Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aya 'bangaren aka sake cewa

"Don..yau mafa akwae zuwa club.." Lumshe idanunsa yayi kamar ba zeyi magana ba se kuma yace

"Irfan...zanje training yau, i will call u later" daga haka be jira amsar da Irfan d'in ze bashi ba ya katse wayar sannan ya wuce part d'in dad... A parlour ya sameshi zaune yana duba wasu takaddu ya 'karasa ya zauna a 'kasan kujera bece komae ba, seda dad ya gama abinda zeyi sannan ya d'ago ya kalli don yace

"Kamar na hanaka saka wannan sar'kar koh ? Ba tare da ya d'ago ya kalli dad ba yace

"Sorry.."

"Sorry 4 ur self, oh yah bani ita.." Dad ya fad'a yana mi'ka masa hannu, babu musu ya saka hannu ya ciro sannan ya mi'kawa dad, Alh kabeer ya kar'ba ya ajjeta gefensa sannan ya maeda hankalinsa kan don yace

"Adnan.." Seya d'ago ya kalli mahaefin nasa bece komae ba dad ya cigaba da fad'in

"Zan maka wata magana me muhimmanci, and plss ka d'auki abin kaema da muhimmanci, na gaji da wannan shirmen da kake Son, ya kamata ace ka fahimci ka girma yanzu haka kaeya kamata ka dinga lura da tarbiyyar Fawaz " Seya juya ya d'auko wasu set d'in mukullae ya mi'kawa don yace

"Ur first Company's keys, mun gama komae duk abinda zanyi munyi shine tare da abokinka sameer, and shiya za'bi sunan companyn wanda yasan zeyi dae_dae da ra'ayinka, akwae dalilin da yasa ban sanar dakae ba se yanzu da komae ya kammala" Cikin rashin fahimta ya d'ago yana kallan dad d'in, gaba d'aya he is confused, how za'a ce ya kula da company ? Cikin dakakkiyar murya yace

"Dad..actually I don't have time da zan iya kula da branch na company guda, in fact ma I don't have experience da zan iya running company, And ta yaya zan samu tym d'in training da kuma na wasana"

"Ohk kana nufin ba zaka iya kularmin da company ba akan wani wasan cricket ? Dad ya fad'a sounding angry, ba tare da wata damuwa ba yace

"Yes pls dad..."


Mhiz Innocent...........✍️




https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_4


____"Ohk fine" Dad ya fad'a yana kallan Mami dake shigowa d'akin, shi dae don kansa na 'kasa be d'ago ba, Mami ta 'karaso ta zauna a kusa da dad fuskarta d'auke da murmushi tace

"Barka da zuwa yalla'bae"

"Barka" ya fad'a a gajarce, Seta kalleshi sosae kafin ta kalli don dake gaesheta, ta amsa tana mayadda hankalinta wajen dad tace cikin sanyi

"Wani abune ya faru ranka ya dad'e"

"Ur son" ya fad'a har lokacin fuskarsa babu annuri, Seta kalli don tace

"Meya faru son ? 'Dagowa yayi ya zuba mata shanyayyun idanunsa sedae bece komae ba ya maeda kan nasa 'kasa, Mami ta kalli dad tace

"Wani abu ?

"Yes, sabon branch d'in dana bud'e akansa muke magana" Seta kalleshi sosae alamar rashin fahimta tace

"Toh meya faru yalla'bae ? Ko akan maganar companyn ne ?

"Yes, he said baze iya ba, na rasa gane kan wannan yaron, in banda shirme babu abinda ya saka a gaba ? Yanzu idan na kwanta na mutu waye ze cigaba da kularmin da dukiya ? Ko kuwa za'a d'auko wani bare ne a d'ora akae" Mami dae kawae kallan dad take, se can ta girgiza kae

"Noo, hakan baze yiwu ba, Son" ta fad'a tana kallan don, Ya d'ago kad'an ba tare da ya kalleta ba, ita kuma ta cigaba da fad'in

