi_jefi na wucewa, wasu daga masallaci suke, wasu kuma harkar gabansu ce ta fito dasu.
Tafiya takeyi babu tsagaetawa dauke da goyo a bayanta wanda ke daure da wani kyakykyawan farin towel, sedae na kaasa fahimtar a yanayin da take ciki, dan kuwa ita ba sauri takeyi ba kuma ba'a hankali take tafiya ba, wani lokacin idan ta wuce ta wani wajen wasu mutanen kan juya su kalleta su cigaba da harkar gabansu, a hankali nakae kallo na zuwa qafarta da iska ta kada zaninta har hakan ya bashi damar dagawa, jini ne busashshe a qafarta ta, komawar zanin inda yake ya bata damar cigaba da tafiya ba tare data kalli ko mutum 1 daga cikin masu kallanta ba, bata tsaya ko'ina ba seda taje wajen wani tudun yashi dake ajje waje guda sannan ta fara qoqarin kwance towel din dake bayanta, hakan ne ya sake bani damar ganin jinin dake kwance akan fararen qafafunta, sedae ita da alama bata damu da hakan ba dan kuwa cigaba tayi da kwanto abinda ke bayanta...dai_dai lokacin wasu mutane su 2 mace da namiji suka fito dattijae, dattijon na bayan matar saying

" Ae dae kya yi da jiki mu isa da wuri.. Kinsan dae.." Be kae ga 'karasawa ba ya hangi wata matashiya na kwanto abu daga bayanta, quri yayi cikin hasken farin watan daya gama washe garin yana kallanta bakinsa na rawa ya furta

"Jirani anan, yau nake ganin wani ikon Allah " ya fada yana yin gaba, kamar wanda aka tsikara se kuma ya juyo ya kalli matar yace

" Aff! Kar nayi wani abun ya zama laefi, ki kula da matar nan don Allah, bari naje na sanarwa me gari tukun na " be jira tace komae ba yayi gaba, tsohuwar ta kalli garin babu kowa se ita se matar, seta maeda hankalinta kan matar wadda ta gama kwanto abinda ke bayanta, wata cute baby ce a cikin towel din wadda ke bacci calmly babu abinda ke damunta, bata kalli fuskar babyn ba bayan ta sakko da ita kawae ta ajjiyeta a wajen sannan ta miqe, tsohuwar tayi wani yunquri tayi baya tana kiran sunan Allah hango jinin da tayi a qafar matar kuma gashi ta ajje jinjinniya a wajen and not minding ga wata halitta na kallanta, binta da kallo tsohuwar tayi harta wuce ta gabanta tayi bakin titi sannan ta maedo da hankalinta kan yashin tana sakin wata gauruwar ajjiyar zuciya, yayinda matar ta cigaba da tafiya abinta harta kawo titi, tana qoqarin tsallaka titi, dae_dae lokacin da wata mota qirar taxi tazo wucewa and matar kuma na qoqarin wucewa ta tsakiyar titin, me motar yayi iya bakin qoqarinsa wajen ganin ya riqe steering motar tasa, sedae ina Allah ya riga ya qadarta, seda yayi gaba da matar wadda a lokacin ta fadi qasa warwass alamar babu rae a jikinta.........


.....Cikin sauri wannan tsohon mutumin suke tafe tare da yaron me gari zuwa wajen da abin ya faru, tsohon na gaba yayinda yaron me garin yake biye dashi har suka qaraso wajen, basu tsaya ko ina ba se wajen yashin nan, ganin alamar matar bata nan ya sanya Malam Inuwa (tsohon) ya kalli matarsa Gaje yace cikin rashin fahimta

" ina matar take ?

