Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Babara bai motsa ba.
Nan take ruwa ya ɓarke tamkar da bakin kwarya. Duk
bayan daƙiƙa biyar sai aradu ta sauka mai ƙarfin gaske.
Ba jimawa wannan ruwa ya fara haɗuwa zafin aradun
dake sauka suka fara narka wannnan dusar ƙanƙara data
cika wannan kurkuku.
Kwana uku cir aka ɗauka ana zabga ruwa kafin dukkan
wannan ƙanƙara ta narke. Wannan kurkuku ta bayyana a
fili. Ashe acikin wannan dusar ƙanƙara manya-manyan
duwatsu ne na wuta wanda aka fafake cikinsu akai gidaje.
Kana ganin wannan gidaje zasu tuna maka da ƙissar
samudawan farko irin wanda akan bayyanasu da cewa
suna ɗumamen safe da zafin rana.
Waɗansu halittu ne sanye fatun namun dawa suka fara
ambaliya daga cikin wannan gidaje na dutse da wani irin
sauri tamkar na aljanun farko. Kafin ƙiftawar ido da
bismillah sama da wannan halittu dubu uku sun bayyana
sun kewaye Babara a inda yake zaune. Ga dukkan alamu
ya tayar dasu daga baccinsu. Fuskokinsu a rufe suke da
fatar farin zaki amma hakan bai hana tsananin ƙiyayya
dake tashi daga cikin idanuwansu bayyana ba. Wata irin
iska mai ɗauke da marmarin yaƙi na fita daga jikinsu.
Sannan suna bada gunji mai amo kai kace samarin
kuraye ne. Sahu-sahu sukai tare da tunkaro Babara a inda
yake zaune, lallai babu ko tantama niyyarsu suyi watanda
da naman Babara. Matsalar ɗaya na bayan ba lalle su
samu ba.
Amma duk da haka Babara bai motsa ba. Idanunsa na
cike da imani da dogaro da fasahar da Armad Wilbafos
zai farkar.
Ba jimawa tokar naman jikin Armad ta fara haɗewa tana
curewa waje ɗaya acikin wannan rijiya wadda tuni ta cika
da ruwa. Ba jimawa wata tsawa ta sauka acikin rijiyar
wadda ta ƙone duk ruwan dake ciki. Babu abinda yai
ragowa acikin wannan rijiya sai tokar Armad.
Ana haka wannan toka ta juye izuwa siffar Armad
Wilbafos. Armad yai wani gunji mai firgitarwa wanda
yasa dukkan wannan halittu jada baya. Wani taku irin na
jaririn aljani ya fara fitowa daga cikin wannan rijiya. Inda
daga bisani sabon saurayi ɗan kimanin shekaru sha tara
ya bayyana daga cikin wannan rijiya, a jikinsa babu
komai sai ɗan bante.
Yana bayyana Babara ya buɗe ido tare da miƙewa ya
kawo gaisuwa. Koda ganin haka sai waɗannan halittu
suka fusata tare da rabuwa izuwa gida uku. Kaso na farko
suka ɗaga hannunsu sama, inda wasu masu, masu ci da
wuta suka bayyana. Kaso na biyu kuwa bakunansu suka
buɗe, inda suka fara yin aman ruwan narkakken dutse
wanda zafinsa zai iya ƙona wuta ita kanta. Kaso na uku
kuwa wani baƙin ruwa ne ya fara ambaliya daga
hannayensu, idan da Armad yana gani zai gane ruwan irin
ruwan da Dordor suke amai ne.
Dukkaninsu sukai ƙaraji tare da sakar wannan hare-hare
izuwa Armad. Babara yai tsalle da niyyar shiga tsakani
amma Armad ya ɗaga masa hannu. Ba shiri Babara yai
gefe. Lallai koda aljanun farko sai sun tsorata da wannan
hari na wannan halittu, wanda ke ɗauke da tsantsar
rashin imani. Domin kuwa idan ka kalli samaniya zaka ga
masu, masu cida wuta sama da dubu, haɗe da guma-
guman ruwan narkakken dutse sama da dubu, tare da
wani baƙin ruwa mai alamun mutuwa. Kuma abu na
farko da zai fara zo maka shi ne waɗannan hare-hare ana
niyyar halaka gari ne dasu, babu wanda zaiyi tunanin wai
mutun ɗaya ake so a halaka.