"Plss ka kar'bi wannan tayin na mahaefinka kaaji koh ? In Sha Allah zaka iya couz I trust u kae d'in na daban ne, kaji koh ? Wani irin numfashi yaja ya sauke, he just can't say No akan abinda Mami keso couz her love for him is uncountable and he loves her more ( Mami ta raeneshi tun yana yaro, he is just 10 lokacin da mamansa ta rasu and Mami ta cigaba da kula dashi ba tare da ta ta'ba nuna wani banbanci tsakaninsa da Fawaz ba, zema iya cewa kamar tafi 'kaunarsa akan Fawaz d'in, shiyasa baya tunanin akwae abinda Mami zata saka baki akan yayi ya kasa yinsa, yana kallantane kawae a matsayin mahaefiyarsa wadda ta haefeshi ) A hankali ya d'ago idanunsa da suka kad'a sukayi jajir saboda 'bacin rae a hankali yace

"Ohk" abinda ya iya fad'a kenan ya tashi ya fice daga d'akin, Be zame ko ina ba se d'akinsa, yana tafiya dae_dae ze wuce ta part d'in Yakumbo, wata 'yar budurwar yarinya chocolate colour ta fito daga part d'in, ganinsa ya sanya ta fad'in

"Barka da safiya bhai" ko kallan inuwar ta beyi ba ballanta sharar data kwasota ya wuce, yana zuwa ya zauna akan bed, ya d'auki bottle water dake kan side drawer ya d'aga ya shanye tass sannan ya ajjiye yana sauke numfashi, a hankali yakae duka hannayensa ya tusa cikin kwantacciyar sumar kansa ya hargitsa ta idanunsa a lumshe, se kuma ya mi'ke kamar wanda aka tsikara ya saka hannu ya zubar da jerin turaruka da maya mayan dake kan mirror d'insa sannan ya koma ya zauna yana sake dafe kansa, wayarsa dake kan gado ta d'auki ringing, beko kalleta ba ballanta wanda ke kiran yasa ran ze d'aga, ya riga yasan a irin wannan lokaci idan abu makamancin haka ya faru Mami kanzo ta lallasheshi, gudun karma tazo dan yau har ita yana fushi da ita ya sanyashi mi'kewa ya sakawa 'kofar d'akin nasa key ya barshi a jiki sannan ya dawo ya kwanta rigingine thinking abubuwa da dama..


_____A hankali take takawa hannunta d'auke da bokiti guda 2 wanda ta tura 1 cikin 1 dan yayi mata dad'in ri'kewa, wajen maghrib ne, mutane anata shirye shiryen shiga masallaci, wasu na alwala wasu na shiga masallaci, dae_dae wani 'kayataccen gini babba wanda ya tsaru tsaruwa ta aenahi, tasha zuwa wucewa ta wajen tana ganin sanda ake ginin wanda yara suke baebaye wajen suna kallo, yanzun ma data kalli gefe seda ta hango wasu yara suna kallan gaban ginin, haka kurum ta tsinci kanta dasan ganin gaban ginin, dan haka ta cigaba da tafiya, iya tsaruwa wajen ya tsaru, ita kanta seda wajen ya birgeta, seta kae dubanta wajen wani rubutu da akayi a saman ginin da manyan ba'ki me turuwa "DON NO 1" ta karanta akan la66anta tana yin gaba ta 'karasa zuwa gida, A tsakar gida ta tadda ilyasu wanda tunda ya dawo daga cikin kano bata ta6a ganinsa da daddare a cikin gidan ba, Cikin tafiyarta ta nutsuwa ta shigo gidan da sallama, Ilyasu ya amsa yana kallanta bakinsa kamar ze fad'o saboda dariya, Tunda tayi sallama bata sake kallansa ba ta 'karasa cikin gidan ta ajje bokitin sannan ta juya ta wuce malallauta ta d'auro alwala, tunda ta tsuguna tana d'auro alwala yake kallanta koze hango wani abun daga jikinta, sedae bata bashi wannan damar ba, tana idarwa ta mi'ke, dae_dae lokacin inno ta fito daga d'akin ta ta kalli Azrah

"Kin shigo kenan ? Kinfi 'karfin ki sanar dani ne ko me ? Kafin ta kae ga cewa komae ta jiyo muryar ilyasu yana fad'in

"A'ah fa inno, shigowarta kenan baewar Allah kuma da alama sallah zatayi" Seta d'aga idanunta masu wani irin mae'ko ta kalli ilyasu a karan farko taji abinda ya fad'a d'in ya birgeta, Inno ta wurgawa ilyasu harara tace