Gaje da tun dazu tayi mutuwar tsaye, ga zafin ciwo kuma ga tsoratar da tayi se a lokacin ta iya dagowa ta kalli malam Inuwa sannan ta tattaro wasu kalamae daga bakinta tace cikin in'ina

"Ta..tayi nan" ta fada tana nuna musu hanyar data bi ba tare data kalli inda take nuna musu ba, yaron me gari yayi gaba yana kallan inda gaje ta nuna wato hanyar titi, yayi iya duban da zeyi a titin shi dae bega kowa ba, se mutane tsilla tsillah da suke wucewa suma kuma maza ne, ta6e baki yayi yana juyowa ya qaraso ya kalli gaje da malam Inuwa yace

"Fisabillahi malam Inuwa da girmanku kuna irin wannan abun, yanzu ni gashi an tashe ni daga baccin da nake qoqarin komawa ba tare........" Maganar tasa ta katse sanda wani sautin kukan jariri ya karade ilahirin wajen da suke, Seya zabura yana juyawa ya kalli inda yake da tabbacin daga nan ne kukan yake fitowa, gaaje ta hadiyi yawu da qyar tana fadin

"Wlh matar ce ta ajjiyeta, duk yadda akayi aljana ce, malam karkaje !! Ta fada tana kallan malam Inuwa dake qarasawa saman yashin, Bismillah malam Inuwa yayi, yaron me gari dae na biye dashi a baya yana kallan ikon Allah, malam Inuwa yakae hannunsa inda yaga towel din ya sakeyin bismillah sannan ya dauko ta

"Innalillahi! Innalillahi" yaron me gari ya fada yana yin baya ganin da gaske jinjirin ne a hannun malam Inuwa se tsandara kuka yake, Malam inuwa ya kalli jinjirar dake cikin towel wadda a sanadiyar budewar da towel din yayi yasa ya fahimci ko kaya babu a jikinta, Seya dauke kae ya kalli gaje yace

"Kizo mu wuce wajen me gari"

Ita dae gaje bata iya sake cewa komae ba, ta bari seda su malam sukayi gaba sannan ta bisu a baya, binsu kawae take kamar wata doluwa bata cewa komae, motsi kadan seta dan leqa ta kalli jinjirar da malam ke riqe da ita seta cigaba da tafiya, shima dae yaron me gari yana daga gefen malam tambayoyi fall a ransa, a haka har suka qarasa gidan me gari. Yaron me gari yayi sallama a gidan, uwar gidansa da bata koma bacci ba kasancewar gari yayi haske sosae tana tsakar gida tana hada wuta taji sallamar yaron me garin, seta amsa sallamar tasa tana dorawa da fadin

"Abdullahi lafiya dae koh? Seda yayi shiru kadan sannan yace

"Ehh toh, idan dae babu damuwa don Allah a taso mana me gari" Mamaki ya qara kasheta amma seta barshi kawae tace

"Toh bari in masa magana, Allah dae yasa lafiya" daga haka ta wuce dakin me garin....

Suna nan tsaye a qofar gidan me garin wanda wajen ya kasance rufaffe ne samansa, gaaje na gefe har lokacin qirjinta bebar bugawa ba kawae dae qarfin hali take, yayinda malam Inuwa shima har lokacin yake riqe da jinjirar, Mintuna wajen 5 sega me gari ya fito daga cikin gidan nasa yana kallansu su duka, Abdullahi ya zube a wajen yana fadin

"Barka da safiya yalla6ai"

"Barka ka dae abdullahi" me gari ya fada yana kallan malam Inuwa fuskarsa fall cike da alamomin tambaya, malam Inuwa ya matsa suka gaesa cike da ladabi sannan yace

"Wato ranka ya dade wata magana ce me muhimmanci ta kawo mu, kaaga wannan 'yar ? Ya fada yana sakko da ita daga kafadarsa sannan ya Dora da

"Yanzun nan mun fito zamuje asibiti, saboda muna so muyi sammako..."

