Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'akin Innon ta sauketa kasancewar da rana a tsakar gidan, Inno ta kasa zama, se ina naka saka ina naka aje take da Hajja kaltum d'in, har seda Hajja kaltum d'in ta gaji tace

"Ki zauna haka nan..sauri nake fa" se a sannan Inno ta 'karaso ta zauna tana fad'in

"Sannunki da zuwa hajiya, ya gida? Hajja kaltum tace

"Alhamdulillah, na sameku lafiya?

"Ahh mukam alhamdulillah, yau na ganki ke d'aya?" Hajja kaltum tace

"Wallahi kuwa, yauma dae da sa'ko nake tafe"

"Toh Allah dae yasa lafiya" Inno ta fad'a tana gyara zama, Hajja kaltum tace

"Hajiya hadeeza tace na sanar dake gobe za'azo a kawo kud'i, kuma in sun kawo zasu saka rana, ko kwana nawa suka saka karku damu, sannan daga yau gaskiya ba lallae ki sake ganina ba, 'kila kuma se ranar da zamuzo mu d'auki yarinyar...sannan kuma tace na kawo miki wannan wayar" Hajja kaltum ta 'karasa fad'a tana bud'e jakarta ta ciro wata keypad ta ajje a gaban Inno sannan ta d'ora da fad'in

"Idan kina da wata bu'katar zaki iya kiranta da wannan wayar, numberta na ciki seki kirata, sannan akan maganar kud'i tace na sanar dake zata dinga aeko miki da kud'i akae_akae sedae idan wani abun ne kuma toh se ki kirata, sannan magana ta 'karshe..." Seta d'an dakata tana kallan yanayin Innon, sannan ta cigaba da fad'in dukda dae bata fahimci yanayin nata ba

"Na fad'a miki daga yau ba lallae ki sake ganinmu kafin bikin ba, idan ma mun had'u ranar bikin ba lallae mu samu damar tattaunawa kamar haka ba, shiyasa zan had'e miki duk wasu maganganu a yanzun nan...idan akayi bikin, kamar yadda ake kae amarya, toh babu bu'katar hakan, base kowa yaje ba saboda ba'a lokacin za'a kaeta gidan mijin nata ba saboda be gama gini ba, amma idan lokacin tarewartata yazo Hajiya hadeeza da kanta zata aeko a d'aukeki kuje akae amarya gidanta tare dake" Inno ta sauke ajiyar zuciyar jin wannan dogon bayani sannan ta karkace tace

"Toh madallah, shi angon zezo ne kafin kawo kud'in ko kuma kafin ranar d'aurin auren? Hajja kaltum ta kalli Inno sosae sannan tace

"Kada ki damu da se kinsan waye mijin, ko kuma kin ganshi wannan ba huruminki bane, idan kuma zaki tsaurara ne dole se kin ganshi, toh sena sani" Inno tace

"Ahh haba haba hajiya, kawae dae na tambaya ne kinsan fa ance matambayi baya 6ata" Hajja kaltum tace

"Hakane, yanzu dae seki sanarwa da Mae gidan zuwan masu kawo kud'i gobe, sannan idan akwae wata matsalar seki kira Hajiyar ta wannan wayar" Inno tana murmushi tace

"Toh babu damuwa, Allah ya kaemu" daga haka sukayi sallama Hajja kaltum ta tafi, duk wannan abinda yake faruwa baewar Allah Azrah bata san meke faruwa ba, bata san me aketa shirya mata ba, Allah sarki......



.......Washe_gari ranar data kasance juma'a Alhaji Kabeer Tajuddeen da d'an uwansa Alhaji Ahmad Tajuddeen da wani abokin dad d'in suka yiwa 'kauyen kima tsinke bayan la'asar, a soron gidan aka tarbesu da ruwa me sanyi kawae, Malam Habu da abokansa guda 2 sune suka kar6i kud'in, toh anyi sa'a maetar baban ilyasu bata fito fili ba saboda bashi ne yayi magana ba, ya bar abokan nasa ne sun wakilceshi, lokacin da suka ga kud'in da aka kawo gaba d'ayansu seda sukayi mamaki dan kuwa 300k suka ajje a matsayin kud'in saka rana wanda sukace sunzo ne da sati 2 dan Dad beyi duba da yanayinsu ko wani abun ba, a'ah kawae yayi duba ne da abinda shalelen d'ansa keso, toh kasancewar Hajja kaltume ta riga ta yiwa Inno magana akan masu kawo kud'i da kuma lokacin da zasu saka yasa ba suyi musu da sati 2n ba, sukayi na'am da hakan, daga haka sukayi sallama suka juya, kae tsaye bayan fitarsu companyn Don no 1 d'in suka wuce dukkansu a cikin motar Abba wanda shike driving, Dad na gefensa yayinda abokin Dad d'in ke zaune a baya, shi kam Dad Allah kad'ae yasan irin farin_cikin da yake ciki na wannan al'amari, ji yake kamar a mafarki wae Adnan ne zeyi aure, be 'karasa tunanin da yake ba ya jiyo muryar abokinsa Alhaji Usman yana fad'in

