Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kunu mana kafin a siyar da zoben nan, se a samu a samo mata wani abin koh ? Itama seta ta'ba" Wata dariya malam Habu ya saki yace

"Lallae ma habi ! Kin ta6a ganin inda jariri yasha kunu ? Wallahi ban ta'ba ji ba" Harara ta jefa masa kafin tace

"Toh ae se kaje ka samo mata madara idan kana da kud'in, ni dae bani dashi" Shiru yayi secan kuma yace

"Bari a kar'bo bashin madara in yaso se a saka a kunun da za'a bata din, kawo zoben ki gani zanje na siyar se a biya me madarar" Mi'ka masa tayi tana fadin

"Don Allah kayi sauri kafin kunne na ya kulle" Mi'kewa yayi ya fita daga gidan, ita kuma ta cigaba da rarrashin azrah tana yi tana mita se kace tana jinta..... Wajen mintuna 20 sega malam Habu ya dawo hannunsa dauke da koko a leda da madarar jarirae ya mi'kawa habi, ta kar'ba kana ta mi'ka masa babyn ya kar'ba, ita kuma ta 'karasa malallauta ta d'ebo ruwa ta tsoma kokon a ciki sannan ta had'a madarar ta had'esu waje 1 a cikin cup sannan ta 'karaso ta kar'bi babyn, a hankali ta d'ebi kokon da cokali takai bakin babyn dahar yanzu kuka take, jin alamar abu na shirin shiga bakinta yasa takae cafka ta sha abinda habin ke bata, wani irin zabura tayi ta fara wani abu kamar zata shid'e se kuma ta fara kuka kamar ranta ze fita, kuka take sosae tanayi tana 'karawa, Habi taja tsaki tace

"Yau na shiga 3 baban ilyasu" Dariya ce ta 'kwace masa yace

"Babu wani shiga 3, wannan yarinyar ae zuwanta alkhaeri ne gidan nan, ba kiga daga zuwanta ga abinda muka samu ba, ahh nikam banga abin tashin hankali ba dan kuwa Allah kad'ae yasan nawa zamu siyar da zoben nan" Ita dae Habi ba tabi ta kansa ba ta koma ta had'a madara da ruwa me dama dama sannan ta bawa babyn, Allah sarki aekuwa gaba 1 wadda ta had'a matan seda ta shanye ta tass sannan ba'a jima ba bacci ya kwasheta...

Tun daga ranar ya kasance duk bayan kwana 5 se me gari ya tako 'kafa da 'kafa zuwa gidan yaga lafiyar azrah, yadda dae yake gani babu wata matsala kuma shima yakan taemakawa da wasu abubuwan wanda azrah d'in zata bu'kata, bayan sun siyar da zoben nan sun samu kud'i masu yawa, seya kasance suna siya mata madara a cikin kud'in sedae tana da wata 1 a duniya suka yayeta daga shan madara suka koma mata wani had'in gargajiya, acewar Habi basu kar'bota dan suyi jegon jaka ba, madarar ma data sha a baya Allah ya amfana.....Tana da shekara 2 a duniya, wata rana garin aka tashi da mutuwar data girgiza mutan garin wato mutuwar me gari sakamakon zazza'bi da yayi na kwana 2, mutane sunji mutuwar mutumin me tarin dattako da mutunci, Sedae fatan Allah ya gafarta masa, Wannan shine silar sake shigarta wani halin......Duk da mutuwar me gari hakan be hana uwar gidansa zuwa gidan Habi ba tana duba lafiyar Azrah, itace kan kawo mata kaya musamman idan yaranta suna so su bayar da kaya ko kuma 'ya'yan 'yan uwanta dake birni sun kawowa 'ya'yanta seta d'auka a ciki ta kaewa Azrah, Cikin hakane itama uwar gidan me garin ta tashi komawa garinsu dan dama ba 'yar garin bace, lokacin da zata tafi Azrah ba wani wayo gareta ba dan haka bata wani damu ba ko irin kukan kewa d'in nan duk batayi ba, ita dae ta kawo mata kaya masu yawa sanda zata tafi d'in haka ta tafi tabar Azrah d'in cikin kewa dan haka kawae take jin 'kaunar yarinyar a cikin jikinta...


