Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰

πŸ‘„ πŸ‘„
πŸ’…πŸΎ πŸ’…πŸΎ
πŸ™πŸ» πŸ™πŸ»
(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍🏾[P~M ~L]✍🏾
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the ReadersπŸ“–}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 All members of PURE MOMENT Of Life Writers, I dey hail wuna Allah yabar kauna, Allah yabarmu tare har AbadaπŸ™‹πŸ»πŸ™‹πŸ»πŸ™‹πŸ»

4 Months later
Abusaiyeed neh kwance a Asibiti yau kwannan sa 10 amman sam baisan inda yakeba sai Tarin jini dayake yi kuma duk sanda zaiyi saiya dafa k'irji sah, hajiya Humaira ce zaune agefen shi sai salati take masa nan likita ya bukaci, ganin tah, bayan tabishi Office neh yake tambayar tah, matsalar Abusaiyeed nan take gaya masa abinda yafaru harya koma haka, ajiyar zuciya likitan yayi yace amman na tausaya masa yana wani stage mai had'arin gaske dan zuciyar shi tah tab'u kuma idan Ummulkhair bata dawo rayuwar shi bah zai iya komawa abnormal kuma akwai probability d'in za ayi masa aiki azuciya sabida yasaka wani irin mugun damuwa aranshi, kuka Hajiya Humaira tafara yi tanah tunanin halin dah Abusaiyeed ya jefa kanshi, komawa tayi tazauna tarik'e hannun shi, ahankali tasoma magana kamar haka, "son daman kana sonta haka and u were being that careless, son u weren't fair to Ummulkhair fa, kayi hak'uri zan tayaka nemo tah" tah k'arasa magana tanah share kwallah, murmushin k'arfin hali yayi, Amal ce kwance ajikin Bilal tayi wani laushi wanda taci kuka kamar bagobe harsai da tasaka Bilal shima kuka, lokacin sallah neh yayi Bilal yad'aga tah yawuce masallaci, nan tah d'auki phone d'insa dake charge takira layin Amrah, Amrah dake yankar Albasa alokacin tacewa Ummulkhair "Antynmu Dan Allah kimin picking sai kisa a hands free", kai amman Amrah kinfiya tak'ura zan gudu gurin Ameesha nayi karatu nah kin sanfa jibi zamu fara final exams dai ko? Wayan dake ringing akaro nabiyu tayi saurin d'auka dan kada ya tsinke, a hands free d'in tasaka nan sukaji Amal tanah kuka sosai harda sheshek'a har muryan tah yanah d'aukewa, Ya Amrah yayanmu zai mutu yanayin aman jini dah tarin jini, d'ip sukaji wayan ya yanke, saukar mari kakeji tas, ke Amal yanzu bakida hankalin dazaki san abinda yakamata da wanda bai Kamata bah, ya za'ayi ki kirata ki d'aga mata hankali abanza dallah fice min anan kitafi kije kiyi sallah kimishi Addu'a, cewar Hajiya Humaira zuwaga Amal wanda tarik'e kuncin tah tanah sharar hawaye, ab'angaren Amrah dah Ummulkhair kuwa duk sunyi mutuwar tsaye kowacce sai hawaye take, Ummulkhair tace Mijinna neh nasan ai shine kuke kira yayanmu, gaskia zantafi Nigeria ni bazan iya jurewa bah tanah kaiwa nan takoma d'aki taje tah kwanta tasha kuka kaman bagobe sai yanzu take missing Abusaiyeed sosai jitake kamar baza takai gobe bah idan bata jita ak'irjin shiba, Amal kuwa kasa cemata komai ma tayi dan haka barin tah tayi harsai dah tah nutsu tayi sallah dah karatun Alkur'ani mai girma, sannan tasamu waje tazauna agefen tah tace, Antynmu Dan Allah kiyi hak'uri bah ya Abubakar baneh bah lafiya yaya Bilal neh mota yabige shi fah, Amrah ta sharara mata k'arya, bawani nan k'arya kukemin bazaku gayamin gaskia bah so kuke naje natarar dah gawansa? Wayan tah neh yasoma ringing tanah dubawa taga AntyMuna ce kekira, d'auka tayi dah sallama amman kanajin muryan tah kasan akwai matsala, Sannu khairat ance k'anin Mijin ki yayi accident koh Allah yakiyaye gaba kinji, bawani nan AntyMuna wlh kinsan mijina neh mesa bazaki gayamin gaskia bah, ke dallah malama rufemin baki sakarai kawai toh idan mijin naki neh kece kika d'aura masa cutan koh kece zaki yaye masa? Eh khairat ina tambayan ki? Toh bara kiji bahaushe yace Addu'a makamin mumini saiki zab'a Addu'a zaki rik'e koh kuka, saida Allah yakawo k'arshen karatun naki zaki sako mana shirme ciki bah? Yaufa Saturday kuma Monday zaki fara Final exams, daman aishi aski saiya zo gaban goshi yake zafi, dan haka wlh kizage kiyi karatu kiyi clearing papers d'inki once and for all, idan bahaka bah U will go back next year and U Will have no one to blame but urself, daga nan AntyMuna takashe wayan, kuka sosai Ummulkhair takeyi tanah fad'in Abusaiyeed duk inda kake ban barka bah kullum ina makah Addu'a Allah zai karemin kai Insha Allah, haka tah k'araci kukan tah kuma taja littafin tah tayi boko, daga baya Amrah tabata baki tah tsara tah akan tah dage tayi karatu dan su koma Nigeria, aikuwa hakan akayi yau takama satin su Ummulkhair biyu dafara exams saura sati biyu sugama, yanzu kuma ita dah Ameesha kullum basuda aiki saidai sukalli junansu sufara kuka, gashi dukkansu gwanayen kuka neh, basusan yanda zasu rabu dah junansu bah, kowa saitaya su jimamin rabuwa yake, Ummulkhair ce take cewa Amrah sanda sukazo Nijar gani take 1year bazaiyi bah amman Allah dah ikon sa even though the journey was nothing easy gashi zasu gama Allah yakawo k'arshen saikuma tafashe dah sabon kuka ita kanta Amrah kukan take sabida dole idan sukaje Nigeria ita kad'ai zata dawo Nijar Ummulkhair tagama Insha Allah, taji dad'in zama dah Ummulkhair kasan cewar bamai matsala bace, oh nikam nace musu kad'an daga aikin rayuwa kenanπŸ˜’ shi daman komai lokaci neh, Next on MDS @Pg64


