Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne a duniya."MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 93: Samari Biyu
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Ragowar kwanakin da Armad yayi acikin wannan jirgi
baiji daɗinsu ba sosai, domin kuwa kowa idan ya ganshi
kaucewa yake tamkar yana tsoron kada ya ɓata masa.
Tun yana damuwa harya daina, shi kuwa Maikiro Inára
kullum a ƙofar ɗakin Armad ya dawo kwana, a cewarsa
ɗalibi kullum yana tare da malaminsa. Babu yadda
Armad baiyi ba amma Inára bai daina kwana anan ba.
Hatta ma'aikatan jirgin duk abinda zasu yi sai sun nemi
izini wajen Armad.
A sati na huɗu suka iso daular Sisiya, ɗaya daga cikin
manyan dauloli shida dake faɗin duniya a wannan
zamani. Armad yayi farin ciki sosai da faruwar hakan
domin koba komai ya ƙara kusantar matakin samawa
mahaifiyarsa lafiya. Yana ji a ransa cewa wannan shi ne
karo na ƙarshe da zai fita nemar mata lafiya domin kuwa
a wannan lokaci zai samu abinda yake nema kuma bazai
ƙara bari ta faɗa cikin rashin lafiya ba koda sama da ƙasa
zata haɗe.
Sannu a hankali jirgin Fataken-dare ya sauka a gaɓar
doron-ƙasa na huɗu sashin arewa inda anan daular sisiya
take.
Gaɓar jirgin acike take da ƴan kasuwa da kuma iyalan
fasinjojin da duka zo taryar su. Cikin ƙanƙanin lokaci
fasinjoji kowa yai sallama da juna sannan suka godewa
Armad kafin kowa ya kama gabansa. Tuni daman Inára ya
sallami dukkan ma'aikatan jirgin ya biya su haƙƙinsu,
saboda baya sa ran ƙara tafiya a kowanne lokaci kusa.
Koda kowa ya ɓace aka bar Armad da Inára sai Inara ya
nemi iznin zuwa ya bada ajiyar jirgin Fataken-dare har
zuwa lokacinda zai dawo kan ciniki. Armad ya amince
kuma ya bayyana masa wajenda zasu haɗu bayan ya
gama.
A lokacinda suka iso gaɓar rana na tsakiyar sama amma
kafin Inara ya hattama komai sai da rana ta faɗi. A
lokacin ya iske Armad a ɗaya daga cikin gidajen-kwana na
wannan gaɓa. Armad na zaune yana tattara bayanai akan
wannan daula ta sisiya. Dama abinda yazo yi kenan. Inara
na bayyana Armad ya tashi suka kama hanya.
Armad ya dubi Inara ya ce, "Da fatan ka gama komai?"
Inara ya gyaɗa kai. "Eh, na gama ya shugaba na. Na samu
wanda zai ajiye min jirgin Fataken-dare har zuwa sanda
zan dawo."
"To yayi kyau." Armad ya ce, "daga binciken da nayi na
gano cewa wannan daula nada adadin mutane miliyan
ɗari biyar zuwa ɗar shida. Wannan mutane sun rarrabu a
tsakanin garuruwa ashirin da tara da babban birni guda
ɗaya wanda ake kira da Jékis.
"Kowanne ɗaya daga cikin wannan garuruwa ashirin da
tara nada sarki amma dukkan wannan sarakai suna
ƙarƙashin babban sarkin dake mulki a babban birnin
tarayya na Jékis. Wanda ba wani bane illa Bihanzin mai
dauwamammen sara. Daga nan zuwa can tafiyar wata da
watanni ce, amma ina da sihirtaccen doki mai suna
Ubbaru wanda zai taƙaice mana wannan tafiya."
Armad na zuwa nan a zancensa ya hanhanga ya tabbatar
babu wanda ke kallo sannan ya sha kwanar wani layi mai
duhu ya buɗe ƙofar zobensa ya ɗakko Ubbaru.
Inara na cikin mamakin wannan zobe na Armad yaji
muryar Armad na masa bayani. "Saboda tsananin gudun
wannan doki jama'a basa ganinsa a yayinda yake tafiya.
Ina ganin ba matsala muyi amfani dashi mu isa babban
birnin."
Armad da Inára suka hau dokin sannan suka ɗau hanya.