Lokacin data fara wayo shine ta fara fuskantar lallae akwae 'kalubale a rayuwarta, akwae wani babban al'amari a rayuwarta dan kuwa har lokacin wata makarantar boko bata santa ba, haka makarantar islamiyya itama bata santa ba, and bata san meyasa ba idan ta fita babu wanda yake son ra'barta, babu wanda kesan yayi wasa da ita, koda ta fita d'in sedai ta zauna a gefe tana kallansu suna wasansu gwanin birgewa amma ita bata da damar shiga cikinsu.

.....Tana zaune kamar koda yaushe tana kallan yara sa'anninta suna wasa ita dae tana daga gefe ta d'ora kanta akan cinyarta, wata yarinya da itama ba zata wuce sa'arta ba ta matso kusa da ita tace

"Azrah ki taso muyi wasan kema" Seta saki murmushi tana mi'kewa tana fad'in

"Toh, amma bansan mena musu ba ko naje wajen korata suke" Hauwa'u ta janyo hannunta tana fad'in

"Muje ba wanda ze koreki" Suka fara tafiya zuwa wajen yaran hannun Azrah a cikin na hauwa'u

"Ke !! Hauwa'u ! Sukaji wata murya ta fad'a cikin d'aga murya, Hauwa'u ta juya jikinta na rawa tana kallan mahaefiyarta

"Cika ta ! Ashe baki da hankali ? Uban me zaki mata da kike ri'ke da hannunta ? Kamar hauwau zatayi kuka tace

"Inna kinga kowa baya son Azrah ta shiga wasansu, sedae tayi ta kallansu a gefe..."

"Ubanki ! Nace ubanki kinji !! Ke mahaukaciyar inace ? Toh uwar data haefeta ma bata sonta ta kasa ri'keta seke ? Yoh waye zeso zama da shegiya ? Dallah wuce muje kafin na 'ba'b'ballaki" ta fad'a tana kaewa hauwau duka wadda tayi saurin yin gaba kafin dukan mahaefiyarta ta ya same ta...Tunda ta fara magana Azrah ke kallanta babu ko 'kiftawa tana magana ne tana rarrabe duk abinda take fad'a d'in, ba tun yau ba, ba tun yanzu ba mutane da dama sunsha kiranta da shegiya, tun bata san me kalmar shegiya ke nufi ba har tazo ta fahimci lallae koma me ake nufi da shegiya wani mummunan abu ne, ba babar hauwau ba hatta inno mari'kiyarta bata barta ba wajen yi mata gori da zarar tayi wani abun ba dae_dae ba, maganar "Uwar data haefe tama bata sonta ta kasa ri'keta waye ze sota ? Toh waye zeso shegiya ? Wannan maganar ta zame mata kamar wani abu me muhimmanci dan kuwa kusan kullum se an fad'a mata shi, idan bata jishi daga wajen wannan ba toh wata zata fad'a mata, danma bata da wayo ne sosae a yanzu ae da tuni ta yayewa fita wajen kodan gudun 'bacin rae, sedae baga mutanen waje ba har cikin gida ma gorin ake mata, bata san dalili ba, bata san meyasa ba, shin meta aekata ne haka me muni da kowa baya sonta ? Ko kuwa tana da wani aebu ne wanda bata sani ba ?ita dae abinda kawae ta sani shine ta tashi ne da zazzafar 'kiyayyar wadda ta haefeta, tun bata jin komae lokacin da bata da wayo har yakae a hankali tana 'kara wayo tsanar matar data kawota duniya na 'karuwa a cikin ranta, kuma tsanar na 'karuwa ne da gudummawar 'yan garinsu...... Tun tana da shekara 6 habi ta fara bata tallan 'kananan abubuwa a cikin 'karamin bokiti, babu karatu a al'amarinta ita dae kawae ayi mata ciniki...Haka rayuwarta ta cigaba da tafiya tana fita tallah ne tun 'karfe 10 na safe ba ita ke dawowa gida ba se sanda ta siyar da duk abinda habi ta d'ora mata, duk ranar kuwa data sake ta dawo mata ba tare data siyar da abinda ta fita dashi ba, zagi cin mutunci gori shine ke biyowa baya, tayi ta fad'a kamar zata ari baki, ita dae Azrah sedae tayi shiru tana jin duk abinda take fad'a din....Wannan shine TUSHEN LABARIMMU yanzu zamu shiga cikin aenahin LABARIN.....

