Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙarfin gaske ta zuƙe shi ciki. Idanun sa suka rufe
saboda ƙarfin iskar da yaji.
Ba jimawa Armad ya buɗe idanunsa inda ya tsinci kansa a
fili fetal babu kowa sai shi kaɗai.
Ya duba hagu da dama amma babu wani mahaluƙi sai
ƙasaitaccen daji da manyan bishiyu. Armad yai ajiyar
zuciya inda ya nemi waje ya zauna ya fara tunano
abubuwan da suka faru dashi. Domin kuwa abubuwan
sun faru da sauri ta yadda har izuwa wannan lokaci bai
samu damar zama ya hakaito suba.
Ya tuno da watannin da yayi yana shan azaba a hannun
wannan aljanu guda biyu. Ya tuno da yadda ya rantse
saiya ɗauki fansa akansu amma sai gashi acikin daƙiƙa
kaɗan Nostaljiya ta gama dasu. Ya tuno da maganar data
gaya masa akan sarkin duba Babara dama sauran
maganganu da dama data faɗa akan wannan allo da
Bayajidda ya bari dama sauran sirrika data gaya masa.
Ya tuno da kalmar data gaya masa cewa tana son sa. A
dai-dai wannan lokaci Armad ya tsaya yai duba izuwa
wannan zobe data bashi. Yana murza zoben, zoben yana
walƙiya tamkar ita mai zoben. Armad ya kula cewa da
wani irin dinare na musamman akayi wannan zobe
tayadda jikinsa har wani ƙanshi yake irin na musamman.
Armad yaro ne amma duk da haka bazai rasa sanin
ma'anar kalmar so ba, kuma lallai yasan cewa abu ne mai
matuƙar wahala mace ta fara gaya maka hakan, amma
gashi Nostajiya ta ajiye kunya ta kuma gaya masa. Lallai
ya amince acikin ransa cewa Nostaljiya da gaske mai
ƙaunarsa ce da gaskiya. Amma babban abinda ya ɗaga
masa hankali shi ne maganar data faɗa cewa ba lallai su
ƙara haɗuwa ba. Abin ya tsaya masa a rai kuma ya kasa
mantawa. Amma koma dai menene Armad ya yanke
shawara cewa da kansa zai nemi Nostaljiya a duk lokacin
daya samarwa mahaifiyarsa lafiya.
*N.....nusi?* A dai-dai wannan lokaci ne Armad ya tuno
cewa tun bayan lokacin da hankalinsa ya gushe a tsakiyar
fafatawarsu da Ikenga da Uznu Ururu bai ƙara ganin Nusi
ba. Hankalinsa yai matuƙar tashi domin kuwa yasan cewa
shi tazo taimako a yayin wannan gasa. Saboda haka koma
mai ya same ta shi ne sila.
Hankalinsa ya ƙara tashi yayin da ya tuno cewa ba
wannan ne karo na farko ba da Nusi tai ƙoƙarin sadaukar
da kanta ta taimake shi ba. Nan take Armad ya miƙe. A
wannan lokaci yasan lallai zama bai same shi ba.
Abu na farko da Armad ya fara yi shi ne duba taskar
Izzarsa domin ganin sabuwar Izzar daya samu. Idanunsa
suka gane masa abubuwa guda uku: shekaru dubu ɗaya,
wani ɗan ƙaramin allo, sannan kuma da wani mutun-
mutumi mai kama da Armad amma sai dai idanunsa
ruwan ƙasa ne masu launin toka.
Armad ya zauna ya lankwashe ƙafafunsa domin tayarda
wannan abubuwa dake cikin ruhinsa. Ya karanta
ɗalasiman da ake buƙata a ransa sannan ya kira wannan
Izza ta shekaru dubu. Nan take yaji wannan Izza ta shiga
jikinsa da wani irin ƙarfi wanda bai taɓa jinsa ba. Armad
ya riga yasan cewa duk da cewa yawan shekarun Izza
nada muhimmanci amma bayan yawa akwai inganci.