Da tsakar dare suka isa babban birnin Jekis, wanda hakan
ke nuna Ubbaru ya taƙaice tafiyar wata da watanni acikin
awanni. Babban abinda ya bawa Inara mamaki shi ne
yadda shi yake iya ganin mutane da garuruwan da suke
wucewa amma mutane basa ganinsu. Kuma duk wannan
azabar gudu iska bata damunsu. Lallai Ubbaru doki ne
mai yawan sihiri.
Inara ya dubi Armad ya ce, "A yanzu sun rufe ƙofa sai dai
mu jira zuwa asuba."
Armad ya amince suka sami gindin wata bishiya suka fake
har zuwa safiya. Abin mamaki har yanzu ƴaƴan itacen da
Nostaljiya ta bar masa suna nan basu lalace ba, saboda
haka Armad ya fito dasu suka ci sukai hani'an.
Da safe suka nufi ƙofar wannan babban-birni mai suna
Jekis. Duk da sammakonsu saida suka tararda layin
mutane a bakin ƙofar wanda a tafe suka kwana. Wani
tafkeken bango ne iya ganinka ya kewaye garin. Duk
wanda zai wuce saiya nuna shedar ɗan-ƙasa ta sisiya da
kuma harajin ayrid hamsin ko ɗari idan baka da sheda.
A wannan lokaci Armad ya tuno bashi da ko sisi duk da
akwai naira miliyan ɗaya da rabi a kansa. Koda Inara ya
fuskanci halinda Armad ke ciki saiya fito da ayrid ɗari da
hamsin ya riƙe a hannunsa. Kallonsa kawai Armad yayi
tare da yin murmushin godiya.
Sannu a hankali layi ya fara raguwa, saura mutun sha uku
a gabansu. A wannan lokaci ne Armad ya hango wasu
samari guda biyu a gabansa. Tsakaninsa dasu mutun
goma ne kawai. Ɗaya daga ciki yana da ƙiba, ɗaya kuma
siriri ne kuma yana ɗauke da takobi. Dukkansu sun saka
hirami sun nannaɗe fuskarsu amma Armad yana ji lallai
ya sansu amma babu dama ya sauka daga layi ya isa gare
su. Saboda haka saiya rufe ido ya gane yanayin-izzarsu.
Bayan wannan samari sun wuce layi ya iso kan su Armad.
Masu gadi ashirin ne a bakin ƙofar. Rabi riƙe da makamai
rabi kuma suna ƙirga kuɗi. Dukkansu sanye da kaya
yalaye masu ratsin baƙi a hannunsu.
Inara ya miƙa kuɗin dake hannunsa tare da katinsa na
ɗan ƙasa yana cewa, "ga nawa ayrid hamsin, gana
malami na ayrid ɗari domin bashi da shedar ɗan ƙasa."
Mai gadin yayi wa Armad wani kallo mai tsayi kamar
wanda ke kallon mai laifin kisa. Sannan daga bisani ya ce,
"daga wacce daula kake?"
Armad ya amsa da cewa, "daular Hán ta doron ƙasa na
uku."
Mai gadin ya ƙara matsawa kusa kamar wanda ke
kokwanton kamannin Armad. A jikinsa yana ji cewa lallai
Armad mai laifi ne. Nan take ya buɗe wani ƙaton littafi a
gefensa mai ɗauke da hotunan mutane masu laifi wanda
aka sa kuɗi akansu.
Duk da Armad yasan kamanninsa a canje suke sai da
zuciyarsa ta buga da yaga mutumin ya buɗo shafin da
hotonsa ke ciki.
Mai gadin ya tsaya tare da ƙara tambayar Armad, "Yama
kace sunanka?"
Armad ya amsa da cewa, "Han Djinn."
Mai gadin yaja dogon numfashi tare da buɗe baki zai
ƙara wata maganar amma sai Inara ya zira hannu a aljihu
ya miƙa masa ƙarin Ayrid ɗari. Lamarinda yasa yai
murmushi tare da buɗe musu ƙofa.
Cikin sauri Armad yabi bayan wannan samari biyu daya
hanga a gabansa. Suna shiga kuwa manyan gine-ginen
birnin sukai musa sallama. Amma duk da haka ya iya jiyo
yanayin-izzar wannan samari guda biyu a ɗan gaba da
inda suke. Nan take ya umarci Inára daya jirashi anan,
sannan yayi amfani sabuwar fasaharsa ta Kaban'shisu ya
ɓace daga inda yake ya bayyana a bayan wannan samari
biyu.
