Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri dan kuwa ta tsorata kasancewar bata san da isowarsa wajen ba, maganar kawae taji, Irfan ya janyo wani dutse ya matsar dashi kusa da ita ya zauna akae, seta d'an matsa daga inda take ta 'kara bada space a tsakaninsu, Irfan yayi murmushi kafin yace yana kallan 'kwayar idanunta wanda ta'ki yadda ta kalleshi

"En mata ya sunanki ? Seta 'kara gyara zama ba tare da tace komae ba, ya sake maemaetawa a karo na 2

"Ya sunanki" Nanma dae shiru, Irfan ya gyara zama yana fad'in

"Ohk nagane..wato dae inna fahimta sunan me tsada ne koh..well yanzu dae ba wannan ba nawa ne abincin ? Se a lokacin cikin siririyar muryarta tace

"Na nawa kakeso ? Irfan yaja numfashinsa jin muryarta me sanyi da taushi na shirin zautar dashi, Seya lalubo nutsuwarsa yace

"Ohk na nawa ne duka nan, Inaso ? Bata san sanda ta juyo da sauri ba tace

"Duka zaka cinye ? Ta fad'a tana kallansa, Irfan ya lumshe ido gami da sauke ajiyar zuciya kafin yace yana dariya

"Toh menene a ciki indae kece kika bani" Ita dae bata sake cewa komae ba, seta fara 'ko'karin bud'e bucket d'in gabanta, can ta d'ago tace

"Dubu hud'u da d'ari biyar da hamsin" Irfan yayi wani murmushi yace

"Toh ga dubu goma" ya fad'a yana d'akko kud'i daga cikin aljihunsa kafin ya mi'ka mata, se tayi saurin girgiza kae har sau 2 tace a sanyaye

"A'ah nikam banso.."

"Ae bake na bawa ba, Na bada ne saboda dad'in abincin dan dagani zeyi dad'i" Ganin hankalin wasu mutanen ya fara dawowa kansu ya sanyata saka hannu ta kar6a tana fad'in

"Angode..a'ina za'a juye maka ? Irfan ya girgiza kae

"A'ah sadaka za'ayi min, Allah ya bani ladan" Murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar Azrah, haka kawae taji ya birgeta, dan da alama ba halinsu 1 da wanda suka fito mota tare ba, kuma da alama shi ba d'an shaye_shaye bane, gashi kuma ya cire kud'i masu yawa duk danya samu lada, Se tace a hankali

"Allah ya bada lada"

"Ameen en mata.." Ya fad'a yana mi'kewa kafin ya cigaba da fad'in

"Sunana Irfan..idan kina bu'katar wani abu ki nemeni ina ciki uhmm ? Seta jinjina kae kawae ba tare data kalleshi ba, shi kuma seso yake hakan ta kasance danya 'kara kallan wannan idanunnata masu maeqo, daga haka Irfan ya wuce ciki yana sakin wani murmushi gami da shafa kumatunsa, ita kuma Azrah ta baewa wani dake kusa da ita ya taemaka mata yayi sadakar sannan ya bata buckets d'inta ta wuce gida..... Da sallama ta shiga gidan, Inno na tsakar gida tana cin gyad'a marau akan wata tsohuwar tabarma, seta tsaya tana kallan Azrah cike da mamaki wadda ta 'karasa shigowa ta ajje bokitan sannan ta 'karaso ta tsuguna a gaban Inno, ita kam Inno kallan bokitan kawae take ganin babu komae a ciki, gashi dududu yanzu azahar tayi, fata take a ranta Allah yasa ba abinda take tunani bane, dan kuwa idan haka ne yau jikin wata zeyi tsami

"Inno gashi" Azrah ta katsewa Inno tunanin da take ta hanyar fad'in hakan, Inno ta kalli kud'in da Azrah d'in ke nuna mata, kamar ba zata kar6a ba se kuma ta kar6a tana 'kirga kud'in, seta dawo da kallanta wajen Azrah tace

"Ke me nake gani ? Azrah tace

"Ehh..wani ne ya 'kara kud'in akae wae saboda abincin yayi dad'i" Wani irin dad'i ne ya ziyarci Inno har bata san sanda ta mi'ke tsaye ba ta fara taka rawa kira take

"Wayyo Allahna dad'i kasheni ni habi.. Dubu biyar zuwet, lallae lokacin da nake jira yazo, ashe banyi gajen ha'kuri ba".....