______"Azrah ! Azrah" Habi ta fad'a cikin d'aga murya sannan ta d'ora da fad'in

"Wae uban me kike a d'aki har yanzu baki fito ba ! Ko tallan ne ba zaki ba ? A hankali nakae duba na zuwa cikin d'akin da Azrah d'in ke ciki wadda ke zaune hannunta ri'ke da kibiya alamar tsifa take, da sauri ta yayimi d'an kwalinta dake gefenta ta yafa akan nata sannan ta mi'ke cikin wata irin murya me sanyi tace

"Shiryawa nakeyi inno" Ta fad'a dae_dae lokacin data fito daga cikin d'akin da take kwana wanda ya kasance ba d'aki bane, irin wani waje ne da yake tsakanin d'akuna 2 toh akwae rufi a wajen se kawae ya zama kamar d'aki wanda take kwana a ciki amma ta samu ta saka wani zani a matsayin labule, Kyakykyawar yarinya ajin farko fara tass da ita me ido dara dara da dogayen gashin ido, dogo kuma siririn hancinta d'os dashi akan doguwar zagayayyiyar fuskarta sed'an 'karamin bakinta pink sosae kamar wadda take shafa masa jan baki sedae ba haka bane haka lips d'inta yake, kallan farko kana yi mata zaka gane lallae indae kyau ake nema aka zo wajen nan an tashi, sedae idan kayi duba zuwa kayan jikinta shi kadae ne ze sanya ka fahimci ita d'in wacece, dan kuwa wata kod'ad'diyar atamfa ce a jikinta wadda taji jiki sedae a wanke take fes fes kasancewar mamallakiyar kayan me tsafta ce...A hankali cikin takun nutsuwa ta sako kanta zuwa tsakar gidan nasu, se tayi baya ganin ba inno kad'ae ce a tsakar gidan ba tana tare da wani matashi ne, hakan yasa ta janyo mayafi ta yafa akanta, duk da 'kirjinta babu komae amma tafi ganewa ta suturtashi d'in, dan haka ta yafa mayafin ta rufe jikinta sannan ta fita, kae tsaye ta 'karasa tana kallan inno ta tsuguna cikin sanyi tace

"Kitson kaena ne ya tsufa shine nake tsefewa"

"Wannan kuma keta shafa, nidae abinda na sani kawae shine kisan yadda zakiyi ki siyarmin da kayan siyarwa kafin ki dawo" Seta mi'ke tana fad'in

"Tohm" lokaci guda tana gyara zaman mayafin dake kanta wanda ke 'ko'karin zamewa, hakan ya bawa sassalkan gashin kanta me santsi damar bayyana wanda har besan sanda ya furta

"Kambu ! Se a lokacin Azrah ta tuna taga wata halitta a zaune seta juya ta kalleshi tace

"Ina wuni" Wani irin kallo yake binta dashi wanda ita bata ma lura da hakan ba ta mi'ke ta koma zuwa cikin d'akin, ya bita da wani mayataccen kallo yana bin mazaunanta da kallo wanda kasancewar mayafin be rufe su ba yasa yana iya hango yanda suke motsawa kad'an, se yayi wani baya yana sauke wani numfashi, Habi dake lura dashi ta jefa masa harara

"Kaee ! Ilyasu meye hakane ? Shiru yayi yana kallan d'akin da Azrah ta shiga, can se gata ta fito da hijab taje ta d'auki bokitin alala dana shinkafa da wake ta fice daga gidan, se a sannan ya juyo da kallansa wajen habi yace

"Inno wacece wannan ? Ta6e baki inno tayi kafin tace

"Ash sha ! Na manta ashe sanda abin ya faru baka nan" Nan ta fad'a masa abinda ya faru, Murmushi ya su'buce masa yana shafa kumatunsa da babu komae a jiki yace

"Ahh lallae inno kin iya kiwo wallahi, irin wannan zazzafa haka, kuma wae a cikin gidammu ? Lallae kice na dawo a dae_dae" ya 'karasa fad'a yana sakin wani murmushin gefen baki.....

