Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tanada domin yin cinikin bayin dai wani
ƙatoton ɗakin taro ne mai hawa-hawa har guda uku.
A hawa na farko akwai mutane gama gari na zaune, a
hawa na biyu kuma ƙananun sarakuna ne, a hawa na uku
kuwa anan sarakunan Jinzidal da muƙarrabansu suke.
Daga gaban filin akwai dandamali mai ɗan tudu. Akansa
akwai wani ɗan akwati da akayi da gilashi. Ba sai ma ka
tamabaƴa ba, kana gani kasan acikin akwatin gilashin ake
saka wannan bayi domin gabatar dasu ga maiso.
Taro yayi taro kuma babu wanda bai hallara ba, saboda
haka ba jimawa aka fara shigo da bayi kala-kala ana
gabatar dasu acikin wannan gilashi ga mai buƙata.
Mai gabatarwar wani ɗan dogon mutun ne mai yawan
ƙasumba. Muryarsa tuni ta dusashe, koda yake dai dama
ba zaƙi ne da ita ba.
Bayan an gabatarda sama da bayi ashirin saiga wani
saurayi nan an fito dashi. Yana tafiya dakyar cikin ankoki
na baƙin ƙarfe. Duk jikinsa jini ne, sannan kuma rigarsa
ta yayyage.
Aka shiga da wannan saurayi cikin wajen nan, sannan
alƙalin ya saka masa kuɗi kimanin kuɗin Ayrid dubu sittin
kacal. Wannan saurayi ba wani bane illa Armad Wilbafos.
Ga dukkan alamu aljani Netti da aljani Kalkutu saida suka
saka wasu ɗalasimai a jikin Armad tayadda babu wanda
zai iya gane shi. Domin lallai da mamaki ace jaruminda
yai suna a gasar Jinzidal ta wannan shekara amma duk
taron dubunnan jama'un nan dake wajen cinikin bayin
babu wanda ya gane Armad.
Sai dai kuma wani abin Alajabi ana shirin siyarda Armad
ga wani attajirin birni kawai sai aka ji murya daga cikin
wajen hawa na uku, wato wajen da sarakunan Jinzidal ke
zaune.
Wannan murya ba wata bace illa muryar gimbiya
Nostalgiya. To koma dai ya ake ciki idanun Nostalgiya sun
gano wannan saurayi, kuma ga dukkan alamu babu
yadda za'ai aƙi siyar mata dashi.
Ana jin muryar daga inda take duk wani mai so yai
jayayya akan cinikin Armad ya fasa. Lallai babu wanda zai
iya jada sarakunan Jinzidal koshi wane ne.
Armad na cikin wannan gilashi yana rantsuwa da dukkan
abinda ya taɓa isa ai rantsuwa dashi cewa lallai tunda aka
saka shi acikin wannan gilashi to kuwa sai yaga bayan
Jinzidal. Kuma lallai ya maida shi dalilin rayuwarsa cewa
sai ya kawo ƙarshen ranar da za'a ringa saka mutane
acikin keji kamar wasu kaji ana siyar dasu. Armad dama
can ya tsani harkar cinikin bayi, to amma bai taɓa sanin
haka waɗanda ake siyarwa a matsayin bayi suke ji ba sai a
wannan lokacin. Ai kuwa nan take Armad yai rantsuwa ya
ƙara rantsewa cewa sai yaga bayan dukkan sarakunan
Jinzidal da dukkan Ururu waɗanda suka kafa harkar
cinikin bayi. Sai yaga ranar da zai kawo ƙarshen komai.
Sai ya hana dukkan cinikin bayi kafin ya daina numfashi.
A wannan lokaci Armad yaji jinin jikinsa ya fara balbalin
wuta yana soyuwa saboda baƙin cikin rashin ƙarfin
Izzarsa. Domin babu wanda Armad yafi zarga a
abubuwan dake faruwa dashi irin kansa. Armad yana
zargin kansa da rashin ƙarfin Izza, da rashin tsayawa ya
koyi abubuwa a lokacinda yayarsa taso ta koya masa.
