Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

acikin saƙon
amma na ƙara baka lokaci naga ko zaka iya farkar da
jininka na wilbafos. Kai sani cewa nayi farin ciki kwanakin
baya da naga hasken farin-wata ya canja kala. Domin
nasan cewa lokaci yayi dazan biya Hidaya bashin da take
bin ƙungiyar ƴan-duba ta duniya.
"Amma fa kai sani wani hanzari ba gudu ba...."
Armad ya katse Babara ta hanyar yin ƙaraji ya zare
takobinsa yana huci, "Wai kana nufin duk wahalar dana
sha ta nemo Tarifil-fakta a banza!!"
Armad bai san lokacin daya kaiwa Babara wani sara ba
cikin ɓacin rai. Babara yai tsalle gefe guda yana
murmushi, "To yanzu da ban tura kaba zaka farkar da
jininka? Kasha wahala, amma yanzu zaka ga amfaninta.
Sannan kuma indai hanyar Izza zaka bi wannan baka ga
komai ba a fannin wahala. Yanzu duniya tasan dakai,
idanun kowa zai dawo kanka. Idan bakai da wuri ba ka
farka lallai yanzu ne zaka san wahala."
Babara yana magana amma Armad kawai huci yake yana
kallonsa a fusace. Bayan ɗan lokaci Babara yaci gaba da
jawabi, "Sai ansha wuya ake samu Izza. Kuma lallai indai
kana so ka zama ma'aboci Izza yanzu ka fara. Saboda
yayarka Hidaya nayi alƙawari zan koya maka yadda zakai
amfani da idanuwanka wanda ita kaɗai ce hanyar da zaka
zama ma'aboci Izza na gaskiya ka iya tsayawa a gaban
Ururu sannan kuma ka ceto mahaifiyarka ta hanyar bata
shekarun Izza. Amma kai sani cewa hatta yayarka Hidaya
wadda hatta a duniyar aljanu ana labarin ƙarfin
kwakwalwarta da gane abubuwanta saida tayi shekaru
uku tana koyar yadda zatai amfani da idanuwanta. Lallai
zaka iya yin shekaru goma kana koya wanda kuma
mahaifiyarka baza takai wannan lokaci ba.
"Naji daɗin ganinka da wannan zoben domin zai taimaka
mana wajen ajiye mahaiyarka aciki." Babara yai nuni da
zoben da Nostaljiya ta bawa Armad.
Babara ya tafa hannunsa tantin dake bayansa ya ɓace,
babu abinda ya rage sai wata ƴar jaka a hannunsa. Ya zira
hannu a jakar ya ɗakko wata leda mai cike da Ayrid ya
jefawa matan nan guda biyu ladan aikinsu. Sannan ya
juyo wajen Armad yana mai cewa, "Zan koya maka yadda
zakai amfani da idanunka dama kuma duk wani abu dana
sani a shekaru na dubu ɗaya da ɗari uku a duniya.
Saboda Hidaya."
Armad yama rasa mai zaice. Kansa yana nema yai tsawa
saboda tsabar caji. Ya za'ai ace abinda yai shekaru yana
nema wai dama duk gwada shi kawai ake. Sannan kuma
babban abin haushin ma shi Babara yana nunawa ba
wani abu bane. Hasalima har ya gama yanke shawara zai
koya wa Armad al'amuran Izza kamar ma babu abinda ya
faru.
Armad ya kasa daurewa, "Zan bika sabida mahaifiyata,
amma idan wannan ma ya zama wani kwajin to lallai sai
na sare kanka." Armad ya buɗe ƙofar wannan zobe ya
killata mahaifiyarsa aciki sannan yabi Babara.
Babara yai dariya, "Kai sani cewa idan na bari
mahaifiyarka ta rasu kona mutu sai Hidaya ta ƙara kashe
ni."
A wannan lokaci hankalin Armad ya dawo kan Hidaya,
inda ya buɗe baki ya tambayi Babara, "Wai kana da
tabbas yayata tana raye? Kakana ya kawo min takobin ta
shekarun baya da suka gabata."
Babara ya kyalkyala dariya yana mai kallon sama tare da
cewa, "Kasan mai suke cewa yayarka a doron ƙasa ta
farko? Hmmm.... Koda yake wasu suna cewa sunan ya
samo asali ne daga jinsin Dordor wasu kuma suna cewa
daga aljanun farko. Amma dai yayarka hatsabibiya ce ta
rubutawa a jarida! Lallai baza ta mutu ta sauƙi ba, kuma
idan ta mutu sai labari ya cika duniya."