Kuyi manage da wannan pls 🤧 bani da charge ne 🥺🤧



Mhiz Innocent..........✍️



https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_8


_____Ita dae Azrah batace komae ba, ta mi'ke a hankali ta shige d'akinta, ita kuwa inno ta cigaba da farin_cikinta kamar wadda aka bawa kyautar million 1, Azrah na shiga d'aki hijab kawae ta cire ta fito tayi alwala sannan ta koma d'aki tayi sallah, sannan ta fara gyara wajen da zata kwanta, dan ba 'karamin dad'in 'karewar abincin nan da wuri tayi ba, haka tayi kwanciyarta bata dad'e ba bacci ya d'auketa tunda tana da tabbaci indae la'asar tayi zata farka...

.......Washe_gari haka ta sake zuwa bakin companyn ta zauna ta fara saida abincin, tana nan zaune wajen 'karfe 1 Irfan ya fito daga cikin companyn ya 'karaso ya zauna kan wani dutse yana mata wani shu'umin kallo yace

"Tun d'azu nake ta le'kowa banganki ba, ashe kinzo" ba tare data kalleshi ba tace

"Ehh" Se yayi murmushi yace

"Toh yauma a sake 'kirgamin abincin nawa ne zan siye" Haka kurum taji jikinta yayi sanyi amma seta 'kirga ta fad'a masa adadin kud'in, ya d'akko ya bata harda 'karin wasu kud'ad'en, anan ne kuma tayi firr cewar ba zata kar6a ba, Irfan ya 6ata rae

"Kamar baki yadda dani ba koh ? Seta girgiza kae kana tace a hankali

"A'ah siyewar ma da kake Allah ya amfana"

"Ehh naji nikam dae ki kar6a" Seta sake girgiza kae ba tare da tace komae ba, ganin haka ya sanyashi bata iya kud'in abincin yana jinjina kae, "lallae sena sake tashi tsaye indae ina son shawo kan wannan cikar" ya fad'a akan la66ansa yana kallanta kafin yace a fili

"Yauma dae amin sadaka"

"Allah ya bada lada" ta fad'a a hankali

"Ameen" Irfan ya fad'a yana mi'kewa yace

"Se anjima koh, ki kula da kanki" ita bata kawo komae a ranta ba da hakan daya fad'a d'in ba, kawae dae ta d'auki hakan a wani nau'i na kulawa daga mutum me mutunci zuwa waninsa, yauma ta bawa wani abincin yayi mata sadaka sannan ta wuce gida... Tun daga ranar seda suka shafe kwana 5 kullum ta kawo abinci se Irfan ya siye, seya had'a mata da wasu kud'in, ita dae bata kar6a indae tasan ya 'kara d'in, shi kuma da yaga haka seya dena 'karawa da yawa yadda ba zataji komae ba inta kar6a... Tafiya takeyi hannunta d'auke da buckets d'inta, a hankali kamar koda yaushe cikin sanyin daya zame mata jiki ta karya kwanar layinsu wadda zata sadata da gidansu, dae_dae lokacin wata mota ta danno hancinta daga cikin wani madaedaecin gida me madaedaeciyar haraba, Alhaji wadata dake zaune a bayan mota ya kalli drivernsa yana fad'in

"Aminu...dakata.." Babu musu drivern ya dakata dan cika umarnin me gidan nasa, dae_dae lokacin da Azrah tazo ta wuce ta gaban motar, Alhaji wadata ya kalli drivern

"Maza ka bimin yarinyar nan, ka ganomin gidansu"

"Toh ranka ya dad'e" drivern ya fad'a yana ficewa daga motar kana sannu a hankali ya dinga bin bayan Azrah har ta shiga gidannasu, seya juyo ya koma ya bud'e motar ya shiga yana kallan Alhaji wadata yace