Mhiss B~hal CeπŸ’…πŸΎπŸ‘„πŸ’žπŸ’•
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf CeπŸ’…πŸ‘„πŸ‘‘πŸ‘’πŸ’•: 🎍🐚NoVelπŸ‘‡πŸΏWriTter 🐚🎍
β˜£πŸ‘„Mhiss~B~halπŸ™‡πŸ»β€β™€πŸ‘„β˜£

⏳64βŒ›

πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€ 🌑🌑🌑 πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€
πŸ€β˜˜Matar DR. Saiyadeeβ˜˜πŸ€

πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰ πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰

πŸ‘„ πŸ‘„
πŸ’…πŸΎ πŸ’…πŸΎ
πŸ™πŸ» πŸ™πŸ»
(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍🏾[P~M ~L]✍🏾
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the ReadersπŸ“–}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 Maryam KWAIRANGA, Maman Hanan Allah yabar kauna dear, Allah kayara manah HananπŸ™‹πŸ»

Yau takama ranar k'arshe dah su Ummulkhair suka gama papers aikuwa sunsha kala kalan parties and dinners,events kala kala harkasa attending dukkah sukayi, wasu suna murna wasu kuma basayi, Ummulkhair dah Ameesha sunanan a minne kamar superglue Ameesha tanata fad'a mata yanda zatayi missing d'inta, Ummulkhair mahakan dan Ummulkhair wannan shekara d'ayan dah sukayi tare hartayi adapting yanda Ameesha ke turanci itama haka takeyi dah tone d'in Indians Ameesha kuwa yanzu tah iya abincin hausawa iri iri nikam Nace zama dah mad'aukin kanwa, abun nasu sai mutum yaji babu dad'i idan yatuna rabuwa zasuyi, saura 1month najiran results dayake su en masters neh results d'insu baya dad'ewa sosai, haka sukayi wannan 1month d'in tamkar sati d'aya sun kar'bi result Alhamdulillah kowacce tafita dah 1st class kamar yanda dai suka saba daga Ameesha sai Ummulkhair, sunyi murna sosai dan basuda matsala lafiya klau sun rabu dah Maryam Abacha American university,
1 Month later
gobe takama Saturday jirgin su Ummulkhair zai d'aga zuwa Nigeria yayinda itama Ameesha Insha Allah zata d'aga zuwa New Delhi, Ummulkhair tayi mata alk'awarin cewa idan har bikin tah yataso toh duk inda za ayi zataje mata, bah k'arramin murna Ameesha tayi dah hakan bah, kuma Ummulkhair tayi mata fad'a akan tarik'e musulunci kuma tah auri musulmi sabida taga familyn su Ameesha mix neh amman Ameesha tanada addini sosai shine yadad'a saka shak'uwar su tayi k'arfi sosai, haka suka rabu suna kuka har suka had'a inasu inasu Amrah ma tah tayasu kukan,
Gida Nigeria
Abusaiyeed neh acikin mota yana driving ahankali, yasamu sauk'i bah laifi sabida yanda Hajiya Humaira tamishi alk'awarin nemo masa Ummulkhair indai tanah raye, hakan bah k'arramin kwantar mishi dah hankali yayi bah dan yasan Hajiya Humaira zata aikata, kwasam yanah tuki Ummulkhair tafad'o masa arai tuni yaji kamar abu ya soke shi azuciya haka yakama k'irjin shi yataka birki, sauran kad'an yahad'a babban accident, tuni titin yazama conjested kowa sai horn yakeyi kuka yafashe dashi yafito yahau kan bonnet d'in motar ya kwanta