"Amma se nake ga kamar babu karamci a lamarin mutanen nan koh? Abba yace bayan ya d'anyi jim ya sake maeda hankalinsa kan driving d'in da yake

"Karamci kamar wanne kenan? Alhaji usman ya gyara zama sannan yace

"Da ruwa fa kawae aka tarbemu, anya kuwa?" Se a lokacin Dad ya magantu cikin yanayi na rashin jin dad'in maganar abokin nasa yace

"Karamci kuwa an riga da an gama mana shi, tunda suka d'auki ersu suka bamu, wannan kad'ae karamci ne" Alhaji usman yace bayan yayi ya'ke

"Ehh...ehhh hakane" daga haka be 'kara cewa komae ba har suka isa companyn... Basu suka bar companyn ba seda Dad ya tabbatar babu wata matsala sannan suka wuce gida.... 'Bangaren baban ilyasu kuwa bayan ya rabu da abokansa ya basu dubu biyar, seya shigo gidan da sauri cikin er d'aga murya yace

"Habee, maza maza fito, aeni se yanzu nasan zamu aurar da yarinyar nan, kae jama'a" ya fad'a yana 'karasa shigowa gidan, Inno ta fito daga d'akin ta tana fad'in

"Ka ganni se zulumi nake wallahi, ya ake ciki?" Yace yana jan kujera er tsuguno ya zauna

"Kar6i kiga ni" ya fad'a yana mi'ka mata kud'in hannunsa, Inno ta bud'e ido tana kallan kud'in sannan tace cikin er rikicewa

"Malam me nake gani haka?" Baban ilyasu yayi wata dariya yana sake gyara zama yace

"Kefa dad'i na dake abu kad'an ke rikitaki, toh kud'in auren wannan yarinyar ne, ki 'kirga ki gani" dae_dae lokacin data fito daga ban d'aki kenan, taso taji abinda baban ilyasun ya fad'a sedae bata bawa abin muhimmanci ba dan haka bata fahimceshi ba, kae tsaye ta wuce d'akin ta ba tare data kallesu ba, Inno ta bita da kallo sannan ta dawo da dubanta kan baban ilyasu tace bayan ta zauna

"Ni kam baban ilyasu don Allah ka fad'amin nawa ne, ina zan iya 'kirga wannan uban kud'in?"

"Toh dubu d'ari uku ne!!" Inno ta zaro ido tana sake kallan kud'in sannan tace bayan ta she'ke da wata dariya

"Oh ni ennan, wae don Allah da gaske?" Baban ilyasu yace

"Toh gashi nan kuwa kina gani" Inno ta saki wata gud'a tana fad'in

"Lallae kam muna da sa'a Malam, tun yanzu har mun fara kur6ar romon damokrad'iyya ina ga kuma nan gaba?" Ta 'karasa maganar tana sake sakin wata gud'ar, Yau kam farin ciki a wajen Inno da Baban ilyasu ba'a magana dan sukam gani suke kakarsu ta yanke sa'ka, tana kwance daga d'akin tana jiyo hayaniyarsu kad'an kad'an har daga baya ta jiyo muryar Baban ilyasu na fad'in

"Ke Azrah!!" Seta mi'ke daga kwancen da take 'kirjinta na d'an bugawa dan indae taji baban ilyasun na mata irin wannan kiran toh fa ba lallae lafiya ba, a sukwane ta mi'ke ta fita daga d'akin ta tsuguna nesa kad'an dasu tace