"Kae abdullahi, shiga ciki ka samo mana tabarma" me gari ya fada yana kallan abdullahi, Abdullahi ya miqe ya shige gidan, can se gashi ya fito da tabarmar ya shimfida ta anan qofar gidan kasancewar ke6antaccen waje ne, Malam Inuwa ya nemi waje ya zauna bayan me gari ya zauna, ita kuma gaaje dama tana gefe tun dazu, Bayan me gari ya zauna ya kalli malam Inuwa yace

"Ina jinka" Jin haka ya sanya malam Inuwa dorawa da fadin

"Ranka ya dade lokacin da muka fito se naga wata matashiyar yarinya da goyo a bayanta ta hau kan yashin dake qofar gida na, toh ranka ya dade kasan sha'anin garin nan, abinda yasa kenan nacewa me daki na ta jira a wajen ni kuma zanzo in kiraka ko wani wakilinka, toh da nazo shine na tafi da abdullahi kasancewar ance mana shigowarka gidan kenan, sedae kafin komawarmu har ita yarinyar ta gudu tabar jaririyar, ga me dakina can ita zata qarasa bayanin" Me gari dae kallan malam Inuwa kawae yake cike da mamakin zancen nasa, se kuma ya kalli gaaje yace

"Bismillah" ya fada yana nuna mata kan tabarmar, a hankali ta qaraso ta zauna kan tabarmar kanta a qasa ta fara magana

"Yalla6ae bayan tafiyar malam, ina tsaye ina kallan matar yadda nasan zata iya gani na, dan nasan idan ta ganni zataji tsoro ta fasa aekata abinda tayi niyya, sedae ga mamakina ko gezau batayi ba sanda ta ganni, ta ajiye jaririyar tayi tafiyarta, ranka ya dad'e abinda ya bani tsoro kenan yasa na kasa tsayar da ita dan nayi tunanin ko aljana ce" me gari yaja numfashi kafin yace

"Yah salaam, Allah yasa dae ba rabota akayi da iyayenta akazo aka yarda ita ba"

"Wa ?? Wallahi ranka ya dade wannan data yarda ita itace ta haefeta, zan iya dafa qur'ani akan abinda na gani wallahi, dan kuwa dukda na tsorata hakan be hanani ganin jinin dake qafarta ba, ba sau 1 ba ba sau 2 ba, kuma indae ba qarya nayi ba jinin haehuwa ne, dan da alama sabuwar haehuwa ce, yalla6ae duk yadda akayi irin masu haefar shegun nan ne suje su jefar dasu kafin kowa ya ankara da hakan shiyasa......"

"Ya isa haka" me gari ya dakatar da gaaje daga bayanin da take sannan yakae hannu ya kar6i jinjirar dake cikin towel tayi shiru abinta tana bacci hankali kwance, kyakykyawa da ita fara sol, dukda sabuwar haehuwa ce hakan be hana dogon hancinta bayyana ba da dan qaramin bakinta wanda ta kama qasan lips din nata a cikin bakinta, me gari ya kalleta cike da tausayawa yana kallan yadda ko kaya ba'a saka mata ba haka zalika ga bushashshen jini jini a jikinta wanda hakan ze alamta maka da ba'a dade da haefarta ba, haka kurum yaji tausayin yarinyar ya kamashi, yarinyar da bataji ba bata gani ba, an haefeta da dattin zina, tunda yasan dae duk d'anda aka haefa na sunnah babu yadda za'ae uwar data haefeshi ta yadda shi, sedae waladiz zina din tunda ba sau 1 ba ba sau 2 ba ya saba kar6ar irin case din kuma daga baya idan akayi bincike se a gano cewa yaron shege ne, seya kawar da wadannan tunane tunanen ya juyo ya kallesu su duka yace

"Kuma ba kiga inda matar tayi ba" gaaje ta girgiza kae

"Wlh ranka ya dade, rudewa tasa banga inda tayi ba amma dae tabbas titi tayi" Me gari ya gyada kae yana jinjina al'amarin sannan yace

"Shikenan zaku iya tafiya, zan saka a bincika min, idan ba'a samu 'kwa'kw'kwaran abinda zamu ri'ka ba to shikenan semu kaeta wajen 'yan sandan cikin gari, duk suka amsa da "Toh Allah ya qara girma" sannan suka miqe suka wuce.
Me gari ya shiga gidansa da sallama, har lokacin uwar gidansa na tsakar gida tana sarrafa musu karin safiya, cike da mamaki ta miqe daga gaban murhun tana kallan me gari sedae ta kaasa cewa komae, ganin yanayinta ya tabbatawa me gari tana buqatar qarin bayani ne dan haka cike da kulawa yace