abinshi ya kanannade k'afa kamar yaro yanah kuka yanah fad'in "wayyo Allahnah Ummunah, Ummunah, Ummunah, Innalillahi kutaimaka kunemo min ita wayyo Ummunah", kash Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Antynmu yanzu koh Nijar ace tafi Nigeria yaushe rabon mushiga irin hold up d'innan amman Kinga Hold up lallai we are really back to Nigeria where gala dah fanta is ur only choice wen stock in hold up, dariya Ummulkhair tayi tace, galan dah fantan dai kikeso koh Amrah, kamar ina ganin abu neh yafaru kinga wancan fah akwance asaman mota sai wani rawan d'ari yake watak'il baida lafiya, lallai amman anyi d'an banza saikace gidan Ubansa, zomuje namishi magana, lallai Amrah dah k'arfin hali kike nidai banida wannan courage d'in kinmanta bah zuwa akayi d'aukan mu bah Cabman muka d'auko sabida kince muyiwa Ummanmu Surprise, sannan kid'auka zan biye miki ayaga min cert d'in shekara d'aya danayi ina karatu a Nijar, badani bah and U also u're going no where wlh, kina complain mai taxi ba dashi akeyi bah yaje gulma kekuma yanzu naga alaman Masscom kike karanta tunda gashi zakije d'aukan rahoto, dariya tah fashe dashi tah mik'awa Ummulkhair waya wanda Ameesha ke kiranta, dauka tayi cike dah farin ciki suka gaisa inda Ameesha take fad'a mata yanzu zasu tashi jirgin su zai d'aga nan Ummulkhair take bata labarin har sunzo Nigeria tama yimata videon datayi alk'awari harta turo on WhatsApp godiya Ameesha tamata sosai, nan Ummulkhair tace bara su k'arasa gida sai suyi waya hold up yayi yawa dahakan sukayi sallama,! Chab Antynmu gaskia keda Ameesha Kunasan junanku yanzu sabon layin dakika siya a airport harkin kirata dashi, wlh Saboda ita ma nasai layin tun a airport kuma ita kad'ai ce numban dan ita kad'ai nakira dashi,
Mai taxi neh yashigo yakatse musu magana yanah fad'in Allah Sarki, Amrah dah gulma tace, wai Malam meya faru neh, wlh mudai bamu sani bah sai faman kuka yake yanah cewa Ummanshi or something koh Babar tashi ce tarasu Allahu A'Alamu amman baikamata yayi driving awannan yanayin nashi bah, Amrah sai d'aga wuya take kozata hango fuskan saidai takasa motan ma bata gane bah sabida yayi accident dah ainihin motan shi so kuma ya canza sabo, hmmm toh Allah yaduba labarin sah cewar Amrah, Ummulkhair sosai taji tausayin Bawan Allah dukda batasan meya same shi bah, toh Bawan Allah haka za abarshi anan babu mai taimaka masa tah tambayi mai taxi cike dah damuwa, ansamu wanda yasan shi ai, yace yakira k'anin shi zaizo! Toh Allah yabashi lafiya, kafin kace me suka isa kabuga, Amrah sai wani murna take kamar tayi tsalle tafita tah window itakuwa Ummulkhair sai fad'uwa gaban tah yake mata, suna shiga ciki sukaji k'amshi ya mamaye koh ina, Hajiya Humaira suka hango a kitchen atare sukace Ummanmu, juyowa tayi cikin tsananin mamaki dah murna bayyane afuskan tah tafara wak'a tanah fad'in