Yana bayyana ya kalli samarin sama da ƙasa. Nan take sai
farin ciki ya cika zuciyar sa. Cikin dariya da annushuwa ya
kira sunansu. "Iliyasis... Cokali... Ina Nusi?"
Iliƴasis ya juyo cikin zafin nama ya ɗora takobinsa a
wuyan Armad yana cewa, "Waye kai? Kuma a ina ka
sanmu? Idan baka bani amsa ba yanzu zan tsinke maka
kai."
**
Yi comment da cikakken sunan jarumi/jaruma acikin
wannan littafiMAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 94: Tsumin Izza
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Wata biyu kafin fitar Armad daga kurkuku.
**
A can daular Infiriya, babban birnin Rafiya inda sarki
Rafiyan Kaltume ke mulki, Cokali da Iliyasis ne suka shigo
domin neman bayanin ƴar'uwarsu Nusi a wajen yarima
Niyashi.
Tafiya suke cikin yadda dakai da rashin tsoro suna
tunkarar babbar fadar ƙasar inda sarki Rafiyan Kaltume
ke mulki. Idan mai karatu bai manta ba yarima Niyashi
shi ne wanda baya tsufa. Kuma shi ne wanda ya taimaki
Nusi dasu Cokali tun suna ƴan shekara shida. Saboda
haka ba abin mamaki bane da Iliyasis da Cokali suka
yanke shawarar su fara neman Nusi daga wajensa. Koda
bai san inda take ba zai iya taimaka musu da kwatance.
Iliyasis ya tsayar da wani saurayi mai jan gashi dogo ya
tambaye shi, "da ALLAH mu baƙin yarima Niyashi ne. Ko
kasan inda zamu iya samunsa?"
Koda jin tambayar sai saurayin ya haɗe rai cikin fushi ya
ce, "yarima Niyashi? Amma banda ku baƙi ne saina sare
muku kai. Faɗar sunan yarima mai jiran gado gatsal
babban laifi ne idan baku sani ba."
Iliyasis najin haka yai murmushi tare da sanyaya murya
yana cewa, "afuwa. kamar yadda ka faɗa mu baƙi ne.
Amma maiya kamata mu ce masa?"
Saurayin yai shiru yana hucewa kafin daga bisani ya amsa
da cewa, "shi dai wanda kuke nema shi ne alfaharin
mutanen wannan daula. Kuma muna girmama shi da
sunan 'Nazára' wanda hakan ke nufin mai ceto. Sannan
kuma kamar yadda ake yiwa ƴaƴan babbar masarautar
wannan daular shima ana saka masa kalmar 'Rafiyan' a
farkon sunansa. Saboda haka daga yau ku riƙe sunansa
'Rafiyan Nazára' ɗan sarki Rafiyan Kaltume." Koda
saurayin yazo nan a zancensa sai yai shiru yana kallon su
Iliyasis domin ya tabbarar sun fahimce shi kafin daga
bisani ya ci gaba da cewa, "Idan kuka miƙe wannan
hanya tsahon tafiyar wuni ɗaya zaku tarar da ɗakin bauta
na sarki Rafiya wanda ke daura da fada. Anan zaku tadda
shi yana karɓar Tsumin-Izza."
Saurayin na gama magana yayi nasa waje ba tare da
sanin ko sun fahimce shi ba. Cokali yana niyyar finciko
shi Iliƴasis ya ɗaga hannu.
Haka suka ji gaba da tafiya suna tambayar sunan Rafiyan
Nazára har saida rana ta faɗi. A lokacin da suka iso wani
ƙaton shinge kewaye da sadaukai ma'aibota izza aƙalla
dubu. Dukkaninsu sun durƙusa ƙasa sanye da fararen
kaya tamkar suna bauta. A can tsakiyarsu wani saurayi ne
zaune yake kallon sama. Abin mamaki ƙanƙarar Sanyin-
babban-sihiri ce ke zuba a dai-dai kewayen wannan
saurayi. Ba jimawa Iliƴasis ya gane saurayin ba wani bane
illa Yarima Niyashi. Duk yadda akai wani babban sihirn
ake haɗawa.
Cikin zafin nama suka je suka samo fararen kaya tare da
matsawa kusa da ɗaya daga cikin sadaukan dake wajen
domin samo bayanai.
Sunan abinda ke faruwa dai Tsumin-izza, kuma yawanci
ana yiwa duk wani yarima mai jiran gado na kowacce
daula domin su sami izza maɗaukakiya. Mutun zai zauna
ya karɓi shekarun izza daga asusun izza na daularsu.