"Ajjiye abinda kikeyi kizo kiji" Ae bata koma ko'ina ba tabi bayan me gari daya shige dakinsa ya nemi waje ya zauna, itama ta zauna, kafin tace komae me gari yayi mata bayanin duk abinda gaaje ta fada masa, Uwar gidan nasa ta girgiza da jin abinda ya fada din, idanunta har sun ciko da 'kwalla ta qarasa ta kar6i babyn tana kallanta cike da tausayi tace

"Kayya!Allah sarki baewar Allah babu ruwanta anja mata, Allah ya kiyaye ta daga gorin asali, yanzu meye mafita malam ? Me gari ya ajje numfashi sannan yace

"Yanzu dae zan saka ayi min wasu bincike, idan hakan be yiwu ba toh semu miqata police station na cikin gari" Gyada kae tayi kafin tace

"Toh Allah yasa hakane mafi alkhaeri"

.....'Bangaren gaaje kuwa asibitin da ba taje ba kenan, ba irin maganar da malam Inuwa beyi mata ba akan zuwa asibitin amma ina firr taqi tace ita ta warke, ta zari jiki da sanyin safiyar nan zuwa gidan qawarta ta labarta mata abinda ya faru, toh kunsan tsofaffi akwae daukaka abu shikenan zance ya fara yaduwa cikin garin, kasancewar qaramin gari ne dad'in dad'awa kuma 'kauye yasa kafin azahar maganar ta baza lungu da saqo na cikinsa "Wata mata tayi cikin shege, a ranar data haefe shegen taje tayar dashi, yanzu haka abinda ta haefe din na gidan me gari" Kafin kace menene wannan maganar ta zama kamar wani topic of discussion, ko ina ka zaga zancen akeyi.WANNAN SHINE MAFARI....


........"Malam lafiya dae koh ? Naaga ka shigo gida kamar a firgice" Wata mata da ba zata wuce 30years ba ta fada tana kallan mijinta, Malam habu ya janyo kujerar dake kusa da ita 'yar tsuguno ya zauna sannan yace

"Wallahi wani zance ne ya dauremin kae habi, kinji zancen dake ta yawo a gari kuwa" Seta saki wani miskilin murmushi tace

"Aff ! Ae nan da kake gani na jiranka nake ka shigo in fada maka abinda na yanke akan maganar"

"Aww, kinji ma kenan ? Ya tambaya yana kallanta, Seta wani yatsine fuska

" Toh banda abinka baban ilyasu wannan maganar inane bata zaga ba a cikin garin nan, kasan dae halin 'yan garin nan dae, ya aka 'kare ma mutum beyi abu ba ballanta yayi ? Ta 'karasa maganar cikin sigar tambaya, Seya gyada kae yace

"Ehh kuma hakane, yanzu dae fadamin meya faru ? Gyara zama tayi akan kujerar da take tana kallansa tace

"Wani hukunci na yanke kuma nasan kaema zeyi maka dadi" bata jira ya bata amsa ba ta cigaba da fadin

"So nake mu kar6o yarinyar da aka tsinta a gidan me gari mu ri'keta" Malam Habu ya wani zabura kamar wanda aka tsikara yace

"Kina nufin mu reni shegiya ?

"Toh ina ruwanmu mu, Allah yasa tsinanniya ce ba shegiya ba mu dae in har burimmu ze cika ba shikenan ba ? Ta fada tana watsa masa wani kallo, kallan da kana ganinsa kasan babu mutunci daga wajen wanda yakeyi din zuwa wanda ake aekawa

"Toh fadi inji menene"

"Yawwah, bafa wae mu dauketa mu riqe tane haka kawae ba, a'ah ina nufin musan yadda zamuyi mu tausashi me gari ya bamu ita mu raeneta yanzu, idan ta girma mu zamu more ta, dan kuwa zata zame mana JARI ne"


Sanadin Kaddarata na kudi ne akan kudi N300kcal, Amma yanzu zan baku the whole Sanadin Kaddarata (the beginning) Free ne, da zarar mun gama Free pages zamu cigaba da tafiya ne da wad'anda sukayi payment kawae, Zaku iya fara payment naku tun yanzu in case muna gama Sanadin Kaddarata (the beginning) mu dora tafiyar cikin Sanadin Kaddarata (the conclusion).