ga 'ya'yana ga 'ya'yana, certificate d'in Ummulkhair nah masters degree Ummulkhair tanuna mata cikin tsananin Murna Hajiya Humaira takama hannun tah tace, "nagode er Albarka Allah yabaki yara masu Albarka" sannu kinji, kinmin biyayya tamkar er dana Haifa, murmushi tayi tace, ina su Abbanmu Amal dah Bilal, Abban ku yatafi meeting Kaduna Bilal kuma yatafi d'auko Amal amakaranta, Kuje kuyi wanka bara nayi serving d'inku,Ummanmu Ina Abusaiyeed Ummulkhair tah tambaya kanta ak'asa, yananan klau Alhamdulillah, nasa an gyara miki gidanki tas kuma namiki sabbin kaya, tamkar sabuwar Amarya kike komai atattare dake anyi renovating d'inshi including ur lifestyle, so am still pleading kiyafe wa nida d'ana Allah yabaki hak'uri kuma mungode, A'a Ummanmu nice dah godiya Allah yasaka dah Alkhairi, murmushi Hajiya Humaira tayi sannan tace idan Kinasan kiyi aiki kigaya min kinji, akwai aikin dazan samo miki Ummulkhair batace komai bah sai murmushin datayi tawuce bathroom bayan tayi wanka taci abinci, takira Ameesha suka gaisa tafad'a mata yanda tayi missing d'inta, bayan sun gama waya, Hajiya Humaira tashigo tace tashi driver yakaiki gida ki gaida Mummyn ki sannan yajira yamaida ki gidan mijin ki, wani dum taji gaban ta nacewa amman tah tashi bamusu tadauki hijabbin tah, kayan ki suna boot Amrah takaisu, kuka tafara yi tana yiwa hajiya Humaira godiya sosai akan komai dah komai, Amrah ma kuka take gani take kamar zasu rabu forever kenan, haka tah k'ank'ame tah tana cewa Antynmu zanzo dubaki gobe, Hajiya Humaira ce tajanye tah, sannan Ummulkhair tawuce cikin mota aguje, tanah shiga unguwar kuntau tafara ji kamar tafita tah window tah k'arasa aguje, sai asannan tagane feelings d'in Amrah nad'azu, aikuwa basu wani jima bah driver yayi parking aguje tafita tanah shiga tah tarar dah Daddy zaune akan can bed Affan yana Sallah agefen shi, aguje tafad'a jikin shi tanah cewa Wayyo Allahnah gani ga Daddynah wayyo Daddy ina Mummynah, I miss U, Daddy yakasa cewa komai sabida tsananin farin ciki cewa yake, My dear kizo Khairiya ce fah, ga Khairiya tazo, Dasauri Mummy tafito kamar bah kullum suke waya bah tah rungume erta, khairat oyoyo kindawo, Affan yanah idar wa shima ya rungume tah sai rungume rungume sukeyi yaukam suna cikin tsananin murna, driver sai shigo dah kayan dah Hajiya Humaira tambayar yake, Ummulkhair tabasu tsaraba tuni suka fara hira suna Murna Ummulkhair tace kwana uku zatayi, horn driver yayi nan mood d'inta yachanza, cewa tayi banan gidan baneh, bara dai naduba Daddy yace, aikuwa yana zuwa driver yace masa ai Ummulkhair yake jira ga yanda akace, tuni Daddy yashigo yace taje gidan mijin tah tadawo bayan kwana biyu kuka tafara kamar yarinya koh d'ankwali bata d'aura bah kanta abaje haka tashiga mota tanah kuka Mummy madai bahakan taso bah amman babu yacce ta iya neh kawai! Next on MDS @Pg65

