Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙaton gado ne wanda zai iya
ɗaukan mutun aƙalla hamsin. Armad yai duba izuwa
manyan gilasan da suka kewaye ɗakin inda ya hango wani
ƙasaitaccen lambu a bayan ɗakin. Wata iska mai armashi
na ƙarawa yanayin ni'ima. Nan take Armad ya
tabbatarwa kansa bai taɓa tsintar kansa a waje mai
kyawu da armashi irin wannan ba a rayuwarsa ta duniya.

MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 97: Sammaci
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
**
Nostaljiya ce fara magana. "Ka jira ni anan ina zuwa."
Sannan ta fice cikin sauri, tun yana hangen jar doguwar
rigar data saka har ya daina. Ajiyar zuciya kawai yayi
sannan ya faɗa kan wannan hamshaƙin gado wanda
tunda yake bai taɓa yin arba da kamarsa ba a tsahon
rayuwarsa.
Abu kamar wasa jikinsa na dira akai ya nutse cikin laushi
ai kuwa sai bacci ya ɗauke Armad. Yayi ta sharar bacci
tsahon lokaci har saida rana ta faɗi. A lokacinda yaji
muryar Nostaljiya na tashinsa. Da kyar ya buɗe ido yana
gani hazo-hazo har dai ya wartsake.
Bayan Nostaljiya Armad ya kula cewa akwai wasu kuyangi
guda bakwai duk sanye da kaya ruwan kasa iri ɗaya sunyi
sahu suna ta shigo da kayan ci da sha. Ƙanshi ne kawai
yake tashi a ɗakin.
"Ka tashi kayi wanka kaci abinci. Mahaifina yana so zaiyi
magana dakai."
Da akwai ragowar bacci a idon Armad amma koda yaji
abinda Nostaljiya tace saiya miƙe zumbur gami da fara
gumi. Ko sirikinka yawon bola yake akace zaku gaisa
dashi sai kaji zufa ballantana ɗaya daga cikin mafi girman
sarakuna a duniya.
Cikin sauri Armad ya tambaye ta. "Da gaske kike koda
wasa?"
Nostaljiya ta fashe da ƴar ƙaramar dariya wadda ta dace
da karfin ikonta. Bangon ɗakin na ɗaukan sautin
kyakkyawar muryar ta. Nan take Armad yaji tamkar
sarewa ake kaɗa masa. Lamarinda yasa ya faɗa cikin
tunani ya manta da cewa shugaba mai dauwamammen
sara yana jiransa.
"Ka tashi yana jiranka?"
Koda Armad yaga ga dukkan alamu da gaske take saiya
miƙe cikin damuwa ya ce, "lafiya dai ko?"
Nostaljiya ta haɗe rai cike da shagwaɓa. "Nima ban sani
ba."
Armad yai ajiyar zuciya a karo na uku sannan ya fara
tunanin mai Bihanzin zai ce masa. Lallai da matsala.
"A ina zanyi wankan? Kuma ni gaskiya..."
Nostaljiya tayi wa Armad wani kallo mai cike da tsokana
tana cewa, "Kai gaskiya me? Ga ƙoramar wanka can ta
musamman nasa an haɗa maka." Tayi nuni izuwa wani
ƙasaitaccen tafki mai ɗauke da filawowi a samansa. Wani
tiriri ne mai alamun ni'ima ke tashi daga saman ruwan.
Kana gani kasan an shirya shi ne domin wankan manya
ƴaƴan sarauta.
Armad ya juya ya nufi ƙofa yana ta zulumi. Har ya kusa
kaiwa ƙofar sai yaji muryarta. "Idan ka fita kasan ta ina
zaka zagaya?"
Armad ya juyo fuska a murtuke yana cewa, "to kizo ki
rakani mana."
Nostaljiya na ganin yadda yake magana ta ƙara fashewa
da dariya tana cewa, "kaci gaba da ɓata rai saina kirawo
maka yaya Kiru da yaya Hasanu yanzu-yanzu."
Armad ya buɗe baki zaiyi magana amma ya kasa ganin
Nostaljiya ta taho tana rangwaɗa irin ta ƴaƴan
sarakunan farko. Kwata-kwata ya manta dasu Kiru da
Hasanu. Amma a wannan lokaci ya tuno da fafatawarsu
da Kiru shekaru da dama da suka wuce a sanda ya fara
fitowa nemawa mahaifiyarsa lafiya.
