Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akama dole

"A huta lafiya" Dad ya bishi da kallo bayan sun amsa masa sannan ya dawo da dubansa kan Mami yace

"Wato d'annan naki baya d'aukar komae da muhimmanci, ji dae yanda yake acting kamar bashi ya kawo zancen auren nan ba.." Mami tayi ya'ke

"Ae kasan halinsa" Dad yace

"Hakane..maganar kaya wannan da ake had'awa yarinya fah?" Mami tace

"Lefe?" Dad yace

"Ehh"

"Ohhh...kabar komae a hannuna In Sha Allah komae zae tafi dae_dae kafin ta kaega tarewa" Dad yace

"Toh madallah, Allah ya taemaka"

"Ameen" Inji Mami..............



**** ****

"Azrah! Azrah!!" Ta tsinkayo muryar Inno na kiranta, da sauri ta mi'ke daga zaunen da take ta fito tsakar gidan tana kallan Inno dake zaune kan tabarma suna hira da Baban ilyasu, Inno tace

"Ince dae kin fara had'a kayanki!" Shiru tayi na en sakanni, seda ta sake jiyo muryar Innon na fad'in

"Kamar da Azrah nake koh?" A sanyaye ta furta

"Yanzu zan had'a" daga haka ta mi'ke cike da sassarfa ta wuce d'aki jin kuka na shirin 'kwace mata, Inno ta bita da kallo kafin ta ta6e baki

"A banza..idan ma zaki bar 6ata ruwan hawayenki ki dena wallahi"....Tana shiga d'akin seta zube a 'kasa ta d'ora kanta kan jakar dake ajje a d'akin wasu zafafan hawaye na tsere akan kuncinta, sedae wannan karon babu sauti, kawae hawaye ne keta sintiri akan kuncinta cike da 'kunar rae, wanda ita kad'ae tasan irin zafin da takeji a cikin rae, zuciya da gangar jikinta, kawae seta mi'ke ta goge hawayen ta 'karasa wajen kayanta ta fara had'awa tana zubawa a wata bagco, tana cikin zubawa ne ta jiyo muryar Inno na fad'in

"Kada fa ki had'a da tsoffin kaya malama, ki d'auki masu kyau, dan gidan masu aji zakije..ah toh" lumshe idanunta tayi tana jin yadda bugun zuciyarta ke 'karuwa, seta samu kanta da cire tsoffin kayanta ta fara had'a masu kyau wanda yawancinsu wanda Inno ta siyo mata ne a kud'in da Alhaji wadata ya bata ta had'a mata lefe ne, a lokacin kawae taji zuciyarta ta 'ke'kashe seta kejin kamar za'a sake maemaeta abinda ya faru ne akan aurenta da Alhaji wadata, seda ta gama had'a kayan sannan ta mi'ke ta zura hijab ta fito tsakar gidan ta tsugunna tace

"Zanje wajen Hauwa'u" ta fad'a ba tare da ta kalli Inno ba

"Hauwa'u kuma?!! kije ki mata uban me? wato kije ta 'kara zuga ki koh?" A hankali tace

"Littafi zan kar6o.." Inno na shirin yin magana Baban ilyasu yace

"Jeki karki dad'e" bata jira ta sake jin komae daga bakin Inno ba ta mi'ke cikin sassarfa ta fice daga gidan, Tana saka kae zata 'karasa fita daga gidan itama ta sako kae, Azrah ta dakata tana kallanta, itama itan take kalla, Azrah bata san sanda tayi wani murmushi ba a lokaci guda wani kuka ya taho mata da sauri ta 'karasa ta rungume ta tana sakin kukan cike da rauni, Umma (matar me gari) itama ta rungumeta sosae tana jin yadda take rera kukan da duka 'karfinta, bata hanata ba har seda ta gaji dan kanta tayi shiru tana jan sheshshe'ka, Umma taja hannunta tace cikin taushi

"Ya isa haka, mu 'karasa cikin gidan" babu musu Azrah tabi bayan Umman suka shige cikin gidan da sallama, Inno ta bisu da kallo haka shima Baban ilyasu, Umma ta 'karaso tana neman waje zata zauna, Inno ta mi'ke tana kallan Azrah fad'i take