Mhiz Innocent..............✍️




https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*

..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_3

_____Wani kallo inno ta watsawa ilyasu kamin tace

"Ka dawo a dae_dae d'in me ? Kaaga idan zaka d'auke kanka daga kan wannan yarinyar ka d'auke bansan iskanci" Shi dae shiru kawae yayi yana tunanin halittar Azrah dan ba kad'an ba ta tafi da imaninsa.... Wajen 'karfe shida ta fito daga ban d'aki hannunta d'auke da buta ta tsuguna tayi alwala sannan ta wuce d'akinta, tayi sallah sannan ta d'auki 'yar 'karamar jakarta da take zuwa da ita makarantar dare wadda ita kad'ae take zuwa bayan ita se kuma tallah, tana fitowa tsakar gidan ta tadda malam Habu ya dawo yana zaune kan tabarma da kwanon abinci a gabansa wanda da alama yanzu aka ajjiyeshi, A hankali kuma cikin sanyi ta kallesu su duka tace

"Baba, Inno na tafi" ta fad'a badan tana neman suyi mata addu'a ba dan bata saba da jinta ba, ta dae fad'a ne kawae dan kar tayi laefi, Inno dake gaban murhu tana kashe wuta ta mi'ke tana kallanta sannan a yatsine tace

"Ke har yanzu babu wani alhajin da yace yana sonki ? Seta gyara zaman jakar dake hannunta ba tare da tace komae ba kanta a 'kasa dan bata masan amsar da zata bayar d'in ba

"Wae nikam ba dake nake ba ? Inno ta fad'a tana ri'ke ha'ba, Da sauri ta girgiza kae kana a sanyaye ta d'aga kae tana fad'i a hankali

"Ehh Inno"

"Na rabaki da saka wannan shegen hijabin, amma kin'ki ji, uban waye ze ganki a haka yace yana sonki ? Shegiya kullum tana fama zungwui zungwui da hijab" Inno ta fad'a tana kae mata duka, sannan ta d'ora da fad'in

"ke a dole kamilalliya, yoh uwarki ma tanbadad'd'iya ce gwara ma ki saki jikinki ah tohh" Idan da sabo ta saba dajin irin wad'annan kalmomin daga wajen Innon, sedae har yanzu zuciyarta ta kasa sabawa, zuciyarta me rauni ce ta yadda duk sanda irin haka ta faru seta karye, a hankali taji wasu zafafan hawaye sun zubo mata a kuncinta, ba tare da tace komae ba tayi gaba ta fice daga gidan, shi dae baban ilyasu abincinsa kawae ya keci yana ci yana sauraran gidan radio hankali kwance abinsa......Tafiya take tana kuka mara sauti zuciyarta kamar zata faso 'kirjinta, a kullum kwanan duniya duk adadin yadda aka aebata mahaefiyarta toh haka tsanarta take ninkuwa a cikin ranta, Tana ta kukan a haka harta 'karasa makarantar... A dae_dae kan wani dakali na hangi wata matashiya wadda itama ba zata wuce 15 years ba zasuyi sa'anni kenan da Azrah, wajen Azrah ta nufa bayan ta share hawayenta, tana 'karasawa ta zauna, hauwa'u ta kalleta tace

"Lafiya dae koh Azrah naga yau harna rigaki zuwa ? 'Dan murmushi kad'an ta saki sedae ta kasa cewa komae, hauwa'u ta kamo hannunta tace

"Ki fad'amin kinji, meya faru ? Akwae wata matsala ne ? Bata san sanda kukan ya sake 'kwace mata ba ta fad'a jikin hauwa'u tana raerawa, itama hauwa'un bata hanata ba sema ri'keta da tayi sosae a jikinta tana jin yadda take kuka kamar ranta ze fita.. seda ta gaji dan kanta tayi shiru sannan ta d'ago tana kallan hauwa'u wadda ke fad'in

" Ya isa haka ! Fad'amin !

