Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ne, idan ɗalasimi guda ɗaya ya wutar
dashi rabin hanya an watsoshi waje, to idan yayi amfani
da ɗalasimi goma a lokaci ɗaya zai iya wucewa.
Daɗin daɗawa wannan sabuwar fasaha ta Armad zata
bashi damar cin galaba akan abokan fafatawarsa cikin
sauƙi. Domin kuwa komin sharrin daya tunkaro shi zai
iya ɓacewa ya dauje masa. Sannan zai iya bayyana a
bayan abokin fafatawarsa ya aiwatar da harinsa ba tare
da an ankara ba.
Armad yayi niyyar sakawa wannan fasaha sabon suna
amma daga ƙarshe ya yanke shawarar yaci gaba da
kiranta da Kaban'shìsu.
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 89: Hannun Aradu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Armad na tafe yana goge takobinsa, rabonsa da amfani
da takobi an kwana biyu. Kai hatta harin ƙawanyar-walƙiy
a an daɗe rabonda yayi amfani dashi. A iya tunaninsa tun
bayan fafatawarsa a gasar Jinzidal. A halin yanzu
hannunsa ƙaiƙayi yake, saboda haka maimakon ya
kewaya ya zagaye wannan daji sai ya yanka ta tsakiyarsa.
Ai kuwa ko taku goma bai yiba Dordor uku masu kai ɗai-
ɗai da wasu aljanun-shirwa guda biyar suka tunkaro shi.
Dordor suna kawo masa hari ta ƙasa, shirwa na kawo
masa hari ta sama. Armad yai murmushi tare da dunƙule
hannunsa na dama. Sannan ya juyarda dashi izuwa
walƙiya ya daki iska dashi yana cewa, "HANNUN-ARADU."
Haka na faruwa wata farar walƙiya mai layin kore-kore ta
fara ɓulɓula daga hannunsa tare da afkawa wannan
shirwowi da Dordor. Wannan shi ne karo na farko da
Armad yayi amfani da wannan fasaha mai suna Hannun-
aradu, wadda ta banbanta matuƙa da ƴar walƙiƴar daya
saba amfani da ita ada. Idan ka kalli dunƙulen hannunsa
na dama zaka ga ya juye izuwa walƙiya sannan kuma
walƙiya tana ɓulɓula daga cikinsa tamkar ana ambaliyar
ruwa. Duk abinda wannan walƙiya ta taɓa saita narkar.
Babu wani abu dake tsaye a gabanta face Armad
Wilbafos. Bayan daƙiƙa bakwai Armad ya saki hannunsa
ya ɗauke walƙiyar sannan yai duba izuwa abinda ya
aikata.
Dukkan abubuwan dake gabansa sun ƙone ƙurmus, babu
shirwa babu Dordor babu koda bishiyu da suka rage.
Babu komai sai ƙarfin izzar Armad wilbafos. Wannan daji
ya ƙone ƙurmus tamkar ba'a yishi ba. Daga inda Armad
ke tsaye yana hango Bango.
Armad yai murmushi tare da tunkararsa. Tuni dai ya
gano wata hanya da zaiyi amfani da ita domin ƙirƙiro
sabuwar fasahar takobi amma ba sauri yake ba zata iya
jira. Saboda haka ya tunkari wannan Bango gadan-gadan.
Yana isa ya juye izuwa walƙiya sannan ya kira ɗalasimin
Kaban'shísu.
Armad ya tsinci kansa a tsakiyar wannan ruwa mai kauri
wanda ke narka jikin ɗan adam. Yana bayyana ya ƙara
ido biyu da wannan baƙaƙen idanuwa na Ururu. Amma
tuni Armad ya shirya musu, kafin wani abu ya faru tuni
ya ƙara kiran wani ɗalasimin, ya ɓace daga inda yake ya
bayyana a gaba da inda yake. Wannan idanu suka ƙara
bayyana suna neman haɗiye amna Armad ya ƙara
ɓacewa da taimakon sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu.
A haka saida Armad yayi amfani wannan ɗalasimi sau
goma, a kowanne lokaci yana ƙara kusantar ƙofa amma
wannan idanu suna ƙara cimmasa. Armad yasan
iyakacinsa ɗalasimi goma, kuma indai ya wuce haka to a
take zai fara aman jini ya sume. Amma babu yadda zaiyi,
baiyi tunanin ɗalasimi goma baza su isa ba. Saboda haka
ya rufe ido ya ƙara kiran wannan ɗalasimi a karo na
goma sha ɗaya. Abun mamakin shi ne duk da yana
walƙiya amma hakan bai hanashi aman jini ba da jin zafi
da radaɗin wannan ɗalasimi ba.