Mhiss B~hal CeπŸ’…πŸΎπŸ‘„πŸ’žπŸ’•
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf CeπŸ’…πŸ‘„πŸ‘‘πŸ‘’πŸ’•: 🎍🐚NoVelπŸ‘‡πŸΏWriTter 🐚🎍
β˜£πŸ‘„Mhiss~B~halπŸ™‡πŸ»β€β™€πŸ‘„β˜£

⏳65βŒ›

πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€ 🌑🌑🌑 πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€
πŸ€β˜˜Matar DR. Saiyadeeβ˜˜πŸ€

πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰ πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰

πŸ‘„ πŸ‘„
πŸ’…πŸΎ πŸ’…πŸΎ
πŸ™πŸ» πŸ™πŸ»
(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍🏾[P~M ~L]✍🏾
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the ReadersπŸ“–}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 All readers Of Matar Dr Saiyadee Novel I don dey Miss wuna ooo, Stay Blessed Always😭😭😭

Cikin mota takoma tanah kuka gashi sai faman hararan driver takeyi kamar idanuwan tah zasu fad'o k'asa, batare dah bata lokaci bah yaja mota sukabar kuntau suka nufi hanyar gidan tah dake zooroad bayan tafiyan wasu en mintuna, suka iso gidan nata tasan tamanta yanda gidanta yake amman from the look of things an canza fasalin gidan dan bah k'arramin kyau yayi bah tanah wannan tunanin har driver yashigar dah kayanta ciki hakan yasanar dah itah tuni tah gyara dankwalin tah, sannan tah shiga ciki, wani k'amshi taji ya mamaye tah tako ina everything about the house looks new, rayuwar tah tafara tunawa abaya dana yanzu tayi hamdala tawuce ciki, wanka tayi tazo tah kunna system d'inta tashiga foldern Ameeshkhair tanah kallon hotunan su itada Ameeshan tah life @ Maryam Abacha was the best tafad'a in a whisper, I miss U Ameesha I miss everything about U and every second we spent togeda, wasu hawaye neh suke zubo mata wanda batasan dasu bah, wayar tah tad'auka takira Ameesha and she was like babe am in my matrimonial home, ihu Ameesha tayi akan waya cire wayan Ummulkhair tayi daga kunnen tah, danji tayi kamar dodon kunnen tah yafashe nan Ameesha tace tanaso taga gidan Ummulkhair aikuwa tuni tazura hijjab har k'asa tayi mata video snapping gidan tun daga sama har k'asa tah tura mata, sannan tadawo tayi alwala tayi sallah,
Hajiya Humaira ce takira Abusaiyeed tace, yau duk inda yake yaje gidan shi yakwana idan bayasan b'acin ranta tah k'ara dacewar yak'are dabin layin hotel kowani hotel yasan sahun shi, hak'uri yabata sabida haka bayan yayi sallah magriba yayi wanka yashirya yakwashe kayan shi yabar farhan guests house, zuwa gidan shi dake zooroad, Ummulkhair horn taji daman dah hijjab ajikin tah wanda tayi sallahn magriba dashi zuwa tayi tah duba taga drivern Hajiya Humaira neh yadawo dah Leda wai gashi inji Hajiya Humaira, karb'a tayi sannan tace sun gode, tashiga ciki tarufe gidan, ciki takoma bayan tah ajiye ledan daya isheta dah k'amshi akan dining, komai sabo tagani Including set of boxes d'inta itadai batasan bakin dazata yiwa hajiya Humaira godiya bah, jin gidan yayi shuru dayawa kuma tagaji dah kallo hakan yasa tah kunna karatun Alkur'ani awaya tasaka earpiece tanabi a hankali, sanda Abusaiyeed yashigo dah Mota bataji bah, bayan yayi parking harya shigo parlour tah ajiye wayan dah niyar zuwa fitsari, toilet tashige,