Armad ya haɗe gira, "Wanne suna suke gaya mata?"
Babara yai murmushi gami girgiza kai, "Bari ta gaya maka
da kanta idan kun haɗu."
________
Alhamdullh rabbil alamin. Dukkan godiya ta tabbata ga
ALLAH madaukakin sarki daya bani ikon kammala littafin
farko na jerin littattafan Magajin wilbafos. Ina rokon
ALLAH ya ci gaba da bani lafiya da ikon rubuta wannan
littafi har zuwa karshensa.
Godiya ta musamman ga dukkan makaranta Wanda suka
kasance tare dani tun daga farko har zuwa karshe.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 63: Eyriyon
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
_____
***
Shekarar 1841 Bayan Amri, acikin garin Kanyu, Armad ne
ke zaune shida kakansa Zaikid Wilbafos da Mahaifiyarsa
da kuma yayarsa Hidaya a kewaye da teburin cin abinci
suna cin abincin dare. Zaikid dai mutun mai yawan farin
gashi da manyan gaɓɓai, kana ganinsa zaka san duk da
shekaru sunja amma yana nan da jarumtarsa. Hidaya
kuwa tana kama da Armad sosai sai dai cewa ita fara
kamar mahaifiyarsu.
Hidaya ta leƙa ta tagar dake dai-dai saitin ta sannan ta
juyo ta dubi Armad tana cewa, "Kaga kai sauri ka cinye
abincinka ka kwanta dare ya fara yi. Kalli kwanon kowa ya
gama amma banda kai."
Tundai fara cin wannan abincin Armad yake ta cakwala
kuma yaƙi tsayawa yaci abincin. Hasalima da Hidaya tayi
masa magana baima nuna yaji ba, kawai yaci gaba da
abinda yake. Zaikid ya kalli Hidaya, Hidaya ta zare ido da
sauri tana cewa, "Dattijo, bafa ninai girkin nan ba kake
kallo na, abincin Mama ne baiyi daɗi ba shi yasa ƙani na
yaƙi ci."
"Hahaha..." Zaikid ya kyalkyala dariya yana ƙifta ido tare
da satar kallon gefe. "Ƴata Fatima kinji dai me ƴaƴanki
suke cewa! Wai abincinki baiyi daɗi ba!"
Fatima dai irin matan nan ne fara re kyakyawa masu
girman jiki. Sau da dama Zaikid yakan ce shi ta gado a
girman jiki da kuma fari domin kuwa yana bada labari
cewa matarsa, wato babarta, bata da girman jiki kuma
baka ce wankan tarwaɗa kamar Armad. Fatima nada
idanu dara-dara masu cike da ƙaunar ƴaƴanta guda
biyu.
Zaikid na kyalkyala dariya irin ta manyan mutane, Fatima
na ɓata rai tana cewa, "Sa'a ta biyu cir ina wannan kirkin
sannan ace baiyi daɗi ba. Ɗana Armad gayamin maiya
hana ka ci."
Armad yai shiru baice komai ba. Wasa kawai yake da
cokalinsa yana kallon kasa. Hidaya taja kujerarta kusa
dashi ta caka cokalinta akan naman dake kan kwanonsa
sannan ta haɗa da wainar dake kan kwanon ta buɗe
bakin Armad ta danna masa.
"Cinye kaji ƙanina." Hidaya ta shafa tambarin Miyurar
dake ɗamfare a goshin Armad tana mai cewa, "Indai
kacinye gobe kafin na fita zan tashi dakai sama."
"Nhi....fa bha tasshi nakeh so ba....." Armad ya furta
bakinsa cike da abinci.
"To mai kake so?"
Armad ya ɗau lokaci ya haɗiye abincin a hankalin sannan
yace, "Ina Abba?"
Tambaya ce mai sauƙi amma duk ɗakin saida yayi tsit.
Armad bai san mai yasa ba amma mahaifiyarsa da
kakansa basa san zancen baban nasa. Nan take sukai
kyaran murya suka fice daga cikin ɗakin suka bar Armad
da Hidaya.
