Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

Hausa ebooks - pdf,txt and doc
www.hausaebooks.cf Download any kind of hausa ebooks here
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 85: Kabilar Nara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
Koda Armad yaga wannan zane na Ikenga sai zuciyar ta
yamutsa, ya rasa abinda ke masa daɗi. Abin mamakin shi
ne fafatarwarsu da Ikenga a shekarar data gabata ita ce
take ta dawo masa.
Yana cikin haka yaji muryar wannan saurayi a gefensa.
"Kasan ɗan-baiwa ne?"
Nan take Armad yai sauri ya farfaɗo daga zurfin tunanin
daya shiga. "Eh... a'a! Na dai taɓa gamuwa dashi a wajen
kurkukun nan."
Koda jin wannan amsa sai saurayin ya haɗe gira cikin
mamaki, kafin daga bisani ya numfasa ya tambayi Armad.
"Ya akai kuka haɗu? Ko kaima mabiyinsa ne a wajen
wannan. kurkuku?"
Cikin sauri Armad ya amsa da cewa, "a'a, ni ban san ma
yana da mabiya ba ballantana na zama ɗaya daga cikinsu.
Shi kuwa meye manufarsa ta haɗa mabiya? Yaƙi yake
shiryawa ko kuma me?"
Wannan saurayi yai murmushi, "Eh.. lallai wannan ita ce
tambayarda kowa yake tayi a tsahon shekara ɗayannan
da ɗai-baiwa ya shigo wannan kurkuku. Sai dai kuma
babu wanda yake da amsarta sai shi kansa da kuma
manyan kwamandojinsa guda biyar dake haɗa masa
jama'a. Kamar dai yadda na gaya maka ana saka ran ɗan-
baiwa zaizo nan yau, kuma koda baizo yau ba lallai acikin
satin nan zai bayyana domin yiwa mabiyansa bayani akan
manufofinsa."
Koda jin wannan jawabi sai Armad ya yanke shawarar
lallai ya kamata yaji wannan manufofi na Ikenga. Domin
kuwa duk da Armad baisan Ikenga sosai ba amma
fafatawar da sukai tasa yana ji a ransa cewa akwai wani
sirrin Izza a tattare dashi. Sannan kuma babban abinda ya
tsayawa Armad a rai shi ne maiya kawo Ikenga wannan
kurkuku, domin kuwa a lissafi shekarar Ikenga ɗaya cir
da zuwa wannan kurkuku. Wanda hakan ke nuna cewa
Ikenga yazo kurkukun lokaci kaɗan bayan gama
fafatarwarsa dashi a gasar Jinzidal. Lallai da sake. Akwai
wani abu dake faruwa a ƙasa.
"Sailári, shin kana ganin nima zan iya shiga naji wannnan
manufa ta Ikenga?"
Wannan saurayi najin wannan tambaya ya fashe da
dariya yana cewa, "Sailári? Wato a duk sunaye na guda
biyar biyar shi ka riƙe. To ba komai, hakan ma yayi.
Amma dole na gaya maka cewa Sailari suna ne da
kishiyar babata ta saka min, saboda haka mahaifiyata
bata faɗarsa. Kai sani cewa ina da wata ƙanwa mai suna
Ranâ-Ƙísa-Hurura-Inshala-Yaƙa-Dása. Ita wannan ƙanwa
tawa indai tayi laifi babarmu ta dake ta to ranar baza ta
faɗi kowanne suna ba sai Sailári, wai itama ta rama
saboda tasan maman mu bata so."
Saurayin ya ƙara yin dariya yana tuno da, kafin daga
bisani ya amsawa Armad tambayarsa. "Eh zaka iya zuwa
mana. Mabiyan ɗan-baiwa suna da yawa, babu wanda ma
zai gane kai baƙo ne."
Armad ya kyaɗa kai ya ce, "to indai haka ne kuwa zanje.
Amma mai yasa dakai da ƙanwarka kuke da sunaye har
guda biyar? Inzan iya tunowa sunanka Indimi-Iyka-Sai
lari-Citta-Abati."