"Gani" Inno data fusata dan wannan miskilancin nata ya fara isarta, ehh tabbas tuntuni dama miskilace sedae yanzu ta 'kara zama miskilar ta gani kasheni tace

"Muma gamu...banda iskanci yanzu yarinyar nan mu zaki dinga yiwa wani nun'kufurci, mu d'in da muka rufa miki asiri muka yi miki abinda uwar data haefeki ma ta kasa miki koda kwatan_kwatan sane?" Runtse idanunta tayi tana jin yadda maganganun Innon ke sauka a cikin kunnuwanta kamar ana watsa mata dalma, bata ce komae ba ta cigaba da saurararsu, se ta jiyo muryar baban ilyasu yana fad'in

"Ya isa haka Habee, yau farin ciki muke, be kamata mu 6ata wannan ranar ba, kee" ya 'karasa maganar yana kallan Azrah, a hankali ta d'ago brown eyes d'inta da suka chanja colour ta saukesu kan baban ilyasu ba tare da tace komae ba, baban ilyasu ya d'auki kud'in dake kan cinyar Inno ya mi'kawa Azrah yace

"Kina gani koh?" Seta kalli kud'in sannan ta kalleshi seta jinjina kae, Inno takae mata duka

"Ki bud'e wannan munafukin bakin naki kiyi magana, se d'aga mana kae kike kamar wata bebiya" Azrah ta lumshe idanunta tana jin yadda bugun zuciyarta ke 'karuwa tace a sanyaye

"Ehh" baban ilyasu yace

"Yawwah, toh kud'in aurenki ne...wanda za'a gabatar da d'aurin auren nan da sati 2" Cakk taji numfashinta ya tsaya na wucin gadi, kunnuwanta sukayi wani dumm kamar wad'anda suke shirin kurumcewa, haka zalika ta nemi ganinta na en sakanni, seda 'kwakwalwarta ta dawo daga hutun rabin lokacin data tafi sannan ta samu damar kaewa numfashinta wata muguwar cafka, se a lokacin numfashin nata ya dawo da wani irin gudun daya wuce 'ka'ida, har lokacin tana kallan kud'in da baban ilyasun ya nuna mata a matsayin kud'in aurenta, kallansu take kawae zuciyarta na hasaso mata abubuwa da dama sedae ta gaza furta komae, can ta jiyo muryar Inno kamar daga sama

"Ki tashi ki bamu waje malama, dama zancen kenan, seki fara shiri dan ba'a cikin 'kauyen nan zaki zauna ba" A hankali ta mi'ke wani jiri na d'ibarta, seda tayi iya 'ko'karinta sannan ta iya kae kanta d'aki, tana shiga d'akin ta zube akan cinyoyinta wani kuka me tsuma zuciyar me sauraro na 'kwace mata, yi take tana 'karawa kamar zuciyarta zata fito, dan yadda takejin zuciyarta na wani irin zillo kamar tana shirin fitowa daga 'kirjinta, kanta ta kifa a 'kasan d'akin tana cigaba da kukan cikin rashin sanin abinyi "shikenan ta faru ta 'kare, yau kam ta tabbatar wad'annan mutanen da babu komae a zuciyarsu se kud'i sun sayar da ita ne, sun sayar da ita ga wani can me kud'i, dan daga yanayin yadda taga tumun kud'i a ajje tasan wannan kam kud'in da aka siye tane, kuma gashi suna mata maganar ba'a cikin 'kauyen zata zauna ba, wannan kad'ae ya isa ya nuna mata kud'in menene a gabansu, Shikenan itama kam ta shiga uku taga ta kanta, a koda yaushe rayuwa se juya mata baya take, rayuwa bata ta6a bin bayan ta ba kullum sedae ta juya mata baya" a hankali ta sake fashewa da wani marayan kuka tana kifa kanta akan cinyoyinta ta cigaba da rerashi cikin yanayi na rashin sauti.... Su kuwa Inno basu masan tanayi ba, suna can suna sha'aninsu da farin cikin kud'in da suka samu hankali kwance abinsu (_Allah ka rabamu da son zuciya da son kud'i irin na Inno da Baban ilyasu, wad'anda saboda kud'i ya rufe musu idanu ko tunanin ko siyar da ita zasuyi ne, basu ta6ayi ba, ko tunanin zasu mi'ka ta hannun mutanen da bana kirki ba, ko kuma wani abun makamancinsa, basu ta6a ganin mijin ba, basu sani ba wane irin hali gareshi shin mutumin kirki ne ko akasinsa, yaya yake, yaya halinsa yake, duk wannan baya gabansu...su dae kawae kud'i kud'i dae kawae, a wajensu kud'i ne kawae me muhimmanci, Allah ya kiyashemu aekin danasani).....