Wato shekarun izza da kowacce daula ke tarawa ta
hanyar fasahar kwangila. Ƙa'idar shi ne duk kwana ɗaya
mutun zai karɓi shekarun izza dubu ɗaya, kuma mutun
zai ci gaba da karɓa har zuwa sanda ƙarfinsa zai ƙare. Sai
dai a ƙa'idar ba ci ba sha har a gama.
A wannan rana kwanan Yarima Niyashi bakwai yana
zaune yana karɓar wannan tsumi daga asusun izza na
daularsa.
A kwana a tashi saida yarima Niyashi ya kwashe kwanaki
tara acikin wannan yanayi. Lamarinda ya bashi izza
shekara ɗai-ɗai har dubu tara. Hatta manƴan sadaukai
uku da ake ji dasu a dukkan faɗin daular izzarsu bata
wuce shekaru dubu shida ba. Amma ga yarima Niyashi
wanda dama yana da sirrin rashin tsufa a jininsa ya samu
shekaru dubu tara. Lallai a wannan rana an ƙara haifar
wani babban ma'aboci izzar wanda ya kamata a saka
sunansa acikin manyan gobe.
Saida akai ƙasaitaccen biki tare da gayyato kowanne sarki
daga cikin sarakuna talatin da ɗaya dake daular Infiriya
domin a taya yarima Niyashi da sarki Rafiyan Kaltume
murna.
Bayan komai ya lafa Iliyasis da Cokali suka samu damar
ganin Niyashi. Labarin ɓatan Nusi bai masa daɗi ba
kwata-kwata amma daga ƙarshe shawarar daya basu
kawai shi ne su nemi Armad. Duk inda take zai sani.
Sunyi mamakin yadda Niyashi ya riƙe sunan Armad to
amma bawai sakawa Armad kuɗi da akai bane kaɗai yasa
kowa ya sanshi ba. Babban abin shi ne yadda gimbiya
Nostaljiya wadda ake ganin tafi duk wata yarinya kyau a
duniya take kareshi a gaban kotu. Zuwa wannan lokaci
kowa ya san cewa Nostaljiya ita ce ta ceci Armad a wajen
cinikin bayi daya gabata, amma saboda matsayin baban
ta a idon duniya ake so a rufe a ɗorawa Armad laifi. Abin
mamakin shi ne har yanzu Nostaljiya taƙi bada shedar
Armad shi ne mai laifi.
Niyashi ya dubi su Iliyasis ya ce, "sarki Bihanzin baya son
yaƙi ya ɓarke tsakaninsa da sauran sarakunan Jinzidal
saboda haka yau kwana uku kenan ya bada auren
Nostaljiya ga yarima mai jiran gado na daular Denizawa
wato Deniz Bizáya. Nan bada jimawa ba za'a saka ranar
bikin. Ina tunanin duk inda Armad yake zai bayyana a
daular Sisiya kafin wannan biki. Indai kuna so ku gamu
dashi can zaku tafi."
Koda jin haka sai Iliyasis ya kalli Cokali cikin jimami. Indai
har da gaske ne maganar auren Nostaljiya da Deniz
Bizaya lallai akwai yiwuwar Armad yaje daular Sisiya. To
amma akwai matsaloli da dama da zasu iya afkuwa.
Bayan sun ƙara ƴan kwanaki a daular Infiriya ƙarƙashin
kulawar yarima Niyashi sai sukai azama suka nufi daular
Sisiya. A lokocin da suka fito labarin auren bai baza
duniya ba domin kuwa suma a bakin Niyashi suka ji,
amma kafin su isa babban birnin Sisiya wato Jekis labari
ya baza ko'ina. Kowa yasan gimbiya Zahra wadda akafi
sani da Nostaljiya Nára zata auri yarima mai jiran gado
na daular Denizawa wato Deniz Bizáya. A wani mataki na
hana afkuwar yaƙin da zaiyi asarar miliyoyin rayuka.
To ta haka Iliyasis da Cokali suka iso daular Sisiya, kuma
gashi ƙaddara tasa suna shigowa sun haɗu da Armad
kafin su isa cikin gari.
**MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 95: Hankakan Mutuwa
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
**
Tun kafin Iliyasis ya janye takobinsa Cokali yai tsalle ya
rungume Armad cikin murna. Saida Armad yai da gaske
sannan ya kwaci kansa.