Saurayin ya amsa da cewa, "A kabila ta duk yaron da aka
haifa yakan samu sunaye daga ɗaya zuwa ɗari. Dalili
kuwa shi ne haƙƙin saka suna yana kan duk wanda suke
zaune gida ɗaya da wannnan yaro da aka haifa. Misali a
gidanmu mu biyar ne sanda aka haifeni. Babata ta saka
min Indimi, babana ya saka min Abati, kakata ta saka min
Iyka, Kishiyar babata ta saka min Sailari, sannan sai kuma
yar aikinmu ta saka min Citta. Shi yasa ƙanwata kuma
sunanta ya zama guda shida saboda nima na ƙaru sanda
aka haifeta."
Saurayin na zuwa nan ya ja Armad izuwa tantinsa yana
cewa. "Muje mu shirya kafin ɗai-baiwa yazo."
Sai dai suna cikin tafiya ya fashe da dariya kamar wanda
ya tuno wani abu. Armad yai niyyar tambayar mai yasa
yake dariya amma ya fasa. Can dai Sailari ya kada baki ya
ce, "na tuno wani aboki da aka haifa a gidan yawa.
Sunayensa guda saba'in da bakwai ne. A lokacinda muka
shiga makaranta akan ɗauki rabin awa ana kiran
sunayensa idan akazo kiran suna."
A zuciyar Armad ya ce lallai akwai al'ada kala-kala a
duniya. Idan kaji wata ma saika riƙe baki.
Suna shiga Sailari ya jefowa Armad ɓarin gurasa yana
cewa, "satinka ɗaya baka ci abinci ba amma jikinka bai
nuna yana jin yunwa ba, lafiya kake kuwa?"
Armad najin haka ya zare ido tare da kallon gurasar.
Lallai kuma haka ne. Abin mamakin shi ne saida ma akai
magana sannan ya tuna, domin kuwa da daida kwayar
zarra baya jin yunwa ko ƙishirwa. Lallai ba lafiya ba.
Amma ba daɗewa Armad ya tuna da cewa ashe fa dukkan
jikinsa ya juye izuwa walƙiya, saboda haka baya buƙatar
yaci abinci dan yunwa sai dai kawai dan marmari. Amma
a haƙiƙa wannan ba abu bane da zai iya gayawa kowa kai
tsaye ba. Domin wannan sifa ce ta manyan sarakunan
aljanun, kuma zaiyi wahala a yadda cewa ba aljani bane
shi indai aka ji. Saboda haka yai murmushi kawai tare da
jefa gurasar a bakinsa amma bai bawa Sailari amsarsa ba.
Shima Sailarin bai damu ba kawai yaci gaba da hirarsa.
A wannan rana saida Armad yasan kusan komai akan
ƙabilar Nára, wadda ita ce ƙabilar su Sailari. Amma
Ikenga baizo ba, washe gari ma haka, har saida akai
kwana uku. Magana ta tabbata cewa mutumin daya haɗa
kan fursunonin wannnan kurkuku suke masa biyayya
acikin shekara daya kacal, wanda akafi sani da ɗan-baiwa
zaizo wannan yankin na ƴan-daban warure, kuma anan
zai bayyana manufofinsa. Saboda haka kullum wajen
ƙara cika yake da mutane. Kullum Armad zai kewaye ya
nuya yana gwada fasahohinsa domin ƙara kwarewa,
sannan kuma yana nazarin Bango domin ganin hanyar
guduwa. Amma hakan bai hana Sailari yin hira dashi ba ta
sama da awa biyar a kowacce rana.
A rana ta biyar Armad ya haƙura da ganin Ikenga yana
niyyar tafiya sai kwatsam ƴan shela suka fara yin shelar
cewa ɗan-baiwa ya bayyana. Nan take fursunonin nan
suka fara ambaliya suna tururuwa izuwa ga ɗan-baiwa.
Armad na tsaye daga gefe tare da Sailari suna kallon. Sai a
lokacin Armad ya gane lallai akwai mutane da yawa a
wajen.
