Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ya fito da ita ya fara 'ko'karin kunnawa, Sameer daya lura da abinda yake 'ko'karin aekatawa yaja wani wawan birki sannan ya dakata yana kallan Don da dukda birkin daya taka hakan besa shi fasa aekata abinda yake niyyar yi ba yace yana kallansa

"Malam meye haka?" Don ya jefa masa wani kallo kafin yace cikin basarwa

"Da akae?" Sameer ya sake had'e rae

"Yanzu saboda rashin mutunci a gaba na zaka sha wannan abar?" Don ya kalleshi cikin tuhuma yace

"Who are u?" Sameer ya dafe kansa sannan yace

"Dama na dad'e da sanin ni ba kowa bane a wajenka, ka aekata duk abinda kayi niyya" daga haka yaja motar da wani irin gudu, Don yaja tsaki sannan ya maeda ta cikin aljihunsa, har suka isa gidan ba wanda ya sake kallan d'an uwansa ko yace masa wani abu........


______Wajen 'karfe 10pm ya shigo d'akin Mamin kae tsaye d'akin Fawaz ya wuce ya d'ora hannunsa ze tura 'kofar wayarsa tayi ringing, seya dakata ya d'auki wayar yana karawa a kunnensa Daga can 'bangaren Irfan yace

"Don!" Yace a hankali

"Ina ka shiga?" Irfan yace

"Hmm ba zaka gane bane Don, wlh kome a ciki cikin satin nan zan gudo haba, baba ya kasa gane bazan iya rayuwa a garin nan ba, na riga na saba da kano" Don ya d'anyi shiru sannan yace

"ohk" daga d'aya 'bangaren Irfan ya shafa kansa kamar Don d'in na ganinsa kana yace

"Don bafa kud'i a hannu na" Lumshe ido kad'an yayi sannan yace

"Ohk zan turamaka"

"Godiya nake" Irfan ya fad'a yana murmushi daga haka ya katse wayarsa, shi kuma ya 'karasa ya tura 'kofar d'akin a hankali, Fawaz na zaune kan gadon da pillow akan cinyarsa ya d'ora wani jotter akan pillown da biro yana rubuta, Don ya 'karasa yana kallansa kamin ya nemi waje ya zauna gefen gadon yace

"Boy!" se a lokacin ya lura da shigowar sa ya d'ago da sauri yana kallan yayan nasa, seya maeda jotter 'kasan pillown yana kallansa da murmushi kan fuskarsa yace

"Bhai...yanzu ka shigo?"

"Ehh" ya fad'a a ta'kaece yana jinjina kae sannan ya d'ora da

"Me kake yi har yanzu ba kayi bacci ba?" Irfan ya d'an sosa kae yana yin 'kasa da kae yace

"Karatu....nake d'an yi gobe muna da test"

"Muga littafin!" Don ya fad'a yana kafeshi da idanunsa masu kaefi, Irfan ya kasa d'ago kae ya kalleshi kamar me tunani seya d'ago yace

"English ne fa"

"Ohk..ayi karatu lafiya" ya fad'a yana mi'kewa da murmushi kan fuskarsa ya 'karasa ya bawa Fawaz d'in side hug sannan ya juya sanda Fawaz yake fad'in

"Gud nyght bhai" bece komae ba ya fita daga d'akin ya kullo masa 'kofar, Fawaz ya sauke wata gauruwar ajiyar zuciya yana d'ora hannunsa a kansa........



.........Washe_gari wajen 'karfe 3pm Ammi ta fito daga kitchen ta 'karasa cikin parlourn Mami ta nemi waje ta zauna, Mami ta 'karaso cikin parlourn tana kallan Ammi tace

"Ba dae tafiya ba?" Ammi tayi murmushi sannan tace

"A'ah, Magana nakeso muyi ne" Mami tace tana neman waje ta zauna

"Toh.. Ina jinki akan menene?" Ammi ta gyara zama sannan tace

"Akan Adnan ne!" ta fad'a tana kallan Mamin sosae, Mami ta sake gyara zama tana kallan Ammi sannan ta d'an motsa kanta alamar tana ji, ganin haka ne ya sanya ta sauke numfashi tace

"Meze hana kafin komae ya kammala a fara yin wani abu daze kawo wani kusanci a tsakaninsu haka..." Mami tana kallan Ammin tace

"Kamar ya fa!" Ammi tace

"Kamar kae masa abinci haka da sauransu dae... " Mami ta gyara zama har lokacin tana kallan Ammi tace bayan ta sauke numfashi

"Ehh toh ban katse miki hanzari ba amma akwae abinda nake jira ko kuma ince lokacin da nake jira yazo, amma ba yanzu ba yanzu dae ki dage ki koya mata girki tukun na" Ammi ta d'ago tana kallan Mami sosae, Mami ta d'auke kae sannan tace

"Haka yayi koh?" Ammi tace bayan taja numfashi

"Ehh amma dae yadda na fad'a d'in ma ki duba zancen" Mami tace

"Toh.. Toh shikenan a fara gwada hakan" Ammi tayi murmushi tace

"Yawwah.." Mami ta mi'ke tana fad'in

"Ni zan shiga ciki Allah ya taemaka"

"Ameen" Ammi ta amsa tana mi'kewa tayi hanyar d'akin da Azrah take, yayinda Mami kuma ta haye sama.....


