Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta furta

"Toh" daga haka ta mi'ke ta shige d'akin wani sabon kukan na zuwar mata, inno ta bita da kallo tana ta6e baki

"Wani sabon salon iskanci..wae toh kawae" ta 'karasa fad'a tana ri'ke ha6a... Ranar haka ta wuni a kwance komae baya mata dad'i alwala ce kad'ae ke fito da ita, komae tana yinsa ne jikinta a sanyaye dan ko makarantar dare ma bata je ba.... Seda ta duba layin taga babu hankalin wanda yake kanta sannan ta fad'a cikin gidan da sallama, habee dake zaune kan tabarma tana cin tuwo ta amsa tana kallan hauwa'un, hauwa'u ta tsuguna tana kallon inno tace

"Ina yini"

"Lafiya lau" ta fad'a fuskarta babu yabo ba fallasa, hauwa'u ta d'an muskuta kad'an kafin tace

"Azrah tana nan" inno tace

"Ehh" ba tare data sake kallan hauwa'un ba, hauwa'u ta mi'ke ta shiga d'akin, a hankali ta yaye labulen d'akin tana 'karewa d'akin kallo ganin bata hango Azrah d'in ba, se daga baya ta hango ta daga d'an gefe kad'an a cure kamar kayan wanki, da sauri hauwa'u ta 'karasa wajen kana takae hannunta ta yaye hijab d'in tana fad'in

"Subhanallahi.. Azrah meya faru ? Ta fad'a bayan ta bud'e fuskar Azrah d'in, se a lokacin ta kula da yadda fuskarta ta tayi jawur gashi se sheshshe'ka take tana sauke ajiyar zuciya, hauwa'u ta janyota jikinta tana fad'in

"Meya faru Azrah ? Wani kukan ne ya tahowa Azrah, bata san sanda ta sakeshi ba sedae a hankali yake fita, hankalin hauwa'u ya 'kara tashi fad'i take

"Don Allah kiyi shiru ki fad'a min Azrah, hankalina a tashe yake wallahi" Seda tayi me isarta sannan tayi shiru ta d'ago tana kallan hauwa'u kamar ba zatace komae ba se kuma tace

"Hauwa'u.. Siyar dani fa zasuyi.." Ta 'karasa fad'a wasu zafafan hawaye na zubo mata a kuncinta, cikin rashin fahimta hauwa'u tace

"Su waye ? Ban fahimta ? Azrah ta sake sauke wata ajiyar zuciyar kafin tace cikin muryar kuka, dan kuwa har muryarta ta dashe saboda kukan da tasha a yau d'in

"Hauwa'u su baba ne zasu siyar dani ga Alhaji wadata" zaro ido hauwa'u tayi sannan ta 'kan'kance idanunta tana kallan Azrah ko 'kiftawa ba tayi tace

"Wanne Alhaji wadata d'in ? Kar kice min wanda na sani ? Jinjina kae Azrah tayi

"Ehh shi"

"Toh su suka fad'a miki zasu siyar dake ? Azrah ta girgiza kae kanta a 'kasa kafin ta d'ago tana lumshe idanu tace

"Hauwa'u wallahi siyar dani zasuyi, wae duk wata ze dinga basu kud'i.. Hauwa'u akwae daraja kuwa a cikin lamarin nan, zuciyata tana gab da bugawa hauwa'u.. Ya zanyi ? Ta 'karasa fad'a tana fashewa da kuka, hauwa'u ta janyota jikinta ta rungume itama kukan taji tana sonyi kodan ta taya 'kawarta ta ba'kin ciki da alhinin 'kaddarorin da suke ta faruwa da ita

"Kiyi ha'kuri..kiyi shiru Azrah komae me wucewa ne kinji ? watarana zakiyi farin ciki In Sha Allah, ki dena kuka" Wani murmushin ya'ke Azrah tayi tana girgiza kae, Allah sarki hauwa'u kullum maganarta kenan watarana zatayi farin ciki, but yaushe ? Bata tunanin akwae wannan ranar, a hankali ta d'ago kanta tana kallan hauwa'u bayan ta goge hawayen dake kan fuskarta tace

"Ya akayi kika shigo gidan nan" yamutse fuska hauwa'u tayi kafin tace

"Ba wanda yaga shigowata, gani nayi baki zo makaranta ba, kuma akwae abubuwa da yawa da zamuyi" Azrah tace

"In sha Allah zanzo gobe.."