Ki tura kudin ta cikin wannan account din👇

8124818273
Zahra Yusuf Ishaq
Opay Bank

Shedar biya ta wannan number 08124818273

Idan katin waya ne screenshot se a tura ta wannan number 08124818273

En niger kumin magana ta 08124818273 se muyi magana

Mhiz Innocent.........✍️






https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_2

_____Wani mayaudarin murmushi malam habu ya saki yana jinjina kae

"Lallae gaskiyane habi matar habu, ni dama nasan ke din ta dabance akwae kwanya" ya fad'a yana nuna saetin kansa, jin yadda ya fasa mata kae ya sanyata itama ta saki murmushin tana bubbude hanci ita a dole tayi abin kirki

"Kasan dae ba'a bori da sanyin jiki, abinda ya kamata muyi yanzu muyi sauri mu wuce wajen me gari, kar a samu wani me irin tunaninmu ya riga mu kar'barta" Da sauri malam Habu ya mi'ke yana fad'in

"Maza d'auko gyalenki muje, ba sanya" Habi ta mi'ke tayi cikin d'aki, se gata ta fito d'auke da wani yalolon tsohon mayafi ta fito tana yafawa sannan suka bar gidan.

Kae tsaye gidan me gari suka wuce, malam habu yayi sallama aka shàeda masa me gari na nan fitowa, suna nan tsaye duk sunyi shiru kowa da abinda yake sa'kawa, ita dae habi shirun nan da tayi tana tsara abinda zata fad'awa me gari ne, sedae kafin ta gama tsarawar muryar kamilallen tsohon ta cika mata kunne, seta d'ago da sauri kamar mara gaskiya, malam Habu suka gaesa da me gari cike da ladabi sannan suka nemi waje suka zauna

"Nima yanzun nan na shiga cikin gidan, ashe ma kuna hanya" me gari ya fad'a cike da kulawa, malam Habu yayi 'kasa da kae yana jinjinawa sannan yace

"Gaskiyane ranka ya dade, Allah ya 'kara girma"

"Ameen" habi dake kusa dashi ta amsa, gyara zama me gari yayi kafin yace

"Me yake tafe daku ? Allah yasa lafiya" Malam Habu ya tsiri gyara zaman da babu gaera babu dalili se kuma can yace

"Wato ranka ya dad'e dama akan maganar nan ce..ta.. ita yarinya da aka tsinta..toh shine me d'aki na take neman alfarma idan babu damuwa a bamu ita seta raeneta..." Numfashi me gari ya ajje yana jinjina wannan al'amari sannan yace

"Allah sarki, Allah ya saka da alkhaeri ya bada ladan niyya, amma sedae wani hanzari ba gudu ba...wannan yarinya dae yanzu ma base anjima ba wajen 'yan sanda zamu mi'kata in yaso sesu 'karasa bincike, dan kuwa mudae munyi namu" Kawae se habi ta fashe da kuka

"Allah sarki baewar Allah, wallahi me gari idan har akayi bincike ba'a gano iyayen yarinyar nan ba gidan marayu zasu kaeta, kuma gani ni har yanzu ban samu yarinya mace ba shiyasa nake kwad'ayin raenon baewar Allahr da ba taji ba bata gani ba ranka ya dad'e" ta 'karasa fad'a tana matse 'kwalla, Shiru me gari yayi bece komae ba, jin hakan ya sanyata d'orawa da fad'in

"Yalla'bae a tausayamin a bani yarinyar nan, In Sha Allah zan kula da ita kamar d'iyar cikina babu algus"