Can bayan Nostaljiya ta fara jan hannusa izuwa waje ya
samu ya tattaro kwarin gwiwarsa ya ce, "Kiru da Hasanu?
Da fatan suna nan lafiya? Na daɗe bamu haɗu ba."
Nostaljiya ta amsa da cewa, "ba wani nan. Da yaushe
rabon da ka tambayesu? Kai dai kawai tsoron yaya Kiru
kake ji. Dan kasan yanzu ya ƙara kwarewa matuƙa a
fannin takobi."
Armad na niyyar cewa shima ya ƙara ƙarfin takobinsa
Nostaljiya ta fara jansa da gudu suna sassarfa. Duk
kwanar da suka sha sai sun haɗu da kuyangi suna hidima,
kuma duk wanda duka gansu sai sun zube a ƙasa suna
gaisuwa. Nostaljiya ko a jikinta, Armad kuma tun yana
amsawa harya gaji. Ga dukkan alamu zuwansa shi ne yasa
aka kawo wannan kuyangi da yawa haka domin sanda
yazo babu kowa a wajen.
Suna cikin tafiya Armad yai ciki da wata tukunyar filawa
garin ya kauce mata. Nan take ya fara jan hannun
Nostaljiya yana cewa, "ki daina gudu. Wai wajen wankan
nan tashi zaiyi ne? Kinga ban san hanya ba ina yi muku
ɓarna."
Amma Armad na magana Nostaljiya kawai ƙara jansa
take tana dariya. "Komai ka fasa zan biya kar ka damu."
Tun yana zuƙewa har ya saki jiki suka ringa zagayawa
suna gudu acikin fadar nan suna shewa kamar wasu yara
ƴan shekara goma. Bayan kimanin rabin sa'a suka iso
wajen. Arnad ya waiwaya ya hango ɗakin da suka fito
daga ciki sannan yaga hanyar da suka biyo, nan take ya
gane cewa Nostaljiya na sane ta ringa zagaye dasu ba
gaira ba dalili.
Kamar ta gane mai yake tunani ta ce, "Eh mana. Ina sane
na kewaya damu kaga yanzu kasan hanya baza ka ɓata
ba. Kayi sauri ka shiga kai wanka tun kafin abba ya turo a
ɗaukeka a tafi dakai."
Armad najin wannan kalma ya fara azamar cire kaya zai
faɗa cikin ruwan, amma a lokacin ya tuna tana wajen ya
juya ya kalleta. "Anan zaki tsaya?"
Nostaljiya ta haɗe rai. "Ko baka faɗa ba tafiya zanyi.
Kawai dai kada ka nutse ka mutu ka barni."
Armad ya fashe da dariya a karo na farko yana cewa,
"kamar wata ke. Ɗan wannan ruwan ne zai kashe ni,
mutuwa ta sai anyi shiri."
"Nidai kayi sauri idan ba haka ba zan dawo na fito dakai."
Nostaljiya ta juya ta fice.
Armad ya jira yana murmushi har saida ta ɓace sannan
ya ƙarasa cire kayansa ya afka cikin tafkin ya fara iyo.
Ruwan ya kasance mai ɗumi dai-dai wanka. Sannan yana
bada wani ƙanshi mai inganci. Filawowin kai kuwa na
bada wani sinadari mai kama da sabulu wanda nan take
ya wanke jikin Armad tas. Idan ta shawarar Armad ne
kada ya futo daga cikin wannan daddaɗan ruwa har sai
ya nutsu amma sarki na jiransa.
Ba shiri ya fito ya maida rigarsa. Akan hanyarsa ta
dawowa ya fara tunanin wanne kaya zaisa yaje dasu.
Tambayoyi sama da ɗari suna ta yawo akansa akan
menene dalilin da yasa Bihanzin ke nemansa. Kowanne
dalili ya tuna sai yaji zuciyarsa ta buga. A lissafin Armad
wannan ba wani abu bane illa sammaci.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo ƙofar ɗakin daya kwanta
aciki ɗazu. Yana shiga yai arba da Nostaljiya zaune tana
jiransa zagaye da abinci.
"Na baka minti goma ka shirya. Idan ka dawo kaci
abincin."
Armad ya zare ido cikin sauri yana cewa, "Yunwa nake ji
fa."
Nostaljiya ta canja fuska sannan ta fara magana cikin
shagawaɓa. "Yana jiranka fa."
Armad bai san sanda ya sanya kaya cikin ƴan daƙiƙu ba
ya bita suka nufi nufi cikin fadar. Ranar da zaiyi arba da
mai dauwamammen sara tazo.