Armad ko gezau baiyi ba, hasalima ko motsa ɗan-yatsa
baiba. Yana tsaye waɗannan guma-guman azaba suka
saukar masa. Wata ƙara mai firgitarwa ta tashi, sannan
ƙura ta turnuƙe. Lallai ko wanda ke tsaye kimanin nisan
tafiyar shekaru dubu zai iya jin wannan ƙara, kuma zai
iya ganin wannan ƙura.
Babara yai ƙaraji saboda ɓacin rai ya afka cikin wannan
hargitsi domin ceto Armad. Amma ba jimawa yaji wani
irin yanayin Izza mai firgitarwa irin wanda bai taɓa ji ba a
duk tsahon shekarunsa. Ba shiri ya fara jada baya kaɗan
da kaɗan kafin wannan yanayin izza ya ƙara dukansa,
lamarinda yasa ya harɗe tare da faɗuwa a ƙasa. Haki
sarkin duba Babara ya fara, badan komai ba sai dan
saboda ƙarfin izzar da yake ji.
Amma waɗannan halittu basu yi ƙasa a gwiwa ba wajen
ƙara fara shirin wani harin. Sai dai a wannan karan
girman kaba'irar da suke nufin Armad da ita ya ƙaru.
Domin kuwa kowa acikinsu girman harinsa ya ƙaru da
sama da sau uku.
Suna niyyar afkawa Armad sai ƙura ta lafa inda surar
Armad ta futo fili. Sai dai ina, kwata-kwata ba irin Armad
ɗin da aka sani bane. Babu komai a jikinsa face walƙiya.
Amma abin mamakin bawai irin yanayin walƙiyar dake
kewaye Armad bace a lokacin da yake amfanin da
ɗalasimai irinsu Kaban'shisu. Wannan walƙiyar daga cikin
tsoka da jinin Armad take. Hasalima zaka iya cewa naman
jikin Armad ne ya juye baki ɗaya izuwa gundarin walƙiya.
A wannan lokaci Armad ya zare wani mashi wanda ya
nutse acikin ƙirjinsa. Amma babu komai ajikin mashin
daya shafi jini ko fatar ɗan-adam. Lallai a wannan lokaci
zaka iya cewa Armad wilbafos ya zama walƙiya, walƙiya
kuma ta zama shi. Armad ya ɗaga hannusa sama ya dubi
gundarin walƙiyar data haɗa hannunsa. Sannan daga
bisani ya juyarda hannun nasa ya koma izuwa tsoka da
jini. Sannan sauran jikinsa shima ƴa koma yadda yake.
Koda ganin haka sai Babara ya zube a ƙas yana gaisuwa.
"Ina ƙara jaddada mubayi'ata magajin wilbafos."
Abin mamaki sai waɗannan halittu suka cire fatar dake
rufe da fuskarsu inda suka bayyana a matsayin mutane.
Sannan suka zube a ƙas suna gaisuwa tare da mubayi'a.
"BARKA DA ZUWA MAGAJIN WILBAFOS, MAGAJIN SARKI
EYRIYON, MAGAJIN SARKI ALDAIMA. Ka yafe mana rashin
ɗa'ar mu, lallai mun cancanci kisa!!!"
A dai-dai wannan lokaci duk wani wanda yasan sirrin
dake ɗauke cikin jinin MAGAJIN WILBAFOS yasan an
farkar dashi.
***
Sanarwa: Zamu fara chapter kullum amma duk chapter
da comments basu kai 30 ba ba lallai nayi post ba washe
gari
*******
Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks


Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafosMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 81: Kwangila
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Haka Lamarudu Wilbafos ya kai Armad cikin wani shinge
wanda aka kewaye shi da manya-manyan jajayen
duwatsu. Daga saman duwatsun kuma ruwa ne ke
gudana zuwa ƙasa tayadda suka samarda wata ƴar
ƙasaitacciyar ƙorama a ƙasa. Lamarinda yasa wajen yake
bada wani irin sanyi mai inganci. Abu na farko daya fara
zuwa ran Armad shi ne wai shin wajen horo aka kawoshi
ko kuma wajen shaƙatawa. Amma kafin ya tambaya sai
Lamarudu ya ɗora hannunsa akan wani dutse inda wasu
hatimai suka bayyana suka kewaye dutsen. Nan take wata
ƙofa ta buɗe a wajen.