"Bansan meye laefina a game da zuwana duniya ba hauwa'u, meyasa abubuwa da dama suke faruwa ? Mahaefiyata ta jawomin abin magana ta cuceni ta zalunceni, bazan ta'ba yafe...." Hauwa'u tayi saurin rufe mata baki

"Ya isa haka Azrah, komae yayi zafi maganinsa Allah, ki cigaba da addu'a In Sha Allah watarana komae ze wuce kinji" Wani murmushin ya'ke wanda ake cewa yafi kuka ciwo Azrah tayi sannan tace

"Bana son na yaudari kaena hauwau kuma kema kibar yaudarar kanki, wace rana ce wannan ? Ke a tunaninki zatazo ??

"In Sha Allah soon" hauwau ta fad'a tana sharewa Azrah hawayen dake kwance fuskarta

"Ohk ya isa haka, yanzu dae a'ina muke ? Hauwau ta fad'a tana janyo jakar Azrah, ta janyo wani littafi ta fara dubawa sannan ta d'akko wani daga cikin Jakarta ta fara koyawa Azrah abinda ke cikin littafinta ( Haka suke kullum, duk abinda aka koyawa hauwau a makarantar boko ko islamiyya idan sukazo makarantar dare seta koyawa Azrah shi, shiyasa suke fitowa daga gida da wuri kafin lokacin da ake shiga makarantar, a wannan lokacin ne take samun damar koya mata wasu abubuwan idan basu samu damar gamawa ba washe gari sesu 'karasa ).



Nassarawa G.R.A....
Kano state...
Nigeria..

______'Katon parlour ne wanda ya amsa sunansa parlour dan kuwa ko ba'a fad'a ba kallo d'aya zaka masa kasan cewa lallae fa an kashe kud'i wajen tsarashi, Komae na cikin d'akin brown da milk ne, yasha ado sosae mara hayaniya amma fa me d'aukar ido, daga gefen d'akin a 'kasa wani tan'kamemen photo ne a ajje window size wanda ke d'auke da hoton wani farin bafullacen babban mutum, kallo 1 zaka masa kasan lallae kud'i sun zauna masa dan kuwa kwanciyar hankalin da yake ciki itace ta 'boye aenahin shekarunsa wanda a kallo 1 baka isa ka fad'i aenahin shekarunsa ba, daga 'kasan hoton an rubuta da babban ba'ki ALHAJI KABEER TAJUDDEEN...Daga gefen d'akin kusa da kujera 2sitter wata mata ce wadda a shekaru ba zata wuce 48 ba zaune akan hannun kujerar, sedae itama saboda yanayin da take ciki yasa idan ka kalleta zaka iya kiranta da 'yar shekara 40..Can kuma daga kan babbar kujera wata kyakykyawar farar tsohuwa ce zaune akae, kana ganinta kaga Fulani sakk sannan jikinta irin d'an 'karamin nan ne...Wajen second 10 ba wanda yace komae se can tsohuwar ta furta

"Wae nikam hadeeza haka kika bar yaron nan ya lalace ? Dubamin fa lokaci yanzu 'karfe nawa ? Kodan bake kika haefeshi ba" Wadda aka kira da hadeezan ta maraeraece fuska da alama bataji dad'in maganar tsohuwar ba

"Wallahi yakumbo bansan meya zaunar dashi haka har yanzu ba, amma ina tunanin wani abu me muhimmanci ya ri'keshi" Yakumbo ta jinjina kae tana fad'in

"Lallae"