_______
Yekuwa Manazartar littafin Magajin Wilbafos
Sarki Kurussa'ayi Ururu Sarki Bisa Doron Kasa na daya 1
yana Gaisheku ya kuma ya gaisheku
Sannan yace a sanar daku cewa kwamitin Rubutun
magajin wilbafos karkashin jagorancin Shuraih 99% sun
canja tsarin Posting,
A yanzu za'a runga posting Kullum sabanin zamanin baya
da sai sati sati,
A kowane Rana za'a runga yi maku post Daya,
.
Sako daga shalkwatar Ururu ta doron kasa na Uku,
Sa hannun sarki Kurussa'ayi Ururu, Dhul ururu,Yarima
Dumakisu Ururu,Uznu Ururu, Haruta Ururu,Maruta
Ururu,deniz ururu
______
dafatan za ku bamu hadin kai
99%

Babi na 98: Armad da Bihanzin
**
Haka Armad da Nostaljiya suka yita keta cikin wannan
fada suna wuce manyan gine-gine masu fasali daban-
daban. Nostaljiya na ƙoƙarin yiwa Armad hira amma
hankalinsa baya wajen harta gaji tayi shiru. Bayan wani
ɗan lokaci suka iso harabar wani ƙaton ɗakin taro da aka
kewaye da mutun-mutumin mutane kala-kala.
Nostaljiya ta nuna ƙofar ɗakin tana cewa, "shiga ka jira
aciki ina zuwa."
Armad ya nufi ƙofar ɗakin ita kuma ta kewaya tabi
hanyar da tabi ta bayan ɗakin.
Ɗakin nada madaidaicin girma amma abubuwan dake
cikinsa basu da yawa. Wani ƙaton teburi ne kewaye da
kujeru a tsakiyar ɗakin. Ga dukkan alamu wannan ɗaki
kullum acikin kula yake domin ko ƙura ɗaya babu. Komai
kyalli kawai yake, shi kansa teburin na gilashi ne. Armad
ya ja kujera ɗaya ya zauna yana jiran shigowar mai
dauwamammen sara.
Ba jimawa saiga Hasanu Sisiyu, yayan Noltaljiya, ya shigo.
Fuskarsa babu murna kuma babu ɓacin rai. Ya dubi
Armad ya ce, "kwana da yawa. Da fatan kana lafiya."
Muryar Hasanu na nan ɗauke da ƙarfi da girma irin na
sarakuna. Fuskarsa ta ƙara cika da kamala, kana ganinsa
kasan ba'a zaune yake ba.
Armad ya amsa da cewa, "ina nan lafiya. Da fatan na
same ku lafiya?"
Hasanu ya nemi waje ya zauna sannan ya dubi Armad ya
ce, "bari na baka shawara a matsayi na na abokinka. Kada
kayiwa mahaifinmu ƙarya domin duk abinda zaka faɗa
zai san gaskiya kake faɗa ko ƙarya."
Armad yai murmushi. "Ai dama bana shirin yin ƙarya."
Hasanu ya girgiza kai kafin daga bisani yai murmushi
sannan su koma hirar takobi. Hasanu yayi ta yiwa Armad
tambayoyi akan fasahar takobinsa shima Armad yana
masa har dai suka ji an buɗe ƙofar ɗakin. Wani babban
mutun sanye da doguwar riga ƴar shara ya shigo cikin
ɗakin. Nostaljiya na tafe a bayansa. Yana shigowa Hasanu
ya miƙe tsaye tare da durƙusawa, shima Armad ya miƙe
ya bashi girmansa.
Mutumin na tafiya kamar ba tafiya yake ba, ƙafafunsa na
motsawa cikin isa da iko irinta sarakunan aljanu.
Idanunsa tsaye suke kan Armad yana nazarinsa. A tsaye
zaka iya cewa wannan mutun ragowar samudawa ne
domin aƙalla yakai zira'i ashirin. Wanda hakan ya ninka
tsayin Armad sau wajen takwas.
Yana shigowa ya nufi kujerar da aka tanada domin sa
wacce ke gaba da dukkan sauran kujerun.
Yana zama Hasanu da Nostaljiya suka fice suka barshi da
Armad. Wannan mutun dai ba wani bane illa Bihanzin
mai dauwamammen sara, ɗaya daga cikin sarakuna biyar
na Jinzidal. Mutuminda akai ittifaƙi takobinsa tafi
kowacce takobi ƙarfi a duniya.