"Rashin kirkin naki sekin gwadawa kowa? Yanzu har rakiya ma sekin nunawa? Ba zaki samo mata kujera ta zauna ba" Ta fad'a tana kalle_kallen inda zata hango kujera, ita dae Umma kallanta kawae take har lokacin tana ri'ke da hannun Azrah, Inno ta d'akko kujerar ta ajjiyewa Umman tana fad'in

"Bismillah..lale marhabin" Umma ta zauna suka gaesa da Baban ilyasu sannan ya mi'ke ya fita, Se a sannan suka gaesa da Inno sannan Innon tace

"Kin kuwa zo a dae_dae..dama inata neman yadda zan sameki in sanar dake zancen bikin nan, se gashi Allah ya kawoki" Umma tayi murmushi sannan tace

"Allah sarki..bikin me fa?" Inno tayi murmushi tace

"Bikin 'yar taki mana" Nan da nan fara'ar dake kan fuskar Umma ta dad'u ta kalli Azrah dake zaune gefenta kanta a 'kasa sedae idanunta sunyi rau_rau amma bata fuskanci hakan ba tace

"Kae Masha Allah..amma wannan abu yayi dad'i, a cikin garin nan yake kenan?" Inno tayi jimm sannan tace

"A'ah wallahi...anan 'kasan mu yake"

"Toh Alhamdulillah.. Allah ya tabbatar da alkhaerinsa" Inno tace

"Bari a kawo miki ruwa" ta fad'a tana mi'kewa ba tare da ta jira amsar da Umman zata bata ba, Umma ta kalli Azrah sannan ta dafa kafad'arta tace a sanyaye

"Azrah!" 'Kwallar dake tare a cikin idanunta ta sauka kan fuskarta, Umma tace

"Subhanallahi, meya faru? Akwae damuwa ne?" Azrah ta shiga girgiza kae tana sake share 'kwalla, Umma ta ri'ko ta tace

"Kodae akwae wani abin ne?" Nanma ta girgiza kae, Umma tace

"Ko nice bakyaso na tafi?" Da sauri Azrah ta jinjina kae tana kallan Inno dake 'karasowa zuwa wajen da suke hannunta d'auke da kwanon sha wanda ta ciko da ruwa a cikinsa, ta 'karaso ta ajje ruwan tana ya'ke take fad'in

"Kukan kuma na menene Azrah? Banda abinki ae zata dinga zuwa koh? Nasan ma zata zo bikin ae" Inno ta fad'i hakan ba dan tana da burin jin amsar da zata fito daga bakin Umman ba, Umma tace

"In Sha Allah kuwa zanyi 'ko'kari nazo, ki bar kukan kinji?" Azrah ta d'aga kanta tana sauke ajiyar zuciya, Inno ta wurga mata harara ta gefen idanu sannan tace akan la66anta

"Lallae ta6ara samun waje...".... Umma bata bar gidan ba seda ta baewa Azrah kayayyakin data saba kawo mata, harma da kud'i ko zata bu'kace su, sannan ta mata al'kawarin indae ta samu dama zata zo ranar d'aurin auren, dukda ba wani dad'ewa tayi ba amma hakan ya kwashe kaso da yawa daga damuwar Azrah d'in.......


****A cikin kwanakin da suka biyo baya a cikinsu ne Don da Sameer suka d'aga zuwa Cyprus, yayinda Mami ta cigaba da shirye_shiryen biki dukda ba wani taro zatayi ba, tace idan zata tare se a yi taron sosae.... Toh sakanni na tafiya haka awanni ma suna shud'ewa suka had'u suka bada kwanaki..akace fa rana bata 'karya sedae uwar d'iya taji kunya....yau ta kama Friday sati 2 kenan da kae kud'i kuma ranar data kasance ranar d'aurin aure........