Wato tayadda zaka samu cewa wani yana da shekaru
wanda basu kai naka yawa ba amma kuma yafi ka ƙarfin
Izza. A wannan lokaci Armad yana ji a jikansa cewa hatta
ƙasa baza ta iya ɗaukansa. Wannan shekaru dubu na Izza
suka shiga jikinsa suka haɗe da ruhinsa. Ya zama su suma
suka zama shi. Armad yaji gashin jikinsa ya fara zafi,
zuciƴarsa ta fara bugawa da ƙarfi kamar zata fito. Kafin
yai wani abu wata kumfa mai zafi ta fara fita daga fatarsa
tamkar ana wanke wata cuta daga jikinsa. Kayan jikinsa
suka jiƙe sharkaf da datti da wannan kumfa mai haɗe da
gumi. Haka ya kasance a wannan hali tsahon sa'a ɗaya
kafin daga bisani wannan kumfa ta daina fita. Armad ya
miƙe tsaye ya kalli jikinsa yaga hatta yanayin fasalin sa ya
canja. Fatarsa kaɗai tana bada wani alamun ƙarfin Izza
wanda shi kaɗai zai iya tarwatsa abokan gaba. A wannan
lokaci ya gane cewa wannan kumfa shekarun Izzarsa ne
guda hamsin da ɗaya aka tarwatsa su aka watso su waje
domin baza su iya haɗa kafaɗa da wannan sabuwar Izza
ta gidan Wilbafos.
Shi kansa yasan cewa yana jin wani irin ƙarfi wanda bai
taɓa tsammanin ɗan adam zai iya jinsa ba a rayuwarsa.
Yai duba izuwa wannan mutun-mutumi dake cikin
ruhinsa ya kira shi da ƙarfin Izzarsa. Nan take wannan
mutun-mutumi ya taho ya shige jikin Armad. Haka na
faruwa idanun Armad suka juye izuwa ruwan ƙasa masu
alamun toka. Wannan idanu na bayyana Armad yaji
ƙarfin Izzarsa na walƙiya ya dawo jikinsa duk da kuwa
babu aljani a jikinsa.
Armad yai kira ga wannan allo inda shima ya gabato a
gabansa. Ya karanta ɗalasiman dake kan wannan allo a
nutse. Yana gamawa yaga takobinsa ta Wilbafos ta
bayyana, amma a kanta maimakon taurari biyar yanzu
sun koma bakwai. Sannan kuma ƙarfin Nauyi dake cikin
wannan takobin ya wuce hatta shi kansa yadda Armad zai
iya misaltawa.
Murmushi irin na Izza kawai yayi sannan ya juya ya nufi
hanya da niyyar samun kogi domin ya wanke jikinsa ya
kuma nufi doron ƙasa ta uku. A dai-dai wannan lokaci
Armad ya gane cewa ai Babara bai ma isa ya sashi aiki ba.
Ya kuma yanke shawara zai koma izuwa Babara ya
tursasa masa yayi wa mahaifiyarsa magani dole ko yana
so ko baya so.
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 59 & 60: Ubbaru
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
______
Armad ya gama wanka, amma babbar matsalarsa kayan
sawa. Rigar dake jikinsa har yanzu a yayyage take. Lallai
bai kamata mutun mai ƙarfin Izza irinsa ya ringa yawo da
ita ba.
Yana zaune a gefen ƙoramar da yai wanka yana lissafin
hanyar da zaibi ya gane a wane doron ƙasa yake sai
hankalinsa yakai ga zoben dake hannunsa. Armad yai
duba izuwa zoben, wanda ba wani bane illa wanda
Nostaljiya ta bashi.
Yana ayyanawa a ransa yaya zaiyi amfani da wannan zobe
sai ƙofa ta bayyana a saman zoben ta kuma fara girma a
hankali a hankali har saida takai yadda Armad zai iya
shiga cikinta. Armad baya iya hango komai aciki sai haske
saboda haka ya fara tunanin ya shiga ko karya shiga.
Daga ƙarshe dai ya yanke shawarar cewa Nostaljiya baza
tayi abinda zata cuceshi ba, saboda haka ya miƙe ya shiga
cikin wannan ƙofa. Yana shiga ƙofar ta rufe.
Armad ya tsinci kansa a wata duniya ta musamman.
Komai acikin wannan duniƴar kyalkyali yake da haske. Ga
wasu ƙofofi nan guda biyu a gabansa. A saman ɗaya ansa
Armad a saman ɗaya kuma ansa Nostaljiya. Kowacce
daga cikin ƙofofin a buɗe take amma bisa mamaki
Armad baya iya hango abinda ke ciki. Idan yai duba izuwa
ciki babu abinda yake hangowa sai haske.