A wannan lokaci Armad ya nutsu tare da tsayawa yayi wa
Bihanzin kallo na tsanaki. Bihanzin dai ya kasance mutun
ne wanda kana kallonsa zaka san yayi matuƙar daɗewa a
duniya. Idan kana kallonsa zaka ga tamkar shekarun
ƙarni-ƙarni ne ke wucewa ta ruhinsa. Idanunsa a kafe
suke kuma suna bada wani haske mai ɗauke da firgici da
saka jimami. Fuskarsa nada tsayi da faɗi kamar dukkan
jikinsa, sannan kuma cike take da farin gemu. Gashin
kansa ma fari ne dogo mai tsayin gaske wanda har
bayansa yake taɓawa. Hatta shi kansa gashin girar
Bihanzin a lanƙwashe yake zubin takobinsa.
Rigar dake jikinsa doguwar ƴar shara ce wadda ta bashi
damar saƙale takobinsa a sauƙaƙe. Armad na ganin
takobin nan yaji hankalinsa ya ɗugunzuma, tsigar jikinsa
na tashi. Yanayin-izzar dake kewaye da takobin iri ɗaya ne
sak dana Hankakan-mutuwan da Armad ya gani. Nan take
Armad ya miƙa hannunsa kan takobinsa ba tare da ya
sani ba. Tuni Armad ya manta da inda yake, babu abinda
yake tunawa sai labarin da mahaifiyarsa ta gaya masa
akan waccan ƙabila wadda aka manta da sunanta.
Ƙabilar da tarihi ya nuna cewa saida ƙabilar Wilbafos da
ƙabilar Ururu suka haɗa hannu da ƙarfe sannan suka ga
bayanta.
"Kada ka damu da takobi na. Ita wannan takobin tawa
babu wanda take yadda dashi idanba ƴaƴa na ba."
Muryar Bihanzin ce ta farfaɗo da Armad daga tunanin
daya shiga. Amma duk da haka bai ɗauke idonsa daga
kan takobin ba.
Takobin dai bata da faɗi da yawa amma tafi tsayin zira'i
uku. Lallai ba daban Bihanzi basamude bane da bazai iya
ɗaukanta ba. Abin mamakin shi ne takobin har wani huci
take tana kallon Armad tamkar tana jin mai ake cewa.
Koda Bihanzin yaga Armad bai daina kallon takobin ba sai
yaja rigarsa ya rufe ta yana cewa, "sunan wannan takobi
tawa Bankái. Indai ka biya ta Bankái haka zatai ta
tsokanarka har sai ta jaka izuwa faɗa."
Mamaki ya ƙara rufe Armad yadda yaji Bihanzin yana
maganar takobinsa yana bata suna kamar wata mai rai.
Nan take Armad ya tuna yadda yayarsa Hidaya take yiwa
takobinta magana. A sau da dama Armad yana yaro
yakanyi tunanin ko Hidaya tsokanarsa kawai take amma
takan ce masa takobin ta tana da ruhi nata na kanta
kuma tana ji idan akai mata magana.
Armad yai murmushi na girmamawa sannan ya ce,
"barka da warhaka. Ina fatan ban ɓata maka ƙa'idarka ba
dana shigo fadarka ba tare da izini ba."
Bihanzin yai gyara murya haɗe da girgiza kai, lamarinda
yasa muryar tayi kama da ana goga busasshen ƙashi a
jikin bango. Dama dai muryar Bihanzin kaushi ne da ita,
amma gyaran muryar da yayi shi ne yasa abin ya ƙara
fitowa fili. A wannan lokaci Armad yayi ƙoƙarin jin
yanayin-izzar Bihanzin amma bisa mamaki baiji komai ba
sai wani sanyi mai ratsa ƙashi wanda ya banbanta da
sanyin-babban-sihiri kuma ya banbanta da sanyin
hunturu ko na ƙanƙara. Wannan sanyin da Armad yake ji
yafi dana tsohon kabari. Nan take Armad ya daina
ƙoƙarin jin yanayin-izzar Bihanzin amma duk da haka
saida yaji ya fara rawar ɗari.
Muryar Bihanzin ce ta ƙara farfaɗo dashi. "Kada ka damu,
Magajin Wilbafos, tunda har ka shigo ba tare an kama ka
ba ai gayyato ka akai."