"In dae shishshigi ne ae kafi kauri a wajen" Shi dae be tanka ta ba dan hankalinsa yana kan Azrah yana kallan narkakkun idanunta dake neman zautar da shi, Azrah ta mi'kawa Inno kud'in tace cikin sanyi

"Gashi" Inno ta kar6a tana murmushi tana kallan kud'in kafin tace

"Yadda kike da wannan sa'ar zanyi tunani akan wani al'amari" tayi maganar a dun'kule yadda duk wanda yaji abinda ta fad'a d'in baze fahimta ba se ita d'in data fad'a, ita dae Azrah tayi gaba 'kirjinta na bugawa tana fatan Allah yasa kuma ba wani abun bane ta wuce d'akinta..Tunda tayi sallahr maghrib bata tashi ba har seda tayi Ishaa kasancewar ranar juma'a ce babu makarantar dare, haka ta zauna tayi ta addu'a akan Allah ya kawo mata mafita akan wannan zaman nata a cikin gidan nan, tana nan zaune tana jin abinda ke faruwa a tsakar gida har wajen 'karfe 10 tana karatun qur'ani aka fara wata iska sosae alamar hadari ke had'uwa, seta kae qarshen ayar da take akae ta ajje qur'anin ta mi'ke ta fito tsakar gidan dan kwashe shanyar da tayi d'azun, da sauri ta koma baya ganin wata halitta daga can wajen soro, kafin ta d'au wani mataki Ilyasu ya taho yana murmushi yace

"Qanwata nine fa, Naji hadari ya taso ne shiyasa na fito" Ita dae ba tace komae ba se wani ya'ke da tayi tana d'aukar kayanta ta koma cikin d'akin, bata barsu ba seda ta ninke su ta ajje cikin jakar kayanta sannan taja er torchlight d'inta ta kashe tana neman waje ta kwanta, tana bala'in son irin wannan yanayi, idan da rana ne ma takan fito cikin ruwan dan a lokacin ne kawae take jinta fresh kuma cikin nishad'i, amma kasancewar yanzu dare ne ya sanya ta kwanciya dukda tasan da wuya ta iya baccin...Wajen 'karfe 12 Inno ta fito daga d'akinta dan zuwa band'aki, seta zabura da sauri ta koma baya tana fad'in

"Na shiga 3 ni Habi" ta fad'a tana dafe 'kirji, ilyasu dake tsaye nesa kad'an da d'akin Azrah yayi wani ya'ke yace

"Uhmm Inno kece ? Kallansa kawae Inno keyi kafin ta 'kan'kance idanunta tace

"Meya fito dakae a wannan daren ? Ga ruwa" Seya shafa 'keyarsa yace

"Ni tun ina kano gaskiya bana iya bacci idan ana ruwa shiyasa"

"Lallae" Inno ta fad'a tana kallansa sosae kafin ta d'ora da

"Yanzu kam ae ruwan ya d'auke koh ? Cikin daburcewa yace

"Ehh...ehh dama d'akin nake niyyar komawa kika fito" Wani kallo ta yiwa ilyasun ba dae tace komae ba ta bishi da kallo sanda yake komawa hanyar soro, itama ta wuce ta d'auki buta ta shige band'aki....Washe gari wajen asuba Azrah ta farka daga nannauyan baccin daya d'auketa kasancewar yadda garin yayi dad'i yasa baccin ya mata dad'i sosae, Da mamaki take kallan yadda take iya hango tsakar gidan nasu tana daga cikin d'akinta, ta riga ta saba komae zafi komae sanyi bata d'age labulen d'akin nata, dan ta d'aukeshi ne kamar wata kariya kuma 'kofa a wajenta, amma me se gashi ta ganshi a d'age, da sauri ta mi'ke tana kallan tsakar gidan, babu kowa dama kuma tasan ba wad'anda zata gani d'in dan daga Innon har Baban ilyasun babu wanda ke tashi sallahr asuba se gari yayi haske, Seta janyo labulen dake a d'age tana kallo zuciyarta cike da tunani fall a haka ta wuce ta d'auro alwala sannan ta dawo d'akin....