Armad ya yanke shawara ya shiga ƙofar da aka sa
sunansa a jiki. Inda ya tafi gadan-gadan ya tura ƙofar ta
ƙarasa buɗewa sannan ya faɗa ciki. Yana shiga ya tsinci
kansa a wani ɗaki mai cike da kantoci sama da goma.
Kowacce kanta na ɗauke da kaya na musamman a kanta.
Kanta ta farko da Armad ya fara gani itace ta kayan sawa.
Riguna irin na alfarma wanda za'a iya sawa a gari kuma
za'a iya fita filin daga dasu kala-kala. Ƙanshi ne kawai ke
tashi daga wannan kaya wanda Armad bai taɓa ganin mai
kyansu ba.
A ɗaya ɓangare kuma akwai takubba, masu, kulke dama
sauran kayan yaƙi na musamman. Sannan kuma a wani
ɓangaren kuma ga kwalabe na magani kala-kala. A wani
ɓangaren kuma ga kayan ci da sha na marmari irin na
musamman.
Wani abu guda ɗaya daya bawa Armad mamaki shi ne
wani ingarman doki wanda tsayinsa yakai zira'i da dama.
Yana tsaye a ɗaure baya ko motsi, ba kuma alamun
abinci ko abin sha a tattare dashi. Lallai kana ganinsa
abinda zaizo kanka shi ne wannan dokin na aljanu ne.
Koda ganin wannan kaya da wannan doki na musamman
babu abinda yazo zuciyar Armad sai cewa Nostaljiya ta
daɗe tana so ta taimakeshi ta bashi wannan zobe, domin
lallai wannan shiri bana dare ɗaya bane.
Armad yai ajiyar zuciya, shidai baya tunano lokacin da
yayi tunanin Nostaljiya tun bayan sanda suka rabu a
shekarun baya amma ga dukkan alamu abin ba haka yake
ba a wajenta. Kuma lallai irin wannan halacci da tayi ya
shiga zuciyar Armad. Abinda kawai zai hanashi komawa
gareta shi ne lashin lafiyar mahaifiyarsa da kuma Nusi.
Domin tuni Armad ya yanke shawara saiya koma daular
denizawa domin gano inda Nusi take.
Armad ya zaɓa daga cikin kayayyakin ya kuma canja
kaya, ya kuma ɗebi kayan itace domin ya cika cikinsa.
Sannan ya nufi wannan doki.
Koda isarsa sai dokin ya durƙusa ba tare da gardama ba,
inda Armad ya hau kansa a nutse. Hakan na faruwa
Armad yaji tamkar yana jin mai wannan doki yake tunani
kuma tamkar zai iya magana da dokin. Armad baiyi ƙasa
a gwiwa ba wajen tambayar dokin sunansa. Abin mamaki
wannan doki ya amsawa Armad ba tare da ya buɗe
bakinsa ba. Wato dai a taƙaice da zuciya sukai magana da
ubangidansa, Armad.
"Suna na Ubbaru." Armad yaji muryar dokin tamkar
haniniyar ingarman doki. Da farko saida yaja da baya
cikin tsoro amma ba jimawa ya ware. Sannan ya umarci
dokin daya nufi ƙofa dashi.
Abu kamar wasa dokin ya miƙe ya nufi bakin ƙofa ya fito
yana sassarfa. Inda ya tsaya a bakin ƙofar da aka saka
sunan Nostaljiya akai amma zuciyar Armad ta gaya masa
bai kamata ya shiga wannan ɗaki ba domin kuwa ba
sunansa bane akai. Saboda haka Armad ya umarci
Ubbaru daya juya ya fita daga duniyar wannan zobe.
Armad na bayyana a wajen wannan ƙofa dake saman
zoben, ƙofar ta ɓace baki ɗaya. Daga Armad sai wannan
ƙorama, sai kuma jaka mai cike da tuffa da inubi dake
hannunsa. Rigar jikinsa doguwa ce ƴar shara ce irin ta
mutanda wadda jarumai ke so domin basu dama da take
wajen watayawa su sarrafa takobi. Kalarta shuɗiya ce.