"A taemaka ranka ya dad'e" malam Habu ya fad'a kansa a 'kasa, Me gari ya sauke wata 'katuwar ajiyar zuciya yace

"Shikenan, In Sha Allah zamu baki ita amma fah se anyi yarjejeniya, kuma ki tabbatar kin cika abinda kikayi al'kawari" Ita dae bama jin me gari take ba tun daga kalmar farko daya fada taji wani dad'i na ratsa ta, bata tsaya taji maganganunsa da suka biyo baya ba...Daga nan me gari ya shiga gida ya yiwa uwar gidansa bayani, da farko ta nuna rashin jin dad'inta akan hakan se kuma daga baya daya fahimtar da ita sannan tayi fatan alkhaeri akan hakan, daga lokacin aka d'auki baby girl d'in aka mi'kawa habi ita cikin matu'kar birgewar yadda ta yadda zata ri'ke yarinyar da uwar data haefeta ma ta kasa ri'keta, da sharadin zata kula da ita amana da tsoron Allah, a haka dae habi ta amince ta kar6i jaririyar cikin farin ciki, dukka akayi wannan yarjejeniyar a gaban aminin me garin, seda suka zo tafiya me gari ya kalli malam Habu yace

"Wanne suna za'a dinga kiranta dashi ? Malam Habu ya kalli habi yace

"Tunda kece uwarta yanzu wanne suna kika za'ba mata ? Se tayi shiru can kuma seta d'ago da murmushi kwance kan mayaudariyar fuskarta tace

"SAYAQULU !! Cikin rashin fahimta me gari ya kalleta yana maemaeta sunan a bakinsa, ita kuma ta sake jinjina kae tana murmushi kanta a wajen jaririyar da take ri'ke a hannunta wadda na lura da tun d'azu take kallan wani waje a jikin yarinyar amma bansan me take kalla ba, me gari ya girgiza kae yace

"A'ah, a kirata da AZRAH, Allah ya raya ta bisa sunnah, ya baki ikon ri'keta da amana"

"Ameen" Malam Habu ya amsa dan kuwa hankalin habi sam baya wajen......

"Wae kasan mena gani kuwa a yatsan yarinyar nan ? Habi ta fada da wani irin mad'aukakin farin ciki akan fuskarta, Malam Habu yace

"A'ah sekin fad'a"

"Wallahi gold ne a yatsanta malam" Zabura malam Habu yayi se kuma ya fara 'ko'karin gyara tsaewatsa tunawa da yayi akan hanya suke yace

"Don Allah d'ago 'kafa muje gida, kada mutane su lura da abinda ke faruwa" Ita dae habi jikinta har rawa yake ta 'kara sauri a haka har suka isa gida, malam Habu ya kalli habi dake 'ko'karin ciro zoben dake hannun babyn wadda ta fara mutsu mutsu tana kwa'be fuska, habi bata bi ta kanta ba ta ciro zoben, dae_dae lokacin da babyn ta saka kuka me 'karfin gaske, habi ta kalli malam Habu ba tare data lura da kukan da jaririyar keyi ba dan hankalinta gaba d'aya ya tashi akan zoben nan tace

"Ka gani wallahi shine" ta fad'a tana nuna masa gami da taka rawa, se yayi dariya

"Wato har kullum ina 'kara jaddada miki kwanyarki ta daban ce" Habi ta wani juya ido

"Ka bari kawae malam, yanzu ya zamuyi da wannan zoben, kasan faaa...." Maganar ta ta ta katse sanda azrah ta sake sakin wani kukan, habi ta 'bata fuska

"Toh bismillahi yanzu fa za'a fara" se tayi wajen jaririyar ta d'auketa ta fara jijjigata

"Don Allah ki mana shiru hakan nan" ta fad'a kamar jaririyar na jinta, kamar zugata takeyi aekuwa ta sake sakin sabon kuka tana wawurar hannayenta wanda hakan ze nuna maka yunwa takeji, Allah sarki baewar Allah, ita dae habi cigaba tayi da jijjigata tana kallan malam Habu tace

"Malam samo mana

Please Login or Register in order to submit comment