Amma yanzu komai yazo ƙarshe. Yana da ragowar wata
ɗaya daya rage masa ya nemo Tarifil-fakta sannan kuma
ya fara shirye-shiryen ruguza dukkan sarakunan Jinzidal
da Ururu. A taƙaice dai a wannan rana ta sha tara ga
watan goma na shekarar 1853 bayan Amri Armad yai
alƙawarin yin faɗa da dukkan duniya ya kawo sabon tsari
wanda bai yadda da cinikin bayi ba.
Ai kuwa abin alajabi, tamkar wani sirri acikin jinin Armad
dama jira yake Armad ɗin yayi wannan rantsuwa, sai nan
take ya fara juyawa. Armad yaji idanunsa suna zafi
tamkar ana tsire su. Gashin jikinsa tamkar anan tsitstsige
geshi saboda zafi. Bada ban bashi da ƙarfin yin ihu bama
da tuni ya kwalla ƙara. Nan take ya fara zubarda gumi ta
ko'ina. Idan ka ganshi fassarar kawai da zakai ita ce yana
tsoron mai zaije ya tarar a wajen waɗanda suka siyeshi.
Sai dai kuma abinda shi Armad da dukkan ƴan kallo basu
sani ba shi ne a wannan lokaci ƙarfin da Armad ya gada
na zuri'ar Wilbafos a jininsa yake farkawa.
____
Ƙarfin Izzar jarumin jarumai Armad Wilbafos zai
bayyana a babi na gaba, ko wacce irin Izza ce?
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 55: Sabon Farin wata
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
_____
***
Idan ka/kin manta abubuwan da suka faru a babi na
takwas zuwa na sha biyu to ya kamata ku duba, domin
kuwa abubuwan zasu fara dawowa yanzu.
***
Wata ne daren sha bakwai a sararin samaniya, hasken
wannan wata ya cika ko'ina a sararin samaniya da sauran
ƙasashen duniyar ƙasa bakwai.
Kwatsam sai aka wayi gari hasken wannan wata ya fara
dusashewa yana duhu. Idanun duk wani abu mai rai ya
koma sama da kallo. Ba jimawa dukkan hasken wannan
wata ya ɗauke ɗif tamkar an ɗauke wuta.
Da dama mutane sun fara tunanin zazzaɓin wata ke
faruwa kuma tuni an fara shiga zulumi, malaman addinai
da dama suma sun fara nasu aikin. Kwatsam sai aka ga
wannan wata ya dawo ya fara yin haske, sai dai kuma
hasken nasa ba irin hasken da aka saba gani bane.
Wannan hasken ruwan ƙasa ne mai launin toka.
Ba jimawa mutane gama-gari suka fara shiga tashin
hankali ana raɗe-raɗen cewa masifa ce zata sauka. Amma
tsofaffin ma'abota Izza wanda suka ga jiya suka ga yau
sun san sarai maike faruwa.
A daular sarkin Jinzidal sarki Bihanzin mai
dauwamammen ciwo wani tsohon mutun ne ya farka
daga cikin wani akwatin gawa, yana buɗe idonsa wata
Izza wadda girmanta ya haura shekaru dubu goma ya
cika wannan ɗakin.
Wannan mutun dukkan jikinsa a bushe yake, fatar jikinsa
tayi ɓawo-ɓawo, bashi da maraba da gawa. Amma duk da
haka sai gashi ya buɗe bakinsa yana magana, "Jinin gidan
Wilbafos ya bayyana."
Yana gama magana ya koma ya rufe idonsa ya ci gaba da
bacci. Wannan magana daya faɗa babu inda ta isa sai
kunnen sarki Bihanzin mai dauwamammen sara.
Haka dai irin wannan mutun mai kama da gawa ya ƙara
tashi a daular Denizawa dake ƙarƙashin ƙasa ya kuma
ƙara faɗar irin abinda na farkon ya faɗa.
A can wani sashi kuwa na duniya dake kan wani siririn
tsibiri, wani mutun ne riƙe da AL'ƘURANI mai girma a
hannunsa. Idanun wannan mutun daɗe a rufe kuma
babu wamda zai iya kwatanta shekarunsa a duniya. Yana
buɗe idanunsa saiga irin hasken wannan wata aciki.
Murmushi kawai yayi irin na mutanen Sannan ya ƙara
rufe idanunsa.
Haka ire-iren wannan abubuwan al'ajabi suka ci gaba da
faruwa a dukkan dauloli na faɗin duniya.