Abusaiyeed neh tsaye yanah kallon yanda gidan yakoma sabo dal arashin yanah cewa nasan aikin Umma neh, amman ai gyaran nan bashida amfani tunda Ummunah batanan, k'ofan d'akin tah yake kallo yana fad'in Allah yabayyana minke, ahankali yana murmushi yataka zuwa k'ofan d'akin, ya murd'a harda zai koma saikuma yabud'e nan yaci karo dah mutum atsaye dah alamun fita zatayi, dukkan su ido suka zaro suna kallon junan su bah kamar Abusaiyeed wanda k'afafun shi sun kasa d'aukan shi hannun ya mik'a zaiyi magana amman yakasa yadafa k'irjin shi dah k'arfi dah alamun yanajin zafi k'asa yayi Ummulkhair sai asannan kanta yace tah d'ebo ruwa yasuma, ruwa tah d'ebo tah yayyafa masa amman bai farfad'o bah hakan yasa tah had'e bakinsu tafara bashi iska amman nanma bai farfad'o bah itah kuma bata sake shi bah harya farfad'o yafara maida mata dah martani, ido tazaro tanah Neman kwatar kanta amman ina sam Abusaiyeed yayi mata wata muguwar runguma wanda dakyar take Numfashi, gabad'aya ya daure tah dah kafafun shi koh motsin arzik'i bata iyayi, kissing d'inta yake kamar wanda yayi shekara dubu babu abinci balle ruwa, ita duk kallon tausayi take masa duk ya lalace yazama abin tausayi haka tayi surrender tafara kissing d'inshi itama, saida yayi hakan na wajan awa d'aya sannan yasake tah yace, "Ummunah kece yana shashafa fuskan tah gabad'aya ya rikice yarasa inda zaisaka kanshi, rungumar tah yayi yasake tah, yanah fad'in dawowa kikayi wajena koh Ummunah, saikuma yasake k'ank'ame tah, itafa koh numfashin arzik'i batayi amman dad'a k'ank'ame tah yake kamar ance yanzu za agudu dah itah, kasa gane kanshi tayi sai cewa take Abusaiyeed nifa banda kwari haka pls kabarni nahuta numfashi nah, k'ank'ame tah yakuma yi sosai yafashe mata dah kuka kamar yaro yace, "nabarki ki gudu kibarni koh?" Wlh bazai yuba bazan k'ara bari kitafi bah, Ummunah am sorry for everything I thought I had lost u forever I thought I would Neva set my eyes on the real U again, kuka yakeyi sosai kamar yaro, shi hankalin shi atashe itama duk yad'aga matah hankali, shhhhh I dnt Understand U pls kabarmin kuka, Abusaiyeed juyo kah kalleni pls d'agowa yayi idanun sah sunyi jajir kamar garwashi wasu zafafan hawaye suna fita daga cikin su, hawaye tashiga share masa amman kamar tanah k'arawa wuta petir, Abusaiyeed wai menene pls tafad'a cikin kuka dah rashin fahimta, Ummunah kece, Ummunah kece I miss U I almost died, cikin kuka tace toh bagani nanba Abusaiyeed, I will Neva leave U again not anymore I promise kaji, pls kah Nutsu nice, kwanciya yayi akan k'irjin tah har lokacin bai bar kuka bah wani bacci neh mai nauyin gaske yayi gaba dashi kuma koda wasa bai saki rik'on dayayi mata bah, kallon shi take har alokacin tanah shafa kanshi ahankali saida yayi baccin awa d'aya dah en kai sannan ahankali yabud'e ido yanah sauke su akanta yafashe dah wani sabon kuka sosai, numfashin shi har d'auke wa yake k'ank'ame shi tayi tanah taping bayan shi ahankali, calm down am here pls, shigewa jikin tah yakuma yi wani zazzabi neh yarufe shi, tashi tayi zata dubo musu mafita, k'ank'ame tah yayi yanah fad'in nashiga uku zata kuma guduwa tabarni, kuka yake sosai hakan bah k'arramin d'agawa Ummulkhair hankali yayi bah, sanyi taga yanaji hakan yasa tarufa musu duvet cover, har alokacin bai rabu dah itah bah, kallon shi take sannan tace, Sannu kaji Allah yabaka lafiya, rinannun idon shi yabud'e ahankali ya lalubo bakin tah, yafara kissing d'inta bata hanashi bah saida yagaji yabari, nanma yasake fashe mata dah kuka sosai harya kasa controlling kanshi itama kukan tafara Next on MDS @Pg 66