Armad ya zare ido cikin mamakin wannan magana,
domin hakan na nuna Bihanzin na sane da shigowarsa.
Nan take Armad ya buɗe baki zai tambayi Bihanzin amma
sai Bihanzin ya riga shi magana.
"Nakan ji yanayin-izzar abokan gaba tsahon tafiyar
shekara guda tun ina ɗan shekara bakwai. A lokacin da na
cika shekara takwas ina iya banbance mutane na gane ko
su waye ta hanyar yanayin-izzarsu koda nisansu da inda
nake yakai tafiyar shekara guda. Kaga bazai zama abin
mamaki ba dan naji shigowar ka daula ta a lokacin da ka
sauka daga jirgin Fataken-dare."
Armad ya zare ido cikin tsananin al'ajabin ƙarfin izzar
wannan halitta dake gabansa. Lallai ba'a zama sarkin
Jinzidal a banza. Koda yake dama wannan shi ne karo na
farko da Armad yai arba da ɗaya daga cikinsu.
Idan dai har Bihanzin zaiji yanayin-izzar mutun kimanin
nisan tafiyar shekara guda kuma ya gane waye, lallai babu
wanda ya isa ya shigo wannan daula ba tare da saninsa
ba. Kuma lallai ba abin mamaki bane dan Bihanzin yasan
Armad shi ne Magajin Wilbafos.
Kai tsaye Armad ya bugi ƙirji ya tambayi Bihanzin. "Mai
kake buƙata daga gareni daka bari na shigo?"

Chapter 99 & 100
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 99: Armad da Bihanzin part 2
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
"Hmm... " Bihanzin yaja dogon numfashi sannan yaci
gaba da bayani. "Wilbafos kai kake neman wani abu a
waje na ba ni nake nema a wajenka ba. Zaka sauƙaƙa
mana wannan tattaunawa idan ka gayamin hakikanin mai
ya kawo ka daula ta."
Armad ya sunkui dakai yana tuno asalin abinda ya
kawoshi wannan daula. Koma meye a bayan samarwa
mahaifiyarsa lafiya yake kuma lallai abinda kawai ya kawo
shi kenan. "Nazo neman shekarun izza domin yiwa
mahaifiyata wadda take fama da cutar izza magani."
Bihanzin ya danyi shiru kafin daga bisani ya ce, "Naji
labarin cewa abinda ya fito dakai daga gida kenan
shekaru uku da suka wuce. Indai wannan ne kaɗai
buƙatarka to babu matsala, a yanzu zan warkarda
mahaifiyarka. Koba komai bai wuce biyan bashi ba,
domin har yanzu bamu biyaka fassarar dakai mana ba a
waccan shekara."
Armad ya zare ido tare da miƙewa tsaye cikin murna
yana cewa, "da gaske kake? Lallai idan ka samarwa
mahaifyata lafiya bani da yadda zanyi na iya sakamaka.
Nagode."
Bihanzin ya ɗaga hannu yana dakatar da Armad alamun
bai gama magana ba. "Nasan akwai soyayya tsakanin ka
da ƴata Nostaljiya, kuma bazan ce maka ka haƙura ba
indai kana sonta, amma akwai abu guda ɗaya da nake so
ka sani." Koda Bihanzin yazo nan a zancensa sai ya dubi
Armad a nutse domin ya tabbatar yana tare dashi sannan
yaci gaba.
"Shi CIKAKKEN MUTUN shi ne wanda yake ɗaukan alhakin
abu idan yasan shi ya jawo shi. Nostaljiya ta ɗau alhakin
abinda ta aikata a wajen cinikin bayi kuma taƙi yadda a
ɗora maka laifi. Idan za'a wanke ta a idon duniya to sai
dai ta yadda ta auri Deniz Bizaya wanda a zahiri ba shi
take so ba. To amma idan bata aure shi ba, hukumar
Jinzidal zata yanke mata hukunci. Hatta ni kaina a matsayi
na na babanta bazan iya kare ta daga sauran sarakunan
Jinzidal ba, kuma idan na hana ayi mata hukunci, yaƙi ne
zai afku. Idan kace kana sonta, shin zaka iya zama
cikakken mutun ka ɗauki alhakin komai a kafaɗunka ka
kare ta, kuma ka shiga yaƙi saboda ita? Idan dai har zaka
iya wannan to ka cancanci ƴata, amma idan baza ka iya
ba to ka manta kawai. Biyo ni." Bihanzin ya miƙe ya nufi
ɗaya daga cikin ƙofofin dake kewaye da wannan ɗaki,
Armad na biye dashi.