"Indai ka cinye abincin nayi maka alƙawari yau zan gaya
maka abu biyu ko uku a game da babanmu. Amma sai
kayimin alƙawari baza ka ƙara yin maganarsa a gaban
mama ba."
Tana rufe baki Armad yai tsalle, fuskarsa cike da
murmushi ya amsa wannan alƙawari. Cikin daƙiƙa kaɗan
ya gama cin abincin. Hidaya taja shi suka fita ta bayan
gidan suka zauna a gaban wasu tagwayen bishiyu suna
suna kallon farin wata.
Hidaya taja numfashi ta dubi Armad, wanda ke kallonta,
ta fara da cewa, "Da tuni sunanka Eyriyon, Eyriyon
Wilbafos. Ina tuno sanda Abba yace shi ne sunan da yake
so a sa maka. Amma mama tace sunan baiyi ba, Armad
Wilbafos take so."
"Eyriyon??" Armad ya karkata kai, domin kuwa bai taɓa
jin sunan ba. Hasalima sunan yafi kama dana mutanan
da.
Hidaya tace, "Eh... Amma dai abinda nake so ka riƙe shi
ne Abbanmu yana sonmu sama da komai a duniya. Yama
fi sonka akaina. Sannan kuma yana da rai kuma zaka
ganshi indai muna raye. Armad...." Hidaya ta ɗan ja
numfashi kamar tana kokwanton ta faɗi abinda ke ranta
ko kuwa. Amma dai daga ƙarshe ta yanke shawarar ta
faɗa, "Armad kasan mai ake cewa Zaɓi?"
Armad ya kyaɗa kai, "Eh.. Shi ne kowa a bashi dama yayi
abinda yake so?" Daga jin sautin Armad bashi da tabbas
domin kuwa sautin yafi kama da tambaya a maimakon
amsa. Amma yaci sa'a Hidaya ta kyada kai.
"To mahaifinmu zaiso ace idan ka girma ka zama jarumi
ko kuma wani jagora ko kuma mai yin doka, kada ka
takurawa mutane akan abinda yake ba dole ba, ko kuma
abinda yake ra'ayinka ne kawai. Zaiso ace kowa ka bashi
zaɓi. Ka gane mai nake nufi?"
Armad yai shiru idanunsa cike kokwanto. Lallai kallo ɗaya
zakai masa kasan bai gane mai take nufi ba.
"Hmmmm..." Hidaya taja dogon numfashi, "Ba sai ka
gane yanzu ba, kawai ka riƙe kalmomin kuma ka tuno su
anan gaba koda na mutu. Kaji ƙanina."
Armad ya kyaɗa kai, sannan a lokaci guda fuskarsa ta
canja domin kuwa baya so ko kaɗan yaji yayar tasa tana
zancen mutuwarta, wanda kuma abu ne data saba.
***
Shekarar 1854BA
____
Babara ya ja dogon numfashi gami da tafa hannunsa
akan iska, lamarinda yasa iskar dake wajen ta kaɗa tare
da yin ƙuwwa. Sannan ya juyo ya dubi Armad wanda ke
tafe a gefensa, "Daga yau zaka iya kirana da Bóka, Boka
Babara."
Armad ya haɗe fuska cikin mamaki, "Bóka kuma?"
Babara ya kyaɗa kai, "Boka shi ne sunan da ake kiran duk
wanda yakai muƙamin sarkin duba."
"Ohoo.."
"Kakanka Zaikid yazo watanni kadan bayan ka tafi. Nayi
mamaki da baka tambayeshi ba."
Armad ya cake ƙafa a ƙas tare da tsayawa. "Ina sane
dashi."
Lallai bawai mantawa yayi da Zaikid ba sai dai kawai
daman bai taɓa tsammanin zai dawo ya tarar da kakan
nasa a gida ba. Abu ɗaya daya sani bayan sunyi magana
dashi ta hanyar Ayrid a shekarun baya shi ne lallai Babara
bai isa ya cutar da mahaifiyarsa ba, tunda kakan nasa
zaije ya same shi.
Armad ya ɗanyi shiru an ci gaba da tafiya sai kwatsam yai
zumbur kamar ya tuno da wani abu, "To mai yasa shi ɗan
tsohon baiyi mata maganin da kansa ba. Ai shima
Wilbafos ne, kuma indai ni ko Hidaya zamu iya shima ya
kamata ace ya iya."