Gabda Armad zai sume ya ga wani haske ya rufe masa
ido, bashi da tabbas mene ne amma yana fatan hasken
fita daga kurkukun ne.
**
A can doron ƙasa na farko kuwa wannan sarewa dake
gadin wannan kurkuku ce ke ƙara bada labarin wani mai
ƙoƙarin ficewa daga cikin kurkuku. Amma a wannan
karan ya samu damar fita, sannan kuma abin mamaki
irin ruhi ɗaya ne sak da wancan mutun da yayi ƙoƙarin
fita a watan baya.
Nan take wannan sarewa ta bada umarnin ayi maza-maza
a kamo wannan mutun sannan a gane mene ne alaƙarsa
da wancan mutun da yayi ƙoƙarin guduwa a watan baya.
Shin duk mutun ɗaya ne bai mutu ba ko kuma wani ne
mai irin ruhinsa.
Gidan Uznu Ururu shi ne gidan da aka ɗorawa alhakin
kamo wannan fursuna.
**
Al'ada ce sananniya kwararrun matuƙa jirgin ruwa sukan
sakawa jiragensu sunaye. Wani suna kawai na sha'awa ne
wani kuma yakan dace da tsarin jirgin. A dai-dai wannan
lokaci wani madaidaicin jirgin ruwa ne ke tafiya akan
Bangon arewa ya nufi doron ƙasa ta huɗu, daular Sisiya.
Sunan wannan jirgi Fataken-dare. Yakan ɗauki jama'a
aƙalla ɗari biyu da hamsin zuwa ɗari uku, kuma shaidar
safararsa tana tsakanin doron ƙasa ta uku data huɗu.
Duk da kasancewar yawan ƙofofin Eycigan da ake tafiya
ta cikinsu amma duk da haka masu sana'ar jirage basu
rasa abinci ba, indai ka yiwa jirgin ka shaidar kariya ta
hukumar tafiye-tafiye ta sarakunan jinzidal to zaka samu
fasinja. Rashin yin shedar na nuna kana daga ɓata gari ku
kuma ɓarayin ruwa.
Jirgin Fataken-dare na tafiya sannu a hankali iska na
kaɗashi izuwa hanyarsa. Fasinjojin wannan jirgi na
harkokin gabansu cikin kwanciyar hankali, sun san nan
da wata ɗaya mai zuwa zasu isa garuruwansu a daular
Sisiya.
Shi kuwa kyaftin ɗin wannan jirgi sunansa Bisaiya Sisiyu.
Asalinsa ɗan daular Sisiya ne kuma tunda ya taso yake yin
sana'ar kwandasta a irin wannan jirage, yanzu gashi a ɗan
shakara talatin ya mallaki nasa jirgin. Duk da bashi da izza
amma yana da ma'abota izza guda shida dake aikin tsaro
a jirginsa. Kuma ko a wannan lokaci mutun biyu daga
cikinsu na tare dashi.
Bisaiya ya dubi ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ce, "idan
iska ta bamu dama nanda kwanaki ashirin zamu isa. Shi
yasa dole saina ɗauki ma'abocin aljanin iska aiki."
Mutumin sanye da fararen kaya ya gyaɗa kai yana cewa,
"gaskiya ne, kyaftin Bisaiya. Amma duk da haka ina
tunanin zamu isa a yadda muka tsara."
Bisaiya baice komai ba, kawai yaci gaba da kallon gangar
ruwan dake gabansu. Yana sane da cewa ƙaro wani
ma'aikacin dole zai jawo ya kori ɗaya daga cikin
ma'aikatansa shida dan bazai iya biyansu ba, amma dole
yana buƙatar wanda zai ringa ɗaure masa 'iska' a yayin
tafiyarsu.
Yana cikin wannan tunani ne sai ya hango wani abu
kwance a gaban jirginsu. Abun yana ta iyo yana sama da
ƙasa kamar ƙirgin itace. Da farko Bisaiya bai ɗauki wani
abu ba saida yaga abin yana motsi kamar ɗan adam. Nan
take ya haska fitilar jirgin saitin abun domin ya
tabbatarwa da idonsa. Ai kuwa wani saurayi ne kwance a
sume ba kaya a jikinsa.
Abu na farko daya fara zuwa ran Bisaiya shi ne wannan
ɗaya ce daga cikin dabarun ƴan fashin ruwa. Domin ka
tsaya ceto suyi maka fashi.
MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 90: Sa'a ko Kaddara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
"Ɗakko shi." kyaftin Bisaiya ya umarci ma'aikacin dake
gefensa daya ɗakko gangar jikin wannan saurayi dake
yawo akan ruwa.
Ba jimawa aka shiga da wannan saurayi cikin ɗakin duba
marasa lafiya na jirgin tare da kirawo wani siririn mutun
sanye da fararen kaya ya dubashi. Idan kayi duba izuwa
wannan saurayi zaka ga ba wani bane illa Armad
Wilbafos.
Shi kansa kyaftin Bisaiya bai san mai yasa ya ceto shi ba,
duk da kuwa yana tunanin ƴan fashi. Amma koda yaga
Armad sai ya zare ido cikin mamaki tare da fara tunanin
mai ya kamata yayi.
Abin mamaki duk da Armad na numfashi amma sun kasa
farkar dashi.
"Ransa yana hannun ALLAH. Amma tashinsa zaiyi
wahala." Likitan ya bayyana wa kyaftin Bisaiya bayan yayi
iya yinsa ya kasa.
A kwana a tashi saida Armad yai sati ɗaya cir a sume kafin
ya farka. Bayan ya buɗe ido ya fara ganin dishi-dishi kafin
daga bisani ya warware ya fara jin surutan fasinjojin
jirgin suna tattauna rayuwa.
Armad ya daddagira ya sakko daga kan gadon inda ya
nufi bakin ƙofa. Jikinsa na nan yadda yake babu gajiya ko
tsami. Yana isa ya buɗe ƙofar, hasken rana ya haske masa
ido lamarinda yasa ya kare da hannunsa. Iska mai ɗumi
ta daki fuskarsa lamarinda ya gano lallai ya rabida
wancan sanyi da ƙanƙara na cikin kurkuku.
"Kunga ya farka... "
"Ashe zai rayu.."
"Yana da ƙarfin ruhi..."
"Kai yaushe rabon da naga wanda yai sati a sume kuma
ya rayu.."
"Ko maiya sameshi?"
Haka dai Armad ya fara tsintar maganganu fasinjojin
daga nesa. Ga dukkan alamu kowa ya san da zuwansa.
Armad ya gano cewa ɗakin cin abinci ya buɗe bayanda ya
fuskanci cewa jama'ar na zaune a zagaye da tebura na
abinci.
"Koma ka kwanta karka faɗi.." Likitan jirgin ya tallafi
Armad ta gefe. Abinda bai sani ba shi ne Armad tar yake
jinsa kamar ya rungumi zaki. Juyewar jikinsa izuwa
walƙiya yana bashi damar shanye gajiya da ciwo cikin
ƙanƙanin lokaci.
Armad ya dubi likitan ya ce, "Ehmm... Nagode amma naji
sauƙi. A ina nake?"
Likitan ya amsa da cewa, "kana cikin jirgin Fataken-dare,
muna hanyar zuwa doron ƙasa ta huɗu daular Sisiya."
Armad najin wannan jawabi yai murmushi tare da cewa,
"Sa'a ko ƙaddara?"
Likitan bai gane mai Armad ya ce ba saboda haka ya
tambaya, "Sa'a ko ƙaddara? Mai kake nufi?"
Armad ya amsa da cewa, "Ba komai. Kawai dai nima
hanyar Sisiya nayi, ban sani ba ko zaku taimaka ku isar
dani domin bani da ko sisi tare dani amma idan muka isa
akwai wacca zata ranta min na biya ku."
Koda jin wannan batu sai Bisaiya ya taso a fusace, "Da
kuɗinka nake buƙata da ban ceto ka ba. Kai dai kawai ka
samu sauƙi kurum."
Armad na ganin Bisaiya ya gane shi ne kyaftin din wannan
jirgi. Saboda haka yai shiru yana kai-komo da karamcin
da Bisaiya yake nuna masa a zuciyarsa kafin ya kyaɗa kai
cikin murmushi yana godiya. "Nagode."
"Zo ga abinci." Bisaiya ya kira Armad izuwa teburinsa.
Tuwo da nama haɗe da kifi soyayye sune cike a kwanon
da aka turowa Armad. Cikin annushuwa ya fara danna
tuwon nan yana korawa da sanyayyar fura samfurin
daular Sisiya. Kowa idonsa na kansa amma ko a jikinsa.
Kan kace meye wannan tuni ya gama da kwanukan dake
gabansa.