Ba jimawa saiga Ikenga nan ya bayyana sanye da jajayen
kaya samfurin alkyabba, rataye da takobinsa. Abin
mamaki sai Armad yaga duk da cewa ga kama nan amma
kamar Ikenga ya ƙara girma da faɗi sosai da sosai. Ba
jimawa ya gane cewa ƙarfin Izza ne kawai ba wani abu
ba. Koda gano haka sai Armad ya rufe idonsa domin jin
yanayin-izzar Ikenga. Amma bisa mamaki babu komai,
tamkar Ikenga baida wata izza. Ya tuno da abinda Babara
ya gaya masa na yadda wasu manyan ma'abota izza suke
ɓoye yanayin-izzarsu domin kada kowa yasan halin da
suke ciki.
Armad na cikin tunane-tunanensa yaji hayaniya, Ikenga
ya bayyana.
.
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

Hausa ebooks - pdf,txt and doc
www.hausaebooks.cf Download any kind of hausa ebooks hereMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 86: Ikenga da Armad
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Mutane sun jejjeru iyakacin ganinka a gaban dakalin da
Ikenga ke tsaye shi da tawagarsa. Kuma saboda da
ragowar hasken rana kowa na ganin kowa tar-tar. Babu
murmushi ko ɓacin rai a fuskar Ikenga saɓanin
mabiyansa wanda keta murna da shewa.
Koda bayyanar Ikenga sai wannan taron jama'a suka ƙara
ruɗewa da shewa. Babu abinda kake ji sai sunan ɗan-
baiwa. A dai-dai bayan Ikenga wani tsoho ne a tsaye,
wanda ba wani bane illa wannan mutun mai suna Kána
dake tare da Ikenga. A bayan Kána wasu sadaukai ne
sanye da kayan yaƙi daban-daban susu biyar. Dukkaninsu
ba'a ganin fuskokinsu.
Armad najin yanayin-izzarsu ya gane cewa babu wanda
acikinsu bai haye izza dubu ba. Amma ko a jikinsa.
Abinda kawai ya dami Armad shi ne yaji manufar Ikenga
ya bar wajen.
Ana jira Ikenga ya fara jawabi kawai saiya juya ya koma
inda ya fito. Lamarinda yasa nan take wajen yai tsit, kowa
ya fara kalle-kalle yana tunanin maike faruwa. Ana cikin
haka shima Kána tare da mutun biyar ɗin dake bayansa
suka bi bayan Ikenga.
Koda ganin haka sai Armad yai tsaki gami da juyawa
izuwa tantinsa domin yin shiri ya kama gabansa. Saboda
haushi ko Sailari bai yiwa magana ba. Amma bisa mamaki
a lokacin ne yaji muryar Ikenga a kunnensa.
"Idan kana so kaji manufata to ka rufe idanunka kayi
tafiya kimanin taku hamsin a jikin bango kana fuskantar
gabas kana kiran ɗalasimin 'Shaibal'shísu' zaka bayyana a
fada ta."
Koda jin wannan batu sai Armad ya haɗe gira yana
mamakin yadda Ikenga ya iya shiga kansa yayi magana ba
tare da ya bashi izini ba. Amma kawai ya share yai kamar
baiji ba. Inda ya nufi tantinsa ya haɗe kayansa ya buɗe
ƙofar zobensa na sihiri ya saka su aciki. Abu ɗaya ya rage
kafin ya bar wannan waje, shi ne sallama da Sailari.
A wajen tantin jama'a ne barkatai suke ta tattaunawa
akan dalilin da yasa ɗan-baiwa baice komai ba, amma
bisa mamaki babu wanda ya juyawa ɗan-baiwa baya duk
da haka. Hasalima wasu da dama daga cikinsu suna ganin
abinda yayi ya dace da girman izzarsa.
Armad na fitowa ya fara laluben Sailari acikin tantinsa,
amma babu shi babu labarinsa. Saboda haka ya nufo
cikin taron jama'ar nan inda ya barshi. Duk da ruɗani da
yawan jama'ar dake wajen ba jimawa sukai ido huɗu da
Sailari a tsaye yana jimamin rashin jin muryar Ikenga.
Armad ya jashi wajen mutane ya ce, "kai yanzu Sailari
baka damu da abinda Ikenga... ɗan-baiwa yayi ba?"
Koda jin wannan magana sai Sailari yai murmushi ya ce,
"ai wannan ba wani abu bane. Mutun biyar ɗin da ka gani
a bayansa sune manya-manyan ma'abota Izza acikin
wannan kurkuku kafin bayyanar ɗan-baiwa. Mutane
kamar mu basu isa suje kusa dasu ba ballantana su
gansu. Ai ganin ɗan baiwa kaɗai da mukai falala ce."