.....Cikin gudun daya saba dashi yake driving zuwa cikin 'katuwar harabar gidan, kae tsaye wajen da aka tanada dan parking ya nufa ya ajje had'ad'd'iyar motarsa sannan ya kasheta, seda ya shafe wajen mintuna 2 sannan ya kulle motar ya fara 'ko'karin fitowa, cikin wani irin taku na 'ka'k'karfen namiji yake takawa zuwa cikin aenahin ginin gidan, dogo ne fari kyakykyawa ajin farko, ba shida jiki sosae seda yanayin yadda jikinsa ya saba da d'aga 'karfe yasa jikin nasa ya kasance murd'ad'd'e ne sosae, yana da dogon hanci siriri da wasu lumsassun idanu wanda na gaza yadda cewar ba yana sane yake lumshesu ba, wuyansa d'auke da wata sar'ka plane irinta maza amma fa daga ganinta kasan an kashe kud'i wajen siyarta, Sanye yake cikin wasu 'kananan kaya riga da crazy jeans, 'kafarsa sanye da takalmi sau ciki d'an ubansu.. DON ADNAN kenan.. A hankali ya 'karasa cikin part d'in mamin tasa ya tura 'kofar parlourn, se yayi turus yana kallansu su duka, se kuma a hankali da sassarfa ya 'karasa wajen mami a hankali cikin muryarsa me dad'i kuma a hankali wanda 'karya ne wanda yake kusa dashi yaji abinda ya fad'a d'in inba mamin ba yace

"Mami..wani abun ya faru ? Yayi maganar kamar baya so fuskarsa babu yabo ba fallasa, Mami ta kalli Yakumbo sannan ta dawo da dubanta wajensa tace

"Ta kaasa bacci saboda baka dawo ba" Fuskarsa da babu annuri ya sake d'inkewa kamin ya kalli inda tsohuwar take zaune sannan yace

"Ta kaasa.." Ya fad'a a gajarce, Mami ta jinjina kae, Seya ta'be baki cikin halin ko in kula yace

"Babu wani abun birgewa"

"Noo...Son..atleast ta nuna damuwarta akanka plss greet her uhmmm" Mami ta fad'a tana kallansa sosae, Shafa sumar kansa yayi yana lumshe lumsassun idanunsa

"Yaron goye ne ni mami ? Bansan irin wannan takurar, yaushe ma 'karfe 12 ta wuce ? Ya fad'a yana sauke numfashi ransa a 'bace

"Is ohk, Is ohk zamuyi maganar but plsss yanzu go and greet her in ba haka ba laefina zata gani" Mami ta fad'a a hankali, Bece komae ba yayi gaba ya kalli Yakumbo dake zaune kan kujera tana karatun qur'ani a zuci, kallo 1 ya mata ya d'auke kae

"Kin yini lafiya" ya 'karasa fad'a yana wucewa wani d'aki dake cikin parlourn mamin, Yakumbo ta d'ago kae ta kalleshi tana jinjina kae kamin tace

"Lallae kabeeru seya tashi tsaye akan wannan yaron dan ana kallan 'kwayar idanunsa anga na meshan 'kwaya, yanzu dama har yanzu be dena saka wannan sar'kar ba ? Allah ya shirya mana zuri'a amma kome ya faru dan ba'a gaban uwarsa ya tashi bane, amma dae tunda yanzu nazo komae ze daedaeta" Yakumbo ta fad'a fuskarta a had'e, Ita dae mami ba tace komae ba tabi don da kallo wanda ya shiga d'akin, A hankali ya tura 'kofar d'akin ya shiga idanunsa akan yaron dake kwance akan bed yana bacci hankalinsa kwance, baze wuce 17years ba, Adnan ya zauna a gefen gadon yana kallan beloved brother d'in nasa se kuma can ya bashi kiss a goshi sannan ya mi'ke ya fito daga d'akin, ko kallan inda Yakumbo take beyi ba ya 'karasa wajen mami yana fad'in

"Gud night mami" daga haka ya fice daga d'akin..Itama Yakumbon bata sake cewa komae ba ta mi'ke ta wuce 'bangaren data saba sauka indae tazo gidan..