___Yakumbo ta kalli buhaisa da shigowarta d'akin kenan tana turo baki tace

"Wae dan wula'kanci cikin gidan ne ba zaki shiga ki gaedasu ba, wannan wane irin Abu ne ? Buhaisa ta sake tura baki gaba tace

"Ni wlh Yakumbo kunya nakeji in shiga ni kad'ae, don Allah ki taso muje" Yakumbo ta ta6e baki tace

"Lallae, wato ga sa'arki koh ? Girgiza kae buhaisa tayi tace

"A'ah ba haka bane..." Kafin ta kaega 'karasa abinda tayi niyyar fad'a sega sallamar Fawaz cikin d'akin, Buhaisa tayi murmushi

"Ashe kana cikin gidan"

"A'ah fa yanzu na dawo daga school, Nazo muyi hira da Yakumbo sirina ne.." Ya fad'i 'karshen a hankali gudun kartaji, aekuwa buhaisa ta she'ke da dariya sannan 'kasa 'kasa tace

"Wlh Fawaz na yadda da sunan nan da kake fad'a mata fa, don Allah kalli Yakumbo wlh koni na fita girma" dariya Fawaz yayi yana neman waje ya zauna ya kalli Yakumbo dake kallansu yace

"Barka da rana granny"

"Barka" ta fad'a a ta'kaice, Seya maraeraece fuska ya 'karasa ya zauna a gaban Yakumbo yace yana 'bata rae

"Se sauri nake in dawo muyi hira waeni me kaka, amma wae barka kawae zata cemin, gaskiya bani da sa'a" ya fad'a yana kauda kae, Murmushi Yakumbo tayi dan harga Allah tana 'kaunar jikan nata sosae tace

"Kaji min ja'iri, zauna muyi hirarmu abimmu" Seya juyo yana murmushi yace

"Yawwah, dats my Yakumbo"

"Amma kafin nan, tashi ka raka buhaisa taje ta gaeda Mami" da "toh" ya amsa yana mi'kewa ya kalli buhaisa yace

"Se kace wadda za'a cinye idan ta shiga can d'in" Harara ta jefa masa tana fad'in

"Ehh d'in, ina ruwanka"... Suka jera suna tafiya har zuwa part d'in mamin, suna tafiya suna hira kasancewar akwae sabo sosae a tsakaninsu kuma sa'an nine dan kwana 7 buhaisa ta bawa Fawaz, da sallama dukkansu suka shiga parlourn Mamin sedae yanzu Fawaz na gaba, buhaisa na bayansa suka 'karasa cikin d'akin, Da fara'a Mami ke kallan buhaisa data 'karaso ta tsuguna a 'kasa tace

"Barka da rana Mami"

"Barka kadae buhaisa, kina lafiya" Mami ta fad'a tana murmushi

"Lafiya lau Mami" Mami ta kalli Fawaz daya d'auki remote ze chanja channel tace

"Toh uban iya, hala nina saka ? Turo baki yayi kamar wata mace yace

"Mami naga ba kalla kike ba"

"Haka na fad'a maka ? Kafin yakae ga cewa wani abun, wani sautin hill shoe ya cika d'akin da sautinsa, cikin en sakanni mamallakiyar takalmin ta bayyana sanye cikin wani wando falazo da wata had'ad'd'iyar riga, ta yafa mayafi wanda ko wuyanta be wuce ba, hannunta ri'ke da wata jaka dake sa'kale a hammatarta, idanunta sanye cikin wani had'ad'den glass haka bakinta cike da chewing gum ta 'karaso cikin d'akin tana tauna shi, hango Mami a zaune ya sanyata 'karasawa da sauri ta rungumeta tana fad'in

"I miss u Mami"

"Miss u too my dear" Mami ta fad'a tana murmushi sannan ta d'ora da fad'in

"Ina Yaya ? Tana lafiya ?