*AZAAD2023* ya kukaji sunan 😁💃

Ranar kuke jira yau gata tazo 😂💃 nima da tambura na gani nazo 😂💃

....Naji dad'i sosae yanda kuka nuna damuwarku na rashin gani na kwana 2 🥺🫶 Nagode sosae da kulawa Allah ya bar zumunci, I heart u so much 🥹😩🫶

Innocent.........✍️


https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_17

Wannan page d'in sadaukarwa ne gareku team AZAAD In Sha Allah zanyi mentioning sunayen ku a next page 😻

_____Tunda ta tashi a yau d'in take jinta sakaka kamar mara lafiya, komae tana yinsa ne a sanyaye duk da sanyin nata naturally ne amma yau kam har yayi yawa, tunda tayi sallahr asuba ta koma d'aki bata sake fitowa ba, tana zaune ta d'ora kanta akan cinyoyinta, haka kurum take tajin fad'uwar gaba tun tashin ta dan haka ta dinga janyo duk wata addu'a da tazo bakinta tana yi a zaunen..Tana nan zaune idanunta a lumshe ta jiyo muryar Inno na fad'in

"Wae ba zaki fito ki shirya bane? Koda yake kiyi ta zama ma meya shafeni!" Tayi maganar duk a lokaci guda, ita dae tana jinta ba tace komae ba dan bama tasan me za tace d'in ba..


......Fitowarsa kenan daga d'akin yana gyara zaman links d'in hannunsa, Mami ta 'karaso hannunta d'auke da hula tana murmushi, Dad ya 'karasa saka links d'in sannan ya d'ago ya kalleta sanda take mi'ka masa hular tace

"Kayi kyau yalla6ae..kamar kaene angon!" Murmushi Dad yayi yana kallanta sannan ya kar6i hular dake hannunta yace

"Allah koh?"

"Sosae kuwa" Dad yayi murmushi sannan ya d'ora hular a kansa yana d'aukar wayarsa dake ajje kan kujera yace

"Yanzu kina nufin boy base yaje ba?" Mami ta nemi waje ta zauna sannan tace

"Ranka ya dad'e ae babu damuwa, kowa ma ze hallatta lokacin da zata tare"

"Shikenan tohh..Allah ya kaemu, mu dae bari mu 'karasa kada mu makara" ya fad'a yana yin gaba, Mami ta mi'ke tabi bayansa tana fad'in

"Toh Allah ya tsare"... Dad ya fita compound inda masu tsaronsa ke jiransa ya shige mota kae tsaye suka nufi 'kauyen kima...

___'Karfe 2:10 na ranar juma'a bayan an idar da sallahr juma'a dubban mutane suka shaeda d'aurin auren ADNAN KABEER TAJUDDEEN da AZRAH ABBAKAR akan sadaki mafi 'karanci wato me albarka kenan....

.....Wajen 'karfe 3pm baban ilyasu ya shigo gidan sanye cikin wata shaddarsa me babbar riga yana ta d'age gefenta fuskarsa d'auke da murmushi, Inno da fitowarta daga d'aki kenan ta kalleshi tana fad'in

"Sannu da zuwa Malam"

"Yawwah..aure fa ya d'auru" ya fad'a yana murmushi..Fitowarta kenan daga band'aki hannunta ri'ke da bokitin wanka wanda Umma (matar me gari) ta sakata ta shirya ta tsinci maganar Baban ilyasun, ba tare da ta shirya ba ta saki bokitin a 'kasa tana jin yadda bugun zuciyarta ke 'karuwa da sauri da sauri, Inno da Baban ilyasu suka juyo dukka suna kallanta, seta lumshe idanun ta tana jin yadda wasu zafafan hawaye suka fara sintiri akan kuncinta, cike da sassarfa ta fara takawa bata ko ganin gabanta ta shige d'akinta har lokacin bugun zuciyarta be dawo dae_dae ba, Inno ta ta6e baki tana dawo da dubanta kan Baban ilyasu tace

"Angon ze shigo ne?" Baban ilyasu ya sake gyara zaman babbar rigar sa yace

"Ehhh toh....gaskiya a'ah dan kuwa angon na can wata 'kasa ne yaje wani taro, haka suka fad'a min" Inno tace