Babara yaja dogon numfashi, "To kai a tunaninka waye ya
koyamin yadda zaka iya sarrafa idanunka. Nima ban san
mai yasa yaƙi yi mata maganin ba, amma dai ya bar saƙo
na baka sannan kuma ya ce na tambaye ka mai kake so
ka cimma a rayuwarka bayan samarwa mahaifiyarka
lafiya?"
Armad yai shiru yana tunani naɗan lokaci kafin daga
bisani ya kyaɗai yayi magana ƙasa-ƙasa, "Daman nasan
ɗan tsohon nan zaiyi abinda yafi haka ma."
"Me kace?" Babara baiji mai Armad yace ba.
Armad ya kyaɗa kai, "Ba komai!Babban abinda nasa a
gaba bayan samarwa mahaifiyata lafiya shi ne hana
cinikin bayi. Kuma ina mai rantsuwa da mahaliccin ƙasa
bakwai, saina hana cinikin bayi a doron ƙasa kafin na
daina numfashi."
"Hmmmm....." Boka Babara yaja dogon numfashi gami
da kyaɗa kai. "Ruwa baya tsami banza. Jini kuma baya
ƙarya. Da bakai haka ba da ba'ace kai jikan Wilbafos
bane. Bari na tambaye ka, shin ka taɓa tunanin mai yasa
mahaifiyarka ta hanaka gayawa mutane sunanka na
wilbafos?"
Armad ya girgiza, "Na sha yin tunani akai amma har
yanzu bansan mai yasa ba."
Babara yayi murmushi, "Ga dukkan alamu ƴan uwanka
basa son gaya maka tarihinka. Amma kada ka damu yau
zan gaya maka mai yasa akan hanyar mu kafin mu ƙarasa
wajen da zaka fara karɓar horo."
______
Ku saurari chapter gobe. Sannan kuma ina buƙatar wasu
daga cikinku su rinƙa yin comment a ɗaya group da nake
sharing littafin domin sauran mutane sufi gani.

Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 64: Magajin wilbafos na farko
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
Babara yai kyaran murya ya fara bawa Armad kaɗan daga
cikin tsohon tarihin ƙasa bakwai, "Yau muna shekarar
1854 Bayan Amri(BA), kamar yadda ka sani Amri kalmar
yaren Aldurish ce wadda take nufin saukar da mutane
zuwa ƙasashen ƙasa. Al'ummar ƙasa bakwai suna da ilmi
akan abubuwan da suka afku acikin wannan shekaru
dubu ɗaya da tamanin na bayan Amri, amma kaɗan ne
daga cikinsu suke da masaniya akan al'amuran da suka
afku kafin Amri. Ni Boka Babara ina daga cikin waɗanda
suka san kaɗan daga abubuwan da suka faru a wancan
zamani domin kuwa an haifeni a shekarar 27 kafin Amri
(KA). Wanda idan ka haɗa zaka ga shekaru na a yanzu sun
kama 1881 da haihuwa.
"Lokacin da aka haifeni lokaci ne mafi tsanani a tarihin
ɗan adam. Lokaci ne na yaƙi, lokaci ne wanda ba'a taɓa
samun irinsa ba a tarihi. Mahaifiya ta tana haifata aka
biyo ta za'a kashe ta, kuma saboda ta ceci ni ta salwantar
da rayuwarta ta hanyar bani dukkan ragowar shekarunta
na Izza. Babana dama ya daɗe da mutuwa a filin daga.
Babu kowa babu wanda na sani haka na rayu saboda
shekarun Izza da mahaifiya ta barmin. Shin kasan
menene ya jawo wannan yaƙi?"
Armad ya girgiza kai, "A'a."
Boka Babara yaci gaba da bayani, "Doron ƙasa ta farko ya
kasanse bashi da sashin Ikwatora, amma a maimakonsa
wani katafaren ruwa ne wanda ya raba ƙasar gida biyu.