Allah ya yadda" hauwa'u ta fad'a

"Wae uban me kuke tattaunawa ne se 'kuss 'kuss nakeji" inno ta fad'a bayan ta d'age labulen, dukkansu kallanta kawae sukayi ba tare da sunce komae ba, inno ta cigaba da fad'in

"Idan ma zugaki tayi akan maganar nan, toh karki d'auka tana miki ba'kin ciki ne dan taga ita har yanzu babu mashinshini, kika sake kika d'auka kuwa sedae kiji tayi wuff dashi" daga haka ta juya ta wuce, Azrah ta d'ago ta kalli hauwa'u wadda ko ba'a fad'a ba tasan bataji dad'i ba, seta mik'e tana fad'in

"Azrah se gobe" Azrah tayi saurin ri'ko hannunta tana kallan fuskarta kamar zatayi kuka, hauwa'u tayi murmushi tana jinjina kae sannan tace

"Karki damu" itama murmushin ta maeda mata kafin hauwa'un ta fice daga d'akin.....




.........Kae tsaye part d'in Mamin ya wuce, bayan ya shiga ya 'karasa d'akin fawaz ya tura 'kofar a hankali gudun karya tasheshi, a zaune ya hangoshi kan gadon hannunsa d'auke da iPhone d'insa yana kallo, Don ya 'karasa yana kallansa da mamaki ya zauna a gefen gadon kafin a hankali yace

"Bakayi bacci ba ? Se a lokacin fawaz yasan da zuwansa, ya kalli Don yace

"Ehh bhai, ina 'kara kallan wasanka ne"

"Toh ya isa haka, its tym for sleep"

"Ohk bhai" fawaz ya fad'a yana kashe wayar sannan ya ajjeta gefensa ya juya ya kwanta, Don yaja masa bargon ya lullu6eshi sannan yace

"Gud night" daga haka yayi switching off na light d'in d'akin ya fita... Yana fitowa yàyi dae_dae da lokacin da Mami ta sakko daga stairs sanye cikin doguwar rigar bacci ta 'karaso tana kallan Don fuskarta d'auke da murmushi tace

"Yanzu ka dawo ? Seya jinjina kae kamin yace

"Barka da dare"

"Barka kadae, ya aekin" ta6e baki yayi yana shafa sumar kansa kafin yace can ciki kamar wanda baya so aji abinda yace

"So bored"

"Ohhhh son.... Nidae ba wannan ba dama inason magana dakae" seya lumshe lumsassun idanunsa da suka 'kara lumshewa saboda baccin daya keji yace

"Bacci.."

"Ohk gobe mayi maganar uhmm" Mami ta fad'a tana kallansa

"gud night Mami" ya fad'a yana wucewa

"Allah ya tashemu lafiya".....



..........Tana zaune cikin d'akin ta qur'ani ne a hannunta tana karanta suratu yaseen, tana dab da gamawa taji sallamar wani yaro, inno dake tsakar gida ta amsa tana kallan yaron dake fad'in

"Wae Azrah tazo inji alhaji wadata.." Tunda taji haka komae ya tsaya mata cakk, kawae seta rufe qur'anin ta ajje gefe tana lumshe idanunta 'kirjinta na bugawa, inno tayi wani murmushi tana kallan yaron tace

"Maza jeka fad'a masa gata nan" daga haka yaron ya juya ya fice, inno ta 'karasa cikin d'akin Azrah tana kallan ta tace

"Maza tashi ki shirya ga mijinki nan yazo"

"Miji" ta maemaeta kalmar, se kawae ta mi'ke ba tare da tace komae ba ta gyara zaman hijab d'in dake jikinta ta fara 'ko'karin fita, inno tace

"A'ah ba zaki d'an gyara fuskarki ba" a hankali kamar wadda akawa dolen magana tace

"A'ah"

"Toh.. Tsaya kiji in fad'a miki..duk abinda ya baki ki kar6o kar kiyi fulako in yaso in bakyaso ni sena kar6a..kinji koh ? Inno ta fad'a 'kasa 'kasa