Sannan kamar yadda ya saba a baya Armad ya samo
maɗaurin kai ya kuma ɗaurashi a kansa dai-dai inda yake
sawa a baya ya rufe tambarin Miyurarsa. Sai kuma
Ubbaru wanda fari ne fat mai yawan faɗin kafaɗu da
dogayen ƙafafuwa.
Armad ya ɗakko tuffa ɗaya da inubi ya cilla a bakinsa
sannan ya nufi hanya. Bashi da niyyar tsaya har sai sanda
yaga gari, a nan kuma zai tsaya ya tambayi a wacce doron
ƙasa yake. Sannan ya kara bazama bazai yada zango a
ko'ina ba sai doron ƙasa ta uku.
Ubbaru yai haniniya, sannan ya miƙa dogayen fararen
ƙafafunsa gaba ya nufi hanya yana matsanancin gudu.
Armad ya kula cewa gaba ɗaya gefensa da duniyar dake
kewaye dashi ta ɗauke saboda tsananin gudun da Ubbaru
yake. Babban abin mamakin shi ne ko kaɗan iska bata
damun Armad duk da wannan gudu, sannan kuma yana
iya hango abinda ke can gabansa kafin ya tunkaro shi.
Armad bashi da wata hanyar dazai iya hakaita iyakacin
gudun da Ubbaru yake, amma lallai yasan al'amari ne
babba.
Kimanin sa'a biyar bayan fara wannan tafiya Armad ya
keta a ƙalla dazuka hamsin. Amma babu abinda ya kawo
masa tsaiko domin duk namun dawar dake wajen tamkar
ma basa iya ganin Ubbaru. To a wannan lokaci ne Armad
hango wani ɗan ƙaramin gida dake can gabansa a
tsakiyar daji. Armad ya sanarda Ubbaru ya tsaya idan
yaje wannan gida. Ai kuwa ba jimawa Ubbaru ya isa gidan
inda ya tsaya cak tamkar matacce babu ko tirjiya.
Yana tsayawa Armad yaji muryar mutane acikin wannan
gida. Wani murmushi yazo masa domin kuwa yasan cewa
zai samu labari akan a wacce doron ƙasa yake.
__________________________________
Armad ya tura ƙofar wannan gida wadda dama a buɗe
take ya kuma shiga ciki. Abu na farko daya fara gani shi
ne jerin tebura da mutane zaune akai wasu suna shan
barasa wasu suna cin abinci. Sannan daga can gefe kuma
ga wani ɗan tsoho mai yawan sanƙo yana ɗago masa
hannu yana tambayarsa, "Mai kake so ɗan yaro, abinci ko
barasa?"
Nan take Armad ya gane cewa wannan waje irin gidajen
nan ne na ci da sha na matafiya da ake gina su a hanya.
Kuma ya tuno cewa da dama daga cikin waɗannan gidaje
basu da nisa da gari.
Armad ya dubi wannan ɗan tsoho yana mai cewa, "Ruwa
kawai nake so."
Tsohon ya kyaɗa kai sannan ya nunawa Armad wajen
zama. Ba jimawa aka gabatowa da Armad abinda ya
buƙata. Wata yarinya sanye da doguwar riga samfurin
al'adar doron ƙasa ta uku. Armad na ganin haka yai mata
murmushi sannan bayan ta ajiye ruwan ya tambayeta,
"Ina ne nan?"
Yarinyar tana da ƙaton wawulo daga saman dasashinta
saboda haka data yiwa Armad murmushi saida ya ɗan
buɗe ido cikin mamaki. Yarinyar ta fahimci haka saboda
haka ta ɗan rufe bakinta cikin kunya tana mai cewa,
"Doron ƙasa ta uku kusa da ƙauyen garin Jari"
"Ehmmm...." Armad yaja numfashi cikin mamaki. Duk da
baiyi yawo da yawa yana yaro ba amma yasan cewa
wannan ƙauye data faɗa yana kusa da ƙauyensu, nisan
baifi tafiyar ƴan kwanaki bace. Nan take wani gagarumin
farin ciki ya cika zuciyarsa domin ko ba komai yau zaiga
mahaifiyarsa.
"Yauwa nagode. Nawa ne kuɗin ruwan."
Yarinyar ta kyaɗa kai, "A'a ba saika biya ba. Ruwa ai
kyauta ne."