Cokali ne ya fara magana. "Armad! Ashe da gaske nan
zaka taho. Amma mai yasa kake tambayarmu ina Nusi
bayan tare muka barku? Kar dai kace kaima bakwa tare."
Nan take wannan tambayoyi suka jefa Armad cikin
tunani. Ga dukkan alamu bama saiya tambaya ba, suma
su Cokali basu san inda Nusi take ba. To amma abin
mamakin shi ne yadda su Cokali suka san zaizo daular
Sisiya.
Armad ya dube su ya ce, "kuma nemanta kuke yi kenan?
Rabo na da ita tun shekarar data wuce a gasar cinikin
bayi ta Jinzidal. Amma yaya akai kuka san zanzo nan?"
Nan take jikinsu Iliyasis yai sanyi. Suna tunanin samun
Nusi a wajen Armad amma shima bai san inda take ba.
Kuma yanzu dole sai sun bayyanawa Armad tsakaninsu
da yarima Niyashi da kuma yadda akai suka gano zaizo
wannan gari.
Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Mu ƙarasa mu samu
mafaka kafin muyi magana."
Armad ya kyaɗa kai sannan dashi da Maikiro Inara suka
bi bayan su Cokali izuwa cikin gari.
Suna tafe suna kalle-kallen wannan ƙasaitaccen birni na
Jekis wanda ke ɗauke da manya-manyan gine-gine masu
samfuri kala-kala. Amma Cokali baiyi shiru ba, saida ya
taɓo labarin faɗan Armad da yarima Niyashi da kuma
yadda Armad yai nasara, domin labarin tuni ya baza
ko'ina. Armad dai baice komai ba murmushi kawai yake.
Ba jimawa suka iso harabar wani ƙaton gidan-kwana a
farfajiyar wata kasuwa. Har yanzu dai Armad bashi da ko
sisi saboda haka Inara ne ya biya masa kuɗin ɗaki kafin
daga bisani duk su huɗun su hallara a ɗaki ɗaya domin
tattauna matsalolinsu.
Iliyasis yayiwa Armad inkiya daya tura Inara waje dan su
tattauna cikin sirri amma nan take Inara ya buɗe baki ya
dubi Iliyasis ya ce, "indai daga daular Maikironomada
kuke kunsan ɗalibi baya barin gefen malaminsa a
kowanne lokaci har sai sanda malamin ya yaye shi.
Saboda haka ina cikin wannan ɗaki, amma nayi muku
alƙawarin duk abinda zaku faɗa baza ajishi a bakina ba
koda bayan raina."
Cokali ya kalli Iliyasis tsahon ƴan daƙiƙu kafin su kyaɗa
kai alamun amincewa.
Iliyasis ne ya kwashe dukkan tarihin dake tsakaninsu da
yarima Niyashi ya gayawa Armad sannan kuma ya gaya
masa yadda suka san zaizo wannan gari da kuma labarin
auren Nostaljiya.
Armad yai shiru yana tunani tsahon lokaci. Dukkan
abubuwan dake afkuwa harda yaƙin dake neman
ɓarkewa tsakanin sarakunan Jinzidal ta dalilinsa ne.
Amma babban abinda yafi damunsa shi ne zancen
wannan aure da kuma ɓatan ƴar uwarsa Nusi.
Wani irin ɓacin rai mai zafi wanda Armad bai taɓa jin
irinsa ba ya taso masa a ƙirji a lokacin daya hango
Nostaljiya a ɗakin yarima Deniz Bizaya. Tun bayan sanda
Nostaljiya ta bayyana masa tana sonsa Armad bai taɓa
tsayawa yayi wani dogon tunani akan maganar ba, kuma
ko a jikinsa. Amma a halin yanzu da yaji zatai aure
hankalinsa yayi mummunan tashi. Da farko yayi tunanin
saboda baya so ayi mata auren dole ne amma ba jimawa
ya gano cewa lallai shima akwai ƙaunar Nostaljiya acikin
ransa.
Cokali ya dubi Armad cikin al'ajabi ya ce, "idanun ka
sunyi ja ja wur. Da gaske kana son ta."
Armad yai shiru baice komai ba.
Iliyasis ya dubi Armad ya ce, "Idan zaka bi shawara ta ka
haƙura. Wannan auren shi kaɗai ne zai kare afkuwar yaƙi
da asarar miliyoyin rayuka. Idan ka hana wannan aure
lallai yaƙi saiya afku. Ina ganin kawai kazo mu juya ba
tare da kun haɗu da ita ba."