Lamarudu ya shige ciki sannan su Armad suka bishi a
baya. Suna shiga wani ƙasurgumin daji mai kama da
kasuwar muridan aljanu ya bayyana a gabansu. Babu
komai sai manya-mayan bishiyun kuka wanda kowacce
ɗaya tafi tsayin zira'i ɗari. Abin mamaki shi ne wasu
manyan ƙayoyi dake kewaye da rassan wannan bishiyu a
matsayin ganyayyaki.
Lamarudu ya ce, "ga wajen koyar horo. Ga kuma
ɗalasimin dazai fitar daku a yayinda kuka gama." Ya miƙa
musu wata takarda mai ɗauke da hatimi. Har ya juya zai
fita saiya waiwayo ya ce, "dajin nan an rabashi izuwa gida
uku. Dajin kuma acike yake taf da jinsin Dordor dana
aljanu masu cin naman biladama. Indai har mutun baya
iya jin yanayin-izza to lallai bazai iya rayuwa aciki ba.
"Kaso na farko na dajin yana ɗauke da abubuwanda
izzarsu take tsakanin dubu ɗaya da dubu biyar. Kaso na
biyu suna ɗauke da izza tsakanin dubu biyar da dubu
goma. Amma kaso na uku duk abinda ka gani aciki izzarsa
ta haura dubu goma. Lallai duk hatsabibancinmu bama
shiga yanki na uku. A fito lafiya." Ya juya ya fice ya bar
Armad da Babara a wajen.
Bayan ya fita Babara ya tambayi Armad, "kaga irin kallon
da wannan mutane ke yima?"
Armad ya amsa da, "eh."
Babara ya ɗanyi shiru naɗan taƙi kamar baya so ya faɗa
amma daga ƙarshe ya ce, "Sunyi imani dakai kuma suna
yi maka kallon zaka cece su. Hakan shi ne ma dalilin da
yasa suka nuna maka waccan tsohuwar daula. Kada ka
manta iyayensu sunyi wa kakanka sarki Eyriyon bauta,
wanda hakan ne yasa aka ƙullesu. Cetonsu da zakai
kamar ramawa kura aniyarta ne. Kuma idan ka yadda ka
shiga cikin wannan daula zaka samu fasahohi da bayi na
aljanu wanda zasu taimake ka a hanyarka ta zama
cikakken sarki Wilbafos. Nidai ina ganin ya kamata ka
shiga wannan tsohuwar daula."
Armad dama yasan tuntuni Babara bai amince da rashin
shigarsa wannan tsohuwar daula ba, saboda haka tuni ya
tanadi amsa. "Duk na yadda da abinda kake faɗa amma
kai sani cewa bazan iya sauka daga manufata ba. Kuma
lallai indai ba ganin mahaifiyata ta samu lafiya nayi ba
bazan iya tsayawa acikin wannna kurkuku ba. Saboda
haka inaga mu fara horo kurum."
Haka dai Babara ya haƙura dole. Sannan ya zana wasu
hatimai guda uku a kewaye da Armad kafin ya bawa
Armad umarnin ya zauna a tsakiya, sannan daga bisani ya
fara karanta wasu ɗalasimai.
Can bayan sa'a ɗaya ana cikin wannan hali sai fuskar
Babara ta canja, inda nan take ya daina karanta
ɗalasiman ya garzayo gaban Armad inda ya ɗebi kaɗan
daga jininsa ya zuba acikin wata kwalba mai ɗauke tsumi.
Armad dai ya ji wani abu amma yai shiru baice komai ba
ya ƙurawa Babara ido.
Can Babara ya kalli Armad cikin alhini yana cewa, "dama
nayi tunanin haka, amma ina ta addu'a ya zama hakan
bata faru ba."
Armad yai zumbur ya ce, "ban gane ba. Mai kake nufi da
dama kayi tunanin haka?"
Babara ya fara bayani, "labarin daka bani na ɓacewar
Miyurarka bawai Miyurarce kaɗai ta ɓace ba, harda wani
ɓangare na ruhinka. A sakamakon haka bazaka iya amfani
da idanuwanka ba har sai ka nemo wannan ɓari na
ruhinka."
Armad ya zare ido. "Eh?!"
Babara ya ce, "bari mu gani idan zan iya gano inda ɓarin
ruhin naka yake."