Armad na niyyar yin magana ya ga an dako ƙofar wannan
gida ta ɓalle, sannan kuma yaji muryar wani bajimin
gardi daga ƙofar, "Kai wannan ko dokin wane ne ya zama
nawa! Idan kuma maishi nada ƙarfi yazo kwata."
Gardin nada shekaru casa'in na Izza sannan kuma a
bayansa akwai girɗa-girɗan mutane wanda duk sunma
fishi girma. Suna tsaye akan Ubbaru suna jira Idan ba
wanda yai magana su kwance shi su tafi.
Dukkan waje yai tsit kamar mutuwa ta gifta, amma
Armad murmushi kawai yayi sannan ya miƙe ya nufi
gurin wannan ƴan fashi. Baiyi ko taku biyar ba yaji an
riƙe hannunsa ana jawo shi baya. Yana waiwayawa yaga
wannan yarinya mai wawulo a bakinta. Yarinyar tana
girgiza masa kai alamun kada ya takale. Tana mai nuna
masa wawulon bakinta alamun dai wannan ƴan fashin
sune suka cire mata haƙoran nata.
Armad na ganin haka tausayin yarinyar ya kamashi
domin kuwa yana da tabbashin cewa wannan tsohon ba
babanta bane. Domin kuwa an saba ganin yara irinta ƴan
shekara goma zuwa ƙasa suna yawo a irin wannan gidaje
neman aiki. Badan komai ba saidan cewa an siyarda
iyayensu a cinikin bayi na Jinzidal. Wasu da dama daga
nan suke lalacewa wasu kuma su shiga duniya. Irin
wannan yara na daga cikin babban dalilin da yasa Armad
ya tsani gasar ta Jinzidal.
"Yaya sunanki?" Armad ya durƙusa ya tambaye ta.
Yarinyar ta amsa a tsorace, "Aisha." Sannan tai ƙasa da
muryarta sosai cikin tsoro ta gayawa Armad wata
magana wanda shi kadai yaji.
Armad naji ya miƙe ya nufi kan waɗannan ƴan fashi.
Babban cikinsu mai Izza casa'in ya dunƙule hannunsa
saiga ƙawanyar wuta ta bayyana akai. Baya ganin Izzar
Armad amma yasan cewa Armad yana da Izza saboda
haka ya fara shiri tun kafin Armad yazo. Na bayansa ma
suka fara dariyar tsokana suna zare takubbansu. Kana
ganinsu kasan sun raina Armad kuma suna tunanin baifi
suyi masa ɗauka ɗaya ba.
Amma dukkanin hakan ya canja a lokacin da Armad ya
bayyana a gabansu. Yana ajiye ƙafarsa sanyin babban
sihiri ya bayyana ya rufe waɗannan ƴan fashi. Idanunsu a
kwale cikin tsananin mamaki suka ƙanƙare a tsaye a inda
suke. Waye zaiyi tunanin samun ma'aboci izzar da zai iya
amfani da sanyin babban sihiri a wannna ƙauye? Armad
ya dubi babban cikin nasu sannnan juya izuwa Aisha ya
tambayeta, "Wannan ne?"
Ta kyaɗa kai cikin tsoro.
Abu na gaba da aka gani shi ne haƙoran wannan ɗan
fashi a ƙas Armad ya zubar dasu.
Armad ya fara magana cikin ƙarfin Izza, "Daga yau
wannan waje yana ƙarƙashin kariya ta. Duk wanda ya
taba shi, to ni ya taba."
Sannan Armad yayi wa Aisha murmushi kafin ya hau kan
dokinsa ya ɓace daga wannan waje ya nufi wajen sarkin
duba Babara.
_____________________________
Babu jimawa Ubbaru yakai cikin wannan daji da Armad
ya haɗu da Babara shekaru da suka gabata. A wannan
waje ne Armad yai bankwana da mahaifiyarsa ya fita
nemo mata magani shekaru da dama da suka wuce. A
wannan waje ne sarkin duba Babara yai masa alƙawarin
indai ya nemo Tarifil fakta to zaiyi maganin cutar dake
damun mahaifiyarsa. A wannan waje ne Armad ya fita
daga ƙasarsa ta haihuwa zuwa duniya yana da Izza
hamsin da ɗaya amma yanzu gashi ya dawo da dubu.