Wannan sabon hasken farin wata kuwa ruwan ƙasa ko
ajikinsa, haka ya ci gaba da ƙaruwa yana game duniya.
A tsakiyar wannan ɗakin cinikin bayi kuwa wani saurayi
ne acikin gilashin da ake tallan bayin nan dashi. Saurayin
ya miƙe ya tsaya a tsaye yana kallon dukkan mutanen
dake wajen. Duk wanda ya ganshi zai iya tunanin tsoron
siyarwa ne yake damunsa.
Amma ba jimawa dukkan hasken wannan farin wata mai
ruwan ƙasa da ratsin toka ya fara raguwa a dukkan sassa
na duniya yana curewa a waje ɗaya.
Kan kace meye wannan dukkan hasken ya gama curewa a
waje ɗaya sannan ya fara sakkowa ƙasa a hankali a
hankali har saida yazo dai-dai idon wannan yaro dake
cikin wannan gilashi, sannan dukkaninsa ya shige cikin
idon wannan saurayi.
Wannan saurayi dai ba wani bane illa Armad Wilbafos.
Nan da nan idanunsa suka fara haske suna bada launin
hasken wannan wata wato ruwan ƙasa mai ratsin toka.
Komai da yake faruwa a idon kowa ya faru, saboda haka
a dai-dai wannan lokaci wannan mutumi dake bada
rahoton akan bayin da aka saka acikin gilashin ya fara
karkarwa yana matsawa baya.
Armad ya kalli wannan ankoki dake jikinsa, nan take
dukkan ankokin suka zube ƙasa, sannan dukkanin
ciwukan jikinsa suka warke nan take. Sannan ya ɗaga
idonsa ya kalli jikin wannan gilashi, ai kuwa hasken nan
ruwan ƙasa na dukan gilas ɗin ya tarwatse.
Armad ya bayyana a waje kamar wani ɗan ƙaramin
bajimin aljani. Inda ya haska idonsa akan dukkan
mutanen dake cikin wannan waje, nan take da dama
daga cikinsu suka fara jin karkarwa suna rawar ɗari
tamkar wanda akace mutuwa ce tsaye ke kallonsu. Koda
yake a wannan lokaci Armad bashi banbanci da mutuwar
kanta.
Idanunsa kawai haske suke suna fitarda tsananin azabar
yaƙi da ƙarfin Izza. Armad ya miƙa hannunsa sama, nan
take wata taga ta buɗe akam iska inda ya miƙa hannu ya
zaro takobinsa ta Wilbafos. Abin mamaki sai ga taurari
guda biyar a saman takobin. Armad yai murmushin
girma bayan da yaga adadin taurarin dake kan takobin
kuma ya tuna wanda suke kai a lokacin da yayi faɗa
Ikenga. Lallai Armad ya samu gagarumin canji a jikinsa
wanda keda ban al'ajabi.
Tun daga kan hawa na farko har zuwa na uku kowa yayi
shiru ba'a cewa komai. Ana haka kawai sai aka ga Armad
ya ɗaga takobinsa ya nufi kan waɗannan bayin da aka
riga aka siyar. Ko ba'a tambaya ba kasan nufin Armad ya
kwance su ya kuma ƴantar dasu a gaban dukkan duniya.
Wanda zarar Armad ya aiwatar da wannan abu, to dai-dai
yake da fito na fito da dukkan ƙabilar Ururu da kuma
Sarakunan Jinzidal biyar. Kuma lallai a wannan lokaci
zaka ga ma'abota baƙaƙen ido sun fara sauka daga ƙasa
ta farko domin kama Armad. Lallai hatta sarakunan
manyan gidajen Ururu goma sai sun sauka idan Armad
ya aikata wannan abu. Domin wannan shi ake kira da fito
na fito da Ururu.
Sai dai kuma amma a wannan lokaci ne kwatsam gimbiya
Nostalgia ta bayyana a gaban Armad tana mai murmushi.
Babi shiri Armad ya tsaya, kuma duk da ɓacin ran da yake
ciki zuciyarsa bata fasa tunano masa wannan kyakkyawar
gimbiya ba da suka haɗu a shekarun baya ba. Gimbiyar
da ta ceto rayuwarsa sau adadi da dama tun bai ma
fuskanci yadda yanayin duniya ke gudana ba.