.....Yau kam data tashi ciwon cikin da sau'ki dae ba kamar jiya ba, dan yau ciwon cikin ne kawae babu ri'kewar 'kafar, wajen ma data gurje jiya ta shafa mae a wajen dama tun jiya, Wajen 'karfe 3pm ne Zarah ta shigo d'akin da sallama, Azrah ta d'aga ido ta kalleta da murmushi kan fuskarta sanda take zaune a 'kasan d'akin kan dadduma, Zarah ta 'karasa ta zauna kan gado sannan tace

"Sannu Aunty Azrah ya jikin?" Kunya duk seta sake kama Azrah d'in, gashi kuma wani dad'in abin kunyar wae Aunty, seta sunkuyar da kanta a hankali ta furta

"Da sau'ki" tana wasa da gefen mayafin jikinta, Zarah tace

"Dama ya sayyadi ne yace ince miki yana miki sannu, Allah ya 'kara afuwa" da sauri Azrah ta d'ago tana kallan Zarahn se kuma ta sake yin 'kasa da kae tace

"Ameen..nagode" Zarah ta d'an dinga janta da hira suna zaune a haka Ammi tayi sallama ta shigo d'akin, duka suka amsa, ta kalli Zarah tace

"Kina nan ashe?"

"Ehh Ammi ina taya Aunty Azrah hira ne" murmushi Ammi tayi tace

"Hakan yayi kyau" Seta maeda dubanta kan Azrah tace

"Zaki iya yimin wani aeki?" Azrah ta kalli Ammi sannan tace a hankali

"Ehh Ammi.." Karo na farko kenan data kira Ammin da sunanta kenan tun zuwanta gidan, Ammi tayi murmushi sannan tace

"Ohk toh tashi ki shirya zan aeke ki ne!" Da "toh" ta amsa tana mi'kewa, Zarah ta kalli Ammi tace

"Amminmu zan wuce gida sekin dawo" Ammi tace

"Toh Zarah" daga haka Zarah ta kalli Azrah tace

"Bye Azrah, se ranar Asabar kenan?" Jinjina kae tayi tana kallan Zarahn sannan tace

"Ehh" Zarah tace

"Allah ya kaemu" ta fad'a tana ficewa daga d'akin....Ammi ta dawo da dubanta kan Azrah tace

"Muje ki chanja kaya" Binta kawae Azrah tayi harta fito mata da wata sabuwar abaya coffee me kyau da mayafinta, babu musu ta kar6a ta saka, Ammin ta 'karasa gaban mudubi ta d'auki turarukan data bata su tace ta saka, nanma babu musu ta kar6a ta fesa d'in sannan ta ajiye, Ammi tace

"Muje koh?" Kallan kanta sosae Azrah tayi a mudubin sannan ta dubi Ammi tace a hankali

"Ammi bazan iya fita waje a haka ba" Ammi tayi murmushi tana sake yabawa da hankalin Azrahn tace

"Ae ba waje zakije ba, a cikin gidan nan ne, babu damuwa uhmm?" Seta jinjina kae kawae tabi bayan Ammin har suka isa kitchen, Ammi ta kwaso wasu warmers guda 2 ta mi'kawa Azrah tace

"Jeki ajje a dinning d'in d'akin Mami" kar6a tayi tayi gaba ta wuce zuwa d'akin, babu kowa a ciki seta ajiye sannan ta koma kitchen d'in, Ammi ta d'akko wasu jugs ta sake mi'ka mata tace

"Idan kin kae ki gaeshe dashi" wani irin bugawa taji 'kirjinta yayi tana tunanin wanda zata je ta gani d'in tunda dae tasan ita matar aure ce, seta mi'ka hannu ta kar6a jikinta a matu'kar sanyaye ta fita daga kitchen d'in tana tafiya a hankali, Ammi ta bita da kallo harta fice, tafiya take a hankali harta 'karasa dinning Area d'in, jikinta ya sake d'aukar rawa yadda ta hango wani mutum zaune kan d'aya daga cikin kujerun kansa bisa wayarsa yana dannawa, ji tayi kamar ta koma toh amma kuma ta koma tace wa Ammi mene? Dan haka kawae tayi ta maza ta 'karasa wajen ta hau step d'in sannan ta ajje jugs d'in wanda bata san da 'karfi ta ajje ba se hakan ya basu damar yin er 'kara wadda ta sakashi d'ago idanunsa daga kan wayar da yake dannawa ya kalleta, itama shi take kallo se hakan ya bawa 'kwayar idanunsu damar shiga cikin na juna, da wani irin hanzari ta janye idanunta, Don ya wani mi'ke a fusace yana kallanta ganin alamar itace ta kawo masa abinci, cikin wata irin murya ya furta