"Bari a ƙaro ma, lallai yunwa kake ji." Bisaiya yai odar
wasu kwanukan. Armad baice a'a ba, koba komai baya so
mutanen wannan jirgi su fara yi masa kallon aljani wanda
baya buƙatar abinci.
Bayan ya ci ya sha sai Bisaiya ya kaishi wani ɗaki domin
ya huta. "Ga ɗakinka kafin mu ƙarasa. A lissafi na nanda
sati biyu zuwa uku zamu isa."
Armad yai godiya, har ya doshi ɗakin saiya waiwayo ya
dubi Bisaiya yana cewa, "baza ka tambaye ni daga ina na
fito ba. Baka tsoron ɓarayin ruwa ko kuma na jawo muku
wata matsalar?"
Bisaiya yai murmushi, "Tuni nasan ko kai waye, Armad
Wilbafos. Amma ka kwantar da hankalin ka babu wanda
ya gane ka acikin fasinjoji na."
Nan take Armad yaja da baya ido a zare yana cewa, "mai
kake nufi? Ya akai kasan suna na?"
Bisaiya ya kada baki ya ce, "Kada ka manta hotunan ka
sun baza ko'ina. Kuma duk wanda ke karanta jarida yasan
fuskarka. Saboda haka nasa likita na yaɗan kyara maka
hanci da baki da ido." Yana magana ya nunawa Armad
mudubi.
Abu na farko da Armad ya gani shi ne hancinsa ya loma
ciki sannan ya gajarce kamar na biri. Idanunsa sun futo
waje sun zama manya-manyan kamar na masu maƙoƙo.
Sannan bakinsa ya ƙara faɗi kamar an yaga. Kalmar farko
data zo bakimsa zagi ne amma ya fasa, "Kut... wa yasa ku
mai dani haka?"
Bisaiya ya dubi Armad babu alamun wasa a fuskarsa,
"Idan ban maida kai haka ba ya zanyi da fasinjoji na idan
suka gano akwai Ayrid miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar
acikin jirgin?"
Armad yai zumbur ya buɗe baki kamar wanda wani abu
ya faɗo masa, "Idan haka ne to mai yasa kai baka miƙa ni
ba? Ko kana jira ka isa gaɓa ne ka miƙa ni?"
Bisaiya ya amsa da cewa, "ba zance maka ka yarda dani
ba, amma nayi maka alƙawarin baza ka samu matsala
daga jirgi na ba. Shekarar mahaifina bakwai a kurkuku
yanzu, saboda an saka kuɗi akansa akan abinda bai kai ya
kawo ba. Kaima ina da yaƙinin ba wani abu ka aikata ba
aka dora wannan kudi akanka. Kawai dai ana so a wanke
gimbiya Nostaljiya ne a ɗora maka laifi saboda kai baka
da galihu. Idan baka yadda dani ba zaka iya sauka a
kowanne lokaci." Yana rufe baki ya juya ya bar Armad a
tsaye a wajen.
________
Shuraih 99%
.
Ai tunda aka ce za'abani Gimbiya Zahra (Nostolgiya Nara) na kidime kuma zan jajirce matuka wajen sambado maku da littafin nan har karshe,
Sai ku jirani zuwa MAKO mai zuwa ta yiwu ma ku jini Gobe, amma fa sai na ga Respond naku akan wayannan MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 91: Gashin Belbela
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Kwanan Armad shida acikin wannan jirgi yana ta kai-
komo da abubuwan dake ransa. Abu na farko gaskiyar
mutanen cikin wannan jirgi, zai iya amince musu ko
kuwa. Abu na gaba mai zaije ya tarar a daular Sisiya.
Tunda Armad yake bai taɓa saka ƙafa a babban birnin
ɗaya daga cikin garuruwan sarakunan Jinzidal ba, saboda
haka bai masan mai zai tarar ba. Yaya yanayin garin yake?
Shin wacce irin karɓa Nostaljiya zata yi masa? Abu ɗaya
da yake da tabbas dashi shi ne mahaifin Nostaljiya
Bihanzin mai dauwamammen sara bazaiyi murna da
ganinsa ba. Ko a gamuwarsa ta farko kuma ta ƙarshe
guduwa yayi dan kada su haɗu.
Duk da Armad bai ga laifin Bihanzin wajen ƙoƙarin kare
ƴarsa ba amma yana jimamin haɗuwa dashi.
Musamman duba da cewa wannan shi ne karo na farko
da zai gamu da Sarkin Jinzidal.
Sannu a hankali Armad yaci gaba da gudanar da ragowar
kwanakinsa acikin wannan ɗaki da Bisaiya ya bashi.