Nan take ya ƙara ɗiban wani jinin daga hannun Armad ya
kuma yaryaɗar dashi akan ƙasa, inda ya zana wasu
hatumai masu rikitarwa akansa. Can daga bisani jinin na
Armad ya fara yin haske, kafin daga bisani ya kama da
wuta. Nan take sukai tsalle gefe, amma kafin suyi wani
abu tuni jinin ya ƙone ƙurmus.
Babara ya dubi Armad ya ce, "ruhinka yana katange
acikin wata sihirtacciyar ƙasa amma saboda ƙasar na
kewaye da Tsari baza a iya gane wacce bace."
Armad yama rasa mai zaice, domin kaf maganar a baibai
yake jinta. Wai ruhinsa ya ɓalle? Bayan kuma gashi nan
da rai da lafiya. A iya saninsa ma wannan ba abu bane
mai yiwuwa ba.
Yana cikin tunani yaji muryar Babara, "nasan mai kake
tunani, kuma kayi sani nima wannan shi ne karo na farko
da naga mutun ruhinsa ya rabe kuma ya ci gaba da zama
da rai. Amma dai maganar tana nan cewa bazaka iya yin
amfani da idonka ba har sai ka nemo ɓangaren ruhinka."
Armad ya kalli zoben dake ɗan yatsansa inda
mahaifiyarsa ke ajiye. Can bayan tsahon lokaci Armad ya
yanke shawara, inda ya numfasa ya ce, "idan za'a fara
bada tarihi na, za'ace na fara ne daga nemo ɓangaren
ruhina daya ɓalle. Saboda haka inaga zaman mu a
wannan kurkuku yazo ƙarshe, lallai inada mahaifiyata a
gabana bazan tsaya neman suna acikin wannan kurkuku
ba."
Babara ya rusunar dakai alamun girmamawa sannna ya
ce, "ya shugaba na akwai wata hanya banda idanuwanka
da zaka iya bawa mahaifiyarka izza da ban gaya maka ba."
Armad najin haka yai zumbur cikin murna ya ce, "ko?
Kamar ya fa?"
"Kamar yadda ka sani kowanne ɗan adam yana samun
ƙayyadaddun shekarun izza lokacin daya farkarda izzarsa,
kuma wannan adadi a ƙa'ida baya taɓa canjawa. Koda
kaima dalilin da yasa naka suka canja daga hamsin da
ɗaya zuwa dubu ɗaya dan kawai baka farkarda izzarka ta
haƙiƙa bane da farko.
"Amma akwai wasu hanyoyi guda biyu kacal wanda ake
iya ƙara yawan izza. Hanya ta farko na riga na gaya maka
ita. Ita ce ta amfani da sirrin dake cikin idanun ƴaƴan
Wilbafos. Hanya ta biyu wadda ban gaya maka ba ita ce
hanyarda ake kira da KWANGILA!!"
---
Mai kuke tunani ake nufi da fasahar KWANGILA?
**
Note
-------
Fasaha/Technique
Farkarda fasaha/Awakening
Sido-Urúrú/Pseudo-Ururu
Hatimi/Ancient runes
Dalasimai/spells
etcMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 83: Bango
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
Duk da gudun dokinsa Ubbaru saida Armad yai kwanaki
goma sha ɗaya yana tafiya sannan ya fara hango Bangon
arewa. Gangar ruwa iyakacin ganinka ta shafe kudu da
yamma gabas da arewa, tana ta kwaranya izuwa ƙasa
amma babu ko halitta ɗaya a samanta. Koda Armad ya
hangi wannan sai yaja linzami ya tsaya, inda ya buɗe
zoben sihiri da Nostaljiya ta bashi domin ya futo da
mahaifiyarsa.
Babara ya gaya masa duk bayan kwana biyu akwai wani
tsumi da zai ringa bata har zuwa lokacinda zai samu
wannan shekarun Izza ya bata. Shi dai wannan tsumi shi
ne abinda Babara ya ringa bata tsahon shekarunda
Armad yayi bayanan kuma har ya dawo ya same ta cikin
ƙoshin lafiya. A lissafin Babara mahaifiyar Armad tana
buƙatar aƙalla shekarun izza dubu goma kafin ta warke.
Wannan shekaru ba wani abu bane a wajen sarakunan
jinzidal masu fasahar kwangila, saboda haka Armad ya
gama yanke shawara kai tsaye wajen Nostaljiya zaije.