"Lafiya 'kalau take, tacema na gaesheki" Matashiyar da a'kalla zata kae 23years ta fad'a tana Neman waje kusa da Mami ta zauna, Seta kalli Fawaz dake kallan T.V abinsa kamar be ganta ba tace

"Autan Mami, yada shariya" Se a lokacin ya kalleta yana ta6e baki yace

"Ohh I thought baki ganni ba"

"Wane mutum Auta" Se yayi murmushi yana juyowa gaba d'ayansa yace

"Aunty Simrah kina lafiya"

"Lafiya 'kalau, but..nifa banga yah adnan ba, wallahi I missed him a lot da kewarsa na dawo" ta fad'a yanayin fuskarta na chanjawa, Mami tayi murmushi tace

"Lallae simrah wlh na yadda baki da kunya, a gabana koh ? Seta maraeraece fuska tace

"Toh Mami kin'ki ki saka baki akan maganar, Allah kuwa da tuni an wuce wajen"

"A'ah nikam ba dani ba" Mami ta fad'a tana kallan buhaisa data mi'ke tana kallan Mami tace

"Mami bari na koma"

"Ohk, ki cewa Yakumbo ina nan shigowa anjima"

"Toh" buhaisa ta fad'a tana yin gaba ba tare da tabi takan Fawaz ba, tana fita daga part d'in ta jiwo muryar Fawaz yana fad'in

"Ke yarinyar nan, wato ni dana rakoki bama zaki jirani ba koh ? Harara ta jefa masa tana fad'in

"Wae yarinya..lallae ma yaron nan" bata jira ya bata amsa ba tace

"Wacece wannan wae ?

"Aunty simrah ?

"Yes" ta fad'a a ta'kaece

"Wae baki santa ba ? Er yayar Mami ce fa.." Jinjina kae buhaisa tayi se kuma tace

"Yes na tuna, but..naji tana zancen yah adnan ne..ko akwae wata alaqar tsakaninsu" 'Daga kafad'a Fawaz yayi kafin ya ta6e baki

"Uhmm toh.. Abinda dae na sani ita ke sonsa..and kinsan halin bhai..ko kallo bata ishesa ba..shikenan kawae nothing more...."

Mhiz Innocent.........✍️



https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_5


_____Ta6e baki buhaisa tayi kamar ba zata ce komae ba se kuma tace

"Lallae iska na wahal da me kayan kara" ta fad'a 'kasa_'kasa, Fawaz yace

"Me kikace ? Ya'ke tayi cikin basarwa tace

"A'ah bance komae ba" d'aga kafad'a yayi bece komae ba, a haka har suka 'karasa part d'in Yakumbo, Suna shirin shiga yayi dae_dae da lokacin da dad shima ze shiga, Dukkansu suka tsuguna suka gaesheshi, cikin fara'a ya amsa musu yana kallan buhaisa

"Abbanki ya shigo yau kuwa ? Seta girgiza kae

" A'ah dad be shigo ba, inaga kose zuwa anjima" Jinjina kae yayi kana ya wuce cikin d'akin, Fawaz ya kalli buhaisa yace

"Lemme go, tunda dad yazo nasan hira zasuyi, anjima zan dawo"

"Ohk" ta fad'a a gajarce tana wucewa ciki, kae tsaye ta wuce kitchen dan yin wata hidimar ko dan ta barsu suyi hirarsu a nutse, Dad ya 'karasa ya zauna a 'kasa kamar yadda itama yakumbon take zaune a 'kasa, da murmushi shimfid'e kan fuskarsa yace

"Barka da rana Yakumbo" Itama cikin sakin fuskar tace

"Barka kadae kabiru, ka yini lafiya" Seya tankwashe 'kafafunsa yana kallan mahaefiyar tasa dake gyara zama yace

"Alhamdulillah" Yakumbo ta numfasa kad'an kafin tace

"Toh madallah, wato dama inaso muyi magana dakae akan wannan yaron, tambayarka nakeso nayi kana sane yake fita tun safe baya dawowa se cikin talataenin dare ? Dad yayi shiru cikin rashin sanin abin fad'a, Yakumbo ta d'ora da fad'in

"Toh kodae kana sane ne bansani ba nake ta kumfar baki, wae ni kana ma kallan 'kwayar idon yaron nan kuwa ? Dad ya sauke ajiyar zuciya yace