...........Tunda abin nan ya faru Mami bata sake bi takan Don ba, ta rabu dashi da maganar in yaso ta sanar dashi ranar d'aurin aure idan an kusa, shima kuma dama sabgogin gabansa kad'ae sun ishesa musamman ma akan wannan maganar dabe d'auketa da muhimmanci ba saboda haka yama manta da zancen..... Da sallama ta shiga d'akin Dad d'in hannunta d'auke da glass jug dake kan wani 'katon tire ta 'karasa ta ajje kan centre table sannan ta koma ta zauna tana jiran ya gama amsa wayar da yake, seda ya gama sannan ya juyo ya kalleta yace

"Sannunki da 'ko'kari"

"Yawwah ranka ya dad'e, ya fama da jama'a?" Yayi murmushi kafin yace

"Alhamdulillah, ya shirye_shirye?" Tace

"Alhamdulillah, ana nan ana tayi, in zuba maka juice d'in?" Dad yace

"Toh zuba" Mami ta mi'ke ta tsiyaya sassanyan lemon a cikin tambulan sannan ta dawo ta mi'ka masa har lokacin da murmushi kan fuskarta, Dad yace

"Sannu" murmushi kawae tayi ba tare da tace komae ba, seda Dad ya sha lemon sannan ya ajje akan centre table d'in, ya juyo da dubansa kan Mami yace

"Magana muke akan ginin da zan saka a farawa Adnan, so nake ayi cikin sauri ayi a gama tunda ga yananin yadda aka saka babu tsayi" Mami ta gyara zama tana kallansa tace bayan ta sauke ajiyar zuciya

"Ae yalla6ae za'a takura masu ginin ne gaskiya.. har suzo suyi abu kuma azo beyi kyau ba" Dad yace

"Ehh toh wannan ba matsala bace tunda sunsan aekinsu, amma idan ba haka ba toh kawae a cikin ginannun gidajen seki za6ar masa d'aya, nasan ze yaba da za6inki" Mami tace

"A'ah a'ah sabon gini Son keso, bama son ginanne" ta 'karasa fad'a da d'an tsokana a muryarta, Dad yayi murmushi yace

"Yawwah ae shiyasa nake so ayi a fara wannan d'in zuwa ranar d'aurin aure" Mami ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Wato yalla6ae nayi mantuwa ban fad'a maka ba..." Seta d'an dakata kad'an tana so taga yanayinsa da kuma yadda zata tsara zancen harya samu waje a wajen Dad d'in sannan ta d'ora da fad'in

"Kasan yarinyar bata gama makaranta ba, toh iyayen ke son aurar da ita tun kafin ta gama, kasan yanayin al'adarsu , toh ni kuma ba zanso ace a dalilin Son a salwantar mata da karatunta ba, shiyasa da na yanke shawarar idan an tashi d'akkota daga gidan nasu a kawota gidan nan ta 'karasa makarantarta ta tunda ta kusa gamawa, in yaso idan ta gama se a mi'kata gidan ta hankali kwance, kaaga kafin lokacin ma an gama ginin a tsanake, kuma kaga daga nan idan ta tsaya duk lokacin data ga dama zata iya d'ora karantunta abinta, ba kamar yanzu ba da idan ta tsaya may be ma shikenan...." Tunda ta fara magana Dad ke kallanta yana rarrabe duk wata magana da take fad'a d'in.........


Mhiz Innocent.......✍️




https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_16

____Mami ta d'anyi jimm tana san gane reaction d'in dad , sedae bata gane komae ba dan haka seta d'an gyara zama tana saurararsa sanda yake fad'in

"Kina ganin hakan babu matsala? Seta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"In Sha Allah yalla6ae babu wata matsala, in yaso daga baya ayi wani taron lokacin da zata tare" dad yayi shiru bayan ya kur6i juice d'in dake hannunsa, ganin hakane yasa Mami d'orawa da fad'in

"Kaga mun taemaketa daga ita har iyayennata koh? Dad ya ajje juice d'in hannunsa sannan ya kalli Mami yace

"Hakane, Allah ya saka da alkhaeri" ya 'karasa fad'a da faffad'an murmushi akan fuskarsa, Mami ma tayi murmushin sannan tace

"Ameen_Ameen ranka ya dad'e, babu dae wata matsala koh? Dad yace

"Keda d'anki kuma? Ragowar aeya rage tsakaninku" Mami tace tana murmushi

"Hakane kuma"

"Toh Allah ya taemaka" daga haka suka cigaba da hirarsu....................