Armad ya ja dogon numfashi sannan ya ce, "idan da
ɗaurin auren ne ya kawo ni da nabi shawararka, amma
nemawa mahaifiyata lafiya ne ya kawo ni wannan daula.
Kuma lallai sai naga Nostaljiya na nemi taimakon ta.
Zarar mahaifiyata ta samu lafiya sai mu tafi."
A wannan lokaci Armad ya kwashe duk abinda ya faru
dashi bayan rabuwarsa dasu Iliƴasis ya gaya musu.
Sannan ya nemi iznin su jirashi ya je yaga Nostaljiya kafin
ya fito su bazama neman Nusi tare.
Daga ƙarshe Armad ya dubi Inara ya ce, "kaima ka jirani
anan naje na dawo."
Nan take Inara ya sunkui da kai cikin alhini yana cewa,
"ya shugabana kayi haƙuri amma lallai bazan iya barin
gefenka ba har izuwa lokacin da zaka sallame ni a
matsayin ɗalibi."
Dama Armad yayi tunanin Inara zaice haka saboda haka
kawai murmushi ya kyaɗa kai.
Da safe bayan sun karya Armad da Inara suka nufi hanyar
fadar birnin Jekis da niyyar ganin gimbiya Nostaljiya
Nára.
Ba jimawa suka tsinci kansu a wata siririyar hanya da zata
kaisu izuwa fadar. Armad ya dubi Inara ya ce, "ka farkar
da fasaharka?"
Inara ya girgiza kai. "A'a."
Armad yai murmushi tare da cewa, "nayi tunanin haka
tunda daman baka da yawan shekarun izza. Amma ba
matsala ba ce. Kamar yadda ka sani zaka iya kwarewa
akan harkar fasahar aljanu, ko kuma akan takobi ko
kuma akan ɗalasimai. Naga kana iya amfani da takobi da
kuma fasahar aljanin wuta. Kai sani cewa wannan bazai
isa ba. Indai kana so ka kware akan harkar izza saika haɗa
da ɗalasimai sannan kuma daga baya bayan ka farkar da
fasaharka sai ka zaɓi hanya guda ɗaya. Ina da malami mai
suna Babara wanda ya kware akan harkar ɗalasimai.
Zarar muka gamu dashi zansa ya farkar da fasaharka,
amma kafin lokacin zan fara da koya maka dabarun
amfani da takobi da kuma fasahar aljanu.
"Kaga dai amfani da aljanu yana buƙatar shekarun izza.
Kuma iyakacin yawan shekarun izzarka iyakacin ƙarfin
fasahar da zaka iya amfani da ita. Da shekarun izza
hamsin da ɗaya da kake dasu baza ka iya wuce mataki na
farko ba daga cikin matakai shida na amfani da aljanu.
Kuma indai...."
Armad na cikin bayani yaji wani yanayin-izza mai
tsananin ƙarfi da buwaya ya tunkaro shi ta baya. Tunda
Armad yake bai taɓa jin irin wannan yanayin izza ba. Idan
a misali zai iya kwatanta girman yanayin-izzar duk daya
taɓa ji a matsayin kofin ruwa ɗaya to wannan izzar takai
girman tekun maliya.
Bawai kuma girman izzar ne yasa Armad ya fara gumi ba,
tsananin zafi da muni da azabar dake cikin izzar ne yasa
Armad yaji tamkar ruhinsa zai fashe.
Kafin Armad yai wani motsi Inara ya faɗi ƙasa sumamme.
Yana juyawa bayansa wani ƙatoton hankaka baƙi-ƙirin
mai ido kwaya ɗaya tak ya kawo masa wafta. Armad ya
manta da cewa zai iya juyewa izuwa walƙiya ya baje a
ƙasa wannan hankaka ya wuce.
Kafin ya miƙe hankakan yayiwo kwana. Cikin sauri Armad
ya kirawo Hannun-Aradu ya fuskanci wannan hankaka.
To amma bisa mamaki sai hankakan ya tsaya cak yana
kallon Armad sama da ƙasa tsahon lokaci kafin daga
bisani ya juya ya ɓace.