" Yakumbo...kinsan sha'anin 'ya'yan yanzu ka haefesu ne baka haefi halinsu ba, kullum cikin yiwa adnan fad'a nake, Haka addu'a ma kullum cikin yi nake akan Allah ya shiryashi, inaga lokacin shiriyar tasa ne kawae Allah be kawo ba..amma In Sha Allah komae me wucewa ne, sannan Yakumbo zancen 'kwayar idanunsa ba shan wani abune ya kawo sauyawarta ba dama can a haka take" Jinjina kae Yakumbo tayi cikin na'am da zancen d'an nata tace

"Toh Allah ya shirya, Amma semun 'kara tashi tsaye akan yaron nan, Allah ya 'kara shiryashi"

"Ameen_Ameen" dad ya fad'a jikinsa a sanyaye kafin ya d'ora da fad'in

"Sannan maganar companyn dana miki an gama komae yanzu haka aeki kawae za'a fara, kinga yanzu daga zarar anyi noman shinkafar se kawae a sarrafata a wancan companyn" Yakumbo tayi murmushi tace

"Gaskiyane Allah dae ya 'kara arzi'ki me amfani"

"Ameen" dad ya amsa da hakan....... A hankali ta 'karaso ta zauna a gefen kujerar da Mami take tace

"Hajiya lafiya naga yau yalla6ae bezo yayi lunch ba, gashi tun d'azu na gama abincin kar yayi sanyi" Simrah dake kusa da Mami ta kalli matar dake magana sannan ta kalli Mami dake fad'in

"Lafiya lau, amma dae bari naje na sameshi" Mami ta fad'a tana mi'kewa, itama matar seta mi'ke tana fad'in

"Nagode hajiya" daga haka ta wuce, Simrah ta kalli Mami tace

"Wae nikam har yanzu matar nan ke masa girki ? girkinta kawae yake ci ? Mami ta Jinjina kae alamar "Ehh" Simrah ta ta6e baki

"Bari muyi aure zan chanja shine" ita dae Mami tayi gaba, kae tsaye ta wuce part d'in nasa... Fitowarsa kenan daga wanka d'aure da towel madaedaeci hannunsa 1 ri'ke da wani 'karamin towel yana goge kwantacciyar sumar kansa, in banda 'kamshin sabulun African Marigold the expensive one ba abinda jikinsa yake, a hankali yake goge ruwan daya ji'ka masa sumar kansa yana kallan kansa a cikin mirror, comb ya d'auka ya sake kwantar da sumar kan nasa, cikin riga da wando kamar yadda ta kasance shigarsa ta ko yaushe ya shirya sannan ya d'auki favourite turarensa ya feshe jikinsa dashi, dama tun d'azu d'akin se wani 'kamshi yake ballantana yanzu kuma wani sassanyan 'kamshi ne ya cigaba da tashi, gefen gado ya koma ya zauna ya janyo takalminsa samfurin slip_on ya fara 'ko'karin sakawa, dae_dae sannan wayarsa tayi 'kara, kallanta yayi "Irfan" ya bayyana akan screen d'in, seya danna accept ya saka a hands free ya cigaba da saka takalminsa, daga can 6angaren Irfan yace

"Don...zaka shigo d'in ne ? Me za'a ajjiye maka" Lumshe idanunsa yayi kamar wanda akawa dole yace

"Shisha is enough"

"Ohk don ba zaka d'an had'a d..." Don yayi saurin katseshi ta hanyar fad'in

"Plsss nothing more..nothing less" be jira amsar Irfan ba ya katse wayar, Dae_dae nan yaji ana knocking 'kofar parlour, se kuma yaji shiru, daga baya se aka fara knocking 'kofar bedroom d'in nasa, ko kallan 'kofar beyi ba seda aka sake bugawa sannan ya mi'ke ya zare key d'in, be tsaya kallan waye ba kawae ya juya ya zauna gefen gadon nasa, Mami ta bishi da kallo sannan ta 'karaso ta zauna akan stool d'in dake gaban mudubi tana kallansa sosae tace

"Son" be d'ago ba sema hannayensa daya d'auka ya cusa cikin sumar kansa, Mami ta sake lowering voice nata tace

"Son..fushi kake dani koh ? Runtse idanunsa yayi sannan ya bud'esu ya sake hargitsa sumar kansa sannan ya d'ago ya zubawa Mami rinannun idanunsa yace