Wannan ruwa shi ake kira da Ruwan maliya. A shekarar
9541KA anyi wani sarki mai suna Aldaima Wilbafos
wanda akafi sani da Wilbafos na farko. Aldaima shi ne
mutun na farko daya taɓa mulkar dukkan doron ƙasa ta
farko ɓangaren gabas da ruwan maliya, kuma ya haɗa
kan dukkan ƙabilu a tafarki ɗaya. Aldaima ya rayu tsahon
shekaru dubu shida zuwa shekarar 4033KA, inda bayan
ya mutu ƙaninsa mai suna Eyriyon Wilbafos ya haye
karaga kasancewar Aldaima bashi da ɗa. Eyriyon Wilbafos
ya zama Wilbafos na biyu. Nima ba'a haifeni ba a lokacin
kuma lallai bansan haƙiƙanin taƙamaimai mai ya faru ba,
amma nasan cewa Ururu ƙabila ce wadda tafi kowacce
girma a ɓangaren yamma da ruwan maliya. Kuma
sarkinsu, Kuyurussa'ayi Ururu da ɗansa Dumaƙisu
Dul'ururu Kuyurussa'ayi sune halitta ta farko da suka
taɓa haye ruwan maliya suka shigo sashin gabas da
ruwan maliya a shekarar 945KA. Wanda idan ka lissafa
zaka ga bayan Eyriyon Wilbafos yayi shekaru sama da
dubu uku kenan yana mulki. Kuma abin mamaki shima
Eyriyon bai sami haihuwa ba har zuwa wannan lokaci.
"Naji labari mutanen gabas da ruwan maliya basu karɓi
Ururu ba, musamman saboda baƙaƙen idanuwansu,
amma daga baya sarki Eyriyon yai magana aka daina
kyamarsu. Shekaru ɗari biyar bayan Sarki Ururu ya
bayyana a ƙasar gabas saiya fara kira izuwa tafarkin
rukunai biyu. Wanda sune dai rukunan daka sani wanda
ɗaya shi ne na Jinzidal, ɗaya kuma na Amri. A wancan
lokaci ana kiransu da 'Amri da Jinzidal'. Bansan maiya
biyo baya ba, amma dai nasan sarki Eyriyon ya nemi
Ururu da su daina wannan tafarki ko kuma su koma inda
suka fito.
"Ururu sukai kunnen uwar shegu da wannan kashedi na
sarki Eyriyon Wilbafos. Shekaru kaɗan bayan sunƙi sai
Eyriyon ya kira kwamandojinsa guda ɗari dake ban ƙasa
izuwa yaƙi da Ururu. Yaƙin da aka shafe shekaru ɗari uku
ana yinsa. Yaƙin da yai sanadiyyar asarar sama da rayuka
miliyan dubu a ban ƙasa. Bazan taɓa mantawa ba ina ɗan
shekara ashirin da biyar saida takai duk wata ƙasa ta juye
izuwa launin ja launin jini saboda tsabagen jini dake
kwaranya.
"Sarki Eyriyon kafin fara wannan yaƙi ya bar wasiyya a
cikin wani sihirtacce littafi wanda akace ya juye izuwa
takobi. Sannan ya aiki ɗaya daga cikin kwamandunsa da
wannan littafi/takobi.
"Wannan yaƙi dai kamar yadda ka sani Ururu ne sukai
nasara kuma a sakamakon haka rukunai biyu wato Amri
da Jinzidal suka kasance. Ina tunano lokacinda sarki
Ururu ya kira wani ɗalasimi wanda yasa dukkan wani
biladama wanda bashi da baƙin ido bacci. Wanda bayan
mun tashi daga wannan bacci muka tsinci kanmu acikin
duniyoyi shida na ƙasa. Shekaru kaɗan bayan munzo
sarki Ururu ya aike da ruduna wanda suka zo suna
binciken wannan kwamanda da sarki Eyriyon ya aiko.
Naji daga baya cewa suna neman wani abu ne da Eyriyon
ya bari mai suna Littafin-takobi. Amma dai ga dukkan
alamu har yanzu basu samu wannan abu ba, domin kuwa
har yanzu akwai tsofaffin ƙungiyoyi dake neman wannan
abu mai suna Littafin-takobi. Wannan shi ne kaɗan daga
cikin tarihin duniyar ƙasa bakwai."