Koda jin wannan magana sai Armad ya fara gane yanayin
yadda ake rayuwa a wannan kurkuku; mai ƙarfi kamar
wani abin bauta ne. Sannan kuma Armad ya tabbatar
cewa Sailari zai iya dagewa saiya bishi idan yaji cewa zai
tattauna da Ikenga. To amma Armad bai san yanayin
yadda zata kaya ba. Ƙazamin faɗa zai iya rincaɓewa
tsakaninsa da Ikenga saboda haka bazai iya tafiya dashi
ba.
Nan take Armad ya fasa gaya masa inda zaije. "Au haka
abin yake... Ai ban sani ba. Bari naje na dawo ai kana nan
ko?"
Sailari ya kyaɗa kai, yana niyyar tambayar Armad mai
yasa yake kiran ɗan-baiwa da Ikenga amma ya fuskanci
sauri Armad yake saboda haka ya fasa.
Haka Armad ya bi ta tsakankanin wannan taron jama'a ya
ratse can nesa izuwa shiyar da Bangon yake. Yana isa ya
nufi gabas tare da fara lissafa adadin takun da yake. Babu
wani tsoro ko kuma tunanin mai zai faru da yake. Yana
jin cewa Ikenga bai isa ya cutar dashi ba a yanayin ƙarfin
izzarsa.
Ba jimawa Armad ya cika adadin wannan taku da Ikenga
ya bashi, inda ya buɗe idonsa ya tsinci kansa a wata ƴar
ƙaramar farfajiya kewaye da rafi. Komai dake wajen dai-
dai yake idan ka ɗauke launin ruwan dake cikin wannan
rafi. Ja ne jajawur, hasalima da dama zasu yadda idan aka
ce jini ne ba ruwa ba.
Armad na bayyana ya iske Ikenga shi kaɗai a zaune kan
kujera ta ƙasaita. A gaba dashi akwai wata kujerar wadda
ba kowa akai, sannan a tsakiyarsu akwai ɗan teburi ɗauke
da abin sha irin na mutanan farko. Ikenga yai wa Armad
nuni daya zauna akan wannan kujera, sannan ya miƙa
masa abin sha.
Armad kai tsaye ya zauna ya kurɓi wannan abin sha
wanda bai taɓa ganinsa ba sannan ya dubi Ikenga da wani
kallo mai cike da tambayoyi. Koda ganin haka sai Ikenga
yai murmushi tare da cewa, "kana da tambayoyi da dama
amma kayi sani na kira ka nan ne domin na baka dama
wadda baza ka ƙara samun irinta ba. Saboda haka
tambayoyinka sai dai su jira.
"Zan fara kai tsaye. Ina so a matsayinka na Magajin
Wilbafos kayimin mubaya'a. Ni kuma zan arzutaka da
abubuwa guda huɗu."
Koda Armad yaji wannnan magana saiya fashe da dariya
yana cewa, "ni zanyi maka mubayi'a ko kai zakai min?"
Amma bisa mamaki sai Ikenga yaci gaba da bayani
tamkar baiji me Armad ya faɗa ba. "Abubuwa huɗu
dazan arzutaka dasu sune; na farko zan gaya maka inda
ɓarin ruhinka yake, na biyu zan gaya maka labarin
mahaifinka, na uku zan baka ɗalasimin dazai fitar dakai
daga wannan kurkuku, sannan na huɗu zan kare ka daga
wani babban sharri dazai faru dakai acikin wannan
shekarar mai zuwa."
.
____
Rashin Response naku akan wannan littafi yasa na daina kawo maku shi gaba daya,,,,,,
Izan har bakwa response to zamu runga daukan lokaci kafin muyi post
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 87: Alkiblar Armad
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Koda Armad ya ga lallai Ikenga da gaske yake saiya canja
fuska tare da kyara zama. Ya dubi Ikenga ya ce, "Idan zan
iya tunowa lokaci na farko da na ganka akan wani tsibiri
ne ana rigimar Littafin-takobi. Kuma a wannan rana ta
dalilinka na rasa Miyura ta tare da ɓarin ruhi na.