*** *** ***

...A hankali ta d'aga idanunta da suka mata nauyi saboda ciwon da kanta yake mata ba tun yau ba ta kalli Hauwa'u dake 'karasowa, ta zauna kusa da Azrah fuskarta d'auke da murmushi tace

"Eyyah Azrah kiyi ha'kuri yau na makara" Murmushin ya'ke Azrah ta d'an saki kad'an sannan tace cikin sanyi

"Babu komae fa" Hauwa'u ta gyara zama tana fad'in

"Ina zamu tashi?" Azrah ta bud'e jakar dake hannunta ta d'auko wani littafi ta fara bud'ewa, Hauwa'u da tun d'azu take kallanta tace

"Azrah!" Seta d'ago a hankali ta zubawa Hauwa'u brown eyes d'inta da suka d'an lumshe kad'an, Hauwa'u tace

"Lafiyarki kuwa?" Azrah ta d'anyi murmushi kad'an sannan tace

"Lafiya mana, me kika gani?" Ta 'karasa fad'a tana yin 'kasa da kanta, Hauwa'u tace

"Ban yadda ba, yanayinki kad'ae ya nuna ba lafiya ba" 'kwallar da Azrah keta 'boyewa karta zubo itace ta samu damar zubowa, seta saka gefen hannunta ta d'auketa, Hauwa'u ta ri'ko hannun nata tace tana kallanta sosae

"Koda baki goge ba, idanuwanki sun dad'e da fallasa halin da kike ciki, yanzu ashe har akwae abinda zaki iya 6oyemin bansani ba?" Azrah ta d'ago tana kallan Hauwa'u kafin tace komae Hauwa'u ta d'ora da fad'in

"Shikenan nagode" Azrah ta ri'ko hannunta sannan cikin sanyi tace muryatta na sar'kewa

"Kiyi ha'kuri Hauwa'u, na gaji da kawo miki 'korafe_'korafe na wad'anda nasan ba 'karewa zasuyi ba, shiyasa nayi 'ko'karin barinsu kawae kada ki gaji" Hauwa'u ta 6ata rae tana sake kallan Azrah cike da tausayinta wanda kullum yake sake turnu'keta tace

"Nice na fad'a miki zan gaji da ji" Azrah ta girgiza kanta kamar 'karamar yarinya er goye sannan ta lumshe idanunta tana bud'esu a lokaci guda sanda wasu hawaye suka zubo daga idanunta zuwa kan kuncinta tace

"Hauwa'u..sun sake siyar dani!"

"Kamar yaya?" Hauwa'u ta fad'a cike da mamaki, Azrah tace

"Baban ilyasu..., Hauwa'u bansan me zanyi ba, bansan yadda zanyi ba, na rasa gane menene mafita, nayi tunanin kodae guduwa zanyi ne in gujewa wannan abinda suke 'ko'karin aekata min?" Ta fad'a wasu zafafan hawaye na zubowa akan kuncinta, Hauwa'u ta ri'ko duka hannayen Azrah tace tana kallan cikin idon Azrahn

"Wannan ba mafita bace Azrah, ki cigaba da addu'a In Sha Allah komae zae zama tarihi kinji koh? Amma waema yaushe Alhaji wadatan ya mutu ne? Kenan har sun samo wani?" Azrah tayi ya'ke sannan ta goge hawayen fuskarta sedae ba tace komae ba, Hauwa'u tace

"Ki cigaba da addu'a kinji?" Azrah ta d'ago jajayen idanunta ta kalli Hauwa'u sannan tace