Mhiss B~hal CeπŸ’…πŸΎπŸ‘„πŸ’žπŸ’•
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf CeπŸ’…πŸ‘„πŸ‘‘πŸ‘’πŸ’•: 🎍🐚NoVelπŸ‘‡πŸΏWriTter 🐚🎍
β˜£πŸ‘„Mhiss~B~halπŸ™‡πŸ»β€β™€πŸ‘„β˜£

⏳66βŒ›

πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€ 🌑🌑🌑 πŸ€¦πŸ»β€β™€πŸ€¦πŸ»β€β™€
πŸ€β˜˜Matar DR. Saiyadeeβ˜˜πŸ€

πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰ πŸ’‰πŸ‘¨πŸΎβ€βš•πŸ’‰

πŸ‘„ πŸ‘„
πŸ’…πŸΎ πŸ’…πŸΎ
πŸ™πŸ» πŸ™πŸ»
(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍🏾[P~M ~L]✍🏾
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the ReadersπŸ“–}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 All PUMITES God bless wuna for me O make wuna last pass corruption O, the Great ONE PMLπŸ™‹πŸ»

Daga baya kuma duk sukayi shuru, Kallon tah yake yanda yaga tayi k'iba tah canza tayi wani fresh sai shek'i take ga gashin tah har wani tsaho ya k'ara dah haushi kamar nah jarirai wannan aikin Ameesha neh dan kuwa kullum bata bari gashin Ummulkhair ya huta kala kalan gyara dah kulawa mayuka iri iri kullum tana cikin yimata applying akai, kinyi kyau yafad'a muryan shi baya fita sosai, kasa magana tayi sabida yanda Abusaiyeed ya lalace, karame tafad'a tareda fashewa dah kuka, janta yayi jikin shi yace, badole bah aidole neh Ummunah babu ke babu labarin ki harna tsawon shekara d'aya har yanzu jinake kamar za akwace minke, rungumar shi tayi tah nutsu tana shak'ar k'amshin perfume d'insa wanda tayi missing kamar ranta, am sorry I wunt do that again tace ahankali, dariya yayi

Please Login or Register in order to submit comment