Kuma tunda a hannunsa akwai wani ɗalasimi daya karɓa
daga wajen Babara wanda zai iya gano masa inda ruhinsa
yake zai iya yin aiki biyu a lokaci ɗaya, yana neman
ruhinsa kuma yana neman Nostaljiya.
Amma koda wannnan tunani ya gilmawa Armad a rai
saiya tuno cewa ai bama abu biyu ba, lallai abu uku zaiyi
a lokaci ɗaya. Domin kuwa akwai alƙawari daya ɗauka na
kawarda cinikin bayi a ban ƙasa, wanda kuma bai manta
dashi ba. Koda tunanin haka sai Armad ya buɗe ƙofar
wannan zobe ya shiga inda ya samu waje ya rubuta sha
huɗu ga wata tara shekarar 1855 Bayan Amri. Wato dai a
wannan rana ce Armad ya fara shirinsa na rusa rukunin
Jinzidal.
Bayan ya gama kallon wannnan kwanan wata saiya juya
izuwa ɗakin daya ajiye mahaifyarsa, inda ya shiga ya
same ta a kwance, idanunta a rufe kamar tana bacci.
Mahaifiyar Armad tana bada yanayin kwarjini matuƙa
wanda saboda haka ba kowanne ma'aboci izza bane zai
iya tunkararta ba a hakan da take a sume. Gashin kanta
na nan baƙi, kuma kamar yadda wannnan cuta ta izza
take a har kullum alamar kawai shi ne mutun zai zamanto
a sume, amma banda haka babu wani abu dazai nuna
rashin lafiya kamar irinsu tari ko zazzaɓi.
Koda zama a gefenta sai kawai wani hawaye ya fito daga
idonsa, babu abinda yake tunawa sai lokutan da yana
yaro da kuma lokaci na ƙarshe daya ganta da lafiya.
Tsahon lokaci a haka kafin ya buɗe bakinta ya ɗisa mata
wannan tsumi dake cikin wata ƴar kwalba. Sannan ya
taso ya futo idanunsa cike da kwalla. Lallai akwai
abubuwa da dama da yake so ya tambayeta idan ta farka.
Saboda haka babu wani abu dazai tsaya a gabansa. Har
Armad yaje bakin ƙofar wannan zobe zai fita sai ya tsaya
ya juyo inda ya durƙusa yayi alƙawari, ƙololuwar
alƙawarinsa cewa a wannan fita kozai rasa ransa bazai
dawo ba sai mahaifiyarsa ta warke.
Yana fitowa ya rufe ƙofar wannan zobe sannan bayan
yaci abinci ya mayarda Ubbaru cikin zobensa ya kuma
nufi wannnan bango a ƙafa.
Yana isa gaban wannan bango wata izza irin wadda bai
taɓa jintaba ta dakeshi tayi cilli dashi gefe. Yana faɗuwa
yaga jikinsa ya fara narkewa, fatarsa tana ɓanɓarewa.
Nan take Armad yai sauri ya juyarda jikinsa izuwa
walƙiya. Wanda hakan ne ya cetoshi tunda hatta wuta
bata isa ta ƙona walƙiya ba.
Nan take Armad yai murmushi tare da cire zoben dake
hannunsa ya cilla a baki sannan ya ɗaga hannunsa sama
ya kirawo ɗaya daga cikin ɗalasimansa daya daɗe baiyi
amfani dasu ba wato Kaban'shisu. Idan mai karatu bai
mantaba wannan ɗalasimi ana iya amfani dashi ayi tafiya
acikin lokaci daga wani waje zuwa wani. Matsalarsa kawai
ita ce sai ɗaya kacal ake iya amfani dashi a shekara.
Tuntuni dai Armad yayi tunanin amfani da wannan
ɗalasimi ya fice daga cikin wannan kurkuku to amma bai
gama abinda ya shigo dashi ba, sannnan kuma baya son
yabar Babara anan.
Nan take ya ƙaddamar da wannan ɗalasimi, inda ya ɓace
daga inda yake. To amma a wannan lokaci maimakon ya
tsinci kansa a bayan wannan bango sai kawai ya ganshi
acikin tsakiyar bangon, kewaye dashi wani ruwa ne mai
tsananin danƙo. Abu na gaba daya biyo baya wasu
abubuwa ne manya-manya guda biyu suka bayyana a
gaban idon Armad.