"Meyasa dole se nayi aeki ? Bana son duk wata harkar takura, wasan nan da nake kawae ya isheni, but kun kasa fahimta ta Mami.." Shiru Mami tayi tana kallansa kafin daga bisani tace

"Is ohk..fushin ya isa haka..son meyasa ka kasa fahimtar duk abinda muke muna yinsa ne saboda 'kaunar da muke maka ? Dad loves his son more shiyasa yake so ka fara koyar abubuwa tun yanzu, kasan yadda rayuwa take uhmm" ta fad'a tana kallansa

"Pls kayi wannan ko dan saboda ni da mahaefinka" Cikin wata sha'ka'k'kiyar murya yace

"Ae dama nace zanyi"

"Dats my son" Mami ta fad'a tana murmushi

"Ohh yah smile.." inji mami, kauda kae gefe yayi kafin cikin basarwa yace

"Mami am not in dat mood plss"

"Ohk toh ka tashi yanzu ka fito, ga Amminka can tana cigiyarka taga bakazo kayi lunch ba" Yamutsa fuska yayi sannan yace

"Just tell her tayi wani abin dashi, yanzu zan d'an le'ka club ne" Kallansa Mami tayi sosae

"Son.." Kafin takae ga fad'in abinda tayi niyyar fad'a ya katseta da fad'in

"Bazan kae dare ba, I promised u"

"Promise" Mami ta fad'a

"Yeah" ya fad'a dae_dae lokacin da wayarsa ta fara ruri, Mami ta kalleshi tace

"Bye son" d'aga mata kae kawae yayi, daga haka ita kuma ta fice, Shi kuma ya maeda dubansa kan wayar dake hannunsa wadda sunan "Friend" keta yawo akae, seda wayar ta katse aka sake kira sannan ya d'aga yakae kunnensa sedae bece komae ba, daga can 6angaren sameer yace

"Don.." ( Sunan don ya samoshi ne tun suna primary school, saboda tun a lokacin baya d'aukar raeni komae yana yinsa ne cikin tsare gida, dan haka ya kasance duk wasu friends nasa da hakan suke kiransa )

"Adnan" sameer ya sake fad'a, Cikin basarwa don yace

"Plss karka cemin komae, ashe za'a iya had'a baki dakae amin haka.." Daga 1 6angaren sameer yayi er dariya kad'an yace

"Me aka maka ? Danma an taemake ka an bud'e maka company ?

"Cewa nayi inaso ? Ya fad'a a dake

"No..baka fad'a ba, but mu munaso.., Pls ba wannan ba kasan dae jibi ne za'a bud'e companyn koh ? 'Daga kafad'a don yayi yace

"How will I even know, bayan komae kuna yinsa ne ba tare da izina ba ?

"Ohk yanzu dae na sanar dakae plss ka shirya as early as possible uhmm" Numfashi don ya ajiye kamin yace

"Is ohk, but.. Zan sanarwa da Irfan tare zamuzo" Kamar don yana ganin sameer ya 6ata rae

"Irfan ? Har yanzu ba zaka rabu dashi ba dae ?

"Yes" don ya fad'a yana katse wayar gami da sauke numfashin irin wannan maganar da yayi me tsayi haka.......

.........'Karfe 5 ta shigo gidan a gajiye, ta 'karaso ta ajje bokitin kana ta 'karasa inda inno take tace

"Na dawo, gashi" ta fad'a tana mi'ka mata kud'in dake hannunta, Inno ta kar6a tana 'kirgawa sannan ta kalli Azrah tace

"Ke.. Naji ana maganar wata ma'aekata da za'a bud'e, ke bakisan sanda ake gininta bane hala shiyasa baki zuwa wajen dan nasan za'a samu masu siye sosae" Azrah ta maraerece fuska dan ba 'karya yau kam a gajiye take gashi har wani zazza'bi zazza'bi takeji tace

"A'ah na sani.. Maza ne sukayi yawa a wajen shiyasa bana zuwa" Wani ashar inno ta laelayo tayi sannan ta d'ora da

"Dan tsabar ba'kin ciki, shine zakice maza sunyi yawa, kiji min iyayi da wani kid'ifiri, toh wallahi ahir d'inki,

Please Login or Register in order to submit comment