"Toh" kawae tace ta 'karasa soron gidan nasu sannan ta tsaya ta goge hawayen da suka fara tarar mata kafin ta wuce 'kofar gidan nasu, yana nan tsaye jikin motarsa wani 'kato dashi, sanye cikin manyan kaya hadda babbar riga, tumbinsa kuwa ya samu wajen zama hakan ya bashi damar zama sosae kuma ya fito ta cikin babbar rigar, hango ta da yayi ya sanyashi fad'ad'a murmushin kan fuskarsa sannan ya tako zuwa wajen data ja birki

"Salamu Alaeki" ya fad'a yana kallanta cike da so, ba tare data d'ago ta kalleshi ba tace

"Wassalam, ina wuni" se ya saki wani murmushin yana jin dad'in yadda yaji sassanyar voice nata yace

"Mu 'karasa cikin mota koh ? Ba tare data kalleshi ba tace cikin rawar murya

"A'ah..nanma ya isa"

"Hakane" ya fad'a yana gyara tsayuwarsa sannan ya fara da fad'in

"Ina fatan baban ya fad'a miki abinda ya kawoni wajenki koh ? Be jira amsarta ba ya d'ora da

"Nidae na ganki, kuma kinmin, yanzu haka bani da wani buri daya wuce na aureki, dukda abubuwan da aketa fad'a akanki ni sam hakan be dameni ba saboda ina sonki kuma zan aureki in har kin amince..." Be tsagaeta ba ya cigaba da fad'in

"Sunana tanimu..amma kowa ya sanni da Alhaji wadata...ina da mata 2 da 'ya'ya 10, mun rabu da matata ta farko yanzu haka da 1 muke tare, itace wadda ke fita aeki toh idan na aureki kinga kya d'an taemaka ko wajen kula da yara ne.." Harga Allah surutunsa ya fara isarta, dan yadda yake ta zubo bayanae babu comma ba full stop, zancensa na 'karshe shine yafi jan hankalinta wato na kula da yaransa, a hankali taji wata 'kwalla ta tarar mata a idanunta, maganarsa ce ta katse mata tunani wanda bata san sanda ta d'ago ta kalleshi ba

"Kin amince zaki aureni ? Ha'ki'ka idan ta bud'e baki zatayi magana tasan kuka ne ze taho, dan haka seta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya cikin rashin sanin abinyi, Alhaji wadata ya matso yana kallanta yace

"Ranki ya dad'e lafiya ? Kin amince ?Seta bud'e dara daran idanunta tana kallansa yadda babba dashi wanda a haefe ma ya haefe ta amma wae yake mata maganar aure,

"Ko na baki lokaci, naga kamar yanzu kina cikin damuwa" Batasan sanda ta jinjina kae ba, Alhaji wadata yace

"Nikam ki bud'e baki kimin magana mana kyakykyawa" se a lokacin ta iya bud'e bakinta da suka mata nauyi tace

"Ehh" murmushi yayi kafin yace

"Yawwah ko kefa..toh shikenan yaushe zan dawo ? Jin tayi shiru ya sanyashi fad'in

"Ko jibi yayi ? Nanma jinjina masa kae kawae tayi har lokacin kanta na 'kasa, yace

"Toh shikenan.. Amma dae kafin na tafi ya kamata a d'ago a d'an kalleni ko" ita kam harga Allah kunya yake bata wallahi, tayi shiru tana wasa da hannun hijabinta, Alhaji wadata yayi murmushi yace

"Shikenan ae.. Ba damuwa wataran za'a kalleni ne sosae" ita dae ba tace komae ba tana nan tsaye harya je motarsa ya fito da wata leda sannan ya dawo yace yana kallanta

"Gashi" seta d'ago ta kalli abinda yake mi'ka matan sannan ta girgiza kae da sauri tace muryarta na rawa

"A'ah" seya d'an 6ata rae kad'an

"A'ah karmuyi haka dake, don Allah ki kar6a" bud'e baki tayi zatayi magana ya 'kara cewa

"A'ah karki cemin komae indae ba kar6a zakiyi ba" Seta saka hannu ta kar6a kana tace

"Nagode" yace

"A'ah babu wannan a tsakaninmu, yanzu ki shiga gida se jibin" juyawa tayi ta shige cikin gidan dae_dae sanda 'kwallar data dad'e a idanunta ta samu damar zubowa, ta 'karasa ta mi'kawa inno ledar sannan ta wuce cikin d'akinta, inno ta d'auki ledar tana fad'in