Armad yana tuno sanda ta hanashi faɗawa rami da kuma
hawayenta guda ɗaya daya faɗa idonsa.
Sannan kuma lallai Armad yana sane da wannan sirri
daya jiyo musu acikin wannan allon tsafi, sirrin dazai
rikita duniya baki ɗaya.
Armad bai manta da fasahar Izza ta musamman, wadda
ake iya duba cikin kwakwalwar mutun aga mai yake
tunani ba wadda wannan gimbiya mai suna Zahra wadda
akewa laƙabi da Nostaljiya take da ita ba.
"N.....nostaljiya? Mai kike anan, babu ruwanki da tsakani
na da wannan mutane da suke so su ringa bautar da bil
adama. Idan kuma kika shiga tsakani na dasu, to lallai zan
manta da duk wani abu daya taɓa faruwa a tsakaninmu
na yaƙe ki, sannan kuma...."
Armad yana magana amma dole ya tsaya cak, badan
komai ba sai dan saboda kwalla daya gani acikin idanun
Nostaljiya bayan da tayi arba da kayan jikinsa a yayyage,
kuma duk sunyi faca-faca da jini.
Armad ya buɗe baƙi zai ci gaba da magana, amma a
wannan lokaci yaji hayaniyar ƴan kallon dake wajen suna
cewa, "Kai.... Wai wannan yaron ba shi ne Armad Djinn
ba daya fafata a gasar Jinzidal ba? Lallai shi ne, ya akai da
bamu gane shi ba? Wai ya akai ma za'a siyar dashi a
matsayin bawa? Mai yake faruwa?"
To ga dukkan alamu an cire dukkan hijabin dake hana
wannan mutane gane Armad, kuma lallai a wannan lokaci
kowa ya gane wanene Armad.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 56 & 57: Nostojiya nara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
_______
Nan take Nostalgiya ta juya ta kalli waɗannan ƴan kallo
da suka zo wannan cinikin bayi, ai kuwa daga cikin
girman Izzar ta sai ga SANYIN BABBAN SIHIRI nan ya fara
sauka acikin wannan waje a yanayinsa na ƙanƙara ruwan
toka. A wannan lokaci ya fara bin jikin dukkan mutanen
dake wajen, kuma duk wanda ka kalla babu abinda zaka
gani sai ƙanƙara ruwan toka nannaɗe a jikinsa.
Nostalgiya tai ƙaraji na ɓacin rai, ta ɗaga takobinta sama
takai sara kan iska. Ai kuwa saiga wasu aljanu nan guda
biyu sun bayyana suna ƙoƙarin kare wannan sara mai
ɗauke da Izzar sanyin babban sihiri.
Abu ne sananne idan ka ɗauke Farar-laya babu abinda
aljanu ke tsoro irin Sanyin babban sihiri. Nostalgiya tasan
haka kuma ga dukkan alamu tayi niyyar halaka wannan
aljanu ne baki ɗaya.
Inda tayi tsalle sama ta dira akan ruwan cikin wannan
aljanu da ƙafafunta ma'abota Izza.
Yau waye ya isa ya jada ƴar gidan Bihanzin mai
Dauwamammen Sara.
A wani irin yanayi mai kama da hauka da tsananin ɓacin
rai Nostaljiya ta hau saran wannan aljanu baji ba gani.
Jinin aljanun yayi sama, kan kace meye wannan yayi faca-
faca da ko'ina. Ko dama ɗaya bata bawa wannan aljanu
ba na kare kansu ba kafin ta aikasu lahira.
Ta juyo da idanunta ga wannan bayi da aka riga aka siyar,
idanunta na sauka akansu nan take duk ankokin dake
ɗaure dasu suka zube a ƙas.
Armad na gefe yana kallon tsananan ɓacin rai wanda har
yaso yaɗan ɗara nasa. Abu na gaba daya ji shi ne hannun
Nostaljiya ta jashi sun tashi sama inda suka fice daga
cikin wannan waje suka tashi sama.