"Lokaci na biyu dana gamu dakai ƴar uwata Nusi ta gano
hanyarda zan samo Tarifil-fakta na ceto mahaifiyata
amma bisa sharadin sai nayi nasara a gasar Jinzidal. Kai
ne sanadiyyar rashin samun nasara ta da kuma faɗawa
hannun Uznu Ururu da nayi, sannan kuma da rasa ƴar
uwata Nusi wadda har yanzu ban san inda take ba.
"To yanzu gashi mun kara gamuwa dakai a lokaci na uku.
Sai dai kuma a wannan lokaci kazo da wani sabon salo na
buƙatar mubayi'a. Kai sani cewa ban damu da me kake
ciki ba, ban damu me kake ƙullawa ba, ban damu da
yadda ka shigo wannan kurkuku ba, ban damu da ko
kana da hanyar fita ba ko baka da ita ba, ban damu da
mai yasa kake haɗa mabiya acikin wannan kurkuku ba,
ban damu wani hasashenka na wani sharri dazai faru
dani ba, ba damu ko kasan inda ruhi na yake ba. Amma
abu guda ɗaya dazan gaya maka, ni Armad Wilbafos saina
kawarda Jinzidal a ban ƙasa kuma saina samowa
mahaifiyata lafiya koda sama da ƙasa zasu haɗu. Idan
kana tunanin kana da karfin izzarda zaka iya hanani to ka
gwada. Wannan shi ne kashedi na farko kuma na ƙarshe
da zan baka."
Koda Armad yazo nan a zancensa saiya ɗauki wannan
kofi ya ƙara kora abinsha. Sannan yaja kujerarsa baya ya
miƙe da niyyar tafiya. Amma a wannan lokaci Ikenga
shima ya canja fuska ya kuma fara bawa Armad jawabi.
"Ni Ikenga O Bayajidda saina mallaki wannan duniya
koda kuwa mutane da aljanu da Ururu zasu haɗa kai su
yaƙe ni. Domin tun a ranar da aka haifeni tauraruwa ta
take bada hasken sarauta. Bari na baka kaɗan daga cikin
tarihi.
"Kafin zuwan Ururu, kafin zuwan Wilbafos, kafin zuwan
Bayajidda, akwai taurari a sararin samaniya. Wannan
taurari su suke tsara tafiyar lokaci da zamani a yadda aka
sanshi. Bayan juyin mulki da Ururu sukaiwa ƙaɓilarka sai
wannan taurari suka dusashe. A shekarar da aka haifeni
wannan taurari suka ƙara bayyanar da haskensu, kuma
tun daga wannan rana alƙalami ya riga ya bushe cewa sai
na mallaki duniya.
"Tun ina yaro nake iya karanta tafiyar taurari na gano
abinda zai faru na gaibu dama wanda ya riga ya faru. Ina
ɗan shekara bakwai na fara amfani da taurari ina sarrafa
lokaci, wanda ta haka ne takobi na take iya tsofantar da
duk abinda na sara ta hanyar zuƙe shekarun dake jikin
wannan abu. Babu wanda yasan tayadda na rayu bayan
yaƙin daya halaka gari na amma da wannan fasaha na
kuɓuta daga hannun Ururu a wannan yaƙi.
"Gamuwa dakai da nayi a lokaci na farko kawai kaciɓis ne
da kuma ƙaddara, amma kafin lokacin ban taɓa sanin
dakai ba a duniya. A gamuwa ta dakai ta biyu na gano
cewa ajikin ka akwai wani sirri na musamman, amma
kuma akwai inuwar mutuwa dake tattare da ruhinka.
Wanda indai ka shallake ta to lallai zaka zamanto magajin
wilbafos da ba'a taɓa gani ba. Nayi niyyar kashe ka a
faɗan da mukai a Jinzidal dan kada ka kawomin cikas,
amma na canja shawara.
"Nayi tunanin idan ka durƙusa a ƙasa kayimin mubayi'a
dani dakai zamu iya kawarda da daular Ururu da kuma
sarakunan Jinzidal mu kawo tamu daular. Saboda haka a
wannan lokaci na ɗora ɗalasimai masu aiki da tafiyar
taurari acikin wannna filin daga da muka fafata tayadda
koda wani abu ya faru zan iya ceto ranka.