Bihanzin na tunkarar ƙofar ta buɗe, Armad ya tsinci
kansa a wani ƙaton fili mai yawan rairayi. Abin mamaki
iskar dake kaɗawa acikin wajen ta banbanta data cikin
dakin daya baro, tamkar wata duniya ta daban suka
shiga. Take saboda sanyi Armad ya tuna da cewa yana da
kayan sanyi a ajiye acikin zobensa. Amma kafin ya fito
dasu sai kwatsam yaji yanayin ya fara canjawa, rairayin
ya fara ɗaukan zafi kamar ana kunna masa wuta. Kafin
kace meye wannan gumi ya fara gudu a fuskar Armad.
Suka ci gaba da tafiya Bihanzin bai ce masa komai shi
kuma bai tambaya ba. Amma abu kamar wasa taku
bakwai bayan an fara zafin kawai sai ruwa ya ɓarke
kamar da bakin kwarya.
Armad ya tsaya ido a zare yana mamaki. Lallai akwai abin
al'ajabi a tattare da wannan waje. Kuma tashin hankalin
shi ne bai san inda Bihanzin yake ƙoƙarin kaishi ba. Yana
cikin tunane-tunane yaji murya Bihanzin, "A cikin
wannan waje duk bayan minti ɗaya yanayi yake canjawa.
Kaga maimakon zafi da sanyi da damina da rani kowanne
yazo a shekara sau ɗaya, kowannensu a wannan waje
yana zuwa a kowacce rana sau dubu uku da ɗari shida.
Acikin wannan waje nake ajiye wani kaso daga cikin
shekarun izza ta na kwangila ta. Ban san shekara nawa
mahaifiyarka take buƙata ba amma nayi maka alƙawarin
bata shekarun izza dubu goma zuwa ashrin. Fito da ita ka
ajiye ta anan."
Bihanzin ya nunawa Armad tsakiyar yashi inda ruwa ya
ɗan taru. Da farko Armad ya fara mamakin yadda akai
Bihanzin yasan mahaifiyarsa na cikin zoben dake
hannunsa amma kuma ya tuna komai ma zai iya faruwa
indai ana maganar sarki Bihanzin sabida haka babu wani
abin mamaki. Nan take Armad ya futo da mahaifiyarsa
sanye cikin fararen kaya kamar tana bacci. Amma yaƙi
yadda ya ajiƴe ta a ƙasa har saida Bihanzin ya tafa
hannunsa wani gado ya bayyana.
Bayan wasu ɗalasimai da Bihanzin ya kira a zuci sai kawai
wani ƙatoton shaiɗanin aljani ya bayyana. A tsakiyar kan
aljanin akwai ƙahunhuna guda bakwai, sannan yana
sanye da wata baƙar hula da aka sarrafa da fatar aljanu
zalla. Abin mamaki ɗauke a kafaɗun wannan aljani
hankakan mutuwa ne baƙaƙe har guda biyu. Yana
bayyana ya faɗi yai gaisuwa ga Bihanzin yana cewa, "Ya
shugaba na. Mai kake buƙata?"
Bihanzin ya amsa da cewa, "mahaifiyar wannan yaro na
fama da cutar izza, ina so ka bata shekarun izza daga ɗaya
zuwa dubu ashirin. Iyakacin yadda zai ishe ta ta warke."
Aljanin ya ware samudawan hannayensa guda biyu yana
cewa, "An gama ya shugabana."
Nan take wani jan haske mai ɗaukar ido ya fara taruwa a
hannayen wannan aljani kafin daga bisani ya karkatar da
hasken izuwa gare ta. Hasken na taɓa ta jikinta ta fara
girgiza kamar mai farfaɗiya. Armad yai wuf zai riƙe ta
amma Bihanzin ya riƙe shi yana cewa, "Kada ka damu,
shekarun Izza ne ke shiga jikinta."
Haka Armad ya haƙura yana kallon mahaifyarsa wannan
jan hasken na shiga jikinta tsahon lokaci. Saida akai sa'a
guda acikin wannan hali sannan hasken ya ɗauke, aljanin
ya dubi Bihanzin ya ce, "An gama ya shugaba na. Na bata
shekarun izza dubu goma sha huɗu da dari biyu da sha
uku, kuma a lissafi na zata farka nan da wata tara."