A can cikin wajen hawa na uku kuwa manyan jarumai ne
masu wakiltar sarakunan Jinzidal. Daga ɓangaren dama
jaruman sarki Rafiya ne guda uku. Dukkaninsu Izzarsu ta
haura shekaru ɗubu biyar. Kai ɗaya daga cikinsu ma shi
ne wanda muka gani a wannan Jinzidal wadda Armad ya
taka rawar gani, wato Asifu wanda akewa laƙabi da
Ruwan Bala'i.
Asifun ne ya fara magana yana cewa, "Wannan yarinya
bata da hankali. Bansan maike faruwa ba, amma ga
dukkan alamu sa'a tana tare damu domin kuwa akwai
alamun soyayya a idanun wannan yarinya, kuma wannan
soyayyar dake idonta ta rufe mata ido ta aikata abinda zai
taimake mu mu ruguza daular babanta baki ɗaya. Saboda
haka baza mu bita ba, kuma baza muyi mata komai ba
anan. Mu barta ta gudu dashi wannan yaron. Kaga da
haka zamu samu damar cin galaba akan tsohon ɗan
adawar mu wato babanta Bihanzin. Tunda kunga duk
laifin daya faru anan kawai saimu ɗora shi akan babanta
kuma rubuta a rubuce mu aikewa da Ururu."
Asifu na zuwa nan a zancensa yai dariya mai cike da farin
cikin, sannan ya ƙara yin ƙasa-ƙasa da muryarsa domin
kada sauran mutanen dake wajen suji, "Ban taɓa tunani
babbar dama kamar wannan zata samu ba a garemu.
Lallai wannan babban labari ne muyi maza mu tashi mu
gabatar dashi izuwa sarki Rafiya."
Sauran manyan ma'abota Izzar guda biyu dake tare dashi
suka girgiza kai alamun amincewa.
_______
Babu inda gimbiya Nostalgiya ta sauke Armad sai cikin
wani sihirtaccen kogo. Wannan kogo dai waje ne na
musamman wanda ke cikin daular babanta sarki
Bihanzin, kuma babu wanda yasan dashi inba ita. A sau
da dama idan tana so ta nutsu ta tuno babarta wadda ta
mutu wannan kogo take zuwa tayi kwana da kwanaki
tana hutawa tana kewar mahaifiyar tata.
Acikin kogon dai akwai ƙorama mai bada sanyi mai ciƙe
da ni'ima da annushuwa. Ga kujeru da shimfiɗu na
alfarma, ga kuma kayan ci da sha duk na sarakuna wanda
Armad ma bai taɓa yin tsinkaye da suba.
Tana ajiye Armad ta ɗakko wata sabuwar rigarta ta
wadda akaiwa ado da dinare ta fara goggoge masa datti
da jinin dake jikinsa. Har a wannan lokaci ta kasa ɗago kai
ta dubi Armad saboda hawaye da tausayin dake idanunta.
Armad ɗin shima ya kasa cewa komai, abu ɗaya dai daya
sani shi ne abinda ta aikata a wajen cinikin bayin can lallai
saiya jawo wa babanta babbar matsala. Saboda haka bai
san mai zai fara ce mata ba. Tunda dai saboda shi take
duk wannan abun, kuma koma mai ya same ta shi ne zai
zamo shila.
Amma abu guda ɗaya daya kasa ganewa shi ne mai yasa
take wannan abubuwa. Wai anya kuwa tana cikin
hankalinta kuwa? Sai dai kuma Armad ya tuna ba wannan
ne lokaci na farko ba data fara sadaukar da rayuwarta ba
domin ta ceto shi. Yana tunano lokacinda zai faɗa
wannan rami kuma wannan dordor ya so ya halaka ta,
amma taƙi sakarsa.
Can bayan wani lokaci Armad ya riƙe hannunta ya tsayar
da ita, sannan ya ɗago da kanta domin yaga maike
faruwa acikin idanunta. Amma bisa mamaki sai kurum
Armad ya ƙara arba da irin sak abinda ya taɓa ji a
shekarun baya, wato yaji tamkar ya santa a wani zamani
mai tsaho daya gabata. Nan da nan ya cika ta yana haki.
Yau dai koma mai ake ciki sai yaji amsar dukkan
tambayar daya daɗe yana so yayi mata.