"Bayanda Uznu ya bayyana aniyarsa a fili ta halaka ka
saina ƙara ƙarfin wannan ɗalasimi, amma sai bayan na
ɓace sai taurari suka bayyana min cewa Uznu neman
littafin-takobi yake bawai taƙamaimai kai yake so ya
halaka ba. Saboda haka sai na juyo izuwa wannan fili da
niyyar na canja fasalin wannan ɗalasimi, amma duk da
nayi amfani da hasken taurari na ɓoye kaina saida idanun
Uznu Ururu suka ganni, lamarinda yasa matsala ta faru a
yayinda nake canja yanayin wannan ɗalasimi. Daga nan
ni kaina ban san maiya faru ba, amma Uznu yayi amfani
da wannan ɗalasimi da nasa domin kare ka ya cillo ƴar
uwarka izuwa wannan kurkuku.
"Bayan komai ya lafa na ƙara yin bincike akanka na gano
cewa ruhinka ya rabe gida biyu, sannan kuma na gano
cewa zaka bayyana acikin wannan kurkuku duk da cewa
lokacin da zaka zo bai bayyana a gareni ba. Saboda haka
na yanke shawara wannan kurkuku ita ce waje mafi
dacewa da kayimin mubayi'a sannan kuma mu fara
shirin yadda zamu mulki duniya.
"A saboda haka ne nazo wannan kurkuku tun waccan
shekara na jira ka amma baka zo ba sai yanzu. Acikin
shekarar data wuce na gano cewa shi kansa Uznu yayi
kuskure, maimakon ya jefo Nusi zuwa wannan kurkuku
sai ta zarce izuwa sashin Ikwatora. Ban san mai take ciki
ba amma lallai bata cikin matsala kuma tauraruwarta
tana bada haske na lafiya.
"Nayi amfani da wannan dama ta kasancewa a wannan
kurkuku na fara haɗa kan mabiya a wannan kurkuku.
Bawai dan ina buƙatar su ba, domin kuwa kai kaɗai ne
abinda ya shigo dani wannan kurkuku, kuma a kowanne
lokaci naga dama zan iya fita cikin sauƙi. Alƙawarurruka
na guda huɗu suna nan, abinda kawai kake buƙatar kayi
shi ne ka durƙusa a ƙasa kayimin mubayi'a."
Armad yai shiru yana sauraron Ikenga, abubuwa da
dama sun ɗau hankalinsa acikin bayanan Ikenga. Akwai
yiwuwar ƙarya Ikenga yake akwai kuma yiwuwar gaskiya
ne. Bayan tsahon lokaci yana tunani sai yayi murmushi
sannan ya bawa Ikenga amsa a nutse.
"Manufarka mulki, manufa ta ceto wanda basu da ƙarfi
daga tafarkin cinikin bayi, lallai alƙiblarmu ba ɗaya bace.
Sannan kuma ina so ka sani koda alƙiblarmu ɗaya ce
kaine zakai mun mubayi'a ba nine zanyi maka ba. Kakana
Eyriyon wanda na gaji fasaharsa sarki ne na duniya baki
ɗaya. Ƙabila ta mulki dukkan duniya. Ina da ƙarfin
fasahar da jikina bazai taɓa halaka ba, bana buƙatar ci ko
sha. Ina da ɗalasimai wanda sun girmi lissafinka. Bama
kaiba Ikenga, babu wanda ya isa nayi
masa mubayi'a a wannan zamani. Kamar dai yadda na
gaya maka a farko, idan kana ji zaka iya hanani aiwatar da
manufa ta, to ka gwada.
Armad na rufe baki ya juya ya fice.
......
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 88: Sabuwar Fasaha
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Lallai akwai raini acikin abinda Ikenga yayi wa Armad,
domin duk wanda ya nemi kayi masa mubayi'a to lallai
yana nuna cewa yafi ka ƙarfin izza. Wannan shi ne abinda
yake ta kai-komo a zuciyar Armad tun bayanda suka rabu
da Ikenga.