"Ikon Allah, toh madallah".... Ko da ta shiga d'akin zubewa tayi a dandagaryar d'akin ta fashe da wani matsanancin kuka me cin rae, yi take tana 'karawa kamar zuciyarta zata fito daga 'kirjinta, waye mijin nata? Wane irin mutum ne shi? Yaya kamanninsa suke? Menene halinsa? Duk ta'ki bawa zuciyarta damar da zatayi ire_iren wad'an nan tunanin, kawae kukan take babu ji babu gani har seda hawayen ya dena zuba ta koma kawae kukan take babu hawaye, Umma dake zaune tsakar gida tana jinta ta 'kyaleta ta gama kukan ko zuciyarta zata yi sanyi, Ita gaba d'aya ma kanta a kulle yake yadda taga har lokacin mutanen dake cikin gidan ba sufi ta 'kirga su da hannunta ba, koda yake hakan ba abin mamaki bane idan ta tuna wacece Azrah a cikin 'kauyen.. Seda ta bada wajen mintuna 10 sannan ta mi'ke ta shiga d'akin, Inno tayi murmushi tana kallanta tace

"Ae gwara ki rarrasheta...amarya na kuka ae ba kanta" Ita dae Umma kawae ta shige d'akin ta zauna tana kallan yadda Azrah d'in keta sauke numfashi akae_akae, tace cikin lallashi

"Kiyi shiru haka Azrah, ya isa kinji?" Ta fad'a tana d'ago kanta, shiru Azrah tayi ba tace komae ba, Umman ta cigaba da fad'in

"Kukan ya isa haka, kowacce mace haka take ji ranar da aka d'aura aurenta da wani kuma ake 'ko'karin kaeta can gidansa, kiyi ha'kuri ki dena wannan kukan kada kanki yayi ciwo, kin riga kin sani a cikin 'kauyen nan ba kiyi 'kan'kantar aurarwa ba, idan a cikin gari ne dae zeyi wuya a aurar da me irin shekarunki, amma duk da haka ki bar kukan haka nan" ita dae Azrah tayi shiru dan ba fahimtar abinda Umman ke fad'a take ba, kawae dae tayi shiru ne dan tana ganin shirun shine kawae mafita.... Wajen 'karfe 5pm Umma ta fito daga d'akin Azrahn ta kalli Inno dake hira da wata ma'kociyarsu tace

"Zata iya shiryawa ae yanzu koh? Naga maghrib na tahowa!" Inno ta kalleta sannan tace

"A'ah..ae bana tunanin zasu zo da wuri" Umma tace

"Duk da haka dae gwara ta shirya d'in" Inno tace

"Babu damuwa fa..ko kin tafi zan shirya ta ae" ta 'karasa fad'a tana ya'ke, Umma tace

"Toh Shikenan" daga haka ta wuce d'akin, tana nan zaune har wajen 'karfe 6 shiru shiru dae ba taga alamar za'azo d'aukar amarya ba, wasa wasa har bayan maghrib dan haka tana yin sallahr maghrib d'in ta mi'ke ta gyara zaman mayafin ta ta kalli Azrah da har yanzu take zaune kamar marainiya tayi shiru tun d'azun tace tana kallanta

"Azrah zan tafi" se a lokacin Azrah ta d'ago idanunta da sukayi jajir ta kalleta kamar ba zata yi magana ba se kuma tace cikin sanyi kuma a rarrabe haka zalika murya a dashe

"Ta..fi..ya?" Umma ta 'karasa kusa da Azrah ta zauna sannan tace

"Ehh Azrah dare nayi, naga har yanzu basu zo ba, In Sha Allah zanzo nan gaba se a rakoni gidan ki kinji?" Azrah ta d'aga kae a hankali ba tace komae ba, daga haka Umman ta d'anyi mata gajeriyar nasiha sannan ta fita, Azrah ta bita da kallo harta fice sannan ta dawo da kanta ta sake kwantarwa.......


........Washe_gari wajen 'karfe 3pm motarsu hajja kaltume ta tsaya a 'kofar a gidan nasu, hajja kaltume ta sauka tana kallan drivern tace

"Bari na shiga yanzu zan fito" daga haka bata jira amsar drivern ba ta shige cikin gidan da sallama, Inno ta fito daga d'akin ta tana amsa sallamar, ganin me sallamar ya sanya ta yin murmushi tana fad'in

"Maraba da mutan birni" Hajja kaltum ta bud'e hanci tana 'kara bubbud'ewa ita a dole er birni, Inno tace

"Shigo ciki" babu musu hajja kaltume ta 'karasa cikin d'akin ta nemi waje ta zauna, suka gaesa sannan tace