Boka Babara ya daki ƙasa da sandarsa inda ƙoƙon ruwan
ya bayyana. Ya kwankwaɗi ruwan sannan ya juyo ya dubi
Armad wanda ke tsaye yana mamakin wannan tsohon
tarihi da yaji. Ko a mafarki bai taɓa tunanin ƙabilarsa ta
Wilbafos takai haka tsufa ba. Sannan kuma ga zancen
Littafin-takobi, sai a yanzu ya gane dalilin da yasa Uznu
Ururu yake matuƙar neman wannan littafi. Kuma Armad
ya gano cewa indai har da gaske littafin ya narke a cikin
jininsa to kuwa lalle bazai taɓa bawa kowa shi ba har sai
yasan meye aciki. Armad ya tuna da zancen ɓacewar
Miyurarsa wanda abu ne wanda har a wannan lokaci bai
daina damunsa ba. Lallai ko a iya haka Littafin-takobi ya
janyo masa masifu da dama kuma babu yadda za'ai ya
rabu dashi ba tare da yaga abinda ke ciki ba.
Muryar Boka Babara ita ce ta katse masa tunaninsa inda
ya juyo ya kwashe duk labarin daya faru dashi akan
Littafin-takobi ya gayawa Babara. Lalabarin da yasa
Babara ya daɗe yana tunani wanda har suka iso inda zasu
fara horon baice komai.
Daga bisani Babara ya juyo izuwa Armad da murmushi
yana mai cewa, "Ga dukkan alamu jininka na Wilbafos ba
ƙarami bane. Amma lokaci ne kawai zai nuna, domin
kuwa ba kai kaɗai ne jinin Wilbafos ba. Idan baka da wata
tambaya zamu fara bayanin horo."
Armad ya dubi Babara fuskarsa ɗauke da murmushin
fahimta yana cewa, "wato idan na fuskanta a shekarun
baya daka tambaye ni suna na tuni dama ka riga ka sani
saboda kasan yayata Hidaya. To amma mai yasa ka turani
nemo Tarifil-fakta indai burinka kawai na koyi horo ne? Ai
akwai hanyoyi da dama wanda zan samu horo wanda
basu kai wannan hatsari ba. Mai yasa?"
Babara ya ƙara yin murmushi, "lallai kana da zurfin
tunani. Wannan haka yake, akwai hanyoyi da dama
wanda da naso da ban tura ka nemo Tarifil-fakta ba, to
amma kada ka manta nasan cewa da Hidaya da
Mahaifiyarka Fatima da kakanka Zaikid suna daga cikin
wanda suka yadda Tarifil-fakta shi ne kaɗai mutumin da
yasan yadda za'a sarrafa Littafin-takobi. Na tabbata wani
daga cikinsu ya taɓa yi maka zancen neman Tarifil-fakta."
Nan take Armad ya tuno da abinda mahaifiyarsa ta gaya
masa akan neman Tarifil-fakta. Komai yanzu ya fara yi wa
Armad ma'ana. Babara yasan iyalan gidan Armad sosai:
yasan Fatima Wilbafos tana neman Tarifil-fakta kuma
yasan neman da take masa yana alaƙa da Littafin-takobi,
sannan kuma yasan Hidaya. Hakan nema yasa ya tura
Armad nemo Tarifil-fakta.
Babara ya daga ɗan-yatsa,
"Amma dai duk da haka kada ka gayawa Hidaya halin
daka shiga a yayin neman Tarifil-fakta, koba komai kaga
ai yayi maka amfani ka samo Littafin-takobi. Ina roƙonka
da koda na mutu kada ka gaya mata."
Armad ya gwale ido cikin mamaki, "Koda ka mutu?"
Babara ya girgiza kai, "Eh koda na mutu! Baka da labarin
akwai wasu Rauhanan aljanu goma da suka yaudari
Hidaya a shekarar 1801BA kuma suka sha guba suka
mutu kafin ta kama su. Amma Hidaya ta kira taron aljanu
tasa aka tashe su sannan ta ƙare kashesu ta mummunar
hanya. Kasan sunan da suke gayawa Hidaya a tsakanin
aljanu?"
Idan Armad yana jin irin waɗannan maganganun a game
da Hidaya sai yaji kamar ba yayarsa ba daya sani. Yai
murmushi ganin yadda fuskar Babara ta fara canjawa,
"Indai kana tare dani kada kaji komai, bazan gaya mata
ba. Amma wanne suna suke gaya mata?"
Wata dariyar mugunta tazo gefen fuskar Armad, lallai ya
samo lagon Babara tunda dai ya gano abinda yake jin
tsoro.
"Ka ƙyale wannan sunan, idan kun haɗu ta gaya maka da
kanta."