"Kaeee masha Allah, lallae hannun alhaji wadata a bud'e yake, Alhamdulillahi mukam".....Ita kuwa Azrah tunda ta koma d'akinta shiru tayi bayan ta kwanta, tunane tunane fall cikin ranta, sedae zuciyarta ta kasa nutsuwa bare harta tsaya tayi tunani me kyau ko na abinda ya kamata, tana nan zaune a d'akin amma gangar jikinta ce kawae a gidan, gaba 1 hankalinta da tunaninta suna wani wajen, dan haka sam bata san me yake faruwa a cikin gidan ba, sedae wani lokacin tayi kuka inta gaji tayi shiru har bata san lokaci yaja ba, can taji fitsari ya matsota dan haka ta mi'ke ta fita daga d'akin ta kalli tsakar gidan tana kallan yadda dare yayi sosae, tayi mamaki sosae ganin yadda ta d'auki lokaci tana tunani ba tare da tasan lokaci yaja haka ba, seta 'karasa ta d'auki buta ta shige band'aki… kae tsaye d'akinta ta shige ba tare da tunanin komae ba, kawae seji tayi an ri'kota, da wani irin 'karfi ta wage baki zata fasa ihu, ilyasu ya rufe bakinta yana fad'in

"Ke kiyi shiru mana..." Cigaba tayi da 'ko'karin 'kwace kanta amma ya'ki bata damar hakan, kawae seta fara lalube da hannunta, aekuwa cikin sa'a hannunta yakae kan wata silver dake ajje kan drawer d'akin, da wani irin zafin nama ta d'auketa ta kwad'a masa ita akansa, cikin ficewar hayyaci da firgici ya saki wani ihu da 'karfi sannan ya saketa da 'karfi wanda har seda ta fad'i 'kasa, shi kuma ya dafe kansa wanda ya fara zubar da jini ya fara laluben hanyar fita, dan wani jiri yaji yana kwasarsa gashi ya fara ganin bibbiyu a haka a daddafe ya fice daga d'akin, dae_dae lokacin da baba da inno suka fito dam duk sunji 'karar tasa suna kallansa yadda ya dafe kansa yana lalulen hanya ga jini yana zuba daga kansa, inno tace

"Don ubanka me kayi mata ? Ilyasu ya juyo yana saesaeta nutsuwarsa gudun karsu fahimci wani abun yace

"Ba abinda na mata, kawae naje taemaka mata ne saboda ihun da naji tanayi, shine ta bugamin kwanan silver ta d'auka nine wanda na shigar mata d'akin, inno duk yadda akayi aljanu ke tsorata wannan yarinyar" Inno ta jefa masa wani kallo

"Almatsutsae ne ba Aljanu ba.. Wato su aljanun basa tashi zuwa se kana gidan koh ?? Ilyasu ya fara kame_kame, inno tace

"Kayiwa Allah kayiwa annabi ilyasu ka fita harkar yarinyar nan, kada ka jawomin abun magana a 'kauyen nan, aurar da ita fa zamuyi.." Baban ilyasu ya kalli ilyasu yace

"Jeka gyara kan naka..gashi nan se zubar jini yake" dama 'kiris yake jira ya wuce malallauta ya d'auki buta.... 'Bangaren Azrah kuwa tunda ya zubar da ita a wajen seta zube ta fashe da wani kuka mara sauti, kuka take kamar ranta ze fita na takaecin wannan rayuwa tata, a hankali ta fara rage sautin kukan nata sannan ta bawa zuciyarta damar yanke hukuncin da zeyi dae_dae da rayuwarta

"Anya kuwa ba da gaske ni shegiya bace !! Shiyasa abinda mahaefina ya aekata nima ake 'ko'karin aekamin ba ? Ta fad'a sautin bugun zuciyarta na 'karuwa, ta tsanesu su duka, ta tsanesu sedae dukda haka tsanar data kewa mahaefiyarta tafi ta kowanne mahaluki a fad'in duniyar nan, Tabbas idan ta cigaba da zama a cikin gidan nan wani abu mummuna ze iya faruwa da ita, Allah dae ya tsaere, "meye mafita ? Ta tambayi kanta, mafita d'aya ce...shine amincewa da auran Alhaji wadata!!!!.............