Ɗaya daga cikinsu yana kama da wata daren goma sha
uku, ɗaya kuma yana kama da rana saidai dukkaninsu
baƙaƙe ne wuluk. Waɗannan abubuwa suka ƙura masa
ido tamkar wasu idanun mayunwaciyar kurar da taga
abinci. Nan take Armad yaji ya fara rawar ɗari. A lokacin
ne ya fuskanci cewa gaba ki ɗaya jikinsa ya narke babu
abinda ya rage face ƙoƙon kansa. Kuma wai a hakan ma
dan ya riga ya juyarda jikinsa izuwa walƙiya ne, lallai da
tuni ya tsinci kansa a lahira.
A wannan lokaci ya fuskanci abubuwa guda biyu. Na
farko dai bawai a waje ɗaya yake tsaye ba, hasalima
mugun gudu yake acikin wannnan bangon saboda
ɗalasiminsa na Kaban'shisu. Wanda hakan ya nuna masa
cewa saɓanin fahimtarsa da ɗalasimin bawai ɓacewa
yake yiba a lokacin da yayi amfani dashi, kawai dai
saboda tsananin sauri ne kawai yake ganin kamar ɓacewa
yayi.
Abu na biyu daya fuskanta shi ne wannnan abubuwa
guda biyu dake kama da rana da wata ba wasu abubuwa
bane illa idanuwa guda biyu na Ururu. Kuma hatta rawar
ɗarin da yake ji daga su ne.
A take Armad ya gane cewa lallai koda ya taho da Babara
lallai bazai iya wucewa dashi ba. Domin ba daban jikinsa
na walƙiya ba da tuni ya mutu aƙalla sau ɗari zuwa
wannan lokaci. Sannan kuma ya gano cewa yayi dabara
daya saka zobensa acikin bakinsa domin da tuni ya narke.
Ana cikin haka wannnan idanuwa guda biyu suka fara
haske suna fitarda wani yanayi mai firgitarwa. Ba shiri
Armad yaji tamkar ana caccaka masa allurai acikin kansa.
Abin mamaki sai kawai ya ganshi ya tsinci kansa a tsakiyar
filin yaƙi, kewaye dashi sarakunan Ashura ne guda goma.
Kowanne acikinsu yana riƙe da baƙar takobi. Kafin
Armad yai wani motsi su goma sunyi tafiya acikin lokaci
sun cake masa wannnan takubba acikin ƙirjinsa. Ko
motsi baiyi ba ya faɗi matacce. Abin mamaki a gaske ma
a wannna lokaci hankalin Armad ya gushe, babu wanda
ya sani ya mutu ko kuwa yana raye.
---------
A dai-dai wannan lokaci acan doron ƙasa ta farko
sarakuna goma mafi girma a duniya, wanda aka fi sani da
ASHURA, ne suke jin wata sarewa mai alamar ƙugen yaƙi
tana kaɗawa. Wannan sarewar nada ban mamaki tayadda
duk wanda yaji ta kawai zaiji sarewa ne amma banda
sarakuna goma na ASHURA. Su saƙo suke ji akan wani
mutun da yayi ƙoƙarin ficewa daga kurkukunsu. Amma
acewar wannan murya, idanuwan sarki Ururu
Kuyurussa'ayi, idanuwanda suka yaki sarki Eyriyon
Wibafos, sun halaka wannnan mutun har lahira
.
2)Yaku ma'abota karatun littattafan Hausa ga wata dama
ta samu. Wepsite din Hausaebooks
wanda zai ringa kawo maku littatafan hausa a cikin apk na ebook ya kuma baku daman downloading zuwa kan wayoyinku kyauta batare da sisin ku ba Zaku samu
sabbin littafai wanda babu su a kasuwa. Muna muku
barka da zuwa.