Abu na farko daya fara zuwa ran Armad shi ne wani
labari da mahaifiyarsa ta taɓa bashi akan wata ƙabila
wadda aka manta da sunansu. Wannan ƙabila sune asalin
tsafin Sanyin-Babban-Sihiri. Dukkan tsafinsu suna yinsa
da baƙin aljanin-hankaka wanda ake kira da HANKAKAN-
MUTUWA. Acewar wannan labari hatta sarki Eyriyon
Wilbafos da sarki Kuyurussa'ayi Ururu baza su iya sawa
wannan hankaka ya durƙusa musu ba. Shi yasa suka haɗa
ƙarfi da ƙarfe suka halaka wannan ƙabila. Kuma tun daga
wannan rana babu wanda ya ƙara ganin Hankakan-
mutuwa a doron ƙasa. Amma indai Armad ba mafarki
yake ba lallai yau yaga hankakan-mutuwa da idonsa.
**MAGAJIN WILBAFOS
Marubuci: Dr Abdullahi Muhammad Ibrahim
Babi na 96: Shiga Fada
Post by: Shuraih Usman
@shuraih 99%
www.facebook.com/hausaebooks
.
Daga:- Taskar Magajin Wilbafos
**
Koda Armad yaga wannan baƙin hankaka na neman ɓace
masa saiya buɗe ƙofar zobensa na sihiri ya cilla Inara
aciki. Sannan yayi amfani da fasahar Kaban'shísu ya ɓace
daga inda yake tare da bayyana acan nesa dai-dai ƙasan
inda hankakan ke tafiya a sama.
Hankakan na ganin haka ya sha kwana tare da ƙara
azama wajen iyo akan iska yana ƙoƙarin gujewa Armad.
Amma murmushi kawai Armad yayi tare da barin
hankakan yayi nisa kafin ya ƙara yin amfani da ɗalasimin
Kaban'shísu ya bayyana a ƙasansa. Sannu a hankali
Armad yana bin wannan baƙin hankaka sai kawai ganinsa
yayi a kusa da fadar sarki Bihanzin mai dauwamammen
sara. Abin mamaki sai wannan hankaka ya ƙara shan
kwana yabi jikin katangar wannan fada ya nufi yamma.
Armad nada ragowar ɗalasimai biyu kacal saboda haka
ya fara tunanin hanyar da zaibi ya kama wannan hankaka
idan bai tsaya ba. Yana cikin tunani ya hangi hankakan ya
tsaya a ƙarshen katangar ta ɓangaren yamma. Har wani
waiwayo wa yake yana kallon Armad tamkar yana jiransa.
A fusace Armad ya yanke shawarar yadda zaiyi ya kama
wannan hankaka. Ya buɗe baki ya kira ɗalasimin
Kaban'shìsu amma a wannan lokaci saiya canja
maimakon ya bayyana a ƙasa saiya bayyana akan
katangar wannan fadar dai-dai gefen wannan hankaka.
Yana bayyana ya miƙa hannu ya damƙe jelar hankakan
tare da finciko shi da niyyar jefashi cikin zobensa na
sihiri.
To amma bisa mamaki sai Armad yaji tamkar ya finciki
dutsen uhudu. Ko motsi wannan baƙin hankaka baiyi ba.
Hasalima kaɗa jelarsa kawai yake ba tare da ya waiwayo
ya kalli Armad ba.
A fusace Armad ya sanya ƙarfin shekarun izza dubu a
hannunsa ya finciko hankakan dashi. Amma bisa mamaki
ko motsi baƙin hankakan baiyiba. Armad ya haɗe gira
yana tunanin maiya kamata yayi domin dai bazai iya
amfani da hannun-aradu ba a wannan hali. Koba komai
duk wanda yaji ƙarar saukar aradu wajen zai taho yaga
ganshi, wanda hakan zai tona masa asiri.
Armad na cikin tunani yaji jelar hankakan dake hannunsa
ta motsa ta fincike shi. Kafin yayi wani abu hankakan ya
jashi ƙasa daga saman wannan katanga sun faɗa cikin
babban gidan sarautar daular Sisiya.
Saida suka kwashe daƙiƙu suna faɗawa sannan suka isa
ƙas, badan Armad yayi sauri ya juyarda jikinsa izuwa
walƙiya ba da tuni ya karairaye. Kafin ya miƙe hankakan
ya tashi ya gudu. Armad ya tsaya yana nazarin wannan
katanga. Kaurinta yakai ƙafa goma, kuma dukkaninta da
duwatsu aka sarrafa ta. A tsaye kuwa takai zira'i casa'in.
Lallai koda kuɗi ɓarawo bazaiyi ƙoƙarin haura wannan
katanga ba.
Yana cikin haka yaji motsin tafiya daga nesa haɗe da
maganganu wanda sukai kama dana masu tsaron fadar.