Mhiz Innocent........✍️

https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_10

____A take a lokacin tayi na'am da shawarar da zuciyarta ta yanke, taji tabbas wannan kad'ae itace mafita, seta d'ora kanta akan cinyarta tana runtse idanunta da suka gaji da fidda 'kwalla se ajiyar zuciya da take ta saukewa akae_akae, baccin da bata koma ba kenan tana nan zaune har asuba tayi, da asubar ma kasa mi'kewa tayi ta fita daga d'akin, dan wani irin tsoron had'uwa da ilyasun takeyi, ba ita tabar d'akin ba seda ta tabbatarwa kanta babu kowa a tsakar gidan, sannan ta fita..... Koda taje bakin companyn haka ta zauna sakaka kamar mara laka komae tana yinsa ne cikin sanyi dukda dama haka yanayinta yake amma yanzu kam kaso wajen 30 ya 'karu akan sanyin nata nada, har aka siye abincin nata bata ga giftawar irfan ba, dan haka yau se wajen 6 ta koma gida....


...........Mami ta kalli Fawaz dake fad'in

"Mami sena dawo"

"Ohk bye" ta fad'a tana d'aga masa hannu, fawaz ya gyara zaman jakar dake bayansa sannan yayi hanyar fita, yana shirin fita, simrah kuma na shirin shigowa, seya d'an dakata kad'an yace

"Morning sis" tana shiga cikin parlourn tace

"Morning boy, school zaka wuce ne ?

"Yeah ! bye.." Ya fad'a yana ficewa daga d'akin, Simrah ta 'karasa cikin parlourn tana kallan Mami dake kallanta, ta zauna akan wata side chair tace

"Barka da safiya Mami"

"Barka dae Simrah..ya momy take ? Mami ta fad'a cike da kulawa, simrah tace

"Tace in gaesheki"

"Ina amsawa" d'an jim Simrah tayi kamin tace

"Amm Mami zuwa nayi inji yadda kukayi da yah adnan.. Kin masa maganar ne ? Me yace ? Ta fad'a muryarta a raunane, Mami ta kalleta sosae kamin a hankali tace

"Naso yi masa maganar jiya so kuma bacci yakeji, but yau In Sha Allah zamuyi maganar uhmm" Simrah ta jinjina kae ba tare da tace komae ba, dae_dae lokacin wayarta tayi 'kara, takae dubanta kan wayar se kuma ta d'aga kae tana kallan Mami, Mami tace tana kallanta

"Ba Momyn bace ?

"Ehh..itace.." Simrah ta fad'a tana d'aga wayar sannan ta kara a kunnenta, daga can 'bangaren akace

"Kina kusa da hadeezan ne ?

"Ehh Momy.." Simrah ta fad'a tana kallan Mami, Momy tace

"Ohk bata wayar mu gaesa" da "toh" ta amsa sannan ta mi'kawa Mami wayar, suka gaesa sannan Mami ta mi'kawa Simrah wayar sukayi sallama da Momy, wajen mintuna 5 sannan Simrah ta kalli Mami tace

"Mami bari na d'an hau sama in kwanta, dama baccin be isheni ba" ta fad'a tana yamutsa fuska

"Ohk dear" Inji Mami, Simrah ta mi'ke ta wuce stairs, Mami ta bita da kallo sannan ta maedo da hankalinta kan T.Vn dake ta aeki... Kafin ta gama hawa benen wayarta ta sake d'aukar 'kara, seda ta tsaya ta duba 'kasan taga har lokacin Mami na zaune a parlourn sannan ta d'aga wayar, tun kafin ta gama karata a kunne ta jiyo muryar mahaefiyarta ta tana fad'in

"Ya kukayi da ita ? Wallahi na kasa sukuni" Ta6e baki Simrah tayi tace

"Wae bata masa maganar ba se yau.."