Babban abinda yafi ɗaukewa Armad hankali shi ne yadda
Ikenga yake nuni da cewa yana iya shiga da fita ta cikin
Bango ba tare da matsala ba.
A halin yanzu Armad baida lokacin tsayawa yayi nazari
akan labaran da Ikenga ya bashi, ko gaskiya ko ƙarya.
Saboda haka ya yanke shawara zai ƙara gwada ficewa ta
cikin wannan bango. Idan ya wuce shikenan, idan kuma
bai wuce ba saiya koma izuwa Babara da mutanen
Lamarudu Wilbafos.
Amma Armad yana da cikakkiyar masaniyar cewa ƙara
shiga Bango ba tare da wani shiri ba lallai halaka ne,
saboda haka tuni Armad yai amfani da kwakwalwarsa ya
gano wata sabuwar fasaha. Hasalima akan hanyarsa yake
ta gwada wannan fasaha.
Wajenda Armad yake tafiya yayi nisa da Bango sannan
yana da ƙarancin ƙanƙara. Amma wata irin iska ce mai
ƙarfin gaske take kaɗawa. Babu gida gaba babu gida baya,
babu wani rai a wannan waje face Armad. Tuni Armad ya
alkinta kansa da kayan sanyi daga cikin zoben da
Nostaljiya ta bashi. Yana tafiya yana ƙara sauri, yasan dai-
dai inda zashi.
Lallai wannan kurkuku ta musamman ce, domin babu
wanda ake ƙullewa acikin ɗaki ko kuma a bayan kanta.
Fili ne kawai fetal iya ganinka. Kowa yana da damar yayi
yawo acikin ta, yayi gini ma idan yana so, ya haihu ya
rayu, yayi duk abinda yaga dama. Amma dai bazai fita
daga cikinta ba har abada. Wannan shi ne sharaɗin
wannan kurkuku. Tuni Armad ya samu taswirar wannan
kurkuku a hannun Sailári, wanda da ita ya gano dai-dai
wajenda yafi ko'ina sharri acikin kurkuku. Wajenda
mutanen cikin kurkukun basa ko ziyara.
Shi kuwa Armad wannan waje nan ya tunkara da niyyar
gwada sabuwar fasahar da yake ƙoƙarin amfani da ita
domin fita daga wannan kurkuku.
Ba jimawa Armad ya bayyana a tsakiyar bishiyu dogaye
masu kama dana tsamiya. Abu na farko daya fara yi masa
sallama shi ne kukan Dordor da aljanu. Koda jin haka sai
Armad yai murmushi tare da cusa kai cikin duhuwar
dajin dake gabansa. Ai kuwa yana shiga wata ƙatuwar
damisa wadda tafi girman duk wata damisa daya taɓa
gani ko ji ta bayyana a gabansa. Babu alamun jira ko
haƙuri a tattare da ita a yayinda ta afko masa da saurin
gaske tana dalalar da yawu.
Armad ya rufe idonsa domin banbance wacce irin
damisa ce. Kasancewar duk jinsin dabbar da suke iya
amfani da izza an ware su, kuma su ake kira da ALJANUN-
DABBOBI, misali idan wannnan damisa tana iya amfani
da izza sai ace mata aljanar-damisa. Aljanun dabbobi
suna da matuƙar banbanci da sauran dabbobin dawa
wanda basu da izza a wajen sauri da tsananin ƙarfi da
rashin imani. Kuma da yawansu abincinsu shi ne naman
mutane. Wannan aljanun-dabbobi su ne dalilin da yasa
jama'ar wannan kurkuku suke gujewa wannan daji.
Armad na rufe ido yaji yanayin-izza a tattare da wannan
ƙatuwar damisa, lamarinda yasa ya tabbatar cewa
aljanar-damisa ce. Amma bisa mamaki duk da wannan
damisa tana gab da cimmasa Armad bai motsa daga inda
yake ba, kuma bai maida jikinsa walƙiya ba.