Nan take ya rufe ido domin jin yanayin izzarsu da kuma
adadinsu da kuma ta inda suke tahowa. Amma bisa
mamaki abu na farko da Armad ya fara ji wata sanyayyar
izza ce mai ni'ima da faranta rai daga can gefensa
ɓangaren arewa.
Ya waiwaya ɓangaren tare da buɗe ido. To amma wajen
cike da yake da bishiyun goba dana inubi wanda sukai
masa duhuwa tayadda baza'a iya ganin wanda ke ciki ba
daga nesa.
Amma bisa mamaki Armad ya gane waye aciki.
Murmushi kawai yayi tare da nufar wannan waje kai
tsaye. Ƙanshi ne ya fara yi masa sallama, ƙanshin da
yasha banban dana turare. Wannan ƙanshi mutun ɗaya
ne kacal yake da irinsa a duk faɗin duniya.
Armad ya tsaya kimanin taku uku kafin ya ƙarasa. Nan fa
zuciyarsa ta fara bugawa kamar zata fasa ƙirjinsa. Bashi
da cikakkiyar masaniyar maike faruwa amma yaji gumi
na ƙoƙarin kwace masa.
Sanyayyar murya wadda Armad ƴasanta sarai ita ce tayi
masa sallama. "Mai yasa ka tsaya?"
Armad ya fashe da murmushi ba tare da yasan dalili ba,
ya amsa da cewa, "Mai yasa kike tsaye a duhu?"
Muryar ta amsa masa da cewa, "ka bani kunya daka kasa
kama hankaka guda ɗaya tak."
Armad ya fashe da dariya yana cewa, "dama ke kika
turoshi. Nasan zaki aikata. Amma meye alaƙar ƙabilarku
da Hankakan-mutuwa?"
Muryar taja dogon numfashi tare da yin ƴar ƙaramar
dariya sannan ta fito daga cikin duhun. Kyakkyawar sura
wadda babu kamarta ce ta bayyana. Wato gimbiya Zahra
wadda aka fi sani da Nostaljiya Nára.
"Baka yarda zoben dana baka ba kenan."
Armad ya kalli zoben dake hannunsa sannan ya ɗago kai
ya dube ta ya ce, "kona mutu dashi za'a binne ni."
Nostaljiya na sanye da doguwar riga mai kwalliya da
bezar gashin farin aku. Jikinta kamar lokaci na ƙarshe da
Armad ya ganta acikin wancan kogo haske kawai yake
yana bada ƙawa da armashi. Gashinta na kwance har
gadon bayanta babu abinda yake sai sheƙi da ƙanshi.
Babu kalmar da tafi dacewa da wannan gashi illa mudubi
domin tsaf zakai kwalliya kana kallon kanka acikinsa.
Armad ya buɗe baki zaiyi magana sai yaji masu gadin
fadar sun matso kusa saboda haka ya fara lisaafin neman
wajen ɓuya.
Koda Nostaljiya ta fuskanci haka saita jashi izuwa cikin
duhuwar wannan bishiyu. Da farko Armad yayi tunanin
ɓuya zasu yi har sai ma'aikatan sun wuce amma sai kawai
yaga sun wuce izuwa wata siriyar hanya wadda ta ɓulle
izuwa wani shinge mai kama da lambu. Baki a buɗe
Armad yaci gaba da kallon ikon ALLAH a yayinda
Nostaljiya take jansa izuwa tsakiyar wannan fada.
Abin mamaki ko mutun ɗaya basu gani ba a hanyarsu.
Amma idan akai duba da cewa wannan fada gidan
Nostaljiya ce kuma anan ta taso to ba abin mamaki bane.
Ba daɗewa Armad ya tsinci kansa a wani kewayayyan
sashi mai dogayen ɗakuna wanda aka gina bangwayensu
da gilasai da yaƙutu. Dukkan wajajenda suka wuce babu
wanda yakai wannan waje kyau da armashi. Hatta ƙasar
wajen da lu'u-lu'u aka shimfiɗe ta. Nostaljiƴa taja Armad
ɗaya daga cikin manyan ɗakunan dake kewaye da wajen.
Suna shiga Armad ya tsinci kansa akan wani farin gilas da
ruwa garai-garai yana gudana a ƙasansa. Kifaye masu
haske kyawawa suna ta wasa acikin ruwa. Daga can gefe
kuma wani ƙasaitaccen

Please Login or Register in order to submit comment