"Yalla6ae, ashema wannan yarinyar ce er gidan Malam Habu" Alhaji wadata ya kalli drivern yace

"Afff! Malam habu dae na nan layin ? Drivern yace

" Ehh ranka ya dad'e"

"Dama Malam habu nada yarinya mace ne ? Alhaji wadata ya fad'a da mamaki shimfid'e kan fuskarsa, drivern yace

"A'ah....ae kaji kaji abinda ya faru" nan drivern ya kwashe duk abinda ya faru ya fad'awa Alhaji wadata, Alhajin ya jinjina kae yana sauke numfashi, se kuma can yace

"Toh muje, idan na dawo zan samu Malam Habu akan maganar" drivern yayi murmushi jin yadda wannan 'yar 'karamar yarinyar ta tafi da me gidansa a lokaci guda... Azrah na shiga gida ta tadda inno na kwashe tuwo daga cikin tukunya, ta 'karasa ta ajje bokitan sannan ta kalli inno tace

"Na dawo" ta fad'a tana mi'ka mata kud'in hannunta, inno ta mi'ke daga zaunen da take, ta kwance ha6ar zaninta ta kalmashe kud'in sannan ta kalli Azrah dake wucewa d'akinta tace

"Ke..zo kiji" Juyowa Azrah tayi ta dawo gaban innon kanta a 'kasa, tana jiran taji yau kuma da wacce tazo..

"Ya sunan wannan wanda yake siye abincin" bata san sanda ta d'ago ta kalli inno ba, inno ta watsa mata harara

"Dallah ni bar kallona da wad'annan idanun naki, kallona nace kiyi ? Tambayarki fa nake" Se a lokacin Azrah ta shiga lalube a 'kwa'kwalwarta, dan ita harga Allah ta manta da wani sunan mutumin, se can kuma ta tuna sannan a hankali tace

"Irfan"

"Ahhh...toh..toh...masha Allah, ki fad'a masa indae ya samu lokaci yazo inason ganinsa" cikin wani irin mamaki Azrah ta sake d'ago idanunta ta kalli Inno a karo na barkatae, sedae bakinta ya gaza furta komae, dan bata masan me zatace ba, inno ta katse mata tunani da fad'in

"Kinji koh ?

"Ehh" Azrah ta fad'a a sanyaye ba dan tana da ra'ayin cika abinda innon ta fad'a ba, ta wuce d'akinta ta zube zuciyarta fall tunane_tunane iri_iri....


.........A hankali ya d'ago idanunsa dake lumshe ya kalli Mami dake masa magana, bece komae ba, Mamin ta cigaba da fad'in

"Ya kamata ka tashi ka tafi haka nan, kar dad ya fito ya sameka" jinjina kae kawae yayi, dae_dae lokacin da simrah ta shigo d'akin, sanye da wata matsatstsiyar straight gown wadda ta fidda shape d'inta sosae dan kuwa komae nata ya fito dan babu laefi tana da diri, d'an 'karamin mayafin da dashi gwara babu ta rataya shi a gefen kafad'arta, fuskarta d'auke da wani glass ta 'karaso cikin parlourn fuskarta d'auke da murmushi ta 'karasa ta zauna kan kujera tana cire glass d'in dake fuskarta hankalinta gabad'aya akan Don dako kallanta beyi ba, yadda ma ya nuna kamar besan da shigowar wani cikin d'akin ba, Cikin iyayi da kuma wani salo ta karya muryarta tana kallansa tace

"Barka da safiya yah adnan.." Ta 'karasa fad'a tana lumshe idanu, Kamar baze amsa ba se kuma yace a hankali ba tare daya kalleta ba

"Kina làfiya" wani irin dad'i ne ya ziyarceta ta yadda har seda ta lumshe ido kafin tace

"Ina lafiya..alhamdulillah..naji dad'i yau kam na sameka.." Kafin ta 'karasa fad'in abinda tayi niyya ya mik'e yana kallan Mami wadda itama shi take kalla yace

"Bye..Mami"

"Ohk..take care son" jinjina kae kawae yayi, daga haka ya fice daga d'akin ba tare da ya kalli inda simrah take ba, simrah ta bishi da kallo kamar zatayi kuka sannan ta mi'ke ta dawo kujerar da Mami ke zaune ta zauna tana kamo hannun Mami

"Mami don Allah alfarma zaki min" Mami ta sauke numfashi tace

"Ina jinki"

"Don Allah Mami ki saka baki akan maganata da yah adnan, wallahi dan ba kiyi magana akae bane, nasan da tuni an wuce wajen" simrah ta fad'a kamar zatayi kuka, Mami kallan simrah kawae take, secan tace

"Kinsan dae ba sonki yake ba koh ?