Suna yin arba da wannan damisa ya buɗe baki ya kira
ɗalasimin KABAN'SHÍSU. Lamarinda yasa ya ɓace daga
inda yake ya bayyana a bayan wannan damisa. Yana
ɓacewa yaji wannan damisa taci birki tana laluben inda
yake. A dai-dai wannan lokaci Armad yaji shekarun
Izzarsa dubu sun girgiza, nan take ya fara ganin dishi-
dishi yana jin jiri. Yaji wani tari mai ƙarfi ya taso masa,
kafin yai wani abu ya fara tari yana aman jini. Wannan
damisa najin tarinsa ta juyo izuwa gareshi da mugun
nufi.
Armad dai yasan maiya taka, domin tunda yake bai taɓa
karya dokar da kakansa Zaikid ya ɗora masa ba akan
ɗalasimin Kaban'shísu, wato bai taɓa yin amfani dashi
sama da sau biyu a shekara ba. Amma a wannan lokaci
yayi amfani dashi sau biyu a wata ɗaya.
Armad na cikin wannan hali wannan damisa ta ƙara
cimmasa, amma ya rufe ido ya ƙara kiran ɗalasimin
Kaban'shísu. Inda ya ƙara ɓacewa ya bayyana a bayan
wannan damisa. Nan take jini ya fara fita daga idanunsa
da kunnuwansa. Armad yai wata ƙara saboda tsananin
zafin da yake ji, tamkar ana jera garwashi akan fatarsa.
Amma wannan damisa ta ƙara yiwowa kansa, inda yai
ƙaraji tare da ƙara kiran wani ɗalasimin a karo na uku.
Nan take yaji mutuwa ta fara yi masa sallama, ba shiri ya
juye izuwa gundarin walƙiya. Amma duk da haka saida ya
faɗi ƙasa sumamme.
Wannan damisa ta faɗa kansa da niyyar tsinke masa kai,
amma koda hasken walƙiyarsa ya dake ta saita jada baya.
Bayan tsananin ɓacin ran rasa abincinta ta ɗanyi turje-
turje da gurnani kala-kala kafin ta bar wajen.
Armad yaci gaba da zama a wannan halin tsahon kwanaki
shida, inda bayan ya farka ya tsinci kansa a kewaye da
aljanun-zakuna farare masu jajayen idanuwa.
Koda tashinsa saiya fuskanci jiransa kawai suke ya juye
izuwa mutun su cinye namansa. Tunda baza su iya
cinyeshi a haka ba to bari su jira.
Armad yai murmushin izza tare da juyewa izuwa mutun.
Wannan aljanun-zakuna guda uku suka nufo shi gadan-
gadan. Armad ya ƙara kiran ɗalasimin Kaban'shísu ya
bayyana a nesa dasu kimanin taku goma. Yana bayyana
ya ƙarajin irin raɗaɗi da tashin hankalin da yaji a baya. Su
kuwa wannan zakuna suka ƙara yiwowa kansa. Armad ya
ƙara kiran ɗalasimin ya ƙara ɓacewa ya bayyana ƙafa
goma gaba da inda yake. Wannan zakuna suka ƙara
fusata suka tisa shi.
A haka a haka saida Armad ya kira ɗalasimin Kaban'shísu
sau biyar sannan ya faɗi ƙasa sumamme. Wannan zakuna
sukai iyayinsu su halaka shi amma tuni ya juye izuwa
walƙiya haka suka haƙura.
Bayan kwanaki ya ƙara farkawa ya ƙara maimaita irin sak
abinda yayi. Sannan ya ƙara maimaitawa. Ba jimawa
Armad ya kai tsahon kimanin wata uku a wannan daji
yana gwada amfani da wannan ɗalasimi. Bayan ya samu
nutsuwa ya koyi abinda ya kawo shi saiya juya izuwa
Bango domin jarraba wannan fasaha.
Ita dai wannan sabuwar fasaha ta samo asali ne daga
ilmin Armad na ɗalasimin Kaban'shisu da kuma ƙarfin
fasaharsa ta walƙiya. Da ita zai iya tafiya cikin tsananin
sauri daga wani waje zuwa wani tayadda za'a ga kamar
ɓacewa yai. Tun a sanda ya shiga Bango a karo na farko
ya gano cewa shi kansa ɗalasimin Kaban'shísu bawai
ɓatarda mutun yake ba, yana saka mutun yai tafiya cikin
tsananin sauri tayadda za'a ga kamar ɓacewa yayi. To
idan kuwa

Please Login or Register in order to submit comment