Lokuta kaɗan yake fita yaga hasken rana saboda baya so
wani acikin jirgin ya gane shi. A rana ta bakwai yana
kwance akan gado yana tunanin yadda rayuwarsa take
kasancewa sai kurum ya fara jin hayaniya daga waje.
Da farko Armad yayi tunanin fasinjojin ne ke caca kamar
yadda suka saba, amma ba jimawa ya gane cewa
hayaniyar tafi ta haka.
Bayan ya ɗauki daƙiƙa ashirin yana nazarin hayaniyar
saiya fuskanci ƙaraji ne kawai da ƙuwwa. Nan take
Armad ya yasan faɗa ake. Kodai ƴan fashi sun kawo
musu hari ko kuma faɗa ya kaure tsakanin fasinjojin
jirgin. Koma dai wanne ne bai shafi Armad ba. Koda ƴan
fashi ne, kowanne jirgi yana da dabarun kare kansa daga
irin haka. Rufe idonsa kawai yayi, yaci gaba da nazarin
yadda zaiyi ya gamu da Nostaljiya zarar ya isa daular
Sisiya.
Abu kamar wasa sai Armad yaji ihun ya fara raguwa,
lamarinda yasa yayi tunanin cewa anci galaba akan ƴan
fashin. Amma kuma wata zuciyar ta gaya masa cewa
lokacin yayi ƙaranci ace har an gama da ƴan fashin.
"Hmmm..." Armad yaja dogon numfashi tare da girgiza
kai. Bai san mai yasa ba amma hankalinsa yaƙi kwanciya,
saboda haka ya rufe idonsa ya fara laluben yanayin-izzar
ma'aikatan jirgin. Nan take ya miƙe zumbur ya nufi ƙofar
ɗakinsa. Yana buɗewa wani koren hayaƙi mai ratsin yalo
yai masa sallama. A ƙasan hayaƙin mutane ne fululu a
kwance sun sume.
Armad na ganin haka ya gane maike faruwa. Wannan
hayaƙi guba ne kuma shi ne dalilin suman mutanen cikin
jirgin. Koma waye ya feso wannan hayaƙi ba abokin
Armad bane.
Armad ya riƙe numfashinsa tare da tsayawa, tsaiwa irin ta
ma'abota izza, sannan kai tsaye ya afka cikin hayaƙin.
Bayan kimanin taku uku sai ya tsaya ya buɗe bakinsa ya
huro iska waje. Amma maimakon iska sai feshin walƙiya
ya fara ambaliya daga bakinsa. Kan kace meye wannan
tuni feshin mai ɗauke da walƙiya ya kawar da wannan
hayaƙi.
A wannan lokaci Armad ya gane ashe wani ƙaton jirgin
ruwa ne ɓoye cikin duhu a gaban jirginsu. Girman jirgin
yasa jirgin su Armad ya zama kama wani ɗan kwale-
kwale. Daga inda Armad ke tsaye yana hangen sunan
jirgin ansa GASHIN-BALBELA da manyan baƙi.
Armad ya dawo da hankalinsa kan mutanen da ke cikin
jirginsa. Da yawansu wannan hayaƙi yasa sun sume,
amma wasu na tsattsaye. Ga dukkan alamu hayaƙin bacci
kawai yake sawa kuma rayuwarsu bata cikin hatsari. Har
Armad zaiyi ajiyar zuciya ya godewa ALLAH saiya hango
Bisaiya kwance cikin jini riƙe da ƙirjinsa. Ƙarshen kibiya
ya leƙo ta gaban ƙirjinsa. Dukkan ma'aikatan tsaron su
shida na kewaye dashi suna ƙoƙarin taimakonsa.
Armad na shirin ƙarasawa ya bada nasa agajin yaji murya
daga cikin Gashin-balbela.
"Ku bamu dukkan kayayyakin ku da makaman ku idan
kuna so ku tsira da ranku."
Kyaftin ɗin jirgin shi ne yai wannan kashedin, amma a
bayansa akwai ma'abota izza guda goma sha bakwai.
Babu ko tantama jirgin ɓarayi ne domin ko fasinja ɗaya
babu acikinsa.
Armad ya dubi ma'aikatan jirginsa guda shida yaga
dukkaninsu sun cika da tsoro, babu ko alamun kwarin
gwiwa a tattare dasu. Ya juya izuwa ragowar fasinjojin da
bacci bai ɗaukesu ba yaga tuni wasu daga cikinsu sun
fara tattaro ragowar kayayyakinsu da niyyar miƙawa
wannan ƴan fashi.