"Kamar yaya ? Momy ta fad'a tana 'kan'kance ido kamar Simrahn na gabanta, Simrah ta sake ta6e baki tace

"Wlh kuwa Momy, haka tacemin"

"Wallahi na dad'e da fahimtar hadeeza bata son auren nan shiyasa take ta wani kwane_kwane, ko meye amfaninsa" Simrah tace

"Toh Momy ya wuce ko dan ni er step sister d'inta ce"

"Kiji shashasha..waye ya fad'a miki wannan ne ? Momy ta katse Simrah ta hanyar fad'in hakan, Simrah tace

"Uhmm Momy mudae zuba ido mu gani tunda tace zata masa magana, amma fa ta d'auka ni shashasha ce, ae kawae dae ayi auren ta gani ba shikenan ba kuma ? Momy tace

"Bari dae sekin dawo ma 'karasa maganar, dama abinda yasa na kiraki kenan"

"Toh Momy sena dawo" Simrah ta fad'a tana katse wayar, dae_dae lokacin da wayar hannun Mami ta daki glass d'in dake jikin stairs wanda hakan yaja hankalin Simrah ta juyo da wani irin sauri

"A'ah Mami.." Simrah ta fad'a tana 'ka'kalo wani murmushi, sedae kana kallan fuskarta kasan wannan murmushin ne da ake kira da yafi kuka ciwo, Mami ta kalleta tana 'karasa hawowa step d'in tace

"Na'am..dawa kike waya ne.. Keda kikace zakiyi bacci ? Wata 'katuwar ajiyar zuciya Simrah ta sauke tana fad'in

"Wallahi wata 'kawata ce..muna magana ne akan lecture d'in gobe"

"Gaskiyane, hakan nada kyau" Mami ta fad'a tana wucewa, Simrah ta bita da kallo tana sake sauke ajiyar zuciya sannan ta wuce wani d'aki dake a jerin d'akunan da suke saman, tana shiga ta saka key ta zauna kan gado tana sake sakin ajiyar zuciya, dae_dae lokacin da wayarta tayi 'kara, ta kalli me kiran nata, seta d'aga tana kaewa kunnenta fuskarta a had'e tace

"Ae gashi nan garin saurin kin nan yasa Mami ta kusa kamani" Momy tace tana dafe 'kirji

"Amma dae bata kamaki ba ?

"Ehh mana ae ina da wayo nima" Simrah ta fad'a har lokacin fuskarta bata saki ba, Momy tace

"Toh yayi".... A d'aya 'bangaren kuwa Mami na shiga d'aki seta fara sintiri kamar me safa da marwa, taje can ta dawo nan, seda ta gaji dan kanta sannan ta dawo ta zauna a bakin gadon hannayenta dukka biyun ajje akan gadon, tafi kowa sanin halin step sister d'inta ta haka zalika d'iyarta ta shiyasa tun farko ta'ki amincewa da 'kudurinsu dan kuwa ta riga ta sani ba dan komae suke son Simrah ta auri Don ba sedan dukiyar daya keda ita kasancewar duk yawancin wasu dukiyar Alhaji Kabeer d'in sunan Don ne akan ha'k'kin mallaka, gashi kuma yanzu ya bud'e wani companyn ma da sunansa, ba su kad'ae bama tasan duk wadda zata aureshi zata auresa ne saboda kud'in daya ke dashi, dole ma ta samo mafita, kamar wadda aka tsikara ta mi'ke ta nufi wayarta dake ajje kan mirror tayi dialing number hajja kaltume ta kira, bugu 1_2 ta d'auka, kafin Mami tace komae hajja kaltume tace

"Kodae sa6a number kikayi ne yau kam ? Mami ta sauke ajiyar zuciya tace

"Noo..ba sa6a number nayi ba..ke d'in dae kena kira"

"Nii hajja kaltume ?

"Ehh ke dae, lokacin amfaninki ne yazo" Mami ta fad'a tana neman waje ta zauna, Hajja kaltume ta she'ke da dariya kana tace

"Dama nasan ko ba dad'e ko ba jima sekin nemeni, dan kuwa ni kujerar zama ce zama dani dole" Mami ta d'an 'bata fuska

"Bar wani cika baki haka nan mana, yanzu dae ba wannan ba kina jina ? Wani aeki zaki min" Hajja kaltume tace

"Qwarae kuwa ina jinki.. Me kike da bu'kata"

"So nake ki samomin er 'kauye me 'kananun shekaru wadda batayi karatun boko ba.." Hajja kaltume tace

"Toh fah.. Er 'kauye kuma ? Hala an amince da kawo er aeki a gidan naki bayan tsayin shekarun nan ? Mami ta murza goshinta kafin ta sauke ajiyar zuciya tace

"Ohhh god.. Ba wannan bane, yanzu dae zaki samomin ko yaya ?

"Wannan kam ae ya zama dole ne, amma nawa ne kud'in aekina ?