Yi hanzari ku ziyacemu
A shafin mu na facebook akan
www.facebook.com/hausaebooks
Nidinne dai Shuraih Usman inkiya
99%
Daga taskar magajin wilbafos

Hausa ebooks - pdf,txt and doc
www.hausaebooks.cf Download any kind of hausa ebooks hereMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 83: Dan Baiwa
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
____
Bayan gushewar hankalin Armad dukkan jikinsa saiya
fara juyewa daga walƙiya yana komawa toka. Kafin
ƙiftawar ido da bismilla Armad ya juye izuwa toka. Nan
take wannan toka ta narke acikin wannan ruwa kafin
daga bisani ayi watsi da ita ta dawo cikin wannan
kurkuku. Idan da zaka ga yadda akai watsi da wannan
toka zaka fuskanci cewa hatta ragowar tokar ba'a yadda
ta fita daga wannan kurkuku ba. Lallai abinda ake faɗa na
cewa indai ka shigo ka shigo kenan haka yake.
Amma ba jimawa ƙarfin fasahar Armad ta ƙara warewa,
wannan toka ta kama ci da walƙiya. Sannnan daga bisani
ta juye izuwa surar Armad, kafin daga bisani ta juye
izuwa Armad a kwance a sume yana aman jini.
Haka Armad yaci gaba da kasancewa acikin wannan hali
baisan inda kansa yake ba har tsahon kwana biyar. A
kwana na biyar ɗinne wasu mutane sanye da kayan farar
fatar raƙumi su biyu suka iso wajen. Dukkaninsu suna
kan ingarmar dawakai, sannan kuma suna riƙe da
takubba.
Na damansu ne ya fara sakkowa inda ya zunguri Armad
da ƙafa domin ya gano da rai ko ba rai. Kafin daga bisani
ya ɗaɗɗaure shi a jikin dokinsa kafin su koma da Armad
inda suka fito.
Armad bai san yadda akai ba, kuma bai san kwana nawa
yai ba, kawai dai ya farka ya tsinci kansa a cikin wata ƴar
bukka shishi kaɗai. Yai shiru yana tunano abubuwan da
suka faru dashi acikin bango, inda nan take wata tambaya
ta faɗo masa. Shin ya fita daga kurkukun ko kuwa har
yanzu yana ciki. Abu ɗaya daya sani shi ne idanda da
matsala da lallai acikin ankwa zai ganshi, amma gashi nan
a sake akan gado.
A wannan lokaci yaji surutan mutane a waje saboda haka
nan take ya gano cewa hanya ɗaya dazai samu amsar
wannan tambaya shi ne ya fita waje ya tambayi ɗaya
daga cikin mutanenda yaji suna magana a wajen tantin.
Saboda haka ba tare da tunanin mai zai faru ba Armad ya
buɗe ƙofa ya danna kai waje. Abin mamaki yana fitowa
yaga babu ko mutun ɗaya dake gadinsa, suma masu
wannan magana suna can gefe kuma kallo ɗaya sukai
masa suka ɗauke kai suka ci gaba da hira.
A kewaye da wajen duk irin wannan bukkoki ne sama da
hamsin. Daga gaba garesu kuma akwai wannan ruwa da
ake kira da bango, lamarinda yasa Armad ya gano cewa
lallai akwai matuƙar yiwuwar haƙarsa bai cimma ruwa
ba. Ajikin bangon akwai wani baƙin ƙarfe wanda yai sama
sosai tayadda ba'a iya gano ƙarshensa.
Akwai mutane a wajen amma basu da yawa, kuma abin
mamaki ba ruwan kowa da kowa, kowa harkarsa kawai
yake. Can dai Armad ya kasa daurewa ya tare wani mutun
sanye da jallabiya ya tambayeshi, "Malan da ALLAH ina ne
nan?"
Mutumin ya kada baki ya ce, "baka ma san inda kake ba.
Kaine wanda aka ce yayi ƙoƙarin shiga ta cikin bango kai
tsaye ko?" Mutumin na faɗar haka ya wuce gaba ba tare
da amsawa Armad tambayarsa ba.
Armad ya haɗe rai yana niyyar finciko mutumin baya sai
yaji murya a gefensa. "Kana shalkwatar ƴan-daban ƊAN-
BAIWA."
Armad ya juyo da kansa ɓangaren inda yaji muryar inda
yai arba da wani saurayi kalar larabawan yamma mai
yawan dogon gashi mai launin ja da fari. "Shalkwatar
ƴan-daban ƊAN-BAIWA? Wane ne ɗan-baiwa kuma?"