"Hauwa'u inno tace min ba'a cikin 'kauyen nan zan zauna ba fa, shine abinda yafi damu na, bansan wajen wa suka saeda ni ba Hauwa'u, abubuwan suna neman sumin yawa, ji nake kamar na mutu gaba d'aya ma na huta da wannan 'kuntacacciyar rayuwar tawa" ta fad'a tana fashewa da wani marayan kuka 'kasa_'kasa, Hauwa'u ta janyo ta jikinta ta rungume wani irin tausayin 'kawarta ta na kamata, tabbas taga abubuwa a rayuwarta wanda ita kanta Hauwa'un kan tayata kuka wasu lokutan sannan ta bata baki, dukda tana bata bakin ne kawae dan hankalinta ya kwanta, amma wasu abubuwan dole suyi wa 'kwa'kwalwa da zuciyar Azrahn yawa, Seta lumshe idanu tana jin yadda 'kwalla ta taru a idanunta, seda ta d'anyi jim ta tabbatar idan tayi magana ba zata fahimci raunin dake zuciyarta wanda har ya bayyana cikin muryatta ba sannan tace

"Kiyi shiru, ki dena fad'in haka kinji? Allahn daya halicceki yana tare dake In Sha Allah, duk nisan inda zasu kaeki kuwa ba abinda ze same ki kinji?" Azrah ta lumshe idanunta tana sake jin 'kaunar Hauwa'un a cikin jinin jikinta, masoyiya 'kwaya d'aya takk wadda take 'kaunar ta tun yarinta kuma wadda take da tabbacin ba zata ta6a samun makamancinyar 'kaunar da Hauwa'un ke mata ba, a koda yaushe ita burinta ta kwantar mata da hankali duk tsananin damuwar da zata shiga kuwa

"In Sha Allah Hauwa'u, Allah ya bar zumunci, Allah ya barmu har abada, nagode sosae" Hauwa'u tayi murmushi

"Oh yeah..ki goge hawayen" Azrah ta d'ago ta goge hawayen da bayan hannunta sannan tayi murmushi tana jan sheshshe'ka a hankali......................


.........Yana zaune akan side chair dake cikin office d'in hannunsa d'auke da wayarsa yana dannawa, aka turo 'kofar sannan aka rufe bayan an shigo, Sameer ya 'karasa shigowa cikin office d'in yana kallansa shima bece komae ba seda yaja kujera ya zauna sannan yace

"Ka tashi mu tafi, dad na jirammu fa" Don ya d'ago a hankali ya kalli Sameer sannan yace bayan ya maeda dubansa kan wayar da yake dannawa

"Ka riga ka san akan wane sharad'i na fara zuwa companyn nan, so pls kada kasa raena ya 6aci, bansan wasu bodyguards" Sameer ya ajje numfashi sannan yace

"Ohk ka tashi ni zanyi driving d'in"

"Better" Don ya fad'a yana zura wayarsa cikin aljihun bayan wandon dake jikinsa sannan ya mi'ke, shima Sameer mi'kewar yayi suka fita tare Don a gaba yayinda Sameer ya rufa masa baya. Sameer d'in ne kuwa yayi driving nasu har zuwa gidan nasu, suna cikin tafiya a motar ne Sameer ya juyo ya kalli Don kafin ya maeda dubansa kan titi yace

"Wae babu wani shirye_shirye da zamuyi ne daga 6angarenmu?" Don ya d'an kalli Sameer a fuzge sannan yace

"Na me fa?" Sameer yace har lokacin kansa na titi

"Bikin nan mana" Don ya d'an juya fuska yana kallan Sameer cike da tuhuma yace

"Bikin waye wae?" Sameer ya juyo ya jefa masa harara na jin irin wannan raenin hankalin da Don d'in ke 'ko'karin yi masa, yayinda ta 6angaren Don harga Allah ya manta da wannan maganar ma gaba d'aya shiyasa ya kasa gane maganar Sameer d'in, Sameer ya 6ata rae

"Kaefa raenin hankalin ka ya maka yawa wallahi, yanzu har nima seka raenawa hankali? Wae meyasa ne kae komae baka d'aukarsa serious ne?" Don ya d'an 6ata fuska yana kallan Sameer

"Kamar yaya? Raenin hankali a'ina?" Ganin yadda yayi maganar ne da gasken gaske yasa Sameer ya fahimci da gasken be fahimci maganar da yake masa ba, dan haka yace

"Auranka mana, ko kana nufin harka manta?" Don ya d'an murza goshinsa, ba tare da ya kalli Sameer ba yayi jimm kad'an sannan yace

"Wato Mami dae tana nan ta dage se tayi wannan abin koh?" (Kae jama'a wae wannan abin 😹😹) Sameer yace har lokacin shima fuskarsa babu fara'a

"Meye aebun Mami dan tana 'ko'karin aekata abin arzi'ki?"