"Ehh Mami babu komae, nidae ayi auren kawae zan sauyashi don Allah" Mami ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Shikenan, in sha Allah I will try my best, amma karki bani kunya" da sauri simrah ta jinjina kae kamar 'kadangaruwa wani 'kayataccen murmushi yana wanzuwa akan fuskarta.....



.........Cikin wani irin tashin hankali gami da firgitar da tayi ta d'ago ta kalli motar da saboda mahaukacin driving d'in da wanda ke ciki yake yayi sanadiyyar zubar da bokitanta dake ajje a wajen wanda kasancewar a bud'e suke yasa lokaci guda abinda ke ciki kowanne yayi nasa wajen, babu 'bata lokaci taji wata 'kwalla ta tarar mata a idanu tana kallan yadda alalar da kuma shinkafa da waken kowanne yayi nasa waje, sannan 1 daga cikin bokitin ya fashe, seta fara 'ko'karin tattaresu cikin matu'kar tashin hankali, hawayen da bata san da zuwarsu ba suka fara zuba daga narkakkun idanunta, duk hankalin mutanen dake wajen seya dawo kanta kowa na tausaya mata, wasu kuma suna ganin kamar ita ta janyowa kanta, saboda duk sunga yadda me motar ya danno motar da gudun gaske, dan haka kowa ya janye kayansa gudun kar a masa 6ari, ita kuma ko bata lura bane ko kuma ta lura kawae tana sane ne, shine basu sani ba,

"Allah sarki, kiyi ha'kuri kinji" maganganun mutane suka fara sauka a cikin kunnenta wanda dasun san yadda suke 'kara mata ba'kin ciki da fad'uwar gaba dasun daena...Se kawae ta mi'ke kamar wadda aka tsikara ta fara tafiya zuwa cikin companyn har lokacin hawaye kwance kan kyakykyawar 'kwayar idanunta....Cikin sakannin da basu wuce 15 ba wani mutum daya sheqo da gudu sanye da ba'ka'ken kaya ya qaraso ya bud'e murfin motar yana fad'in "Barka da isowa DON" shi dae don ko kallan mutumin beyi ba, se sako 'kafafunsa da yayi wanda suke cikin wani had'ad'd'en takalmi sau ciki kamar koda yaushe samfurin slip_on,Sanye yake cikin wata bomber jacket da black jeans en ubansu wanda kana gani bama se an fad'a ba kasan an kashe ma'kudan kud'i wajen sayensu, kwantacciyar sumar kansa data sha gyara se sheqi take wadda akayi wa aski me kyau, saman kansa sumar na nan da yawa yayinda gefe da gefen kansa kuma an aske kad'an daga ciki, bud'e murfin motar da yayi ne ya sanyani jiyo warin wani abu me kamada taba,sedae kafin qarasa tunanin DON ya fito daga cikin motar hannunsa d'auke da cigarette da yake kaewa bakinsa lokaci zuwa lokaci, sannan ya jefar da ita a 'kasa ya murjeta, Azrah ta kalli mutumin daya fito daga motar, seta lumshe idanu wasu hawayen na zubo mata, dan kuwa ta gane fuskar kuma gashi yauma shaye_shayen dae yake.. Seta 'karasa cike da karsashi wanda bata san sanda ta aroshi ba ta matsa kusa dashi dukda bodyguards d'in dake gurin, duk se hankalin mutane ya dawo kanta ganin tana 'ko'karin wuce gona da iri.. Reverse d'in da Don yayi ne ya sanyata itama ta dakata, dae_dae lokacin da 1 daga cikin bodyguard d'in ke watsa mata wani mugun kallo, kota kansa bata biba dan bama tasan yanayi ba ita dae burinta kawae ta had'u da Don, Don ya juyo yana kallan bodyguards d'in yace