"Ina amaryar tamu? Ta fad'a kamar da d'an izgilanci, ita kuwa Inno bama ta lura da hakan ba se wanshare baki take tace

"Tana d'aki, bari nayi mata magana" ta fad'a tana mi'kewa ta fice daga d'akin, kae tsaye d'akin Azrahn ta wuce tana kallan ta yadda take a takure kamar me jin sanyi tace

"Ki tashi ki shirya lokacin tafiyarki yayi" wani irin bugawa taji 'kirjinta yayi kamar zuciyarta zata fito, ta d'ago ta zubawa Inno idanunta, Inno ta watsa mata harara tana fad'in

"Ba cewa nayi ki zuba min wad'an nan idanun naki ba malama, ki mi'ke kiyi da jiki ba jiranki za'ayi ba" Daga haka ta fice daga d'akin, Azrah ta mi'ke tana jin yadda jiri ke d'ibarta ta 'karasa inda ta ajje jakarta wadda ke d'auke da kaya 'kalilan a ciki ta ciro wani hijab ta saka sannan ta fito daga d'akin har lokacin jikinta a sanyaye, jin komae take kamar a mafarki, kuma kamar wasan yara, a haka ta 'karasa d'akin da Innon ke ciki ta zauna kanta a 'kasa, Inno ta bita da kallo sannan tace

"Toh Azrah...abinda zan iya fad'a miki kawae shine don Allah karki bani kunya, yi nayi bari na bari..kar inji kar in gani kinji koh?" Ita dae Azrah d'aga kae kawae take yi dan bakinta ya dad'e dayi mata nauyi, Hajja kaltum ta mi'ke bayan ta direwa Inno kud'i tace

"Toh mu zamu wuce, se Allah ya sake sadamu" Inno itama ta mi'ke tana fad'in

"Toh shikenan, Allah ya kiyaye hanya ya tsare"

"Ameen" Hajja kaltum ta fad'a tana yin gaba, Azrah ta mi'ke tabi bayan ta, yayinda Inno itama ta bisun har 'kofar gida bayan ta janyo mayafinta dake kan 'kofa sukayi waje..... Ganinsu da drivern yayi ne yasa fito ya bud'e musu 'kofar baya, Hajja kaltum ta shiga sannan itama Azrah ta fara 'ko'karin shiga idanunta fall 'kwalla 'kiris take jira ta saki kukan

"Azrah" ta tsinci muryar Hauwa'u, da sauri ta juya tana kallan inda ta jiyo muryar Hauwa'un, Hauwa'u ta 'karaso da sauri ta rungume Azrah, dama 'kiris take jira aekuwa ta fashe da kuka mara sauti, itama Hauwa'un kukan take babu me rarrashinsu, Inno ta ta6e baki kafin tace

"Lallae fa 'kauna" sedae basu hana su kukan ba har suka gaji dan kansu sukayi shiru, Hauwa'u ta d'ago tana kallan Azrah sannan tace

"Tafiyar kenan?" Jinjina kae Azrah tayi a lokacin da wasu sababbin hawayen suka sake zubowa daga cikin idanunta, Hauwa'u tace

"Allah ya tsare, ya 'kaddara saduwar mu" Ita dae Azrah ta gaza cewa komae kawae kallan Hauwa'un take, Hajja kaltum da har lokacin take cikin mota tace

"Kiyi da jiki kar muyi dare" Hauwa'u ta saki Azrah tana goge hawayen idanunta sannan cikin sanyin murya tace