"Well..Kada Allah yasa a fasa wannan abin kaaji!!" Sameer yace

"Dama babu wanda ze fasa ae" daga haka duk sukayi shiru ba wanda ya 'kara cewa uffan, dan kowa yana ciki_ciki ne da d'an uwansa har suka 'karasa gidan..... Kae tsaye sashen Dad suka nufa da sallama suka 'karasa cikin parlourn, Dad ya amsa yana kallansu fuskarsa d'auke da murmushi yace sanda sameer ke 'ko'karin zama kan carpet d'in dake shimfid'e a tsakiyar d'akin

"Ahhh haba haba Sameer..tashi ka zauna kan kujera mana" se ya mi'ke yana murmushi yace

"Barka da rana Dad"

"Barka dae Sameer ya aekin?" Dad ya fad'a yana kallansu su duka, sannan ya 'karasa maganar ne yana kallan Don dake zaune kan kujera, shi dama beyi gigin zama a wani 'kasa ba, suna shigowa direct ya haye kan kujera, a hankali ya furta

"Alhamdulillah, barka da rana" Dad yace

"Barka kadae...toh madallah" Se kuma ya gyara zama sannan yace har lokacin yana kallansu

"Wato magana ce dama akan wani taro da za'a gabatar this week a Cyprus, toh dama kun riga da kunsani duk shekara ina wakilta, toh wannan karon gaskiya so nake na huta, dan haka nakeso na sanar daku inaso kuje ku wakilceni a matsayinku na wakilaena" Dad ya d'anyi shiru sannan ya d'ora da fad'in

"Ina fatan dae babu wata damuwa" Sameer yace

"Ehh Dad In Sha Allah..." Ya 'kare maganar yana kallan Don, seya lumshe idanu kad'an sannan yace

"In Sha Allah" Dad yace

"Toh madallah..Allah yayi jagora" Dae_dae lokacin da Mami tayi sallama cikin d'akin, duka suka amsa mata sallamar, sannan ta 'karaso cikin d'akin ta zauna suka gaesa da Sameer sannan ta maeda dubanta kan Don tace

"Ashe ka dawo?" Yace

"Ehh yanzu..barka da rana" Mami tace

"Barka dae Son.. Ya aekin?" Yace

"Alhamdulillah" seta maeda dubanta kan Dad dake fad'in

"Kamar kuwa kinsan yanzu nake shirin kiranki"

"Eyyah..Allah yasa dae lafiya" Mami ta fad'a tana murmushi, Sameer ya mi'ke yana kallan Dad yace

"Bari mu wuce" Dad ya d'ago ya kalleshi sannan yace

"A'ah koma ka zauna tukunna akwae maganar da zamuyi" seya koma ya zauna kansa a 'kasa, Dad yace yana kallan Mami

"Maganar tafiyarsu Cyprus, bansan yadda za'ayi ba, ko d'aga bikin za'ayi zuwa satin gaba? Shine nakeso muyi shawara" Mami tace

"A'ah yalla6ae, ae inaga maganar d'aga biki bata taso ba, tunda dae dama ko an d'aura auren ba yanzu zata tare ba..." Dad yace

"Ehh toh hakane.." Seya maeda dubansa ga Sameer yace

"Babu wani shiri da zakuyi kafin tafiyarku?" Sameer ya d'aga ido ya kalli Dad sannan ya maeda dubansa kan Don wanda ke danna wayarsa calmly bema nuna alamar yana jin abinda suke fad'a ba, Sameer ya girgiza kae sannan yace

"A'ah Dad babu komae.."

"Toh shikenan..ku tashi kuje zamu 'karasa maganar da Mamin taku" Sameer ya mi'ke ya d'an dunguri Don, se a lokacin ya d'ago ya kalleshi, aekuwa ya watsa masa wata uwar harara, kobi ta kansa beyi ba ya sauka daga kan kujerar ya kalli Mami da Dad dake zaune kan kujera d'aya yace kamar wanda

Please Login or Register in order to submit comment