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 65: kasa bakwai
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Haka dai Armad da Babara suka ci gaba da tafiya sannu a
hankali har zuwa faɗuwar rana. Mafi yawancin hirar tasu
Babara ne yake yiwa Armad tambayoyi akan abubuwan
da suka faru dashi a yayin neman Tarifil fakta. A dai-dai
wannan lokaci ne suka fara hangen ƙatoton bangon
ruwan nan wanda akewa laƙabi da bangon arewa. Babara
ya tsaya tare da neman waje ya zauna a ƙasan wata
bishiya.
"Nayi wa kakanka Zaikid alƙawari zan koya maka yadda
zaka sarrafa idanuwanka ka taimaki mahaifiyarka, amma
daga nan dani dakai zamu yi hannun riga. Saboda haka
har zuwa wannan lokaci, Zaikid ya barmin amanarka a
matsayin ɗalibi da malaminsa. Zanyi zaton ka bani irin
girmamawar da kake bawa Zaikid a yayin da nake koyar
dakai."
Armad yayi murmushi. Dama dai shi Armad ba mutun ne
mai raina manya ba, kuma koda Babara bai faɗa ba bashi
da niyyar raina shi.
Babara ya ƙara duban Armad, "Mai ka sani game da
tsarin ƙasa bakwai? Ina so kayimin bayani dalla-dalla."
Armad ya ɗanyi shiru yana kokwanton wacce alaƙa
wannan tambaya take dashi akan abinda Babara zai koya
masa, amma daga bisani ya yanke shawara yayi wa
Babara biyayya kawai kada yace ya rainashi.
"Ƙasashe bakwai sune kaɗai wajen da bil adama zai iya
rayuwa aciki. Nasan waɗannan ƙasashe a jere suke ɗaya
a saman ɗaya; daga doron ƙasa ta farko zuwa na bakwai.
Nisan dake tsakanin wannan ƙasashe bazai misaltu ba,
kuma haka ne yasa ƙasa ɗaya bata taɓa iya hangen wata
ƙasar. Hasalima wata ƙasar baza ta taɓa sanin samuwar
wata ƙasar ba idan banda kasancewar bangon ruwa
wanda ya haɗe dukkanin wannan ƙasashe. Shi dai
wannan bangon ruwa ya sakko ne tun daga doron ƙasa
na farko har zuwa na bakwai, kuma tun a farkon lokaci
yake tsaye a yadda yake bai daina zuba ba. Da dama daga
cikin masana sunyi rubutu akan wannan ruwa da dalilin
da yasa yake ta zuba amma yaƙi ƙarewa, sannan kuma
wajen da yake zubar yaƙi cika da ruwa yayi ambaliya,
amma har zuwa wannan lokaci amsar kawai da suka
samo ita ce 'TSAFI'. Wato dai kowa ya yadda tsafi ne ke
riƙe da wannan katafaren gangar ruwa wanda ake kira da
BANGO."
Armad yaja numfashi sannan shima ya nemi waje ya
zauna a gefen Babara kafin daga bisani yaci gaba da
bayani, "Ada bansan mai yasa ake cewa wannan ruwa
bango ba, amma lokaci na farko dana fara ganinsa shi ne
shekarar dana zo wajenka. Bayanda na tafi na haɗu dasu
Nostajiya naga yadda ake ganin wannan gangar ruwa ya
shafe ko'ina sannan yana ambaliya a tsaye cikin ƙasaita
tamkar tamkar wani bangon duniya wanda bazai taɓa
faɗuwa ba. Nan take na gane dalilin da yasa ake ce masa
Bango. A sannanne na gano cewa ashe akwai Bango ɗaya
a ɓangaren gudu ɗaya kuma a arewa: wadanda ake kira
da bangon kudu da bangon arewa. Waɗannan bangwaye
guda biyu sune suka datsa kowacce doron-ƙasa acikin
ƙasashen nan guda bakwai izuwa gida uku: ɓarin arewa,
ɓarin kudu, da kuma ɓarin tsakiya wanda shi ake kira
Ikwatora.
"Kowanne ɓari duniya ce mai zaman kanta wanda take
ƙunshe da mutane miliyoyi. A kowanne lokaci na shekara
ɓarin kudu suna da sanyi sosai kuna a sau da dama har
ƙanƙara ke zuba, amma ɓarin arewa zafi ne dasu kaf
shekara. Kakana Zaikid ya gayamin ɓarin Ikwatora sune
suke da sanyi da zafi: rabin shekara ai zafi rabi kuna ayi
ƙanƙara.