"Who are u?" Shiru tayi jikinta yana cigaba da rawa ga cikinta daya sake murd'awa, tana tunanin wanene wannan mutumin? Bata gama tunanin ba ta sake tsintar firgitacciyar muryarsa bayan ya saka hannu yayi fatali da wasu daga cikin abubuwan dake kan dinning d'in yace cikin d'aga murya

"Who are u?" Mami da sakkowarta kenan daga sama ta 'karaso wajen jin hayaniya ta kalli Azrah data toshe kunnuwanta tana kuka sannan ta dawo da dubanta tana kallan Don tace

"Ya isa haka Son" Cikin d'aga murya yace

"How dare her? Wacece ita?" Mami ta bud'e baki zatayi magana ya sake tarar numfashinta da fad'in yana huci

"Mami...who is she?" Mami ta sake kallan Azrah sannan ta kalli Don tace

"Ur wife!" Se yayi shiru yana kallan Mami yana so ya fassara kalmar wife a 'kwa'kwalwarsa amma 'kwa'kwalwar ta'ki bashi had'in kae, se can daga wani 6angare ya tuna fa wife fa na nufin mata ne, seya sake d'aga lumsassun idanunsa ya saukesu kan Azrah ya sake kallan Mami sannan yayi wani ya'ke wanda akace yafi kuka ciwo yace yana kallan Azrah

"Who the hell do u think u're? Ni? The whole me? Oh god" seya dawo da dubansa kan Mami yace

"Kina magana ne fa akan wannan abin" ya fad'a yana pointing Azrah, sannan ya cigaba da fad'in

"Bagidajiya er 'kauye kuma bazawara, god of mercy" ya fad'a yana dafe kansa saboda yadda yaji kan nasa yana sara masa haka zalika saboda tsananin 6acin rae jijiyoyin kansa sun fito rad'a_rad'a, se kuma ya d'ago ya watsawa Mami jajayen idanunsa da suka rine daga aenahin coloursu zuwa ja haka zalika yanayin yadda shanyayyun idanunsa suke yasa dole ya tsoratar da wanda yake kalla, cikin dakakkiyar murya yace

"Well, kinyi abinda kike so Mami, nima kuma zanyi abinda nakeso.." Ya d'an dakata sannan ya cigaba da fad'in

"She will never ever be my wife, bata da wannan matsayin hasalima ma ba zata ta6a kaewa ba, who is she? Ohk lemme just make it clear.." Seya sake yamutsa sumar kansa yace

"Ohhh..ohhh imagine fa wannan abin shine mat...." Se be 'karasa ba yace

"Shettt! Though dae ban ta6a kallanta a matsayin wife d'ina ba, in fact ma hakan ba abune me yiwuwa ba, but idan nayi mata saki 3 shikenan komae ya 'kare koh? Ya fad'a yana jefa musu jajayen idanunsa, Tunda ya fara magana Azrah ke kallansa babu ko 'kiftawa tana kallan yadda yake magana tana rarrabe duk wata kalma da yake fad'a d'in, zuciyarta a lokacin ta 'ke'kashe hawayen nata ya tsaya cakk, haka zalika bugun zuciyarta yana fita ne a hankali a hankali, 'kafafunta ma sun dena wannan rawar da sukeyi ta tsaya ne kawae kamar an dasa ta tana kallansa, Mami kuwa is speechless dan bata ta6a tsammanin haka daga Don d'in ba, she thought duk wani abu da zata mishi ko bayaso ze kar6a ne da hannu biyu sedae yau taga sa6anin hakan tun daga cikin 'kwayar idanunsa, dan tunda take Adnan d'in be ta6a tsayawa kamar haka gabanta yana fad'a mata maganganu makamancin wad'an nan ba, haka zalika bata ta6a ganin irin fushin dake kwance a fuskarsa yau d'in nan ba, kafin ta gama tunanin ta sake tsintar firgitacciyar muryarsa yana fad'in bayan ya maeda dubansa kan Azrah

"Yau kam ki tabbatar kin bar cikin gidan nan, base gobe ba...dan kuwa ni Adnan na datse...........





End of SANADIN KADDARATA (THE BEGINNING)

_Anan na kawo 'karshen Sanadin Kaddarata (the beginning) me son cigaba da karanta Sanadin Kaddarata (the conclusion) zata tura 300 ne ta wannan account d'in_👇

_8124818273
Zahra Yusuf Ishaq
Opay_

_Shedar biya ta wannan number 08124818273_

_Dan neman 'karin bayani za'a iya tuntu6ata ta wannan number 08124818273_

Mhiz Innocent......✍️



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment