Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan nata, badae tace komae ba ta wuce band'akin tana kallansa cike da mamaki yadda za'ace wae wannan band'aki ne, kasa 'karasa shiga ciki tayi ta tsaya kawae cike da tsoro da kuma ganin Ikon Allah, Ammi dake lura da ita ta 'karaso 'kofar ban d'akin tace

"Ko kina bu'katar wani abu ne?" Da sauri Azrah ta juyo tana kallan Ammin, se tayi 'kasa dakae tana kallan wani wajen, Ammi ta nuna mata bathtub tace

"Kiyi wankan" bin inda ta nuna mata tayi da kallo har lokacin ba tace komae ba seta hau girgiza kae kamar 'kadangaruwa dan harga Allah tsoro take ji ba zata iya shiga ba, ganin haka ya sanya Ammi yin murmushi kana ta shiga band'akin ta d'akko mata kayan wankan ta ajje mata sannan tace lokacin da take fita

"Gashi nan se kiyi uhmm?" Azrah ta jinjina kae sannan ta tura 'kofar band'akin tana sakin ajiyar zuciya.. wajen mintuna 10 ta d'auka a wankan bayan ta gama ta d'aura towel d'in sannan ta maeda hijab d'in tayi shiru tana tunanin yadda zata fad'awa matar ta gama, tana nan tsaye harta gaji dan kanta ta d'an ta6a 'kofar, Ammi dake zaune kan gado ta mi'ke ta 'karasa toilet d'in tace a hankali

"Kinyi wankan?" Jin shiru ya sanya ta d'an buga 'kofar kad'an, se a lokacin Azrah ta kae hannunta ta bud'e 'kofar, Ammi ta shiga sannan ta janyo sabulan wanke kae tana kallan Azrah tace

"Matso na wanke miki!" A hankali Azrah ta 'karasa kusa da Ammin cike da kunyar yadda zata cire hijab d'in a gaban ta bayan ga yadda towel d'in yake, seda Ammin ta sake mata magana sannan ta cire hijab d'in bayan ta tsuguna, Ammi takae hannunta ta zare d'an zaren da Azrahn ta d'aure gashin nata, aekuwa hakan ya bawa tulin gashin nata damar bazuwa a kanta har gadon bayan ta, Ammi ta furta

"Masha Allah" tana murmushi, sannan ta fara wanke mata kan nata, dukda babu wani datti akan kawae dae rashin samun sabulu me kyau ne ya sanya ba'a ganin kyansa sosae sedae yawansa kawae, seda ta tabbatar ta wanke mata shi tass yana ta tashin 'kamshi sannan suka fito daga band'akin, ita dae Azrah har lokacin ta kasa sakin jiki, suna fitowa Ammi ta janyo wasu had'ad'd'un mayuka cikin drawer ta shafe yalwataccen gashin Azrahn dake ta had'e jikinta waje guda saboda sanyin dake ratsata, sannan ta taje mata shi sosae ta d'aure shi a tsakiyar kan nata, yayi kyau sosae kamar gashin en India, suna gamawa ta d'akko mata wasu kaya abayas ne da yawa wad'anda zasuyi mata dae_dae, ta d'auka ta saka, ita dae Azrah binta kawae take duk abinda tace tayi, seta fito tayi wani irin shahararren kyau me d'aukar hankali, Ammi tace

"Masha Allah kinyi kyau sosae! Meye sunan ki?" Se tayi d'an murmushi kad'an sannan tace a hankali

"Azrah"

"Wow! Suna me dad'i..ya dace da meshi" Ammi ta fad'a har lokacin da murmushi kan fuskarta, sosae take kallan ta dan ta burgeta sosae yadda taga nutsuwarta kamar tafi shekarunta yawa, komae tana yinsa ne cikin sanyi babu hayaniya babu garaje, itama Azrahn murmushi tayi sannan tace

"Nagode" daga haka Ammin ta fita daga d'akin, bayan ta kawowa Azrah abinci seta sake fita... A parlourn ta sami Mami har lokacin sedae sa6anin d'azu da take tare da Fawaz yanzu ita kad'ae ce, ta 'karasa ta zauna tana kallan Mami wadda ke fad'in

"Taci abincin?" Ammi ta 'karasa ta zauna tace

"Ehh yanzu na kae mata"

"Toh madallah..sannu da 'ko'kari"

"Yawwah" Ammi ta fad'a tana murmushi, Mami ta gyara zama sannan tace

"Yanzu ta ina zamu fara?" Ammi ta ajje numfashi kafin tace

"Inaga a fara nema mata gurbi ko a makarantarsu Zarah ne both bokon da islamiyyar" Mami ta d'anyi shiru se can tace

"A'ah ki bar bokon nan, just islamiyyar ta isa" Ammi tayi shiru tana kallan ta bayan ta d'anyi jim sannan tace

"Toh hakan ma yayi.. Allah ya saka da alkhaeri"

"Ameen_Ameen, yanzu zan baki kud'i In Sha Allah se kiyi duk abinda ya dace na shiga makarantar, daso samu ne ma ko zuwa gobe ne ta fara zuwa" Ammi tace tana jinjina kae

"In Sha Allah zanje akan maganarta ta" daga haka suka cigaba da tattaunawa sannan Ammi ta mi'ke ta koma d'akin Azrah, sanda ta shiga seta same ta tana sallah, Ammi ta tsaya tana kallan yadda take sallahr, ta jinjina kae ganin yadda take yi cike da kura_kurae a ciki, dan haka seta juya bayan ta janyo mata 'kofar ta fita daga d'akin.... Kae tsaye gida ta nufa tana shiga d'akin dae_dae sanda Ummu ta fito daga d'akin ta kalleta tace

"A'ah Ammin yara yau kuma da wuri haka?" Ammi tayi murmushi

"Wallahi kuwa makarantarsu Zarah zanje, zan samu ya sayyadi yanzu?" Ummu ta 'karaso ta zauna sannan tace

"Toh meya faru kuma?" Ammi tace

"Lafiya 'kalau, za'a yankowa ba'kuwar gidansu Fawaz form ne" Ummu ta kalli agogo sannan tace

"Amma bakya ganin yanzu ba lallae ki sameshi ba? Dan nasan suma suna kan hanya yanzu haka" Ammi tace

"Bari na jarraba" ta fad'a tana mi'kewa, Ummu ta bita da kallo sannan tace

"Toh Allah yasa a dace"

"Ameen" Ammi ta fad'a tana ficewa..... Kae tsaye Islamiyyar da 'ya'yan gidan kuma wadda Fawaz ke zuwa ta nufa aekuwa tayi sa'a ta samu ya sayyadin, a lokacin ta gama komae na shigar Azrahn makarantar, bayan ta gama abinda zatayi suka taho tare dasu Fawaz d'in suka dawo gida.......

........Tana zaune a d'akin tayi shiru kamar munafuka ta takure a waje d'aya dan kuwa ba 'karamin yawa sanyin A.C d'in ya mata ba, gashi kuma bata san yadda zatayi ta kashe ba ta huta da yadda yake ratsa mata 'kasusuwa ba, tunani ne fall a cikin kwanyarta wanda tasan babu me amsa mata su, ita dae ance aure akayi mata, amma bata ga alamar nan d'in yayi kama da gidan aurenta ba, ta ina ma hakan zata ta6a kasancewa? Tafi yadda da wani 6angaren na zuciyarta dake sa'ka mata 'kilan dae aeki aka kawo ta, Mami tayi sallama cikin d'akin, d'aga kae tayi tana kallan ta bayan ta amsa sallamar, Mami ta 'karaso tana kallan yadda ta takure a waje d'aya hannayenta ri'ke da 'kafafuwanta, ita Mami bata d'auka ko sanyin ne ya mata yawa ba dan bata ji wani sanyi na azo a gani ba se saffa saffa, dan haka ta 'karasa cikin d'akin har lokacin tana kallan ta ganin yadda ta fito tayi kyau abinta kamar ba ita ba, seta maeda dubanta kan gashinta wanda mayafin data yafa ya d'an zame kad'an wanda hakan ya bawa kwantaccen gashin nata damar fitowa, Mami tace

"Kina bu'katar wani abu ne?" Girgiza kae tayi tana yin 'kasa da kanta, Mami ta sake cewa

"Kinci abincin?" Azrah tabi abincin dake ajje a 'kasa da kallo sannan tace a hankali

"Na 'koshi"

"Kin 'koshi kuma?" Seta jinjina kae tana kallan Mamin, Mami ta mi'ke tana fad'in

"Ohk...tashi muje ki gaeshe da uwar masu gidan!" Babu musu ta mi'ke ta sakko daga kan gadon dukda bata fahimci wadda Mamin ke magana akae ba, Mami tayi gaba sannan ta rufa mata baya....Suna tafiya Azrah nabin inda suke giftawa da kallon mamaki har suka isa wani part d'in shima kamar irin wancan, Mami na gaba tayi sallama cikin d'akin, buhaisa dake zaune tana yankawa Yakumbo tufa ta amsa sallamar, sannan Yakumbon ma dake lazumi ta 'karasa sannan ta amsa sallamar, Mami ta 'karasa ta zauna kan kujera sannan Azrah ta nemi 'kasan kujera ta zauna kamar zata shige cikin kujerar, buhaisa ta bita da kallo sannan ta dawo da kallan ta wajen Mami tace

"Barka da dare Mami"

"Barka dae buhaisa" Mami ta fad'a tana maeda dubanta kan Yakumbo suka gaesa, buhaisa ta kalli Azrah tana murmushi tace

"Heyy" Azrah ta d'ago idanunta ta kalli Buhaisa sannan tace a hankali kamar wadda bata so tayi magana

"Hy" Buhaisa ta ajje wuqar hannunta ta mi'ke ta dawo kusa da Azrah tace

"Am Buhaisa u?" Azrah tayi 'kasa da kanta sannan tace

"Azrah" Buhaisa tace

"Woww nyc name" ta fad'a tana kallan yadda Azrahn keda kyau kamar ita tayi kanta, Yakumbo ta kalli buhaisa tace

"Ki tashi ki samo musu ruwa koh?" Buhaisa ta mi'ke tana tura baki ta wuce kitchen, se a lokacin Azrah ta juyo tana kallan Yakumbo sannan tace bayan tayi 'kasa da kanta

"Ina wuni?" Yakumbo tace

"Lafiya lau en nan, ya mutan gidan?" Azrah tace

"Alhamdulillah"

"Toh madallah" Yakumbo ta fad'a tana maeda dubanta kan Mami dake fad'in

"Toh Yakumbo kishiyar taki ce fah?" Yakumbo tayi murmushi tana fad'in

"Kae masha Allah madallah da wannan kyakykyawar halitta, lallae wannan yaro dole yace se ke, na yadda Adnan ya iya za6e tunda gashi ya za6o wadda ta fini kyau"

"Adnan!!" Ta maemaeta zuciyarta na bugawa, "waye shi? Wanene shi?" Tambayar dake ta sintiri a 'kwa'kwalwarta kenan, seta tsinkayo muryar Mami na fad'in

"Ae dama Son ba daga nan ba Yakumbo" dae_dae lokacin Buhaisa ta fito daga kitchen d'in bayan ta tsinci maganganun dasu Mamin keyi, seta 'karaso cikin d'akin jikinta a sanyaye haka fuskarta babu walwala kamar d'azun, ta ajje ruwan sannan ta mi'ke ta wuce d'aki ba tare da ta sake bi takan kowa ba, ita kuwa Azrah bata masan tana yi ba dan har lokacin kanta na 'kasa ne, Yakumbo ta d'an ja Azrah da hira kad'an inda ta fahimci yadda take shiru_shiru kamar a fuska haka take a zahiri, se taji yarinyar ta burgeta sosae, har suka bar d'akin Buhaisa bata sake fitowa ba ita kam Azrah tama manta da ita........

..........Washe_gari wajen 'karfe 2:00 ta fito daga wankan da Ammi ta sakata tayi, ita kam harta gaji da shiga ruwan nan a koda yaushe kamar wata kwad'uwa, tana fitowa ta shirya cikin doguwar rigar data gani kan gado, dae_dae nan Ammi ta shigo d'akin hannunta d'auke da wata leda, ta 'karaso tana kallan Azrah tace

"Yawwah maza ki shirya, jiranki suke" ta fad'a tana fito da wani dogon coffeen hijab daga cikin ledar ta mi'ka mata, Azrah ta kar6a ta sanya sannan ta kalli Ammi dake mi'ka mata wasu turaruka tace

"Gasu nan zan ajiye miki idan zakiyi amfani dasu se kiyi" jinjina kae Azrah tayi sannan tabi bayan Ammi data fita daga d'akin....Kae tsaye compound d'in gidan suka nufa, seda sukayi tafiya me d'an tsayi kafin suka isa inda wata blue black d'in GLK take, ganinsu da Zarah tayi ya sanya ta bud'e backseat d'in da take zaune a ciki ita da Abun nasi, Ammi ta 'karaso tana kallansu tace

"Gashi nan ku kula da ita, kun san dae ba'kuwa ce" Zarah tayi murmushi sannan tace

"Babu damuwa Amminmu" Ita dae Azrah binsu kawae take da kallo ba tare da tasan su waye su ba kuma tana mamakin yadda koda yaushe take ta ganin ba'kin fuska, Ammi ta kalleta tace

"Sekun dawo koh?" Jinjina kae Azrah tayi sannan ta shiga motar ta zauna, Ammi ta rufe 'kofar kafin ta d'aga musu hannu tana murmushi, Driver yaja motar suka fice daga gidan, seda suka fara tafiya sannan Zarah ta kalli Azrah tana murmushi tace

"Azrah koh?"

"Ehh" Azrah ta fad'a a ta'kaece, Zarah ta jinjina kae, Fawaz ya juya daga gidan gaba da yake zaune yana kallan Azrah yace

"Ba'kuwa yau zaki ga makarantarmu, am sure zata birgeki" se tayi murmushi a ta'kaece ba tare da tace komae ba dan haka kawae take jinta duk a takure, Fawaz ya dinga 'ko'karin janta da hira, ita dae sedae tace "uhmm, ehh, a'ah, ko tayi murmushi" Abunnasi dake kusa da Zarah dama tun d'azu shine bece komae ba yace

"Wato Fawaz shira kake so koh? Allah yasa baka iya hadda ba ya sayyadi ya sakaka a ofis ya had'a maka jikinka" Ya 'karasa fad'a sanda dukkansu suke fashewa da dariya, shi kansa drivern seda yayi dariya dan dama ya saba da wuya suje su dawo daga islamiyyar basu saka shi dariya ba, haka kuma babu ranar da zata wuce akan hanya basuyi zancen ya sayyadi ba, Fawaz ya juya yana kallan Abunnas yace

"Haba dae, ae sedae ya had'a maka jikinka" Drivern ya katsesu da fad'in

"Wannan ya sayyadi...wannan ya sayyadi kuna 'kaunarsa ku kam" Dukkansu dariya sukayi kafin Zarah tace

"Wallahi kasan meye ne, bafa izgili bane ko wani abu, shi fa babu ranar da zata wuce be fad'i maganar nan ba, ae ya sayyadin mu d'an chapter ne" Fawaz yace

"Wallahi kuwa" A haka har suka 'karasa makarantar, ita dae Azrah tana jinsu haka kurum taji sun burgeta yadda suke rayuwarsu cikin farin ciki da nishad'i wanda ita sam bata sansu ba sannan ba taga alamun akwae ko 'kan'kanin damuwa a tare dasu ba....Aekuwa ilai sanda sukaje makarantar duk aji d'aya suke dan haka seda suka fara zuwa wajen ya sayyadi sannan suka koma aji, kafin ya sayyadin ya shigo suka d'an fara hira Zarah na jan Azrah da hira ko dan ta sake dasu, ya sayyadin na shigowa kuwa ya kalli Zarah fuskarsa a had'e yace

"Wato so kike ki koya wa ba'kuwa shira koh? Toh wallahi kiyi a hankali kafin na sakaki a ofis kuma in had'a miki jikinki" Azrah ta d'anyi murmushi jin da gasken sarar ya sayyadin tasu ce......... Basu suka dawo gidan ba se dab da maghrib, mazan dama kae tsaye masallaci suka wuce yayin da Zarah tayi mata sallama ta shige gidansu, ita kuma aka 'karasa da ita cikin gidan, drivern ya zagayo ya bud'e mata 'kofar ta sauka a hankali tana jin kunyar yadda babban mutum kamarsa yake bud'e mata 'kofa ita da ba kowan kowa ba, ta cigaba da takawa zuwa part d'in Mami cikin nutsuwarta... Sakkowarsa daga mota kenan kae tsaye ya wuto part d'in Mamin, yazo dab da shiga part d'in ya d'an dakata seya sanya hannu ya ciro sar'kar dake wuyansa dan sam yama manta da ita a wuyan nasa, Cikin wani irin bugun zuciya tayi wani reverse tana kallansa zuciyarta na bugawa da 'karfin gaske, cikin en sakanni jikinta ya d'auki rawa kamar wadda taga wani mugun abu tana sake kallansa "meya kawo wannan mutumin gidan nan?" Tafiyar ta cigaba dayi tana janyo addu'oi a bakinta ba tare da tasan inda 'kafarta ke takawa ba, wani mugun tuntu6e tayi bata san sanda ta saki wata 'kara ba gaba d'aya tabi ta rikice tana kallan 'kafarta ta, 'karar data saki ce ta d'auki hankalinsa, a hankali ya juya yana kallan wajen da yaji 'karar, dae_dae lokacin data d'ago tana kallan wajen da yake idanunta sunyi rau_rau har 'kwallar ta fara sintiri akan kumutunta, da wani irin mamaki Don ya kalli Azrah har besan sanda ya furta akan la66ansa ba fuskar nan kamar koda yaushe a tamke

"U again!?"............

Nima bari na d'ana SHIRA KUKE SO KOH?😹😹


Mhiz Innocent..........✍️



https://chat.whatsapp.com/CNoLsXVGhSe9XZXghGxjZV


*♡☆SANADIN KADDARATA☆♡*

( _Is similar to *DON ADNAN's* destiny_ )




⚡ *THE BEGINNING*⚡




STORY AND WRITTEN

BY

*♡ MHIZ INNOCENT ♡*


..Sanadin 'kaddarata na kudi ne akan N300, da zarar mun gama free pages zamu cigaba da tafiya ne da wadanda sukayi payment kawae, zan ajiye muku yadda zakuyi payment din a last page na The Beginning..


Free page 19-20 (Last free page)


_____Da wani irin sauri tayi 'kasa da idanunta tana sake kallan 'kafarta, duk da yaga alamar wani abun ne ya sameta hakan be hanashi jan 'karamin tsaki ya juya ba dan be masan ya furta wani abu ba, yana sake sa'kawa a ransa tabbas yarinyar nan bata da hankali, seda ta tabbatar ya shige parlourn Mami sannan ta mi'ke cike da sassarfa tana jin 'kafarta na d'an mata zugi ta shige d'akin da take zama...... Yana shiga parlourn ya tadda Mami na waya seya 'karasa ya zauna kan kujera yana fito da wayarsa dake cikin aljihu ya fara dannawa, Mami tace har lokacin da waya kare a kunnen ta

"Toh shikenan, Allah ya dawo dake lafiya Simrah" daga haka ta katse wayar ta dawo da dubanta kan Don tace

"Ka dawo?" Se a lokacin ya d'ago lumsassun idanunsa ya kalli Mami sannan yace

"Yeah..yunwa" ya fad'a yana 6ata fuska kamar 'karamin yaro, Mami tace

"Ohk maza ka tashi kaje kaci abinci ae nasan Ammin ta gama" ta fad'a tana mi'kewa tayi gaba yayinda shima ya mi'ke yabi bayanta suka wuce dinning area....... Ko da ta shiga d'akin babu kowa a ciki se abincin ta da aka ajjiyeshi kan stool, ta 'karasa ta cire hijab d'in tana sake duba 'kafarta taga yadda ta gurje "anya kuwa mutumin nan bata aljani bane? Idan kuwa hakane abubuwan sun masa yawa, ga shi aljani kuma gashi d'an giya" ta sa'ka a ranta, se kuma tace "kae ba aljani bane, amma meya kawo shi gidan mutunci irin wannan?" ta 'karyata kanta sannan tayi wannan tunanin, se kuma ta mi'ke ta shiga band'akin dan jiya da tayi wanka ba sau 1 ba taji dad'in jikinta sosae, ga kuma yadda taji cikinta na wani irin juyawa, tama d'auka ko cikin nata ne ya juya saboda wannan tsoratar da tayi sedae da taje band'akin taji ba haka bane, se tayi wanka sannan ta fito har lokacin tana ri'ke da cikin nata dake ta juya mata, gaba d'aya se taji bata sha'awar komae dan haka tana idar da sallah ta haye kan gadon taja blanket tana sake ri'ke cikin nata sosae, se kuma ta fara tunanin ko yanayin abincinsu ne daya bambamta da nasu ya sanya cikin nata ke mata haka? Sedae duk yadda ta d'auka ashe abin ya wuce haka dan ji tayi kamar zata sume, bata san sanda ta saki wani kuka ba tana sake takurewa waje 1 ba tana jin yadda hatta 'kafafunta seda suka ri'ke, haka ta dinga juyi ita kad'ae akan gadon gumi na keto mata kamar mara lafiya, ranar dae da 'kyar ta iya rintsawa saboda yadda take ji......... Washe_gari da safe Ammi ta shigo d'akin nata da sallama, da mamaki sosae take kallan yadda har lokacin Azrah d'in bacci take gashi har wajen 8 ta wuce kuma yadda ta gani jiya da alama ma tun asuba data tashi bata koma ba, seta 'karasa cikin d'akin a hankali ta d'an bugi pillown da Azrah ke kae, jin shiru ya sanya ta yaye bargon daga kanta tana kallan yadda fuskarta tayi wani fayau gashi se gumi take had'awa, Ammi tace

"Subhanallahi, yanzu duk wannan gumin da kike hadda wata lullu6a kuma? Ko zazza6i kike?" Ta fad'a tana kae hannun ta goshin Azrah, babu wani zafi jikin nata kuma har lokacin bacci take, seta kae hannu ta yaye bargon daga jikinta tana fad'in

"Ae kyaji iska...." Bata 'karasa fad'a ba ta kalli yadda rigar dake jikin Azrah ta 6aci da jini haka har jikin gadon wanda da alama ita Azrahn bama ta lura da hakan ba, Ammi tace

"Ohh god" tana mi'ka hannunta tayi tapping goshin Azrah d'in, da sauri Azrah ta fara bud'e idanunta tana mutsutstsuka idanu, seta bud'e idanun nata tarr akan Ammi dake kallanta bata iya furta komae ba dan tashin da tayi ya tuna mata da ba'kar azabar data sha jiya akan ciwon cikin nan, seta kae hannunta tana ta6a cikin nata dae_dae sanda ta tsinci muryar Ammi na fad'in

"Ki tashi ki gyara kanki kinyi bleeding" Azrah ta kalleta ba tare da fuskanci abinda take fad'a d'in ba ta fara 'ko'karin mi'kewa dan sauka daga gadon idanunta ya sauka akan gadon daya 6aci, seta kalli Ammi sannan ta sake kallan gadon zuciyarta na wani irin bugawa da sauri da sauri, Ammi tace

"Tashi kije" bata ce komae ba ta mi'ke tana jin yadda 'kafarta tafi ri'kewa akan jiyan, Ammi tace tana kallanta

"Meya faru?" Se tayi 'kasa da kae kafin tace

"Qafa ta da ciki na ke ciwo.." Ammi tace

"Allah ya sauwa'ke, maza kije ki gyara kanki" se a lokacin tayi 'karfin halin mi'kewa ta fara takawa a hankali dae_dae lokacin da idanunta suka sauka akan rigar ta data riga ta gama 6aci, da sauri ta juya ta kalli Ammi wadda itama take kalla, Ammi ta matso kusa da ita tace

"Ko baki zo da pad bane?" Seta girgiza kae kamar ba zata ce komae ba se kuma tace a rarrabe kanta a 'kasa

"Bansan yadda zan...."

"Ko baki ta6a yi bane?" Ammi ta tambaye ta tana kallanta sosae, jinjina kae Azrah tayi cike da kunya ta kasa d'ago ido ta kalli Ammin, Ammi tace

"Ohk je ki jirani a toilet d'in, bari na samo miki abinda zaki yi amfani dashi" daga haka ta yaye bargon da zanin gadon ta kaesu band'akin sannan ta fice daga d'akin, ita dae Azrah ba tace komae ba ta bita da kallo har lokacin 'kirjinta na bugawa da 'karfi ne haka zalika idanunta sun ciko da 'kwalla fall.... Mintuna wajen 5 Ammi ta d'auka sannan ta dawo d'akin hannunta d'auke da leda, tana kallan Azrah da har lokacin take tsaye kamar wadda aka sassa'ka tace

"Muje koh?" Babu musu Azrah tayi gaba ita kuma Ammi ta rufa mata baya, Ammi bata bar d'akin ba seda ta tabbatar ta koyawa Azrah duk wani abu daya kamata, ita kuwa Azrah kunya kamar zata nutse haka take ji, ba ta iya cewa komae sedae ta bita da "ehh" ko "toh" ita kuwa Ammi se Azrahn ta sake birgeta dan haka tace mata ta dena jin kunyarta ta d'auke ta kamar mahaefiyarta, shiru Azrah tayi ba tace komae ba har Ammi ta gama abinda zatayi ta fita daga d'akin, Azrah ta nemi waje a 'kasan gadon ta zauna tana jin yadda zuciyarta take a kusa, ko minti 1 ba tayi da zaman ba kuwa ta fashe da kuka kamar wadda aka yiwa wani abu, seda tayi me isarta har ta gaji dan kanta sannan tayi shiru....... Wajen 'karfe 2pm Ammi ta sake shigowa d'akin, har lokacin tana zaune ta d'ora kanta akan cinyarta kamar me tunani, Ammi ta 'karaso cikin d'akin tace tana kallanta

"Zaki iya zuwa makarantar kuwa?" Azrah ta d'aga ido tana kallan Ammi a hankali tace

"Ciki na..." Kafin ta kaega 'karasawa Ammi tace

"Yi zamanki, ae da lafiya ake yin komae, Allah ya sawwa'ke" daga haka ta fice daga d'akin taje ta sanarwa da drivern akan cewar su tafi Azrah ba lafiya, duk seda suka jinjina lamarin kuma suka ce zasu je dubata idan sun dawo daga makarantar.... Sanda suka je makarantar kafin su shiga aji ya sayyadi ya kira Zarah yana tambayarta akan rashin ganin Azrah, Zarah tace

"Wallahi ya sayyadi ba ta da lafiya ne shiyasa" ya sayyadi yace

"Subhanallahi, Allah ya 'kara afuwa, kinsan tunda ba'kuwa ce ya kamata a sanya ido sosae a kanta, ayi mata sannu don Allah" Zarah tayi wani miskilin murmushi tana fad'in

"Ehh hakane, zataji" daga haka ta juya ta koma aji tana wani murmushin yadda ta fuskanci wani abu game da ya sayyadin nasu..........



.............Fitowarsa kenan daga cikin wani d'an 'karamin joint hannunsa d'auke da handkerchief yana goge zufar dake karyo masa a goshi wayarsa tayi 'kara, ya sanya hannu ya d'auko wayar sannan ya d'aga kiran yana karawa a kunnensa, daga can 6angaren Sameer yace

"Kana ina?" Seda ya d'an lumshe idanu kad'an sannan yace

"Wani abu?" Sameer yace

"Noo inaso muyi magana ne? Kana ina?" Nan ya fad'a masa sunan wajen sannan Sameer yace

"Ohk ka jira ni semu wuce gidan tare" bece komae ba har Sameer ya katse wayar ya 'karasa ya shiga motarsa dake ajje, wajen Mintuna 5 Sameer ya 'karaso ya shiga motar wajen me zaman banza sannan Don ya fara driving, suna fara tafiya Sameer yace

"Wae Mami bata maka magana ba?" Ya d'anyi jimm sannan yace

"Akan?" Sameer yace

"Amaryarka mana!"

"Amaryata kuma? Wani abin ne haka?" Ya fad'a cike da basarwa yana cigaba da driving, Sameer ya sha'ka iya sha'ka dan haka yayi shiru kamar ya ha'kura da tambayar se kuma yace

"Plss joke apart, ka riga kasan da maganar auren nan kafin muje Cyprus, yanzu kuma mun dawo naji shiru" Don ya ta6e baki har lokacin kansa na titi yace

"Uhmmm, may be tama kanta 'kiyamal laeli ne ta fasa" Sameer yace

"Tafasa kuma?" Don ya juyo yana kallan Sameer sannan ya maeda hankalinsa kan tu'kin da yake yace

"Kamar kana da number Mami koh?" Sameer ya jefa masa wata harara sannan yace

"And so?"

"So meyasa ba zaka kirata kuyi magana ba" ya fad'a a nutse sanda yake jan burki ya gangara gefen titin yace

"Pls will u drive us?" Sameer ya d'aga kafad'a kamin yace komae Don ya bud'e 'kofa ya fita, shima fitar yayi daga motar sukayi exchanging seat, Sameer yaja motar suka fara tafiya, Don ya saka hannu a aljihunsa ya lalubo taba

Please Login or Register in order to submit comment