"Akwai hanyoyi biyu kacal da bil adama suke iya yin
safara daga wata doron ƙasa zuwa wata. Hanya ta farko
ita ake kira da Eycigan, hanya ta biyu kuma hanyar
jiragen ruwa. Eycigan kalma ce ta yaren Aldurish wadda
take nufin gida. Kuma haka abin yake, Eycigan tsarin
gidaje ne guda goma sha huɗu wanda aka gina su a
kowacce tasha na ɗaya daga cikin doron ƙasashen nan
bakwai. Babu wanda yasan yadda aka gina su ko kuma
yadda suke aiki, amma indai ka biya kuɗinka ka shiga ciki
to zaka bayyana a inda kake so. Bayanda ka buɗe min
wannan ƙofa na shiga a shekarun baya na gano cewa
Eycigan tana kama da irin wannan ƙofofi na tsafi da ake
yawo ta ciki. Nostaljiya ma ta buɗe min wata a ƴan
kwanakin baya.
"Hanya ta biyu ita ce amfani da jiragen ruwa ayi tafiya
daga ƙasa zuwa akan Bango. Amma duk da cewa hanyar
Eycigan nada matuƙar tsada mutane sunfi amfani da ita
saboda sharrin ƴan fashin ruwa da Dordor masu cin
naman mutane da kuma lokaci da ake ɗauka a jiragen."
Armad yai shiru yana jira Babara ya jinjina masa, domin
a ganinsa babu wani abu daya shafi fasalin ƙasa bakwai
da bai faɗa ba, amma Babara yai masa irin kallon nan
mai nuna ana so kaci gaba. Armad haɗe gira, yaya za'a ce
da saura.
Babara ya kyaɗa kai, "Eh... bayaninka yayi to amma baka
faɗa min yadda ake safara daga wani ɓarin zuwa wani ba
akan doron ƙasa ɗaya. Wato dai ina so naji yadda zaka
iya ketawa daga ɓarin arewa zuwa ikwatora zuwa kuma
ɓarin kudu duk akan doron ƙasa ɗaya? Kai sani cewa
hatta gidajen Eycigan da ƙofofin daka ga muna buɗewa
basa iya kai mutun daga wani shashi zuwa wani."
Nan take Armad gwale ido cikin mamaki. Bai ma taɓa
tsayawa yayi wa kansa wannan tamabaya ba. Duk a
tunanin Armad tafiya daga doron wata ƙasa zuwa wata
shi ne mai wahala, amma tafiya daga wani sashi zuwa
wani ba zaiyi wahala ba.
Armad ya gurgiza kai, "Ban sani ba gaskiya."
Babara yayi murmushi, "To wannan shi ne dalilin da ya
na tambaye ka bayani akan doron ƙasa bakwai, domin
najin ko kasan irin haɗarin da zaka shiga nan bada
dadewa ba."
"Hatsarin dazan shiga kuma?" Armad ya kasa yin shiru.
Babara yayi kamar baiji tambayar Armad ba yaci gaba da
maganarsa, "Ketawa ta cikin Bango wani babban abu ne
wanda hatta manyan ma'abota Izza suke jin tsoro. Kai
sani cewa Bangon arewa dana kudu suna da girma sama
da yadda kake zato ko tsammani, kuma acikin su akwai
sharrika wanda kaɗan ne daga cikin biladama suka taɓa
gani ko ji. Ina daga cikin wanda suka yadda cewa duniyar
dake cikin Bango ita ce waje mafi hatsari a duniya. Dani
dakai zamuyi tafiya acikin wannan waje, kuma aciki zan
koya maka yadda zaka sarrafa idanuwanka. Kai sani cewa
sau ɗaya kacal na taɓa iya keta rabin wannan waje. Lallai
dani dakai duk zamu iya halaka, amma na riga nayi wa
kakanka alƙawari zan koya maka yadda zaka sarrafa
idanuwa ka, kuma lallai mu ƴan ƙabilar Bayajidda bama
saɓa alƙawarinmu."
_______
1) Na ɗan samu free time, so zaku ga post ya ƙaru amma
fa ba cewa nayi zai ɗore ba. Saboda kada kuga daga baya
mun koma yadda muke yi da.
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna

Please Login or Register in order to submit comment