"Ki kula da kanki" jinjina kae Azrah ta sakeyi sannan ta juya ta shige cikin motar, Hajja kaltum ta janyo 'kofar ta kulle tana kallan yadda wasu yara suka taru a wajen suna kallansu, Inno ta cigaba da d'aga musu hannu, driver ya tada motar babu 6ata lokaci ya jata suka bar layin, ji tayi kamar yaja da numfashinta seda ta kae masa wata cafka sannan ya dawo, dae_dae lokacin data fashe da kuka ta jinginar da kanta jikin window ta cigaba da rera kukan nata, ta shafe wajen mintuna 10 tana kukan sannan ta share idanunta a hankali ta d'ago tana kallan titi, seta shagala da kallan yadda suke ta wuce wajaje da dama, tun suna cikin 'kauyensu har suka fita daga cikinsa, duk se jikinta ya 'kara yin sanyi, tayi lamo a cikin motar iska na kad'ata kamar zata tsaga 'kasusuwanta, seda sukayi tafiya me nisa sannan taga sun fara sauka daga titi a hankali suka gangara zuwa cikin wani babban layi me kyau wanda gine_ginensa ma kad'ae abin kallo ne, a hankali take bin gidajen da kallo se kuma ta koma ta sake yin shiru kanta jikin window, tana jin sanda Hajja kaltum ta d'aga waya, ita dae tana nan kwance seda taji sun tsaya sannan ta d'ago kae, a wani 'katon had'ad'd'en gida taga sunyi parking ta d'auka sauka zasuyi, se taga an bud'e musu gate d'in, drivern ya tura hancin motarsa cikin gidan, da wani irin mamaki take bin inda suka shigo da kallo zuciyarta na bugawa da 'karfin gaske, nan d'in dae beyi mata kama da company ko wata masana'anta ba, dan haka seta zuba ido ta cigaba da kallan ikon Allah, tafiyar wajen second 30 drivern yayi sannan ya 'karasa wajen parking d'in motocin gidan, ya parker motar sannan Hajja kaltum ta bud'e 'kofar ta fito, drivern ya zaga ya bud'ewa Azrah inda take zaune, A hankali ta zuro 'kafafunta har lokacin bugun zuciyarta na fita ne da sauri da sauri, Hajja kaltum ta kalleta tace

"Ki biyo ni" se tayi gaba ri'ke da jakarta wadda drivern yace

"Kawo in shigar miki da ita" binsa kawae tayi da kallo ba tace komae ba harya kar6i jakar shima yayi gaba, seta fara binsu a hankali tana sake kallan gidan "nufin su dae nan gida ne?" Ta tambayi kanta, tasan babu me bata wannan amsar dan haka ta cigaba da binsu har suka 'karasa aenahin inda part part d'in gidan suke.......


.........Fawaz dake zaune kan kujerar da Mami ke kae ya turo baki yace

"Amma ae dukda haka Mami sena wakilceshi koh?" Mami tace

"Banda abinka boy..yanzu da baka je ba meya sameka?" Fawaz na 'ko'karin magana Hajja kaltum tayi sallama cikin parlourn, Mami ta bisu da kallo kafin tace

"Sannunku da zuwa" Hajja kaltum ta 'karaso cikin parlourn Azrah na bayanta kamar wata munafuka se ra6e ra6e take, Hajja kaltum ta nemi waje ta zauna yayinda Azrah ta zauna a 'kasa, drivern ya ajje kayan sannan ya fita bayan ya gaeshe da Mami, Mami ta kalli Hajja kaltum tace

"Ya hanya?"

"Hanya alhamdulillah, gamu fa mun 'karaso"

"Toh sannunku da zuwa" Mami ta fad'a tana kallan Azrah wadda tun shigowarsu kanta ke a 'kasa tana jin yadda bugun zuciyarta ya 'kara tsananta gudu ga wani tsoro daya cika mata zuciya, seta jiyo muryar Mami na fad'in

"Kunzo lafiya?" A hankali ta d'ago ta kalli Mami tace

"Ina yini?" Mami tace

"Lafiya 'kalau" Seta maeda dubanta kan Fawaz wanda tun shigowarsu yake kallan Azrah hadda yin tagumi yana 'kifta idanu a hankali, shi kam 'kwayar idanunta ne suka birgeshi brown dasu gasu dara_dara, haka gata er 'karama da ita kyakykyawa, shi kam bema lura da irin shigar dake jikinta ba kawae dae kyakykyawa ce, Mami tace

"Kaee!" Seya d'ago da sauri yana kallan Mami yace

"Na'am" Mami tayi 'kasa da murya kafin tace

"Lafiya?" Shima 'kasa yayi da muryar yana matso da bakinsa saetin kunnen Mami yace