"Ku dakata daga nan" yana 'ko'karin juyawa ya jiyo muryarta cikin sanyi tana fad'in

"Ka 'bararmin da kayan siyarwata fa.." Cakk ya tsaya sannan a hankali ya d'ago ya sauke lumsassun idanunsa akan Azrah, wadda itama shi take kallo, hakan yasa idanun nasa a cikin idanunta suka sauka, bata san sanda ta d'auke kae da saurin gaske ba, dan wad'annan 'yan iskan idanun nasa ba zata iya jure kallansu ba dan kana ganinsu kaga idanun d'an iska, (amma fah inji ta..ahh toh) Kallanta kawae yayi ya juya ba tare da yace komae ba fuskarnan kamar ko yaushe ba annuri, Wani daga cikin bodyguard yabi bayansa, ganin suna shirin wuce ta ba tare da sun lura ko sunyi wani abin game da 6arnar da sukayi mata bane ya sanyata yin gaba zuciyarta na tafasa ga wani irin bugawa da take ta fara takawa zuwa wajen da Don d'in yayi,tana shirin binsu inda suka nufa taji an janyo hijabinta wanda hakan yayi sanadiyyar sata tayi taga taga zata fad' se kuma ta tsaya akan 'kafafunta,wanda ya janyota yayi mata wani banzan kallo yana fad'in "Ke wace irin 'kidahuma ce ? Don kike 'ko'karin bi saboda man kanki ya tsotse ?????? Kallansa kawae take yadda yake magana kamar wani mutumin arzi'ki aka yiwa wani abu, waye shi wannan d'in da besan darajar d'an adam ba, yanzu duk wannan 6arnar da yayi mata kenan sedae tayi shiru dan kawae ya kasance yana da kud'i ??... Don ya kalli bodyguard d'in daya biyoshi cikin tsare gida

"What brought her here ? Dan shi bema fahimci abinda ta fad'a ba, mutumin yace

"Sir..d'azu da kake driving aka samu akasi..kayan siyarwarta suka 6are.." Don ya sake 6ata rae

"Kasan babu mace a companyn nan, meyasa baku taka mata birki ba ?

"Sorry sir..za'a kiyaye In Sha Allah"

"Better" Don ya fad'a yana wucewa ba tare da ya sake bi takan maganar Azrah d'in ba, Bodyguard d'in ya 'karaso ya kalleta tana tsaye idanunta cike da 'kwalla, seya saka hannu a aljihu ya d'akko kud'in dabe 'kirga ba ya mi'ka mata yana fad'in

"Muje.." Seta sauke wata 'katuwar ajiyar zuciya tana kar6ar kud'in sannan tayi gaba, mutumin ya kalli masu gadi