Cikin sauri Armad ya durƙusa a gefenta yana share mata
gumi. Yana cikin haka kawai sai yaga a karo na farko
acikin shekaru uku mahaifiyarsa tayi motsi. Cikin murna
yai ihu yana niyyar yin tsalle yai shewa kawai sai yaga ta
buɗe ido. Ta kalli Armad, Armad ya kalleta. Nan take
hawaye ya fara zuba daga idanunsa. Ta buɗe baki zatai
magana amma kafin tayi magana saita ƙara komawa ta
suma. Amma duk da haka murnar Armad bata ragu ba.
Yana cikin haka yaji muryar Bihanzin a kunnensa. "idan
ka daɗe da yawa acikin wannan waje komawa duniyar
daka fito zaiyi maka wahala."
Armad najin haka ya maida mahaifyarsa cikin zoben
sannan cikin murna da annushuwa irin wadda ba'a taɓa
ganinsa aciki ba ya biyo bayan Bihanzin suka nufo waje.
Koda suka dawo cikin wannan ɗaki sai suka tarar da
Nostaljiya na tsaye tana jiransu. Tana ganin murnar dake
fuskar Armad ta fashe da murmushi, lallai tasan an samu
abinda ake nema. Koda Bihanzin yaga haka saiya dubi
Armad ya ce, "Ni zan barku anan. Ka tuna da abinda na
gaya maka. Ka zama CIKAKKEN MUTUN."
Babi na 100: Shawarar Armad
**
Armad da Nostaljiya suka nufi hanya izuwa ɗakin da aka
saukeshi. Akan hanyarsu kowa yayi shiru bai ce komai ba.
Nostaljiya tana jira Armad ya gaya mata abinda suka
tattauna da mahaifinta amma Armad yayi shiru. Ita kuma
bata tambaya ba.
Koda isarsu ƙofar ɗakin sai Armad ya shige ɗakin ba tare
da yace uffan ba sannan ya turo ƙofa. Nostaljiya ta buɗe
baki zatai magana amma ta fasa. Cikin ɓacin rai ta juya ta
tafi. Har ta kusa ƙulewa ta juyo ta dubi kuyangar dake
ƙofar ɗakin ta ce, "Ku bashi duk abinda yake buƙata, idan
ya nemi ku nuna masa hanyar fita daga fada ku nuna
masa." Tana rufe baki ta juya ta tafi.
Armad ya faɗa kan gado yana jinta harta ƙule. Yai shiru
yana tunanin maganarda Bihanzin ya gaya masa. Abu ne
mai sauƙi tunda mahaifiƴarsa ta sami sauƙi ya fice daga
wannan daula kada ya ƙara waiwayarta. Yaje can wani
waje ya tsara sabuwar rayuwarsa cikin kwanciyar hankali.
To amma Armad yasan cewa tun daga ranar da yayi
rantsuwa zai tarwatsa cinikin bayi rayuwarsa baza ta ƙara
kasancewa cikin kwanciyar hankali ba. Irin wannan
rayuwa wadda za'ai aure a haihu a sami ƴaƴa biyar ko
goma, sannan a zauna cikin kwanciyar rai har a tsufa a
mutu ba tasa bace.
Dama dai tuntuni abinda yasa Armad bai maida hankali
ba akan shirinsa na tarwatsa cinikin bayi shi ne halinda
mahaifiyarsa ke ciki. Amma ga dukkan alamu wannan ya
kau. A yanzu ne lokaci mafi dacewa daya kamata ya fara
aiwatar da shirinsa.
Auren Nostaljiya lallai zai ɗaukaka martabarsa a idon
duniya kuma zai saka rundunar sarki Bihanzin ta zama
kamar tasa. Daɗin daɗawa daga abinda Nostaljiya ta gaya
masa a wancan lokaci da suka haɗu, akwai rigima
tsakanin sarakunan Jinzidal tayadda kowannensu zaiso
yaga bayan ɗan'uwansa. Duk da cewa manufar Bihanzin
ta yaƙi da sauran sarakunan Jinzidal ba lalle bane ta zama
ɗaya data Armad ba, amma dukkaninsu suna da abokan
gaba iri ɗaya.
Matsala ɗaya ita ce; shin Bihanzin akan kansa yana so ya
tarwatsa cinikin bayi ko kuma kawai yana so ya tarwatsa
sarakunan Jinzidal ne? Domin zata iya yiwuwa Bihanzin
yana goyon bayan cinikin bayi amma yana rigima da
sarakunan Jinzidal.