"Mami she's beautiful" Mami tayi murmushi kafin tace

"Allah ya shiryamin kae boy, jeka kira min Ammin yara" Fawaz ya mi'ke ya wuce, Mami ta dawo da dubanta kan Hajja kaltum suka cigaba da magana, bayan wajen mintuna 5 sega Fawaz da Ammin sun shigo tare, Ammi ta 'karaso suka sake gaesawa sannan ta nemi waje ta zauna, Mami ta kalleta tace tana nuna mata Azrah

"Ki kaeta d'akin da nace ki gyara, ta samu tayi wanka taci abinci, se kizo zamuyi magana"

"Toh" Ammin ta fad'a tana bin Azrah da kallo sannan tace bayan ta mi'ke tazo dab da ita

"Muje koh?" Babu musu Azrah ta mi'ke tana shirin d'aukar kayan ta Fawaz yace

"Bari na d'aukar miki" bata tanka masa ba har yayi gaba, seta bishi, Ammi na gaba se Fawaz sannan Azrah a haka har suka 'karasa d'akin, ta dinga bin ko'ina da kallo cike da mamaki tsoro da fargaba, suna zuwa Ammin ta tura 'kofar d'akin ta shiga, se Fawaz ya dakata ya juyo yana kallanta itama ta dakata, a hankali ta mi'ka hannunta kamar zata kar6i jakar, shi kuma Fawaz ya d'auka gaesawa zasu yi seya mi'ka mata hannu, ta kalli hannun sannan ta kalleshi, cikin siririyar murya ta furta

"Jakar!" Fawaz ya d'un'kule hannunsa yana kae hannun ya shafa 'keyar sannan yace

"Ohhh..." ya fad'a yana sakko da jakar daga kafad'arsa sannan ya mi'ka mata, ta sanya hannu ta kar6a sannan ta 'karasa cikin d'akin har lokacin jikinta a sanyaye...............

Naso nayi muku yafi haka yawa 😥 amma naga dare yayi, anyway gobe In Allah y kaemu ma had'e 😇

Mhiz Innocent.......✍️


https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_18 _(Second to d Last Free Page)_


This page is dedicated to u Malam Abbas's students, na san zaku ji dad'in page d'in nan saboda son shirarku 😹😻


____A hankali ta 'karasa cikin madaedaecin d'akin dake ta tashin 'kamshi hannun ta ri'ke da jakarta ta, Ammi dake tsaye gefen gado ta kalli yadda take ta ra6ewa har lokacin, se tayi murmushi tace

"Ki 'karaso mana" cigaba da tafiya Azrah tayi harta 'karasa dab da gadon sannan ta fara 'ko'karin zamewa ta zauna a 'kasa, Ammi tayi saurin ri'kota

"Ahh haba haba tashi ki zauna akan gadon mana" babu musu ta mi'ke ta zauna d'in kanta a 'kasa, ammi ta kar6i jakar hannunta ta ajje akan stool sannan ta dawo da dubanta wajen Azrah tace

"A kawo miki abinci? Ko zaki fara yin wanka?" Se a lokacin Azrah ta d'ago ido ta kalli kyakykyawar matar sannan cikin sanyi kuma a hankali tace

"Duk yadda kika ce!" Murmushi Ammi tayi sannan tace

"Toh muje ki fara yin wankan" ta fad'a tana 'karasawa wajen da wardrobe take ta bud'e ta ciro wani wani lafiyayyen ninkakken towel ta ajje gefen gadon sannan tana kallan Azrah tace

"Ki d'aura bari na had'a miki ruwan wankan" daga haka ta wuce toilet, kallan towel d'in Azrah tayi, seda takae wajen minti 1 sannan ta mi'ke a hankali ta fara zame kayan dake jikinta har lokacin kallan yadda d'akin yake takeyi, tana gama d'aura towel d'in ta maeda hijab d'in jikinta dan dududu towel d'in ko cinyarta be kae ba, sannan ta koma ta zauna, dae_dae nan Ammin ta fito tana kallanta da murmushi kan fuskarta tace

"Gashi can na had'a miki ruwan, kije kiyi wankan, idan kin gama kimin magana zanzo na wanke miki kae" jinjina kae kawae Azrah tayi tana mamakin wannan iyayi haka, bayan wanka ma wato hadda wani wanke kae za'ayi bayan jiya_jiyan nan ta wanke

Please Login or Register in order to submit comment