Ana haka Armad ya lura da wani jarumin saurayi tsaye
akan Bisaiya riƙe da takobi, idonsa babu ko alamar tsoro.
Cikin ƙiftawar ido Armad zai iya ƙarar da wannan ƴan
fashi amma mutanen jirginsa zasu gane waye shi, wanda
kuma hakan zai jawo masa matsaloli da dama a yayin
tafiyarsa. Daɗin daɗawa wannan ƴan fashi basu cancanci
ya kashe su ba indai ba wani suka taɓa ba, sannan kuma
fasinjojin jirginsa sun yadda da sharaɗin ƴan fashin.
Wasunsu tuni sun fara haɗo kayansu. Armad ya yanke
shawara maimakon yaƙar wannan ƴan fashi kamata yayi
ya fara ƙoƙarin ceto rayuwar kyaftin Bisaiya. Saboda
haka ya nufi inda yake.
Yana isa ya fuskanci cewa wannan kibiya a kusa da
zuciyar Bisaiya ta cake, lallai ana taɓa ta zai rasa ransa.
Duk ƴadda akai hayaniyar farko daya ji ƴan fashin ne
suka fara yi musu sallama da kibbau kafin su aiko
wannan hayaƙi maisa bacci.
Kala-kalar tunane-tunane suka fara yawo a zuciyar
Armad. Akwai tausayi na mutumin daya taimakeshi,
akwai kuma haushi na wannan ƴan fashi.
Ana haka Armad yaji wannan saurayi dake riƙe da takobi
yayi ƙaraji ya afkawa Gashin-balbela. Wuta ce mai
ruruwa tayi tsiri ta tsinin takobinsa ta daki akalar Gashin-
balbela. Nan take wajen da wutar ta daka ya tsage, jirgin
ya fara ƙara zai fashe. Ana cikin haka ɗaya daga cikin
jaruman dake cikin Gashin-balbela ya tafa hannunsa, ya
samarda wata ƙanƙara wadda ta ɗinke wajen daya tsage.
Sadaukin ya ƙara tafa hannunsa ya samarda ƙatoton
mutun-mutumin ƙanƙara wanda ya aikawa saurayin da
saurin gaske. Kafin saurayin yai wani abu ƙanƙanra tayi
masa akwati. Armad ya lalubi izzar wannan saurayi yaji
hamsin da ɗaya ce kamar tasa a lokacin daya fita daga
gida. Shi kuwa ma'aboci ƙanƙarar izzarsa shekaru ɗari da
sha bakwai ce.
"Yaro kayi ganganci. Babu wanda ya isa ya kwana da rai
bayan ya taɓa min Gashin-balbela." Kyaftin ɗin jirgin
Gashin-balbela ya gayawa saurayin. Kafin ya juyo ga
mutumin dake gefensa. "Kawo min kansa."
Mutumin yai tsalle ya diro cikin Fataken-dare. Sannan ya
zare takobi ya nufi saurayin da niyyar sare masa kai.
A wannan lokaci ne Armad yai tsawa mai tsananin
firgitarwa daga yake zaune. Abin mamaki Armad bai ɗaga
muryarsa ba, amma babu wanda baiji tsawar ba har cikin
ransa, musamman mutanen cikin Gashin-balbela.
Nan take wannan sadauki daya tunkaro saurayin ya tsaya
cak a inda yake, kafin gumi ya fara keto masa. A hankali
ya ɗaga kansa cikin tsoro yai tsinkaye da ma'aboci
wannan tsawa, lamarinda yasa ya fara karkarwa kamar
wanda aka jefa tubalin ƙanƙanra acikinsa.
Armad yakai ƙololuwar ɓacin rai, kuma tuni ya yanke
shawarar nitsar da Gashin-balbela. Ya dubi wannan
sadaukin dake ƙoƙarin kashe saurayin ya kirawo ɗaya
daga cikin kalaman izzarsa, "Sanyin-babban-sihiri!"
Nan take ƙanƙara ruwan toka ta haɗiye sadaukin. Armad
ya nunashi da ɗanyatsansa, lamarinda yasa ƙanƙarar ta
tamke shi tamau kamar zata fasa ƙasusuwansa. Kan kace
meye wannan ya faɗi ƙasa sumamme.
Armad ya dubi kyaftin ɗin Gashin-balbela ya ce, "idan
kana so ka tsira da ranka, toka koma inda ka fito. Amma
kayi sani cewa anan zaka bar wannan jirgin naka."
**MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 92: Maikiro Inara
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Armad bai jira amsar ƴan-fashin dake cikin jirgin Gashin-
balbela ba ya wuce izuwa wannan saurayi ya rusa akwatin
ƙanƙarar daya rufe shi. Sannan ya juya izuwa jirgin dake
gabansa.
Kyaftin ɗin cikin jirgin, wanda ƴan daƙiƙu kaɗan da suka
wuce shi ne ya bada umarnin a kashe wannan saurayi
saboda ya taɓa masa jirgi, shi ne ya fara yin tsalle ya afka
cikin ruwa. Kafin daga bisani sauran ƴan fashin su bishi.
Lallai duk wanda ya rayu a wannan zamanin yasan
menene sanyin-babban-sihiri, babu ko tantama akwai
ratar izza mai yawan gaske tsakanin mutumin da yake iya
sarrafa sanyin-babban-sihiri da wanda bai iya ba.
Armad yai ajiyar zuciya sannan ya juya izuwa kyaftin
Bisaiya, a lokacin ne ya gane cewa dukkan mutanen dake
cikin jirgin kallonsa suke kamar wanda suka ga wani
mala'ika. Kowa ƙoƙari yake yasan wane ne shi.
Kasancewar Armad yana iya sarrafa sanyin-babban-sihiri
hakan na nuna yakai aƙalla izza shekaru dubu ɗaya,
wanda hakan ke nuna Armad ya futo daga ɗaya daga
cikin manyan dauloli biyar na ƙasa bakwai. Domin kuwa
bawai abu ne mai sauƙi ba ka samu wanda shekarun
izzarsa suka kai dubu, saboda duk hanyoyin da ake iya
samun izzar da takai dubu hanyoyi ne wanda zaiyi
matuƙar wuya wanda baya cikin wannan dauloli ya
samu.
Koda isar Armad saiya tarar Bisaiya na kakarin mutuwa,
inda yana ganinsa yayi masa manana jini na fita daga
bakinsa. "K....kayimin abu ɗaya badan na... isa.. ba."
Armad ya riƙe hannunsa cikin tausayi. Bai san mai Bisaiya
zaice ba amma kawai ya kyaɗa kai.
Bisaiya ya ɗaga ɗan-yatsansa da kyar yai nuni izuwa
wannan jarumin saurayi ya ce, "Ka kularmin da ɗana."
Armad najin haka ya zare ido cikin mamaki da al'ajabi.
Tun farko dai bashi da masaniyar Bisaiya nada ɗa, sannan
kuma shi kansa wahalhalun kansa sun masa yawa
ballanta ace ya kula da wani. To amma a halinda Bisaiya
ke ciki na gabda mutuwa babu yadda za'ai yace masa a'a.
Daɗin daɗawa kafin Armad ya gama tunani yaji kakarin
da Bisaiya ke yi ya ƙaru, kafin daga bisani ya faɗi
matacce.
Armad na ganin Bisaiya ya mutu ya canja shawara yai
tsalle ya faɗa cikin ruwa yabi wannan ƴan fashi. Cikin
ƙanƙanin lokaci sai gashi ya dawo dasu a ɗaure cikin
igiya. Wannan saurayi na zaune a gefen Bisaiya yana
hawaye. Sauran ma'aikatan cikin jirgin duk kuka suke,
kana gani kasan sunji daɗin aiki da Bisaiya. Duniya
budurwa wawa, yanzu kake da rai in anjima babu. Waye
zai taɓa tsammanin Bisaiya wanda ke da cikakkiyar lafiya
ƴan daƙiƙu da suka wuce zai faɗi matacce yanzu.
Su kuwa sauran fasinjoji wanda ke kwance a sume sun
fara farkawa, abu na farko da suke iskewa shi ne gawar
Bisaiya.
Nan take Armad yasa aka rataya igiya a wuyan dukkan
ƴan-fashin goma sha bakwai. Sannan ya dubi wannan
saurayi ya fara bayani. "Wanda ya kashe wani shima
kasheshi za'ayi. Idan kana so ga igiya." Armad ya miƙawa
saurayin igiyar dake hannunsa wadda ana janta zata
ƙarasa rataye ƴan-fashin.
Babu wani kokwanto wannan saurayi ya miƙe ya nufi
inda Armad yake ya karɓi igiyar dake hannunsa.