Armad na zuwa nan a tunaninsa ya yanke shawara, Idan
har Bihanzin ya amince ce zai taimake shi ya rusa gasar
Jinzidal to shima zai taimaka masa ya karya sarakunan
Jinzidal.
Bayan Armad ya cimma wannan matsaya saiya fito da
Maikiro Inara daga cikin zobensa. Har izuwa wannan
lokaci Inara bai farfaɗo ba, amma ga dukkan alamu ruwa
kawai yake buƙata.
Ai kuwa Armad yana yayyafa masa ruwa ya farka, inda
Armad ya kwashe dukkanin labarin daya afku bayan ya
suma ya gaya masa. Inara ya taya Armad murnar samun
lafiyar mahaifƴarsa sannan yayi masa fatan alkhairi.
---------
Armad da Inara suka kwana acikin wannan ɗaki, washe
gari da safe Armad ya kaisu wannan tafki sukai wanka
sannan suka ci suka sha. Bayan sun dawo ɗaki Armad ya
fara jira ko zaiga Nostaljiya amma shiru har yamma ta
kawo kai rana ta faɗi ba labari. Da magariba Armad ya
tura ɗaya daga kuyangin dake kawo musu abinci ta kira
masa Nostaljiya amma bisa mamaki hakan bata samu,
Nostaljiya ta amsa amma bata zo ba. Haka ya gaji da jira
har dare yayi gari ya waye.
Washe gari Armad ya ƙara tura wata kuyangar, Noltaljiya
tace taji amma har dare yayi bata zo. Nan take Armad ya
fara shiga damuwa saboda yasan haƙiƙanin dalilin da
yasa Nostaljiya bata amsa kiransa ba.
Washe gari Armad ya yanke shawara ya taka yaje wajenta
da kansa. Koda ya fito bakin ƙofa saiya tarar da ɗalibinsa
Inara na tsaye yana gadin ƙofar. Murmushi kawai Armad
yayi ya bashi umarnin yazo ya rakashi.
Armad ya dubi ɗaya daga cikin kuyangin dake wajen ya
ce, "Muje ki rakamu wajen gimbiya."
Amma wannan kuyanga ta kada baki ta ce, "Ai ba'a shiga
wannan ɓangare daga mu kuyanginta sai ita kanta,
gimbiya."
Maganar bata yiwa Armad daɗi ba, ya tsaya yana ta
tunani kafin daga bisani ya juya ya koma ɗaki. Har ya isa
bakin ƙofa sai wata dabara ta faɗo masa, yaci birki ya
tsaya tare da juyowa izuwa wannan kuyanga ya ce, "muje
naga wajen saboda tsaro."
Kuyangar fara ce mai tsaho sanye da farar doguwar riga.
Tana jin abinda Armad ya ce ta zare ido tana mamaki.
Abinda bata gane ba shi ne mai Armad yake nufi da
'saboda tsaro'. To amma ba muhallinta bane a
matsayinta na kuyanga ta tsaya tana yiwa Armad
tambaya, saboda haka ta shige gaba ta fara tafiya, su
Armad suka bi bayanta.
Abin mamaki sai Armad yaga sun ɓulle ta wata ƙofa
wadda ta shigar dasu wani ƙaton fili. Duk kewayen da
Armad yayi na kwana biyu bai san da wannan filin ba.
Haka suka ci gaba da bin kuyangar har suka ƙarar da
wannan fili suka nufi ɓangaren arewa, sannan daga bisani
suka iso wata farfajiya mai yawan bishiyun dabino.
Wannan bishiyun dabino sun kekkewaye wannan sashi ta
yadda ba'a iya gano cikinsa sosai. Suna ƙara matsowa sai
Armad ya fuskanci cewa wannan ɓangare an raba shi ne
izuwa gida uku manya-manya. Abin mamaki shi ne hatta
katangar da aka kewaye wannan waje da zinare aka yaɓe
ta. Komai kawai walwali yake. Nan take Armad ya fara
tunani yana mamakin irin dukiyar dake cikin wannan
fada.
Suna isowa gindin wannan bishiyu sai wannan kuyanga ta
tsaya tana nuni da ginin dake tsakiyar gine-ginen guda
uku. "Wancan ne na tsakiyar. Na ɓangaren dama kuma
na ƴarima Kiru ne, na ɓangaren hagu kuma na yarima
Hasanu me. Amma daga nan babu wanda yake da damar
haurawa

Please Login or Register in order to submit comment