Saurayin ya ja dogon farin gashin dake kansa tare da yin
murmushi yana cewa, "kamar yadda ka sani wannan
kurkuku an rabata tsakanin ɓangarori guda uku. Shekara
ɗaya baya, ɓangare ɗaya basa ƙoƙarin guduwa daga
wannan kurkuku, amma dama can ɓangarori biyu sun
daɗe suna ƙoƙarin guduwa. Amma a yanzu hatta
wannnan ɓangare ƙoƙarin guduwa suke. Wanda hakan
ya jawo sauye-sauye da dama acikin wannann kurkuku.
Da dama ana ganin wannan canji yana faruwa ne saboda
bayyanar wannan mutun da ake kira da ƊAN-BAIWA,
duk da babu tabbashi akan wannan maganganu amma
lallai a yanzu sama da kaso sittin na wannan kurkuku
suna biyayya ga wannan mutun mai suna ɗan-baiwa.
Babu wanda yasan daga inda yake ko kuma tayaya ya
shigo wannan kurkuku amma bisa mamaki tuni jama'a
suka naɗashi a matsayin sarkinsu. Suna na Indimi Iyyka
Citta Sailari Abati. Ni ne na ceto ka daga inda ka suma."
Wannan mutun ya kammala bayaninsa da miƙawa
Armad hannu su gaisa.
Abubuwa da dama Armad bai fahimta ba saboda haka yai
shiru yana tunanin mai zaice masa. Baima kula da dogon
sunan wannan saurayi ba. Koda saurayin yaga haka sai
yai tunanin ko Armad bai yadda dashi ba ne, saboda haka
ya ce, "Kada da damu, dani da abokina muka ceto ka.
Kuma a wannan waje babu wanda ya damu dakai, sai dai
kawai kai sani cewa muna zaune Tsarin dake jikin bangon
nan ya fara haske irin wanda ke nuna cewa wani yayi
ƙoƙarin guduwa. Hakan ne yasa akai ƙungiya ta mutun
bibiyu domin su kewaya su gano inda abin ya faru. Ta
haka ne dani da wanda aka haɗani muka gano ka."
Armad ya numfasa ya ce, "nagode. Amma ina da
tambayoyi da yawa. Da farko dai wanne sunanka acikin
sunayen daka gayamin?"
Saurayin yai murmushi tare da cewa, "suna na Indimi
Iyyka Citta Sailari Abati. Kada ka damu a hankali zaka riƙe
su. Da dama sukan ɗau lokaci."
Armad yaja numfashi mai tsayi kafin ya girgiza kai. "To
amma menene manufar wannan shugaba naku mai suna
Ɗan-baiwa? Sannan kuma shin zan iya tafiya idan ina
so?"
Wannan saurayi mai dogon suna ya ce, "Eh zaka iya tafiya
mana, amma idan har kana so kaga Ɗan-baiwa to ka
tsaya domin kuwa yau zai biyo ta wannan waje."
Armad ya tsaya yana tunani kafin daga bisani yai ajiyar
zuciya. Babban abin shi ne duk wata tambaya da Armad
yayi wa saurayin bao amsa masa ita ba kai tsaye.
Hasalima har yanzu bai masan taƙamaimai meke faruwa
ba. Daɗin daɗawa jikimsa bai gama warewa ba.
Yana cikin tunani yaji muryar wannan saurayi a kunnensa
yana cewa, "zo kaga zanensa kafin ya ƙaraso." Saurayin
yaja Armad izuwa wata kwana. Suna isa wasu mutane ne
guda shida suke ta kallon wani ƙaton zane dake kafe a
jikin bango.
Suna matsawa kusa sai Armad ya fara jin abinda suke
cewa. "Shi ne Ɗan-baiwa. Yadda ka ganshi a jikin hoton
nan haka yake a gaske. Kana ganinsa kasan jarumi wanda
zai iya canja duniya."
Koda Armad yaji wannan kalamai sai ya ƙara azama
domin yaje ya ga wannan ɗai-baiwa da idonsa. Amma
yana isa ya tararda hoton wanda ya sani kamar tafin
hannunsa ajikin wannan zane.
Wannan dai ba wani bane illa Ikenga O Bayajidda.
Koda ganin wannan zane sai Armad yaja da baya cikin
tsananin mamaki da ɗimuwa. Ya dubi wannan saurayi
mai dogon suna ya ce, "Wannan ne ɗan-baiwan?"
Saurayin ya kyaɗa kai, "Eh shi ne. Kasan shi ne?"
**
.
2)Yaku ma'abota karatun littattafan

Please Login or Register in order to submit comment