Shin mai Babara ya taka? Ta yaya zasu ƙarke? Domin
Armad yazo ne yayi wa Babara dole! Dole ya bawa
mahaifiyarsa magani. Ko yaƙi ko yaso! Yaya wannan
al'amari zai kasance?
____
Kuyi hakuri da jinkiri, kunsan wani lokaci abubuwa zasu
taso babu yadda za'ai.
A Babi na gaba zamu zo karshen littafin magajin Wilbafos
na daya. Saboda haka duk wanda ya canki yadda tsakanin
Armad da Babara zai kasance to shi zamu nada MAGAJIN
WILBAFOS na shekarar 2018. Sannan kuma ni
marubucin MAGAJIN WILBAFOS zan bashi kyautar
babban kyauta
,
,
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos
Kada ku manta banine na rubuta littafin ba hakanan ba ni
bane na typing ba,
Ni dai kawai na posting makune don ganin yadda littafin
yake da matukar nishadi,
Bayanai na
,
____
suna : Shuraih Usman
____
Matakin izza: 99%
____
Nambar waya: 08170707521
Kowa ya rubuto nashi yayin bayar da amsarsa akan
wanga tambaya na sama
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 61 & 62: Abul babara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
______
Armad yai duba izuwa kwazazzabon rafin dake gabansa
mai yawan duwatsu. Komai na nan dai-dai tamkar yadda
ya rabu dashi a shekarun baya. Yana tuna dai-dai lokacin
da ya ɗakko mahaifiyarsa yazo wannan waje yana neman
sarkin duba Babara. Yau gashi shekaru da dama sun
shuɗe kamar ba'ai ba.
Armad ya sauka daga kan Ubbaru ya mai dashi Cikin
zoben sihirinsa sannan ya ci gaba da nufar cikin wannan
duwatsu yana tunkarar inda yake tunanin zai samu
Babara. A wancan lokaci ya tuna cewa ya samu Babara a
cikin ƴar bukka wadda ke cikin wannan daji to amma
shekaru sunja, bashi da tabbas zai kara samun Babara
acikin irin wannan yanayi daya barshi.
Bai jima da fara tafiya ba yaji motsin halitta a bayansa,
inda ya labe sannan yakai hannunsa kan takobinsa. Ba
jimawa ya gane motsin na takun sahu ne, kuma
ɓangarensa yake yiwowa. Armad ya laɓe a bayan wani
ƙaton dutse domin ya ga waye ke tafe. Ai kuwa ba jimawa
yaga wata budurwa sanye da farar riga doguwa irin ta
ma'aikatan asibiti ta bayyana. A hannunta akwai ɗan tulu
na ruwa, yanayin ta na nuna alamun sauri. Armad ya
haɗe gira cikin mamaki. Bai taɓa tunanin ganin mace irin
ta acikin wannan daji ba. Idan zai iya tunawa da kyau shi
kansa Babara saboda an kore shi daga cikin gari ƴasa ya
tsinci kansa a wannan waje.
Bayan da tai gaba sai Armad ya fara binta a baya. Bai san
inda zata je ba amma koba komai zata iya sanin inda
Babara yake. Ba jimawa suka isa bakin wani ƙaton tanti
wanda Armad bai san dashi ba a lokacin daya ziyarci
Babara. Nan take ya laɓe a bayan wani farin dutse
tayadda zai iya hangen abinda ke faruwa a gaban wannan
tanti. Ana haka wannan budurwa daya biyo ta fito daga
cikin tantin amma tare da wata budurwa ita ma sanye da
kaya irin na ma'aikatan asibiti. A hannunsu suna ɗauke da
wata mata sanye doguwar riga. Nan take sukai shimfiɗa
sannan suka kwantar da wannan mata suka farai mata
fifita.
Kallo ɗaya zakai wa matar da suka kwantar kasan tana
cikin ƙoshin lafiya. Abu ɗaya kacal da zai nuna ba'a cikin
hayyacinta take ba shi ne idanunta, wanda suke a rufe
ruf. Amma fatar ta sheƙi kawai take sannan kuma babu
rama a tattare da ita.
Wata ƙwalla ce mai zafi ta fito daga idanun Armad a
lokacin da yaga wannan mace, domin kuwa ba kowa
bace illa mahaifiyarsa. Ba tare da wani tunani ba Armad
ya fito daga bayan wannan dutse ya nufi inda wannan
mata suke. Koda ganinsa sai suka miƙe suka jada baya.