"Kada ku sake barinta ta shigo nan" 1 daga cikin masu gadin yace

"Yalla6ae na d'auka me gida ne yace taje saboda 6arin da aka mata..amma ayi ha'kuri".. Azrah ta 'karasa ta d'auki buckets d'inta tana kallan yadda 1 daga ciki ya fashe, seta sake jin wata 'kwalla ta zubar mata, A hankali take takawa kamar wadda bata da laaka a jikinta, ita kad'ae tasan yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso 'kirjinta, kyawawan narkakkun idanunta sun ciko da 'kwalla dan batasan yadda zasu 'karke da innar ilyasu ba, dan akan fashewar bokiti kawae tasan se anji kansu, tana 'ko'karin karya kwana ta jiyo wata murya kamar ta baban ilyasu, bata san sanda ta dakata ba dukda tashin hankalin da take ciki, dukda hakan ba d'abi'arta bace amma se taji yau kam tanaso taji abinda yake fad'a d'in "Amma dae Alhaji kasan itace take samar mana abinda zamuci, ma'ana dae da ita muka dogara, tunda nidae sana'ar ta'ki kwata_kwata, toh idan na d'auketa na baka aurenta...dawa ta 6are kenan ? Alhaji wadata yayi murmushi yana fad'in "Kada ka damu indae wannan ce matsalarka, zan dinga baka 30k a duk 'karshen wata, nidae fatana kawae ka auramin ita" Baban ilyasu ya wanshare baki kafin yace "Ahh toh toh hakane abin, toh kasan abinda za'ayi yanzu ? Kawae ka fad'i yaushe kake so a d'aura auren ? Ni ban'ki ko gobe a d'aura ba indae da gaske zaka cika abinda ka fad'a d'in" ya fad'a yana sakin wani shu'umin murmushi. Ji tayi wani jiri na shirin zubar da ita, 'kafafunta suka fara rawa, alamar suna gab da gaza d'aukarta, bata san sanda ta zube a wajen ba cikin rashin sanin abinyi, A hankali ta runtse brown eyes d'inta wasu zafafan hawaye na sirnano mata a kuncinta "Meyasa ita ? Meyasa 'kaddararta ta kasance haka ? Meyasa 'kaddararta take zuwa a hagunce ? Meyasa tun farko ma tazo duniyar ne ? Meyasa a koda yaushe KUDI ya ke kasancewa SANADIN QADDARARTA ? Meyasa tunda aka haefeta kowa baya sonta ? Abin takaecin ma shine cikin marasa 'kaunarta ta harda mahaefiyar data tsuguna ta haefeta ? Shin wannan wace irin rayuwa ce ? Wata irin tsana ce ta sake had'uwa a lokaci guda a cikin ranta, ta tsani matar nan, ta tsaneta, tsana mafi muni...Cikin siririyar muryarta ta furta "Babu muguwa kamarki, kece silar komae, Tirr da kasancewarki mahaefiya a gareni !!!.............


Mhiz Innocent.......✍️


https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page_9


_____Ta shafe fiye da mintuna 20 a wajen ba tare data sake sanin abinda Alhaji wadata ke tattaunawa da baban ilyasu ba, sannan ahankali ta mi'ke ta fara tafiya cike da sassarfa, wani jiri na janta hakan yasa tafiyarta ta ta zama kamarta wata 'yar maye, tafiya kawae takeyi ko kallan gabanta batayi dan kuwa zuciyarta ta gama 'ke'kashewa harta dena kuka me sauti se hawayen daketa tsere a kuncinta, ko sallama batayi ba ta fad'a cikin gidan wanda hakan ba sararta bace, amma yanzu kam hankalinta ma baya jikinta, inno da fitowarta kenan daga band'aki ta kalli Azrah wadda kyawawan fararen idanunta sukayi jaa sosae kamar an watsa musu garwashi, Azrah ta ajiye buckets d'in hannunta da kud'in dake hannunta duka akan bokitin sannan ta wuce cikin d'akinta ba tare data nemi kowa ba ko tace wani abu, 'kirjin inno ya buga da 'karfin gaske ta ajje butar hannunta fad'i take

"Na shiga uku ni habee" daga haka ta 'karasa d'akin Azrah d'in, a kwance ta hangota ta cure waje 1 cikin hijabi kamar me jin sanyi, ta 'karasa kamar wadda aka jefota ta janye hijab d'in tana fad'in

"Ke tashi ki fad'amin wani abin kika aekata ? Nidae Allah yasa ba wani abin kunyar kike nema ki jawomin ba..kamar yadda uwarki tayi" ta fad'a cike da alhini tana kallan Azrah dako kallanta batayi ba, A hankali wasu zafafan hawaye masu d'umi suka sake zubowa Azrah akan kuncinta, seta sake curewa waje 1 tana sake jan hijab d'in nata ba tare da tace komae ba, inno ta kaewa hijab d'in cafka tana lalubarta tace

"Don uwarki bari na bincika..duk yadda akayi wani abin kikayi bakiso na sani" inno ta fad'a tana yaye hijab d'in gaba d'aya sannan ta fara duba ta kira take

"Tashi ki sake tafiya na gani.." Wani sabon kukan ne ya tahowa Azrah, bata san sanda ta sakeshi ba, tanayi tana 'karawa kamar zuciyarta zata fito