Nostalgiya taja dogon numfashi sannan ta goge fuskarta
da hankici. Ta miƙe daga inda take tana murmushi
sannan ta fara da cewa, "Ka taɓa gani na babu hijabi?"
Tambaya ce amma ga dukkan alamu ba amsa take nema
a wajen Armad ba, domin kuwa tasan cewa bai taɓa ba.
Shima Armad ɗin yasan haka, kuma nan take ya fara
ƙinƙina a lokacinda yaga kamar tana nufin cire rigar dake
jikinta. Muryarsa na rawa yana cewa, "Ehm....
Tsaya.....tsaya..... Ba saikin cire komai ba, na taɓa....."
Kawai Armad yaji Nostaljiya tasa hannu ta doke shi aka.
Nan da nan ya haɗe gira, "Laifin me kuma nayi miki
harda duka?"
Nostalgiya ta ɓata rai matuƙa tana mai cewa, "Mai ka
ɗauke ni, a gaban naka zan cire kaya. Kawai kai mana
shiru kaga mai ake yi mana, a'a!"
Bayan data gama magana saita durƙusa a gabansa tana
mai murmushi tana lallashinsa, "Kayi haƙuri na dake, ba
zafi ko?"
Armad yana rasa mai zaice, tambayar kansa kawai yake,
towai mai take nufi ne? Waishin mai ake ciki nema?
Ai kuwa ba jimawa Armad yaga dukkan wannan kogo ya
cika da wani irin haske mai matuƙar ƙayatarwa. Da farko
Armad yayi tunanin wata fitilar aka kunna, amma a
lokacin ne Nostaljiya ta kashe fitilar dake ɗakin amma
hasken kawai ƙara ƙaruwa yake. Ba jimawa Armad ya
gano cewa wannan haske daga jikinta yake fitowa. Fatar
ta gaba ki ɗaya ta juye izuwa wani abin kyalkyali da
walƙiya mai tsananin kyawu. Armad ya fara tunowa da
labarai daya karanta na tatsuniya akan wata wadda ake
kira da Lasina Naitingele wadda aka ce tafi kowa kyau a
duniya. Nan take Armad ya gano cewa wadda take
gabansa lallai ta ma fita kyau. Idanun Nostaljiya na
kaɗawa da tsananin ƙauna da tausayin Armad. Nan da
nan Armad yaji jikinsa ya mutu murus.
Dama Nostaljiya tama ɗan fishi tsaho saboda haka koda
ta jashi ya tashi ya tsaya a gefenta ya kuma kalli dattin
dake jikinsa sai yai matuƙar raina kansa. Lallai Armad ya
tabbatar babu wata mai kyawun wannan yarinya a
duniya. Fuskarta madaidaiciya ce kuma Armad bazai iya
siffanta ta taba sai dai kawai yasan cewa wannan fuska ta
ƙunshi duk wani abu da kyau zai iya bayarwa. Jikinta ya
ingantu matuƙa sama da na duk wata budurwa da Armad
ya taɓa gani, ba shiri Armad ya fara kamuwa da surar
wannan mace dake gefensa.
Nostaljiya ta fuskanci hakan sabida haka kawai tayi
murmushi ta kuma ja hannun Armad izuwa ƙarshen
wannan kogo. Suna zuwa ƙarshe suka ga wata ƴar
ƙaramar ƙofa. Suna shiga ƙofar suka tsinci kansu a wani
ƙaton lambu mai bada yanayin ni'ima da annushuwa.
Armad ya fahimci cewa ashe wannan kogo a tsakiyar
lambu yake.
A wannan lokaci ne Nostaljiya Sisiyu da Armad Wilbafos
sukai tafiya a matsayin saurayi da budurwa a karo na
farko a tarihi.
Nostaljiya ce ta fara magana, "Bari na fara, nasan kana da
tambayoyi da yawa, amma idan na gama wataƙila ba sai
kace komai ba.