Amma bai kula dasu ba, kurum yaje ya durƙusa a gaban
mahaifiyarsa yana mai kuka da muradin ina ma zatai
masa magana.
Abu na farko daya fara fuskanta shi ne babu alamun
wuya a tattare da ita. Amma kuma dai kamar ƴadda ya
rabu da ita har yanzu tana cikin suma. Yanzu abinda ya
rage masa shi ne ya tursasawa Babara ya bata magani ta
dole. Saboda haka ya juyo ga waɗannan mata guda biyu.
Amma kafin yayi magana ɗaya daga cikin su ta fara
karkarwa tana cewa, "Ma'aikatan asibiti ne mu, babu
abinda ya kawo mu face mu kula da ita. B......babara ne
ya ɗakko mu."
Armad najin sunan Babara hannunsa yakai kan
takobinsa, "Ina Babaran?"
Amma duk su biyun babu wadda ta iya amsa masa.
Karkarwa kawai suke. Ana cikin wannan hali Armad yaji
muryar Babara kamar yadda yasan ta a shekarun baya da
suka gabata.
"Armad Wilbafos! Barka da dawowa, ina fata ka dawo
min da abinda mukai alƙawari?"
Armad yai duba izuwa ƙofar tantin nan inda wani wada
mai yawan farin gashi ya fito. Wannan wada ba wani
bane illa sarkin duba Abul-Babara. Mutumin da shekarun
da suka gabata yayi wa Armad alƙawari zai samarwa
mahaifiyarsa lafiya zarar ya nemo Tarifil-fakta. Sai dai
kuma gashi Armad ya dawo bayan tsahon lokaci amma
ba tare da Tarifl-fakta ba. Koda yake duk da cewa Babara
bai yiwa mahaifiyarsa tasa magani ba yadda Armad yaga
Babaran ya ɗakko ma'aikatan lafiya suna kula da ita yasa
ya ɗan rage zargi dake cikin ransa. Amma hakan bai hana
Armad zare takobi ba tare da tunkarar Babara.
"Zan baka dama ɗaya tak kayi wa mahaifiya ta magani ko
kuma takobi ta tasha jininka."
Babara yai murmushi gami da girgiza kai, "Idan ka kashe
ni waye zaiyi maka bayanin ciwon dake damun
mahaifiyarka kuma waye zai gaya maka labarin ƴar
uwarka Hidaya. Samu waje ka zauna."
Babara ya tafa hannayensa inda wasu kujeru suka
bayyana. Babara ya zauna a ɗaya amma Armad ya tsaya
da takobinsa a hannu, domin ba komai Babara ya gaya
masa zai yadda ba.
"Hidaya kuma?" Armad ya haɗe gira cikin mamaki. Shi
dai dama yana ji a jikinsa yayar tasa na nan da rai. Amma
da kakansa da babarsa sunƙi gaya masa wani abu akanta.
Babara yayi kyaran murya tare da fara jawabi, "Sama da
shekaru dubu da suka wuce ƙungiyar ƴan-duba ta
duniya ta daɗe tana rikici da jinsi daban-daban na aljanu.
Asalin rigimar aljanu ne suka fara zargin ƴan duba da
keta musu haddi su kuma ƴan duba suna zargin aljanu
dayi musu ƙarya. Rigima ce data fara ƙarama amma daga
baya ta zama hamshaƙiya wadda ta halaka dubban ƴan-
duba da aljanu. Shekaru sittin da huɗu da suka wuce
Hidaya ta shiga tsakani ta raba wannan rigima, lamarinda
ya kawo zaman lafiyar da ake dashi a yanzu. A sakamakon
haka a matsayina na shugaban yan duba nayi alƙawari
zan saka mata da sak irin alkhairin datai mana komai
daren daɗewa.
"A wancan lokaci bazan manta ba Hidaya ta bugi ƙirji
tana cewa bata buƙatar komai daga waje na. Amma sai
gashi ko shekara ɗari ba'ai ba yaƙi ya haɗa da ita a
tsakanin aljanu masu biyayya ga Ururu da kuma sauran
sarakunan aljanu. Yaƙi mai tsananin gaske wanda babu
yadda zatai ta iya barin filin daga duk da kuwa
mahifiyarta bata da lafiya, kuma ƙaninta yana buƙatar
taimako.