Idanuwan wannan ƴan-fashi suka zazzaro cikin tsoro,
sun san cewa rayuwarsu na gab da ƙarewa. Wasu daga
cikinsu suka fara roƙon yafiya wasu kuma suna jiƙa
wandonsu. Wannan saurayi ya ja igiyar ya rataye su. Da
dama daga cikin fadinjojin kasa kallo sukai suka koma
ciki. Amma Armad da saurayin da ma'aikatan cikin jirgin
na tsaye suna kallon har ƴan-fashin suka gama harɗe-
harɗensu suka mutu. Armad ya jefa gawarwakinsu cikin
ruwa sannan ya bada umarnin ayiwa Bisaiya wanka.
Bayan Armad ya tambayi ɗaya daga ma'aikatan jirgin
akan al'adun ƙabilar da Bisaiya ya fito daga ciki ta fannin
binne mamaci saiya fuskaci cewa ƙonawa suke sannan su
jefa acikin ruwa. Armad ya tambayi saurayin idan akwai
abinda yake buƙata ko kuma wani canji da yake so ayi
wajen binne mahaifinsa, saurayin ya amsa da a'a.
Sun samu dukiya mai yawa acikin jirgin Gashin-balbe
wanda hakan ke nuna ba ƙananan ƴan fashi bane aciki.
Daga ƙarshe suka zaɓi suci gaba da tafiya acikin jirginsu
domin girmamawa ga Bisaiya.
Kwanaki uku akai ana jimami acikin jirgin Fataken-dare
kafin Armad ya samu damar tara kowa ya fara yi musu
bayani cikin tattausar murya mai cike da kwarjini.
"Marigayi kyaftin Bisaiya shi ne wanda ya ceto ni daga
cikin ruwa yayimin maganin ciwuka na a lokacinda bai
sanni ba. A lokacin rayuwarsa ya kasance jarumi ne mara
tsoro, domin kuwa baiji tsoron komai ba a lokacinda
yake ceto ni. Lallai bazan taɓa mantawa da abinda
yayimin ba. Kowa da lokacinsa, lokacin ɗan-uwanmu
Bisaiya yayi babu wanda zai iya hanawa. Amma nayi
muku alƙawari zan kare wannan jirgi daga nan har zuwa
sanda zamu isa daular Sisiya." Armad ya ɗanyi shiru na
ɗan lokaci kafin ya wuce izuwa ɗakinsa yana tunani akan
wasiyyar da Bisaiya ya bar masa taya kular masa da
ɗansa. Tsahon kwanakin nan uku bai cewa ɗan komai ba,
domin bai san mai zaice ba. Bai san mai ake buƙata daga
gareshi ba.
A rana ta shida saurayin ya gabato izuwa ɗakin Armad.
"Suna na Maikiro Inàra." Saurayin ya ce, "Asalin mu ƴan
daular Maikironomada ne amma dani da mahaifina mun
zaɓi zama a daular Sisiya. Idan ka yadda zan bika na koyi
al'amuran izza daga gareka na ɗan lokaci kafin mu rabu."
Armad yaja dogon numfashi, sannan bayan ɗan tunani
ya amince. Koyarda al'amuran abu ne mai tsada wanda
sai anje manyan makarantu na manyan dauloli kafin a
koya, amma idan kana da babban ma'aboci izza wanda
zai koya maka ba saika je ba. Shi ma Armad kakansa shi
ne ya koyar dashi. Koyawa wannan saurayi ba wani abu
bane, kuma zaisa Armad ya biya bashin ceto shi da
Bisaiya yayi.
"Na amince zan koya maka al'amuran izza amma a halin
yanzu ina kan hanyata ta zuwa daular Sisiya domin
samawa mahaifiyata lafiya. Ban san yadda zata kaya ba,
kuma abubuwa zasu iya rincaɓewa. Bazan iya gaya maka
koni waye ba, amma ni mutun ne wanda keda kuɗi
akansa. Bina zai zamo abu mai hatsari a gareka. Abu na
ƙarshe idan zaka bini saidai ka haƙura da sana'arka ta
tuƙa jirgi, domin kaga nidai ba'a ruwa nake yawo ba."
Saurayin yai murmushin takaici tare da zubewa akan
gwiwowinsa yana cewa, "Nasan haƙiƙanin kokai waye,
Armad Wilbafos. Kuma a kowanne lokaci zan iya dawowa
sana'ar tuƙa jirgi baƴan na gama koyon al'amuran izza.
Koyon al'amuran izza shi ne abinda rayuwata ke buƙata a
yanzu, babu wanda na zarga da mutuwar babana sai
rashin ƙarfin izza ta. Indai zaka koyamin al'amuran izza
zan bika ko'ina

Please Login or Register in order to submit comment