"50k" Mami ta fad'a a ta'kaece, Hajja kaltume ta jinjina kae sannan tace

"Ohk yayi..amma fah kinsan nima wata zan bawa aekin, dan akwae wata dana sani takan zuwa cikin 'kauye haka ta dinga samowa gidan attajirae irin naku en aeki, toh kenan a cikin kud'in zan bata ? Mami tace

"I will give her 10k, pls ayi aekin cikin sirri and kar a wuce sati 2 pls, da zarar an samu kimin magana"

"Baki da damuwa hajiya hadeeza ikon Allah, mata a wajen Alhaji kabeeru uwa..."

"Thank u" Mami ta katseta da fad'in hakan, sannan ta kashe wayar tana lumshe idanunta gami da sauke ajiyar zuciya, lallae aeki ne babba a gabanta wanda dole seta tashi tsaye akan hakan.....


..........Wajen 'karfe 8 ne na daren ranar juma'a, tana zaune a d'akinta tana bitar wani littafi da aka fara musu a makarantar darensu na fawakihush shahiyya, daga tsakar gidan ta jiyo muryar inno na kiranta, seta ajje littafin sannan a hankali ta mi'ke ta fita tsakar gidan, ta 'karasa ta tsugunna tace

"Gani" Inno tace

"Alhaji wadata na jiranki a waje" Jikinta a sanyaye ta mi'ke ba tare da tace komae ba tayi hanyar soro, Inno tace

"Ke..zonan wallahi baki isa ba ! Wato so kike ki koreshi koh ? Shiyasa idan yazo kike tafiya furkae furkae dake kamar wadda aka koro, zoki d'auki wannan mayafin ki saka" Wani yawu ta had'iya da 'kyar sannan ta juya a sanyaye ta koma cikin d'akin, can se gata ta fito ta kalli Inno tace

"Yayi daud'a" Inno ta mi'ke tana fad'in

"Bari na samo miki wani" daga haka ta shige d'akinta, can se gata ta fito daga d'akin hannunta d'auke da wani yalolon mayafi ta mi'ka mata tace

"Gashi nan..maza saka kije, kice ina gaeshesa" Ba tare da tace komae ba ta kar6i mayafin ta wuce d'aki ta cire hijab d'in ta yafa mayafin yanda ya kamata sannan ta fito bata kalli Innon ba tayi hanyar soro kawae, kamar ranar nan yauma a jikin mota ta hangoshi sedae sa6anin ranar yau kam 'kananun kaya ne a jikinsa, suit da wando yasha stocking wanda hakan ya bawa 'katon tumbinsa damar fitowa yayi d'ass dashi, kansa d'auke da irin hular nan ta comrade, a bakin 'kofar ta tsaya kanta a 'kasa, ganinta ya sanyashi 'karasowa yana murmushi yace

"Barka da fitowa kyakykyawa, irin wannan kyau haka" bata d'ago ba se tace a hankali

"Ina wuni" yana murmushin dae yace

"Lafiya 'kalau tare da 'kaunarki" Seta sake yin 'kasa da kanta tana wasa da gefen mayafinta, Alhaji wadata yace

"Ina fatan anyi tunani me kyau game da wannan d'an bawan Allahn" ya fad'@ a maraeraece kamar wani 'karamin yaro, nan take kuma a lokaci guda bugun zuciyarta ya 'karu, se tayi shiru na wasu en sakanni, har seda ya sake cewa

"Wane hukunci aka yanke kyakykyawa ? Seta lumshe idanunta sannan ta bud'e su a lokaci guda tana jin yadda sautin bugun zuciyarta ke 'karuwa kamar zata fito daga 'kirjinta, ta sani yadda yazo da sigar neman auren nata kwata_kwata be mata ba, haka zalika kamar ya nuna ze siye tane, sedae bata sani ba koh yayi hakan ne saboda son kud'in baban ilyasu ? Dan duk wasu alamu sun nuna mutumin kirki ne a zahiri sedae bata san bad'ini ba, amma dae hukuncin data yanke d'in shine dae_dae ko dan ta tsira da mutuncinta, dan haka cikin siririyar muryarta ta furta

"Na amince !!!!!!......

Kuyi manage da wannan pls 🥺🤧

Innocent Gee.......✍️


https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN



Please Login or Register in order to submit comment