"Kaga dai mahaifina Bihanzin ya daɗe yana neman
hanyar da zai ruguza wannan Rukunai na Jinzidal guda
biyu. Amma hakan ba abu ne mai yiwuwa ba indai baka
da ƙarfin Izzar da zaka iya cin galaba akan sauran
sarakunan Jinzidal biyar ba. Hakan ne ma yasa zaka ga
ma'abota Izza wanda suke ƙin jinin cinikin bayin amma
dole sai dai suyi biyayya saboda al'amarin na girman Izza
ne da kuma girman runduna. Babu wanda ya isa ya fito
shi shi kaɗai ya ce yau zaiyi fito na fito da dukkan manyan
ma'abota Izzan dake kare cinikin bayi. Hatta mahaifina
wanda ɗaya ne daga cikin sarakunan Jinzidal bashi da
wannan ƙarfi. Kai hasalima bari kaji, na taɓa tambayar
mahaifina akan irin ƙarfin Sarakunan Jinzidal yake cemin
hatta daular Ururu da kanta baza ta iya yin fito na fito da
dukkan sarakunan Jinzidal ba, koda kuwa zasu yi nasara
to kuwa zasu rasa sama da rabin rundunarsu da
mutanensu wanda kuma Ururu baza su yadda da hakan
ba. Hakan nema yasa zaka ga Ururu na bawa wannan
sarakuna na Jinzidal ƙima da mutunci sosai da sosai.
"Mahaifina yayi bincike ya gano cewa idan ka ɗauke
Tarifil-fakta wanda har yanzu ba'a san waye ba ko kuma a
ina yake ba, akwai wani mutun ɗaya wanda ya taɓa yin
faɗa da Ururu kuma yaci nasara. Wannan mutun kuwa
shi ne Bayajidda, kuma shi ne wanda kaji muryarsa a
cikin wannan gari dana ceto ka daga ciki.
"To a binciken mahaifina ya gano cewa Bayajidda ya bar
wani allon sihiri. Tun daga ranar da mahaifin nawa ya
gano wannan allo yake ta bincike a kansa har zuwa
wannan rana da muke magana. Wanda idan kai lissafi
shekaru dubu ɗari da uku kenan, kaga shekaru tamanin
da biyar kenan kafin a haifeni.
"Mahaifna ya bani labarin yadda ya gano sirrin wannan
allo amma a yanzu bamu da lokacin da zan baka wannan
labari domin kuwa ba ƙaramin dogon labari bane. Amma
dai kai sani cewa wannan allo shi ne dai wannan allo
wanda muka baka kaji mana muryar Bayajidda aciki
shekaru da suka gabata. Mahaifina ya gano cewa sirrin
Izzar da yake buƙata ya rusa Jinzidal dashi yana cikin
wannan allo, kuma kaida kaji wannan murya da
kunnenka zaka fi kowa gane mai nake nufi da wannan
Izza. Dalilin da yasa kaga mun neme ka domin kaji mana
wannan murya ta dake cikin wannan allo shi ne babu
wanda ya isa yaji wannan murya sai wanda yaji muryar
Bayajidda a cikin wannan gari wanda kuma dani da ƴan
uwana duk mun kasa, hasalima ni kaɗai nake iya shiga
garin amma nima ɗin ban taɓa jin komai ba. Ranar dana
fara ganinka kwance cikin jini acikin wannan gari nasan
cewa ƙaddararka da tamu ta riga ta haɗu a wannan
duniya kuma babu wanda zai iya rabata domin kuwa kai
kaɗai zaka iya jiyo mana sirrin wannan allo wanda shi
kaɗai muke buƙata mu cimma burinmu.
"Da farko da na ganka acikin garin nan jikinka yana ci da
wuta kawai na ceto kane sabida ina so kazo ka fassara
mana wannan allo. Amma daga baya dana karanta
tunaninka naga kana so ka taimaki mahaifiyarka ne sai
naji tausayin ka ya kamani. Nakan so duk wanda naga
yana son ya taimaki iyayensa.
"Amma a lokaci na farko dana taɓa jikinka sai naji tamkar
na taɓa ganinka a wani zamani mai tsaho daya gabata,
harma inajin cewa dani da kai mun taɓa soyayya wadda
aka rubuta a tarihi. Da nayi zaton ni kaɗai nake jin hakan
idan na taɓa jikin naka, amma sai na gano cewa kaima
kana jin irin abinda nake ji. Bansan yadda abubuwan
suka ci gaba da faruwa ba a cikin zuciya ta ba, amma tun
daga wannan rana na kasa daina tunaninka. Na tambayi
mahaifina ko irin hakan zai iya faruwa a gaske, amma
yace min bai taɓa samun labari ba a tarihi. Saboda haka
sai naci gaba da bincike.