"Habee matar Habu...fito kiji abin arzi'kin dake shirin faruwa damu" daga tsakar gida ta jiyo muryar baban ilyasu yana fad'in hakan, dae_dae lokacin da take 'ko'karin d'aga Azrah daga zaunen da take, seta saketa ta mi'ke tana fad'in

"Bari naje..zan dawo kanki wallahi sekin min bayani" daga haka ta fice, dur'kushewa Azrah tayi a wajen wasu sabbin hawaye na zubo mata, gaba 1 tunaninta ya d'auke, hankalinta a matu'kar tashe yake, shikenan dan mahaefiyarta ta aekata abu se kowa ke tunanin itama zata aekata ? Wannan wace irin rayuwa ce ?.... Inno ta fita daga d'akin ta 'karasa tana fad'in

"Malam meya faru ? Baban ilyasu ya 'karaso cikin gidan har lokacin fuskarsa d'auke da murmushi yace

"Ke dae..mu zauna tukun na" babu musu inno ta nemi waje ta zauna dan daga ganin yanayin baban ilyasun tasan lallae wani abun farin ciki ne ya samesu, baban ilyasu ya saka hannu a aljihu bayan shima ya zauna kan tabarmar ya fito da wasu kud'i ya ajjesu akan tabarmar, inno ta saki baki tana kallo gami da bu'katar 'karin bayani, sedae ta kasa shiru dan haka bata san sanda ta furta

"Malam..wad'annan kud'in fa.."

"Kayya..dad'ina dake gajen ha'kuri, yanzu zan fad'a miki ae" seta sake gyara zama tana kallan kud'in sannan ta maeda dubanta kan baban ilyasu

"Ina alhaji wadata nanan 'karshen layinmu wanda ya dawo nigeria wancan satin ? Baban ilyasu ya fad'a yana kallan inno

"Ehh 'kwarae na ganeshi, wani abune ya faru ? Baban ilyasu ya sake gyara zama

"Yazo da batun neman auren Azrah"

"Kae malam.." Inno ta fad'a tana dafe 'kirji

"Ae ba wannan ne abin duban ba, kinga wannan kud'in ? Ya fad'a yana d'aukar kud'in daya ajjiyesu sannan ya cigaba da fad'in

"..dubu 30 ne, toh duk wani watan duniya da kika sani ze dinga bamu kamarsu" wata 'katuwar gud'a habee ta saki, tanayi tana 'karawa fad'i take

"Lallae komae lokaci ne malam.. Allah mun gode maka, Allah ya kaemu lokacin nan malam akwae shagali" ta 'karasa fad'a tana sakin gud'a, baban ilyasu ya bud'e murya yana kiran

"Azrah..Azrah..fito nan" tana kwance lokacin ta gama kukan da take se sheshshe'ka ta jiyo muryar baban ilyasun, a hankali ta mi'ke kamar wata mara laka tana jin yadda kanta ke juya mata a haka ta 'karasa tsakar gidan ta tsuguna ba tare da tace komae ba, baban ilyasu yace

"Toh ki bud'e kunnenki da kyau.. Kina jina ko ? Be jira amsar da zata fad'a ba ya cigaba da fad'in

"Alhaji wadata ya ganki yana so, ni kuma a matsayina na mari'kinki naga ya dace kuma na yadda da halayensa dan haka na amince masa ya fara zuwa wajenki, saboda haka kowane lokaci zaki iya jin an aeko sallama dake daga wajen Alhaji wadata, idan hakan ta kasance ki fita dan kuwa baki da wani miji seshi, dan tunda muka riga muka gama magana dashi shikenan zance ya 'kare, ba wani uzuri dazan kar6a haka kurum ki maedani 'karamin mutum" daga haka yayi shiru, ita dae Azrah jinsa kawae take badan tana fahimtarsa ba, abinda kawae take tunawa shine siyar da ita zasuyi, Seta jiyo muryar inno tana fad'in

"Wae wane iskanci ne yau kike ji dashi ne.. Se magana ake miki kin yiwa mutane shiru ? Se a lokacin ta d'ago ji'ka'k'kun idanunta ta kalli inno sannan a hankali

Please Login or Register in order to submit comment