____Washe gari da safe wajen 'karfe 7 ya shigo part d'in mami, kae tsaye dinning area ya wuce ya zauna yana fito da wayarsa ya fara dannawa, Wata farar mata kyakykyawa wadda ta 'karaso hannayenta d'auke da kuloli ta ajjiye akan dinning d'in tana kallan don tace

"Barka da safiya ranka ya dad'e" Be d'ago daga danna wayar da yake ba, dama kuma tasan ba d'agowar zeyi ba ya cigaba da dannawa sannan a hankali yace

"Barka" Dukda a shekaru ta girme masa sosae dan kuwa zata kae 35years yayinda he is just 25 amma besan shine ya dace ya gaesheta ba ita ba, Shi dae tunda ya tashi besan wani abu wae girmama na gaba dakae ba a haka aka d'orashi, abinda ya sani kawae shine yana saman kowa dole a girmamashi musamman tunda suna da kud'i dan kuwa mahaefinsa Alh Kabeer shahararren me kud'i ne a cikin garin na kano...Kamar koda yaushe ya tsakuri abincin sama sama sannan ya mi'ke yana d'aukar sandar cricket d'insa dake ajje gefensa ya fara 'ko'karin fita, dae_dae lokacin fawaz ya sauko daga stairs sanye da jakar goyo ya 'karaso kyakykyawar fuskarsa d'auke da murmushi dan kuwa suna kama da don ne ya 'karaso ya rungumeshi yana fad'in

"Barka da safiya bhai" Karan farko kenan da naga wani sassanyan murmushi ya wanzu akan fuskar adnan d'in, wani irin shahararren kyau ya bayyana, da yasan yanda murmushi ke masa kyau da se ince kullum ya kasance cikin yinsa, ya rungume 'kanin nasa kamar me rad'a yace

"Barka boy" Fawaz ya d'ago yana kallan dinning sannan ya dawo da dubansa kan adnan yace yana maraeraece fuska

"Wae kayi break ? Gyad'a kae don yayi kamin yace

"Ina sauri ne, zanje training.."

"Aou dama a irin safiyar nan kake fita amma baka dawowa se cikin talataenin dare ? Suka tsinci muryar Yakumbo tana fad'a sanda take shigowa d'akin, Ko kallanta don beyi ba hasalima kallan agogon hannunsa yayi, da gudu Fawaz ya tafi wajen kakartasu ya rungume ta yana fad'in

"Saukar yaushe Yakumbo ? Murmushi tayi tana fad'in

"Jiya da dare, sanda nazo kayi bacci" Fawaz yace

"Bari nayi sauri naje na dawo daga skul yau akwae hira Yakumbo sirina ta" ya fad'a yana she'kewa da dariya, ita bama ta jishi ba dan hankalinta nakan don da yake 'ko'karin fita daga d'akin, Da sauri tace

"Karka kae dare yau kam ka tuna ina cikin gidan, kuma shima kabeerun yau ze dawo" Kansa ya dafe dan harga Allah surutunta ya fara isarsa yana neman saka masa ciwon kae, Ya juyo ya watsa mata shanyayyun idanunsa da suka 'kara shanyewa a hankali yace

"Hayaniyarki na neman sakamin ciwon kae, plss allow me to rest" ya fad'a yana barin parlourn, da ido ta bishi ta kasa cewa komae, Fawaz yabi bayan yayan nasa..A compound suka had'u don ya kalli Fawaz yace

"Ba zakayi break ba ? Turo baki yayi yana sosa kae

"Am full" ya fad'a yana shafa cikinsa..Kafin ya kaega cewa komae wasu motoci wajen guda 4 suka fara shigowa harabar gidan, seda suka gama parking sannan bodyguards d'in mahaefinsu suka fara sakkowa d'aya bayan d'aya kafin daga bisani Alh Kabeer Tajuddeen ya sakko dukda haka bodyguards d'in basu bar kusa dashi ba, Fawaz ya 'karasa ya rungume dad yana fad'in

"I miss u dad"

"Miss u my boy" dad ya fad'a yana shafa bayan Fawaz, A hankali don ya 'karasa wajen dad kansa a 'kasa yace

"Welcome dad" Binshi da kallo Alh Kabeer yayi se kuma yace

"Ina son ganinka yanzu" Daga haka yayi gaba, don ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalli dad seya sauke ajiyar zuciya yana d'auko wayarsa dake ringing ya kaara a kunnensa, daga d'aya 'bangaren akace

"Don..." Bece komae ba yayi shiru yana sauraron me wayar lokaci guda yana tafiya zuwa part d'in dad d'in nasa, daga

Please Login or Register in order to submit comment