"Haka na ci gaba da bincike amma har ila yau ban samu
komai ba.
"Amma daga baya nayi alƙawarin zan taimakeka ka
samarwa mahifiyarka lafiya koda kuwa zan rasa raina.
"Kayi sani cewa yanzu naga ka farkar da Izza mai ƙarfi
acikin jininka, amma kana da buƙatar lokaci kaje ka sami
horo ka gane yadda zaka sarrafa ta. Kuma idan ka ɗakko
faɗa da Ururu yanzu baza ka sami wannan damar lokaci
ba. Saboda haka nema na hanaka aiwatar da abinda kaso
ka aiwatar a baya a wajen cinikin bayin can. Ni kuwa kaga
ina da mahaifina dazai kare ni. Kuma kaima kasan saƙon
da muka karɓa daga wannan allo, wanda kuma sauran
ƙiris mu kammala haɗa wannan Izza. Zarar kuwa muka
gama to babu wani Sarkin Jinzidal da zamu ji tsoro.
"Armad.... " Nostaljiya taja hannunsa suka tsaya a gaban
wata bishiyar giginya sannan ta matsa kusa da jikinsa
tana murmushi, "Ina sonka Armad. Karɓi wannan," Ta
kama hannun Armad ta saka masa wani zobe a jiki, "Ba
lalle mu ƙara haɗuwa ba a wannan duniyar. Amma
wannan zoben zaisa ka ringa tunawa akwai wata data
taɓa sonka wai ita Nostaljiya. Ba jimawa mahaifina zaizo
nan, kuma bazan so ku haɗu ba. Sabida haka ka shiga
wannan ƙofa zata maida kai ƙasa ta uku. Nayi bincike na
gano akwai wani sharri a tattare da wannan ɗan duba
Babara, kaje kaga halin da mahaifiyar ka take ciki kafin ka
ci gaba da neman wani Tarifil fakta wanda babu wanda
yasan taƙamaimai inda yake. Idan kana so kaje kayi horo
a shashin Ikwatora to akwai ruhi na a jikin wannan zoben
zai nuna maka hanya. Akwai ajiyar abinci da abinci da
shekarun Izza ɗari biyar aciki da mahaifiya ta barmin a
lokacin da zata mutu. Idan kana so zaka iya amfani dasu."
Ga dukkan alamu Noltajiya bata so taji amsar da Armad
zai bata a yayin ta buɗe wata ƙofa ta tsafi ta tura Armad
ciki ta rufe. Armad yana shiga ya waiwayo da niyyar yayi
mata magana amma sai kawai yaji wani ƙarfin Izza na
musamman yana zuƙe shi ciki kuma bashi da damar
magana.
Abu na ƙarshe da Armad ya gani shi ne kwalla guda ɗaya
daga kowanne idon Nostalgiya na fitowa. Sannan kuma
daga bayanta yaga wani mutun ya bayyana wanda
ganinsa ma kaɗai yasa Armad yaji ruhinsa yana neman
fashewa ya tarwatse. Ba komai ya jawo hakan ba illa Izzar
wannan mutumi. Armad baya jira a gaya masa cewa
wannan mutun shi ne Bihanzin mai dauwamammen sara
kuma lallai ransa a ɓace yake matuƙa.
Armad yaso a ransa ya fito ya tsaya a gaban wannan
mutumi duk wani abu da zaiyi wa Nostaljiya yayi masa,
idan ma kashe shi zaiyi yayi, amma dai kada ya sake ya
taɓa Nostajiya, amma ina kafin yayi wani motsi wannan
ƙofa ta ɓace dashi.
____
Sunan Nostaljiya zaku ga ya canja da ina saka mata
Nostalgiya, sorry mistake ne saboda da english ina rubuta
shi da Nostalgia so saina manta cewa saina juya 'G' ta
koma 'J'
Tirifil fakta ma zai koma Tarifil-Fakta (shima Triple Factor
yake da english)
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 58: Sabuwar Izza
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
Bayanda Armad ya shiga wannan ƙofa sai yaji wata irin
Izza mai

Please Login or Register in order to submit comment