"Ciwon dake damun mahaifiyarka ana kiransa da Cutar-
Izza. Ciwo ne wanda ake samu a yayinda ma'aboci Izza
yake ƙoƙarin ƙara yawan Izzarsa. Duk wata hanya da ake
amfani da ita wajen ƙara Izza zata iya jawo wannan cuta
amma bansan taƙamaimai wacce hanya ce ta jawo wa
mahaifiyarka wannan cuta ba. Kai sani cewa wannan
ciwo ciwon ajali ne. Duk wanda ya sameshi ƙarshensa
kabari. Kuma wannan ciwo shi ne yasa zaka ga sama da
kaso casa'in da tara na mutane sun gwammace su
haƙura da izzarsu a iya shekarunta, domin ko yaya aka
samu matsala a lokacin da mutun yake ƙoƙarin ƙara
yawan Izzarsa to lallai ƙarshensa kabari. Abu guda ɗaya
tak dake maganin wannan ciwo shi ne idan mutun ya
karɓi shekarun Izza daga wani. Wato a misali ka ɗiba daga
cikin shekarunka na Izza ka ƙarawa wannan mutumi.
"Kai sani cewa kamar yadda ake haifar ƙabilar Ururu da
baiwar Baƙaƙen idanuwa haka ake haifar iyalan Wilbafos
da baiwa ta musamman. Wannan baiwa ita kaɗai ce
abarda zata iya maganin wannan ciwo."
"Wannan baiwa kuwa ba wata bace illa fasahar dake cikin
idanunku. Idanu ruwan ƙasa masu ratsin toka. Duk
wanda yake da irin wannan idanu yana da wannna baiwa,
kuma iyalan wilbafos su kaɗai keda wannan idanu.
"Da wannan idanu zaku iya bayarda izza, za kuma ku iya
karɓa tamkar yadda ake saka kaya a cire. Wannan ita ce
baiwar ka a matsayinka na ɗan ƙabilar wilbafos. Kayi sani
cewa turaka da nayi ka nemo Tarifil-fakta bashi da alaƙa
da ciwon mahaifiyarka. Sai dai kawai na jefi tsuntsu biyu
ne da tsakuwa ɗaya. Kaga tafiyar ka keda wuya na ɗakko
waɗannan ma'aikata da kake gani na sasu su ringa kula
da mahaifiyarka, ni kuma na tafi duniyar aljanu domin
sanarda Hidaya abinda ke faruwa. Nasan duk duniya
babu wanda zai iya yi mata magani sai ita, domin kuwa
kai baka ma san komai ba acikin alamuran Izza a lokacin.
To amma bansan halin da zan tarar da Hidaya ba,
wataƙila ma bata raye, saboda haka kaima na tura ka
duniya domin kaga yadda duniya take, kayi ƙarfi ka zama
ma'aboci Izza tayadda koda ban samu Hidaya ba kaima
zaka iya taimakon mahaifiyarka. Amma nasan baza ka iya
nemo Tarifil-fakta ba. Kada ka manta hatta Ururu sun
kasa nemo shi.
"Sai da na ɗauki shekaru biyu ina bilayin yadda zan shiga
filin yaƙin da Hidaya ke ciki amma ban samu damar shiga
ba, domin kuwa naji aljanu suna cewa hatta mutuwa tayi
hijira daga wannan fili. Wasu aljanun ma suna cewa shi
yasa yaƙin yaƙi ƙarewa saboda babu mutuwar da zata ci
gaba da ɗaukar rai a wajen. Kai daga ƙarshe dakyar na
samu wani tsohon aljani ya shigar dani filin yaƙin. Amma
muna shiga wannan aljani ya rasa ransa. Nima ALLAH ne
ya taimake ni na tsira dakyar amma duk da haka saida
nayi asarar shekarun Izza ɗari biyar kafin na fito daga
wannan fagen-daga. Tun daga nan nasan cewa ganin
Hidaya ba abu ne mai yiwuwa ba. Kuma lallai babu
wanda ƴa rage dazai ceto mahaifiyarka sai dai kai.
Saboda haka na dawo na aiko maka da saƙon daka gani
na wata bakwai.
"Naso na gaya maka haƙiƙanin mai ake ciki

Please Login or Register in order to submit comment